You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
abin farinciki, yaya asama'u tace duk kuzo nizan fada muku
sunayenku domin kowannenku nasan fuskarsa,
Sosae sukayi mamakin ganin batayi kuskure wurin fadar sunayen suba tazo kan lubna tace
kekuma kanwar maza ke photo copy nace sak dukda bantaba ganinkiba amma nasan sunki kece
lubna,
Dasauri lubna tafada jikinta tana dariya harda hawayen jin dadi tace dama haka dangi suke?
Ranar da qafa suka taka har gidansu badee,
Ummansu ta rungumeta tana kukan farinciki daganan komai yawuce se kallon gidan badee take
komai ya sauya yasha fenti da tile ko ina se kyalli yake kamar gidan wata amarya,
Bari na Dan leqo majid,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un nafada ina ja dabaya ganin mutum yashe akan gado yarame kamar
Wanda tunda aka haifeshi yake asibiti kai kamarma an tonoshi daga rami bayako motsi se ido dake
yawo se wari yake ga jikinsa babu alamar yaji ciwo balle nace ciwon ne sanadin warin,
Inanan ina sharar kwalla Sega hajiya safara'u se kamshi take tashigo dakin,
Yabude bakinsa zeyi magana kawai se jini kamar yana amai kusan sau uku yana attempting yai
magana amma jini dake fita ya hanashi,
Hehehe,waikai baka gajiya da magana ne sokake jinin ka yakare? To zuwa nai namaka wanka
domin warinnan naka yana takurani,
Gani nayi ta saka hand gloves tajanyoshi kasa kafin ta karkatashi ta kwantar dashi kasa tajashi har
tsakar gida tacire zanin gadon tabayar akai shara se kuma tajona tiyo jikin famfo takunna kamar
me wankin mota haka taringa fesamai ruwa numfashinsa nayin samasama,
Kayan jikinsa tacire tabi jikinsa daruwan kafin ta sakamai jallabiya tamaida shi daki bayan tasa
inno me aikin ta tagyara dakin.
Kuka sosae nake majid yazaama abin tausayi kamar bashiba gashinan awulakance😭😭😭
Ya Allah look at us wit idon Rahama ameen.
[8/11, 6:26 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
A birthday isn't complete without wishes.here is mine for a scintillating year ahead,happy
birthday meena parrot.
Page 35
Gidan su badee a cike yake kamar ana wani biki koda na leka yayan gidan ne suduka da jikokai se
murna suke lubna na tsakiyar cousins dinta harda masu aure wayanda suka girmeta se sauran
sa'annin da yayansu wani sanyi takeji a ranta,
Abduljabbar kam idonsa nakan juwairiyya diyar yaya asama'u itama da naga alamar taga saurayi
me kyau daji da gayu daganandai naga yaimata signal sun fita wajen gidan,
Badeee kuwa bacci take irin Wanda harta manta rabonta da shi akan gadon ummansu su Fareeda
ko se gadin ta suke lokaci zuwa lokaci umma ke leqowa kutasheta taci abinci farida tace umma
kibarta harta tashi daga ganin baccin yaimata dadi,yanzuma zuwa tai taga anyi azahar bata tashiba
tasameta azaune tana murmushi su asama'u na mata tsiyar wai tazo sha nono gun umma shine ta
bige da Bacci, miqewa kawai tayi tsaye tace muyi sallah mana yunwa nakeji,
Muryar umma sukajiyo tana cewa yawwa dama kenazo natayar wannan bacci haka kuma bakici
abinci ba sunhana natashe ki,
Ai umma yanzu natashi sallah zamuyi muci abinci,
Bayan sungama cin abinci suka hallara a palon alhaji yakara bawa badee hakuri sosae daga nan
tabasu lbrn rayuwar da sukayi,
Se palon yakoma kamar gidan mutuwa sbd kowa kuka yake se alhaji kadai dayake kallonsu yana
murmushi ganin yadda suka rungume juna suna kuka,
To kuyi shiru haka tausayin ya isa tunda gasunan da rai da lpy,
Abduljabbar yace Dan Tsoho don Allah naga amaryar ka kuma ta kwanta min arai ko zaka bani?,
Juwairiya datasan ita yake nufi dagudu ta fita daga palon suka bita da kallo suna dariya,
Abdulrahim ya harareshi yace waikai meyasa bakada kunya ne shikenan daga ganin yarinya,
Badee tace baruwanka kabar min y'ay'ana aini abin farin cikina ne wannan hadin zan hada kuma
zeyi kyau,
Yaya mukhtar yai murmushi yace kai abdulrahim dawonan kusa daani inma kanada wacce kakeso
ka fadamin ko yar sarkin garin nan ce se inda karfina yakare,
Yana Sosa keya yace dama kanwar mijin lubna ce,
Dukansu suka maida dubansu ga lubna data zaro ido tana dafe kirji,
Yaya asama'u tace yaushe kuka aurar min da y'a ban saniba?,
Lubna tace bafa gaskiya ya fadaba,
Badee tace amma dai kinsan nasan soyayya kuke keda Mus'ab ko?,
Dagudu tafita tana cewa kai mama nidai bance haka ba,
Farida tace to ni wa kuka barmin duk kun kwashe y'ay'an,
Kamar hadin baki abdulkadir da Abdul'aziz suka karasa kusa da ita suna cewa gani mama,
Dariya tayi tace kinga nasamu twins dina ko?,
Alhaji yace to Ku tashi kubani wuri inhuta,
Lubna tana daki zaune itada juwairiyya,laila diyar farida,da jalila kusan dukansu sa'anni ne se
rahama dake gefe tana fama da tsohon ciki haihuwa tabiyu kenan zatayi wayar lubna tayi kara
tana dubawa taga Mus'ab ne dasauri ta daga,
Baban baby ya akayi?,
Tambaya ta ma kike yau tunda kin hadu da en uwanki shikenan kin manta da miji kuma,
Ni na isa in manta da Rabin raina?kana raina kawai dai tundazu muna tare ne kasan dole hankalina
yadauku kayi hakuri kaji habibi,
Rahama tadan tabo lubna,to rasa kunya seki bawa kanki excuse ko kifita can waje in kinga dama
ma daga soyayyar seki soye,
Miqewa kawai tayi tana cewa sory sister's,
Daganan kuma suka sha soyayya,
Atakaice dai ranar cikin nishadi suka wuni,
Bayan kwanaki su Abdul suka fara fita aiki yayinda abdulkadir yake final year dinsa shi kuma
Abdul'aziz yafara zuwa har sun fara karatu sedai fatan Allah yabasu sa'a,
Badee taji damuwarta ta ragu sosae sedai bayan lafawar komai hankalinta yakoma gun mijinta
sotake kawai ta ganshi ko hankalinta ze kwanta tanaji a jikinta kamar yana cikin wani hali,
Wannan karon kuka nake kamar anmin mutuwa Dan ganin majid a tsakar gida kwance duk yafita
hayyacinsa sakamakon safara'u data janyoshi tsakar gida zatayi mai wanka yanda ta saba Sega
waya ankirata a gaggauce tafita tabarshinan tana cewa jirani zandawo kuma rufe gd zan Dan inno
batann,
Anan tabarshi tun ba rana har tazo ta cimmasa nan gashi ko motsi be iyayi se magana yake jini na
fita a bakinsa,
Nalura duk lkcn dayake son yin magana sejini yaringa fita abakinsa hakan nanufin anrufe masa
bakin ne,
Saurarar sa nayi naji meyake cewa se jinayi yana cewa badi'a,
Akace ko karema yanada rana balle mutum kuma komai Nada lkc yadda komai yake da farko
haka yake da karshe yau ina badeen dayake hanawa abinci?yau ina badeen dayake tauyewa haqqi?
ina badeen dayabari da Sha'awa bayan yariga yasaba mata da yanayinsa idan bame hakuri bace da
tsoron Allah dayanzu ta afkawa halaka,
Wannan tunanin yake yana kuka sosae yana haka Sega safara'u ta dawo haka tawankesa
awulakance tajashi tamaidashi daki Sega ta da tarin takardu,
Kai inkana son samun salama ka saka hannu kan wannan takardun karka damu darashin aikin
hannunka indai signing zaka mun hannun zeyi aiki,
Kallon papern yayi taga ta gidansace dake sama road gidan daya Dade da ginawa abdulrahim
lumshe idonsa kawai yayi baze taba signing wannan ba yafi bukatar mutuwarsa akan hakan,
Kanta ta dafe kusan sati daya kenan yaki signing dinsu dole takoma gun malam,
Ga mahaifiyarta ba lafiya batamasan metakeyi ba batasan wake kantaba
Mayafinta taja tabar gidan gaba daya,
Duk yadda tayi damajid abin yacitura gashi yanzu taji Sha'awa ta addabeta mijinta baze iyayin
komai ba,wani alhaji takira kafin ta tattara majid takai shi dakin megadi daga shi se tabarma,
Akace kowa yabar gida gida yabarshi to hakane a gurin sa yabar dangi da iyayensa suma
sunbarshi babu menemansa balle yasan halin dayake ciki.
Asia m inuwa sefa kunyi hakuri da lazy writer momma na CE ta shagwaba ni kuma kar kibari
tajiki kina cemin lazy Dan bataso atakuramin 😉
Meena parrot nayi late ko?sory baby.
[8/12, 11:56 AM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 36
Kuka yakeso yayi irin dakarfinnan kozeji sanyi amma gani yake idan yayi jininsa ze qare,ahankali
hawaye ke sauka daga idonshi addua yake azuci Allah yakawomai dauki,(ina sharar kwalla nima
nace ameen😭),
Zuwa yanzu kam badee takasa jurewa bacci ma gagarar ta yake idan tatuna da majid tadora duka
laifin akanta meye nata nabaro gdnma tabaroshi da matarda batada imani kokadan a zuciyarta
itakam komawa gidanta zatayi koba komai idan tana ganinsa hankalita ze kwanta dama ba korarta
yaiba,
Miqewa tai tadauro alwala tayi nafila raka'a biyu da addu'o'i kamar yadda ta saba inta kasa bacci,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,lubna tafada tana zabura dasauri badee tazo kusa da ita,ke
menene?,
Mama mafarkin baba nai wai ya rasu,sosae gaban badee yake dokawa tadaure tace kwanta
kicigaba da baccin ki,
Mama muje mudubashi,kikwanta nace bakisan dare bane idan gari ya waye zamuje,
Dakyar ta samu lubna tai bacci washe gari tunda sassafe lubna ruwa kawai tadafa wai asha tea fita
zasuyi,
Ke ina zaku tunda sassafe dazakibamu tea kawai kintaba ganin munsha tea?inji abdulrahim,
Ai hardaku zamu baba zamuje dubowa,
Babu inda zamu harku ma yana gama fadar haka yashiga daki inda mama Da hajiya,
Eh shi zamuje dubawa tunda shima mutun ne dazakazo ka tsaya min akai kana tambaya ta sekace
ubana idan kai bazaka ba bazance dole sekaje ba amma nida lubna zamuje Dan naga alamar
kanwar ka tafika hankali sbd tasan darajar ubanta,
Guri yasamu yazauna ganin yadda tadau zafi, mama bawai bansan darajar sa bane abinda yaimana
ne bangama hucewa ba kuma banaso muje Wannan matar tasa ta cutar damu don Allah kiyi
hakuri,
Shikenan mu mun tafi tafada tana miqewa tsaye, zanbiku nima inji hajiya,
A a yizamanki keda kefama da ciwon kafa kizauna aiba jimawa zamuyiba,
Su abdulrahim suka hau mashin lubna kuma suka tsaya jiran adaidaita bayan sun samu sunatafe
wayarta tafara ringing baban baby tagani,bayan sun gaisa yace kina inane naji kamar iska da karar
ababen hawa,
Eh muna kan hanya nida mama zamuje can gidanmu dubo baba,bani address din gidan mana
nakwana biyu ban ganki ba ga baby tana kuka wai se mama take kiramin,kwatancen gidan taimasa
kafin suyi sallama,
Wai nikam wannan bawa akwai kazanta kuji yadda wari ya baibaye gate din nan daka doso kamar
ka amaye hanjinka,tab..bari na wankeshi tun ba ayi zaton gawa na ajiye ba.injiw safara'u data
dawo daga gantalinta,
Anan tajanyo shi kan tarbarma ta jona tiyo tafara shekamai ruwan,
Su badee kam suna zuwa ba wata wata suka shigo gidan dukansu mutuwar tsaye sukayi suna
kallon safara'u dake ta sheqawa bawan Allah ruwa hankali kwance,
Lubna data gano baban sune awulakance haka tai kukan kura ta shaqo wuyan safara'u takaita kasa
dakyar abdulrahim ya bambare ta zuwa lokacin har tasoma fitar mata da jini ita kanta lubna tsabar
bala'i da safara'u ta shuka a gidan hankalinta ya bar jikinta seda Abdul'aziz yafita gate da ita
sekuka take,
Badee kam kan mijin tai tadagoshi batadamu da kazantar dake jikinsa ba,
Majid don Allah katashi ka yimin magana me matar nan tai maka?duk acikin kuka take maganar,
Abdul kukaimin shi cikin gida,abdulrahim yadorashi akafada yawuce dashi toilet din tsakar gida
yakai shi kafin yashiga dakin safara'u yadauko sabulu da soso yakawo wa badee,
Ka dauko min kayanshi kaduba adakinta da sauri yakoma dakin yadauko kayan gasunan ajere
amma ambarshi cikin muguwar jallabiya,
Sunanta yake kira ahankali jini nafita bakinsa dasauri tarufe mai baki kayi shiru kar jininka
yakare,
Sosae ta wankesa ta saka masa kayan abdulrahim yadauko yadawo dashi harabar gidan karkashin
bishiya kan tabarma,
Mus'ab yakaraso dasauri Yana tambaya meyasa meta,dasauri taja hannun su ta nuna musu wannan
katon dutsen,yaya kudaga shi akwai wani Abu agurin,
Da addua abakinsu suka karasa wurin layune sunfi dozen awurin,Mus'ab yace siyo kalanzir da
ashana mukona,
Haka kuwa sukayi suka kona duka,Abdul'aziz yace muje ciki mana,
Abduljabbar kitchen yashiga yasamo wuka yadawo yahau bishiya yakaryo itace masu kauri
yadawo inda yabar ta abdulqadir ya tsareta se muzurai take,
Yace ke inkina bukatar kanki da lafiya to ki dauke masa wannan wahalar kuma duk inda kikasan
kinsaka wani mugun Abu ciki da wajen gidannan kifada mu toneshi ko wallahi mujibgeki mun
jibgi banza,
Shiru tayi tana kallonsa,
Au ba zakiyi magana ba?
Abdul kuzo mufara aiki inaga seta soma jin maza zata fada,
Dasauri tana kuka tace wallahi zanfada,
Badee kam tanacan rungume da mijinta tana kallon ikon Allah se en kananun hawaye da take,
Rana dubu ta barawo rana daya tak tame kaya.
[8/13, 5:35 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Na sadaukar da wannan shafin ga en gidan Sophie G fatan alkhairi agareku.ILYSM❤
Page 37
Nidai ban binne komai a gidannan ba wallahi ciwo ne Allah ya Daura masa banida sa hannu aci....
Kyakkyawan mari abdulrahim yadauketa dashi yakara mata wani dabayan hannu,
Abduljabbar bani itacen nan inaga sena saka jikin ta yaitsami,batayi auneba taji sun soma rangada
mata itacen,
Abdulrahim banda duka inji badee,
Mama idan kinajin tausayinta ne seki tashi kikoma cikin gida koki fita waje babu Wanda ze
hanamu jibgarta indai bata fada mana gaskiya ba,
Shiru tayi Dan bata taba ganin zuciyarsa irinta yauba,
Azuciyar safara'u kuwa cewa take sedai Ku kasheni bazan fadaba,
Shiru tayi tana kallon su babu alamar zatayi magana,
Aiko suka shiga dukanta kamar ankama barawon daya addabi unguwa,
Zaki fadane kose mun kakkaryaki?
Ganin dagaske suke yasata cewa zan fada wallahi zanfada,akasan zuciyarta tunanin sharadin da
bokansu yabasu take tace shikenan tawa takare,
Nan tashiga nuna musu harseda suka tsorata babu inda bata binne mugun Abu a gidanba layu sunfi
akirga har wani Abu dabasusan meye ba hardasu rayyyayyen maciji dakunama akwanrya aka
Daura wa laya aka binne lkcn da suka hako su daga ramen bayan dakin badee seda suka tsorata
Dan macijin sakunamar ba cewa sukayi b'it,hmm
Aiko majid jiyaye kamar andaukemai katon dutse aka jinsa yake wani sabo hannayensa dakomai
Na jikinsa suka shiga kakkarwa nan take ya sume agurin dasauri majid yaje mota zedauki waya
yakira malam se ganin badee yayi tana bawa baby abinci yana zuwa ta kwadamai harara,
Kabar yarinya ita kadai amota koda nazo tana kuka idan aka sacemin itafa?,
Sory baby bari mugama da wannan matsalar tukunna,
Malam yazo yaduba shi yabashi addua da magani da yardar Allah zedawo daidai,
Ruga gida kadaukomin key din part dina tafada tana kallon Abdul'aziz dasauri yaje yakawo ta
bude dakin zanin gadon kadai tayaye aka kwantar da majid,
Safara'u kuwa dakinta suka turata suka kulle bayan sun karbe wayanta ,
Hajiya tazuba ido har tagaji basu dawoba danhaka tamiqe tarufe gidan tana fitowa ta hadu da
yayan anty asama'u maza su uku abubakar,Ibrahim da muhsin sunzo gaisheda badee,
Ai batanan sunje can gidan haryanzu basu dawoba yanzuma bayansu zanbi,
To hajiya muje mu sauke ki daganan ma semu gaishe ta mubata sako kuma,
Hajiya tunda taga majid take ihun kuka tanawa tsinewa safara'u dakyar aka samu tai shiru nan en
samarin sukayi waje suna bawa su abubakar labarin dukan dasuka yiwa safara'u da abinda suka
gani danma har sun kona da sun nuna musu,
Badee kindawo dakinki kikula da mijinki nikuma zankoma da lubna Dan ban iya zama nikadai har
mijinki yaji sauki ko,
Kunya sosae takama badee tace uhm kawai tana kaida kai,
Lubna kamar tayi kuka tabi hajiya itafa bata taba bacci ba ajikin mamanta ba Dan haka take bakin
cikin bin hajiya tunda suka isa kokallon Mus'ab da baby batyiba tashige gidan tana kumbura fuska
bece komaiba yawuce gida saukinsa daya baby bacci take,
Yo lubna Dan anrabaki da uwarki sekizo kinamin kumbure kumbure?to idan kinyi aure senagani
koda uwarta ki zaki tafi zoki dora mana tuwo,
lubna kuka taringayi da dare tana kiran mama seda abdulrahim ya rarrasheta kafin tayi shiru tayi
bacci,
Majid be farka ba se washe gari tunda ya hada ido da badee yafashe da kuka,
Badee'a don Allah kiyafemin nasan na yimiki babban laifi amma don Allah ki gafartamin gashinan
tun ba aje ko ina ba nagane kuskurena,
Yi tayi kamar bata jishi ba ta kauda kanta tana goge kwalla wani sabon sonsa take jin yana tsarata
kamar taje ta rungumeshi,
Dakyar ya rarrafa ya rungumeta yana bata hakuri dakyar tajuyo,
Yawuce majid bakada lpy ka kwanta ko zaka iya tashi kayi wanka kayi sallah,
Eh yace yanajinjina hakuri da juriya irin na badee ita takama masa yayi wanka tana kakkauda kai,
Badee'a ina y'ay'ana?
Wani kallo tai masa cike da mamaki,
Cikeda gayya tace dama kanada yaya ne?,
Sosae gabansa yafadi azuciyarsa yace kodai bata hakura bane?.
Wayyo Allah na gaji😩
[8/14, 11:51 AM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 38
Badee'a don Allah kiyi hakuri wallahi nima ba asonraina nake muku haka ba duk yadda naso in
kyautata muku se insamu kaina dakasa yin haka,daganan kuma seya sakuka yana kara bata hakuri,
Itafa yasoma bata kunya danhaka ta janye idonta daga nasa tace,
Meye haka kakeyi kamar wani yaro?Dan Allah nidai kabari,ta miqe tana cewa ni Allah ma yasa
yarannan suyi hankalin kawomin kayana da abinci nasomajin yunwa,
Jikinsa ba karfi amma haka yamiqe dasauri bari nasiyo miki masa IET,
A'a bari muka zuwa 10 inbasuzoba zanje dakaina nasiyo kaikam yaushe zaka iya fita aiseka fadi
ahanya,
Rufe bakinta keda wuya sukajiyo sallamar yaran a palon badee suka tsaya Sega su sunfi to dasauri
lubna taje gun mamanta,
Mama ina kwana?kina lafiya? Babu abinda ke damunki dai ko?,
Badee kam kallonta kawai take yadda idonta suka kumbura daga ganin ta kuka tayi,
Majid idonsa suka cika da kwalla,Allah sarki dayanzu yayansa sunyo kansa amma ji karamar ma
kota kansa batayi ba lafiyar mamanta kawai take tambaya,
Bazaku gaisheda babanku bane?,
Kusa dashi suka karasa sunayimasa yajiki,
Ya amsa yana zubar dahawaye durqusawa yai ze nemi ga farar su dasauri suka rigashi,
Baba plssss rungumesu yai yana kuka suma sunayi,
Ihu lubna tasa tafadi kasa tana birgima cikeda tsoro suka juyo suna kallonta kafin badee tace ke
meye haka sekace wata ta goye?,
Mama bakiga sunrufeshi ba Niko ganin sa ma banyi ba,
Mtsww to shine zaki samana ihu haka?inji abduljabbar,
Dakansa yakarasa kusa da ita yadago ta Ku kyale min lubna ta ai gaskiya tafada yakarashe
maganar yana murmushi,
Dukansu sukayi murmushi daganan suka zauna cin abinci,
Shiru babu motsin safara'u badee tace su bude ta ko lafiya shirun yayi yawa kuma abata abinci
itama ai mutun ce kamar su,
Safara'u kam nacan reshe yajuye da mujiya se muzurai take tunda ta tashi daga bacci takasa koda
motsa Dan yatsanta ne kuka kawai take tana Dana sanin biyewa mahaifiyarta datayi yanzu gashi
bataga lpyrta kuma bataga dukiyarda tazo ci Dan sun karbe komai har kudin dake account dinta
sun tursasata tatura su account din majid domin dama ba nata bane,
Sosae badee'a ta tausaya mata majid yace sukira bakanike ya duba lafiyar motocinsa zasu maida
safara'u kware inda mahaifiyarta,
Haka kuwa akayi dukda badee bataso tafiyarba amma babu yadda zatayi haka suka hada kayan
safara suka miqata kware babanta yai kuka kamar ransa ze fita dakyar suka rarrasheshi dganan
majid yabawa safara'u takardar ta saki biyu babanta yace kayimin daidai Dan haka ke Hajiya
tunda kindan samu sauki seki cigaba da girban abinda kika shuka gashinan tun ba aje ko ina ba
kinfara gani dama Na fadamiki inasane daduk abinda kuke kuma Allah baze kyalekuba koda
dabba kika cutar balle Dan Adam rai yakai hamsin Wanda kika saka cikin mawuyacin hali saboda
biyan bukatarku ta banza,hmm
Daganan suka dawo sokoto gidansu badee suka fara zuwa majid yanemi ga farar su suka yafe mai
suka karayimai nasiha sosae yai godia,
Umma tace badee'a zo inason magana dake,
Ke kina ganin babu matsala ko?banason abinda zekara cutar min dake,
Umma babu wata matsala kibari idan hankali ya kwanta zanbaki labari yadda zakifi gamsuwa,
To shikenan Allah yayi muku albarka,
Ameen,
Part din safara'u majid yasa aka kwashe mata kayanta kaf aka tura mata kware,
Part dinsa suka koma yasa aka gyara gidan yai kyau,yaje dasu Abdul kasuwa suka ga shagunan
kasancewar baya nan yasa shagon duk arufe yaran sa sungaji sun rufe sun gudu da Dan cinikin
dasu kayi,
Office ma yaje yai reporting abinda yafaru kuma yana bukatar Hutu yakara warwarewa,
Wai!duniya sabuwa Dan har hajiya aka dauko ta dawo gidan danta da zama lubna ko da dakinta
kullum zatayi bacci setayi kuka wai an rabata da mamanta,
En uwan badee da yayansu wuni guda suka yiwa badee agidanta abinci har seda suka gaji
daganinsa lubna Dan ba'asaba ba taci abinci har babu iyaka ranar seda taikiba ta musamman,
Badee tafito daga wanka sotake ta kwanta tahuta tasha yawo har tagaji,
Tana tsaye gaban mirror taji an rungumeta,majid mai zan shafa fa,
Bana bukatar jikin ki da mai,yahade bakinsu,dasauri tazare bakinta tace,
Lahhh meye haka sekace yaro?
Nafi Abdulrahim jin luv da kuruciya daganan sukayi gado,
Ai a 200 nabaro dakin ina dafe kirji wannan luv haka sekace meela da adeel😉
[8/15, 12:58 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 39
Bayan awa uku nadan leqa don in gani ko akwai wani rahoto dazan dauko,lahaula wata sabuwar
soyayyar dagani yasa nayiwa kaina kiyamullaili nabar gidan gaba daya sedai zuwa gobe daidai
komai ya lafa😉
Washe gari seda nai wanka nai sallahn asuba ko kwalliya ban tsaya yiba nakama hanyar domin da
kafa zani babu kudin adaidaita kuma nakafe kai dafata sena dauko muku rahotonnan saboda
nacika alkawarin Dana dauka,
Bansamu isaba se karfe takwas harda rabi,
Majid kasa ke ni mana intashi kofa sallah bamuyi ba kalli yadda rana tafito,
Dasauri yamiqe zaune yana murtsike ido,
Subhuhanallahi Ashe munmakara haka ya'akayi,
Ka tambayeni ya akayi bayan Kaine ka hanamu bacci,
Munacin lokaci tashi muyi wanka,
Kadaiyi ninayi dakina,tattara kayanta tayi tabar masa dakin sefaman murmushi yake seyaimin
kamar wani ango,
Zaune tasami lubna fuska shabe shabe da hawaye,
Ke meye haka kika zauna kina kuka?,
Bake bace kinsan bamu kwana tareba kuma baki fito ba seyanzu kuma ni inaso inganki,se wani
sabon kuka,
Waike yaushe kika lalace da wannan shagwabar?inace aure zakiyi?shikenan kuma sekice danmun
saba kwana tare yanzu bazaki kwana ba seda ni?kinada aiki ja agaban ki maza tashi kiyi shara da
moping,
Tashi tayi tana turo baki tafice daga dakin ta share ko ina har tazo dakin badee ta sameta zaune kan
sallaya,
Zama tayi tana jiranta harta shafa adduarta,
Mama wai sallar me kikayi yanzu?
Kingama shara da moping din?,a'a nadaiyi shara nan dakin zanshare senayi moping,
Shine kika zauna tambayar abinda be shafeki ba?to ki tabbatar kafin nagama hada breakfast kin
kammala shara Da moping,
Hmm,kawai tace tacigaba da aikinta,
Tana zaune adakin badee tana game awaya Sega kiran Mus'ab,
Ummm uhm uhm nikam na shiga uku kabar sona tafada tana kukan shagwaba,
Kekam yaushe kika sangarce haka komai shagwaba?,bakaibane kusan awa ukufa yanzu baka
kiraniba,hmm yi hakuri nidai yanzu baba na nan zanzo ingaisheshi ne,
Eh yananan befara fitaba tukun,OK to gani nan zuwa,
Majid anzama baba yazauna shida Mus'ab se labari suke ya yaba da hankalinsa sosae kuma
yaimasa godiya akan taimakon daya yiwa su badee,
Babu komai baba ai yiwa Kaine dama nazo ne neman izinin zuwa gurin lubna kafin naturo
magabata na ayi magana tunda naga insha Allah komai ya daidaita,
Babu komai Mus'ab insha Allah zaka iya cigaba Dazuwa,
Sosae yayi godiya kafin yaimasa sallama yafito a harabr gidan suka sha hirar soyayyar su kafin
yawuce,
Bayan sati biyu Mus'ab yaje gidan yayan mamansa dakuma kanin babansa Wanda yaje babu
Wanda be zubda kwalla ba acikin su sbd watsi dasu kayi da zumunci suka ringa Neman gafarar sa
yafada musu cewar dama za aje nema masa aure ne ranar asabar me zuwa iyayenta suka bashi
yaturo,
Ranar Saturday akayi magana kuma an bawa Mus'ab lubna,majid sukaje gurin iyayen juwairiyya
nemawa Abduljabbar aurenta sekuma safnar abdulrahim wacce bansan lokacin da suka dinke ba
seganin majid nayi da sauran mutane sunje gidan dayamma alhmdllh komai yatafi yadda akeso
sedai majid yace se ayi hakuri da auren se bayan sundawo aikin hajji shida iyalansa,
Ai lubna dataji labari dagudu taje ta rungume babanta tana murna wani sanyi majid yake ji
azuciyarsa yace wai dama Ashe haka yaya suke jiyake kamar ya hadiye su,
Baby kinji baba wai sekunje hajji kindawo nifa nagaji na matsu wallahi senan da wata uku fa,
Kadaina kirana dasunan yata kuma bangane ka gaji ba ka matsu dame?,
Naganki matsayin matata mana bakisan yadda nakeji bane idan nace inason ki sosae senaji
kalaman sunyi kadan,
Uhm kayi hakuri kaji Dan samari kamar gobe ne insha Allah,
To Allah yakaimu lokacin da rai da lafiya,anjima zan kawo miki baba Dan safna zataje gidan
kawu kwana biyu kafin ta dawo,
Aikam dai wallahi nayi kewarta ina zuba ido,
To shikenan en mata na se anjima.
Soyayya ruwance inkasha sekaba masoyi nima nasha naba nawa masoyin😉
Kamar yadda meenar parrot kebawa masoyinta abdul😜
[8/16, 11:57 AM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Ameera IbrahimY'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Ameera Ibrahim wannan shafin nakine dalilin kyautar dakika min jiya har mafarkinnayi nasiya
miki mota😎 Allah yabar soda kauna ameen.
Page 40
Alhamdulillah su lubna andawo daga makka se shirin biki ake domin saura sati biyu adaura aure
majid bakin nan yaki ruhuwa ze aurar da yayansa su uku sejinknsa yake daban kamar ba shiba,
Hello ramla banason wulakanci tun dazu nake kiranki kinki dauka,
Dalla kirabu dani da abinda yake damuna dama yau nake da niyyar zuwa hargida infada miki
salim ya takura seda aka matso da date din bikinmu kusa bayan tafiyarku jibi za afara bikin ga
ankonki nan nasiyo miki shi zanzo nakawo miki bansan kozaki samu zuwaba tunda kema ankusa
bikinki,kawai seta fashe da kuka,
Ke kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa bari gani nan zuwa gidannaku kuma biki aidole
dani za'ayi koda kuwa ankaini yaune akafara bikin washe gari senazo bare ma akwai sati daya a
tsakani,
Ajiyar zuciya ramla tasauke,to shikenan amaryar Mus'ab sekinzo,
Yawwa matar salim,
Ranar Saturday saura sati daya bikin su lubna kuma aranar aka miqawa salim matar sa ramla sedai
fatan asha amarci lafiya,
Majid dakansa yatura abduljabbar kware yakai wa goggonsu invitation arabawa dangi Dan hajiya
tayi rantsuwa lubna bazata kuma fitaba se an fara biki,
Takowane bangare se shirye shirye ake safna ma se gyara ake sha juwairiyya yaya asama'u tace ta
tattaro tadawo inda lubna susha gyaran tare dakyar ta samu tazo wai ita kunyar badee takeji koda
tazoma tana dakin lubna babu abinda ke fitar da ita idan badee tazo kawo wani Dan abin gyara da
gudu take shigewa toilet sbd kunya yauma suna zaune da sassafe badee ta shigo da Dan hadinta a
kofuna da sauri riyya
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500