You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
story 2017
Idan nabaku wannan shafin banyi laifi ba haka kawai na tuna da abubuwa dayawa nasan kuma
zaku tuna kuma zaku gane me nake nufi,Ummeejay,Ummeekay,zeenasir,bellzahra,husaena
ubandiya(in-law),ummi rilwan(matar big bro),Sha'awa,dizuwa and fatima (matar nu'aym)pls let's
reunite😍😭.
Page 30
Na dade inajiran wannan ranar,ranar dazaku zo kuna kukan rashin er uwarku nayi tunanin kunada
hankali sena iske sabanin haka,
Tajuya kallonta gun alhaji,
Alhaji badee'a er kace kanada damar yanke mata hukunci akan kowane laifi amma wannan yayi
tsauri,kayan ke mata hukuncin rabata da duka en uwanta batareda kayi tunanin wane hali ni
uwarta zan shiga ba fiye da shekara ashirin bansata a idona ba kuma nayi shiru ban maka zancen
ba kaima ka yimin shiru,
Asama'u kekikafi kowa shaquwa da Badee amma wannan karon kika rufe idonki kika watsar da
ita kukan me kikeyi yanzu?,
Farida kekika yiwa badee rashin mutunci harkikeda bakin zuwa kina fada to yanzu bakin cikin me
kike?,
Dukanku kunada aure kuma kunason mazajenku meyasa kuke so ita tabaro mijinta awaccen
lokacin anya kuwa kunsan darajar soyayya?kukasan metake angowa idan tarabuda mijinta? Babu
wani yanayi na rayuwar duniya dayaze dawwama farinciki ne kokuma sabanin haka,kunsan zafin
haihuwa kunsan zafin rabuwa da yayaye to akan me zakuga laifinta Dan taki baro yayanta tabiyo
ku?gunwa kukeso tabaro su hajiyar Abdul wacce batabawa dancikinta tarbiya mekyauba balle Dan
wani?,
To daga yau kar Wanda yasake kulani acikin Ku harse kunganomin yata kuma Ku tabbatar da tana
cikin yanayi me kyau harkai alhaji domin Kaine silar komai dakaida mukhtar da tsoron cikin ta
tazo amma ya kwada mata mari yakoreta itada gidan ubanta,
Daki tashige tabar su jiki amace Shiru sukayi suna hango girman laifinsu gashi uwarsu tayi fushi
dasu ahaka suka bar gidan,alhaji ma yadade jikinsa asanyaye matar sa bata taba daga muryarta
akansa ba segashi yau tana fada masa magana kanta a tsaye dole yatafi Neman yarsa me cike da
hakuri da kawaici,
mukhtar ma dayaji labarin abinda ummansu tace hankalinsa yatashi yayi yawon gidan majid har
yagaji amma bayasamunsa a gida,a haka suka shafe sati biyu babu wani labari,
Bayan sallah la'asar lubna tafito domin siyan kayan Dinki sedai me shagon dake layinsu baya nan
danhaka ta karasa layin dake gaba dasu kadan kamar ranar dazasuzo taga shagon da ake siyarda
kayan dinki,
Tundaga nesa alhaji ya hango ta yana tsaye a kofar gidan abin duniya ya isheshi sosae yake
kallonta wallahi wannan yarinyar kamarta da asama'u ta shahara badan asama'u tazama babbar
maceba babu abinda zehana shi cewa itace kuma yayan asama'u babu wacce takamo hanyar
haskefatar wannan yarinyar, koda yawo daga tunani beganta ba,to kodai aljanace?
A a wannan mutunce yaba kanshi amsa, tabar ma yashimfida ko Allah zesa tasake biyowa,
Lubna data siyo abinda zata siyo takamo hanyar komawa gida seji tayi an rungumeta
tabaya,dasauri tajuya cikeda tsoro waye Wannan,
Ramla kawarta tagani batasan lokacin datace,wayyo dadi kashe ni ramla yaushe kuka dawo?
Aimunjima da dawowa naje gidanku akace kuntashi daga nan ina kuka koma ne?
Wancen Layin nasama,
Gidan hajiyarku kenan?kicema muna kusa muma nan muka dawo sedai mu daga farkon layin
muke,
Dadi yakama lubna bakinta yaki ruhuwa se ganin sukayi mota ta tsaya gefen su,
Ahh yaya Mus'ab daga ina haka?,
Daga gida mana ga gidanmu can,yaimata nuni dawani gida mekyau irin gidan masuji da naira,
Allah sarki,
Mekikazo yi anan?,
Kayan Dinki nazo siya sekuma na hadu da kawata muka bige da hira,
OK muje nasaukeki gida dama inaso naga jikin mama,
Aitaji sauki sosae,Baku gaisa da kwataba sunanta ramla,
Gaisawa sukayi kafin su shiga motar ramla suka fara kaiwa gida kafin sukarasa gidansu lubna,
Har cikin gidan takaishi yagaisa da sumama da hajiya yadan zauna kafin yai musu sallama lubna
tarako shi dama tanaso ta tambayeshi,
Ina fatan mahaifiyar baby ta dawo?,
Bata dawoba na buga dambu taliya taki dawowa so nakarbi wannan kaddarar ahaka akayi suna
bawani taro yanzu ina fafutukar Neman me reno nakasa samu,
Subhuhanallahi tace sekuma tayi shiru kafin tayi saurin juyawa cikin gida tana fadin ina zuwa,
Paper ta samu da Biro takawomai,
Samun numbernka anjima zan kiraka yanzu inada aiki akaina kuma gobe nakeso nagama idan
yaya yadawo zan ari wayarsa nakiraka,
Murmushin jin dadi yayi asaukake yasamu yadda zekusanto kansa da ita, rubuta mata yayi kafin
yamata sallama,
Tana Dinki tanabawa mamanta da abdulrahim labarin Mus'ab seda takai gun datake son fada musu
buqatarta ta ajiye dinkin ta fuskance su,
Mama na fada miki duk Wanda yakeso yaga bacin raina yatabaki zannunamasa halina koshi
wanene haka kuma duk Wanda ya farantamiki nikuma da izinin Allah sena taimakeshi sedai in
abin yafi karfina,sosae nake tausayawa bawan Allahn nan matar sa tabar mai jin jira kutaima
kubani izinin zuwa tun safe zuwa yamma nai masa renon yarinyar nan don Allah,
Ajiyar zuciya abdulrahim yasauke yace,lubna bawai naki ta taki bane domin yana bukatar
taimakon sedai kisani ke macece bekamata abarki asakeba kullum kina hanya and haka kawai
bakomai a tsakaninku bazamu barki kije gidansa ki zauna ba dama dai ace zeringa kawo yarinyar
ne da bazamuki ba,
Yaya mahaifiyarsa da kanwarsa nanan fa kuma sunada me aiki sedai abubuwa sun mata yawa
kuma idan kalura shikanshi damuwa ta lullubeshi,
Akwai haka kuma seki tambayeshi idan ya yadda,
Yawwa yaya nagode sosae Allah yataimake mu,
Ameen kawai yace yana fita daga dakin,
Wai mutuminnan kodai sonki yake lubna?inji badee,
Lahhh mama rufani kisayani,kedaganin wannan mutumin kinsan yafi karfi na kawai dai yanada
kirki ne,
Badeee kallonta kawai take tana murmushi.
Banan yakamata na tsaya ba amma wallahi nagaji😩❤.
[8/5, 2:52 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Anty Sophie yauba y'ay'ana?
Anty Sophie y'ay'ana shiru kwana biyu,
Anty Sophie munajira fa😀
Baby Sophie ina badee?
Baby Sophie muna missing lubna fa
Anty Sophie nifa inajira naga yadda safara'u zatayi da majid.
Duk wacce tasan tace haka to su suka sakani typing yau sbd haka wannan shafin nasune sukadai😍
anty Sophie, baby Sophie nagodiya😘.
Page 31
Tundaga sallamarta yagano itace domin sosae muryarta sosae take San yaya zuciyarsa amsawa
yayi yana gyara zamansa bayan sun gaisa tace,
Am yaya majid dama nace zancen wacce zatayi renon baby ne shine nace idan ba asamu ba kuma
babu damuwa insha Allah zanyi,
Jin zancen yayi daga sama Dan haka yayi saurin miqewa yana cewa gani nan zuwa,
A'a tsaya mana yanzu dare yayi amma idan ka amince gobe ma zan fara zuwa kuma bawai zaka
biyani bane kawai zanyi ne saboda Allah sanadin taimakon dakayimin nida mahaifiyata,
Wani dadi yakeji sosae magana ma kasa yi yayi sedai jitayi kawai yace alhmdllh,
Yaya kayi shiru ko akwai Matsala ne?,
Dasauri yace A'a wallahi babu komai na gode sosae gobe dakai na zanzo nadaukeki,
To Allah yakaimu amma baka fadamin sunan y'ar tawaba,
Murmushi me sauti yayi yace sunanta Fatima amma dai ninafi kiranta da baby,
To Allah yaraya mana baby Fatima ameen yace kafin sukayi sallama,
Dagudu takoma dakin su tasamu badee nagoge mata kayan da tadinka dazu dama haka suke sesun
goge Dan dinkin zefi kwanta wa yayi kyau,
Mama yaya Mus'ab ya yadda kuma yace dakansa zezo yadauke ni sedai mama zaki bimu kiga
gidan?
Meyakaini ni badeeyatu Allah dai ya kiyaye insha Allah baze cutar dake ba,
Mama don Allah kibini muje kiga gdn zakuma gaisa da mamansa kinji,
Ganin ta marairaice fuska yasa badee tace to shikenan amma bazan zauna ba dawowa zanyi,
aidama mama bazaki zauna ba,
To Allah yakaimu lubna se kije ki karasawa indo dinkin ta Dan yanzu dinkin zesami gibi tunda
bakya zama,
Wallahi kuwa mama ai hannu yarage kawai nasa se zip gara na kashe darennan nadinka mata
kayanta naji anacewa batada mutunci kar tazo tayimin RM(inji anty badee) wallahi na gurji bakin
yarinya,
Bazama tayi miki ba Dan naga alamar ke Sam bakya gudun fitina,
Shiru tayi tana cigaba da dinkinta,
Washe gari karfe 8:15 am a gidan tayiwa majid sbd zumudi ganinma yayi Daren yai masa tsayi
har cikin gidan yashiga shi dai yana jinjina tsaftar su,
Yaya nace zamuje da mamana su gaisa ta hajiyarka kuma zataga gidan,
Babu damuwa yace yana murmushi,
Ta kofar gidan su badee aka bi kasancewar layinsu daya sedai akwai Dan nisa a tsakanin gdnsu
Dana su Mus'ab,
Sosae badee ta kurawa kofar gidan ido Sega alhaji yafito yana shimfida tabarma, sosae take kallon
sa yananan yadda yake sedai alamun tsufa ya bayyana sosae ajikin sa ai dole ya kwana biyu,
Alhaji kuma zaman cikin gidan baya masa dadi Dan ummansu badee bata wani kula shi iyakacinta
da shi gaisuwa se gabatar masa da abinci ko magana yaimata a daqile take amsa shi abin
yadameshi yarasa hanyar samun badee se addua yake,
Tunda suka shiga gidan tsikar jikin lubna ke tashi tana jin hankalinta na miqewa daurewa kawai
take har suka shiga palon gidan yai musu iso dakin hajiya,
Dasauri lubna tai baya danji tai kanta ya masifar sarawa,badee tayi saurin kallon ta,
Lubna meye haka?
Mama bazan iya shiga dakin nan ba,
Mus'ab yai saurin dawowa da baya yace,
Meyasa?
Yaya Mus'ab kayi hakuri Ku bincika dakinnan ina Palo inajiranku,
Kallon badee yayi yace,
Mama kokingane me take nufi?
Um...tanada matsalar iskane idan kaga tayi haka to taji a jikinta akwai abinda ya shafi
asiri,tsibbo,da sihiri nagane haka ne tun tana karama hankalinta baya taba kwanciya a wurin ina
baka shawarar kanemo mataimaka aduba dakin nan dagidannan dakyau,
Mutuwar tsaye yayi yana tunani to su Waze musu wani asiri agidn kuma wa suka tsarewa wani
abu?shi sema yanzu yake tuno abubuwa da dama,
Mama bari nakira larai tadawo da hajiya Palo zan dauko safna megadi ya tayani muduba
hankalina yatashi,
Babu matsala tace tana juyawa,
Sunanan zaune Sega larai riqeda hannun hajiya takuma goyo baby dasauri lubna takarasa ta na
karbar baby bayan sun zauna suka shiga gaisawa da hajiya dama tasan da zuwansu,
Kukane ya kwacewa lubna ganin kyakkyawar budurwa akwance komai se an mata babu baki
bakafa balle hannu se idanu kawai tana kallon mutane, Allah sarki batasan hawaba batasan sauka
ba ankwantar da ita haqiqa duk yadda kake ganin rayuwar ka tayi tsanani ka godewa Allah domin
akwai wayanda tasu tafi taka wuya da wahala,
Goya babyn tayi daketa bacci dayake batada rigima kokadan, zuwa tai tana kallon safna taimata
murmushi tace sannunki,gyada mata kai kawai safna tayi tana kura mata ido,
Hajiya tace maman lubna mungode sosae Allah yabiyaki da gidan aljanna Mus'ab yamin bayanin
komai mungode,
Babu komai hajiya muma godiyar mukazo yi,murmushi kawai hajiyar tayi,
Mus'ab yazo da wasu maza su biyu zasu shiga dakin hajiyar lubna tace,
Kufara binciken tun a bakin kofa idan takama har tile din dakin a bambare baruwanku da gado ko
wardrobe naji a jikina wannan abin yajima adakin gadon kuma bazefi shekara biyu ko ukuba,
Ya jinjina wahalar dazasuyi Dan tile din bana yanzu bane sesun sha wahalar daga shi,
Katifar suka soma dagawa suka cire komai najikin gadon basuga alamar komai ba secan idon
Mus'ab ya sauka kan wani tile dabe zauna sosae kamar sauran ba seya tuna lokacin da za adaura
gadon,
Ranka yadade ga wani tile mun gani be zauna sosae ba kuma munfara Daura gadon,
Musbahu tile din akasan gadon yake?
Eh,
To indai kun fara aikin kubarshi kawai baze zama matsala ba tunda akasan gadone,
Dasauri yakarasa ya daga tile din wani kalar Abu yagani kamar randar ruwa er karama bakikirin
ga takarda a jikinta andaura da zare bismillah yayi yadauko tafito palon yana cewa mazn suci
gaba da dubawa,
Kuga abinda naciro yace yana nunawa badee dasauri tamiqe takarba sukayi waje Dan tasan idan
lubna ta gani birkicewa zatayi.
Washhh anty Sophie tagaji😰
[8/5, 3:45 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 32
Mus'ab menene Ku fadamin kuna ina tana kokarin tashi larai tayi saurin maidata zaune hajiya ki
zauna suna zuwa kinji babu komai, wannan larai tamusu halacci batada matsala kuma tana tausaya
musu,
Suna zuwa waje badee tai bisimilla hadi da adduar neman tsari daga muggayen aljanu da mutane,
Papern jiki tasoma cirewa ta bude rubutu ne na Hausa anyishi kasa sama dakyar ta iya hada
kalmomin makaranta
Sunan wata tagani arubuce da manyan haruffa ankuma bada yadda za akarya asirin ta hanyar kona
wayannan abubuwan idan wacce akayi wa ta chanja ra'ayinta na kar yawa,
Tana gama karantawa Mus'ab yai saurin zuwa yadauki fetur da ashana suka kona abin seda
yazama toka kafin suka koma cikin gidan,
Muryan Hajiya sukaji Tana cewa innalillahi wa inna ilaihirraji'un larai haske nake gani suna shiga
tana faduwa asume,
Dasauri sukayi kanta badee tace mus'abu kakira wani malamin idan akwai shi nan kusa atake ya
kirashi kasancewar basuda nisa segashi yazo cikin mintuna a shirin,
Addua yai mata sosae sekuma bacci yadauketa yace abarta tahuta kafin yatafi suka bashi lbrn
yadda akayi yajinjina al'amarin sunanan en mazannan biyu suka fito megadi yace,
Alhaji mun matso wardrobe gaba sedai munga alamar anfasa gini dasauri ya dauki hammer suka
shiga dakin daidai wurin yafasa Sega laya guda biyu sun fado,
Dauka yayi da bismillah yafito palo yanuna musu atake malam yace akona a palon yadora kan tile
yasa kero da ashana yakona,
Seji sukayi safna tace maaama😳,
Kuka kawai Mus'ab yasa wato duk wannan wahalar da mahaifiyarsa da kanwarsa keyi fiyeda
shekaru goma Ashe wanine yakunsa musu Ashe haduwarsa da lubna alkhairi ce atake yaji wani
sonta yakaru azuciyarsa,
Juyawa yayi yana kallonta daniyyar yimata murmushi seya ganta a dunkule ko motsi batayi,
dasauri yayi gunta hakan yajanyo hankalin su malam yakoma gunsu,
Badee takarasa tadaga zaune se ganin jini tayi yana fita ta hancinta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
tafurta, batason ganin nose bleeding dinnan Dan yanzu setajiyawa kanta ciwo,
Bayani taiwa malam ganin alamun kansa yakulle ruwa yace abashi a Kofi yai Addis aciki dakansa
ya matse bakin yadura mata ahankali jikinta yafara saki se sauke ajiyar zuciya take,
Alhmdllh bayan kwana biyu lubna na zuwa gidan yanzuma ita kewa baby wanka larai takoya mata
kuma hajiya tadan soma gani ba sosae ba safna ma tafara zama sedai bata jimawa azaunen kuma
bata magana sosae amma duk malam ya basu magani suna sha dakuma addu'o'i majid yarasa inda
ze Dora lubna sbd shukin sonta daya kamashi ga son babyn sa datake sosae take kula da ita yauma
yaji dadi sosae yaga ta dinkawa baby riguna guda biyu sunyi kyau ta gwada mata se surutu take
mata kamar Tana gane me take cewa yarinyar ko se dariya take kwasa,
Adakin hajiya suke zaune suna hira hajiya tana jinjina wannan lamarin,
Lubna tai murmushi tace nifa Momy Sam bana mamakin wannan abin naga abubuwa da dama
arayuwata masu kamada wannan babana yakasance mutum Wanda bayason haihuwa dukda
wadatarda Allah yaimasa ya watsar damu bamusan meye kulawa daga bangaren uba ba muntaso
cikin tagayyarar rayuwa mamanmu itace komai namu se mahaifiyar babanmu dake taimaka mata
daga baya kuma ya auro wata er uwarsa daganan komai yakara lalacewa bin malamai dabokaye
take tanaso ta hallakamu muda babanmu mudai Allah ykaremu sbd munriqeshi kuma mundogara
dashi sedai babanmu tasamu sa'arshi be riqe ibada kamar yadda yariqe Neman kudiba yanada
dukiyar dabesan adadin ta ba akowace kasuwa dake garin nan yanada shaguna akalla biyar ko
shida ana haka yakawomin miji mugun miji Wanda yakasance shedani Na karshe munyi kokarin
ganin hakan bata kasanceba amma abin yacitura se kawai muka hada kayanmu mukabar gidan
yanzu haka muna gidan hajiyarsa kuma har yau betaba zuwa nemanmu ba muma bamu koma
Neman sa ba,
Sosae Momy ta tausaya musu tace yanzu haka kuka baroshi da muguwar mata idan ta kassarashi
fa?
Komai tayimai Momy shiyaso yawulakanta mu fiye da zato bezo nemnanmu ba muna bazamu
nemeshi ba,
Kiyi shiru kawai lubna ke yarinya ce,safna dake gefe tana saurarensu tayi dariya da muryarta slow
slow tace Momy kibarta su sukasan rayuwar dasuka yi dashi, kiyi shiru kema safna bakisan komai
na rayuwa ba,murmushi kawai tayi bata saba magana me tsayiba wannan datayi setaji duk ta gaji,
Ke nifa Momy Allah kadai yasan iya adadin bala'in da matar nan ke kullawa dayanzu kila ta
kassaramu,
Tafada tan dariya suma dariyar sukayi,
Yauma suna zaune a Palo suna hutawa Dan lubna Goya baby tayi sukaje motsa jiki da safna dan
tafara tafiya,
Mus'ab yashigo yabasu wayoyi masu kyau kirar Gioni A1 safna se murna take lubna kam sake
baki tayi ina ita INA Wannan zankadediyar wayar daurewa tayi taimasa godiya tace to aini yaya
bansan yadda zanyi dawayar ba ko kira ban iyayiba,
Zama yai yadan koya mata masu sauki yace takoyawa safna fita zeyi,aiko tasamu abinyi baby
tasha pics ba adadi,
Bari mu leqa majid,
Kwance nasameshi yana ko bayida lpy ne oho,
Safara'u kinsan dai ina bukatarki ko dakinacewa sena baki kudi yanzu kuma kona baki kudin
bakya karba kitaimakeni karna mutu kinsabamun da abinnan karki gujeni yanzu pls,
Kallon uku saura kwata taimasa tace kaikam ka boni da jaraba namiji kullum cikin buqata sekace
doki?kaibaka gajiyane?nikam wallahi nagaji bakada lpynma sekayi jaraba?tobari kaji inada abinyi
yau basussukan danake bi zanje karbowa kuma kila bazan dawo yauba Dan daganan har kebbi da
zamfara zani ban kuma CE ga ranar dazan dawoba sedai kawai kaganni,
Shiru yayi yana kallonta taja mayafinta taita tafiya,
Ahankali hawaye ke zubo masa kila wani bala'i ne ke shirin samun sa sbd jiyake kafafuwnsa duk
sun soma sakewa ga wani nayi da qirjinsa yaimasa,badee ce tazo masa arai dasauri yatashi zaune
sauri sauri yashirya yazari key din mota,
Hanyar gdn hajiya yakama amma ga mamkinsa akasuwa ya gakansa se kawai yasamu wuri yai
parking yadafe kansa da yai masa nauyi da hannayensa.
Nidai INA bayan safara'u yadda takecin uban majid yamin daidai😎
[8/7, 5:31 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to you anty billy❤
Page 33
Mama kiyimana addua Allah yasa ayi nasar samun aikin nan kinsan Dan tsohon governor din
garin nan muna mutunci sosae yanzu da muka gama service yace mukawo takardunmu nida
abduljabbar insha Allah babansa zesama mana aiki,abdulrahim yafada yana murmushi,
Tun yaushe Abdul?shine bansaniba seyau?,
Jiyanefa nabashi nazata abduljabbar ya fada miki,
A a nikam,Allah yatabbatar mana da alkhairi,
Ameen ya amsa yana miqewa,
Bari na dubo lubna lafiya har yanzu bata dawo ba akwai mamaki Dan bata saba kaiwa hakan ba,
Daka kyauta kuwa amma kada kayi mamakin tana tareda majnun dinta ne?
Tsayawa yayi yana cewa,wa kenan?,
Mus'ab mana aini tuni naganosu inata so nafada maka kasata agaba ta fada ma gaskiya amma
bansamu lokaci ba,
Ummm lallai ma lubnar nan nita maida bi can kenan?,nafa tambayeta Dan kar afara surutu tace
min itafa bakomai mutunci kawai suke dashi haka takejinsa kamar ni,
Hmm yanzu kam asiri yatonu seka fadamata ka gano Dan asan abinyi,
Lallai kam yace yana fita,
Dakafa yataka yazo daidai gidansu badee ya hango ta goye da baby da waya akunnenta Mus'ab na
gefenta yayinda safna ke tafiya daga gefe ita kadai,
Ke gani nazo gidanku bakya nan,wai ke bakyajin kunya kinje kin tare a gidansu saurayi?,inji
ramla da wannan shine zuwanta nabiyu gdnsu lubna amma batanan,
Dariya lubna tayi tana kallon Mus'ab da shima ita yake kallo bakin nan kamar me tallar Maclean,
Eh din ai gidanmu ne,meye kike nemana?,
Hajjaju Dinki nakawo miki kuma express ne,
Wazaki kawowa Dinki express?,
Ke dalla banason iskanci gasunan nabarwa mama anjima zan dawo bikin kanwar mijina za ayi
shine seyau yakawomin kayan danya raina ni,
To masifatu naji sekinzo, bata jira ta amsaba ta katse wayar Dan ganin abdulrahim ya iso kusa
dasu,
Bayan sun gaisa da Mus'ab yace wannan kanwar tamu nafito dubawa ganin bata saba kaiwa
warhaka bata dawowa,
Gaskiya kam,wallahi baby ce batajin dadi taki yadda dakowa sekuka take yanzu ma nace don
Allah tatafi da ita har taji sauki,
Aiba komai danan dacan duk dayan....
Juyowa yai jin ana gaidashi safna yagani,
Ahh kanwar mu ansamu sauki kenan harda yawo?,
Murmushi kawai tayi tajuya, shima murmushi yayi yana cewa seku koma ko kar dare yayi tunda
gani ma karasa gidan tare,
To shikenan inji Mus'ab yaiwa lubna sallama yanaji kamar karsu rabu itama haka take ji amma
bayadda za suyi (bansan yaushe wannan luv ya kullu har yakai wannan stage din ba)
Salamu alaikum
Wa'alaikumussalam abdulrahim ya amsa yana kallon tsohonnan dake tsaye idonsa yayi ja sosae
ga hawaye kwance acikin idon sa,
Dan Allah idan babu damuwa zanso kuzo mukarasa gidana inason zanyi magana daku ne don
Allah badon halina ba,
Abdulrahim yakalli Mus'ab dabasu Riga sun tafiba,alama yaimasa dakai subi tsohon,
Har tsakar gida yakaisu amma kowa bakinsa dauke da addua akan tabarma suka zauna,
Na Dade ina ganin wannan tana wucewa tanan sosae jikina kebani ita jini nace amma saboda
girman laifina yasa banida karfin halin tunkararta naimata magana seyau Dana ganku atare nakasa
jure abinda nakeji don Allah Kuyafe min Ku nunamin mahaifiyarku inaso naganta kafin nabar
duniya,
Dukansu baki asake suke kallonsa meye hujjarsa idan sudin jininsa ne amma ita lubna tagane
meyake nufi sedai tayi shiru tanaso taji yafada da bakinsa,
Nasan kanku ya daureko?,
Insha Allah Ku yayan badee'a ne idan banyi kuskureba Kaine abduljabbar ko kuma abdulrahim
saboda kune manya a yayanta wannan kuma naji labari sunanta lubna kece karama acikinsu
naganeki ne saboda tsakanin kama dakike yi da yayar mahaifiyarki asama'u,
Arayuwata bantaba ganin mutun me zurfin ciki ba irin maman mu, Ashe muna kusa da iyayenta
bata taba nuna mana ba Dan tasan zamu iya zuwa,
Dasauri umma ta fito daga daki tana kallonsu karasawa tai kusada lubna tana shafa fuskarta se
hawaye tarasa Na menene na bakincin rasa yarta datayine duk wannan shekarun kokuma na farin
cikin ganin jikokanta ne dakuma jiyo kamshin erta dake kokarin kusantota,
Ganin hawaye afuskar umma yasa bade yin murmushi ta juya tana kallon su Abdul,
Yaya kuganemin wannan tsohuwar wai kuka take,tafada tana murmushi kafin tajuya gun alhaji
tace,
Dan tsoho angona mekake bawa kishiya ta ne datake da hawaye a idonta har yanzu?
Basusan lokacin da dariya ta subuce musu ba, da alama jikar tasu me barkwanci ce,
Abdulrahim yace kunaso mukawo muku itane kokuma zakuje dakanku Ku ganta,
Eh kuje kukawo mana ita inji umma,
Dasauri lubna tace a'a yaya baza ayi haka ba zamu kasan mama Nada ciwon zuciya so zamu bita a
hankaline,
Alhaji mamana ta cemin bazata taba nemankuba indai kuna sonta dolene Ku nemeta dakanku
danhaka inaga Ku fara tura yayyen nata da kannenta su gwada lallashinta I'd an ta sauko dakanta
zatazo da ganku amma fa kunada aiki ja agabanku kunsan ance wanda baya fushi duk ranar dayayi
to saukar sa abune me wahala,
Abdulrahim ya akayi kanwar ka tafika wayo?inji umma,
Tadai fini sanin halin mama ne,
Dariya sukayi suduka kafin suyi musu sallama Dan magriba ta gabato,
Ranar umma kasa bacci tayi saboda murna itada Allah bayan er tsohuwar soyayyar su sukayi
nafila domin nuna godiya da jin dadi ga Allah.
Naso ganin yadda tsofaffi ke soyayya🤣🤣🤣nikadai Dana fadi abin senaji shi bambarakwai
[8/9, 1:30 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Sadaukarwa ga daukacin masoyana fatan alkhairi agareku Allah yabar soda kauna❤
Page 34
Alhmdllh abdulrahim yasamu aiki shida abduljabbar, abdulrahim a federal inland revenue shida
abokinnasa dayai masa hanya abduljabbar kuwa abangaren health ne,(👃🏻najiyo kamshin yarannan
zasu zama young billionaires),
Ranar jumu'a ne da sassafe aka turo masa ta email Abduljabbar se Monday nasa yashigo sunyi
murna kamar zasu zuba ruwa akasa susha se hamdala suke,
Aranar kuma 10:00 am tana zaune itada lubna da baby dake zaune tanata wasanta,
Lubna shikenan kin karbe musu yarinya?nifa banason shishshigi Dan kinga sun sake damu haka
sosae zaki kwaso musu yarinya kwana da kwanaki kinsanfa halin mutane balle ma babu dangin
iya babu na baba,
Mama ki kwantar da hankalinki sunada kirki sosae kuma nifa bani nace zanzo da itaba itace ta
maqale min babanta yace nazo da ita kuma tausayinta nakeji karma dai idan natuna yadda uwarta
ta ajiye ta akasa cikin asibiti ko sau daya batasan dumin jikin uwarta ba,
Um Allah yakyauta bari intashi yau dambu nakeson ci,
Nikuma drinks zansiyo yau baki zanyi kawayena zasu zo tafada tana murmushi kafin tasaka hijab
ta dauki baby,
Ke kam ina kikaga kawayen?,
Sababbi nayi umma idan sunzo zaki gansu,daganan tafice tasiyo su exotic da five alive,
Su mama da hajiya anbaje an zubo dambu dayaji zogale se tururi yake kowa da plate dinsa hajiya
se afawa ake ana yabon dan danonsa,
Badee dai se murmushi take batace komaiba, sallama sukajiyo daga waje hajiya ta amsa tanacewa
kosuwaye sukaraso gamunan,
Da sauri badee tamiqe hawaye cike da idonta tama kasa magana,da sassarfa suka karasa gabanta
sekuma suka zube akasa suna kuka kamar ransu ze fita dakyar asama'u tayi karfin halin riqo
hannunta,
Badee'a bamuda bakin rokon ki amma kisani mun gane kuskuren mu don Allah kiyi hakuri
kitausaya mana,
Farida ta karbe, yaya badee kikarbi tubanmu Dan Allah da darajar umma munyi ta Neman ki
gdnki munje babu adadi amma bakya nan kuma bama ganin mijinki umma tayi fushi samu ko
kallon mu batayi dagamu har alhaji,
Shiru tayi tana hawaye to ita me zatayi da kin amin cewa dasu bayan Allah ne amshi adduarta
wannan abin farincikine agurin ta en uwanta gatanta sun dawo gareta atake taji 70% na damuwarta
yakau,
Jin tayi shiru kusan minti biyar yasa yaya asama'u miqewa tace,nasan abune me wahala kiyafe
mana da wuri amma munbaki lkc kiyi tunani kuma bazamu ga laifin ba domin laifin mu me
girmane,
Ganin sunjuya yasa tayi azamar janyosu ta rungumesu ta saki wani kuka me sauti tana cewa,
Yaya bakuda laifi nice me babban laifi kunnuna minso kunso kufitar dani acikin wahalar rayuwa
Amma so yarufe min ido nayi babban kuskure wahalar Dana sha bansan dame zan kwatantamuku
ba bamusan meye dadin rayuwaba har seda takai ga mun gudu daga gidan,yaya Allah ne ya karbi
addua ta yadawo min daku yadawo min da gatana yaza ayi na butulce masa,
Lubna dake jikin kofa tana kallon su tasulale kasa tana murmushi hawaye na zuba daga idonta
tanajin wani sanyi na ratsata babu abinda yafiye mata ganin farincikin mahaifiyarta,
Badee yaya mukhtar na waje fa tare mukazo,
Ku shigo dashi mana kunbarshi Awaje,
Kai atakaicedai ranar ta shirya da en uwanta suka ringa neman gafararta aka kawo musu abinci da
lemu sukaci se santi suke har yaya mukhtar daya zama magidanci dole yasaki jikinsa amma sosae
yake kallon badee tarame sedan haske datayi dama ita ba fara bace sosae amma ba baka bace,
Su abdulrahim duk sundawo suka iske
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500