ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutumen wani show zekara hadawa bari naje naji dame yazo
yau,




Daga kofa ta tsaya tace malam gani,kikaraso mana keda za ataimaka kin wani tsaya daga kofa,

Kamar ya?wane irin taimako?,

Dallah malama kikaraso jarrabar bata isheki bane da kika tsaya acan kina iyayi,



Ahankali takaraso cikin dakin,dani dakai waye jarababbe?kai naji ma inada jarabbar amma daga
yau nayafe indai ta gefena ne Allah yabani hakuri,

Tnangama fadar haka ta kama hanyar fita daga dakin zuciyarta Na wani irin kuna tayi abinda bata
taba yiba Allah ka gafarta min wato ma nizai taimakawa ko ai wallahi yanzu bakina yabude,



Lokacin dayake kallon fuskarta seyaji kamar yaimata mugun bugu seta dauke wuta, amma tana
juyawa yaji babu abinda yake muradi kamarta,kardai dagaske matarnan tafiya zatayi be ankaraba
yaji ta bude kofar da azama yadamqota yadawo da ita bayaso yaji abinda yakeji idan yakalli
fuskarta dasauri ya kaisu gado bayan yakashe wutar dakin duk iya kokarin ta takwace takasa
shiyasa tabarwa Allah amma bada son ranta ba,



Kuka take harda sheshsheka rabonta dajin haka tun haduwarsu ta biyu wannan mugunta yai mata
kuma se Allah yasaka mata tundai ai daga baya tahakura bata hanashiba shine ze mata wannan
aikin,
Malama seki samu damar tashi kike wani kukan munafurci kamar wata amarya nikitashi kifice tun
bankasa jurar kukan nan naki ba na doddokeki anan gurin,



Zaninta tadaura tasa hijab dinta kafin tamiqe tsaye dole ta jure wannan zafin tasani baze jimaba ze
tafi haihuwa bakwai aiba wasa bane zafin mutuwa kadai yarage taji,



Allah sarki nida nakeda danda yabawa shekara goma baya ni ake duka yanzu kuma akan gaskiyata
nake ko abdulrahim yawuce duka akan wasu kanannan laifuka balle nida nahaifeshi Amma
zankara fada maka Allah yana gani kuma namiqa dukkan lamurana da damuwata agareshi zeyimin
magani kuma seya sakamin nida yayana,

Bata jira jin mezece ba tafita,



Kallonta yake tafiyarta ta chanja dagangan yaimata haka sbd tabarshi shiyake kidansa shiyake
rawar sa kokadan beji tausayinta ba amma fa he's more than satisfied badeee capital A ce, lol



Ruwan zafi sosae tayyi wanka dasu kafin yakai yaranta masu fitsari sukayi tagyara musu
kwanciya,



Kusan makara sukayi yaran ko wanka basu samuba suka tafi makaranta,

Abangaren safara'u kuwa wani dadi taji domin tasamu yin abinda malam yace ba ita take zuwa
mahaifiyarta ke zuwa seta karbo mata mugun abu ,



Wannan karon yace kasan gadonta gefen damijin ke kwanciya anan zata yi rami ta binne laya,



Haka kuwa tayi ta daga katifa tayi yanda yace,murna take seyanda tayi dashi kafin taje kan
yayansa,

Dayamma suna zazzauna ita dayaranta tana yiwa Lubna homework se ga Abdul ya shigo bayan
safara'u tagama zugo shi,



Baby Dan Allah ka karbomin Lubna mana nasan kanada iko akanta kadaici yamin yawa yadda
nakesonka haka nakeson yayanka sedai su ko gaiaheni basayi,
Cikeda kissa take magaanr tana gwadawa ne taga aikinta yayi,
En matan baby kwantar da hankalinki koyanzu kikeson Lubna tadawo gunki zata dawo barikiga
ina Zuwa,



Malama hadomin kayan Lubna zata zauna hannun safara'u zaman kadaici yai mata yawa,



Tasani sarai Lubna bazata taba yadda ba setace,gatanan mana idan tayarda nimeye nawa aciki
ammafa seka tambayeta idan bataso bazaka takurata ba,

Sosae yaji haushi, ai umurni ne Dan haka baseda yaddar taba,

Lubana najin haka takoma jikin uwarta, mama kice yakyaleni nafison muringa kwana dake bazan
bi waccenba tayi nuni da kofar dakin safara'u,



Tana kuka yana janta tana tirjewa dayaga tacika taurinkai seya fara dukanta kamar wata babba ita
kanta ta tsorata dole tahakura tabishi itadai maman kallonsa kawai take,



Tananan zaune segashi yashigo yana huci kamar wani zaki,

Zaki hadomin kaynne kokema se kinji bugu,kinmaida yarinya bata jin magana har ubanta yace
tayi Abu takiyi wallahi .zakija Na illatata,



Shiru yai ganin tamikomai jakar kayan yakarba yawuce azuciyarta tace lallai maza azzalumai ne
betaba sanin shi ubnta bane seyau, nasan dole zata dawo indai Lubna ce,



To ensamari kuzo kubiya karatu kuka tsaya cirko cirko kuna kallona,



Abangaren safara'u kuwa tsalle take tana murna lallai abin indai hakane cikin kankanin lkc zata
tarwatsa gidan dama ta tsani lubnar nan me ido kamar an soya wake,

Lubna kuwa akasan tile daya jefar da ita anan ta gama kukanta bacci ya sureta sukayi gabas😂
Kuyi hakuri u know fiyya is always lazy🙈
[7/13, 4:33 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG

A very heart touching story 2017.



This page goes to all the active members of taskar billy galadanchi #one love❤ you made my
day😂😂.



Page 17



Ni yarinyar nan bansan halin wa tayo ba shegen taurin kai , haryanzu fadan be gadi karewa ba
kenan,



Koda yayi taurinkai bekamata ka doketa irin haka ba kasan raba da da uwa se Allah baby,



Kekikasan wannan ko uwarsu taimin irin haka ba Abu bane me wahala aguna nai mata duka ba,



Naji dai nikam banason duka kalli yadda kasamin yarinya bacci akasan tile haka aise sanyi
yakamata,daukar Lubna tayi takaita dakinta har kan gado,



Lubna anji jiki har lkcn kwanciyar su bata farka ba,dayan dakin safara'u takaita Dan bazasu kwana
daki daya ba sedai tabar kofa bude koda ta tashi,



Ina Lubna ne?yatambaya lkcn dayake shirin kwanciya,

Tana can dakin amma nabar kofa abude koda ta tashi kasan babukyau kwana da yaro daki daya,

Bece komaiba ya kwanta,

Cikin dare Lubna ta tashi tana kuka tayi kofar Palo kuka take tana dukan kofar,
Mama zoki tafi dani dakin ki banason nan bazan kwana ba mama kizo kidaukeni karya kuma
dukana,

Tsawa ya daka mata,ke maza kikoma kikwanta kona kara zaneki wallahi,
Nace maka nafiso nakwana wurin mamana banason nan dakin,sena kuma dukannaki kenan,bata
kaunar ataba lpyr jikinta shiyasa tafara tafiya ahankali suna biye da ita takwanta kan gado tana
kuka ahankali,safara'u ke shafa bayanta don munafurci hartakoma yin bacci,



Da asuba safara'u taiwa dakin tsinke bayan sun gama sallah,tasamu Lubna akwance idonta arufe
ruwa ta debo ta daga Lubna ta zuba kafin tamayar da ita yadda take,



Baby wai dama yarinyar can tana fitsarin kwance ne?,ban taba jin dakin dakin mamanta yana
warin fitsari ba gsky batama yi inndai tayi yau iskanci ne kawai kuma sena zaneta,



Sedai kar akuma kam kuma meyawa tayi banmasan yazanyi ba amma duka bashine magani bari
natasheta naimata wanka,



Yana tafe tana bin bayansa nidai karka daketa baby banason duka,

Aidole tgane kurenta da gangan tayishi sbd kokadan mamanta bata shiri da fitsarin kwance,

Lubna tana kwance sejin duka tayi afirgice ta tashi tana kuka,wayyo Allah Na menayi ?nibanyi
komaiba ake dukana?,mamaki yakama shi yadda kokadan bakinta baya mutuwa,

Dan iskanci shine zakiyi fitsari akwance air bakya yiwa uwarki zaki gane indai haka zakyi
muzuba nidake,

Seda yaimata duka da sleepers yakyaleta acikin kukan yaji tanamagana tana kallon safara'u dake
gefe tana murmushin jin dadi,

Ai malaminmu a islamiyya yace zalunci babu kyau Wanda yayi kuma se Allah yasa shi cikin
wutar jihannama yakonashi,😭



Jan hannun safara'u kawai yayi suka fita daga dakin,

Anan taci Ku kanta ta koshi hartagaji tayi shiru tana tunanin mamanta,

Abangaren badee kuwa dakyar tai bacci lkcn datakejin kukan Lubna kuwa itama seda tayi kukan
Tace ,Ya Allah kana ganin abinda bayinka suke mana ya Allah kataimake mu😭,



Lubna tashi ayiwanka lkc atafiya karki letti a a makaranta,
Batareda tayi magana ba ta miqe,bayan tayimata wankan tashiryata cikin uniform tabata tea kadan
tasha tace takoshi,

En matan baby naje naga mamana🙄tafada tan kallon safara'u,

Cike da mamaki takalleta kafin tagyara mata ba Anty zaki kirani ba en matan baby ba kinajina
kokuma nasa babanki yazaneki,

Ai haka naji ya kiraki dazu,kiyi shiru kije gun mamanki tabaki lunch box Dinki nibanzan iya girki
yanzuba kice tasaka miki abincin data girka,

dagudun ta tafita,
Tana zaune seji tai anrungumeta sosae murmushin jin dadi tayi dantasan lubnarta ce,

Mama shine jiya bakizo kin kwaceniba yaudasafe matarnan tasaya zaneni wai nayi fitsari akwance
kumafa itace tazuba ruwa agurin,



Kiyi hakuri muje narakaki makaranta,uhm tace kiban abincin dazanje dashi ita bazata iya girkiba
wai,ai yananan nahadamiki,

Cike dafarinciki ta rakata ta dawo,



Bayan tadawo daga makaranta ta hadu da babanta a harabar gidan sauri sauri take tafiya Dan
bataso ma yai mata magana kuma yau bazata kwana gun wannan antyn ba,

Lubna ta,yfda yana tahowa kusa da ita yakarbi lunchbox dinta yanabudewa Ita dai batayi magana
ba,



Iyye Lubna er gayu yau da Irish akaje makaranta lallai sabuwar mamanki naji dake,

Mamana ce tabani ba wannan antynba,nikam bani abina nakara sa cinyewa,

Gani kawai tayi yawuce fuuu bayan yamiqa mata lunchbox dinta,



A tsakar gida yasameta tana wanke wake yau alala take Sha'awa ,kaudin meye naki nabawa Lubna
abincin zuwa makaranta iye kobakya jina,ita taturota wai nabata abincin,karya ne bakar munafuka
nakara ganin kinmin irin wannan kaudin kiga,
Wai majid yaushe lubnar tazama yarka inace duk kabarni da lalurar su tomeye naka natada
jijiyoyin wuya kana nufin zaka fara nunamin iko akan ya....

Marin dayai matane yasa t yinshiru,

Lubna takaraso kusa dasu tace, mama mubar gidannan tunda dukanmu yake mukoma gidan
babanki dakike bani labari,



Bata amsata ba tashige dakinta tana kuka me ban tausayi harseda taji kanta ta yafara ciwo kafin
tahakura,

Nayi danasanin rashin binka babana gashinan kungujeni dalilin haka rayuwata tana cikin tsaka
mewuya nadauki soyayyar miji data yaya gashi tana wahalar dani banida mafaka dole senan gidan
majid idan nafita bansan inda zan dosaba waxe karbeni da yaya haka kuma bazan iyabarinsu ba
rayuwarasu ta lalace, Allah ka kara bani hakuri da juriya Ameen Lubna dake gefenta tashare mata
hawayen fadar ameen dukda bata fahimci komaiba.




Feeyah tayi kokari yau💃🏻💃🏻💃🏻
[7/16, 9:43 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG

A very heart touching story 2017.



Sadaukarwa ga dukkanin masoyana Allah yabar so dakauna ameen❤



18



Wai wannan wane irin iskanci ne Lubna kitson ma kice bakiso?haka za abarki dakai kamar
mahaukaciya?,

Ni bance banason kitso ba Na mamana nakeso wannan bata iyaba kuma da zafi,tafada tana kara
sautin kukan Ta,



Wane irin zafi zaki zauna ne kosena jibgeki yadda muka saba?,nikam banaso zanje gun mamana
tayimin nata babu zafi,
Haushi ya kamashi yasa takalmi yaimata duka safara'u ta matseta cikeda mugunta ta taimata kitson
kuma batama iyaba (kunsan kitson Dan koyo yafi komai zafi haka maman nu'aym taimin lkcn
datakeso ta iya kitso ina gudu tana kamoni sun rankwashi ba abinda banshaba😂),



Badee Na zaune korido tana jiyo kukan Lubna babu yadda zatayi mamaki take yadda tanaji tana
gani ana so arabata da yarta,



Uban waye yashafamin maiko ajikin fenti? Ko kallonsa batayi ba yadda yazo yana mata ihu
akai,wai bakwa jinane? Nace uban waye acikin Ku yashafamin maiko ajikin fenti?,

Miqewa tai tafita daga cikin yaran takoma gefe,wani mugun kallo daya bita dashi tai kamar
batasan me yakeba,

Ke kuma meye nakomawa gefe?,cikeda rashin kula tace, naji kace ubanwaye shiyasa nadawo gefe
kazagesu su kadai Dan ni bazaka zagi ubana ba,



Sosae yaji haushi shiyasa Yakoma kan yaran kafin yadawo kanta,

Bazaku fadaba kuka zubomin ido kamar Na uwarku? Shiru yaran sukayi dama gasu ba magana
sukeyiba,haushi yaturnuqeshi,



Takan abdulrahim yafara yaimasa duka sosae kafin yajanyo abduljabbar badai sokuke Ku
lalatamin fentiba kunkwaso mungun halin uwarku ko? Itadai tana tsaye tana kallon ikon Allah
yana zuwa kan abdulazeez yaruga ya kankame uwarsa,mama kibashi hakuri bani bane karya dake
ni don Allah,



Tayi mamaki sosae ganin yadda majid yayo kansa ze dake shi,

Dakata malam badai dukansa za kayi ba yazo jikin uwarsa? Toko mutuwa na kunyar idon mahaifi
Dan haka bazaka dake shi agabana ba seka kara gaba idan ka hadu dashi awaje koyankashi zakayi
gaka gashi,



Ke har kinada bakin magana matar databar iyayenta tabi namiji mezata yi taburge mijin kuma
mace kamar akuya se haihuwa aure ko shekara Tara beyiba haihuwa bakwai Dan ma Allah
yataimake ni daya ya rasu,
Sosae zancensa yataba kahon zuciyar ta amma tadake tagano majid danyaga tana masa shiru
ne,majid bansan ka zama Dan dauduba seyau seka bari waccen uwar daka tafadi wannan
bakaiba,kuma zancen haihuwa dakake fada da nice kai tun dakaga ina kwasar cikin seka daina
raba ta kaga basena kwashi cikin ba,jabir kuma ina rokon Allah yasa me cetona ne tunba yauba
nasan bakayi bakin cikin mutuwarsa babu abinda yake bata min rai irin nabude idona naganka
agabana waikaine uban yayana,

Batajira yabata amsaba tai shigewarta daki jitake inama tanada wurin zuwa daba abinda ze hanata
barin gidan majid,

Bangaren Lubna kuwa taci kuka harta gode Allah,

Tana zaune agefe tana kallon safara'u dake kallo tace,

Anty don Allah ki bude min kofa naje inyi wasa,

Wasar uwarki?kice wurin iyayi da Gulma zaki tunda anriga ankoya miki shegen iyayi kamar ba er
shekara biyar ba,



Mamana tace Gulma bakyau kuma bata koyamin ba Dan Wanda yake Gulma dashida me zalunci
duk wuta za a saka su kuma wutar Allah zafi gareta,
Cike da yarinta take maganar kuma iya gaskiyarta take fada,



Dallah daga can babu inda zaki dauko tsintsiya kisharemin palonnan tun shekaranjiya kikejin kasa
da datti idan kintaka amma dayake kinyo gadon kazanta bakisan koda wasa kice zaki share ba,



Mamana tace zata koyamin shara amma sena kara girma idan nakai girman abdulkadir,

To ni bazan jiraba maza jekidauko tsintsiya tunban jibgekiba wallahi,

Ganin dagaske take yasata shiga kitchen tadauko,kwata kwata batasan me takeyiba idanma taga
abin wasa seta ajiye sharar se taji safara'u ta yimata tsawa kafin tacigaba,

Anty nagama inje inyi wasan?tafada tana leqen fuskar safara'u,



Kitchen zamu shiga har girki zaki koya,tafada tana jan hannun ta suka shiga kitchen,

Anty mamana tace zata koyamin girki amma sena kara girma don Allah kibarni inga
mamana,takarasa maganar tana kuka,
Babu inda zaki,tunkafin tarufe bakin ta Lubna tafara ihun kuka tayi juyin duniya taki yin shiru,
karshe dai ta kyaleta tace zamu hadu dake,



Washe gari Lubna tana bacci dukan da majid ya sabayi mata yatasheta ga baccin yamata dadi Dan
kwana tai kuka ita se wurin mamanta zata kwana,



A firgice tamiqe zaune tafara kuka,indai bazaki daina mana fitsari akwance ba wallahi na dinga
jibgarki kenan,

Dagudu tafito daga dakin taci Sa'a kofar abude se part din mamanta ta sameta tana shara kafin ta
ankara majid ya damqota yahau dukanta tun tana iya kuka har ta kasa itadai badee se kallon ikon
Allah take yadda yahaukace yana dukan Lubna kamar yasamu wata babba koda ace babba ce
mace bata cancanci irin wannan dukan ba balle Lubna dabatasan komai ba,



Ganin daya yi tazube akasa ko numfashi batayi yasa yadaina dukanta yafara Dane tabarmar kunya
da hauka,



Zoki kama yarki gatanan tasuma kinkoya mata munafurci komai setace ke tahanamu bacci ta
hanamu hutawa wallahi wata rana sena illata ta kuma tana farfadowa kidawo da ita gun safara'u,



Idonta dasuka chanja kala ta dago tana kallonsa dasu,
Wallahi majid indai kaga Lubna takoma gun waccen algungumar matar taka to bana doron duniya
kadaina wannan tunanin kuma kacigaba dadukansu haka ranar daka kashe daya sekayi sunan ka
kashe danka na tabbata zakayi bugun gaba dahakan,




Harta juya zata shiga daki bayan ta dauki Lubna tajuyo,

Kacewa safara'u ta hado min kayan diyata Dan bazan bari takoma ba.




Don Allah kuyi hakuri darashin jina kwana biyu nima badason raina hakan yafaruba,ina fata
zakuyimin uzuri?🤗😍❤
[7/17, 8:23 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG

A very heart touching story 2017



Wannan shafin nakune matan gidan homel&SophieG novel group nagode Allah yabar kauna
ameen.



Page 19



Tsaya wa yai agurin kamar andasa shi Zuciyarsa namasa zafi jiya ke kamar yaje yaita dukanta seta
daina numfashi,wato shi zata gayawa magana irin haka?Ashe garada datake kyaleshi akan yanzu
datake maida masa da magana?lallai dole yasan yadda zeyi da ita inbahakaba renin zewuce wuri
idan takama ko korarta ne yai itada yayanta dole yayi sbd yanzu babu abinda ya tsana irin ganin
su,gajiya yai da tsayuwa yawuce yana hura hanci,(daga baya kenan),



Dakyar tasamo kan Lubna ta farfado tun lkcn kuma take kuka tana rarrashinta har tagaji tadaina ta
zubawa sarautar Allah ido,



Nidai kaje kadawo da Lubna ta,tafada tana tunzuro baki,ki kyalesu nifa koson ganin yarinyar
banayi wallahi wani Abu nakeji inasonta sosae azuciyata amma banaso naganta kodan tanada
taurin kaine,

Bakaramin dadi tajiba Dan dama haka takeso,shikenan tunda uwarta tanunamin ita tahaifeta,

Kiyi hakuri kinji en matan baby,zomu kwanta kardamuwa tahnaki bacci,



Washe gari Sunday bayan fitan majid yatafi kasuwa safara'u tafito Neman fada, badee nawanke
uniform din yaran bayan sun tafi islamiya Lubna CE kadai a gdn ganin har yanzu tana wasu en
firgice firgice yasa bata turata islamiyan ba,



Sannu bakar munafuka to kin karbo yarki sae me?,

Nakarbo yata sekuma shikenan babu yadda za ayi Dan bakukukamin naqudarta ba dazan zauna
inakallo ana jibgarta kamar jaka sekijira idan kinhaifi naki kibashi yadaka yadda yakeso badai
nawaba,
Angaya miki kowa irinki ne?kamar wata dabba kikesta sako yaya,Toni ba jahila bace senagama
gurje amarcina koda zan haihu balle ni wannan baya cikin tsarin rayuwata, haihuwa bakwai
ashekarun dabasukai gomaba gida yakoma kamar gidan Reno,



Babu jahili dayawuce Wanda yake tsarawa kansa abinda ba Allah ne yatsara masa ba kuma
haihuwa baiwace ki jira ranar dazakiso ganin yayanki amma lkcn yakure miki Niba shashasha bce
inada aikin yi idan kin gama surutunki sekin kara gaba,




Allah yawadaran naka ya lalace ni ina zaune da iyayena lpy Nafi wacce tazabi tabi namiji akan
iyayenta kuma Na mijin ma batada daraja a idonsa amma dai wallahi anji kunya,takarashe
maganar tana karkade kugu,




Kekika damu da wani miji ninan zaman yayana nake bazan yadda nabarwa ballagaza irinki suba
Dan bazafin haihuwa kika saniba kuma banso kikoya musu muguwar tarbiyar da tsohuwarki
takoya miki tunda har tsohonki bata bariba yanaji yana gani ana abinda ba daidaiba amma be iya
magana nikuwa iyayena zaunensu suke qlw,



Sallamar majid suka jiyo yadawo kila koyai mantuwa ne,



Take safara'u tafara birgima,wayyo ni Allah Na shiga uku na lalace,

Aidasauri yazo yarungumeta yana jin Ku kanta har zuciyarsa,

Lollipop dina ya akayi ne?,
Matarka kemin gorin haihuwa kuma harda marina tayi kilama kunnena yadaina ji,



Babu wani bincike yahau dukan badee,ai gara ita akanki inaga sena illataki zaki gane kuskurenki
abin naki yawuceni haryakai kan baby na to wallahi kindebo da yawa,



Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Abdul dukan babbar mace Ashe lalacin naka yakai haka kuma
agaban yarta?

Hajiyarsa ce tazo dubasu sbd majid yafi karfin wata beleqa gidan ta ba,
Shiru yayi yana kallonta azahiri ya tsorata daganinta amma akan enmatan baby babu abinda baze
iyayi ba,



Kalleni dakyau munafuki sekazo muzauna naji dalilinka nadukan matar ka sannan katanadai
hujjoji kwarara dazaka fadamin narashin zuwa kaduba lpyta na stawon wannan lokacin,




Haryabi baynta seyaji muryar safara'u tace,

Baby kazo kamin tausa kuma kasan kace idan kadawo zamuyi magana fa,ta fada cikeda shagwaba
tana rausayar dakai kamar karamar yarinya,ai kawai sebinbayanta yayi yama manta da kiran
uwarsa,

Bema damu da Kiran datake masa ba yacigaba datafiyarsa,



Hajiya da abinya girgizata kawai tashige part din badee itama tabi bayanta dalubna ahannunta
taana goge hawayenta,



Tana kuka ta labartawa Hajiya komai damarsu daya baya hanasu abinci sedai ba isashshe ba,

Yanzu badee kina wannan halin baki taba fadamin ba?Hajiya naga yai nisane bayajin kira,

Aiseki fadamin yanzu wayake biyan kudin makarantarsu?abdulrahim kadai yake biyawa shima
yacireshi daga makarantar kudi sauran ninake kukutawa,



Sosae tajinjina al'amarin tabawa badee hakuri tace gobe zata dawo dantasan ba abar majid hakaba
amma dalaifinsa,

Dasauri Lubna tace,Hajiya inaganin wani bakin Abu mekamada mage a dakin Anty safara'u
akasan gadonta,

Take gaban badee yafadi sbd sosae take tsoron al'amarin Lubna yanzu.




🤗🤗🤗🤗
[7/18, 10:32 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG
A very heart touching story 2017

*ban taba tunanin rubutu ze zama sanadiyar hadu wata da masu kaunata ba burina be wuce na Isar
dasaqon danake son isarwa ba kuma ya amfanar,

*Bawannan ne Na farko dana farajin hakaba amma wannan karon senaji ni daban kamar ba
safiyya ba,natsinci kaina cikin tsananin nishadi dajindadi,



*wani lokacin kusancinka damutun bashine zesa kushaku ba,

*A rayuwa sewanda baka taba saniba kuma baka taba ganiba seyai maka rana irin wacce baka
zato,

*base mutun yafada maka yana kaunarka ba azaman tare kaida kanka zaka fahimci hakan,akace
kukan kurciya gamai hankali bayanine,

*ina rokon Allah yabar kaunar dake tsakaninmu Fatima(baby nurse)Allah yasa munada rabon
ganin juna Ameen,

Kiyarda dani wani lokacin senayi kamar nahaukace idan natuna yadda kike min banaso nadaina
tuna wasu abubuwan sosae nakejin dadi😍,



Daga karshedai wannan shafin nakine ke kadai fatima (baby nurse).



Page 20



Lubna na hanaki irin wannan surutun kosokike muyi fada?,

A'a banaso muyi fada,fada babu kyau kamar yadda kuke da babyn Anty safara'u har yana dukan
ki,yarinta afili take maganar,



Badee ta runtse idonta batason yarinyar nan tacika surutu irin haka gashi tagano Sam Lubna
batayo halin ta ba batasan taboye abinda keranta ba kuma bata shakkar fada ko agaban waye,
sanin idan takara kwabarta wata kwabar zata kumayi yasa taimata shiru,



Hajiya ma kallon lubanr take aranta tace,majid yayi gudun haihuwa gashi be tsallaketaba,be
tsallake zuwan Lubna dunaniyaba kuma be tsallake tonuwar asirinsa ba,idan batayi tantamaba
yarinyar nan bazata rasa mutanen boyeba,ta tuna lokacin da margayi megidanta yake bata labari
tun bayan aurensu lokackn bata jima datarewa ba,duk inda mugun Abu yake mugayen iskokai
ne,wani mugun sammu ne,ko kuma maye hankalinsa baya taba kwanciya da wurin, takuma
tabbatar dahakan saboda abubuwan dasukayita faruwa kafin rasuwarsa,



Badee bari natafi segoben idansu Abdul sun dawo kigaishemin dasu(daga baya kenan),



Tou Allah yakaimu Hajiya Allah yakara girma, ta amsa da ameen,

Lubna gashi asiyamiki bobon zuwa makaranta,

Tana murna taakrbi kudin harda godiya,badee kam mamaki ne yakamata ganin yadda Hajiya
keson jansu ajiki yanzu kometake nufi da hakan?Allah masani sedai yayi kokarin kawarda
mamakinta har gate taraka hajiyar taleqa titi abinda tajima batayi ba taga mutane dadama suna
harkokinsu ajiyar zuciya tasauke kafin tace kowa da bukin zuciyarsa Allah kaimana
sassauci,ameen inji Lubna dake biye da ita,



Hajiya kam kwana tayi tunani Sam bata zaton er uwarta tayi mata haka sedai idan safara'u ce me
mugun hali idan hakaneko zatakai karar safara'u gun mahaifiyarta domin ataka mata birki sbd
bazata yadda tanaji tana gani arabata da danta ba,wani gefe na zuciyarta kuma mamakin kalar
hakurin da badee take,arayuwarta bata tunanin akwai mace irin badee haka kamar ma uwarta ta
gado sbd itama batada magana sosae ba kuma haka kawai ake gano damuwarta ba,

Allah sarki badi'a kusan shekaru fiye dagoma kina kwasar takaaici nakasa gano kina son dana
tsakani da Allah ammani dafarko baniyyata na tagayyara rayuwarkiba,

Toshi wancan shashasahn batasan ma ta Ina zata soma da lamarinsaba,

Asubar fari ta shirya tayiwa gidan majid tsinke,

Sauri Sauri yake tafiya kamar wanda aka aiko masa uwarsa batada lpy,



Kai Abdulmajid INA zaka?,

Hajiya wani guri nayi yanzu zan dawo,

Kazo nima sauri nake kware zaniyau idan mungama magana seka tafi koda birnin sin ne,



Wayyo Hajiya kijirani safara'u ce ta aikeni tace inyi sauri, yafada yana kara speed,
Lahaula walaquwati illah billah tafada tana tafa hannayenta,majid haka aka shanyeka?mace
kakewa wannan azarbabin?nashiga uku ni jikar mallam🤔,(uhm kya gama sallallaminki kikarasa
ciki majid ai bashida duwawun zama tunda en Matan baby ta aikeshi),



Hakuri sosae tabawa badee kamar ba hajiyar da badee tasaniba har seda badee tace,don Allah
Hajiya kidaina bani wannan hakurin kuma aike uwace sedai muyi fatan Allah yasa mugama da
iyayenmu lpy,

Ameen ta amsa,badi'a ya maganar iyayenki kuma,

Ai Hajiya kidaina batunsu idan har suna sona zasu nemeni nayita zuwa basu hakuri basu
saurareniba Dan haka nabarwa Allah komai inajira ne yayi ikonsa,

Sosae Hajiya taji tausayin badee taquduri niyyar taimaka mata da yayannnan nata datake bugun
gaba dasu kuma tana fatan suzama ABIN ALFAHARINTA,



Abinda hajiyar zata iya nataimako tayi ciki harda yiwa mazan dinkin sallah dake tafe sekuma
harkar karatunsu insha Allah zata taimaka Dan itama bawani abin kirki garetaba sbd mugun maqo
irin na majid,




Tafito rakiyarta hajiyar tace bari naje dakin waccen isashshiyar nagaisheta tunda ni bazatazo
tagaisheniba,




Nikam wai yakumbo meye haka?safara'u tafada dayake haka suke kiranta Dan haka taji en
gidansu nakiranta,

Ai dole zaki tambayeni kuma kisani kin bani kunya Wallahi,

A'a toni menai miki tunda sanyin safiyarnan zaki bugamin kofa inabacci kintasheni kuma ki
tsiramin masifa,kujimin fitinanniyar tsohuwa,



Tabdi jam ni Hajiya rabi diyar muhammadu jikar maryama da mallan,

Wai menene haka aketa hayaniya en matan baby,majid ya tambaya yana leqo kansa ta kasan
hannun safara'u,
Hajiyace kemin fada babu gaira babu dalili,tafada tana hararan badee da hajiyar,



Ko uwarki baztamin haaka ba kuma yanzu can nayi naji ko ita tasaki kiyi min haka karamar Mara
kunya kawai,

Aiko safara'u tasa kuka Yakoma ciki tana diddira kafafuwanta daqasa,

Hajiya meye haka kinga kimsaka min ita kuka ko yanzu dakyar zansamu kanta,kekuma munafuka
kike kallona ko?zamu had...

Kafin yakarasa yaji safara'u na kara sautin kukan ta air arikice yabibayanta yaran rufo kofar,

Hajiya kam baki ya mutu se kawai taakama hanyar fita,bata wani jimaba ta is a kware,



Yo ke yakumbo aikinsan kahaifi da ne baka haifi halinsaba sedai muyi ta hakuri da addua,

Maman safara'u tafada bayan tagama sauraren korafin Hajiya,(korafi bekarbu ba hajiya😜)

Hajiya taji haushi ganin er uwarta bata basa zancen muhimmanciba hakan yasata baro garin babu
shiri,



Bari mu leqa bangaren yaya asama'u,



A palonta takee zaune ta tasa hoton Lubna agaba tana kallo zuwa yanzu tanaso taji halinda er
uwarta take ciki amma shiru ba labari,mamansu har kuka tayi wa asama'u kan tashawo kan
mukhtar badee tadawo gida amma abin yafaskara baban suko shima yanaso yaji halinda take ciki
amma besan yazeyiba seyanzu yagano yayi katobara daya yarda yahakura lkcn datazo nakarshe
segashi yanzu ko labarinta yadaina ji,

Mijin yaya asama'u ma yayi fushi d ita akan maganar badee danyaita binta suhakura tamai kafiya
yanzu tayi lallashin duniya yake gun mukhtar yaki harta tadaina masa zancen sedai taita kallon
hoton Lubna datakai akacira daga wayarta akayomata na kati akayo enlarging dinsa takafa a
palonta.



Safara'u kinji wai yakumbo tazomin nan dashirme,

Maman safara'u ke maganan awaya,
Mama kyaleta ni sonake har ita agamamin da ita kawai Dan naga tanaso takawowa shirin mu
cikas,

Murmushi naga tayi tana sauke wayar daga kunnenta.




Luv u oll❤
[7/20, 8:45 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG

A very heart touching story 2017



happy birthday Anty billy Allah yakaro shekaru masu albarka ameen.



Masu Neman yayana daga farko suna biyoni private suyi hakuri don Allah idan sunji shiru u know
I'm lazy wahalar marking nakeji🙈.



Page 21



A'a mama ni banason asakashi yahanasu abinci sonake asakashi yadasa musu bakin cikinda suna
kallon abincin ma amma cinsa yagagaresu daga uwarta sa har badee da yayanta sonake rayuwarsu
ta tagayyara harsesun gudu da kafafunsu kinga idan anyi haka semufara da uban gayyar,

Safara'u ke waya da mahaifiyarta,



Toke safara'u bakyaganin abin zedau lokaci?

Babu wani daukar lokaci

Please Login or Register in order to submit comment