You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ai ance idan masara taji wuta ita dakanta zata fada,
Nida sonayi ko muce yasako musu ciwo nadan wani lokaci harse ransu yabar jikin su wallahi
jinake kamar sumutu yanzu wannan uwar dukiyar tadawo hannun mu,
A'a baza ayi hakaba aise ayi saurin ganomu,idan wuya tai wuya tsaf zaki nemesu kirasa,yadda
kikeji haka nakeji wallahi Dan majid din maqon masifa ne dashi koyanzu senayi dagaske nake
samun wani Abu hannun sa Wanda na aiko miki satowa nayi yatambata nace kila ya zubar ne yaita
mita, yanzu dai kije kicemasa akara sako masa tsanarsu har uwar yaji bayason ganinta,
To shikenan sekin jini,
Dahaka sukai sallama nikaina seda na tsorata (anya wai badee bazata mutu ba🤔abin yaimata
yawa),
BAYAN WASU SHEKARU
Tundaga Wannan lokacin babu abinda Abdulmajid yasawa gaba irin Neman kudi, yatara dukiyar
da shikansa besan adadin taba,
Yayansa,uwarsa da matar sa badee bemasan da zaman suba sesuyi satidaya basu ganshi ba,
Abincin dasuke ci yadamqawa safara'u se abinda taga dama take basu ,
Uwarsa tayi yawo harta gaji dole tahakura addua kawai take masa yanzu sosae take wahala,
Duka kuma sedai idan majid be hadu da daya daga cikin yaran ba har abdulrahim daya zama
saurayi yanzu bewuce duka awurinsaba yo ko uwarsa ta tunzurashi se yaimata duka,
Lubna ce kadai matsalarsu yanzu,tazama budurwa wani kalar kyau ne da ita har tafi wacce tayo
kyau,bata tsoron sa shida matar sa kokadan indai tana kusa bawan da ya isa yataba uwarta yanzu
zaunenta take gida batada matsala dan tagama secondary skul tace kozataci gaba bayanzu se
islamiya datake zuwa,kuma tana koyon dinki awurin wata makociyarsu amma da Dan tafiya
tsakaninnan,
Yauma kamar kullum tafito zataje gidan datake koyon Dinki ta iso kusada wata qatuwar bishiya
abinda takeji yafara tasomata wani kalar tashi gashin jikinta yake kullum tana so takarasa Dan
tasan bakaramin abubane wannan koma menene amma setaji abin yana kara yawa,
Afili tace nakusa fara avoiding hanyar nan,
Lokacin da ta dawo tasamu safara'u na surfawa badee rashin mutunci ita kuma tatsaya kallonta
kamar hoto,
Wai mama meyasa kike kyale matarnan tana surfa miki ruwan rashin mutunci kina kallon wallahi
ki jibgeta seta fita hayyacinta,
Lubna kinsan na hanaki irin wannan ko idan baki dainaba nizan jibgeki bakyajin manya na
magana sekin sako bakinki,
Kiyi hakuri mama manyan naga girma ya Riga hankalinsu zuwa,kuma wallahi dabadan duk
abinda kayi se anmaka ba babu abinda ze hanani gurzar bakin wata yau,
Shiru badee tayi Dan tasan yanzu idan ta takurata da fada zata hau bori tajiwa kanta ciwo,shine
abinda yake damun Lubna idan ranta yabaci shikenan seta fara nose bleeding daga an tabata seta
ringa buga kanta duk inda tasamu se anmata ruqiyya kuma dakyar take dawowa daidai,
Safara'u ta buga tsaki, mayun banza ke bakida daraja awurin miji kuma kinkafe kinki tafiya
shekara da shekaru kokwana dakin ki bayayi amma kin nace saboda kwadayin abin duniya kinga
babu cigaba kinki tafiya ko ina kikai jarrabar ki oho, kodayake ma inkin tafi babu gidan zuwa
iyaye sun yafeki sbd anzabi abin duniya akansu shiyasa aka cika gida da yaya sedai Haryanzu
babu alamun fidda uwa balle akaiga riba mtswwwwww(ai dasauri najanye fuskar badee nace
wannn tsinin baki haka duk wurin tsaki ne karki tsokanewa baby badee ido😂),
Safara'u kenan Aiduk Wanda yayi zagi akasuwa yasan da Wanda yake, tana gama fadar haka
tashige daki Dan jin ana kiran sallahr magrib,
Lubna dake tsaye tace, maye dai yasan inda yake kuma kema daknki nan gaba zaki tantance maye
acikin mu,kuma wallahi kurwan mu our sedai shi zakiyi wa megidan mu munriqe Allah
dankinsani wallahi har hanjinki inagani sedai ina jiran naga ranar da reshe ze juye da mujiyane
kuma kaikayi zekoman kan masheqiya, itama binbayan mamanta tayi,
Cike da takaici takoma gefenta lallai yakamata tadau mataki akan Lubna, amma tayaya?ga Hajiya
ma itake rage musu wani zafin shiyasa sukeyin kamar basuda damuwa gashi tafara ganin alamun
nasara arayuwa Dan abdulrahim da abduljabbar suna kusada kammala degree dinsu ga Abdul'aziz
ma yana 100level,abdulqadir da lubna kadaine basu samu admission ba, kuma duka mazan ba
azaune sukeba kowannensu yanada sana'arsa ta hannu,
Dole na riqe takuna Lubna nashirin ruguzamin komai,
Kamar wani zaki haka yashigo dakin badee daya fi wata be leqoba yaka yaringa ihun kiranta
dasauri tafito gabantanafaduwa dan tasan ba alkairi ke kawo shiba,
Ban hanaki yiwa enmatan baby gorin haihuwa ba,
Shiru tayi tana sauke idonta kasa,
Hakan yatunzurashi bazata daina yimasa shiru ba kenan shifayarasa abinda yahana shi sakinta ko
kuma korarta itada yayanta ya tsani ganin su,
Kyakkyawan mari yadauketa dashi,dasauri Lubna tafito tanajanta gefe,
Metai maka? Tafada muryarta da alamun kuka,
Zaki kaucene kosena jimiki ciwo,badee tace, Lubna banason irin haka kije kicigaba da aikinki,
Mama kidaina bata yawun bakin ki babu Wanda ya isa ya wulakantaki ina kusa,
Saukar mari taji hakan yasata tsaya wa tana kallon majid sekuma jini yafara fita daga hancinta.
Ku yarda dani idan aka kirani Anty wani dadi nakeji senaji nazama wata babba,irin anty Sophie
ina wuni ya typing😎 wayyo dadi sanaji kamar nabawa wacce takirani Anty sweet🍬,
Inkinaso kiga yadda murna ke lullubeni kicemin baby Sophie 🤔 ranar sekin goyani kuma da
zani😂.
LUV U ALL❤
[7/21, 5:49 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
*Wani Abu se rayuwa lokacin dakake dariya lokacin wani ke kuka,lokacin dakake ta kamar
kanada lpy lokacin waninacan yana shan wahalar ciwo,haka a kullum aka haihuwa haka kuma
kullum ake mutuwa😭,
*yayinda kake takama da tarin dukiya wani yana can yana tunanin ina ze samu abinda zeci yanzu
anjima bema San ya zeyi ba, don Allah kada mu jira se munsamu dayawa zamu bayar, Dari biyun
daka fi karfin ta koda a kullum irinsu zasu fadi daga jikinka bazakama lura ba itace zata saka
rayuwar wani cikin nishadi da jin dadi na wuni daya,
*nera goman dazaka bawa wani bawan Allah baka saniba ranar gobe kiyama kilama itace zata
zama cikon mizaninka Na shiga aljanna,
Ya Allah kabamu badon murama ba sedan mukasance masu jinkai da taimakon en uwanmu Allah
ka kara rufamana asiri duniya da lahira ameen thumma ameen,
Page 22
Daga hannun sa yai ze mareta badee ta janyeta,
Haba majid yanzunnan idan ta birkice ni zaka bari da ita kuma kasan yadda take don Allah kai
tafiyarka karka tadomin rigima,
Wallahi ban haifi danda ze fifita uwarsa akainaba ni zaki nunawa soyayyar uwa har za kice bazan
yimata hukunci ba,gorin haihuwa za tayiwa matata wayasanima ko duk cikin datake samu yana
zubewa kece sila,ni nafara zarginki ma wallahi bakar munafuka dole nai bincike akan ki Dan
nafara gano take takenki kuma wallahi duk nakara jin anmata gorin haihuwa sena illataki mutanen
banza mutanen wofi,
Majid kadai San inda mutanen banza suke Dan kana tareda su,ni wallahi nafi karfin nayiwa
kishiya wani mugun Abu wai dan karta haihu,ta haihu mana gatanan ga gidan da mijin,inda
saniyar gaba tasha ruwa wallahi anan ta bayan ta zata sha,ba dai kabawa Neman kudi muhimmaci
ba akan bautar Allah da kiyaye dokokinsa badai kayi watsi da tarin tulin haqqoqin mu dake kanka
ba?to wallahi ka shirya ranar da Allah ze damqeka ranar da zakayi kidanka kuma kayi rawarka,
Haryayi niyar fita yaji ta ambaci haqqi se yadawo ya kama hannunta, dama Riga da zanin jikin
sunmata kyau Dan haka yakauda idonsa daga cikin nata dama haka kesa yaji ya tsaneta,
Sekicemin haqqinki kikeso abaki jarrabar ta motsa kenan to ai ba kiyi magana da wuriba,
Nidai bahaka nake nufi ba kasakemin hannuna inada aikin yi,
Taji tsoro sbd tajima batasha maganiba Dan ganin yana Neman share shekara be nemeta ba to ita
yanzu yama zatayi?Lubna dake kan Ku jira zaune ta kalla da alama ma bata hayyacinta,
Janta dayayi dakarfine yasa tadago tana kallonsa dasauri yadauke kansa danbayaso abinda yai
niyya yaruguje, dakin sa dabaya tuna rabonsa dayashiga ba ya tura kofar, yayi mamaki sosae ganin
dakin agyare da alama anadan kula dashi sedai yadanyi kura,
Waike wane irin wulakanci ne wannan?se kibarni inata.....sekuma yai shiru yana kyacci hadida
girgiza kansa,
Seda ta Daura zaninta tace,inaso ne nanuna maka yanzu bakina ya bude kuma kasani niba zaman
ka nakeba zaman yayana nake zancen jaraba kuma kaika koyamin kuma nadaina yi Na barka da
abinka banida damuwa dakai,ka kiyayi ranar dazaka nememo karasa kuma daga yau in ka kwaso
yayan jarabarka ga en matan baby can always available karka kara zuwa gurina balle katadamin
hankali Dana yayana,
Baki asake yake kallonta, gsky zata kwafsamai domin tafi safara'u akomai amma besan meyasa
yake jin kamar yakasheta ba inya ganta dukda inya tuna yadda tacika mai gida ransa yana baci, to
wai duk ina soyayyar danake mata?(yadda naji kamar nabuge bakin dan air),
Miqewa yai yashiga bayi yayo wanka badee kuma dakinta takoma,
Tasami Lubna adaki tana jera kayansu a wardrobe batako kalli inda takeba tawuce toilet gani take
kamar duk Lubna ta fahimci komai,
Ita kuma bin maman tayi da kallo hartashige toilet,murmushi kawai tayi afili tace inama waccen
matar zata barku kuzauna lpy?,
Safara'u taga shigarsa bangaren badee amma tayi jiran fitowarsa har tagaji be fito ba,
Meya tsaya yi ohh ni safara'u, daga karshe dai tahakura tazauna tunanin yadda zatayi da lubna,
Lubna ta dawo daga islamiya da safe around 12:15 a gate tasami wani manna'u daya manne mata
yasan lkcn datake dawowa daga islamiya Dan haka anan take samun sa tayi kora harta gaji,
Yi tayi kamar batasan da zaman sa awurinba Dan haka yai saurin shan gabanta, haba lubna ta
kisaurareni koda minti biyarne,
Malam banida lokacin ka Inada abinyi kabani hanya,
Tana gama fadar haka tabi gefensa zata wuce seya riqo hijabinta daqarfi ta kwace tana masa
mugun kallo Dan haka Yakama kansa,
Tana shiga tai wanka ta Dora musu abincin rana fara damai har sun saba kullum shinkafa ba miya
sedai mai da gishiri sharrin safara'u ne wannan,
Tafito tsakar gida dibar ruwa taga safara'u da majid sun gito da alama seyanzu zefita ko kallonsa
batayi ba tacigaba da aikinta,
Ke lubna baki iya gaisuwa bane?majid yatambayeta ganin da koba komai tana gaisheshi,
Batako dago ta kallesu ba,
Yaushe zata gaishemu kuwa yarinya ta girma taga kirjinta ya cika takai daidai dakowa aure takeso,
Ita tafada miki tana son aure?
Dazu naganta dawani harda riqe mata hijab aiko nace sena fada maka kaga inbaka yardaba ga
shaida,
Tanuna masa hoto awayarta, sbd tasan wannan saura yin wata rana tanaganinsa yana tare Lubna
sedai bata taba kula shiba Allah yasa burinta yacika a aurar da Lubna auren dole Wanda bazata
taba jin dadiba yadda uwarta take ayanxu (safara'u kin manta dadi da wuya babu Wanda ze
dawwama),
Nikam da lubna ta lalace ai gara ka aurar da ita nikam inason ta kuma ai da nakowane, yadda take
maganar dukse yaji ya yadda da ita amma wannn hoton ya harzuqashi,
Kusa da lubnar yatafi,yanzu kinzabi kizubarmin da girma da mutunci akan ki fadamin kina son
aure namiki?,
Ni bancewa kowa inason aureba kuma bantaba yin iskanci ba kaima kasani banaboye abinda ke
raina matukar inada gaskiya,
Karya kikeyi kinkoyo munafurci gun uwarki Dan haaka dole nadauki mataki dole na aurar dake
akan kijanyomin abin fada kihanani shiga mutane,
Itakam cigaba tayi da aikin ta tana tabe baki Dan bata bawa zancen muhimmanci ba,
Safara'u dake gefe tayi wani murmushi alamun jin dadi aranta tace, dole akarawa malam kudi
Aikinsa nakyau(kuji Dan Allah majid ba bincike hujjar dabata hujjaba yahau kai yazauna),
Anty Sophie
Baby Sophie luv u buhu buhu❤
[7/22, 7:42 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Bance dole se kowa ta karanta littafina ba,babu abinda ze bakanta min rai irin mutun fiye da dari
su karanta littafina amma basu wa'azantu da abinda ke cikiba, su karanta littafina batareda
sundauki darrussan dake ciki ba,koda mutun daya yakaranta littafin kuma yadauki wa'azi da
darasin dake ciki to zanfi alfahari da hakan kuma nayi bugun gaba dashi ako'ina,ba don in burge
kokuma in Tara tarin masoya nakeyi ba inayine saboda Allah.
23
Mama Wannan gashin naki dani nakeda shi dole mane na saka mai relaxer kigafa yadda yakeda
uban yawa gashi seyaita nannadewa,
Lubna dakewa badee kalaba take fadar haka,
Kuma ahaka dakika ganshi bantaba saka masa relaxer ba ko bayan aurena ba yadda babanku
beyiba nace bazan saba karyazo ya lalace min irin na Fareeda Dan gashinmu iri daya da ita wai
ita batason shi ahaka taje tana saka relaxer aiko duk ya kakkarye,tafada tana dariya,
Itama lubna murmushi tayi tace inaso naga kanwar nan taki amma nafiso nafara ganin yaya
asama'u Dan yadda kike ban labarin ta,
Hmmm,Ashe kinada jira lubna adadin shekarunki aduniya shine adadin shekarun da suka guje ni,
inaso naga mahaifiyata amma banida hali nasan ita tanaso taganni idan su basa sona fatana dai
Allah yasa suna cikin koshin lafiya,
Ni fa mama nayi mamakin yadda kika ki binsu kika tsaya gun Wannan mutumin nifa ina
danasanin shine mahaifina wallahi Sam Sam banso yakasance u....
Lubna yakamata zuwa yanzu kifahimci abinda nake kokarin nuna miki a kullum, eh naji ke
yarinya ce amma duk yarinyar data kusa shekaru a shirin a duniya yakamata tagano abinda ake
kokarin nuna mata,
Yau inaso ki tsaya ki saurareni dakyau idan da a can baya ina fada miki magana atakaice to yanzu
Zn miki bayani sbd kina bukatar sani Dan ke macece watarana kina gidan aurenki,
Lubna idan akace miki aure to magana ce da babu wasa acikin ta magana CE me girma kuma
aruyuwar duniya wuya ko dadi babu Wanda ze dauwama kamar yadda rayuwar mu bazata
dauwama a duniya ba,
Eh Allah ya hallatta saki amma koshi bayasonsa beside inason babanku sosae lokacin dough
yanada laifi babba ma dan bekamata yabarni da dawainiyar yayansaba Dan bayason haihuwa,
kuma tarbiyar yaya yakamata ace sunsameta ne daga gurin mahaifiyarsu,
Lubna kinsan duk abinda babanku yake yi ada dasa hannun mahaifyarsa?idan natafi nabarku Waze
kula min daku dukda lkcn ba ahaifekiba nasan abune me wahala idan narabuda babanku
subarminke sanin kanki ne banason hayaniya Allah ne kadai yakawoni gidannan, lubna inason
kusamu tarbiya mekyau idan nabarku wahala kawai zakuyi kiga yanzu da ace bananan ya auro
safara'u duk tarbiyr data doraku akai ita zakubi which bana tunani zaku samu tarbiya ta gari,
Yadda kikejin anacewa uwa uwace to haka ma uba ,iyaye dakika gani ba'acanza su duk yadda
sukakai ga lalacewa dole ne abasu girman su na iyaye Dan haka inaso ki kiyaye harshen ki akansa
kodan yadda kike ganin su Abdul sunayi kinji,(yanada kyau muringa nusar da yayan mu irin
wannan),
Bayan haka lubna akwai hakuri a rayuwar duniya bakitabajin Wanda yakeda hakuri ya wulakanta
ba Dan haka idan baki dashi tun yanzu kikoya ina fatan wannan rayuwar damuke ciki mu
gaggauta barinta Allah yatabbatar mana da alkhairi yakuma baki miji nagari,
Ameen ta amsa tana rufe fuskarta dadukan tafin hannayenta,
Murmushi kawai badee tayi tanajin son yayanta fiye datunanin me karatu,
Babuko sallama yafado dakin yana kiran sunan lubna fitowa tayi tana kokarin rufe zip din rigar ta,
Gani ta fada bayan tafito,yawwa sako hijab Dinki ga bako kinyi awaje sunansa Mubarak Dan
gidan wani abokin kasuwanci nane Dan naga kinfara kula maza yanuna kina son aurene dan haka
gara na aurar dake akan kizubarmin da mutunci,
To baba ni banfa cemaka inason aure ba,takarashe maganar tana turo baki,
Koma dai menene kije yana waje,fita yayi daga dakin,
Hmm wallahi se yatafi da kafafunsa haka kawai,
A tsaye ta same shi yajingina da motarsa taimasa sallama shiru be amsa ba,
Seji tai yace wooo wannan mezafin ce,dasauri takalleshi da alama besan maganar a fili yaiba,
Tab....wannan ko gaisawa bazata bari yayiba taga alamar riqaqqen Dan iska ne wato yama gano
me zafi ce hmm,
Ban baka damar yin magana ba inaso kasaurareni dakyau kaji,
Dafarko dai tundaga ganin ka danayi baka kwantamin ba in fact u'r not my type karkabari abata
ma lokaci idan aure kakeso kaje kanemi daidai kai, ina fatan zaka fadawa Wanda yaturo ka baka
dace dani ba? Nagode,
Baki asake yake kallonta harta bacema ganin sa,lallaima yarinyar nan dama haka take batada
mutunci to wallahi dole nasan yadda zanyi tazo hannuna nazata mesaukin kaice na wawusheta
nabar kasar gaba daya🤔,
Yaukam dukansu yaran suna gida Dan haka suka zauna palon mamansu sunata hira Sega majid
yashigo dukansu suka gaidashi be amsaba segun lubna ya tsaya beyi wata wataba ya kifa mata
mari afirgice ta miqe,
Ni zaki maida karamin mutun,naturo yaro gurinki ki walakanta shi dankina takama da rashin
mutunci?,
Nifa nagansa ne beminba shiyasa nafada mai gaskiya dankar na wahalar dashi,
Ni nace miki se Wanda kikeso zaki aura?Wanda nakeso naturo miki kuma dole kiyi yadda nakeso,
Wallahi ni banason sa nagwammace na mutu akan na auri wannan Dan iskan,
Chajan dake gefe ya zaro yahau dukanta, ko uwarki ba ta isa ina magana tana magana ba balle ke
kuma gidannan idan ana kaunar zaman lafiya dole ayi yadda nakeso,
Sunso su kyaleshi amma abdulrahim yaga hankalin baban baya jikinsa da haka dasauri ya kwaceta
yana boyeta bayansa dama yana cike da haushin baban,
Ya'isa haka baba tadaku sosae kalla har jini ya soma fita,inace kuma kasan yanayinda take ciki?
kuma ajirata takawo Wanda takeso bawai akakaba mata Dan iska ba,
Abdulrahim har dakai kakoyi rashin kunyar?inace kaima kasan halina Dan haka miqomin itanan,
Basuyi auneba suka soma jin ihun safara'u, labe take musu Dan taga yadda zasuyi,Ashe lubna
taganta kuma dama majid ya tabo abubuwan,
Dakyar da bala'i aka kwaci safara'u a jaka tabar part din badee sbd ta daku,majid kuwa kokarin
dukan lubna ya soma yi sedai abinda yagani ya matukar firgitashi duk yadda suke fada beyizaton
abin yakai hakaba,
Ka gani ko majid?yanzu a tsaye zamu kwana wallahi jiwa kanta ciwo zatayi abdulrahim kukama
min ita karta kashe kanta.
Anty Sophie ta gode😎
[7/23, 8:34 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to u Jidda (dota) & umzeey Allah yanunamin aurenku in kwashi Shoki ameen❤.
To kardai kuyi min fada yadda kuka saba Dan nahade Ku a page daya😏.
Page 24
Wani kalar faduwa tayi da seda hankalinsu yatashi sun tsaya suna kallonta kowa yakasa isa inda
take, daganan kuma bata kara motsiba,
Ko mutuwa zakiyi sedai ki mutu akaiwa Mubarak gawarki aljanin jikin ki ma yaci ubansa,dakici
gaba da borin kiga inban saka muciya ko tabarya na bugeki ba bakar munafuka,
Fuuu yafita kamar ze tashi sama (kadai tafi zuwa gashin jikin enmatan baby😡),
Abdulrahim ya kwashe ta ya kaita dakin mamansu abduljabbar yai mata addua ajiyar zuciya
tasauke sekuma ta gyara kwanciyarta se bacci,
Zama sukayi adakin suna maida zancen,
Abdulrahim yace,mama waime baba yake nufi damu ne kusan shekara goma bamuda maraba da
babu a gidannan sedai idan yana Neman amfani damune musamman lubna,
Numfashi badee tasauke,Abdul nima bansaniba amma nasan duk kalar hakurin danake yakusa
kaini maqura,sundauki karan tsana sundorawa lubna karkaji mamakin safara'u ce tazugo shi in
kuma ba hakaba to yanada wata manufa,
Abduljabbar yace ,lallai kam dole dabiyu yabijiro da Wannan zancen haka kawai ya dauko mata
zancen aure ba batareda wata manufa ba,
Abdul'aziz yamiqe yana cewa karfa kuji mamakin saboda kudi ne zebada ita Dan babu abinda
baba yasawa gaba irin Neman kudi,
Abdulqadir yayi murmushi yace, idan dagaske auren yakeson yimata bayaso tazubarmai da
mutunci meyasa bazece ta kawo mijin dakanta ba?wallahi idan ya takurata bataso wannan
Mubarak din zamuyi wa duka seya fita hayyacinsa,
Bance kudaki Dan mutane ba amma dai kome zakuyi indai zakukarbowa kanwar Ku yancinta ne
kuyi amma karku illata yaran mutane,
Abdulrahim yatashi tsaye yana fadin Hajiya zamu fadawa kawai,
Yome hajiyar ta isa tayi banda tsufa daya tasomata ma,ga baba bayajin maganarta ko kadan, inji
aabduljabbar,
Aiko wallahi barmasa gidan zamuyi Dan baze kashemu daranmu ba, fadar abdulqadir,
Abdul'aziz yace wallahi kuwa dama bamuda wani amfani a gidannan sedai kawai yana amsa
sunan ubanmu ne,
Kuyi tunani dai dukanku bayara bane koba komai ubankune kuma shiyake cidamu,
Mama kidaina zancen abinci,muntaba ci mun koshi ne? Ana ganin mu anga yunwa kullum cikin
cin fara damai kekanki kina marmarin cinnama amma kinfi sati ko takardarsa baki ganiba, duk
abinda muke samu a sana'ar damuke tabawa aharkar makaranta yake karewa,inji abdulrahim
yadda yake maganar abin yakai shi maqura kenan,
Kusani dai duk lalacewar gidan uba gara ace kunadashi kuma inaso kudan masa uzuri dukda wasu
abubuwan dason ransa yake yi amma bayinkansa bane, kuma idan munbar gidan ina kukeso
mutafi?kunsandai banida inda zan kaiku ko?
Abdul'aziz yace mu babu ruwan mu dashi danki zamuyi danhaka mujira muga mezeyi ,in zancen
gidane ai akwai gidan Hajiya daki semun zaba danhaka ki kwantar da hankalinki,
Shiru kawai tamusu Dan taga alamar ba abinda yashafesu da mahaifin nasu,
Kukan lubna ne yasa duka suka maida hankalinsu gareta,
Yaya kubani ruwa don Allah karku dauko a cup nafison nacikin bucket Jinake kamar Na shekara
bansha ruwa ba,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yaukuma da shan ruwa abubuwan suka zo?
Abdulrahim yadebo ruwa a cup ya tofa adduo'i aciki yabata ko sauke hannun sa beyiba yaga ta
ajiye kofin yaleqa yaga bakomai aciki kallonta yai yaga ta lumshe idonta,
Dariya Abdul'aziz yai yace wannan mutanen na lubna inaga daga birnin sin suke kuma da alama
kasa suke zuwa wannan shan ruwa haka sekace garin kwaki😂
Dariya sukayi dukansu kafin suyiwa maman sallama suka nufi dakin su,
Washe gari koda suka tashi hannun lubna ya kumbura sosae da alama taji ciwo ne lkcn data fadi,
dakyar suka ga gari yayi haske danse kuka take,
Dole tace su Abdul sukaita gidan me gyara targade a duba hannun Dan babansu baya nan bazata
fita ba izinin sa ba,
Mama kikamamin nasa Riga,inji lubna,
Meye kuma sekin canja kaya kayanma na bacci?
Mama sababbi ne fa kuma kinga Wando ne banaso naje anajan hannun ina tsalle Allah tsaf zan
hankade zanennan, amma kinga inwando ne nayi wulli yadda raina yakeso,
Sosae badee tai dariya tace Allah ya shirye ki lubna
Ameen tace bayan sun gama saka rigar,
Da shigarsu zauren gidan taga wani hadadden saurayi da wata matashiyar mata agefe da
alamamatarsa ce Dan ga cikinan jikinta zekai wata biyar se matsar kwalla take tana kallon
kafarta data kumbura,se sannu matashin ke mata,
Lokacin da akazo Jan kafar ihu take tana lailayo ashar, shi kuma se sannu yake mata kiyi ahankali
karkiji wa baby ciwo,
Seda akazo daure kafar tayi shiru tana kallon mijin nata daya shagala wurin kallon cute face din
lubna,
Hawaye take ahankali ganin yadda wannan matar ke ihu kila da zafi sosae,
Me dorin yacewa su Abdul bisimillah,bayani sukai masa faduwa tayi kan hannun kafin safe
yakumbura yana mata zafi,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tafada lkcnda akafara Jan hannun, Dan matashin saurayinnan se
kallon yadda take damqe hannun nakusa da ita take tana kuka ahankali dukseyaji ta burgeshi,
Wani uban tsalle tayi lkcn da akasa abin daurewar ya tsuke sosae, dukansu seda sukayi
dariya,kekuma ki tsaya mana karki batamin aiki,
Bayan angama haryanzu mata damijinna zaune da alama wani Abu suke jira,
Tunda suka shigo talura yana kallonta har suka fice, jyuowa tai taga haryanzu ita yake kallo suna
hada ido se yasakar mata murmushi Dan kallon matar sa tayi se taga ta ware mata yatsunta guda
biyar ta motsa labbanta alamar Uwar ki?
Zaro ido tai sosae sekuma tayi saurin dauke idonta tacigaba da tafiya da sauri sauri Dan su Abdul
sunyi gaba.
Anty Sophie na fatan yauba korafin yayi kadan? 🤗
[7/28, 3:03 PM] Babee Feeya: [7/26, 12:40 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y'AY'ANA (abin alfahari
na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine yar uwa rabin jiki billy galadanchi❤
Page 25
Daganan gidan Hajiya suka wuce dama Abdul'aziz ne kawai se abdulrahim suka kaita suna zuwa
suka samu hajiyar azaune tsakar gida ita kadai da kofin koko agabanta da sauri lubna ta karasa
gaban hajiyar tana murmushi,
Hajiya barka da hutawa,barka dai kanwar maza yakuke ya mamanku?
Lpy lau suka amsa,
Kokon dake gaban ta lubna tadan kurba tace haji wai anya ba kwakwa a kokon nan jinake ina
wani lulawa,
Dariya sukayi dukansu Hajiya tace kikarasa shanyewa naga alamar ko karyawa bakiyiba,
Wlhy kuwa Hajiya kamar kinsani,
Meyasameki a hannu?
Jiya na fadi Ashe naji ciwo seyau dasafe natashi hannun yakumbura shine aka gyara,
Nan abdulrahim ya zazzage mata abin da yafaru,
Tabdijam...idan aure yakeson yimata aiseyace ta fito damiji, towaima yaushe yasan Ku yayansa ne
dahar zenuna isa akanku?
Kunga Ku tashi Ku tafi zuwa sabogoginku kubarmin ita nan nayi wanka naje gidan kobayanan zan
jira shi Nagano take takensa iskanci ne danhaka wallahi dole na dauki mataki danyaga nazuba
masa ido ne shiyasa iskancinsa ke ta'azzara harni zekawowa batun banza,
Shiru sukayi suna saurarenta dasuka masifarta bamekarewa bace suka barmata gidan,
Wanka kawai tayi komai bata shafa ba tasaka kayanta suka nufi gdan majid,
Suna tafiya kafin su samu adaidaita tana faman mita,
Yaushe zanyadda atura yarinya gdn mijin da bataso, daya aka kare ma da auren soyayyar balle
Wanda babu ko digonso acikinsa,ga yaron fandararre wallahi dasake,
Har suka samu adaidaitan suka isa gdn surutu take har tsoro tabawa lubna ,wannan mita har ina er
tsohuwa?
Batakobi takan lubnar ba ta shiga gidan dakin safara'u tafara zuwa taringa buga kofa amma bata
bude ba dole tahakura tayi bangaren badee,
A kwance suka sameta Palo tayi shiru tana tunanin abin duniya,
Gaisawa sukayi da Hajiya ta kawomata Dan waken datayi yau dashi suka karya kuma dashi zasuyi
abincin rana,
Kai amma er nan kin kyauta dama inajin yunwa da babu komai acikina tunjiya se ruwan kunu,
Allah sarki Hajiya yakika zauna da yunwa kunu aiba ya rike ciki?,
Badi babu komai gidan se farar shinkafa komai babu, er wannan yarinyar dake gurina
shekaranjiya uwarta tazo ta dauke ta wai aure zasu mata banida Dan aika ga su Abdul ma
sunkwana biyu basujemin ba,
Zaro ido badee tayi tace, Hajiya zama ke kadai a gida babu dadi ko zaki tafi da lubna ne?,
Bazan je da iyaba kema ai kina bukatarta sedai inkosu Abdul dayansu ze koma can,amma lubna
kam kodan Wannan munafukar matar ta majid bazan daga da itaba Dan nasan koba komai tana
tare miki wani abin,
Hakane kuma bari abdulrahim yazo muji seya fadi Wanda zekoma candin Allah yakauda bacin
rana kar wani Abu yataso bakowa kusa,
Uhm,ke dalilin zuwana gidannan abdulrahim yacemin wai aure majid zewa lubna kuma batason
mijin?
Eh haka
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500