ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

oho pls kafadan sai dai inka yadda na fadi ba dai dai ba xaka fadan ko wace eh naji wace inbanda zakiyya hhhh jafar yaushe ka fara duba yai dariya aiko karamin yaro xai fiskance ku gaba daya kunasan juna kun kasa showing kai kake ganin haka mata sunada wuyar fahinta kuna mutunci kana cewa kanasanta sai wulacin kaga ni shine banso hhhh to basan gaske kake ba aishi so bakaji ana cewa rigar wahala ba to dole kasata kafin ka warke.

Tun jafar da mubarak na boye boye harsuka hakura suka bayyana abinda ke ransu soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu yayin da zafira da zaem tuni sukai nisa asan junansu.

Jafar ya takurawa zara kan yanasan aturo dan hk tasamu muhd ta fada ms dan bata da kamarsa shine yasamu malan y fada ms yaiko farin ciki sosai dan burinsa ya aurar da zara'unsa

. manya sun shiga mgnar tun sa'adda umma taga irin kufin da ake kawowa na nagani inaso kawai hankalinta ya tashi sosai hankalinta bai kara tashiba saida taji sunan mahaifin jafar hankalinta ya tashi sosai dan haka ta tashi tsaye sosai.

Abu kamar wasa asirin da umma take ya fara daukan jafar dan insuna tare da xara sai yadinga jin haushinta zahra ta kasa gane kansa dan kullum ynx sai sunyi fada yaita mt fada. Takanas umma taje gidansu jafar ta fadawa umman jafar aikuwa tahau ta xauna fada kamar mai taima umma godiya.

Abu kamar wasa sai gashi yaxama gaske dan mahaifiyar jafar tace ita bata yadda adaura auran ba ta inda tashiga batanan tashiga ba mahaifin jafar bai dauki abin da mahimmanci ba ganin ya dau abin dawasa dan hk taje tasanar da innarsa taxo tai ta bala'inta indai yasake aka daura bashi ba ita yai ta bata hakuri dakansa yaje ya samu yayanta yace ya vashi lokaci danyai buncike.

Kawun nasa yakirashi kamar yadda nace mk xanyi bincike nayi abunda suka fada hakane yarinyar batada asali yayarsa taxo da ita daga kaduna kawu yafa tabvatar mana shine ya haifeta ehto koshi ya haifeta to bada aureba.

Inko haka ne gaskiya malan sule bai kyautaba ta yaudaremu aida sai ya sanar damu komai inmumga xamu iya muyi gaskiya koda inada niyyar dana ya auri yarsa tunda ya rufeni baxan yardaba.

Koda yakoma gida yakira jafar ya fada masa yadda suka yanke bai wani damuba dan daman kwanannan hanya kawai yake nema da xasu rabu balle kuma ga wannan mgnr .

Tun abin vai damun zahra har yaxo yana daminta rabonta dashi yau sati biyu kenan takirashi

yafi a kirga akashe wataran kuma ta kari ringing dinta yaki dauka tunaninta ko baida lpy dan haka yau tasa aranta after lecture xasu je gidansu itada su xafira dan dubo ko lpy.

Basuyi maganar ba jira take sai anfito ta musu mganar lecture dinma gaba daya batasan mai akeba duk bayan minti kadan sai ta duba wayarta ada indai xasu shiga ajaka take ajiye wayar anman yau tana hannunta ji take karta ajiye jafar ya kirata kamar ance duba ta duba alamar sako ta gani ya shigo tana ganin daga jafar ne ta saki wani murmushi da batasan ma ta sakiba bata wani jiraba ta bude shi.

*Assalamu Alaik*

*Bana bukatar tambayar yaya kike ko lafiyarki dan banjin kin cancanci haka*

*Zahra ban tabajin ko ganin axxaluma munafuka macuciya kamarki bantava tsanmanin kedin haka kike ba zahra kin cuceni mai yasa tun farko kika kasa fadan ke wace ko da yake kinso munafinta ta keda macucin marikinki da kike fafa dashi inasan kisani ki kuma daka aranki babu ni babu ke ki mance dani pls kamar yadda na dade da cireki araina kitaima kawa kanki ko sunana kikaji karki tuna dani balle kiyi tunanin kin taba soyayya da me sunan*

*Jafar*

Hawaye ne kawai ke bun fuskarta da gudu ta mike tabar ajin tama mance a lecture room take gaba daya suka bita da kallo malamin ya tabe baki gami da watsa hannu alamar i don't care ya cigaba da abinda yake.

Da'ace lokacin da zahra ta tari adai daita sahu tasan idan taxo gida abin da zata tadda kenan dana san wani gun xata ce ya kaita ba nanba.

****************

Malan mahaifinta ta gani tsaye yana hawaye wasu mt na xaxxaga bala'i sina ganinta suka hada da ita sukai mta tatas taja malan sukai ciki dan ita saima taji gaba daya kukan ya dauke.

Ada zahra vata taba yadda malan bashine mahaifinta ba bata taba yadda batada iyaye ba sai yau tabbas buri yayi kama da mutun dan ko bahaushe yn cewa ba rami mai yakawo rami.

Ganin malan baijin dadi tun bayan abunda ya faru yasa zahra takasa tunkararsa da batun da ke ranta duk tabi ta rame tai fiyat baka ganin komai sai dogon hancin nan idanunta sun fada alamar cuta.

Tun bayan cin kashin da'aka ma malan jiki yaki dadi kullun cikin cuta da wannan an samu ya lafa sai wancan tun yn iya fita har abu yaki dadi makarantarma xahra ba koyaushe take xuwaba tana kula da malan koda muhd yaxo hutu dakyar ya roki malan suje asibiti ai kuwa suna xuwa aka basu gado jininsa ya hau sosai ga xuciyarsa data kamu .

Hankalinsu ya tashi sosai abu kamar wasa ciwo yaki dadi daga karshema nasarawan suka maidasu Aminu kano.

Yau kam jikin dadan sauki zahra na xaune akan kujerar da ke gefen gado malan na bacci muhd kan tabarma yana bacci duda itama din ba cikakken bacci take ba tana dan gyangyadawa sama sama kamar daga sama taji muryar malan zahra bakiyi bacci ba tai saurin bude ido eh baba ya miko mata hannu tai saurin kamo hannayen gani baba kece zahra eh nice baba sai gani tai yana hawaye sannu baba ciwonne bari na kira doctor yi xamanki ba ciwo bane inaso muyi mgn kaf labarinta ya bata har yadda yaxo gurinsa kiyafemun xara'una naso kaina da tun farko ban bari kinsan iyayenki ba ban bari kin taso da sansu ba sai nasa miki sona da kaunar yan uwana na bari kullum addu'arki akaina take karewa bacin iyayanki suka fi bukatar

addu'arki tasa hannu tana goge masa hawayen yayin da nata yaki tsayawa haba baba ka daina

neman afuwata ko kadan ni baka mun komai ba nasan kamun haka ne dan kana sona duniya banda wani uba bayan kai umnata kuma Allah ya jikanta kije dakina xakiga wata akwatu to ciki akwai dan wasu abu buwan na ummanki to baba Allah yakara sauki jitake kamar tai tsuntsuwa taje gida dan yau xatace ta rike wani abu na ummanta .

Washe gari sukai sallama da malan tai gida dan kawoma muhd abinci.

Tana xuwa gida dakin malan ya shiga tahau dube dube taiko sa'ar ganin akwatun a kuryar daki jikinta na tawa ta bufe ba komai sai hotuna guda biyu sai yan takardu na makaranta ta bude hoton matasa ne guda biyu mace da namiji sanye da uniform din hygiene sai dayan macen ce kawai .

Kallon hoton take cikin ranta tana jin dadi duk su biyun sun kwanta mt arai wani sansu ke shiga ranta ta rungume hoton a kirjinta sai takejin dama ummanta ce ta rungume da yau tafi kowa jin dadi bata wani dade ba tai asibiti dan tanasan xuwa ta tambayi malan ko dayanne mahaifinta duda kuwa taga kamarsu daya amman tafisan tabbatarwa.

Su aunty xulfa tagani duk sunyi tsaye a bakin dakin muhd nakai kawo tai saurin xuwa gun anty xulfa aunty lpy ya jikin baban yana ciki tun daxu likitoci ke kansa ana hira kawai sai haki kinga har yanxu basu fitoba sai hawaye wayyo babana Allah ya baka lpy kaine gatana kai kadai karagemin banida kamarka xulfa ta ruketa kiyi shuru zahra xai warke Doctor ya fito yana share gumi gaba daya sukai guns ya kallesu ya dubi muhd biyo ni office ku kuma ku jirashi sukai office din.

Naga kai kadaine na miji yan uwan naka duk mata ne nasan xaka fisu dauriya duniya ba matabbata vace komai yai farko xai karshe sai kunyi hakuri likita ban fuskance kaba ya jikin malan din jiki kam yayi sauki cuta ta tafi na har'abada malan yaje inda ba'a dawowa muhd yasa salati sai hawaye likita bai hanashi ba sai dayai mai isarsa sannan yace Allah yajikanka baba ynx likita xamu iya daukan gawar yana fita gabaki daya su shidan da yayansu da sukaxo sikayo gunsa yana ganin yan uwan nasu sai kuka tausayinsu ya kara kamashi musanman zahra suna ganin haka suma suka fara kuka aka rasa mai rarrashin wani muhd yai ta maxa ya je yasamo mota suka dauki gawar sai gida.

Zahra bata kara yadda ta rasa malan ba saida taganshi kwance cikin likkafani kan makara jitake kamar karya ne babanta xai tashi masu daukan gawa suka daukeshi sukai waje wani sabon kukan yaxo mata ta mike xata bisu juwa ta debeta ta xube yub jama'a suka kanta.

A hankula take bude idanta da xatonta aranta tana fadin Allah yasa mafarki nake anman mai mai makon ta dora idanta kan malan kamar yadda in ta suma shi take gani kanta sai ta dora kan wasu kuka ya kwace mata shikenan na rasa babana mai sona tasani duniya bata da kamarsa wayyo ni na shiga uku shikenan babu wanda xata bugu kirji tace shidin mai santa ne tasani komai da yafaru akan ta ne wayyo kai cona .

Bayan arba'in malan salihu abokin malan ne yaxo da wasiyar malan kan yace yanasan a hada auran zahra da muhd sannan ya bata dakin mamarta kyauta daman gadon yayar tasa ne ta kuma bata da sahannun doctor sai shaidu biyu umma ta hau ta dire ina wallahi bata yadda shiko muhd yace ina sai ya cikawa babansa burinsa.

Tun tasowar zahra muhd yake santa saidai sirrin da mahaifinsa ya boye yasa ya kasa bayyanawa dan gudun wani abu ya tabbatar dashi ya bayyana baban ya rasu baxai taba yafewa kansa va.

Aure kam ansa rana komai anma zahra muhd sai rawar kafa yake waishi ango abunda umma

bata saniba yadda batasan auran xahrama haka bata so tanai ma muhd din karane kawai dan wani sa'inma intaga ya xage yana mata kalaman soyayya ko yana kokarin faranta mata har mamaki take wato shi namiji baida kunya ko kadan yama manta ita kanwarsa ce ita inyana wani abun kunyama yake ba.

Yau sauran sati guda auransu da muhd har mamaki take wai ita xata auri yayanta koya xasu xauna da umma ko xataso xurriyarta aikema kinsan baxata taba soba muhd ya tafi xariya dan karbo wasu takardunsa zahra na kwance umma ta shigo da sauri ta tashi xaune adan tsorace dan ita bata taba ganin xuwan umman ya xame mt alkairiba..

So nake in rokeki alfarma ki taimake ni ki bar gidannan dan Allah ki daure ki bar mn gidanmu ki tai mk ki bar mn xurriyarmu ta huta dan Allah kibarni ha karasa rayuwata cikin jin dadi ina tabbatar miki inkika ci gaba da xama damu tabbas nima ciwon xuciya xai kasheni kamar yadda ya kashen miji ta durkusa tana gawaye wallahi zahra na tsaneki ki daure kisa aranki kin taba rayuwa damu zahra ta mike basai kin rokeni ba xan tafi insha Allah xanyi abinda kika ce harta kai waje ta dawo au dankinga ina rokonki shine xaki dawo takarduna xan dauka ta diba dana ummanta tabar gidan gaba daya kwakwalwarta ta tushe ta manta da kowa da komai kidaure ki mance kin taba rayuwa damu abinda take tunawa kenan to yaxatai ta manta dasu kibar kanon kawai tabi shawarar xuciyarta sai tasha tana sauka a adai dai ta samu taji mai lodi na fadi kanya babura magarya batun yauba taji ana cewa magarya nijar ce xuciyarta ta ce to mai xai hana kibar Nigeria dinm tinda kowa yaki acikinta ta aminta da xuciyarya dan haka kawai ta shiga.

Hatsarin ya farune dai dao lokacin da suka wuce kanya wata mota ta tunkaro su mai motarsu yai kokarin kauce mata saidai mai ya kasa yai dadi inda ya daki wata bishiya baiko shura ba yayin da da dama suka suma wandama basu sumanba basusan inda kansu yake ba inkadaike

wani yaro dake kuka kan ummansa yana ta tashi rayika kam anrasa.......

*Zahra Yar'amana*

*95-100*

*Na F.A.Ya'u*

*wannan paging naki ne zulaihat Abdullahi isa (my zuly)*

Cikin wadanda basu san inda kansu yake ba harda zahra dan tayi mummunar buguwa ga karaya kafa da hannu banda daddaujewa.

Kai tsaye asibitin garin aka kaisu abin yafi karfinsu taimakon gaggawa kawai suka iya basu aka wuce dasu asibitin koyar wa dake xariya har sukakai su asibitin zahra batasan inda kanta yake ba.

Sai da zahra tai kwana bakwai da barin gida sannan muhd ya dawo dauke da tsaraba kala kala wadda inka dauke tsirari duk na zahra ne a kokarinsa na kyautata mata daya ke da

yadawo masallaci ya wuce koda ya dawo daga masallacin yaga umma taxubo ms abinci iya

saninsa dik runtsi zahra ke zuba wa kowa abinci bai ce komai ba zatonsa ko umma ta sauya tsarin ya cinye ya baima umma tsarabarta bega tsaraba nan xuciyatsa ta dan zargu duda yasan xahra ta sauya anman hakan baisa ta dena bashi girma ba ya mike gami da ture kwanon abincin yai dakinta wayam yaga dakin sai kura da tarkace da yada da haushi yakara kuleshi iyakar saninsa da zahra bata kaxanta tun tn yarinya to dan mene se ynx data girma adan fusace ya fito yana tambayar umma wai ina yarinyar nan ta shigene taji tambayar kamar daga sama gabanta ya yanke ya fadi ta hade rai wacce yarinya fa umma zahra fa nake nufi au kace karuwa haba umma inda kara kodanni aikya rangwantawa xahra yanxufa surukarki ce ta xaro ido rufan asiri dannan Allah ya kiyashe ni da surukuta da wannan tambadaddiyar maras asali naji umma ynx dai tana ina tatafi yawan ta zubar dinta kasan ta tsotsa a mama yadan kada kai umma mai kike nufi abinda nake nufi shi nake nufi yau rabonta da gidannan har na manta rabonda nasata a idona kwana bakwai mun kwanta da ita bamu tashi da itaba kasan tsintacciyar mage malan kesanta anman ita batasan malan da xurriyar malan tunda gashi dan kawai yace ka aureta ta gudu bai karasa jin batun ummanba yai waje idansa ya kada yai jawur iyakar kololuwar tashin hankali hankalinsa ya tashi fatansa Allah yasa tn gidan su zaem koda yaje suma hankalinsu yai mummunan tashi dan bataje ba tun rasuwar malan sukai sukai ta dawo tace tunda da ran malan bai bada itaba bayan ransa baxata vada kanta ba gidansu xafira yaje da xakiyya suma hankalinsu atashe yasa mesu dan sunxo nemanta fanin bata xuwa sch umma ta koresu.

Duk inda muhd yake tunanin zara na xuwa yaje ba labarinta nan ya kom asibitocin dake garin

kano da police stations babu koda mai kama da ita.

Muhd ya kasa dangana akullum ranata fito akullum sai ya fita sati uku kacal da batan zahra yabi yai baki ya rame muhd da yake fari doga mai yar giba dedai shi shine yai baki ya rame kai kace yai jinya ne.

Tun jafar naganin abun kamar wasa har'abu yaxama babba kullum baya iya bacci sai tunanin zahra tabbas koda jikinsa sun abince sun br xahra xuciyarsa baxata taba iyawaba sai ayanxu yakejin haushin kansa toma wai ada mai yasameshi bashi da buri ayanxu inbanda yaga zahra yasani da wahala ta iya yafe ms anman xaiso gwada sa'arsa koda sau dayane shi ya amince koda daga sama ta fado yanxu xai aureta.

Yau yai niyar zuwa har hall dinsu dan bata hakuri ko mai xata mai yaji xai jure yau sati uku kenan yana jele tsakanin faculty dinsu danasu zafira baya ganinta inda suka fara haduwa kuwa kullun sai yaje babu kosu xakiyar yasani tanasan gurin tasha fada masa watakil yanxu ta tsani wajen duk lefinka ne inji xuciyarsa .

Yau kam lecture dinsu gabaki daya ba wadda bai shiga ba saidai ba xahra dan haka yana fitowa yai faculty dinsu zafira koxaiga daya daga cikinsu zafira ya hango suna mgn da wani ta hangoshi ta hade rai baima kula da yanayin fuskarta ba dataga da gaske ita ya doso dasauri tace muklis mu hadu anjina ok yace tai saurin yin gaba ganin haka yasa yadan dada sauri pls zafira badanniba dan sanki da annabi dan girman Allah ki tsaya kariga ka cuce ni ka hadani da wanda ba'a hadani dashi nakiyi minti uku xan iya baka taja ta tsaya inajinka daman xahra nake san gani tadan xaro ido ne kace yasan taji bai kasa aguwwa ba ya mai maita wai wace xahran kake nufi xahra nawa kikasan inada ta tabe baki lallaima kai harkana da karfin guwar kiran sunan xahra ka kirata taka kai harka na da damar kiran zahra taka mai yasa ne wasu mutanen

gabaki daya basa aiki da kwakwalwarsu to inasan fada maka burinka ya cika zahra ta bata inma

neman ta kake ka karadata to sai kaje ka xuba ruwa a kasa kasha tai tsaki tabarshi nan tsaye kamar dutse.

Tunda ya koma gida ba'abunda yake iya tunawa sai batun zafira burinka ya cika zahara ta bata gabaki daya haushin kansa yakeji yakasa ko sau daya yaji xafin xafira na maganganun datai masa da gaske xahransa ta bata kuma a dalina gaskiya baxan tava yafema kaina ba.

A hankula take bude idanta dishi dishi take gani daga bisani ta dora idanunta kan fankar dake wulgawa a ta maida kallonta gefe inda tai arba da robar jinin dake shiga jikinta gefenta kuma wata ce kwance daure da robar ruwa hakan ya tabbatar mata tana asibiti ne ta yunkura xata mike da sauri doctor din dake rubutu kusa da ita ya komar da ita hihakuri kina da ciwo ne ta daga ido ta kalleshi sannu ko ya kike jin jikin bata ce komai ba kingaji da kwanciya ko tai shiru nurse da ke baima wata magani ya kira sister tagaji da kwanciy xaunar da ita to doctor ya wuce daya gadon sai da yagama round dinsa ya dawo gadonta badai abin dake damunki ko bata ce

komai ba illah ta bishi da ido.......

*Zahra yar'amna*

*100-105*

*Na F.A.Ya'u*

Baxan gaji da gode miki ba

Zulaihat Abbdullahi Isa amaryar gobe.

Asannu ahankali jikin xara ya a kyau yau satinta na biyar kenan a asibiti yanayin kulawar da likitan ke bata yasanya tadan bafara sakin ranta dashi yadamu sosai akan rashin lafiyarta duda ta kula halinsa ne haka bawai ita daya yake ma haka ba duk marasa lafiyar dakin na yabonsa.

Sunyi sabo sosai da doctor nasir dan har mahaifiyarsa ya kawo ta dubata abincinta da magani duk shine.

Yau bashi da aikin safe na dare gareshi dan haka yashigo asibitinne dan duba jikin xahran xaune yake kan kujerar dake gefenta suna fira kai kace sun shekara da juna can yace kinga yanxu kin warke sarai sai abinda ba'a rasaba ina xatonma jibi xamu baki sallameki tai dariya ai doctor da temakonka komai yai dedai intambeki mana inajinka wai ko ina xakuje kukai hatsarinnan taishiru can tace magarya yai dariya ashema yar kasarmu ce kinsanfa babana da dan niger ne a wane unguwa kuke a magarya nima bansani ba tace yakada kai badai kyasan fadamun to yanxu bananba ko number din wani naki ne kibani nakirasu dansuxo daukanki sai hawaye nan yahau rarrashinta saida tai mai isarta haba zahra kiyi hakuri mn innan miki wani abu kiyi hakuri ta share hawayenta doctor baka mun komai ba wallahi tunawa danai cewar banda kamar kaina bani da wani daxan bugu kirji inkira da masoyi na yasani kuka uwata ta rasu marikiyyata me sona yarasu babana yarasu banda sauran wani da xankira mesona haba zahra rashin iyaye bashi ke nufin baka da kowa ba sai kace mara dangi taisaurin cewar haka nake doctor banda dangi iyayena basu da dangi yakada kai kodai kin bar gidane bakisan komawa ta fuskanci me yake nufi wato zata yawon duniya nan ta baahi labarinta tun daga wayonta har yaxuwa inda sukai hatsari ya tausaya mata sosai .

Koda ya koma gida yasanar da iyayansa komai na xara suka tausaya ya rokesu alfarmar zai

kawo zahra gidan suka amince.

Koda aka sallami zahra kai tsaye gidansu zahra aka wuce da ita dakyar nasir yasha kanta ta amince dan cewatai tafisan tai rayuwarta ita kadai bata son takara sabawa da wasu karshe su gujeta karba ta mutunci ta samu kannensa biyar Fadima ita ce kusan sa'ar zahran dan haka dakin fadimar ta sauka duda tadan girme mata .

Yanayin yadda suke mata yasanya ta gamsuwa iyalan gidan sun san darajar mutum ko daki ta shige sai fadima ta kirata tun tana dari dari harta sake ana komai da ita duda har yanxu tana dingisawa haka ta daure komai na aikin gida take yi duda kuwa sunada masu aiki.

Yau suna zaune a falo tadan kalli mumy mami pls ki rokar min dad atai maka a bincika mini kayana gurin police tai dariya yanajinki ai yace indai bata da bakin fadi mini ni baxan jeba tai dariya pls dad to shikenan xan dubatai godiya.

Dady da mu'allim da ita sukaje suna gurin aka bugowa dad waya yanada baki a office anan ya barta ita da mu'allim ya wuce an futowa da zahra kayan tai sa'anata yananan da yake yan tarkace ne takarba sukai gida da mu'allim.

Hoton ummanta kuwa kullum sai ta kalleshi na tsawon lokaci kafin tai bacci ji take kamar ummanta ce take kallo wani abu dake bata mamaki bai fice daya saurayin dake kusa da ummanta ba kamarsu da dadinsu Fadima take gani sai dai takasa yadda gani take kamar

idanunta ke ganin haka dan haka tabar batun aranta.

*Zahra Yar'amana*

*105-110*

*Na F.A.Ya'u*

Yau zahra sun fita da fadima dan dady yaima abokinsa dake nan college of health zariya mgn kan yanasan form yai sa'a kuwa yace taxo ta karba dan ya gaji da xaman da take saidai tai girki ta kwanta yai takaicin katsewar karatunta dan cewarsa damar da tasamu bakowa kesamunta ba ta karatun likita.

Gidan shiru nasir ya shigo yan aikin gidanma duk suna bangarensu mami ce kawai a xaune tana kallo ya xauna kujerar gefenta gami da cewa wash ta dan kalleshi yadan rissina mami sannu da gida ta amsa da yawwa yau ina yan matanki naji gidan shiru daxunnan suka fita nasan yanxu suna hanya nasan wannan uwar gantalin ce ta jasu ko tai dariya kaidai kanasan dorama fadima lefi to ba ita ce ta jasu ba aiken dady ne yasosa keya alamar jin kunya ya mike yunwa nakeji wallahi yau mai aka dafa mn mutuminka ne ya yamutsa fuska kai fadima bata kyautawa wallahi tai dariya nasiru kenan to dai yau ba fadima ce tai girkinba zahra ce mami sanin tane bakiyi ba tsaf xatasa zahra ta dafa dan tasan banso oho dai kaji dashi Allah dan inajin yunwa ne da baxanci ba kaga ni karka isheni inbaka ci xaka iya bar mana abunmu be kwantai ba yaxanyi haka xan tuttura.

Duk runtsi nasir be cin abinci awaje danshi irin mutanan nan ne masu kyan kyami hakan yasanya dasunyi tsiyar da yan matan gidan sesu fara dafa abinda beso musanman fadima da basa rabo da hatsaniya seta jera sati tana girka abinda beso.

Yana mita ya bude kular hadadden kule le ne a ciki wanda yaji hanta kwai da attaruhu kamshin ya bugi hancinsa baisan ya cinye duka biyar dinba sai da ya tsiyayi lemon dake gefensa lemon amarba hade da madara mai sanyi yaji wani sanyi ya xiyarci kirjinsa yakai hannu

dan sake diban ala la yaji wayam mami ya fada ta kaga ni ka isheni inbaka ci kabar min abuba

ba adole wai kuwa kinga abinda suka ragen a'a tace wai aras mai xa'a ragen sai alala guda biyu tai dariya ni nadauka ma daya ne kaida baka iya cinye biyu haba ashe daya ne nake xaton biyu ne shiyasa ban koshiba tai dariya gaskiya zahra ta ciri tuta ka cinye alala biyar kace biyu ne na sara mata ya suri jug din lemon mami se nadawo ina kuma xaka min da kofi mum kinsan aiki inyai yawa in ina korawa dashi na rage xafi tai dariya ashe iskanci ne da yake sawa kake cewa bakasan kule le yasosa keya mami duk cikin yunwa ne kaji dashi ta fada.

Koda su zahra suka dawo sunci dariya ai kuwa da ya dawo fadima ta takura masa da tsokana yai dariya ai duk cikin yunwa ne kaidai kawai kace kaji dadin abinci eh naji kema kiyi xuciya ki iya adinga jin dadin naki ki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment