ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takemaba sai yarta itace abin

tausayi.

Watanta tara da haihuwa ta kuma gwada xuwa gida aka kuma kwatawa bama su tsaya suji

bayanintaba ko ganin abinda ta haifa suka korota ta dawo kaduna.

Tun dawowarta daga kano jiki yaki dadi ciwuka kala kala ga ba dangi kusa sai wata makociya dake kula da ita.

Shekaran zara biyu tana gudunta ko ina harda dan gwarancinta yarinyace mai shiga rai tashaku da makociyarsu ita take mt komai wani sa'inma agunta take kwana itama ta yayeta.

*****************

Yaukam jikin dina yaki dadi hajiya barira keta bata baki kan ta rage damuwa sai tai murmushi umma kenan nidai ko bayan raina kitaimakeni ki riken xara koda babanta xai dawo kibashi

diyarsa haba kekuwa cuta ba mutuwa bace sai kikaga kinga girmanta ni ban ganiba.

Zara xaune keta faman bugun uwar da gwarancinta ki tashi ta mike ta dauko takalmi yadda taga tanayi kamar xata daketa ganin bata kulata ba sai kuka umma barira ta shigo haba dina yaxaki bar yarinya na kuka aiko yadda ta ganta ya kidima ta subhanallahi ta dauki xara aiko babu uwar

ta mace.

Tun rasuwar xarah babu wanda yaxo gurinta dan naiman xara haka take ta kula da ita itama

fa sai kansar mama dan haka kaninta sunaiman dake kano yaxo ya tafi da ita da yar amarta.

Tun zuwansu gidan matar malan furai tabi ta tsani yarinyar dan kawayenta sunce watakil yar

malan dince yayarsa ta rufa masa asiri ta rike yarinyar ko lekowa batai dan in ba haka ba kuwa taci na jaki.

********************

Yayan malan biyar hudu mata daya namiji duk sunyi aure muhd ne kawai agida Allah ya hada

jininsa da xara duk yadda umma taso rabasu ta kasa hakan yasa take cewa xaran mayya ce. Muktasira itace babba zulfa mai bi mata sai bilkisu mansura itace karama

Muktasira da bilkisu kamar uwarsu sike sun tsani xara vabu irin hantarar da basa mata indai sunxo gidan.

Mansurace dai ba sawa ba fitarwa bata shiga sabgarta yayinda zulfa ke tausayin yarinyar ko kwancen kayan yayanta ita take kawowa har saboma tana kawo mata halin malan gaba daya ta

deve su.

Ko bayan rasuwar umman xaran zulfa tace xata dauki xaran umma tace indai ta dauka sai ta tsine mata lokacin xara na primary 3 aiko axaba kala kala dan daman idan umma nasa wa

arage mata.

Makarantarma sai ta gadama take barinta duka ba kama hannun yaro abinci ba koyausheba

duk wai tanasan ta mutu.

Maganar xara da yaji ya katse ms tunanin da yake tace baba kuka kake yace a'a gumi ne ta

yun kura xata mike bari naima fifita sai ta kasa wash kafata sannu xara kiyi hakuri asannu xaki warke to baba.

Wajan hudu zaem da kakarsa suka xo dan tun da yakoma yabata lbri tace xata xo koda malan yagansu yaji dadi duda bai sansuba sai yaji ya yarda dasu ya barmusu xara yace xaije gida ya

dawo .

Koda malan ya koma gida baibi takan furairaba wanka yashiga sannan yaxo dan yin sallah itako koda taga yadawo shidaya batare da gawa ba sai takaici duk ya rufeta dan taso ace ta mutu duda tana tsoron kar axargeta.

Sai bayan yama idar da sallane ya tuna baiko ci abinci ba tun karin safe tana kallonsa ya gama komai xai fice bata tambaye shi mai jiki ba malan baxaka ci abin ci bane yako watsa mt wani

kallo gami da tsaki ya fice.

Saida ya tsaya ya sayi biredi duda bashi ya dauka sannan ya wuce asibiti sunanai sai dai xaran na bacci zaem ya fice inna nabgefe a xaune suka kara gaisawa da da malan sannan take kara tambayarsa mai yasamu xahran yake fadi mt ai gini ne ya fado mata ta nuna tausaya warta sosai kafin su tafi harda ajiye masa kudi gashi koxa'a naima yaiko ta godiya.

*******************

Satinsu biyu a asibiti aka sallamosu ta warke sosai saidai karayar dataine sai ahankali.

Duk xaman dasukai a asibiti umma furai bata taba koda dawasa tace ma malan yamai jiki ba balle tai gigin cewa xataxo dubata a asibiti balle kuma sauran yayanta inka dauke mansura da taxo sau daya sai xulfa da kullum sai taxo muhd kuwa shi yaxama mai jinya harsun saba da xaem kai kace sun shekara danshima kullum yana tafe shida kakarsa.

Makotansu xaran kuwa kullun sai an samu mai xuwa.

Koda suka koma gida ma kullun gidan akwai masu xuwa kaxalika da abinda xasu kawowa

xaran ko an baima umma cewa take bataso duda kuwa ranta naso.

Ko agidanma umma bata kalletaba balle tamata sannu kallon kirki bata isheta ba dan tafuskanci malan babu abinda xaiyi sai muxurai duda kuwa randa xasu dawo yaja mata kunne

kan xaran takuwa ji dan saidai hararar ba damar duka.

Yadda xulfa'u ke wani kula da xaran ke mata girki yasa take masifar jin haushinta harma fiye da muhd danshi tace xahra ta lashe ms kurwa kumadai tafi sansa dan tace da namiji jari.

Ba'abinda ke kaita dakin xahra sai abinci shim daga bakin kofa take tura mata tai gaba.

********************

Zahra ta warke sosai dan harta koma makaranta ayanxu komai yai mt sauki tun wani duka data mata malan bayanan makota suka kira mt hijba shikenan ta dena dukanta saidai uban aiki dan ita in akwai abinda ta tsana jami'ai masu saka uniform dan haka saidai xagin da masifa agidan in malan bainai xara da ita damai xaman kanta daya ne babu kwaba ina xaki ko ina kikaje babu

ruwan umma dik dadewar daxarai aguri ita burin umman yau yarinyar ta lalace tunda dai taki

mutukedai.

Tun kwanciyar xahra a asibiti xumunci ya kullu tsakanin gidansu xahra da gidansu xaem dan har hutu take xuwa yi musu sunyi harsun gaji kan malan din yabasu xahran yace ina shi xai rike

diyarsa.

Awoyi na shudewa kwanaki na tafiya kaxalika shekaru yau take ranar farin ciki gurin xahra dan yauce final pape dinsu a waec wadda daga ita sunyi bai bai da secondry murna gurinta ba'a mgn tun jiya da dare in tafarka saitaga still dare ne gani take goben taki xuwa gashi kuwa taxo burinta ya kusa cika xata kammala makaranta ta auri isma'il dinta abinsanta wanda tun tana karama batasan kantaba yake kula da ita ko lokacin daxata tafi garko malan baisan boarding shi ya sama mata day science lokacin yana teaching a science and technical lokacin da ya kammala masters dinsa yasamu lecturing a northwest university dan ashekarar aka bude ta

duda kuwa da karancin shekarunsa.

Umma furaira bata taba daukan batun ismail da gaskeba sai da taga ankawo kudin aure har dubu hamsin kai hargidan daya gina saida munafukai suka kaita aiko hankalinta ya tashi dan ko rabin kudin auren ba'akawo ma yayanta ba acewarta babu ta yadda bare mara asali xatafi yangida kuma ba yanxu ta shiryama auran xarah koma xatai aure tai alkawarin ba inda xata

hutaba.

Aikuwa takanas ta aika muhd ya kira mt atine dillaliya ta saida mata kayanta kawarta xata

rakata gurin malamanta tace indai tana raye saita hana aurannan ko xata tafi tsirara.

Yayin da adaya hannun dangin zaem sunma malan kara dan kayan daki kam sun kammala mata malan sai xumudi yake burinsa sai cika xai aurar da xarah duk yayansa inkadauke xilfa da muhd shima da yake yana xariya babu mai farin ciki duda kuwa umma tacema xulfa inbata cite hannunta kan mgnar auranba sai ta tsinemata hakan yasa ta dena zuwa ta koma haduwa da

xaran gidansu xakiyya xaton umma ta ji batunta.

Iya kololuwa hankalin umma yakai ga tashi ganin kullum batun auren kara karfi take kudinta nata tafiya abanxa dan xara duda ta taso cikin halin rashin kwaba mutunce mai ruko da addini

bata sakaci da addu'a kaxalika shima angon.

Kinsan mai sai kin fada na gano mana mafita kinga inbatun yandanfarar malaman nanne kibarni dan Allah ke matsalata dake kin cika garaje tunda munbi tacan va'adace ba inkina dabkudi kawai gobe kishirya sai kura me kuma xamuyi acan acandinne uwar ismail ke aure muje mukitsa mata xata iya hana auran kema daba dankiba kike gyashin ya aureta inaga uwassa

kinkawo shawara Allah yakaimu goben kedai.

******************

Da duku duku haka suka tafi kasan tuwar malan baya gari ai kuwa tara ma acan ta musu saka

makon binta tasan gidan sun kuma saba da mahaifiyar ismail din lokacin tana aure anan unguwar gini sunko samu karbuwa ai kuwa suka xugeta tas karya da gaskiya haka suka fada mata zaran mabai *shegiya ce* ai kuwa ta hau taxauna nasani dan bananan ne akeso a cuceni a batan xuria to wallahi baxai yiwuba bunkuma xanyi aurannan sai dai in bani na haifi ismail ba anman wallahi baxa'a yishiba binto ta xaro ido kibi suwa ai sai dai ki bari in mun koma kyaxo salon kijamana salalan tsiya sai yanma suka baro kurar umman ismail nata xuba musu godiya

banda kayan kauye data jibgo musu suka tawo rai fes burinsu xai cika.

Aikuwa washe gari sai gata taxo tanata kumfar baki ba irin fada da rashin mutun cin dabatai ba wai tasan makircin marikiyar ismail dinne dan mai baxata yadda nata dan ya auri xaran ba ke banda abunki da nawane yace yanaso wlh ba abinda xance to muna fika wallahi bada dana ba baban ismail ya hau ya dire sai anyi.

Takanas taje gidansu xaran ta wanketa tas umma na xugata itadai xara bata da ta cewa sai kuka

Ganin da gaske baban ismail yake baxai fasa auren ba yasa ta kira ismail kasani wallahi ko bayan taina inka auri yarinyar nan wallahi ban yafe maka ba yanxu kuma in ka aureta wallahi saina tsine maka wlh kagi na rantse yana kuka yana bata hakuri ina bama ta kwana a unguwar ba .

Ala dole ismail yasamu mahaifinsa kan ya fasa ya hakura juyin duniya ya fadi dalili yaki to wallahi baxaka maidani karamin mutun ba inba dalili wallahi sai anyi nan ya fada masa komai yanxu ita kubra abinda ta daukanma kanta kenan ai bakomai xan samu mahaifin yarinyar to baba na gode kayanma abar mata basai ankarbo ba to shikenan Allah yamaka albarka.

Koda ya samu malan ya fiskance shi karkaji komai ba abinda xai samu alakarmu kasan mata sai hakuri kaya kuma kuxo kukarba bakomai wlh ai yariga ya barmata to shikenan Allah yasaka da alkairi.

Nasiha sosai malan yama xahra kafin ya fadi mata abin da yafaru aikuwa bata gama sauraron abinda ya ke fadeba taji komai ya dauke mata sai ganinta yai ruf ta fadi subhanallahi yai kanta

xara'u xara'u....

Dasauri ya debo ruwa ya shafa mata a fuska kamar sau uku sannan ta saki ajiyar xuciya idonta ta dora akan baban nata ta fada jikinsa tana kuka dan Allah baba karka fadan ba mafarki nake ba ya dagota haba xara'una karki bani kunya mana kefa mutunce da nasanki mai tawassali kiyi hakuri daman Allah yayi ismail ba mijin ki bane ki cireshi aranki Allah xai kawo miki wani wanda ya fishi ta share hawaye anya kuwa akwai wanda yafi ismail kul ki daina fadin haka kinji ko in akace Allah ba'a kawo komai kinji ko to baba yawwa xahran babanta.

Koda ismail yaxo gidansu xahra kin fitowa tai dakyar malan yasa ta fito yadda ismail yaganta ta kara bashi tausayi saiyaji kamar ya bijirema ummansa basuyi wata hira ba sai baki da hakuri dayai ta bata tana kuka yanayi duk dauriyarsa haka suka rabu tana ganinsa har yabar lokon nasu dan akafa yaxo yana barin lokon wani sabon kukan ya kwace mt da gudu ta shige gida. Abinda ya faru yasanya xaran cire batun makaranta aranta dan tasan daman shine xai samo mata makaranta duk tabi ta rame ta kara baki takasa cire ismail aranta.

****************

Wata uku da yin haka zaem yaxo hutu dan yn abuja can gidansu da yake acan yake karatu ya

tausaya ma xaran nan yake tambayarta makaranta tace ai ta hakura da karatun haka yai tamata nasiha ya karbi takar dunta kan kace mai ne yasamo mata health technology.

Fara xuwanta makaranta da yadda suke cudanya da jama'a yasa ta fara cire komai aranta dan daman harda kadai ci duda karatune bana wasaba anman xara tafi da kyan fani tayi kiba fiye da kwanaki sunyi nisa da yake ijmb take ana fara saida form din jamb muhd ya sai mata lokacin yi nayi ta je ta xana tai sa'a kuwa ta samu sosai tai murna sosai.

Kasan tuwar har yanxu muhd baya aiki yasa umma bata taba tunanin karatu wata hanyace ta cigaban mace ba dan danginsu duk suna kauye ita gurinta cigaban mace ta auri miji mai kudi hakan yasa bata taba yunkurin hana muhd yima xara hidimar karatu ba .

Xahra tanasan makaranta burinta akullum ace taci exam dinsu dan taje ita bata burin xuwa university.

Koda aka kafe exam din babu sunan xahra wato bata ciba aikuwa tai kuka kamar mai muhd yai tamata nasiha harta hakura.

Koda aka fara bada admission a buk tai sa'a sun bata abinda ta naima wato MBBS .

Karatu ya kankama tayi alkawarin baxata kuma barin damuwa tasanyata ta fadi a karatunta ba komai tare suke da xakiyya wadda take biochemistry tare sukai primary anan unguwarsu daya sai xafira wadda take lab science ko fa duk rintsi tare suke xuwa tare suke koma .

Yau zafira bataxo dan daman ita take kawosu xakiyya ta tafi capteria dan cin abinci ita kuma axumi take tace baxata iya rakata ba zaune take tana bin daliban da ke shawagi da kallo iska mai dadi na kadata har bata sanin sa'ad datake sakin murmushi wanda ke kara ma fuskarta kyau.

Kamar ance daga idanki wani matashin saurayi ta hango ya nufo inda take tai kamar bata ganshi ba ta ci gana da kallon jama'a dan xatanta banan yayo ba kamshin turarensa mai ratsa xuciya ya daki hancinta tai saurin dago kai yaiko sa'a suka hada ido yako sakar mata murmushi tai saurin daike idanta sannu ko yace da ita ko xan iya xama mai xai hana mai xai hana da'alama kanwar tawa bata da rowa ta murmusa gefen kumatunta ya kara lutsawa ahankula ya fadi subhanallah shi bai taba ganin black beuty ba sai yau ita din xara ce cikin mt.

Zahra ba fara bace xamu iya cewa ma baka ce mai matsakaicin tsayi dan baza'a kirata doguwaba ta kuma fi karfin a kirata gajeria mai yawataccen gashin kai dana ido gashin girar ta akwance kamar an xana mt idanunta dai dai wanda suk dace da fuskarta bata cika hanci ba saidai ya dace da siririyar fuskarta bakinta dan karami wanda bai cika san mgn ba gashinta baki ne sidik wanda yake har goshi in har bata dauro dan kwali har gaban gishinba sai ka ganshi .

Shirun dasu danyi ne yace baki fadan sunanki ba tai dariya baka tambaya ba to ynx na tambayeki sunana zahra'u sulaiman jafar what ya fada tai saurin kallonsa ya daga mata gira ni sunana jafar sulaiman muhd tai dariya haba koda naji ashe kakale ne shiyasa ka isheni da mgn au isarki ma nai eh mn tun da kaxo nan kke xuba kamar radio kin mant tibi ne tai dariya naga alama anman dai ke sabuwar daliba ce eh wane faculty medcine wane course medcine and surgery masha Allah abinda kullum nake san naga mata na karanta tai dariya kai wane course ne biochemistry nai degree a unimed ynx ina masters dina anan kafin tai mgn xakiyya da ta karaso gurin tai mgn shine kina kallo xamu shiga lecture ko ki kirani ko dan wulakanci yi hakuri ban kulaba eh ai bakya kula ba tunda kinata soyewa kefa bakida m fa tai dariya har z ma banida ta juya ga jafar yi hakuri inata xuba bamu gaisa ba ai bakomai na xatama baki ganni ba

tunda na tawo kai na hango dan badan kai ba nasan ba lallai in ganta ba ka haskata yai dariya

kodai ta haskani ba sukai dariya baki daya kinga ni na wuce ya juya ga xarha kai wannan frnd din taki yar cafta ce ya sunanta zakiyya anman ba course dinku daya ba ko mai yas ka tambaya naga tace ta tafi lecture ke kina xaune tai dariya eh ita tana biokmiss3 ya kada kai bari na wuce to sai anjima.

Zahra yar'amana

50-100

Na F.A.Ya'u

Inda sabo ta saba in basu da lecture ko suna jiran daya anan suke xama tun insun xauna basa shiga sabgar kowa har yakai suna hira da duk wanda ya xo.

Yanayin yadda jafar yake nuna kulawarsa akansu dik abinda ya shige musu duhu yana kokarin fitarsu haske yasa suke kiransa yaya baya nuna banbanci yadda yake wasa da dariya da zahra haka yake da zakiyya da zafira baxaka taba cewa ga wadda yake so cikin su zakiyya yake koyama karatu takai ta kawo invasu da lecture xama suke suji karatun da yake mt dan ba karya ya iya koyarwa.

Duk irin gorin shegiya da umma ke mt bata taba yadda ita din shegiyar bace dan kullum baba cikin kareta yake shine babanta bata taba yadda ita din ba diyarsa bace ko fasa auranta da ismail ce mt yai mahaifiyarsa ce bataso dan taima danta mata abu daya tasani tai makanta alkawarin cire duk wani namiji aranta da rayuwarta ko waye kai dik yadda kuke kana kawo mta batun soyayya kun bata.

Juyi kawai yake yakasa bacci in ya rufe idansama zahra yake gani tana sakar masa tassausan murmushinta akullun ya tunkareta da batun da ke ransa sai yaga tana ms wani kwarjini kullun ji yake santa na karuwa cikin ransa xumbur ya mike daga kwanciyar da yai dan tunawa da yai da hirarsu da mubarak watakilma kana nan kana haukanka ita tanacan tana da wanda takeso kananan tana faman kiranka yaya waikai awayo xakai winning din love dinta sai dai ka ganta da ibin aurenta ina baxai yuwuba ya dauko wayarsa cike da kwarin gwiwa yau xai fada mt ya wuta ma ransa sunanta ya danna kira yanaji ya fara shiga ya gyara xama gami da kara kankame wayarba kunnensa kai kace in bai haka ba baxai jiyo mai take cewa ba.

***************

Har kiran ya katse bata daga ba akaro na biyu ya kara gwadawa sai yaji akace tsaki yaga gami da fadawa gado ya shiga tunani karar wayarsa yaji kwanciyar da yai yaji dadinta dan hk baijin xai wani tashi dauka.

Yah jafar jiya ka kirani bana kusa naxo da gudu daukan wayar dai ta fadi nakuma biyo kiran kaki dauka ayimun afuwa yai dariya daman ba'a rikeki ba suka sawo wata firar.

Mutuncin su xara da jafar mutunci ne mai karfi wanda duk mai hira dasu yasan da wannan mutunci tuni mutuncin nasu ya shafi muhd da zaem dan sun xama abokai duda jafar da zaem basu taba ganin juna ba hakan bai sa sun kasa gaisawa a waya ba. Balle kuma shi mai uban gayyar babu wanda bai san da xaman yan matanba a gidansu musanman xaran.

Yau basu da lecture dan haka ta roki malan tanasan xuwa gidansu xaem dan yi week end malan bai hn taba dan inda sabo tun tn karama take xuwa.

Akofar gidan dan sahu ya sauketa malan wato kakan xaem yana kofar gidan kamar koyaushe

indai yamma tayi anan xaka ganshi yn jan carbi ya ganinta ya washe baki ita m ta saki fuska ta durkusa ta gaidashi kafin tace dan tsoho ana nan ana kwashe ladan to ya ranki so kike in mace ko dan karki auri tsoho ai kai mutuwa ba ynx ba sai mun mace mun barka gadin duniya yai dariya wani rufan asiri da gadin duniya aikai dinne bakasan mutuwa in ba gadin duniya ba mai xakayi ko istiqfar din dakai m ya isa yai dari ai inxan shekara dubu bai isaba baba kenan waya ganka da shekara dubu tab yankwani tasa dariya bata jira amsarsa ba tai ciki bari naje gun daya tsohuwar karta ce in koma ya bita da kallo yana dariya yarasa mai yasa yakesan yarinyar sun saba sosai tun tana karama yake gojen babanta ya bashi ita yaki anman jinta yake kamar su zaem kodan baida jika mace ne oho.

Da sallama ta shiga da ladidi sikai ka cibis bayan sun gaisa take tambayarta ina hajiya tn sama ta kada kai tai xamanta anan dan film din mutamin ta ake wato SRK .

Au zahra kece kika xo shine bazaki iya karasawa saman mu gaisa ba aikece mutun ya tsufa anman kullun yana sama gani nai ana wannan film din na xauna kalla ah koda naji aike duk inda indiyawa suke kinanan tai dariya Allah ba hk bane samanne baxan iya hawa ba yimun shiru mutum sai san jikin tsiya in baka motsa jikinka ai cutace xata kamaka hh wace cuta sai dai karame da'ace karame ai gwara ace kayi kiba eyye lallai ni da'ace ba karatun lpy kike ba zahra da anga shirme a hakanma mai makon kidinga abinda xai ciyar da lpyr ki gaba kinbar san jiki xai cuce ki kaga su kaka kenan kikga ni xoki hadan kayannan dasu gobe Alhaji xai tafi shago. Duda Alhaji ya tsufa yayansa sun taso sunai ms komai hakan baisa yakashe xuciyarsa ba kullum yn xuwa shago in xaem nanan su tafi tare dan yace jira sai wani ya baka ko roko shike kawo raini .

Tunda zaem yazo hutu kullum yn gidan su zahra suna shan fira duk irin abinda umma ke mai bai kulawa.

Yauma kan hanyarsu ne na xuwa makaranta dan yace yau xafira ta huta shi xai kaisimu xai kuma xo ya tafi dasu hirarsu suke gwanin sha'awa zahra ce agaba xafira da xakiyya abaya tun kunnowarsu area din akan idan jafar karaf ya dora idanunsa kan xarah dake dariya hankalinsa inyai dubu ya tashi wani kishi ya cika masa rai..

Saida suka dan jima a motar kamar bazasu fitoba sannan zafira da xakiyya suka fito suna dariya ita kuwa zara fafur taki fitowa wai ita ba'anan zafira ke sauketa ba shi kuma yace wlh ba inda xai kara jin ya rantse su xakiyya suka fito fitowa yai yaxago barin da take ya bude gami da dan durkusawa haba kanwis pls ki futo kinga na rantse ta juyar dakai gami da makeshi alamar a'a ya kaikaici idonta yai mt gwalo karaf a idanta aiko tace vaxata fitoba yai saurin durkushewa ya km kunnensa pls kinga na rantse tai dariya daga yau saika daina saurin rantsuwa jafar yana daga nesa vaijin avinda suke fade saidai idanunsa na hango ms drama dun da suke idanunsa suka kada sukai jajur lallai yarinyar nan ta rainashi wato bama ta taba xata santa yake ba kenan ita tanacan da wani yi hakuri yar kanwata ki sauko xan saya miki ice cream da chocolate promise yace promise ta fito tana dariya yai saurin rufe motarsa da karki fito mn can ta hango jafar xai juya da sauri tai gunsa yah jafar ta kwala ms kira kamar karya tsaya xuciyarsa tace xamto jarumi mn ta karaso dan Allah kaxo ku gaisa dawa inkaje ka gani to baxani ba wallahi sai kaje me duda sun saba wasa yau sai yaji yarinyar ta bashi haushi tama raina ms hankali wato hartana da kwarin guwar nuna ms masoyinta ni na jama kaina ya fada dakaimai bansan mgnr ta fitoba dan haka ya maxe ban saniba bata cika jan xance va ita sai ta basar nadai fuskanci yah

jafar bakasan kugaisa da yah xaem sai yaji duk kunya ta rufeshi mai ys yacika garaje yai dariya

haba ni ba isa suka yo gurin kafin su karaso zaem yaxo ya mika ms hannu jafar ko eh ai na ganeka yai dariya mai yasa kannen nw sunce kai farine yah mubarak baki kaga in akace xa'a hadamu xan gano tunda kune kawai frnd nasu na kusa yai dariya ina mubarak din shi ance bakine kamar yar dunarmu xahra tasan da ita yake tace dadinta mai fadinma dunanne oho dai nafi wasu ko ba hk ba jafar sukai dariya baki daya.

Abu kamar wasa zahra tarasa mai yasa take jin zafin mata inta gansu da jafar koda kuwa ada tana ganinsu tare koya batasan ace baya kusa da ita suna hira to wai mai hakan ke nufi ta tambayi kanta sansa kike kishinsa kike xuciyarta ta bata amsa iba baxai yuwuba ta fada a fili.

*********************

Haba malan karka bada maxa mn karasa waxakai shakko koma ince tsoro sai mace kasan Allah danine da tuni anrufe wannan babin dan wallahi da tuni na fada mt uhum mubarak kenan ai garani na na iya fada mk kaida ka kasa fadawa kowa kabarshi yn nukurkusarka kai kuma ka vada wa kenan kaga malan bansan sharrifa ai shiyasa naga san na ramar dakai hhhh to wace sharrin naka ya hango

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment