ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþZahra yar'amana. 1-95

Written by

F.A.Ya'u

I am forever grateful to Allah(S.W.A)

In Dedication to my Parents.

My appreciation goes to Salma Ali Wada Zakiyya Aminu Ibrahim Hawwa Usman Ya'u

Rasheeda Isah (Mrs Idris)

For their helpful support.

One love to Readers no word to express by thanks.

Banhakuri

Ina mai kara bawa makaranta hakuri kan sauyin suna na wannan littafi daga yar'amana xuwa Zahra yar'amana hakan yasanya nayi kokarin hade muku shi a page daya nagode.

Bismillahirrahmanirrahim

Kuka kawai take kai kace an aiko mata da sakom mutuwa wai badake nakeba wallahi kika sake na dauko hijabina baki shigoba saina kure miki gudu na kamaki nakuma dakekin mara mutunci kawai ahankula take bin bangon kai kace wata wahainiya ce saida taxo daf da ita ta xuro hannu xata cafketa tai wani tsalle ta koma baya lallai ma yarinyar nan nikikai ma haka ko jibi yadda

kika sanya na kurje hannu na tai ciki a fusace.

Dasauri ta bi bayanta tana kuka dan Allah umma kiyi hakuri baxan kuma ba xan wanke karma ki

wanke sai afkin ki cuci mutum kixo kina bashi hakuri shegiyar yarinya mara tarbiya tako hauta

da duka kai kace tasamu jaka saida tai mata lilis sannan ta saketa dauran inkin gama kukan ki

fice inkin dawo na dada miki munafika ta shige daki.

Au baxaki tashi kimin abunda nasakiba ko dukanne be ishekiba yar marasa mutunci to inma malan kike jira ya dawo ki hadani dashi ba yanxu xai dawoba sauran ya dawo naji lbr gobe kici na jaki .

Zara yau bazaki makarantar bane xani yaya so nake na gama wannan wanke wanken to kiyi sauri karki makara dakinshirya ai damun tafi tare lah yaya kai tafiyarka karka rasa exam din to sai kin tawo to yaya Allah ya bada sa'a amin ya leka daki umma na tafi to dan albarka sai ka dawo yana fita umma ta leko ke wai yaushe xance miki kidaina kula yaronnan umma dan Allah

kiyi hakuri wallahi baxan kuma ba ta dungure mata kai kima kuma.

Umma na tafi ke zonan ina xaki umma makaranta mn eyye wato makaranta mn ko kin gama aikin dana sanyaki eh umma to sai kindawo tamurmusa gami dayin zauro ke sunan datake kiranta kenan zonan tazo ta durkusa ba wata nakaranta da zaki kinma daina zuwa tasa kuka

umma dan Allah kiyi hakuri nace kinmun lefine .

Kuka kawai take tana rokon umma kan tabarta ta tafi makaranta itako tai mata banxa tuwonta ma take ci tana sautaron waka ta cillo mata kwanon data gama ci maxa jeki ki wanken daga nan ki wuce dakinki in inada bukatarki xan nemeki sun sun ta mike tai gun wanke wanken bayan takai kwanon madafa tai xaure dan nanne dakinta yake indai malan benan ko yai tafiya ke ta juyo kikace kin gama komai eh umma kya iya tafiya anman inna fito naga wani aikin wallahi kika dawo saina dakeki jitai kamar ta daka tsalle dan murna saidai ba dama aduniya tatsani abinda xaisa yau ace baxata makaranta ba dan bata da inda take jin sukuni kamar nan din duda goma saura haka ta daure tai makarantar dan ta fiye mata gidannasu sau dubin

bubata.

Tai sa'a ba'akoma break ba dan haka ta saje da sauran yara daketa wasa kamar ba'a lokacin

taxo ba.

*******************

Zarah!!! Na'am yaya ganinan ta fito rike da hijabinta kinshirya ne a'a yaya wai mai tasa kwanakinnan bakyasan mutafi tarene ko kekenne bakyasan hawa tai dariya lah wallahi yaya ba haka bane ban karya bane katafi karka makara to aishikenan kiyifa sauri karki makara kinji ko to

yaya se kadawo.

Muhammad kenan dan kimanin shekara goma sha shida xuwa sha bakwai sanye yake da

uniform dinsa na Rumfa college inda yake ss3 yayin da zara ke primary 4 anan Kwalli special primary sch.

Furai yarinyar nan kuwa ta dawo eh tana daki kasanta bata san zaman waje kodai kika hanataba kajika kaima dai malan inna hanata maye ribata kinga ba musu nace muyi ba maza kiramin ita mezata maka yau naji ikon Allah shikenan mutun da diyarsa baxai kirataba sai ace danmai yi hakuri mai ya maxa ni kiramin ita tamike tai ribabben dakin da shine na xaran tun

rasuwar ummanta.

Ke kixo inji ubanki kuma sauran inya tambayeki kinci abinci kice a'a saina karya miki kafa inya fita gobe ta juyo dan komawa inda malan din yake asanyaye ta mike sabida wata irin yunwa takeji ga wani irin ciwo da kanta yake har wani jiri ke dibarta rabonta da abinci tin jiya tunjiya da safe shima dan da sch ne tasamu kawarta taxo da abinci suka ci yau ba mkranta gashi yini tai

tanai ma umma aiki ko kanxo ta hanata yaya muhd mai sai mata kosai shima tunjiya baya gida.

A hankula ta xauna baba sannu da xuwa yawwa zara kinko ci abinci tai saurin kallon umman dake gefenta tako gallo mata harara eh baba naci anya kuwa kin koshi eh nakoshi anya kuwa ni banga alamar koshi atattare dakeba ya miko mata na gabansa da umma ta ijiye ungo ci wannan umma tai saurin mikewa wa wallahi baza ta ciba aiba ubanta ya sayoba ke Fure mene haka bansan wulakanci aikaji mainace wallahi baxata ciba tabari in ubanta ya sayo sai taci aike naki uban ya sayo ko kai malan karka xageni kan shegiyar yarnan taka yanzu diyar tawa ce shegiya to karya nai wallahi ki kiyayeni nine ubanta karki kara sheganta min diya hhhhh lallai eh kaine

ubanta seka fadan sanda ka auri uwarta abincine dai ko ki cinye abinci yai tsaki yai waje.

To mayya aisaiki koma dakinki ko kin wani xuban ido kamar xaki cinyeni ta mike tai dakinta ke xonan dan wallahi ban yarda dakeba sai kin fadan inda kike cin abinci sai kin fadan dan iskan dake baki abinci tsananin ciwon da kanta keyi da yadda cikinta ke murdawa yasanya maganar umman ma taji kamar tana kwara mt ruwan xabi aka kawai saita juya danyin dakinta aiko umma ta kufa ta fincikota lallai yarinyar nan wato ga yar iska na mgn shine xaki wuce dakinki ko tako jawota kofar sakin muhd ta ciro wayar cajar fitilarta ta hau duka ko ihu bata iyawa se hawaye kawai dake bin kunxinta kan umma ta ankara sai ganin yarinya tai asandare na shiga uku karfa yarinyar nan ta mutu ga dan rigimar nan na gari wato malan aiko sallamarsa dataji ta kara daga

mata hankali.

Salati ya saki furai karfa kiyi kisan kai kasantuwarta jaruma mai taurin rai in nakasheta ma ai na rage mata takaici ta murguda baki gami da yin dakinta ganin da ranta ya debo ruwa ya shafa mata a fuska sa'annan ta farfado shayin da yasayo mata ya bata kasantuwar cikinta ya nade tana gama sha tayo amansa subhanallahi ya fada gami da daukanta yasanyata bayan mashin dinsa sai asibinta Wata tazo dake nan bayansu saida suka saka mata ruwa koda ya kare suka

rubuta mata dan mgni sai isha'i suka baro asibitin.

Wai yau malan baxaka fita ba dake kike sawa na fita a'a gani nai shuru har tara baka fita ba shine nace bari na leko ko lpy to banga dama ba ko xaki fito dani ne tai tsaki dan Allah ka

shekara adakin ta kade labile gami dayin dakinta.

Shima tsaki yai gami da mikewa yai madafa kofi ya dauko yai waje koko mai xafi ya sayona

xara ya amso kosan da tun daxu yabada kudin saida ya biya kanti ya sayo madara yar ashirin

da biyar ya dawo gida.

Tana kwance adaki ya shiga dakin yai kaca kaca duk tarkacen umma ne yace zara ya jikin ina kwana baba lpy kalau yar albarka taso ki karya saida ya tabbatar ta koshi sa'annan ya bata

magani ta sha yadan gyara mata dakin kafin ya fito.

Saida yai wanka ya shirya tsaf da niyar fita sannan ya leka dakin Furai Furai ni xan fita sauran indawo intarar kin bugarmin diya ko kin hanata abinci kibari randa kika fara ciyar damu saiki fara hanata tai dariya to inna hanata mai xaka mun sakinki xanyi wallahi akan yata tas xamu rabu ta rike hanci tana buda sai mai to akaina aka fara rabuwar aure balle irin auranka auran kaddara auran jidali eh duk naji anman wallahi kitsaya kiji rufe ido xanyi na manta da yayan dake tsakaninmu in hadaki da police kinsan inada shaidu duk unguwar nan duk wanda na kira sheda ne abinka da mutumin kauye da tsoron yan sanda banda abinka malan mai kuma yakawo maganar wadannan masu bakar xuciyar nidai na fada miki wallahi ko yau na dawo na taras kin mata abinda bai gamshenma kisan makomarki.

*****************

Tun daga wannan lokacin xara ta samu saukin duka da horon yunwa saidai faduk wani aikin wahala ya koma kanta bata da takaimai mai lokacin kanta kafin ta tafi sch aikine inta dawo ma

aikine ta rage hanata abinci duda bawani isarta yake ba yafidai babu.

Yar albarka kina inane ta fito da sauri gani baba kinje makarantar kuwa eh naje daxunma na dawo to yayi kyai xoki gwada kayannan muga koxasu miki ta karba tana dariya jeki ki gwado muga kai anman sun miki kyau kamar mai saidawar yasanki saida nace baxasu mikiba yacw

mai xai hana tai dariya nagode baba Allah yasa da alkairi amin zara'una.

Nifa malan ban gane mai kake nufiba dan maine xaka dinga sayawa wannan yarinyar kaya alhalin ni ba isata yai ba to banda abinki har yaushe na siyo miki ina dawo wata wancan watan kena siyowa to naji anman ai wannan nuna banbanci ne in gaskiyane ai muhd ma na bugata eh nayi rashin adalcin komai xaki ce sai dai kice ba xan siya masa ba to karka siya dadinta bani Allah xai kona ba sau ki godema Allah tunda ba kabarinmu daya ba yai tsaki gami da shigewa

dakinsa.

Kasan tuwar bata san take makara a makaranta yasanya duda karancin shekarunta ta sabarma kanta tashi tun asuva ta kammala komai yau ma haka ta kasance kiran sallar fari ta farka kafin biyar ta gama komai tai sallah ta dauko kayanta xuwa dakinta dan kar baba ta ganta a dakin zaure dan haryau baisan tana kwana adakin xaureba sai ya duba yaganta adakin ummanta sannan ya kwanta ko tai bacci sai umman muhd taxo ta maidata dakin xaire bakwai dai dai ta gama shiryawa umma na tafi ina makaranta ubanki ne xaimin wanke wanke wanken umma ai nayi eyye kin isa wato ina mgn kina mgn ko watakan ga sa'arki yi hakuri umma anman nayi wanke wanke tau ta bata mari nafiskanci yarinyar dan na dena dukanki kin rainani to banyi

sanyi ba maxa ni jeki kimin abinda nasaki ga mamakinta kwanikan data wanke an kada kuka da

manja an sheka musu haka ta gama umma ta kara debo mata tabarmi wai ta wanke ta shiga

daki dan cire uniform koma maxa dasu nake san wanke.

Sai tara ta gama a haka ta tafi ajike zara yarinya ce nai kwaxo duda kasantuwar bata xuwa kullun kusan kullun a makare take anman hakan baisa take iya daukan ta biyar ta shidaba bata taba wuce ta gomaba a makaranta sun dena sukanta dan muhd da kansa yaje ya musu bayani

sun kuma fuskance shi.

*****************

Yanayin garin yasanya yau malan musa tashin su zara da wuri hadarine ya hado bakikkirin ga iska dake kadawa mai karfi tunanin xara daya wanda bai wuce dakinta data ke kwanaba wato dakin xaure ga muhd benan dama yananan ne tasan iyaji ruwa xaixo ya maidata dakin ummanta to ya tafi sakkoto yin jamb ga dakin wata irin mahaukaciyar xuba yake ga kanta na wani irin ciwo sauran yan makaranta ta gani suna gudu dan xuwa gida jitai inama itace ace

take murnar komawa gida.

Ruwan da ya sauko yasanyata rugawa da gudu xuwa gida ganin yadda ruwan ke xuba yasa ta shige dakin xaure kasantuwar da wuta yasa ta ganin yadda dakin daxu ta fita tabarshi fes anman ynx yai kaca kaca duda kanta na ciwo haka ta gyarashi kukan sauro ne kawai ke tashi adakin takardunta da bataso ta kunna hayaki ya turnuke dakin ta daga labile tana korosu waje aiko dip aka dauke wuta umma dake sallah ta hango haske itako xara koda hayaki yadan kare taje tsinmokaranta ta rufa tuni bacci ya deveta da'alama taji dadin baccin jitai an bugeta eyye sannu yar kanta watakan banma isa kixo kicemun kin dawoba ko wallahi umma naxo naga

kika sallah ta daki bakin shegiya wadda ba'a fadi saita karyarta.

Maxa ni kixo kimin wanke wanke umma daxufa na wanke eyye wato harkinkai nasanyaki aiki kice baxakiyiba ko to wallahi invaki wankeva baxakici abinda na girkaba wato ga baiwa ingirka inbaki onmiki wanke wanke to vaxai yiwuba yi hakuri umma xan wanke karma ki wanke kibarshi

banso tasan halin umma dan haka ta fito ta fara wanke wanken .

Kwanukan data wanke daxu duk Anbarbaxasu ruwa ya musu duka aiko tana farawa wani ruwan ya tsugewa ahaka tana wanke wanken ruwan na dukanta koda ta gama umma tace saita wanke gidan atakaice ruwannan akanta ya kare kije kidauki tuwonki yana nan a kwanonki

tuwan ya sandare sanyi kalau miyarma ruwa duk ya shiga haka ta dauko tai daki.

Dakyar take iya tura tuwon danma yinwar datakeji ne daba lallai ta iya ciba yadda yasandare yadda xaxxabi ya rufeta ko sai karkarwa take umma ta shigo to muna fuka kinxo kin lanjarw

anan salon malan yaxo yaganki ta mike tai dakin ummanta.

Da'alama tanajim dadin baccin dan kayan data kima ajikinta tadanji dumi umma tasa kafa ta

doketa a firgice ta farka wato kekinji dadin harda bacci maxa ki koma dakinki ta mike batai

ishaba tai alwala dakyar tai sallah .

A bude ta taras da dakin umma ta barbaxashi hawaye suka xubo mata ta goge abinta gami

da dan marmatsar dasu taja gefe ta kudunduna dan umna ta kwace kayan rufar.

Cikin dare ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya ga iska mai karfi data ke bugawa sanyi da

iska gamida ruwan dake digowa sun hanata bacci.

Iskar data tasoce ta yaye rufin dakin yai gefe kasan tuwar da wuta wta yasata saurin mikewa danyin gefe aiko wani cikin rufin yai sa'ar yankarta a cinya tako kurma ihuuu tafadi nan sauran

suka rufeta karfin ruwan yasanya sumalan rashin jiyo kararta.

******************

Koda malan ya fito bai kawo komai akan yayewar rufin dakinba dan saninda yai babu komai mai anfani adakin dan haka alwalarsa kawai yai ya wuce sallar asuba koda ya dawo baibi takan dakinba ya fadama umma abinda ya faru dan yataras da har lokacin baccinta take atsorace tace nashiga uku wane daki malan dakin xaure mn ta dafe kirgi gami da waro ido ya kalle ganin yadda ta tsorata ganin asirinta xai tonu ta mike bari naje na dora dumame ta fice kai tsaye dakin umman xara ta wuce tana addu'ar Allah yasa ta dawo nan duda wani barin na ranta na fadi mt Allah yasa ma xaran ta mace kowa ya huta. Dan hk kawai ta hadama malan kari ta kai masa fatanta yaxo ya fice tunda garin xai bari inyaso inya dawo yasamu lbarin rasuwar ta ta aminta

da xuciyarta.

Ya shirya tsaf har yakai xaure da mashin dinsa ya juyo kinga bari naduba dakinnan ah ah da saurinta kaga malan kayi wankanka tsaf karka bata jikinka kabari xan gyara yai dariya banda abin furai nida xanyi aikin gini kan in wuce bata jiki na ina saidai kar'akuma ya xira kai dakin yadan farabmatsar da kwanukan gami da daga wasu ga mamakinsa yaga jini jikin wani kwanon da sauri ya daddaga sauran da dan birbishin bululluka sai ayanxu ya tuna yau ba xara ce tai dumameba bai kuma ganta tana wanke wankeba kamar kullun tabbas kuwa xara ce ba shassha yadda yaga furai ta tsorata zaran kuwa yagani kwance cikin jini baijinma tana da rai surarta yai yai waje.

Muktar ya hango yana goge dan sahunsa yai wajensa da sauri shima ganinsa dauke da xaran kamar gawa yasanyashi saurin kama mishi da ita suka shigar da ita dan sahun yatada baiko tambayi inda suka nufaba yai bammali dasu koda sukaje babu likita ko nurses babu sai primary health officers sukuma sukace abin yafi karfinsu dan haka yai murtala dasu nan sukace sai sunxo da police domin yanayinta yanayin wanda akai hatsari gaba daya sun dururuce sai can muktar ya tuna da abokins hanxa police ne ya kirashi awaya ya masa bayani kaga wallahi mashin dina ba mai banda kuma kudin mashin wallahi kana inane ina gwale police station to gani nan.

Koda sukaxo da Hamza ai sai sukace musu babu gado duk yadda sukaso karvarta nurse din

taki shikam malan yama gama fidda rai da yarinyar muktar ke kara bashi karfin guwa kai tsaye nasarawa ya wuce dasu koda suka isa yai emergency dasu da gudu ya dauketa sukai ciki sukai

kuwa kacibus da wata doctor ta tausaya musu duda ta tashi anman hk ta tsaya ta basu tai makon gaggawa ta baima malan takarda gashinan ana bukatar wannan da gaggawa dan sai anmata yar karamar tiyata sai mun mata dinke dinke in kakawo kabaima nurse xata baima doctor mai duty kai tsaye ya wuce gurin rubuta kudi sai dai mai kudin sunfi karfin tunaninsa baidasu bai kuma bada ajiya ba ya dawo ya xauna ya rafka tagumi.

Komai ya tuna oho yai dakin da xaran take Allah sarki muktar har ynx vai tafi ba ya bashi takardar ya duba dan rokon likitar ta tafi muktar yace wallahi baba banda ko dari jiya nakai balance dake mashin din bane ya tsurama yarinyar ido tausayinta yakamaahi yarinyar tun xuwanta duniya take wahala har yau furai ta hanta sukuni.

Muryar nurse yaji na cewa malan kaifa muke jira kakawo abinda doctor ta rubuta in ba haka ba kadauki yarka ka kara gaba ya kalleta dudu du batafi sa'ar kharima yarsa ba anman tarike kugu tanai masa tsawa kabi kawani tsareni da ido ko so kake inxama maganinne yi hakuri yanxu xanhe ah karma ka kawo tai tsaki tai daya gadon.

Muktar ya dafa baba gwanda akawo kudin kar yarinyar ta galabaita wallahi muktar bandashi to baba mai xai hana kasaida mashin dinka to banda abinka ina xan samu mai siya shi ba kamar goal bane eh to hakane anman da gwaji akan dace muje nasan wani mai siya summa manta ita daya suka bari suka tafi.

******************

Nurse ce taketa bala'i haba wannan ai rashin mutunci ne mutane sukawo yarinya su gudu

subarta fada take ba kakkautawa.

Kai wannan nurse din ta fiye fada bari na leka naga waya tabota doctor din yai dariya indai

mairo ce sai ka gaji da jinta.

Matashin saurayin dabaifi shekara sha takwas ba ya fito daga office din yadda yaga yarinyar ta bashi tausayi haba nurse ku dubata mn mudubata kamar yaya baka ganin halin datake ciki ne ko so kake ni inxama mganin da xamu mata mun basu wanda suka kawo sun gudu ya fiskanci

nurse din yar xafi ce don haka yai tsaki ya koma office din doctor.

Pls doctor kataimaka ka ceci rai yarinyar na cikin wani hali aikaji mai tace basu kawo alluran

bane ni rubuta min sai in kawo yace muje naganta bayan yadan duddubata ya ya rubuta masa mgnin shi kuma yai wajen biya.

Datai makon Allah dana yaron doctor yai mata komai shi kuma yaxauna dan kula da ita.

Duk inda muktar yasan xaikai malan dan sayen mashin dinsa yaje anman ba labari dan saidai sice bayan sati yaxo ya amshi kudin sai asannan ya tuna ita daya ya bari hankalinsa ya tashi watakilma ta mutu inyaje to maixaice da ma'aikata suna tafe muktar na kwantar masa da

hankali har suka isa.

Inda suka barta wayam hankalin malan inyai dubu ya tashi wata nurse ya gani xata wuce ya

tambayeta ta nuno masa emergency room tana ciki da sauri ya shige gadonta ne na karshe

tana kwance sai wani matashin saurayi dabaifi muhammadunsa ba axaune abkujera da'alama bacci yakeji muktar yace baba bara naje gida karsuga ban musu sallama na tafi toshikenan dan albarka nagode yaron da ke xaune ya dago kai yaga yana shafa mt kai kasanta ne baba eh

yaro diya tace Allah sarki ya mike daga xaman da yake ga guri xauna yi xamanka.

Anman baba mai yasa ka tafi ka barta wallahi ba tafiya naiba naje nemo kudine gashi duk yadda xanyi nayi bansamuba haka ne karka damu anbiya anman dan Allah baba kadena irin haka gangancine kaxo kabarta ba kowa gwandama ka tsaya inma mutuwa tai ku koma da ita eh hakane duk na gigice ne wallahi ai dakyar muka samu nurse tabar xancen da cewa tai baxata tafi ba sai ka dawo wallahi police xata hadaka yaxaro ido towa ai ansha kanta akiyaye gaba dai

insha Allah.

Ya mike baba ni bara naje kar anaiman agida to yaro baka fadan nawa aka kasheba yai murmushi baba kenan karka damu ni dan Allah nai wallahi nagode yaro Allah yasaka yanata saka albarka yaron na amsawa Allah ya kara sauki amin yaro sai dai baka fadan sunanka ba yashafa kai sunana *Zaem* kijerar da ya tashi malan yabi yaxauna tunanin yanayin rayuwar xaran duk sukabi suka cika masa rai yadda aka haifeta yadda take tayuwa duk suka dawo masa baisan sa'adda hawaye suka biyo kuncinsa ba.

**********************

***********

*wace ce Zahara*

Dina haifaffiyar garin kano ce mahaifinta hamshakin dan kasuwane sananne afadin Nigeria su shida iyayansu suka haifa biyu sun rasu tun suna yara sai yayansu mai suna zaem mai bimasa zikir sai ita Dina dan autansu salman kasantuwarta mace daya da suka mallaka yasanya duk

san duniya suka dora mata.

Lokacin da dina ta kammala secondary ne yasamu damar tafiya sch of hygiene inda take environmental health.

Ranar da baxata taba mantawa da ita ba itace ranar exam dinsu ta parasitology ta xauna gefen wani saurayi shi dan EVT ne yayin da ita take yar EHT kafin akawo papers har sun saba

sunata hira akan nata course din yafi dole ya girmamata shi kuma yana ta zolayarta.

Tundaga sannan suka xama frnds indai ba lecture ce dasuba xaka samu islam cikin mata duk

inda kaga dina kaganshi kai ko agidansu dina ansan da xaman abokinta islam.

Ada dina batasan hygiene anman yanxu koda dad yai mata batun yin jamb ai sai cewa tai tafisan kawai tai diploma a health inyaso daga baya tayi degree din aiko ya kyaleta.

Dina batasan tasaba kuma tanasan islam ba sai da sukai hutun semester ending dake shi ba

dan kano bane ya hostel ne .

Dina na NDll dad yace aure xai mata da dan abokinsa aiko tahau ta dire ita basansa tana da

wanda takeso yace waye ta fadi mai yace shikenan ya aminta anman xai bincike.

Sati biyu da batun yakira kan yanasan ta rabu da yaronnan baida asali tace ina ita haka

takesan abunta duk yadda yaso ta rabu dashi taki .

So yagama rufe mt ido dad yace shikenan tayaji xai auranta dashi anman tasani bashi ba ita

yayunta sukai sukai taki ita ta yadda haka aka daura auran.

Murna gurin sabbin ma'auratan ai ba mgn idanunsu ya rufe basa tunanin komai haka islam ya

dauki matarsa sai bauci gaba daya suka watsar da karatun.

Zuwansu bauci komai dai dai yake tafiya kafin rayuwa tai wuya su kwaso su dawo kaduna anan dimma ba dadi tsi tsi suke in anci na rana ba lallai asamu na dareba haka dai sike hakuri ana haka Dina ta samu ciki gata da dan banxan laulayi duk tabi ta rame komai yai musu xafi.

****************

Cikin ta nada wata bakwai tace xata kano ganin gida yace ina ba inda xata bacin basanta sukeba tace itadai haka xata tafi.

Agajiye ta sauka ga yunwa da takeji yadda mamanta ta ganta yasa dasauri da abinci ta fara taryarta aiko sai loma kamar ba dina mai kincin abincin data sani bace aiko sai hawaye dad yana dawowa yace vaisan xance ba taxo tabar masa gida tana kuka mama nayi yan uwanta na

bashi hakuri yai kemai mai haka bata kwanaba ko abincin bata gama ciba ya korata.

Haka ta dawo gida tana kuka maiyasa dad baxai mata uxiriba ta gane kuranta .

Duk yadda dina xatai islam yakaita danginsa yaki yanxima yashiryane dan xuwa xaitawo da

kakarsa tai tai xata bishi yace tayi hakuri inta haihu inxasu maida kaka sai su tafi tare ahaka sukai sallama ya tafi.

Kwanansa hudu da tafiya ta haifi diyarta mace dayake yabar komai ranar suna aka yanka rago

taci sunanta *zahara*.

Tun abin bai damun dina har tafara damuwa dan yau watan islam uku bako labari bashi ba kakartasa har bauci taje sukace baixoba daman ai daga Niger yaxo canma vasu da tabbacin inda yake koma dan canne aiko tai kuka mai isarta ita bama kanta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment