gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading ZZEE BABYZ Dawowar ’Yar Tawaye By Real Ladingo Chapter 17 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abunci Nisha"

"gwara da kikazo kika tasota ai mik'ewa tayi taja Nisha suka nufi kan dining,"

"Ban garan Aunty amarya ko bayan sun dawo zamanta tayi tace bazata komaba sai dare Asiya tamata sallama ta tafi itako tanan sai bayan sallah isha tayi shirin tafiya uwarta ta kara jadada mata yada zata kula da sharunda da malam ya fada mata, zaune suke aparlo zee da Nisha da khalisat sai hira shirme zee take musu hafeeza sai dariya take musu yada nisha ta biye mata Mahabeer ne ya shigo da sallama zee ta Mike ta tarosa harda riko hannusa ""my heart wlh nayi missing d'inka ""my zeena nima nayi missing d'inki sosai da fatan kina lfy? "" lfy lau zama sukayi nisha ta gaishesa da su hafeeza ya amsa fuskarsa asake ""Ya Mahabeer bari kaga pic d'in da mukayi nisha bani wayata idanu ta zaro""au kina nufin baki dauko ba wlh tana part d'in Daddah harata nayi na Mike ""Ya mahabeer tsaya na amso da gudu ghaisha ce ta fito ta zauna mahabeer ya koma kusanta ya zauna yanama zee magana ta tsaya amma ta fice da guda""Allah my heart sai na amso akofar parlo tajita tayi karo da mutum male male ta fada saman faffadan kirjinshi wani irin mugun shock ne ya debesu atare zuciyoyunsu suka buga atare da sauri tana k'ok'arin janyewa shima yana k'o'karin janyeta kansa ya kauda ya tureta ta fadi k'asa ya shige parlo mik'ewa nayi raina ab'ace amma sanin bamu harakar juna yasa nayi hakuri dan shma da dane sai ya mareni ya shigar dani jikinsa na shaki kamshinsa haka na nufi hanyar gidan"

Daddah kamshinsa ya dagamun hankali jina akirjinsa yasa tsikar jikina mik'ewa ga kasala

"amma Dole na basar ina shiga na dauko wayar na dawo part d'inmu kusan mahabeer na zauna shiko yana jikinta ghaisha sai kansa take shafawa tamkar wani dan jariri yamun mugun kyau Ya Mahabeer nashiga nunawa pic d'inmu ina dariya ta karfin hali asace nake kallonsa ko kallon inda nake bayayi haka yasa nima na daina masa kallon sata na shiga sha'anina khalisat kuwa ta zuba masa idanu tamkar zata cinyesa sab'anin nisha da Allah ya samata mugun tsoron Sardauna sam bata iya zama inda yake yanzuma jitake ta takura su Daddy suka shigo da sallama shida Aunty amarya zee baby ta dago tana dariya ""Oyoyo Daddy ai tanakai kallonta ga Aunty amarya ta Mike zumbur jikinta na karkarwa idanunta suka rikide sukayi jajur da gudu tayi kan Aunty Amarya ""Wallahi baki isa ki shigo mana da wannan masifar ba Aunty Amarya tanajin haka tayi kofa da gudu jikinta na rawa zee beby kafin ta cinma Aunty Amarya ta fara ganin duhu luuu tayi zata fadi kafin ta isa gunsu Mahabeer da gudu yayi kanta itako Aunty Amarya tuni tana kofa tana zaro idanu duk abinda ake Sardauna ko kansa bai dagoba ko ghaisha da tace ya dagata kansa ya dauke saman cinyarta ya Mike ya ficiwarsa daga parlon Mahabeer ya tarota jikinsa ta zube tana buge buge ""wlh sai nayi maganinta muguwa ghaisha ta karaso gunsu tana mata Addu'a kamar yada Mahabeer yake mata Daddy ya iso""Wai me ke faruwane da momy"

Mahabeer yace Daddy Aunty Amarya ce

Yar ilu ce.

* ZZEE BABYZ  *

*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*

*¢22*

"....""naga tana nunawa wai karta shigo sunkuyowa Daddy yayi yana mata Addu'a ""Mahabeer inaga kamar Aljanunta fah basason Mariya ne bakinta ya fara fitar da kumfa abinda ya tsorota Nisha ta fado kanta tana kuka gaisha ta janyeta hafeeza ma kuka takeyi Daddy ya buga musu tsawa"" Mahabeer ko muje asibitine?? ""Daddy ba ciwon hospital bane Addu'ar sukaci GABA da mata cikin ikon Allah tayi wata irin atishawa mai firgitarwa da ihu mai uban karfi saida khalisat da hafeeza suka gudu amma nisha na gunta tana hawaye tana tofa mata Addu'a Mahabeer yasa nisha ta kawo ruwa ya karanta suratul yasin ya tofa aruwan ya dura mata da karfi tasha ya"

shafa mata ajiki ta kuma atishawa da hamma tai lamo jikin Mahabeer sai bacci Daddy

"yace""Alhmdllh tayi bacci kai momy Allah ya rabaki da Aljanun nan sun dameki Mahabeer kaita ka kwantar da ita mik'ewa yai ya dauketa ya nufi bedroom d'insu yaje ya kwantar da ita ya lulubeta ya fito ghaisha harda kwalla tausayi Mahabeer zama yai kusan ghaisha yayi tagumi kansa ta shafa ""kayi hakuri ba komai bane zataji sauki tana tashi lfy zata tashi amma abun yabani mamaki irin wannan lamarin watarana sai sunga abinda bai musu bane ba suke haka Mahabeer yace"" wlh nima nayi mamaki Daddy yace babu abin mamaki sharrin jinnu yawane dashi ""Khadija ina mariya wai? ""naga fah ta nufi kofa da gudu inajin tsorata tayi kofar Daddy ya nufa abin dariya yabashi da taji tsoron zee yana fitowa ya ganta rab'e ya nufi gunta ""haba mariya saikace wata yarinya tsoron Aljannu kara matse Jakarta tayi ta tataro nutsuwarta dan kar yagano itace sila""Daddyn nanah wlh tsoron Aljannu nakeyi gashi aljannunta basu sona dariya yayi ya kamo hannuta ""mujeto ga yarki can yar k'arama da ita ta tsaya a parlo tana zaune gun ghaisha shiru tayi yana rike da hannuta har parlo ya saketa wuff ta shige d'aki ta boye"

maganin ta fito parlo

"""Aunty ghaisha sannu da gida? "" mariya kece da sannu ya mama da jikinta? "" Alhmdllh tana gaisheku ya jikinta momy? ""tayi bacci"" Allah bata lfy hira suka ci gaba dayi Daddy yace""khadija abamu abunci mana Dariya tayi ta Mike ta kalli mahabeer ta kamo hannusa""muje kaci abunci kayi hakuri zata tashi lfy mariya tashi muje kuci abunci khalisat kirawo Aisha da hafeeza maza kuci abunci mik'ewa tayi ta nufi bedroom suko suka nufi kan dining khalisat na shiga taga Nisha rumgume da zee gam idanunta arufe tace""hafeeza Nisha bacci takene?"" idona biyu meye ai duk uwarkice taja mata tunda ita takebi hafeeza ta rufe mata baki""yi hakuri Nisha tashi muje kici abunci? "" banaci na koshi mik'ewa tayi suka fito itako tana kwance rumgume da zee, Dr Sardauna yana fita ya shiga motarsa yabar gidan danma karsu nemesa ya dubata kai tsaye gidansu mashakurah ya tafi, yau har cikin ya shiga da motarsa ya kirata ta fito suka shiga ya gaishe da iyayanta ta kaishi parlon baqi inda suke zama sai surutu take zuba masa kallonta yayi""wai meyene yanzu kika koyi rufe rufen jiki kina wani sunne kai sweet baby ko shirin amarcin ne? "" kai my Dr wlh ba haka bane nafiso karka sake ganin kome nawa sai na shiga gidanka baki ya tab'e daga baya Kenan ya fada cikin rainin hankali ya dan jima sosai sun dan tab'a hira ya Mike ta rakoshi harda shagwab'arta dariya ma ta bashi ya lallabata ya shiga mota yamata key direct gidansu Ahmed ya nufa har parlon su umma ya shiga ya gaishesu tukun ya fito ya nufi bangaran Ahmed yaga arufe yayi mamaki dan umma tace yananan baki Sardauna ya ciza""shege munafuki ko ina ya tafi adaranan ya fada yana wucewa mota ya shige ya bata wuta ya nufi gida kida ya kunna ya kure sauti wakar ethiopia ce dan yana mugun son wakokinsu sigari ya kunna yana zugarta yana kada kansa saida ya biya shopping mall yayi tsince tsince abubuwa ya kashe kudi ba kadanba kan kayan ciye ciye da turaruka masu uban tsada, yana zuwa gida part d'insu ya shige ya nufi bangaransa ya bude hadaddan d'akinsa sai uban kamshi ke tashi carpet malale ko ina ga manyan kujeru tamkar d'akin Amarya bed d'insa kadai abun kallone ledojin hannusa ya ajiye harda su ghaisha yama sayaya amma bashida niyar komawa part d'insu ayau yayi niya sai gobe kayan jikinsa ya cire ya daura towel ya nufi bathroom shower"

ya kunna yasakarwa kansa

ruwa yajima sosai kafin yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito dan bacci yakeji sosai yau ga gajiya

jikinsa ya goge ya murza maiyukansa masu kamshi da dadi yasaka jallabiya ya shimfida

"darduma ya tayar da sallah wayoyinsa har biyu sai ringing suke atare, raka'a hudu yayi ya dauki Alqura'ani ya fara karatu yajima sosai dan yafi awa guda yana karatu akinrasa yafi so goma sujada yayi nanma yajima yana tasbihi ga ubangijinsa yana nema gafara Allah yana kara neman kusanci ga Allah subahanahu wata'alah yanama Annabinmu Muhammad s,w,a kirari Yajima sosai ya dago ya daga hannuwansa sama yashiga kwararo Addu'a ya shafa ya Mike ya nufi gun wayarsa yana dubawa Wanda suka kirasa yaga bandar yamasa kira uku mashakurah kira hudu Daddy kira biyu Ahmed kira uku sai number da babu suna kansa ya dafe""oh sweet baby ko miyene kiranta yayi wayar akashe kin Kiran Ahmed yayi yana murmushi ya kira bandar shima akashe wayar kiran Daddy yayi bugo daya ya daga""Faisal ina ka shiga bakaci komai ba""Daddy gidansu Ahmed naje da nazo bacci ya daukeni"" to maza fito ko tea kasha ko coffee maza mu har mun kwanta dare yayi"" to Daddy ganinan""yauwa Dr dariya Sardauna yai ya kashe wayar ya nufo parlo Mahabeer na zaune da casbi ahannusa Dr ya kallesa ""bro bakayi bacci ba har shabiyu? "" wlh tunanin halin da zeena take ciki ya hanani bacci baki ya tab'e ""ni na tafi cikin gida nasha coffee nazo na kwanta wlh bacci nakeji mik'ewa Mahabeer yayi""muje naga ko ta tashi ko tea na hada mata baiwar Allah bataci komaiba Dr Sardauna baice komaiba suka fito can ko lokacin da Sardauna yakira Daddy d'akin Aunty Amarya yake tanajin yana maganar Sardauna yazo yaci wani abu kar ya kwanta haka zuwat ta Mike ta saci kallon Daddy taga baya kallon gefenta cikin rawar jiki ta nufi idan ta boye maganin ta dauko ta shiga toilet ta ciro Wanda Sardauna zai tsallaka ta fice daga dakin direct dakin su khalisat ta nufa cikin sa'a taci Karo da khalisat ta fito shan ruwa ta kirata suka lab'e ta sinto ledar ta maganin ""amshi babu lokaci da safe namiki bayani kiyi maza kije kofar parlo ki Barbada maganin wannan Sardauna zai shigo yanzu kinga darene babu Wanda zai shigo yanzu ki badeshi baki daya ""momy na menene?? "" kece zaki San ko nameye nan gaba badai sonsa kikeba? "" eh momy""to maza jeki ba lokaci ta"

fada tana komawa

"bangaranta da gudu khalisat ta nufi kofar parlo cikin rawar jiki ta barbade kofar parlon zuciyarta fari tas tana murna kuma daidai lokacin tajiyo murya Sardauna na tafe yana waya da gudu ta nufi hanyar bedroom tana cikin farin ciki Karo sukayi da Nisha""ke lfy me ya fito dake kuma kike irin wannan dariyar yawa zarara batace komai ba ta rab'e ta shige ciki Nisha kuwa ta nufi kitchen don hadama zee tea ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ko da khalisat ta shigo zee tana bathroom Dan haka ta haye bed ta shige cikin blanket hafeeza ma bacci takeyi Dr Sardauna ko suna fitowa suna dab da shiga bandar ya kira Sardauna ya daga rike hannu Mahabeer yai ""bro ka jirani mana murmushi yai ya jirasa suna ta hirasu da bandar Akan yana tafe insha Allah nan da kwana biyar mahabeer ganin hirasu ba mai karewa baceba ya janyo hannu Sardauna ""muje mana ciki wai kuyi wayar kiyawa Sardauna yai mahabeer ko ya fizge hannusa""to Nima kabarni naje naga Rabin raina ya fada yana murmushi ya nufi parlon yana sanyo kafarsa kansa ya Sara gabansa ya fadi da Sauri ya furta"" Auzubillahi minal shaidaninr Rajim bismillahir Rahamanir la'ilaha innah anta subahanaka inni kutum minal zalumin ya fada yana shiga tsakiyar parlon kamar cira qaya yaji bayajin faduwar gaban sai kasala kadan kadan parlon shiru alamun kowa yayi bacci motsi yaji a kitchen ya nufin kitchen din Nisha na kokarin hadama zee tea ganin irin kayan dake jikinta yayi maza ya juyo ya fito ya lab'e""Nisha zee ta tashi ne?? dariya tayi ""bro yo meye na labewa eh ta tashi tea ne zan kaimata ka ajiye"

"hankalinka tana lfy dariya yayi""yauwa kanwata nagode ki gaishemun ita sai da safe na koma ya"

"fada yana tafiya lokacin Dr Sardauna ya shigo akofar parlo suka hadu Mahabeer yace da ka hakura da coffeen mun koma? "" haba wlh sai na hada nasha Daddyna fah yace nazo nasha kafada mahabeer ya daga yana dariya ya fice Dan yasan Nisha najin motsinsa zata Ari ta kare ficewa yayi Sardauna ya shigo direct kitchen ya nufa Nisha ma ta hada tea ta dauko ta nufo kofa ita zata fito shi zai shiga Karo sukayi saida tea din ya Dan zubar masa akirji saboda tsabar tsorata da kaduwa kasa motsi tayi tsawar da ya buga matane yasa ta Saki cup d'in ya tarwatse ak'asa jikinta ya dauki rawa ta rumtse idanunta""Dan ubanki me kike nema awanan Daren idanu ta bude jikinta na rawa""yaya kayi hakuri wlh ban San kana hanyaba ta fada fitsari na kwararo mata daga k'asan cinyoyinta idanu yazo ganin tana tsiyayar da fitsari dama rigar yar guntuwace cinyoyinta duk awaje saboda tsabar bakin ciki da haushinta wai fitsari take atsaye yasa ya Kara marinta ya harbata da Kafarsa ta fadi k'asa ya taketa ya wuce yabar kitchen din ya fasa shan coffeen ya fice daga parlon fashewa tayi da kuka ta Mike tana jamasa Allah ya isa toilet din parlor taje ta wanko jikinta ta dawo ta sake hadama zee wani tea tana hawaye. ta kawo mata zee zaune take ta kunna wakar larabci Tasha sirot da kwaya ba kadanba Nisha ta shigo tana matsar kwalla zee tace ""ke dawa? "" wlh yaya Dr ya dokeni zee cikin masifa tace""Allah ya isarmiki shege Dan iska halan matsarki yajeyi kika kiya ya manmareki ta fada azafafe tanama Nisha wani mugun kallo idanunta sunyi jajir? Idanu Nisha ta zaro"" wlh A,A Dan na zuba masa tea ban ganiba ne wlh Allah bai tabani ba shi ba Dan iska bane ajiyar zuciya zee ta sabke ta rumgume nisha ta amshi tea din Tasha suna hira Nisha taje ta sake wanka ta canza rigar bacci suka kwanta suna hirasu har zee ta fara maye tana sambati tana kiran Sardauna Nisha ta Rumgumeta tana mata Addu'a jinta ko Aljanunta ne zasu motsa ahaka har bacci ya dauketa itama Nisha baccine ya dauketa suna rumgume da juna Asuba ta gari, Dr Sardauna na komawa ya saka kayan bacci yasha lemo guda ya haye saman bed ya shige blanket bai jimaba bacci ya daukesa mahabeer ma yana zuwa yayi alwalla ya fara sallahr nafila sai kusan karfe biyu ya gama yanama zee dinsa Addu'a Allah ya rabata da jinnu yajima kafin ya Mike yai shirin"

"kwanciya bai jimaba da kwanciya barci ya daukesa asubah ta gari,"

**********************************

*Bayan kwana ukku*

Bayan wannan lokacin abubuwa sun faru kamar su gabar Sardauna da zee baby ta dore Dan ko dawasa baya kallon inda take itama haka saidai ita rashinsa na mugun daga mata hankali har ta Dan rame sha'awarsa tana damunta ta rasa ya zatayi ta gaji da rashin Sardauna tana bukatarsa tanason gumin jikinsa tanason kamshinsa da sauraron zazagar muryasa da sweet d'in lips dinsa amma haka ta daure ta basar yada ya basar da ita suke rayuwa cikin k'unci da takura Nisha ko tun wahegari da sasafe ta gudu gidansu tace bazata iya rayuwa dukaba dama saboda zee ta matsa abarta ta dado tarinka zuwa makaranta daganan Najib ya kaita gida mahabeer dai yananan ras babu abinda ya samesa soyayyarsu da zee sai abunda yaci gaba suna kula da junansu zee said sangarta take maza iri iri zee ko ita da Aunty amarya basa wani shirin duk da ita zee sam batasan abinda ya faruba ranar amma washe gari fur ta hana ta zaman parlo gashi malam yace karta kuma nemansa sai wa'adi ya cika ita da khalisat farin ciki

sukeyi Sardauna ya tsallaka magani jiran lokaci kawai sukeyi na wajan Daddy kuwa tun washe

gari da zata hada masa babban aminin mairan karfe Alhaji Nuhu ya rasu a daura daga zuwa ganin dangi dama jikin tsofa ba lfy bace dashi gabaki dayansu mazan suka dunguma daura har Dr amma shi da mahabeer basu kwana ba su Nuhune suka kwana Daddy ko na can shine ya saka bata bashi maganin ba sai yaune zata bashi khalisat yaune zata wanke fuskarta da

"magani,"

"da misalin karfe shida na Yamma Dr Sardauna ya bari asibiti ya nufo gida yana zuwa yayi parking ya fito ya rufe motar cikin takunsa na isa da kasaita ya yake tafiya cike da kuzari waya manne akunnesa sanye yake cikin suit bakake sunyi masifar yi masa kyau gashinsa ya Dan sabko wuyansa said zuba uban kamshi yake ya nufi part d'insu ghaisha a parlo kuwa baby kowa said zee baby zaune tana game awayarta su Aunty amarya ko tana kitchen Ana k'ulla mugun Abu sai nanah da nawwara na kallon Tv da sallama ya shigo parlon yana waya sai murmushi yake aciki na amsa sanin darajar sallama ko kallo bata ishesaba ya wuce ta gabanta ya nufi kujerun can nesa da ita Wanda ko kallon juna basayi ya zauna tunda na kallesa na dauke kaina zuciyata na bugawa da karfi saboda irin kalaman da na tsinto yana fadama mashakurah ga muryasa ta kashe mun jiki ga kamshinsa kasala naji ta kamani daurewa nayi naci gaba da sha'anina cikin dauriya kiran ya katse dama hira irin kayan da take sone sukeyi dan asatinan zai hado akwatina ganin ita dayace a parlon yasa ya Mike yana kiran ghaisha shiru bata amsaba ya nufi d'akinta zee tashi tayi jikinta amce tabar parlon bedroom ta shige Nawwara tace""yayamu mama tana gidan Daddah sai Aunty amarya a kitchen juyowa yayi ya nufi kitchen d'in har ya shiga kuma ya fito ya juya zai fita kenan khalisat ta fito daga d'akin Aunty"

"Amarya fuskarta sharf da ruwa cikin farin ciki ta karasa""Yayamun Dr "

Idan nasamu dama zan k'aro muku zuwa yamma

Year ilu ce\

* ZZEE BABYZ  *

*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*

*¢23*

"....bai ko juyoba yaci gaba da tafiya hankalinta ne ya tashi da gudu Tasha gabansa ""please yayamu ka tsaya don Allah bai ko d'agoba ya kalleta kuma baiyi magana ba y rab'ata ta ya wuce Dan haka kawai yarinyar yaji baya ra'ayinta kuma idan ka bashi haushi baya garajan magana gudun kar yama illah hankalinta atashe ta nufi kitchen gun mamarta jikinta ta fada ta saki kuka""ke lfy kuwa? "" momy bai kalleniba kuma bai mun maganaba""innah lillahi wa'innailahir raji'un kiwa Allah da manzo s.a.w kibishi kimasa magana"" momy wlh bazai amsaba karfa ya dokeni ""to bari ajima zuwa dare kisake shegen yaro uban jarabar taurin kai ai mungodawa Allah tunda anyi mai wuyar ya tsallaka maganin jeki zauna yau sai ya amsa maganarki fitowa khalisat tayi tana murmushin jin dadi ta zauna a parlo zee baby kuwa tana shiga bedroom d'insu ta fada saman bed ta fashe da kuka wi wi da ta rasa ko na menene saida tayi mai isarta ta Mike taje ta wanko fuskarta ta dawo ta kwanta tana rawar sanyi blanket taja ta rufa tana karkarwa, Dr Sardauna yana fita part d'insu ya nufa ransa ab'ace yana shiga ya bude d'akinsa ya fada saman bed ya lumshe idanunsa ya dafe kansa ya rasa meke damunsa sai juyi yakeyi tsikar jikinsa na mimmik'ewa yanajin wani yanayi rasa dalilin hakan ya Addu'a ya shiga karantowa amma yaji feelings bai raguba mamaki yakeyi abunda yasashi yanayin ya rasa ko menene basarwa yayi"

ya lumshe idanunsa

"Tunanin ko menene yaga Aunty amarya na zubawa cikin wata yar tukunya tana Kiran sunan Daddy tsaki yaja ya basar da zancan ya Mike saboda an fara Kiran sallah bathroom yashiga ya dauro alwalla ya k'ara fesa turare ya fito da Mahabeer suka hadu akofar gida suka nufi masallaci zee na rawar sanyi taji ana sallah haka ta Mike ta dauro Alwalla tayi sallah azaune saboda bata iya tsayawa ko fatiha batayi ba ta kwanta saman dardumar. bayan sallah isha ghaisha na zaune aparlo Nuhu ya shigo da sallama yana rike da hannusa meerah ta sakeshi ta ruga gun ghaisha""Oyoyo Meerah dariya tayi Nuhu ya zauna kusan ghaisha yana gaidata""ya su maryama? "" suna lfy ina momy tazo muje yau ina gaiyatarta Ashe jibi ummi raiyan take isowa d'azu Daddy yake fadamun agun aiki? "" eh jibi take zauwa hafeeza tace""babban yaya nima ina zuwa dariya yayi"" to jeki kice ta shirya kema ki shirya ku fito da gudu ta nufi bedroom Daddy ne suka shigo da su Mahabeer atare khalisat ko kunya babu ta kalli Dr tace""yayamun sannu dan Allah maganin ciwon kai zaka bani da kallo suka bita baki dayan parlon har Daddy amma banda Sardauna Wanda ya kwashe mata iska yaje ya zauna kusan nuhu ya rumgumeshi kunya yasa ta Mike tabar gun mahabeer ya bita da kallo""babban yaya ina gaisuwa Nuhu yace""Dr namu wlh maryama na nemanka tace wai amarya ta mata kwace dariya yai""tayi hakuri gobe zan zagaya Daddy ya zauna yana musu dariya mahabeer tace""babban yaya ya gajiyar daura ""wlh ai mun huta ai Aunty Amarya tazo ta zauna suka gaisa da nuhu tana tambayarsa gida, hafeeza tana shiga taga zee akwance k'asa tana rawar sanyi gunta ta matsu ta dafata ""sister zazzabine"

kikeyi?bata iya ko bude idanu parlo hafeeza ta dawo da gudu

"""Babban yaya wlh batada lfy jikinta zafi sai karkarwa takeyi ko idanu bata iya budewa da sauri mahabeer ya Mike ""muje na ganta bedroom suka nufa nuhu ma yabi bayansu Daddy ya kalli Sardauna da yawani kwanta jikin ghaisha ""Dr maza tashi ka kaita hospital dan Allah ka dubata da kyau momyna bansan meke damunta ba kwana biyu duk ta rame shiru yayi dan bayaso yayi"

musu ran Daddy ya baci kamar yada yaga yanzu hankalinsa a tashe ghaisha ta dagoshi ta

"masa nuni ya tashi badan yasoba ya Mike""Daddy idan sun fito ina mota ya fice yana fita suka fito Mahabeer ya daukota ahannu nuhu yace ""Daddy ina Dr ne? "" kuje yana mota shida nuhu suka fice Aunty amrya ranta fari Tas har Addu'a take Allah yasa ta mutu ghaisha ranta duk babu dadi ganin haka yace ta sanyo hijabi su bisu abaya Aunty amarya dan kar aga gazawarta itama tace zata Daddy ya ce ta zauna su Mahabeer suna fitowa Dr Sardauna na mota yana jiransu baya mahabeer ya zauna da zee nuhu na gaba Sardauna yaja motar honr yayi bakin get mai dagi ya wamgame masa get ya fizgi motar da karfi ya harbata saman titi Nuhu na Lure dashi bayason tafiyar kai ya girgiza ya dafa kafadarsa ""Dr namu baidai ce komaiba har suka Iso hospital d'in ko gama parking baiba mahabeer ya bude motar ya fito da zee baki Sardauna ya tab'e ya bishi da harara yanajan tsaki Nuhu ya kallesa ""Faisal meye wai? "" ni

Please Login or Register in order to submit comment