gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading SAFIYYAH Aminar da Ta Karye by Maman Maama Chapter 7 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai neman aurenta bata baka layin da take amfani da shi a can ba?"

Ya ajiye wayar akan cinyarsa tare da sunkuyar da idonsa kasa, abubuwa da yawa suna yawo a ransa. Ta kuma daukan wayar and kafin ya fahimci me yake faruwa sai ta kama hannunsa ta saka fingerprint dinsa ta bude wayar. Ya dago kai da sauri yana kallon ta, trying to process abinda yake faruwa "Mama! Mama Please don't!" Ta juyo tana kallon sa tace "ko zaka kwace wayar ne? Ko kuma akwai abinda kake boyewa ne wanda baka son in gani? I cannot just seat idle and watch you turn into this, sai dai in abinda yafi karfina ne".
Yayi shiru tare da saka hannu biyu ya dafe kansa, shi dai yasan babu wani abin ashsha da yake cikin wayarsa wanda ba zai iya budewa a gaban ta ba, abu daya ne baya so ta gani wanda kuma ya san shine abinda take after, chats dinsa da Safiyya.

Tun shekaran jiya Safiyya tayi blocking din calls dinsa, amma kuma ta manta bata yi blocking dinsa a WhatsApp ba, wanda dama shine kadai social media app din da yake yi anan ne kuma suka fi yin hira. Tun shekaran jiyan kuma yake tura mata sakonni, amma ya fahimci kamar data dinta a kashe take gaba daya dan sakonnin basa zuwa gare ta, amma hakan bai hana shi rubuta wa ba, hakan bai hana shi gaya mata duk abinda yake zuciyarsa ba, all the things that he wanted to say to her, hoping that zata bude ta karanta ko da ba yanzu ba ne ba. Ya tabbatar kuma idan Mama ta karanta sakonnin zata fahimci gaskiya abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya, zata fahimci cewa Safiyya matar aure ce kuma har tana dauke da ciki.

Bata jima tana danna wayar ba kuwa ta ga abinda yake boyewa, tun daga expression din fuskarta ya gane ta gani.  Da sauri take karantawa harshenta har yana hardewa. Wadansu maganganun a fili wasu a zuciyarta. Har tazo kan wanda ya warware mata warware mata damuwarta ya kuma ɗora mata wata damuwar data ninka waccan.

"I only want to know me yasa kika yi min haka, me nayi miki da zaki yi min haka, how can you let me fall this deeply in love with you alhalin kina matar aure?"

Mama ta saki wayar daga hannunta ta fadi akan carpet, "Muhammad!"

Ya jawo hannayensa daga kansa ya rufe fuskarsa da su yana jin wani zazzaɓi mai zafi yana saukar masa.

"Matar aure fa Muhammad. Yanzu Gidado dama da matar aure kake tare? Matar wani?"

A muryar ta yana jin irin zafin da yake zuciyarta and how much disappointed she was in him. Ya zame daga kan kujerar ya sauko kasa "Mama.... Mama wallahi..... Na rantse miki wallahi ban sani ba" ta mike tsaye sannan ba tare da tace komai ba ta yi hanyar fita. Ya mike shima ya bita a baya da sauri "Mama, Mama" bata waiwayo ba har suka zo suka wuce Mufida a falo , Mufida ta bisu da kallo cikin tunanin abinda ya faru, har sai da ta shiga dakin ta sannan ya samu ta juyo ta kalle shi, sai dai ganin hawaye a idonta ya saka ya ji kafafuwansa sun kasa daukan sa. Ya zame ya durkusa a gabanta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Mama dan Allah kar kiyi kuka a kaina. Wallahi ban san tana da aure ba. Boye min tayi" ta juyo da tsawa tace masa "ka tashi ka fita ka bani guri, ka tashi in daina ganinka a gaba na kar kasa inyi maka abinda ni da kai gabakidaya zamuyi nadama" ya mike da sauri ya fita, ta turo kofa ta rufe, amma sai ya kasa tafiya ya jingina da jikin kofar sannan ya zame ya zauna a gurin, babu abinda bakinsa yake furta wa sai innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi kansa ya kasa tantance me yake faruwa da rayuwarsa, a cikin kwanaki biyu rayuwarsa ta juya daga good zuwa bad and now it has turned to terrible.

Tun tasowarsa he has always been Mama's boy, akwai shakuwa da fahimta sosai a tsakanin sa da ita. She raised him and his siblings with love, da soyayya ta raine su da soyayyar kuma ta tarbiyyan tar da su. Tun tasowarsa kuma ba zai iya tuna ranar da ya ganta cikin bacin rai irin na yau ba. He has always been a good boy. Da wahala yayi laifin da zata daga masa murya ma ballantana har ta kai ga zubar da hawaye a kansa. Ya tuna da maganar da Ya Ameen ya fada masa dazu, cewa Safiyya is not worth bacin ran iyayensa, a lokacin maganar bata dake shi sosai ba sai yanzu da yaga bacin ran na gaske.

Yana nan zaune har Mufida da ta ji su shiru ta taso ta biyo bayansu, a lokacin ne ta ganshi a zaune a kasa a kofar dakin Mama, hankalin ta ya tashi dan bata taba ganin yayan nata a cikin irin wannan halin ba. Ta durkusa a gabansa tare da dafa kafadarsa "Hamma? Lafiya? Me yake faruwa?" Ta fada muryar ta tana rawa kamar zata yi kuka. Ya dago jajayen idonsa yana kallon ta yace "Mufida. Kiyi min addu'a. In kinyi sallah kiyi min addu'a" ta rike kukan da yake neman kwace mata tace "kullum ina yi maka addu'a dama Hamma, amma yau zan tashi cikin dare zanyi sallah musamman dan kai, zanyi maka addu'a, insha Allah Allah zai yaye maka dukkan damuwarka".

Ranar cin abincin daren su sam bai yi armashi ba a gidan. Dan yau damuwar Gidado tafi ta kullum yawa, Mama ma kuma juya abincinta kawai take yi ba ci take ba. Daga baya ma sai ta tashi tace musu zata je ta kwanta. Gidado ba haka yaso ba, so yayi tayi masa fada, so yayi ta gayawa Abba in yaso sai ya samu damar yi musu bayani tare da kare kansa, amma maimakon haka sai ta bashi silent treatment.

Kwanan su biyu a cikin wannan yanayin. A rana ta biyun ne Gidado ya samu Mama a kitchen tana aiki tare da Mufida ya ajiye mata wayarsa. "Mama dan Allah in ba zaki saurare ni ba ma fa wayar tawa nan ki duba, ki karanta sakonnin gabaki daya zaki fahimci gaskiya ta" ta juyo ta kalle shi, zuciyarta tana yi mata zafi akan yadda dan lelen dan nata ya koma saboda mace, tace "bana bukatar duba wayarka, na riga naga abinda nake bukatar gani. Kaje kawai, zanyi addu'a akan ka zan kuma yi tunani, sannan zan gayawa mahaifinka halin da kake ciki dan ya damu da ya sani, abinda duk muka yanke a kanka kuma dole shi zaka bi". Ya gyada kai cikin amincewa. Shi indai zata daina fushi da shi to kowanne hukunci ne ya yarda zai dauka.

Washegari ya fahimci cewa ta gaya wa Abba abinda ya faru, dan sanda ya gaishe shi bayan sun dawo daga masallacin sallar asuba kin amsawa yayi, rana ta farko a rayuwarsa daya gaishe da mahaifinsa bai amsa masa ba. Wannan ya sa a ranar ko dakinsa bai koma ba anan falo ya kwanta anan falon yana jiran Abba ya shirya ya fito ya sake gwada sa'ar sa ko zai samu ya kula shi, yayi masa fada, kai ko dukansa ne ma ya yarda yayi in dai zasu daina fushi da shi.

Yana nan kwance Mufida ta fito, yaji tazo tana taba wuyansa sannan ta koma suka dawo tare da Hafeez, yana ji suna ta maganganun su sannan Hafeez din ya tafi suka dawo tare da Abba. Yaji Mama tazo itama. Ya tashi zaune yana jin sanyin acn falon tayi masa yawa a jikinsa. Abba ya aika Mufida yace ta kawo masa abinci daga nan kuma sai ya sallame su ita da Hafeez. Gidado ya dauki cup din tean da aka ajiye a gabansa ya kai bakinsa amma bai kurba ba sai ya ajiye shi, pretending kamar yasha. Mama tace "dauki ka shanye" babu musu ya dauki kofin ya shaye tas duk da kona mishi baki da yake yi.

Abba ne yayi magana yace "mamanka ta bani wani labari da ban taba tunanin jinsa ba. Tace min yarinyar da kake ta maganar za'a je nema maka auren ta, Safiyya, matar aure ce, haka ne"

Gidado ya gyada kai, har lokacin zuciyarsa ta kasa sabawa da jin sunan Safiyya tare da kalmar matar aure a hade a sentence daya. Abba yace "to me zaka ce game da haka?" Gidado yayi gyaran murya yace "ban san haka bane ba. Sai last gani na da ita take gaya min hakan" mama tace "take gaya maka me?" Yace "tace min..... Tace she is married".

Abba ya gyara zama "amma kai tun da kuke da ita ba ka taba gane cewa matar aure ba ce ba? Ta yaya? Kana me zata ninke ka a baibai tsahon lokaci baka gane ba? Wanne irin so kake mata da zai rufe maka ido from the obvious?"

Gidado yace "Abba ban san ya zanyi bayani ku gane ba. Da ace kun santa zaku fi yarda da magana ta. Babu wani alamun aure a tare da ita. Ban taba zuwa gidan su ba ballantana in gane daga nan...." Mama tace "baka taba zuwa gidan su ba? All these while har ka yi gini ka saka ni hada kayan lefe amma baka taba zuwa gidan su ba?" Gidado ya dafe kansa "how foolish he might have looked a idon iyayensa, how foolish duk wanda yaje abinda ya faru zai dauke shi, amma kuna it is easy to judge idan har abin bai faru da mutum ba.

Yace "Mama, Safiyya student ce a MD, a hostel take zaune, asalin iyayenta yan Kano ne, mahaifinta ba mazauni bane kusan ko da yaushe baya kasar. Duk sanda akayi hutu itama tana binshi whichever kasa yake a lokacin. A cewar ta kullum tana kokarin samun chance idan yazo gari ta kaini. Tace bata son kaini gurin kaninsa, wanda yake zaune a garin nan, tafi so in ganshi direct because of some family issues that she didn't mention. I didn't push sosai saboda baban bashi da lafiya, kusan ko da yaushe yana asibiti. She ......"

Mama ta katse shi "wannan shine abinda ta gaya maka? To bara in gaya maka gaskiyar magana. Babu wani gurin babanta da take zuwa. My guess is gurin mijinta take zuwa in anyi hutun. Yana kasar waje ita kuma tana nan tana karatu, in anyi hutu kuma ta tafi gurinsa. In ta dawo kuma kai gaka. Ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya".

Gidado ya rufe idonsa yana tuno hotunan Safiyya da Daddyn ta, most of them a asibiti, ya girgiza kansa, baya son yayi tunanin abinda zuciyarsa take hasaso masa.

Abba yace "to a karshe kuma ya akayi ka sani?"

Ya bude idonsa yace "taje holiday kamar yadda ta saba, and she have been acting off for months, she came back tace tana son ganina, muka hadu a office dina, and she told me".

Abba yace "and kai me kake tunani? Do you believe she is really married ko kuma she is lying tana so ne dai kawai ta rabu da kai?"

Gidado yayi shiru because that was a million dollars question, bai san amsar ba, zai kuma iya bayar da komai dan yasan amsar. Cikin jikinta shi yake convincing dinsa akan cewa tana da aure din, amma kuma yanayin yadda tayi masa magana, da abubuwan da suka gudana kafin ranar, suna so su gaya masa cewa da akwai wata a kasa. Amma ya kasa fahimtar if those things are real ko kuma zuciyarsa da take cike da sonta ne take imagining dan ta bata kariya kamar yadda Ya Ameen ya gaya masa.

Ya dago kai yana kallon Abba yace "I don't know Abba. I don't know what to think. I don't know what to believe " yayi shiru kuma sai yayi deciding ya gaya musu all he knows, idan akwai wanda zai taimaka masa kaf duniya to su ne. Sai ya kara da cewa "she is pregnant".

Da sauri Mama tace "ita ta gaya maka?" Yace "gani nayi" tace "to wannan shine dalili, ta gaya maka gaskiyar ita matar aure ce saboda cikin jikinta. Shi ciki ai ba'a boye shi. Bata yi niyyar fada maka ba sai data tabbatar in bata fada ba ma zaka gani da idonka" Abba ya gyada kai cikin amincewa sannan yace "that will be all. Tashi kaje".

Gidado ya mike, a ransa yana jin mix feelings. Na farko yana jin dadin iyayensa sun fahimce shi duk da dai har lokacin suna ganin da laifin sa a ciki, amma kuma yana jin babu dadin yadda suka dauki maganar, a gurinsu a yanzu babu halitta worst than Safiyya.

Yana rufe kofa Abba ya juyo yana kallon Mama da bacin rai a fuskar sa yace "da ace nasan wacece yarinyar nan da ta mayar min da ɗa haka wallahi da sai na san waye uban ta a Nigeria" Mama tayi murmushin takaici tace "she can be traced, tunda daliba ce a MD, shima kansa Gidadon zai iya tracing danginta idan yayi niyya but to what end? Menene amfanin hakan? Allah zai saka masa kawai. What we should concentrate on a yanzu shine ganin ya dawo hayyacin sa".

Ya gyara zamansa yace "abinda muka yi magana akai kawai shine" tayi ajjiyar zuciya tana girgiza kanta. "I don't know dear, what works for some might not work for others. Aure kuma is a life sentence. Bana son garin neman gira mu rasa ido".

Ranar Gidado wuni yayi da wayarsa a hannun sa. Ya daina kiranta ya kuma daina tura mata messages amma wuni yayi yana kallon pictures da videos dinsu together, trying to figure out a ina hint din cewa tana da aure yake, trying to see beyond the obvious amma babu abinda ya gani sai soyayya, tsantsar soyayya. A karshe sa yaji kamar zuciyarsa zata fashe sai ya rufe wayar ya kuma rufe idonsa, a haka bacci ya dauke shi, cikin baccin ne yayi mafarki da Safiyya a tsaye a kofar office dinsa hannayenta biyu rike da cikinta, hawaye sharkaf a fuskar ta, ta mika masa hannu daya tana kiran sunan sa "Gidado please, I am sorry. Muhaammaaad...." Yayinda shi kuma ya saka hannu biyu ya hankada ta waje sannan ya rufe kofar.

*Her* 🧕🏻

Kwanaki ukun nan sun wuce wa min very slowly. Bawai ina ganin rashin saurin kwanakin bane saboda kasancewarsu event-less, a'a, abubuwa ne da yawa suke faruwa not one after the other but all at the same time, abubuwan da suka cika min kwakwalwa ta har suka sa ka bata gane komai. Mommy ta saka ni a gaba da zancen auren Mukhtar, Mukhtar ya takura min da kokarin chanja min ra'ayi a kansa, Abdul ya cigaba da rokon na akan kar na zabe shi a matsayin miji, yayin da Daddy ya cigaba ta tambaya ta akan wanene zabina.

Ni kuma a gurinta zancen aure shine least of my problems, babban matsalata shine lokaci yayi sauri yazo a raba ni da cikin jikina ko na samu freedom ɗin da zan ji daɗin jinyar Daddy, ko hakan zai bani damar rekindling relationship din mu. Sai dai kuma shi Daddy kullum maganar sa ita ce "bana son in tafi in barki a wannan yanayin Safiyya. So nake in gyara rayuwarki kafin in tafi in barki".

And through all these, Gidado weight heavily in my heart.💜 Tunanin halin da yake ciki ya kara wa wuni na tsaho, mafarke mafarken sa kuma sun hana min bacci mai nauyi.

A ranar da muka kwana biyar a garin ne na samu nayi dogon bacci da safe irin wanda na jima ban yi irin sa ba. Har Mommy ta tashi ta shirya ta tafi asibiti gurin Daddy ta barni bacci. San da na farka na danji dadin jikinta sosai, dan rashin baccin ma yana daya daga cikin abubuwan da suke toshe min tunanina. Na tashi nayi wanka na fito ina shirya wa ina tunanin yadda zan kai kaina asibitin tunda babu kuɗi a hannuna dan tunda muka zo ban yi chanjin kudi ba. Na zauna tana lissafe lissafen abun yi sai ga Aunty Hajjo ta shigo dakin. Na gaishe ta ta amsa sai naga ta samu guri ta zauna akan kujera, wannan ya saka ni feeling uncomfortable na sunkuyar da kaina, hoping cikina bai fito sosai ba. Sai naji ta fara magana "Safiyya dama ina ta so muyi magana da ke amma bana samun damar kasancewa da ke ke kadai, kuma maganar da zan yi miki da ke kadai nake son yinta.

Na cigaba yin shiru ban ce komai ba, ta cigaba "Sa'adatu ta bani labarin abinda ya faru dake, ko kuma ince abinda ke kika gaya musu cewa ya faru da ke, dan a yadda na fahimta basu yarda da labarin ba nima kuma har yau labarin bai kwanta min a rai ba. Amma kuma na kasa ganin laifinki ballantana in zauna inyi miki fada ko inji na tsane ki ko inji ina kyamar ki. Hakan kuma yana da alaƙa da mahaifiyar ki. Allah ne shaida ta har ta rasu ina yi mata kallon yaruwa ta, in fact zan iya kiranta da role model dina dan nakan kwaikwaye ta akan abubuwa da yawa musamman harkar kula da miji da kuma nuna soyayya ga yaya. Ina iya tuno da sanda ta haife ki Safiyya, ina tuno irin tarin soyayyar ki da na gani a idonta a lokacin da naje yi mata barkan haihuwar ki. Ban yi mamakin yawan soyayyar ba saboda la'akari da nayi da jimawar da tayi tana neman haihuwa kafin ta same ki, na kuma kara fahimtar soyayyar sanda ta gaya min cewa likitoci sun tabbatar mata da cewa bayan ke ba zata sake haihuwa ba".

Na saka hannu na goge hawayen da already ya fara bin fuskata, ta cigaba "ina kuma iya tuno lokacin rasuwar ta Safiyya, a gaba na aka yi mata sutura. Abinda nafi iya tunawa a lokacin shine sautin kukan ki. You were barely two years old. Kowa a gidan yayi kokarin ya rarrashe ki amma kina ta kuka kina kiran sunan da kike gaya mata 'ammi', abinda yafi tayar min da hankali a lokacin shine idan na kalle ta a kwance babu rai kuma na tuno da cewa ruhinta yana gurin kuma tana jin kukan ki amma bata da damar rarrashin ki duk kuwa da irin tarin soyayyar da take yi miki. It broke everyone's heart, musamman saboda yadda mutuwar tata ta kasance".

Ta dakata tana kokarin daidaita muryarta, daga alama kuka ne yake kokarin kwace mata. Ta cigaba "wannan shine nightmare din kowacce uwa, and I couldn't help but think about dan karamin dana Abdul Hakim, na lissafa idan nice na mutu what will happened to him? Nayi kuma tunanin taki rayuwar ya zata kasance? Tun a lokacin na fahimci kina cikin jarabawa babba kuma kin rasa wani bangare na rayuwar ki da ba za'a iya replacing ba, amma kuma ban dauka gibin da aka samu zai kai ki ga matsayin da kike ciki a yanzu ba. I offered to take you, dan inyi kokarin cike wannan gibin, bayan ni mutane da yawa sunyi kokarin daukan ki amma babanki ya hana, yaki bawa kowa ke yace shi zai raini abarsa da kansa. Ina iya tuna wata rana da muka je tare da mai gidan nan dan mu duba halin da kuke ciki, muka tarar da shi ya goya ki da zani a bayansa kina tayi masa rigima, duk da ma'aikatan da suke gidan ku amma ba zai iya bawa kowa ke ba saboda girman soyayyar da yake yi miki".

Ta sake yin shiru. Muka yi shiru baki daya sai sautin kuka na kadan kadan, ta cigaba "ban sani ba ko ma'anar labarin nan da nake baki tana fitowa, ban sani ba ko kina gane me nake nufi. But you are so precious Safiyya. You are far greater than yadda kika mayar da kanki. And you have enemies everywhere. Labaran da Sa'adatu ta bani akanki, ban san wanne ne gaskiya wannan ne akasin hakan ba. Ba zan kuma yi claiming nasan abinda yake zuciyar mutane ba. Ta gaya min cewa za'a hada auren ku ke da Mustapha idan kin haihu. Amma kuma mai gidan nan shima ya gaya min cewa suna son idan kun amince zasu hada auren ku ke da Abdul. Ban san wanne ne gaskiya ba. Amma ina son gaya miki har yanzu a raina ina da niyyar daukan ki in rike ki in dai har zan samu wannan damar. In kin zabi Abdul zan so hakan. In baki zabe shi ba kuma ina so ki san cewa I will be here for you whenever you need a mother".

To gain access to the book contact

👇

0704 203 0419

Ta manhajar telegram



****. ****. ****. ****.

❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹
*By*
*Maman Maama*


*Episode Seven (7): The Good and the Bad Choices*


A ranar ban je asibiti ba sai dare, na zauna a daki ni kadai with my thoughts thinking in nayi spending a day with my self zan iya yanke wa rayuwata shawara. Amma sai dai har daren ban zamu na yanke din ba, sai dai kamar kullum, ranar ma nayi adduoi sosai akan Allah ya dube ni ya kawo haske a rayuwata.

A ranar ne kuma na fahimci dalilin da yasa na kasa samun zabi a cikin samarin da Daddy ya lissafa min, dalilin kuwa shine Gidado. In dai har zan cigaba da yiwa aure hangen da muka yi masa ni da Gidado to kuwa sai dai in Daddy yayi zuciya ya zabar min da kansa dan ba zan iya zabar kowa ba. Amma kuma sai naji cewa ina ma dai zaiyi hakan? Da ya dauke min wani babban nauyi a kaina, da ya cire min guilty feeling da nake ji a raina a duk lokacin da nayi tunanin zabar wani ba a matsayin miji wanda ba Gidado ba.

In dai har ba Mustapha zai zabar min ba to bani da matsala.

Abdul na san idan na zabe shi bani da matsala da iyayen sa, dan maganar da Aunty Hajjo tayi min yau ta kuma tabbatar min da kaunar da take yi min, sannan Uncle Sufyan kuma zan iya kiran shi da second father dina dan duk duniya Daddy bashi da aminin da ya amince wa kamarsa. Amma kuma Abdul yana da wadda yake so kamar yadda ya gaya min baki da baki. Kuma experience dina da soyayya ya saka na fahimci cewa kowace ce ma yana kaunar ta sosai. Duk sanda nayi tunanin zabarta sai in hasaso cewa Muhammad ne sanda muke tare muke tsara rayuwar mu tare sai iyayensa su haɗa shi aure da wata saboda selfish reason ɗin su. It would have destroyed our lives. And I do not want to destroy someone else's life dan ni in samu farin ciki.

Mukhtar on the other hand yana so na, dan yana daga cikin few mazan da suka taba physically confessing soyayyar su gare ni. Mukhtar ya jima yana so na, soyayyar da ni a gurina na fara daukan ta obsession har ta fara irritating dina kuma tasa yayi loosing girmansa na yaya na a idona. In na aure shi at least zan zauna da wanda yake sona ko da kuwa ni bana son nasa amma kuma iyayensa fa? Uncle Ahmad shine dan uwa daya tilo da Daddy yake dashi a duniya, komai namu a hannunsa yake tunda Daddy ya fara rashin lafiya more than five years ago, sai dai kuma tun ina karama nake samun problem dashi da matarsa dan suna min kallon spoilt girl da bata da tarbiyya, problem din namu kuma ya karu a shekarun bayan nan, sannan ya zama worst bayan bayyanar ciki na. Zasu karbi aure na dole, and zasu iya farinciki ma da hakan, sai dai hakan baya nufin zamu daidaita dasu ko kuma zasu kasa goranta min ko nan gaba.

And Mustapha, in na zabi Mustapha rayuwa ta will be a disaster, dan ban taba tsanar mutum ba kamar yadda na tsane shi and there is no way da zan iya neman aljanna ta a karkashin

Please Login or Register in order to submit comment