gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading SAFIYYAH Aminar da Ta Karye by Maman Maama Chapter 3 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabaki daya bakin ya gauraye da daci kamar da ruwan madaci aka dafa abincin, makogwaron sa ya toshe abincin ya kasa wucewa ciki. Haka yayi ta taunawa dan babu damar ya zubar da shi, har daga karshe ya samu ya hadiye shi da kyar.

Ya dago kai suka haɗa ido da Abba da Mama a lokaci daya, yayi sauri ya sake mayar da kansa kasa ya cigaba da juya abincin. Abba ya yi magana "Malam Muhammadu, what is it?" Ya ajiye chokalin hannunsa tare da yin kokarin bada uzurin da zai masking damuwar sa "uhmm.... Abba dama ..... Dama maganar aikin da muka yi da kai, ina ganin in ka yarda zan bar wannan din in dawo gurin ka kawai. Wannan ɗin is exhausting. Na gaji". Abba ya sake cewa "shi kenan?" Gidado ya gyada kansa kawai bai ce komai ba.

Kamar daga sama yaji Mama tace "ya maganar Safiyyan? Tazo ɗin? Kunyi maganar?" Gidado ya sake daukan chokali ya cigaba da juya abinci ba tare da ya kalle ta ba yace "bata zo ba Mama. Bata samu damar zuwa ba" tace "but am sure kunyi magana da ita a waya ko? Kasan dai next week za'a zo saka ranar Mufida, ka kuma san na jima ina fadar cewa tare zan haɗa ku" ya gyada kai "na sani Mama. Bamu yi waya ba. Zamuyi amma".

Sai kuma ya mike. "Bana jin dadi, bana jin cin abincin nan. Zan je in dan kwanta" Mufida ce tace "Allah yasa dai ba zazzaɓi zaka yi ba Hamma, fuskar ka tayi pale. Ya danyi mata murmushi yace "Ameen dear". Daga haka ya nufi hanyar da zata kai shi inda dakunan su suke. Har ya shiga ya rufo kofa yana jin idanuwan iyayensa a kansa.

Yana shiga dakin sa direct gaban dresser ya tafi, ya tsaya a gaban full mirror dinsa yana kare wa kansa kallo. Ya saka hannu ya shafa fuskarsa yaji ta dauki zafi kamar mai zazzaɓi. Sai kuma ya lura da abinda Mufida tace fuskarsa tayi fari tas kamar takarda. Sai yaji muryar Safiyya a kunnen sa yadda take tsokanar sa.

"Da wata farar fuskar ka anan"

Tana fada ne a matsayin tsokana duk he knows she is saying it as a compliment, or so he thought.

Duk sanda ta fadi haka shi kuma yakan mayar mata da cewa "da wata beautiful face dinki anan".

Ya tuna ranar da ta fara ce masa me farar fuska. Ranar da ya fara ganinta a duniya. Shekaru da dama da suka wuce. Shekaru goma da suka wuce.

He was just seventeen years old. And she was eleven years old.

****.    ****.    ****.    ****.    ****.     ****

A cikin jirgi ne, ranar da zai bar Nigeria zuwa Manchester , United Kingdom dan fara karatun degree dinsa na farko. An riga an gama yi masa komai dan haka shi kadai aka saka a jirgi ya tafi. Wannan shine karonsa na farko na yin tafiya mai wannan tsahon shi kadai. Tun yana dan karamin yaro, ya kasance yana da aerophobia ma'ana fear of flying, duk sanda ya hau jirgi ya kan ji tsoro musamman a gurin tashi da sauka ko kuma in aka shiga turbulence.

A duk sanda zasu yi tafiya tare da family yakan rike hannun Abba ko Mama, har sai jirgin ya daidaita sannan ya saki. A ranar kuma kasancewar babu Abba babu kuma Mama sannan babu kowa a seat din kusa da shi, sai ya kama handle din seat ɗin ya kankame tare da rintse idonsa. Sai dai duk da haka jiri yake ji, kansa juyawa ya ke yi.

A cikin haka ne yaji an rike hannunsa. Ba tare da ya kalli waye ba sai ya damke hannun daya rike nasa ɗin da karfi har sai da jirgin nasu ya dai daita. Ya sauke ajjiyar zuciya tare da bude idonsa a hankali, sai kuma yayi sauri ya kalli side din da aka rike hannun nasa.

Yarinya ya gani yar karama wadda ba zata fi sa'ar Mufida ba. Ta karkata kai side daya tana kallon sa fuskarta dauke da murmushi. Yayi sauri ya saki hannun ta yana yarfar da nasa hannun "You? Who are you? Where are your parents?" Ya karasa maganar yana duddubawa around them. Sai dai bai ga kowa da yayi kama da iyayen ta ba, kusan ma inda suke zaunen basu da yawa.

Ya sake dawo da dubansa kanta yace "where are your parents?" Direct tace "my mother is dead. My father is in Manchester yana jirana" ya koma ya zauna sosai "are you telling me ke kadai aka sako a jirgin nan daga wata kasar zuwa wata?" Ta daga kafada tace "there is nothing to it really. Uncle Ahmad ya kawo ni airport ya danka ni a hannun cabin crew, they will take care of me har mu sauka and my Dad will be waiting" ya tsaya kawai yana kallon yadda take zarar magana yace "awwn, rich kids, yayan Daddy da Mommy. Now if you don't mind i need to sleep. Ki koma wherever it is that you came from. I don't want any trouble".

Ta gyara zama. "i won't trouble you. I prefer sitting here" ya bata rai irin yadda yake yiwa Mufida "ke! Bar gurin nan nace miki" amma maimakon tabi umarnin sa kamar yadda Mufida take yi sai ta kyalkyale da dariya tare da kwaikwayon yadda yayi maganar "ke! Bar gurin nan nace miki" ta sake wata dariyar sannan tace "fillo". Yaji wani takaici ya kama shi kamar ya rufe ta da duka, amma maimakon haka sai ya mike tare da ɗaukan headphone dinsa da niyar bar mata gurin.

Sai dai yana mikewa jirgin su ya shiga turbulence. Ya koma ya zauna da sauri tare da mayar da seatbelt dinsa, sai da suka fita daga turbulence din sannan ya lura cewa ya kuma rike hannun ta da hannayensa biyu. Ya sake cika ta yana gyara zamansa. Tace "you have aerophobia you cannot help it. There is nothing to be ashamed of"

Ya bata rai a ransa yana tunanin wannan wacce irin yarinya Allah ya hada shi da ita yau. Yace "wai ke parents din ki basu warning dinki not to talk to strangers ba?" Ta gyada kai da sauri tace "Mommy did" yace "you just told me mamanki ta rasu" tace "yes, Mommy is my step mom. But she is more like a mother to me because she loves me so much" yace "ohh, shi yasa ba kya jin maganar ta kenan ko?" Ta yi shiru tana kallon sa da alamr bata gane me yake cewa ba.

Yace "she told you kar kiyi magana da strangers, amma gashi kina yi min magana ni" ta girgiza kai "saboda you won't harm me" ya bata rai "ya akayi kika san hakan? You don't know me" ta daga kafada tace "I don't know how I know, i just know" yadda tayi maganar yasa yayi murmushi, sannan yace "you are too smart for your own good, zaki iya cigaba da zama anan, amma kar ki dame ni da surutu" ta yarda da hakan, amma kuma bata cika alkawarin ba dan for the hours da suka dauka suna tafiya sam bata barshi ya runtsa ba, labarai dai kam ya sha su, duk yan gidan su babu sunan wanda bai ji ba, Mommy, Daddy, yaya Mustapha, Hassan, Hussain, Safina har zuwa kan yan aikin gidan su.

And he held unto her hands sanda jirgin su zai sauka. Sai bayan sunyi landing sannan yace mata "kim fada min sunan kowa a gidan ku amma baki fada min naki ba" tace "Safiyya. Sunana Safiyya Adam Muhammad. Amma yan gidan mu suna ce min Fiyya. I don't know why"

"Piya?" Ya maimaita

Tayi dariya "Fiyya. With an F and double y"

"Piya" ya sake maimaita wa

Tayi ajjiyar zuciya "fillo" ya bata rai, tayi dariya.

"In kace Piya kana nufin something totally different from my name" ya bata rai yace "me Piya din yake nufi?"
Tace "love ko beloved, in India" ya gyada kai yace "ohh"

Tace "and ina da wata super power, I can tell you your name. You are Muhammad Auwal Muhammad" yayi sauri ya kalleta da mamaki, sai ta daga masa flight ticket dinsa da ya fadi kasa bai sani ba. Tace "har ka ji tsoro, da wata farar fuskar ka anan".

To gain access to the book contact

👇

0704 203 0419

Ta manhajar telegram

****.    ****.     ****.    ****     ****.    ****

❤‍🩹*SAFIYYAH*❤‍🩹

*By*
*Maman Maama*

*Episode three (3): the two choices*


*Her🧕🏻*

Har dare yayi na kwanta bacci babu wanda ya kara shigowa gurina babu kuma wanda ya neme ni sai Mommy da ta shigo ta matsa min  naci abinci sannan nasha prenatal vitamins dina. Tun da na tashi da assuba kuwa nayi wankana na shirya na saka jilbab ɗin da nake fatan zai rage nuna wa mutane cikin da yake jikina. Dama kayana a hade suke ban fito da su daga jaka ba, duk abinda na fito da shi kuma nayi deciding cewa ba zan tafi dashi ba dan bani da karfi na jiki dana zuciya da zan iya yin wani abu akai.

Na koma na kwanta a kan gado na nannade jikina da jilbab ɗin, na rufe idona da fatan bacci zai dauke ni ko na samu na ɗan rage ciwon da kaina yake yi min, amma sai dai a maimakon bacci, memories ne suka yi ta overlapping a cikin kaina, memories of yarintata, memories of relationships dina da family dina a da da kuma a yanzu, memories din Gidado and all the hopes we had for a future together, and the memories of daren da ya lalata komai a rayuwa ta, daren last birthday din Gidado.

Na tashi zaune tare da dafe kaina da hannayena ina jin yana barazanar tarwatsewa. Sai kuma na daga kaina sama ina kallon hoton da yake facing ɗin gadona, hoton mahaifiyata a kwance akan gadon asibiti rike da yar jaririya a hannunta, fuskarta cike da tsantsar farin ciki. Nayi ajjiyar zuciya, ina ma dai rayuwa tana da control button, ina ma dai zan iya rewinding komai na koma yar jaririya na cigaba da jin dumin mahaifiyata, inama.......

Sai nace a fili kamar mai magana da ta cikin hoton. "you set me up to be devoured by the blood thirsty vultures, yanzu gashi sun kassara rayuwata" nayi tsaki na juyawa hoton baya, sai kuma na sake juyawa nace "I miss you though".

Knocking din da naji a bakin kofa ya saka na dawo da dubana kan kofar sannan na kalli agogo, 7:35. "Yes?" Nace ina gyara hijab dina tare da sake haɗe fuska. Sai dai kuma ana bude kofar yanayin fuska ta ya juya zuwa murmushi. At last, someone I can talk to, someone who truly loves me.

Suka shigo a tare suma fuskokin su dauke da murmushi, na bude musu hannayena amma maimakon su fada jikina kamar kullum sai suka zauna a sides dina sannan suka rungume ni a tare. Nayi ajjiyar zuciya ina kara rungumar su jikina, ina jin yadda suka kara girma duk su biyun, a tsaho yanzu duk sun kere ni.

"Yan biyun yaya Fiyya, I am glad you made it. Ina ta jin babu dadi na dauka ba zan ganku ba har mu tafi".

Hassan ya dago kansa daga kafada ta yace "kinga gudun da muka yi a mota kuwa? Mommy tace mu hakura mu zauna tunda jiya ma evening paper mukayi amma muka dage sai da muka zo dan mu ganki kafin ki tafi"

Hussain yace "Mommy tace zaki jima baki dawo kasar nan ba, haka ne? Amma zamu iya zuwa mu kai miki ziyara in mun gama waec ko?".

Na gyada kai nace "duk sanda kuke son ganin mu kuyi min magana ko kuyi wa Daddy magana, za'a siya muku ticket ku tafi. And anything you need, ko menene, ku kira ni ku gaya min".

Suka gyada kai a tare, Hassan yace "but this is not fair, Daddy is not being fair to you. Me yasa zai miki aure yanzu? Mommy tace aure zai yi miki da yaya Mustapha. Yaya Mustapha fa for God's sake. It shouldn't be. Kamata yayi a barki kiyi healing, ki kuma samu wanda kike so ku fahimci juna sannan sai kiyi aure"  na kalle shi ina murmushi nace "all that sounds so good. Amma kuma ba haka Daddy ya zaba ba, and I am sure Daddy ba zai zaba min abinda zai cutar da ni ba, da abinda ka fada ɗin shine zai fi min dai dai I am sure Daddy shi zai zaba min, you should be kinder to him".

Hussain yace "but what about you. You are obviously not happy" nace "it doesn't matter. Maybe I will be nan gaba. Hussain, a yanzu haka happiness dina kadan ne a cikin irin abinda zan iya sacrificing dan in gyara relationship dina da Daddy, zan iya bayar da komai, ko da kuwa rayuwata ce to have Daddy hug me and say 'I love you Safiyya'" na karasa maganar ina share hawaye da bayan hannuna".

Suka yi shiru gabaki daya sannan Hussain yace "he loves you, you know.  Yafi son ki akan kowa" na yi yar karamar dariya mai kama da kuka nace "my dear brother, am not sure about that. To him, I am just a big fat disappointment".

Hassan yace "no you are not. He loves you. We all love you". Nayi kokarin chanja topic ta hanyar cewa "sooo, waye yayi driving a cikin ku, naji kunce kun sharara gudu" Hussain yana dariya yace "Hassan ne" Hassan yace "i passed my driving test last week, shine yanzu na gwada skill dina" nace "yayi kyau. Amma a daina gudu da yawa. An kawo muku motocin kenan?" Hassan yace "no... Ta wani friend din mu ne" na bata rai "why? Me yasa ba'a kawo muku ba? Kun sake yiwa Uncle Ahmad maganar?" Hussain yace "munyi masa fa, sai kawai ya rufe mu da fada wai me zamuyi da personal cars bayan akwai motoci a gida"

Na fara girgiza kaina ina cewa "nasan akwai motoci a gidan ai, ni nayi niyyar zan siya muku motoci a matsayin gift na jamb da kuka ci. Zanyi masa magana. Allah yasa zai zo yau yayi wa Daddy sallama, zanyi masa magana".

Hassan yace "uhm uhm, kar ki sa yayi miki faɗa kema. Yanzu kula da lafiyar ki yafi komai muhimmanci. Ki rabu da shi kawai". Na sake girgiza kai stubbornly "zan yi masa magana".

A haka muka cigaba da hirar mu har sai da Esther ta shigo da tray din breakfast ɗina ta kuma sanarwa su Hussain da cewa nasu abincin yana kasa  sannan suka mike suka yi min sallama. Na tashi tsaye nima na rike hannayen su a cikin nawa nace "idan kunje gurin Daddy, be nice to him please, ku fada mishi maganganu masu daɗi and tell him you love him, hug him" suka tsaya kawai suna kallona amma kuma fuskokin su sun nuna cewa sun fahimci abinda nake cewa, a tare suka gyada kai, nayi musu murmushi sannan ta saki hannayen suka fita jiki a sanyaye.

Suna fita Mommy ta shigo ta kuma saka ni a gaba sai da na ci abinci, ina ci tana yi min hira. "Gwara ki ci abinci ki koshi dan ba lallai bane ki iya cin abincin jirgi. Kuma gwara ki ci abinci a daki dan ban san waye zai shigo gidan nan yau ba, ko ma'aikatan gidan ma ban yarda su san halin da kike ciki ba, dan hausawa sunce munafukin ka tabarmar ka".

Muna nan zaune Safina ta shigo ta zauna tana kallona ina shan tea din da Mommy ta hada min, tace "I will miss you little sister. Though na san ba dadewa zakiyi sosai ba. Kina dawowa kuma sai mu sha biki" ta karasa tana murmushi. Ban ce komai ba har sai da Safina ta mike zata fita sannan na daga kai nace mata "I will miss you too. Allah ya bada sa'ar karatu" tace "Ameen. Nagode" sannan ta fita.

Ban fita ba har sai da aka gama saka duk kayan mu a cikin mota, sannan Mommy tazo da kanta tace inje in shiga mota, shima sai data tabbatar jilbab din jikina ya boye cikin sannan ta kama hannuna muka fita tare.

Sai dai muna fita compound din gidan motar Uncle Ahmad tana shigowa, driver yana tukawa, Mukhtar a gaba, Uncle Ahmad a baya. Mommy ta tura ni gaba "sauri ki je ki shiga mota gani nan zuwa" amma sai na makale, ina so nayi magana da Uncle Ahmad akan maganar motocin twins. Mommy ta sake turani amma maimakon nayi hanyar motar da zamu tafi airport a cikin ta sai nayi hanyar inda su Uncle Ahmad sukayi packing.

Kafin na karasa suka fito, kallo daya Uncle Ahmad yayi min ya dauke kai, yayin da Mukhtar kuma ya taho direct gurinna yana washe baki. Sai a lokacin nayi nadamar kin jin maganar Mommy. Ya tare min hanya yayin da ni kuma nake kokarin wuce shi na tafi gurin Uncle Ahmad. Yace "Fiyya ko gaisuwa babu? Ko nayi wani laifin ne wai? Ni ina ta jin dadin zan samu na ganki ke kuma ko kallo ban ishe ki ba ko?"

Na tsaya tare da juyowa ina kallon sa. "Yaya Mukhtar, barka da zuwa, ya hanya. Nice to see you. Bye". Na juya zan tafi ya sake tarar gabana. "Dan Allah Safiyya ki tsaya. You don't have to be cold. Ki bani dama muyi magana ta fahimtar juna please. Minti biyu ya ishe ni" nayi ajjiyar zuciya ina lura da Mommy da ta bata rai a gefe tana kallon mu. Nace "ina jinka" ya gyara tsayuwa sa, na lura da yadda yake kokarin kar ya kalli cikina, yace "ina jin yau kusan shekaru biyu kenan da na fara gaya miki abinda yake zuciya ta. So kin riga kin sani. Ina so ne in gaya miki cewa babu abinda ya chanja a zuciyata a game dake duk da rejecting dina da kikayi the first time. Babu abinda ya chanja a zuciyata duk da wannan abin da kika yi" ya fada yana waving hannunsa around cikinta ba tare da ya kalli cikin ba, naji zuciyata ta tattare ta dawo wuyana, na nade hannuna a kirjina nace "what do you want, Mukhtar?" Ya dago kai yana kallon cikin idona, nima ban dauke nawa ba, yace "you know exactly what I want" nace "no, I don't. Just skip the whole preamble ka gaya min direct. Menene kake bukata daga gare ni".

Ya sauke idonsa kasa yana hadiye yawu yace "idan kin amince ..... A matsayi na na dan'uwanki na jini, ina so in kin haihu, zan taimaka miki in aure ki, har abada babu wanda zai san me ya faru. Har abada babu wanda zai san me kika yi" na kankance idona a kansa nace "Mukhtar, a tsakanin ni da kai tabbas akwai wanda yake bukatar taimako, kuma daga ni har kai mun san waye".

Na juya da sauri na bar inda yake, raina a matukar bace, blindly nake tafiya ina magana da kaina kasa kasa, ban ankara ba sai gani na nayi a gaban Uncle Ahmad, na dan ja baya sannan na gaishe shi a diririce "uhmm. Uncle. Ina kwana" yana danna wayarsa ya amsa. "Lafiya" har na wuce shi sai kuma na tuna da alkawarin da nayi wa twins dan haka na dawo da baya. "Uncle.....dama ina so zanyi maka magana ne ... Dazu munyi magana da twins akan cars din da nace a siya musu. Shine nace bara in tuna maka maybe ka manta ne".

Wani mugun kallo daya watso min ne ya saka a lokaci daya naji ina ma dai jiya da na kwanta bacci yau ban tashi da rai ba. Na ja da baya taku biyu cikin sauri dan a tunani na rufe ni zaiyi da duka amma instead sai yace cikin daga murya "Safiyya? Yanzu rashin kunyar taki har ta kai haka dama? Zamani har ya kai haka lalacewa? Ke sam baki ma damu da wannan abun kunyar da yake jikin ki kike yawo da shi ba har kina da karfin halin tsayawa a gaba na da abun kunya a jikin ki kina bani umarni?" Na juya da sauri na yi gurin motar mu ina jin kafafuwa na suna harhadewa a cikin juna, ina kuma jin idanuwan duk mutanen da suke gurin a kaina.

Kafin in kai mota hawaye sun jika fuskata, ta gefen idona na ga twins sun taho gurina amma sai nayi sauri na bude kofar gidan gaba na shiga sannan na rufe da karfi, still ina cigaba da jin muryar Uncle Ahmad yana cigaba da fadar bakaken maganganu a kaina. "Kaf dangin mu ba'a taɓa yin irin wannan abun kunyar ba. Saboda daurin gindi amma wai har tazo ta tsaya a gaba na tana gaya min maganar banza" na saka hannayena duk biyun na toshe kunnuwa na tare da kifa kaina akan dashboard ina cigaba da rusa kuka kamar wadda aka aikowa sakon Daddy ya bar duniya.

A cikin kuka na naji shigowar Mommy cikin motar ta zauna a baya tayi min magana amma banji me tace ba, sai dai na dago kaina na fara kokarin goge hawayena. Yaya Mustapha yazo ya bude daya kofar bayan ya taimaka wa Daddy ya zauna sannan ya rufe ya dawo seat din driver ya zauna. Na cigaba da ƙoƙarin tsayar da kuka na dan sam bana son Daddy ya san abinda ya faru ballantana ransa ya baci.

Sai dai yaya Mustapha yana tayar da motar naji Mommy tace "ki daina wannan kukan haka tun kafin ki saka wa kanki wata cutar kuma, ki gaya wa Daddyn ku abinda ya faru" nayi shiru ban ce komai ba, sai naji muryar Daddy yace "menene ya faru?" Na sake yin shiru amma kuma sai hawaye na ya dawo sabo. Ya sake magana cikin tsawa "magana nake miki Safiyya, menene ya faru?"

Cikin kuka nace "Uncle Ahmad ne yayi min hayaniya a cikin mutane" yayi shiru kamar bai ji ne nace ba, sai kuma yace a hankali "me yace?" Nayi shiru a raina ina jin nauyin maganar. Mommy tace "zagin ta yayi, ya goranta mata akan abinda ya same ta, a gaban duk yaran gidan nan" Daddy ya sake yin shiru, amma duk da ban kalle shi ba nasan ransa yayi matukar baci, ni kuma abinda nake gudu kenan.

Har yaya Mustapha ya ja mota sai Daddy yace "tsayar da motar nan Mustapha, zo ka kama ni in fita". Nayi sauri na juyo ina kallon sa hankali na a tashe. "Daddy please" Mommy ma ta rike hannun sa da sauri. "Dan Allah kar ka fita, dan Allah kar ka kula shi. Abinda yake so kenan dama. Mu lafiyar ka tafi mana komai. He isn't worth it. Ko babu komai yanzu mun san inda ya sa gaba".

Daddy ya karbe hannun sa da ta rike ya kama handle din kofar yana kokarin budewa. Na juya na kalli yaya Mustapha cikin tashin hankali nace "rufe lock ɗin. Ja motar mu tafi" yayi abinda nace muka bar harabar gidan a guje.

Har muka yi nisa babu wanda ya kuma yin magana. Sai daga baya naji Daddy yace "Mustapha kira min Ahmad a wayar ka ka bani shi" na dafe kaina. Ba zai hakura ba dai. Wata irin zuciya ce da Daddy da sam baya barin magana ta wuce sai ya rama. Ina kallo yaya Mustapha ya daukl wayar sa yayi dialing sannan ya saka a kunnen sa, aka dauka sai yace "Uncle Ahmad, Daddy ne yake son magana da kai" sai kuma ya mika wa Mommy wayar ita kuma ta bawa Daddy, ya karba direct yace "kar ka biyo ni airport, bana son rakiyar taka. Allah yayi min komai, bana bukatar komai daga gare ka".

Daga haka ya ajiye wayar. Mommy tace "kash. Ni dai ban so ka kula shi ba wallahi" amma a raina sai nayi mamakin abinda yasa naji kamar farin ciki a cikin muryar ta.

Bamu jima a airport ba aka kira jirgin mu, na rungume twins da suka biyo mu har airport a baya muka yi sallama, na tabbatar sunyi sallama mai kyau da Daddy sannan nabi bayan yaya Mustapha da yake tura Daddy a

Please Login or Register in order to submit comment