You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
rayuwata na sani, amma kuma na san cewa dan Adam baya taba wuce kaddarar sa, rayuwar da tayi ita ce tata kaddarar, nima kuma halin da nake ciki shine tawa kaddarar, kuma na sani cewa addu'a tana chanja kaddara dan haka har yanzu ban gaji ba kuma ba zan taba gajiya ba wajan gyara rayuwata.
She was my role model, she has always been. Courage da determination dinta su suke hana ni giving up a lokuta da dama. Yadda ta chanja rayuwar ta from worst to best haka nima nake fatan chanjawa. Giving up has never been in her dictionary and it is not in mine. Kamar yadda Daddy yake yawan yin comment a lokuta da dama, lokutan da muke good time da shi, cewa her fire is burning in me, cewa I have her zeal, strength, bravery and stubbornness, wannan shi nake so in yi proving right.
Maganar Daddy ce ta dawo dani daga tunani na. "Safiyya, daga ina kike? gurin sa kika je ko?" Na dago kai na kalle shi, sai na yi sauri na sake sunkuyar da kaina dan ba zan iya cigaba da hada ido da shi ba.
Mommy tace "baban Mustapha, kasan dai ɓata lokacin ka da ranka zaka yi a gurin tambayar Safiyya a game da maganar nan, ba zata yi magana ba, wata nawa ana fama? Wacce irin tambaya ce bamu yi mata ba?" Yayi ajjiyar zuciya cike da damuwa yace "na sani Sa'adatu, na kasa hakura ne, gani nake kamar watarana zata tausaya min a matsayi na na mahaifin ta"
Naji hawaye na yana sauka akan hannayena da suke kan cinyata.
"Am sorry Daddy " na fada a hankali
"Sorry she said" ya maimaita. "Abinda ta iya fada kenan in anyi mata magana tace sorry" ya fada cikin kokarin daga murya, sai kuma yayi shiru yana mai da numfashi.
Mommy tace "abinda yasa kika dage da nacin sai mun biyo ta Abuja kenan ko? Kika yaudare mu mukayi tunanin you are after your father's health ashe ke kina da plan din ki da kika shirya ko Fiyya?" Na girgiza kai da sauri amma kuma part of me knows gaskiya take faɗa, except maganar daddy's health, tabbas dan in ganshi na nace sai mun tashi ta Abuja.
"Ba kuma zaki fadi ko waye shi ba ko?" Ta sake tambaya with hopelessness in her voice. Daddy yace "ba zata fada ba kin sani. Wallahi da na san zaki iya risking mutuncin ki da na family dinki ki fita ki tafi gurin sa da na ɗana miki tarko, da na saka an biki a baya an gano min ko waye shi, kuma wallahi da nayi masa abinda har ya mutu ba zai manta ba kamar yadda yayi min abinda har in mutu ba zan manta ba, da na rusa rayuwar sa kamar yadda ya rusa taki, da na....." Sai yayi shiru yana jan numfashi a kokarin daidaita numfashin sa da ya fara fita sama sama.
Na fara tracing tun sanda na fita har zuwa sanda na dawo a raina, ina so inga ko na haɗu da wani da ya san ni ko kuma na bar wani hint da zai taimaka wa Daddy yayi tracing Gidado, har sai da na tabbatar babu sannan naji hankali na ya fara kwanciya. Ba damuwa ta abinda Daddy zai wa Gidado in ya kama shi ba, cos I doubt idan zai iya yi masa komai, damuwa ta shine in akayi tracing Gidado to zai san komai, zai san gaskiyar komai and his parents will be involved too, our school management will also be involved, wannan duk yana nufin bacin sunan Gidado, sannan yana nufin goga masa baƙin fenti na har adaba. Wannan kuma shine abinda nake gudu, shine abinda zuciya ta ba zata iya dauka ba.
Ina cikin tunani na naji Daddy yana waya, "Mustapha kazo sama yanzu ina neman ka". Sai hankali na ya dawo jikina, wancan tashin hankalin ya marsa ya bawa wani sabon tashin hankalin gurin zama a cikin zuciya ta. "God, not him please" na fada a hankali ina mummurza yan yatsun hannuna cikin tsananin damuwa.
Tabbas ni nace da Daddy na amince da duk wani hukunci da zai yanke a kaina duk a kokari na ganin na rage masa radadin abinda yake tunanin nayi masa, amma kuma zuciya ta tana kakkaryewa a duk lokacin da ta hasaso hukuncin nasa, na san aure zai yi min, kuma na amince da auren amma kuma damuwa ta shine wa za'a aura min? Wanene Daddy zai zaba min a matsayin abokin rayuwata ta har abada. Shin zai zama blessing to me or a curse?
A raina nasan few choices ɗin da Daddy zai iya yi. A kokarin sa na kare mutuncina dana family din mu dole na san auren gida zai yi min. Wannan yayi limiting choices dinsa zuwa mutum uku kacal, mutum ukun da dukkan su babu wanda ba zai iya lasar tafin kafata ba in dai za'a aura masa ni, mutum ukun da duk kan su babu mai sona, mutum ukun da duk kan su babu wanda nake so. Mutum ukun da daya daga cikin su yake da hannu wajan bata tsakanina da Daddy, daya kuma yake da hannu dumu-dumu a cikin halin da nake ciki a yanzu.
Sai dai bani da tabbas ɗin who is who. Ba kuma ni da shaidar nuna wa Daddy.
But the fork is my only way out.....
If only I can find the fork.....
If only I can find it's marks....
Muryar yaya Mustapha ta katse min tunani na. Na dago kai muka hada ido sai nayi sauri na mayar da kaina kasa ina jin bugun zuciya ta yana ƙaruwa. Ya zauna a kasa nesa da ni kaɗan. "Daddy gani" Daddy yace "kaje motar Safiyya, check the dashboard camera, find out ina taje dazu, if possible, find out da wa ta hadu".
Ban daga kai na kalle su ba har ya fita, sai dai yawun baki na gabaki daya ya dauke, numfashi na ya tokare a kirjina. "Why didn't I think of the damn camera?" Na rafa lissafin way out a raina. Tabbas camera ba zata nuna Gidado ba, amma zata nuna makarantar mu da kuma dai dai inda nayi packing wato kofar building din da yake dauke da offices na some staff. And weekend ne. Few staff ne suka shiga a ranar. If police got involved zasu iya gano wadanda suka shiga a ranar and it will take Daddy closer to Muhammad.
Mara ta naji ta rike da wani mugun fitsarin tsoro. Hawayen ido na ya kafe. Na zauna zaman jira ina jina kamar akuyar da aka kai mayanka take jiran turn ɗin ta.
Bai jima sosai ba ya dawo ya sake zama a inda ya tashi. "Daddy ta kashe camera din kafin ta fita" ya fada yana kallon Daddy. Na dago kai da sauri na kalle shi. Muka haɗa ido sai ya kuma dauke kai fuskarsa expressionless ya cigaba da kallon Daddy.
Daddy yayi ajjiyar zuciya "I should have known. She is always too smart for her age, tun tana yarinya she has always been two steps ahead of mates din ta. But still ban dauka zata yi tunanin wannan angle din ba".
Mommy tace "ban taba dauka kawaye zasu yiwa mutum rana ba sai akan case ɗin Safiyya. Da ace tana da kawaye na tabbatar zamu samu wani information ko yaya ne daga gare su. Safina kuma tayi iyakacin nata kokarin"
Na tuna da kokarin da Mommy take nufin Safina tayi. A raina nace "munafuka ba" tunanin abinda tayi ɗin ya kara min zafi a zuciya ta.
But yaya Mustapha, me yake up to da zai yi wa Daddy karya? Akwai wani abun da yake bukata tabbas.
"Tashi ki tafi" Daddy yace
Na mike still idona a kasa, har na fara tafiya naji Mommy tace "ko parlor ban yarda ki sake fitowa ba sai in zamu bar gidan nan. Kuma wallahi kika fita sai ranki yayi mugun baci". Na ɗan dakata sannan na juyo ina kallon ta nace "to Mommy" a raina nace na riga na gama abinda ya kawo ni abuja ai, na gama da Nigeria ma gabaki dayan ta, bana fatan wani abu ya sake dawo dani kasar nan.
Na kai bakin kofa naji Daddy yace "kai Mustapha ka zauna, akwai maganar da zamuyi" na sake dakatawa tare da rintse ido na, sannan ba tare da na juyo ba, na yunkura na bude kofar na fita.
Kafin in shiga dakina na haɗu da Esther duk a tsorace. Ta biyo bayana "Madam am sorry, ban san an shiga dakin ki ba. Sai dana ce mata kar ta shiga. Na dakata da tafiyar ina kallon ta ina mamakin yadda ta daga hankalin ta akan karamin abu nace "it is okay Esther, relax, she is my elder sister ni kaina ba zan iya hanata yin abinda take so ba".
Na dauka Esther tana yi min maganar knocking da Safina tayi dazu a dakina ne, sai da na bude kofar dakin na shiga sannan na fahimci ba wannan bane ba.
Duk an zazzage contents ɗin cikin jaka ta akan gado, da alama wani abun ake nema sai dai ban san menene ba ballantana in san ko an samu ko ba'a samu ba. Naga wayata a yashe a gefe, na dauka naga ta nuna alamar anyi ta trying budeta an kasa. Na zauna a bakin gado ina tsince tarkace na tare da mayar da su cikin jaka. Na bude wayar using face lock ina kallon hoton da na saka a matsayin screen saver dina. Hoton hannun Muhammad Gidado ne, ya dora akan sitiyarin motar sa, da zubunan azurfa guda biyu a yatsunsa, da agogo a wrist ɗin sa.
Na tuna sanda na dauki hoton, muna cikin motarsa ne, motar da take holding most of our memories together.
****. ****. ****. ****. ****. ****
Lokacin yana yi min korafi ne kamar kullum, yayin da ni kuma nake ƙoƙarin mayar da korafin nasa wasa ta hanyar tsoakanar sa.
"Abba yana ta yi min maganar komawa gurin sa da aiki" nace "inye, rich kid.... Irin born with a golden spoon din nan ko? Babu ruwan ka da neman aiki sai neman ka ma ake yi ko?" Ya bata rai "you know what I mean kina so ki chanja magana ko? Dazu har fushi yayi, he thought pride ne ya saka nake zaune a makarantar nan bana so inyi aiki a karkashin ss and I am hurt that he thinks that" na gyara zamana with a serious face nace "then do what he wants. You are just enslaving your self here and it is hurting me too"
Yace "you think so? Tell me in na bar makarantar nan how am I gonna be seeing you? Safiyya ko gidan ku fa ban sani ba and it has been years muna tare, i know cewa ina barin makarantar nan ko ta kaina ba zaki sake bi ba"
Nayi shiru ina kallon sa, yace "what? Ba gaskiya na fada ba?" Nace "kasan me yake damunka?" Yace "insecurity, yes, I am insecure when it comes to you, bani da wani concrete stand and I know anytime zaki iya ajiye ni a side and the thought alone is given me nightmares and...."
Nace "you once jokingly asked me me yasa nazo makarantar nan out of all the universities in the world, you jokingly said I followed you here because I cannot live without you, I laughed then amma abinda ban gaya maka ba shine gaskiya ka fada a lokacin, I came here because you mentioned ranar nan da muka hadu cewa kana nan makarantar for the time being. I wanted to be with you. I wanted to see you again. I literally threw a tantrum a gaban Daddy akan lallai nan makarantar nake son zuwa"
Na fada ina tuna yadda na kwanta ranar na ringa birgima a gaban Daddy ina kuka shabe shabe da hawaye.
Bai ce komai ba ya saki baki yana kallona, na sunkuyar da kaina na cigaba "I was hoping in mun sake haduwa zaka karbi number ta. And maybe say you love me"
Yace "Piya? Are you saying that you... " Na saka hannu na biyu na toshe kunnuwana "forget I ever said that. Lala la lala" yayi dariya amma naji relief da excitement a cikin muryar sa sosai, hankalin sa ya kwanta ya samu assurance ɗin da yake so. "Piya, you are impossible. But if that is true then ki kaini gidan ku mana please, at least let then know me yadda zamuyi all these the right way"
Na gyada kai "soon insha Allah. Na gaya maka family house din mu yana kano shi yasa ban taba kai ka ba, and Daddy bashi da lafiya yana Pittsburgh ganin likita. In yazo gari I will talk to him and he will tell me what to do. We have nothing to worry about".
Yayi ajjiyar zuciya "am sorry Piya, nasan ina ta damun ki kullum, i don't know why zuciya ta ta kasa nutsuwa, ina ta feeling restless kullum. But i promise zan gyara halina" ya fada guiltily.
Nayi kokarin chanja topic ɗin ta hanyar daukar hoton hannun sa da ya ke kan stirring "wow! rich kid! Wa ya siya maka sabon agogo? Mommy ko Daddy" na fada cikin tsokana, ya kalli agogon sannan ya kalle ni da sigar harara "ni ne rich kid ɗin? An gaya miki mina ɗan zaman kashe wando ne irin ki? Ma'aikaci ne ni if you don't know" Nace "I don't know nawa suke baka but am sure albashin ka ba zai siya maka wannan agogon ba. So, tell me the truth, I promise ba zan fada wa kowa ba. Mommy ce ta siya maka ko Daddy?" Yayi dariya "ask those who call their parents mommy and Daddy that question, misali you. Ni dan gidan Mama da Abba ne. And I don't throw tantrums idan ina son abu" na dafe kai na "shi kenan kuma na shiga uku a hannun ka. Kayi ta tsokana ta kenan har illa masha Allah " yace "tabbas, har ƴaƴan mu sai na bawa labarin yadda kika makale min kike bina duk inda na tafi" na rike bakina ina jin haushin fada masan da nayi nace "me and my big mouth" yace "you and your cute lips".
****. ****. ****. ****. ****. ****
Karar knocking kofa ta dawo dani daga tunani na. Ba tare da na dauke ido na daga kan hoton ba nace "come in". Naji an bude kofa an shigo an mayar an rufe, a tunani na Safina ce, sai dai kamshin turaren da naji ya saka na dago kaina na kalli wanda ya shigo. Yaya Mustapha.
Kallo daya nayi masa na sake mayar da kaina na cigaba da aikin kallon hoton da yake kan screen din wayata. Ya zauna akan side drawer yana kallo na. Ganin bani da niyyar yi masa magana sai yayi gyaran murya yace "babu godiya ma ko?" Still ban ce komai ba kuma ban kalle shi ba. Yayi ajjiyar zuciya sannan ya mike tsaye ya tsaya a gaba na. "I just saved you and your precious love a gurin Daddy amma ko godiya ba zaki yi min ba?" Na dago kai da sauri ina jin zuciya ta tana yin zafi nace "yaya Mustapha, what do you want? Me kake bukata daga gare ni?" Ya koma ya zauna muna kallon juna yace "at least a little concern. Fiyya ni yayan ki ne and I love you with all my heart amma I can't help but feel like kin tsane ni kuma ni har ga Allah ban san me nayi miki ba. Tunda abin nan ya faru babu abinda nake yi sai kokarin ganin na faranta miki na rage miki radadin abinda yake damun ki. Only God knows how many times nayi wa iyayen mu karya dan in kare ki. I have nothing to do with abinda kika yi, I have nothing to do with decision ɗin iyayen mu na haɗa mu aure. But why are you cold toward me bayan da ba haka kike min ba?"
Na dauke idona daga kansa ina maimaita abinda yace a raina, decision ɗin iyayen mu na haɗa mu aure, so shine kenan, shi Daddy ya zaba, and he is the worst among the three.
A hankali nace "Dan Allah.... Ka tashi ka fita..."
Ya sake yin ajjiyar zuciya yace "okay zan fita. But just know that in akwai wani abu da kike bukata, just let me know "
Bance komai ba har ya mike tsaye. Ban ankara ba kawai sai ji nayi ya kwace wayar hannuna. Na mike tsaye da sauri kamar wadda aka dorawa garwashin wuta a cinya, yayi sauri ya matsa daga kusa dani yana kallon hoton yana murmushi.
"Wow. Nice hands...... And that skin...... I bet he is Arab"
Ban ce komai ba na tsaya kawai ina kallon sa zuciya ta tana tafasa.
Ya cigaba "and he is rich too..... Cos wannan wrist watch din nasa zai sayi kayan jikina kaf har da chanji"
Ya dawo yazo ya tsaya a gaba na "I feel for you dear. But it is what it is. Allah yasa haka shi yafi alkhairi".
Ya ajiye wayar akan gado kusa da ni sannan ya ce "lecturer ne ko student? Ko kuma non-academics ne?" Naji kamar in rufe shi da duka amma ko motsi ban yi ba. Ganin bani da niyyar ce masa komai sai ya daga kafada yace "okay. Whenever you want to talk I will be glad to listen"
Daga haka ya juya ya fita. Na koma na zauna na dauki wayata na fara aikin goge ta kamar wadda aka shafa wa datti. "Munafuki" na fada a fili "munafukai. Bunch of munafukai. Dukkan ku munafukai ne"
Na tuna tambayar da yayi min akan dalilin da yasa na tsane shi. Tabbas a yanzu kusan na tsani kowa amma tashi tsanar ta musamman ce. Wannan kuma yana da nasaba da sunan shi. Sunan shi aka ambata a lokacin da aka kira ni. Kiran da ya chanja dukkan rayuwar.
"Fiyya! Kina ina? Mustapha ne. Jikin Daddy ya tashi mun tafi dashi asibiti. Hurry up"
Na rufe idona ina jin maganar tana amsa kuwwa a cikin kaina. And it sounded just like him.
"Allah ya isa" na fada a fili.
*Him 👳🏻*
Ya dauki hours a cikin office dinsa dan har sai da yaga magrib ta gabato sannan ya fita, shima kuma ya fita ɗin ne kawai dan yasan rashin zuwa gidan sa zai tayar da hankalin mahaifansa. A gidan su suna da wata doka da ya fahimci cewa ta samo asali ne tun daga kakannin sa na wajen uba, dokar kuwa itace kowa must be home before magrib komai girman ka in dai kana gari, dole tare zakuyi sallah magrib da Abba, tare kuma zakuyi dinner. A dinner din ne ake discussing must of the issues da suka shafi family. A dinner din ne kuma must of the times ake matsa masa da zancen aure.
Ya dinner ɗin jiya ne yayi musu alkawarin yau Safiyya zata shigo gari, and yau din ne yake saka ran zata bashi go ahead na zuwa gurin iyayen ta.
Ya rufe office din ya sauko daga stairs din blindly ya bude motar sa ya shiga. Kafin ya tayar da motar ya dauko wayarsa for like the hundredth time ya kira layin ta. Still baya shiga. Ya kuma san ba zai shiga din ba tunda ya tabbatar tayi blocking dinsa. Amma kuma ya kasa daina kiran ta. He just couldn't let her go. Ba zai iya ba. Ya tabbatar ba zai iya ba.
Ya san cewa dating dinta da yayi a matsayin ta na matar aure ba laifin sa bane ba tunda bai sani ba, Allah kuma ba zai kama shi da laifi ba, amma kuma in ya cigaba da bibiyarta a yanzu bayan yasan tana da aure to tabbas Allah zai kama shi. Amma ya zaiyi? "I just want to confirm" ya fada a fili kamar mai kokarin kare kan sa. But confirm what? Wanne confirmation yake bukata bayan wanda ya gani a jikinta? Ciki ne fa da ita, cikin ma kuma ya kwana biyu, duk da shi ba mace bane ba amma yasan cikin zai kai around five to six months. Ciki a jikin Piyan sa.
Ya rufe ido tare da dora kansa a jikin stirring yana jujjuyawa. Me zai yi ne? Ta ina zai rarrashi kansa? Wacce amsar zai bawa Mama a yau in ta tambaye shi game da maganar da suka yi jiya? Shi dai ba zai ce mata ashe Safiyya tana da aure ba, he can only imagine irin kallon da zata yi masa idan ya fada mata haka.
Ta ina zai fara.....
Ina zai samu ruwan da zai kashe gobarar da ta tashi a cikin kirjin sa?
His worst nightmare have come to be. Safiyya ta barshi.... Bari na har abada.
Ya daga kansa ya jingina shi a jikin kujera, komai ma baya yi masa dadi. A lokacin ne yaji danshi a fuskar sa, ya saka hannu a hankali ya shafa sannan ya tsaya yana kallon abinda ya shafo. Hawaye. Sai ya samu kansa da yin murmushin takaici. Kuka? Wai shine yake yin kuka? Ba zai iya tuna sanda yayi kuka ba tunda yake a rayuwar sa. He has always been strong, emotionally and physically. Mama tayi training dinsa to be a strong man. Amma kuma dama can when it comes to Safiyya to he is the weakest man alive, a hopeless romantic.
Da ace labari za'a bashi cewa zai yi wa budurwa kuka da tabbas sai ya kusa faduwa saboda dariya. Amma kuma dama hausawa sunce duk abinda kace ba zaka iya ba to bai kama ka bane ba.
Ya bude kofar motar ya dauko ruwa ya wanke fuskarsa, there is no way da zai bada damar a gane cewa yayi kuka, ballantana a gidan su, no way.
Yana zuwa gida ya tarar har Abba ya fito zai tafi masallaci, Haidar yana take masa baya. Yayi sauri yayi packing a waje ya bisu a baya yana gode Allah daya kasance Abban sauri yake yi yasan da sai ya sha tambaya. Har suka yi sallah suka fito suka dawo gida bai yanke hukuncin amsar da zai bawa Mama ba.
A parlor suka zauna kamar kullum suka kamo tashar labarai, ya wayan ce yana ta danna waya dan baya son yin magana da kowa, gani yake in yayi magana za'a gane me ya faru a cikin voice din sa. Sai dai ba abinda yake ganewa a wayar da yake danna wa dan hankalin sa sam baya tare da shi.
Dariya yaji an kwashe da ita a parlon, ya dago kan sa sai yaga duk shi suke kallo suna dariya. "What?" Yace yana rarraba ido cikin tsoron kar dai maganar da yake yi a zuciyarsa ce ta fito fili. "Tunanin me kake yi ne haka?" Abba ya tambaya da dariya a muryar sa. "Tunanin Safiyya" Haidar ya fada shima cikin dariya. Amma maimakon Gidado ya taya su dariyar sai ya mayar da kansa ya sunkuyar ya cigaba da danna kira a layin Safiyya.
Mama da ta gama guiding Hanifa ta zauna a kujera tana kallon Gidado, fuskarta cike da damuwa. " Me ya faru?" Ta tambaya tana kallon shi. Ya ajiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya yace "babu komai Mama. I am just exhausted ne kawai. Tun safe nake aikin marking script har yanzu kuma ban gama ba". Ta gyara zamanta tace "abinda nake gani a fuskar ka ba stress bane ba, damuwa ce, in ma da akwai aiki to akwai wani abun daban. Me ya faru?"
Ya mike tsaye yana kirkiro murmushin da ko lips dinsa bai wadatar ba yace "da gaske nake Mama. Bani da damuwa. Ko kadan. Yunwa dai nake ji" ya wuce su ya tafi dining ya zauna a kokarin sa na ganin ya gujewa cigaba da yi masa tambayoyi.
Bai jima da zama ba suma suka taho. Yayi saurin wayancewa da zuba wa kansa abinci. Yana jin Daddy da Haidar suna maganganu akan karatun Haidar ɗin, Mufida tana saka musu baki kaɗan kaɗan, yana kuma jin idanun Mama a kansa. Ya debi loma ya saka a bakinsa, ji yayi