You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
karya ko?”
A maimakon ya amsa mata sai kawai ya sakar mata ido yana kallonta, fuskarsa da mirmushi. Ɗan sunkuyar da kai ta yi itama tana maida masa da saƙon murmushin.
“Amarya ta”
Ya faɗa, tana mai cigaba da kallonta.
“Amaryar ka tana nan zuwa, ni kuma na zama uwargida a yanzu”
Murmushi yayi mai sauti, dan yaga kishinsa a cikin idonta.
“Ai ba gida ɗaya zaku zauna ba, kuma ita zata zauna da yara ne, that's means ke ce Amaryar”
Kai ta girgiza tana dariya, kamin ta mike tsaye.
“Bari na je na wanki bakina”
“Lemme help you”
Ya miƙe tsaye shi ma suka shiga banɗakin tare.
NAMRA POV.
Tun da ta shige ɗakin, bata fitowa sai idan fitsari zata yi ko shan ruwa, duk ta bi ta damu kanta, ta takura kanta. Duk yadda Neina ta so ta fito waje su yi fira sai ta ƙi, haka ta wuni da yunwarta daman can ba abinci take ci ba, sai Maltinar da Lamido yake badawa ana siyo mata, yau kuma ko maltinar ta ƙi ta sha.
Bayan sallame sallar isha'i yaro ya shigo, da sallama yana riƙe da kwanonsa ya bara yace
“Sallamu alaikum wai ance ana sallama da Namra, wai Abdullahi ne daga Katsina”
Tana cikin ɗaki ne, amman hakan be hanata jin abunda almajirin ya faɗa ba, sai kawai ta lumshe ido tana sauraren tsaran da kanta ke mata.
‘Wannan wane irin mutum ne?’
Ta tambaye kanta, tambayar da bata da amsa.
“Je ka ce bata nan”
Cewar Lamido zuciyarsa har wani kawowa take.
“A'a kai je ka ce gata nan zuwa”
Yaron na ficewa Neina ta kalli Lamido ta ɗora da
“Saboda girman Allah ka rufa mana asiri, muna neman abunda za mu ci ka jefa mu cikin wani halin kuma”
“Amman Neina tun da bata so ai ba ci aka ana cilasta ba”
Cikin yaren fulatancin ta mayar masa da amsa.
“Lamido babu ruwanka baka san yadda abun nan yake ba, kai dai ka cinto gefen tiri baka san tsakanin su ba, ka kama kan ka, ɗan Sarki ne fa”
Tana gama faɗar hakan ta nufi ɗakin da Namra take.
“Namra tashi kije yana kiran ki”
“Ni babu inda zan je”
Ɗukawa Neina tayi kamar zata zauna ta haɗe hannayenta.
“Ki yi ma girman Allah ki rufa mana asiri kije, haba Namra kar ki ba ni kunya mana na faɗa masa ga ki nan zuwa, dan Allah ki tashi ki je”
“Neina ko naje mi zan ce masa? Ni na riga na faɗa masa karya sake dawowa ƙofar gidan mu”
“Wallahi ban ce ki faɗa masa komai ba, saurarasa zaki yi, ki rufa mana asiri Namra”
Magiya Neina ta riƙa yi ma Namra kamar zata fasa mata kuka, sannan Namra ta tashi cikin ɓacin rai da zafin zuciyata ta fita.
Gurin da ya tsaya ɗazun a nan ya sake tsayuwa, duk da dare ne hakan be hana farin wata haskar fatar jikinsa ba, ga manyan idonsa da ya tsare ta da su har take ƙoƙarin faɗuwa kamin ta ƙaraso kusa da shi. Kasa furta masa komai ta yi, duk wasu kalamai da take da unƙurin faɗa masa sai ta kasa, suka tsaya mata iya cikin cikinta zuwa maƙogaronta, dan bakinta ƙin bata haɗin kai ya yi, ga ƙamshin turarensa da ke ta kaiwa hancinta hari.
Hannayensa dake rumgume aƙirjinsa ya cire ya maida cikin aljihu.
“Bude ba ki kiyi magana, faɗa min duk kalmar da kike tunanin ta cancanta a da ni, ki yi duk abunda kike ganin idan kin min saki samu salama.
Ayau na tsayu gabanki ne saboda kawai na ji tarihin rayuwarki, ban je neman auren ki, amman nasa a min bincike akan ki, tsakanin jiya zuwa yau labarin ki da hawayen ki sun nuna min akwai abunda kike boyewa”
Hawaye ta fara, tana ƙoƙarin ture kalamansa dake son su yi tasiri a zuciyarta.
“Ba lallai ne na cimma burina akan ki ba, mman lallai ne na faranta miki rai, kuma na taimaka miki ki cimma na ki burin, ina roƙon ki ki bani kaɗan daga tarihin rayuwarki ko zan samu sukunin rayuwa, Namra ni ba ƙaramin mutun ba ne, kuma ba wasa ya kawo ni nan ba, ki taimaka min wata ƙila ni ne silal farin cikin ki”
Ɗaga kai ta yi ta kalleshi.
“Ta ya farinciki zai dawo ga yarinyar da ta butulcewa iyayenta? Taya farinciki zai dawo ga macen data zaɓi saurayinta sama da iyayenta? Faɗa min ta ya?”
Yayi shiru yana karantar kalamanta. Yawun bakinta ta haɗiye.
“Ba kowa ba ce ni, fa ce wacce ta butulcewa iyayenta, da zabi saurayinta sama da su, wanda shi ne ya kai ni ga hakala.......”
Ƙoƙarin tsagaita kukanta take, dan ta samu damar labarta masa tarihin rayuwarta ko zai samu salamar rabuwa da ita. Zagayawa yayi ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko carpet ya shimfiɗa mata. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna nesa da ita zuciyarsa cike da tsumayin jin labarin nata.
Sai da ta share hawayenta, sannan ta soma bashi tarihin rayuwarta...
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *73*
Idonsa sun kaɗe sosai sun yi ja, duk ɗigar hawayenta ɗaya sai ya ji kamar an watsa masa ruwan zafi, ya kasa ɗauke kansa daga barin kallonta, har cikin ransa yake jin kukanta da kuma zubar hawayenta, samun kansa yayi da mugun tausayinta.
Ita kuma ta rumgume ƙafafunta sai kuka take, ba ƙaƙƙautawa.
Handkerchief ya riƙo daga aljihunsa ya aje mata, ba tare da ya ce da ita komai ba. Hannu ta kai ta ɗauka ta share hawayenta sannan ta fyace majina.
“Kin yi kuskuren zabar saurayinki sama da iyayen ki. Shiyasa Allah ya jarrabe ki, bayan Ubangiji babu wanda ya cancanci girmamawa sama da iyayenki”
Ɗagowa tayi ta kalleshi idonta taf da hawaye.
“Amman wanda mahaifina yake son na aura ba cancance ni ba...”
Ya tari numfashinta.
“Amman ai ya baki damar fitar da wanda kika so, sai kika nace sai shi saboda kar ya ce kin yaudareshi, ko ba haka kika faɗa min ba yanzu?”
Ta yi shiru tana sauraren hawayen dake bin fuskarta.
“Daga ƙarshe sai kuma ya yaudare ki, ya ci amanar ki, da ace kin aure wanda mahaifin ki yake so, babu yadda za a ayi ya guje ki, wata ƙila sanadiyar hakan sai ya shiryu, kuma duk abunda yayi miki dole su ne da laifi ba ke ba, baki san fushin Ubanguji yana tare da fushin iyaye ba? Idan iyayen ki sun yarda da ke, to haka shi ma Allah ya yarda da ke, kin yi aure mahaifinki yana fushi da ke taya za ki ga ribar auren?
Kin yi kuskuren rashin komawa gida Namra, ko yanka namanki za su yi su dafa su ci, bai kamata ki dawo nan ki tare ba”
“Idan kuma suka ƙi karɓa ta fa? Mahaifina ya ce karna kuskura na dawo gidansa da sunan saki ko yaji”
“Komai ya ce miki haka ne, saboda yana cikin fushi ne, da kin koma ai ba zai iya korar ki ba, idan kuma har idonsa ya rufe ya kore ki, to duniya zata miki masauki, su kuma ta juya musu baya, jama'ar gari kuma su zage su, har sai shi da kansa ya koma neman ki”
Ta bikita ɗaƴan ɓangaren na handkerchief ya share majiyar data cika mata hanci.
“Na yi nadama yanzu, na gane gaskiya”
“Kin yi nadama a lokacin da bata da amfani, kin sake tafka kuskure a cikin kuskure. Namra ba mutum kika aura ba, mutum mutume ne mai kama da mutum, siffarsa da kamarsa tasa kika ɗauka mutum ne, har kika masa inuwa, shi kuma ya saka ki a rana, mutumen da bai shirya haɗa zuri'ah da ke ba, amman Namra da yanzu a ace m cikin ki yana nan, a nan za ki zauna ki haihu kenan? Ba tare da kin koma gurin iyayen ko ba?”
Miƙewa ta yi tsaye ta yi tsaye ya saka takalminta, da zimmar komawa cikin gidan. Sai shi ma ya miƙe tsaye.
“Can i have my handkerchief!”
Juyowa ta yi ta kalli handkerchief ɗin, sannan ta kalleshi.
“Yayi ƙazanta”
Ya faɗa cikin muryarta mai gaf da yin kuka.
“Please...”
Ya ɗaga mata gira ɗaya, like he's serious. Ta ɗan ɗauki mintuna kamar mai shawarar miƙa masa abunda yake mallakinsa na ne.
“Please stop cry..”
Ya faɗa cikin muryarsa mai rawa kamar mai shirin yin kuka. Sai kawai ta miƙa masa handkerchief ɗin cike da ƙyama. Shi kuma ya miƙa hannu ya karɓa idonsa na kan fuskarta. Bata tsaya komai ba ta shigerwa tana ƙirƙirar wani sabon kuka.
Damƙe handkerchief ɗin yayi da dukan no ƙarfinsa, kamar abunda za a ƙwace masa, ya kai fuskarsa ya lumshe ido.
Har cikin zuciyarsa yake jin sanyin hawayenta, ya samu mintuna biyu zuwa uku a haka kamin ya buɗe motarsa ya shiga. Still da handkerchief ɗin a hannunsa yake driving.
“Da kin auri wanda Mahaifin ki yake so wata ƙila da ba mu haɗu ba, da ba zan iya kawowa rayuwarki ɗauki ba”
Ya faɗa yana mai sa ɗayan hannunsa ya fiddo wayarsa, sai da ya hau babban titi sannan ya rage gudun da yake ya danna ma Mai Martaba kira.
Ta ɗan jima tana ringing kamin a ɗauka.
“Assalamu alaikum”
“Wa'alaikassalam, Allah ya taimaki Mai Martaba”
“Babana kana lafiya?”
“Lafiya ƙalau Mai Martaba, Mai Mairtaba yanzu idan Madina (Sister sa wance suke uba ɗaya) ta zaɓi saurayinta sama da kai ya zaka ji? Bayan kuma kai ka yi mata zaɓi?”
“Ba zan ji daɗi ba, sai dai kuma ba zan hana ta aurensa ba, amman kuma ba zata ga da kyau ba, ba kuma dan ina mata fata ba, no saboda ba kasafai auren da iyaye basa so yake zama alheri ba”
“Idan kuma bayan ta yi auren mijin ya sake ta fa? Bayan ya gana mata azaba, sai ta dawo gare ka, ya za kayi?”
“Zan karɓe ta da hannu biyu na mata masauki ta yadda zan shimfiɗa mata sabuwar rayuwar, ita da kanta zata yi nadama ta gane lallai Uba, Uba ne, ta yadda wata rana idan ta ga wanda zai aikata hakan ita da kanta zata hane shi”
“Lallai Mai Martaba kai ne za ka taimaka min wajen dawo da martabar Namra”
“Wacece Namra?”
“Gobe da safe zan dira Katsina zan tabarta maka komai Mai Martaba”
“Allah ya kai mu”
“Amin mu kwana lafiya, Allah ya ƙara mana nisan kwana da lafiya”
Ya aje wayar yana murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa.
AMIRA POV.
Tana gama rubuta wasiƙar ta naɗe cikin wata paper, sannan ta ɗauki salati ta saka, ta ta saka ta cikin wani madaidaicin kwali ta yi rolling da wani jan gayenta sai ya fito kamar gift.
Sai da ta gama abunda ta ke sannan ta kwashe komai ta gyara gurin. Saman gado ta koma ta kwanta tana kallon sili kamar mai tunanin wani abu. Haleema ce ta turo kofar ɗakin ta shigo fuskarta ɗauke da damuwa dan ita har ga Allah tausayin Amira take.
Kusa da ita ta zauna tana kallon kwalin dake gefenta.
“Yau duk baki leƙo mu ba? Ko abinci ba ki ci ba”
Sai a lokacin Amira ta tuna rabonta da abincin tun jiya da rana. Sai dai kuma har yanzu bata jin yunwa. Duk ta wani zurma kamar marar lafiya.
Unƙurawa ta yi ta tashi.
“Bana jin yunwa, Dan Allah Haleema ki taimaka min ki kai ni tasha na bada wannan saƙon”
“Saƙon minene Amira?”
“Wasiƙa ce na rubutawa mutumen da ya fara cuta na, wata ƙila idan ya karanta zai gane ina raye har ya wanke, na koma gurin iyayena ko Allah zai sa Yayan ki ya so ni”
Bata damu da sanin abunda yake cikin wasiƙar ba, ta miƙe tsaye
“Okay, bari na ɗauko mayafi na”
Tana ficewa Amira ta tashi cikin rashin kuzari ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta da hawaye ya ɓata ta fito. Wannan karon Hijabi ta ɗauka ta saka, sai ta zauna gefen gado tana kallon kwalin zuciyarta sai bugawa take.
“Mu tafi”
Haleema ta baɗa yayinda ta turo ƙofar ɗakin makulin motarta na hannunta. Da sauri Amira ta ɗauki kwalin suka fice. Maganganu masu daɗi da tausasa zuciya Haleema ta riƙa mata har suka isa tashar. Suna shiga aka riƙa tambayar inda zasu sai Amira ta amsa da
“Motar Sokoto muke nema”
Aka nuna musu, almajira suna haɗawa da gudu ganin haɗaɗiyar mota a zatonsu ko da kayan dako ne. A gafen motoci Haleema ta faka motar suka fito tare, da ƙafa suka ƙarasa kusa da inda ake lodin motar sokoto suka samu direban yana daga gefe zaune yana jiran a gama haɗa masa passengers. Sallama suka fara masa sai ya amsa tare da mutanen da suke gurin.
“Dan Allah saƙo za a kai mu a sokoto”
Cewar Haleema.
“Ok na minene?”
Amira ta dire musu kwalin, kana ta ɗora da.
“Wannan abun za a kai ga addireshin”
Ta ƙarasa tana miƙa masa wata ƴar ƙaramar takardar. Hannu ya kai ya karɓa.
“Okay to zaki bada kuɗin mota, da kuma number wayarki da wanda za a kaiwa saƙon”
“Zan dai baka number na, amman ban da number wanda za'a kaiwa saƙon, shiyasa na rubuta maka addireshin sa, dan Allah ka taimaka min ka kai masa har gida”
“Okay ba matsala, amman gaskiya ko baki yo ba sai kin bada dubu uku, dan za a kai masa har gida ne, kuma kin ga yanayin da ake ciki ba mu cika son karɓar saƙo ba ma”
“Ina zuwa”
Haleema ta faɗa, sai ta juya ta nufi gurin motarta, bata ɗauki lokaci ba ta dawo ta miƙa masa dubu uku ƴan ɗari biyar biyar.
“Gashi amman dan Allah ka tabbatar saƙon ya isa, ki bashi number wayarki so that idan ya kai sai ya kira ya faɗa miki”
Ta ƙarasa tana kallon Amira. Ba musu Amira ta karɓi number wayarsa ta saka a wayarta, sai ta masa flashing number ta ta fito, sai da ta tabbatar yayi saving sannan ta juyo ita da Haleema suka nufi gurin da suka faka motar su.
Haleema ce ta fara shiga sannan Amira, har suka isa gida babu wanda yace da wani uffan, Haleema na wani tunanin na dabam, Amira ma haka har suka isa gida.
Tun kamin su faka motarsu Haleema ta gane yayanta ya dawo, ganin yadda sojojin suka koma cikin natsuwarsu sosai.
“Big bro ya dawo kenan!”
Ta faɗa tana zare key ɗin motar, Amira dai bata ce komai ba, har suka fita motar suka nufi ƙofar shiga falon.
Gabanta ya faɗi sosai lokacin data saka ƙafarta cikin falo, ta yi ido biyu da Abdool.
Abinci yake aunawa a cikinsa yana zubawa Ummi satti, yanayin fuskarsa kawai zaka kalla ka fahimci baya cikin damuwa, dan annuri ne shimfiɗe a fuskarsa.
Cikin sanyin jiki Haleema ta ƙarasa kusa da Ummi dana wasar haƙura, dan tasan laifinta na fita bata faɗawa Ummi ba.
“Daga ina kike?”
Ummi ta tambaya fuskarta babu alamun dariya. Ta ɗan sosa kai tana tunanin irin ƙaryar da zata yi ma Ummi dan bata jin zata iya faɗa mata gaskiya.
“Ya Abdool an sauka lafiya”
Amira da ke can gefe Haleema ta miƙawa Abdool gaisuwa. Ba tare daya ɗago ya kalleta ba ya amsa.
“Lafiya ƙalau”
Sai ya miƙe tsaye yana yi ma Haleema wani kallo.
“Daga Ina kuke?”
“Pizza na ce ta raka ni na siyo kuma ban samu ba”
Ta faɗa tana pretending like she's serious.
“Amman idan zaku je siyen Pizza sai kawai ki kama hanya ku fita without permission?”
“I'm sorry Ummi i promise ba zan sake ba”
“You're very stupid, haka kawai zaki saka kafa ki fita ba tare da kin faɗa ba? Baki san rayuwarku tana cikin haɗari ba? Ba ni kaɗai za a riƙa farauta ba har da ku”
Abdool ya faɗa yana kallonta har handkercheif ɗin dake hannunsa ya faɗi.
“Haba Big Bros Wallahi ba zan ƙara ba, dan Allah ku yi haƙuri”
Ta faɗa kamar mai shirin yin kuka. Amira kan idonta na kan Abdool, annurin fuskarsa kawai take kallo, a ɗayan ɓangaren kuma tana Allah-Allah ya manta da handkercheif ɗinsa ta ɗauke, ta yadda zata fi jin daɗin tuna sa idan tana tare da shi.
“Miya hana ki zuwa makaranta?”
Ya tambaya yayinda ya risina ɗaukar handkercheif ɗin.
“Yau ba mu da lacca sai four”
Be sake ce mata komai ba, ya kalli Ummi.
“Zan je gurin Mai Martaba”
“Mu zaka ku? Tun da ka sauka naga ka kira shi fa, akwai abunda kuke shiryawa ko?”
“Kedai Ummi kawai ki sa ido ki yi kallo, wannan tsakanin ɗa da uba ne”
“Idan tayi tsami ma ji, miye sunan in-law ɗin tawa?”
“Da saura Ummi, bata kama hanyar zama in-law ba tukuna, sai mun yi settling abubuwa. Her name is NAMRA...!”
Wani irin faɗuwa gaban Amira yayi har sai da kanta ya tsara.
‘Namra’
Ta maimaita sunan a ranta tana, tuna wacan Namra wacce take ganin ita ce silar shiga ta wannan halin rayuwar. Kamin ta kalli Abdool da ya kai hannu ya ɗauki apple ya fice yana wasa da shi. Ummi kuma ta tashi ta nufi Kitchen, sai ya rage daga Amira sai Haleema ne a falon. Amira ta matsa kusa da Haleema ta dafa kaɗatar.
“Haleema zan shiga ciki, idan Ummi fa faɗi abunda za a girka da ranar nan kya sanar da ni please”
“Okay Sleep well”
Cikin sanyin jiki ta juya ta nufi ɗakin Amal da ya zame mata kamar ɗakinta.
ABDOOL POV.
Cike da zumuɗi ya isa faɗar Mai Martaba, kai tsaye ya wuce part ɗinsa da yake zama. A babban falonsa ya same shi, Hajiya Shafa na haɗa masa abun karyawa, yana ganin ɗansa ya washe haƙura, wanda hakan sam be yi ma uwaegidan Mai Martaba daɗi ba.
Cikin girmamawa Abdool ya gaishe ta, ta amsa masa kamar babu komai sannan ya gaishe da Mai Martaba yana masa kirari.
“Ba wani daɗin baki da zaka min sai da ka fara gaishe ta sannan zaka miƙa min gaisuwa”
Dariya yayi shi da Hajiya Shafa, sannan ya ce
“Ayi haƙuri Mai Martaba, zafi zafina na zo dan labarta maka komai”
“Muma nan ai mun aje maka labari har da ɗuminsa”
Hajiya Shafa ta faɗa. Abdool ya ce
“Tau a fara bani na sha”
“Wannan albishir kuma Mahaifinka zai maka shi”
Ta tashi ta fice tana dariya. Mar Martaba ya miƙa ma Abdool tea da aka haɗa masa shi kuma Abdool ya aje tea a gefe ya shiga haɗa ma Mai Martaba wani yana labarta masa labarin Namra.
Sai kusan Sha ɗaya da rabi suka gama karyawa tare da Mai Martaba yadda Abdool ya zage yana cin abincin ba zaka ce ya ci abinci gurin Ummi ba.
Mai Martaba ya jinjina lamarin Namra sosai kuma ya tausaya mata duk da be ganta, bama abunda ya fi taɓa shi kamar yadda ya ji tana raɓe a gidan wasu bayan kuma uwarta da ubanta suna raye.
“Amman Ina ka haɗu da ita?”
Abdool ya yi shiru yana tunanin faɗawa Mai Martaba gaskiyas lamari.
“Ranka ya daɗe ina binka bashin albishir fa”
“Albishir ɗin ka, zan faɗa maka idan ka samu natsuwa kun kai ƙarshen wannan matsalar”
“Yanzu ya kake ganin za a ɓullowa lamarin?”
Mai Martaba ya gyara zamansa.
“Abunda za mu yi, zan sa a rubuta masa wasiƙa daga nan Masarautar zuwa can inda yake, ai kana da addireshinsa ko?”
“Eh ina da shi, dan nasa an min bincike akan sa”
“Okay zamu saka a aika ma Sarkin Musulmi na sokoto shi kuma zai aika wani ya kai masa wasiƙar”
“Amman Mai Martaba me zai hana ka aika masa kai tsaye?”
“Ai mu sarakuna bama haka, dole ne sai sarkin gari ya san da abunda wani sarkin yake so a garinsa. Musamman babban sarki kamar shi”
“Okay zuwa yaushe za a aika?”
“Yau zamu aika, ina tunanin gobe zata isa gare shi”
Abdool ya ji daɗin haɗin kan da Mai Martaba ya bashi sosai da sosai. Daman ya tsammaci haka, dan ƴasan yana samun goyon bayansa a dukan abunda zai yi.
KALSOOM POV.
*Bayan wata biyu*
Tun da aka soma shigo da kayan har aka aje,be ji motsinta a falon ba hakan ya tabbatar masa da tana kitchen, kai tsaye ya nufi kitchen ɗin, fuskarsa ɗauke da murmushi. Ta baya ya yi hugging ɗinta ya aika mata da kiss a gefen fuska.
“Me kike girkawa?”
Wuƙar dake hannunta ta aje ta juyo tana dariya.
“Hancin ka zan girka”
“An ya zaki iya cin hancin na?”
“Kwarai kuwa ta yadda Amaryar nan da taga baka da hanci zata ce ta fasa auren”
Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, ya zageye kunkurunta da duka hannayensa.
“Shikenan sai ki kashe min kasuwa ko?”
“Eh mana ai ƙara ni kaɗai zan riƙa ganin kyan ka”
Ya riƙa hannunta yana dariya.
“Zo ki ga wani abu”
Gabanta yayi mugun faɗuwa, haka kawai ta annayana a ranta ba abun alheri ba ne, cire hannunta ta yi cikin na shi.
“Bari na juya miya sai na zo”
Be mata musu ba, ya juya ya fice. Ta ɗauki minti goma a kitchen ɗin tana ta fargabar fita, duk da bata san abunda zai nuna mata ba, tana ji a ranta kamar ba alheri ba ne. Ba ƙaramin dauriya ta yi ba kamin ta wanke hannayenta ya juya miyar sannan ta nufo ƙofar falo.
Tana ganin akwatuna jere a tsakiyar falonta, bugun gabanta ya ƙaru, idonta kuma ya cika da hawaye. Ga invitation card da kwalayin minti da cinka a saman akwatunan mai yawa ana ɗora. Jikinta yayi sanyi sosai, hawayen dake maƙalle a idonta ya gangaro zuwa kumatun ta.
“Ashe haka Rashida ta ji lokacin da za a auro ni ko?”
Ta faɗa muryarta na rawa. Ɗagowa Hilal yayi ya kalleta, sai ya miƙa mata hannu alamar ta zo, sannu ta fara takowa har ta kawo inda yake ta miƙa masa nata hannun. Sai ya zaunar da ita ƙasan kujerar ya ɗora mata hannayensa saman kafaɗunta, kasancewar shi yana saman cushion zaune ne.
“Ki duba ki ga idan akwai abunda babu zan ƙaro”
Kai ta girgiza ta miƙe tsaye.
“A'a ni nabar mata kayan duka ka kai mata, ina da kayana”
Shima.ya miƙe tsaye.
“Na sani ai, ba tsirara na auro ki ba”
Sai ta yi ƙasa da kanta tana hawaye. Hannunsa ya saka cikin nata yaja zuwa ƙirjinsa, sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.
“Sorry dear, zan canja miki komai idan kina buƙata, just be strong”
Kuka tayi sosai har sai da ta ɓata mishi gaban riga da majina, sannan ta sake shi ta nufi toilet ɗin falo saboda amai da taji ya cika mata baki.
ASIM POV.
Tun safe ya tashi ko da goma tayi yana cikin garin sokoto, A hotel ɗin Shukura ya kama ɗaki, sai da ya ɗan huta sannan ya kira Ubangidansa ya sanar masa da ya iso. Ya bashi tabbacin sai dare zasu gana, da alama can zai kwana inda yake, dan ya faɗa inda zai same shi a gidansa da ke Sama road.
Fitowa yayi ya biya kuɗin wuni ɗaya, sannan ya ɗauki hanyar gidansu, zuciyarsa cike da nishani, yana mai jin kansa lallai shi a yanzu wani ne.
Ko da ya isa unguwarsu ƙarfe ɗayan rana yayi, dan haka irin mazan nan masu zaman kashe wando duk basa nan sai da yamma suke zama, kasancewar unguwar minannata, haka suke da yamma ta yi, amman hakan be hana wasu ganinsa ba, dan tabbatar da shi ɗin ne yasa wasu gayu zuwa su bashi hannu shi hannu su gaisa suna masa yaushe gamu.
“Kai ke da wannan?”
Ɗaƴan ya faɗa yana nuna motar dake kusa da su.
“Eh Wallahi sai a taya mu addu'ah”
“Toh Allah ya taimaka ya tsare. Kace kai ma ka shigo gari, ko da yake kana sirikin Manjo Usman ai dole ka hau wannan motar”
Ɗan murmushi yayi.
“Babu ɗigon dukiyarsa nan”
Duk dariya suka yi, ba dan sun yarda ba, sai suka ƙara gaba suna nasu zancen.
Da farinciki ya shiga gida, yana doka sallama kamar wani baƙo. Da gudu Mama ta fito dan tabbatar da muryar ɗan na ta ne ko bashi ba, ganinsa yasa ta daki ƙirji tana ƙare masa kallo
“Ibrahim kai ne? Allahu akbar”
Ta shiga shafa kayan jikinsa tana kuka, shi kam sai dariya yake yana kallon ƙanensa dake sanye da uniforn ɗin makaranta suna kallonsa. Da alama suma basu gama tabbatar da shi ɗin ba ne.
“Ji yadda kuka tsaya kallo na”
Sannan suka yi dariya suka rugo a guje suka rumgume shi, suna murna. Sai da suka gama zumuɗinsu sannan Mama ta ɗauko tabarta ta shimfiɗa masa tsakar gida, ko zama be yi ba sai ga maƙota sun soma shigowa ƴan ganin gwan, kar ayi ba su, dan kace kwabo har labari ya fara zaga unguwar.
Ya sha gaisawa da mutane sosai, dan sai a lokacin wasu ke masa ya jiki. Sai kusan La'asar ya samu keɓewa da Mama suna tattauna lamuran duniaya.
“Amman wannan matar Allah yayi mata tausayi, irin wannan hidima haka? Ko dai
Book Chapters
Chapter 49
Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71