You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da sake fashewa da kuka wanda ya kusa saka

numfashinta Waukewa.

"LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI."

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI .

5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5Ø
Ü 5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ

LABARI ME CIKE DA

"BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, "

"KUNCIN CUZIYA, "

"SADAUKARWA, "

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.

WRITING BY

MARYAM STAR

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*

THE NOBLE WRITER'S TEAM

PAID BOOK 500 ONLY

BOOK TWO

CHAPTER 12

EJ-1D' FE-1D' 'DDG E3(.

Ta na ganin dishi-dishi haka ta mi™e ta saSi mayafinta da carkey ta fice zuwa parking lot ta Wauki motarta

"ta fice da mugun gudu ta na sharSar kuka, ga fuskarta kaca-kaca da jini, sai da tai gudu sosai ta tabbatar da ta fita daga garin Abuja sannan ta nemi waje tai parking tare da kwanciya ta baya akan kujerar."

SADIYA

"Tsaye ta ke ta na bawa masu aiki umurnin yanda zasu shirya abinci, fuskarta gwanin kyau domin kuwa"

"kwalliya ta caSa kamar me shirin zuwa gasar ado da kwalliya, ta na gama sallamarsu ta fice zuwa main"

parloun inda ya ke cike da ba™i ´an barka da taya murnan sake samun rabo bayan tsawon shekaru da ta

kwashe bata sake haihuwa ba.

"""Ai Sadiya baiwar Allah ce, ga kirki da tawassalin Waukar ™addara, yo idan wa ta ce aka sacewa ´a´a"

"har karo biyu ai ba zata sake zama da mijinba, musamman yanda ake ta raWe-raWe akan wai shike"

"sadaukar da ´a´anshi ga dodon tsafi."" Wa ta dattijuwar mata ta faWa cike da gulma, yayinda wace ke kusa da ita itama ta caSe da faWi."

"""Ai babu wai, yo ai daganin wannan farin jini da tarin dukiyar ta Alhaji Umar ku kunsan ba banza ba, a"

"yanda ake faWi fa yanzu shine na bakwai a jerin ´an kasuwa masu kuWin Nigeria."""

"Sallamar Sadiya wace ta rigada taji dukan firar da suke, ita ta katse Iya Laraba daga zancen ™anzon"

"kuregen da ta ke, sai kuma tahau burin kunya gami da ™a™alo fara'ar dole ta yaSa akan fuskarta."

"""Kaga Halimatus Sadiya uwar gida me pacasity a gidan Alhaji Ummaru sarkin ´an kasuwa, yau dai"

"Allah ya nufa bayan tsawon shekaru ashirin kin sake ganin kwanki a duniya, ni Balaraba ina tayaki murna, Allah ya rasa akan sunnar Ma'aiki."""

"Murmushi kawai Hajiya Sadiya ta yi, fuskarta babu alamun komi ta gabatar musu da lemo kafin abinci ya"

"sauka, babu kunya suka naWe lemon a jaka, su na faWin sayiwa yara guzuri da shi, da yake Baba Laraba ´ar uwar Sadiya ce kuma anan ™auyen abuja take da zama itada mijinta, sanin halin Alhaji Umar na son ba™i da talakawa ya saka bata kwashe wata guda cir ba tare da tazo gidan ba, idan ta tashi zuwa haka za ta Wibo gayyar mutanen arziki ta taho da su dan samun abin duniya, dayake karamci a jinin Alhaji Umar ya ke, hakanan yake zagewa ya saki bakin aljihu yayiwa Baba Laraba da tawagarta kyauta ta bajinta da"

ban girma.

"A wunin ranar haka Sadiya taita karmar ba™uncin ´an uwa da abokan arzi™i, musamman matan abokan"

"kasuwancin Alhaji Umar da ´an siyasa, yara kuma sunsha kyaututuka sosai a wajen ´an barka, sai dare Sadiya ta samu kanta, ta je Wakin barcinsu ta taradda Alhaji Umar na sana'ar ta shi wato tunani, idan ta kalleshi sai zuciyarta ta tsinke saboda yanda ya zama abin tausayi, yayi wani sukuku da shi kamar marar laka a jiki, har yanzu Sadiya bata saba da wannan yanayin nashi ba, ta lura yanzu abin na shi gaba yake sake yi, domin kuwa kullum sai ta lura da wani sabon canji a tare da shi, yanzu bai damu da yayi komi da kanshi ba sai shiga toilet, da kuma zuwa gaban photon yaransu da suka rasa yai tsaye ya na kallonsu ya"

"na kuka, alamomi da yawa a bayyane suke waWanda daga gani tasan ba lafiyar mijinta lauba."

"Kife kanta tayi a kan gado wani irin kuka na rashin mafina na kwace ma ta, sai da tai kuka sosai"

"kamar ranta zai fice, naman ™asan idonta yai jajur, su kansu idanuwan na ta sun kaWa sun koma launin"

"jah, sai ta ke jin kamar abin ya mata nauyi ba zata iya Wauka ita kaWai ba, da gaskiyar Malam da yace"

"akwai rikitattun al'amuura da zasu fuskato rayuwarta masu kama da ZAFIN WUTA, wanda suk juriyarta ba zata taSa iya jure su ba, dole ne za ta nemi taimako, abin da ta ke yiwa kallon shirka da kanta za ta nemi a aimaka ma ta da shi, ba zata taSa mance kaifafa maganganun da ya watsa ma ta ba kafin ya"

tattare kayanshi yai tafiyarshi.

"Zumbur ta tashi kamar wacce aka zabura, sai kuma ta shiga laluben wayarta, bayan ta ganta a saman"

"pillow sai ta shiga neman number da ta Wauki shekaru ta na dannawa delete amma ta saka gogewa, saboda batasan mi gobe za ta haifar ba, da ace ta goge number da tashin hankalin da zata shiga sai ya ninka wanda take ciki."

"Gabanta ne ya shiga luguden suka, wa ta iriyar kunya ta baibayeta, sai ta ji duk ta muzanta, ita ta"

"koreshi daga rayuwarta, kuma itace ta nemoshi kamar yanda ya ce zata nemeshi idan al'amurra suka"

"rikice, wa ta iriyar hantsalowa zuciyarta ta yi kamar zata faso ™irjinta ta fito lokacin da ta cinkayi sallama"

"daga muryarshi, ba zata iya fasalta halin da take ciki ba, sai cintar kanta da ta yi tana faWin."

"""Malam!!! Malmam,, Malam na sare, ™arfina ya ™are, zuciyata ta karaya bazan iya Waukar komi ni"

"kaWaiba, ina bu™tarka a kusa da ni, ina bu™atar taimakonka atare da ni, bazan iya Waukar nauyin ba, na raunana yanzu na yi rauni zuciyata ta karaya, badan ni ba badan halayyata ba ka taimaka ta dawo, na yi imani da Allah kaima na yi imani da maganganun da ka gaya min a baya, tabbas wa ta jarabtar ba lallai"

"mutum ya iya jureta ba duk kuwa ™arfin imani da zuciyarsa, na haWa ka da girman Allah Malam."""

"Kukan da take ri™ewa ne ya kwace ma ta ya shiga rero kanshi, yayinda acan Wayan Sangaren Malam ya yi"

"shiru ya na sauraren kalamanta, sai wani murmushi ya kwace ma shi, yasani ba zata iya Wauka ita kaWai ba, abin yayi ma ta yawa, ko a bayama yaga mugun ™o™arinta, kuma ya yaba ma ta, ya jinjina da irin ™arfin da zuciyar mace take da shi, sai ya sauke numfashi yana jin kukanta na ratsa kunnuwanshi, a"

hankali cike d rarrashi ya ce.

"""Ha™i™a kinyi namijin ™o™ari, na yaba da ™o™arinki Halimatu, kin neme ni da kanki bayan tsawon"

"lokaci, ki saka a ranki matsalolinki zasu fara warwarewa tun daga tushen da aka soma gina su, komi ya zo ™arshe, yanzu ya™in namu ne, kuma da izinin Ubangiji mune da nasara, zamuyi nasara akan mugaye kuma azzaluman mutane, waWanda suke azabtar da ruhin ´an uwansu da ZAFIN WUTA, zan zo gare ki"

"Halimatu.""."

5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5Ø
Ü 5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ

LABARI ME CIKE DA

"BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, "

"KUNCIN CUZIYA, "

"SADAUKARWA, "

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.

WRITING BY

MARYAM STAR

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*

THE NOBLE WRITER'S TEAM

PAID BOOK 500 ONLY

BOOK TWO

CHAPTER 13

EJ-1D' FE-1D' 'DDG E3(

"Sauke wayar Sadiya ta yi, tana jin wani ™arfin gangar jiki da zuciya na zuwa ma ta lokaci Waya, sai ta tashi"

"zumbur tare da kama hanun Alhaji Umar ta nufi toilet da shi, alwala ta Wauro shima ta taimaka ma shi yayo alwalar suka fito a tare, sallaya ta shimfiWa musu, nan suka shiga jero salloli babu ™a™™autawa, yayinda take sauke dukkan bu™atunta idan tai sujjada, duka rauninta da gazawa take tattarowa ta ro™i ubangiji ya yaye musu wannan wahalhalun rayuwar da suke fuskata, ya sau™a™a musu ™addarorin da ke"

sake kutsowa cikin rayuwarsu.

AGEGE

ABBA

"Tun ranar da Umma ta satarwa Abba kuWi ya canza salo, yanzu baya zama da kuWi a jikinshi, banki ya je"

"ya buWe account har guda uku, ya zuba rabi da kwatar kuWin, sannan ya bazama wajen malamai ya na neman fassarar mafarkan da suka addabi rayuwarshi, muddin zai kwanta ya rufe ido da sunan barci, to sai yayi mafarki akaina, kuma ya bada sunan Mama akan a karkato da hankalinta gareshi, dan yanzu ta zage sai Wibar albarka ta ke ma shi, bata ragawa kowa ba yanzu, bata barin bashin magana, sannan kuma ya na so a rufe mashi bakin Umma aka kuWin da yake so ya bawa Mama wanda Alhaji Abdallah me gwalagwalai ya umurta akan a bata, duk da ba duka zai bata ba amma yasan dole za'ayi rigima da Umma"

akan kuWin.

"Ranshi fes ya dawo gida ya ci gaba da gudanar da sabgogin gabanshi, yau dai shiru kukejin bakin"

"Umma, ko ´an kudaWen da ake damfarar Abba ba'a amsa ba, sai faman kaiwa da komowa take ta na shafce gumi, aikin girki ta ke, amma idan kukaga zanin jikinta kamar me yin aikin ™uli zanin dawan- dawan da shi kamar tsuman sauke tukunya, takalmi gamin bauta ne ta saka a ™afarta, sai faman zarya ta ke daga Waki zuwa inda ake girki, duk bayan mintuna uku sai kaga ta kamo haSar zani ta fyace majina,"

sai ta buWa tukunya ta jujjuya sannan ta rufe ta koma Waki.

"Mama ma yau ta na Waki zamanta ta ci kwalliya tana girki a gas Win sai ™amshi ke tashi gwanin daWi,"

"yanzu Mama idan ba alwala ko shiga bayi ba ba ta fiye fitowa waje ta zaunaba, tafi zamanta a Waki ita kaWai abin ta, duk wanda tsautsayi ya saka yai ma ta ba daidai ba zai fuskanci Sacin rai, bata shayin kowa"

yanzu ta zama masifaffiyar ™arfi da yaji.

ABUJA LAWAN.

"Zaune ya ke a gaban wani rami, hannunshi a zura tare Wauko wa ta ´ar tsana wacce aka Waure ™irjinta da"

"wa ta yar tsoka, jikin tsokar an caccaka allurai, wani jini ya Wauko cikin ´ar ruba ya shiga kwararawa a jikin ´ar tsanar ya na diga cikin ramin, maida ´ar tsanar yayi tare da mayarda ™asa ya rufe sannan ya maida grass carpet a wajen kamar ba'ayi komi ba, kakkaSe hannunsa ya yi tare da zuwa gaban tap ya"

wanke tsa sannan ya fice daga gardeng Win.

"Manyan mutane ne zaune a babban parlon su uku su na, ko wannensu da ™aton tunbi a gaba, ga"

"gemunansu duk farin gashi alamar anfara kwana biyu, fuskokinsu a murtuke babu fara'a ko kaWan."

"""Barkanku da ™arasowa manyan giwaye, yanzu nike """

"""Dakata Lawan, ba zuwa jin tatsuniyar da ka saba shirya manah ya kawomu nan ba, zuwa muka yi jin"

"muye dalilinda yasa baka cika aikin da muka umurceka da shi ba tun shekaru ashirin da Waya da suka shuWe, mufa ba yara bane da zaka zauna kana tsara mu da ™arairaki, munzo ne muji ta inda ka bari aka"

"samu matsala."" Šaya daga cikinsu ya faWi tare da cafar tufa ya gatsa a baki babu ko basmala."

"""Mu™uttt"" Lawan ya haWe yawu me kauri, hasashe ya ke wane aiki ne nasu bai cika ba, tun da har suka"

"yo tattaki suka suka zo har inda yake a daidai wannan lokacin babu sanarwa yasan ™iyamarshi na daf da tsayawa, sake bin su da idanu yayi yana ™are masu kallo a zuciyarshi yana furta."

"""Ale Dikko Zakin fama, Alhaji Balarabe Basani ba sabo, Alhaji Mas'ud Cinnaka bakasan na gida ba, sai"

"na ™arshensu oga kwata-kwata Alhaji Muhammad Bello Kuraye, manyan mutanenda ake damawa da su a fannin siyaya da kasuwanci, mutanen da al'umma ke yiwa kallon shuwagabanni na kwarai, har talaka"

"na yi musu la™ani da baya goya marayu, saboda yanda suke hidimtawa jama'a da aljihunansu, sai de kash,"

"su Win kura ne lulluSe da fatar akuya, sun kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen ™untatawa talakawa ta ™ar™ashin ™asa, suWin taurarine masu wutsiya ganinsu sam babu alkairi."

"Saita kanshi ya yi tare da sake sunkui da kai ya aro bangon nutsuwa ya yafawa kanshi, sannan ya"

rausayar da murya yana faWin.

"""Kuyi min aikin gafara, nidai a iya sanina ban bar ko Waya daga cikin ayyukan da kuka taSa saka ni,"

"niWin tamkar ™as™antacen bawa ne a gabanku, na kasance ina jiran umurninku dan biyanku akan halaccin da kuka taSa yimin, kuyimin aikin gafara saboda ni Wan Adam ne kuma ajazi, ko zan iya sanin aikin dana kuskure akanshi idan da hali in gyara shi yanzu-yanzu."""

"Wa ta dalleliyar ba™ar harare Ake Dikko ya dallawa Lawan, yana jin kamar ya murWe wuyanshi ya raba"

"shi da numfashinsa, sabosa tsabar fusata da abin da ya yi musu."

"""Shin ko kasan cewa ´a´an tsohon amininka Alhaji Umar su na nan raye a duniya, shin ko kasan cewa"

"rayuwa da burikanmu su na dab da rushewa ta sanadiyyar sakacinka, shin tayaya yaranda ka tabbatar"

"manah d sun mutu suke a raye, ta ina wanda ya mutu zai dawo, shin ko za ka iya faWa mana ta yanda akai haka ta faru."" Cewar oga kwata-kwata Muhammad Bello."

"Wani irin ™ugin tashin hankali ne cikin Lawan ya yi, yayin da idanuwansa suka firfito waje cike da tashin"

"hankali gami da firgici, zufa ce ta shiga karyo ma shi daga cikin kai ta na tsiyaya har cikin rigarshi, sau bakwai ya na buWe baki zai yi magana amma sai maganar ta ma™ale ta gagara fitowa sakamakon"

numfashinshi da ke barazanar Waukewa.

Babu ko tausayi a fuskokinsu suka shiga zayyano ma shi kalolin u™uba da tashin hankalin da zai fuskanta

"matsawar bincike ya sake tabbatar musu ´a´an Alhaji Umar su na raye, tsallake shi sukayi ba tare da ko"

tausayi ba suka fice suka barshi a halin firgici da Wimauta.

"Zarya ya ke tsakanin bango zuwa bango, ya na lissafa ta yanda za'ayi ace yaranda Fatima Abbas ta"

tabbatar masa da mutuwarsu za'ace su na raye.

"""Wait, shin wai ma wacece Fatima Abbas, kuma wacece Sadiya matar Alhaji Umar."""

Ya jefawa kanshi tambayar tare da tsallakawa tunanin abubuwanda suka shuWe acan baya.

"Alhaji Abbas Wan kasuwa ne babba, ya na kasuwancin siminti da buloluwa, tun farko ya fara ne da gina"

"gidan bulon ™asa, kafin daga bisani zamani ya zo aka fara yin ginin bulon siminti, a wancan lokacin za'a saka Abbas cikin jerin ´an kasuwa masu faWa a ji, babu inda simintin Abbas bai zagayaba a Nigeria, yayi aure tun ™uruciya inda akai masa auren haWi shi da ´ar uwarsa Hadiza, kasancewa Hasiza nutsatsiyar kamilar yarinya ya saka Abbas fara sonta, dan shi yana son mace me kamun kai da kunya, bayan aurensu sun gina rayuwa me tsari dabin turban addinin musulinci, su na girmama junansu sosai hakan ya sake ™arfafa soyayyar tsakaninsu ta rikiWe ta koma zazzafar ™auna, sun Wauki lokaci basu samu albarkar aure ba wato haihuwa inda iyayen Hadiza da kansu suka matsa akan ya ™ara aure gudun kar ace matsalar daga Hadiza ne, da farko yaso yai tiejiya amma da suka bashi kwararan hujjoji sai ai na'am da hakan ya kuma basu wu™a da nama akan su zaSa ma shi wacce ta dace, sunji daWin karamcin da yayi musu hakan yasaka mahaifiyar Hadiza ta nema ma shi auren ™anwar abiyar zamanta, itama ta na da nutsuwa sosai ga girmama mutane sannan ta na da addini dan kusan tare suka taso da Hadiza, ba'awani Wauki lokaci ba aka saka ranar aure Abbas da Karima, inda Hadiza ta shiga sahun gaba wajen masu murnan haWin wannan auren da iyayenta sukai, bayan anyi auren Karima da Abbas suka haWe kansu da Hadiza suka"

samar sa wanzajen farin ciki a gidan Abbas.

"Bayan shekara Waya da aure Karima ta haifawa Abbas ´a mace, wace taci sunan mahaifiyar hadiza ana"

"Fateema ana kiranta da Inno, Hadizama ba'aWauki lokaciba ta santalo ´an biyu kyawawan gaske"

"waWanda suka biyo ta, tsakanin Karima da Abbas aka rasa gane wanne yafi farin ciki, dan su suka raini"

´a´an iyakar Hadiza da su shayarwa.

"Rayuwa na ™ara gaba Abbas na sake samun dukiya da arzi™i me tarin yawa, inda ya baro garin Katsina ya"

"dawo Kano da zama yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hadiza nada yara uku yan biyu Hassan da Husaini sai gambonsu Aama'u, ita kuma Karima tun haihuwar Fatima ba ta sake samun haihuwa ba, bayan an yayeta yayar Karima Wasila ta Wauketa daga yaye ta ri™e ta ce tayi ´a, bayan dawowarsu kano da shekara biyu Hadiza ta haifo sntaleliyar ´ar auta, wace ta biyo ainahin kamanin maaifinta Abbas, fara me dogon hanci da manyan idanuwa haWi da sisilkan ba™in gashi, aka saka mata suna Halimatus Sadiya, sha™uwa me tsanani ce ta shiga tsakanin Sadiya da mahaifinta, inda ya je ririta ta, sosai Karima ke nunawa Sadiya soyayya ta gaske, komi ta samu Sadiya ahankali ta janyota tadawo da ita Wakinta da"

kwana.

"Shekaru sun ja da dama, yanzu Alhaji Abbas ya zama babban mutum, kuma Wan kasuwa wanda ake"

"damawa da shi ta harkar kasuwanci, Allah yayiwa Hassan Wanshi rasuwa sai Husaini da sadiya da Asma'u ne kawai ´a´ansa, tuni ya barwa Anty Wasila Fatima kyauta halak malak saboda Allah bai basu haihuwaba ita da mijinta, Karima kuma bata ce komi ba akan hakan dan yanzu ida ba sa ni kaiba ba zaka"

ce ba ita ta haifi Sadiya da Asma'u ba.

"Hussaini yayan Sadiya ya taso d son ilimin islamic, inda ya gaji Kakanshi Malam Iro ta fanin sanin"

"magungunan gargajiya da likitanci a musulunci, sannan ya na tare da baiwar gane sihiri ko sammu,"

"wannan yasaka ace kiranshi da Malam, Malam na matu™ar ™aunar Sadiya, bayason duk wani abu wanda"

"zai Sata ma ta rai, idan ka ji hayaniyarshi to akan an taSa Sadiya ne."

Sadiya ta gama secondary school Alhaji Abbas ya turata Zaria gidan Wan uwa kuma babban abokinshi ta

"yi kadatu a A B U, a canne Sadiya ta haWu da Fatima Abbas wacce itama tazo karatu a fanin kasuwanci, ba tare da sanin suWin ´an uwa ba ne suka ™ulla ™awance, koda yaushe su na a tare, duk inda kaga"

Fatima to zaka ga Sadiya a wajen.

"LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI."

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI .

5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5Ø
Ü 5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ

LABARI ME CIKE DA

"BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, "

"KUNCIN CUZIYA, "

"SADAUKARWA, "

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.

WRITING BY

MARYAM STAR

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*

THE NOBLE WRITER'S TEAM

PAID BOOK 500 ONLY

BOOK TWO

CHAPTER 14

EJ-1D' FE-1D' 'DDG E3(

"Kowane lactura yasan da zaman Fatima Abbas da Sadiya Abbas, kasancewarsu masu ™o™ari da maida"

"hankali sosai akan karatu, lacturas na alfahari da su sosai saboda ™wazonsu."

"A makaranta ne Sadiya ta haWu da wani kyakkyawan matashi me ji da naira, ba dalibi bane lactura ne"

"shima, shike Waukarsu a fanin kasuwanci, tun ranar da ya Wora idanuwansa akan Sadiya matsananciyar ™aunarta ta mamaye shi, sam baida sukuni sai yaga Sadiya, gashi ya rasa ta hanyar da zaibi wajen sanar da ita yana sonta, ganin zaiwa kanshi illa sai ya shirya takanas ya je har ™ofar shiga hostel Winsu ya nemi a kira ma shi Fateema Abbas, sosai Fateema Abbas tai mamakin jin cewar sir Umar Aminullah na nemanta,"

"saboda zumuWi kasa tsayawa tai Sadiya ta fito daga wanka ta sanar ma ta tai, sai kawai ta shiga gyara"

"fuskarta ta na fatan ace yazo wajenda da wani abu me kama da soyayya, cike da Wauki ta fita ta nufi"

"wajen da aka kwatanta mata, da zuwanta ta taras da shi tsaye kusa da tsadaddiyar motarsa ya na jifarta da tsadaden murmushi, da kyar ta saita kanta ta dan karta kwafsa, dan sai yanzu ta sake nutsuwa ta na ™arewa halitarshi kallo, wa ta kibiyar ™aunarshi ce ta soke ta a ™ahon zuciyarta nan take, murmushin da"

yake sakar ma ta ya sake ingizata ta afka cikin kogin ™aunarsa.

Ta na maida ma shi da martanin murmushin ta tsaya tare da yin sallama cikin saura ainahin sautin

muryarta wanda itama batasan ya aka yi ta samu kanta da sauya murya ba.

"Sai de kash, Umar yayi nasarar dugunzuma tunani da zuciyar Fateema Abbas ta hanyar faWa ma ta yazo"

"ne ta shige mashi gaba wajen samun soyayyar ™awarta Sadiya, inda ya warware ma ta yanda yake fama"

"da gyambon sonta a zuciyarsa, yanzu yakai matakin da ko barcin kirki baya samu."

"Wa ta zufar tashin hankali ce ta tsatsafowa Fateema Abbs, yayinda ta ke kokowa da harshenta wajen"

"ganin bata dannawa Umar manya-manyan ashariya ba, ta daWe bata ce komi ba, shiko ganin shirun yayi yawa ya saka shi tunanin ko Sadiyar na da wanda take so, tunanin hakan kaWai sai da ya dugunzuma"

"nutsuwar zuciyarshi, amma yai ™o™ari wajen saita kanshi."

"Fateema bata da wani zaSi a lokacin sai cewa da tayi karya damu zata tuntuSi ™awarta akan zance, duk"

abin da kenan zata sanar da shi.

Sosai Sir Umar ya ji daWin wanan zance hakan ya saka yaiwa Fateema kyautar kuWi masu kauri waWanda

suka sake karyar ma ta da zuciya ta kuma sake jin soyayyarshi na yun™uron ma ta da ™arfin gaske.

Bayan tafiyar Sir Umar Fateema ba ta koma

"hostel ba ta nemi wani Wan tudu ta zauna ta na sharce hawayen ba™in ciki, ta na nan zaune wasu ´an"

"class Winsu gungu guda suka zo wajen, ashe duk abin da ya faru tsakaninta da Sir Umar akan idonsu ne,"

"hakan ya saka suka taho dan suji gulma, har musayar yawu sukai akan zuwa yai wajenta ya ce ya na sonta, dan Fateema Abbas babu laifi kyakkyawa ce itama, gata doguwa kamar Sadiya."

Kuka ne me sauti ya kubcewa Fateema Abbas lokacin da suke tambayarta abin da ya faru suka ga ta na

"hawaye ga kuma kuWi a hanunta, sanna kuma duk sunga zuwan Sir Umar wajenda."

"Fateema Abbas sam bata da sirri, tanan wajenne kawai ake jin kansu ita da Sadiya, kwashe komi ta yi"

"ta faWi ma su tana sakw fashewa da kukan takaici da hassada, aiko nan suka zagaye ta suka dinga famfata akan karta yarda ta barwa Sadiya Sir Umar, da ita ya dace ba da Sadiya ba, sannan suka hanata"

"faWawa Sadiya yana sonta, aiko Fateema Abbas tahau kan zugarsu ta zauna, a maimakon ta koma hostel"

"sai kawai ta bisu nasu hostel Win can suka shantake su na ta firar duniya, da yawa daga cikinsu sun daWe su na jiran wannan rana da zasu samu damar shiga jikin Waya daga cikin ™awayen, kowa na son mu'amula da su saboda baiwarsu ta karatu, amma Sadiya sam bata bawa mutane fuskar, har gara ma"

Fateema Abbas ita takan Wan kula wasu dan ta na da son mutane.

"A ranar Sadiya ta nemi Fateema Abbas amma bata ganta ba, ta yi ™o™arin kiranta a waya amma bata"

"same ta ba, haka ta ™arashe wunin sukuku da ita, sun saba duk inda zasu je su na tare, koda fita ta kama Waya to dole ´ar uwarta za ta sa ni, Fateema Abbas bata dawo ba sai can cikin dare, lokacin har Sadiya ta kwanta barci saboda ta n tashi tayi karatu cikin dare saboda tunkarowar exam, harara Fateema Abbas ta aikawa Sadiya sannan ta juya baya tai kwanciyarta cike da tunanin Sir Umar har barci yai awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai da asubahi shima Sadiya ce ta tada ita, lokacin da ta buWe ido tai arba da innocent face Win Sadiya tunanin yanda Sir Umar ya karkace ya saki baki ya shiga karanto ma ta yanda yake ™aunar Sadiyar, nanda nan ta haWe dai ta kuma daina ganin kyawun fuskar Sadiyar sai wani muni da ba™i da take gani, a yatsine ta tashi ba tare da ta kula Sadiya ba ta shige toilet, koda ta fito ta iske har Sadiya ta gama shirinta ta na shirin Waura girkin abin kari, dakatar da ita Fateema Abbas ta yi akan karta haWa da ita idan ta tashi ta haWa

Please Login or Register in order to submit comment