You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwantar da kanshi akan pillow sannan na zare hannuna ina jera ma shi sannu, lumshe ido kawai ya yi"

"tare da sake min hannu, a hankali na tashi daga wajen tare da kwashe kayan sannan na gyara wajen tsaf,"

"bayan na gama ne na koma gefe na rakuSe nai shiru ina tunanin duniya da irin ™alubalen da ke cikinta,"

haka wani kalar nannauyan barci yai gaba da ni.

"Sarauniya Zubudiyya ce zaune akan bango ta na kallon dukanin abin da muke yi, yayinda tausayina da na"

"Fauzan ya sake kamata, ita Win hallita ce me tsananin tausayi, sam bata son zalinci kuma bata shiri da duk wani me aikatashi, daga inda take ta na ganin inda Zuka yayi ajiya a jikin Fauzan, wanda hakan ke taimakawa wajen sake tsananta ciwon na shi, daga inda take zaune ta ziro hannu ta tattaro ajiyar kakaf, hakan yayi daidai da lokacinda na bashi maganin sha, shine ya amayar da sukanin ajiyar, sai ya ji wasai cikin cikinshi kamar an Wauke ma shi wani nannauyan dutse, cikin sanyin da ta saka min ta huro ma shi"

iska wace ta saka shi barcin rahama da salama.

ABUJA NG.

MAITAMA.

Tsaye ya ke agaban makeken frem Win da ke Wauke da hotunan kyawawan ´an mata guda biyu masu

"tsananin kama, babbar ba zata wuce shekaru huWu ba alokacin da akai hoton, Wayar kuma jinjirace fara sol kyakkyawar gaske."

Idonshi na zubda ruwan hawaye ya ke kewaye daidai fuskar jinjirar ya na shafawa.

"Wa ta kyakkyawar ma ta ce me kama da laraba ta shigo Wakin inda mutumin ya ke, taWan jima a"

"bayanshi ta na kallonshi, fuskarta Wauke da matsananciyar damuwa irin wacce tafi ™arfin a bayyanata a baki, tabbas ta na cikin matsananciyar damuwa, amma hakan bai hana ta yi tawassali da Allah ba, domin tasan dukan abin da ya samu bawa to yana rubuce a jikin littafin ™addararsa, kuma babu me gujewa ™addara face ta biyo shi da mugun gudu, irin gudun da idan har ta cimma masa to kuwa sai ta Allah kawai, ita Win mahaifiyace kuma me rauni, akwai raunin da yakai a raSa uwa da ´arta tun bata gama tantance iskar duniya ba, akwai raunin da yakai a raba uwa da ´arta lokacinda ta gama wahalar shayarwa da reno, ita tasan me rauni ce gaba da baya, amma batabawa zuciyarta damar raunana har ta kaita ga samun matsala ba, ta riga da ta dangana, ta bar komi a wajen Allah, mudin rana na fitowa ta na faWuwa tasan wannan ranar za ta zo, ranar da duk wani ™ulli zai warware kansa da ™arfin ™udurar ubangiji, ko da bata raye tasan ta yi babban tanadin zuwan wannan ranar, abu Waya kawai take jira,"

shine wanzuwar ikon ubangiji ta hanyar bankaWo duk wa ta ajiya da aka bizne a cikin ba™in duhu.

Cike da ™warin gwuiwa ta taka zuwa inda mutumin yake tsaye ya na ta faman sharSar kuka tare da

shafar fuskokin jikin photon.

"""Bansan har zuwa yaushe gwarzon jarumina zai yi tawassali da ™adararda ta daWe da yanke wannan"

"damSarariyar ™aunarba, ha isa hakan, ya isa!! yanzu ba lokacin yin kuka ko nuna damuwa bane akan zarenda ™addara ta daWe da yankewa ba, yanzu lokacin farin ciki ne da nuna godiya ga Allah da akan manya-manyan kyaututtukan da ya bamu, zo muje muyi tafiyar da za ta sada mu da farin ciki"

"madawwani wanda bazai yanke ba da izinin Ubangiji."""

"Ta ™arashe maganar ta na janyo hannuwanshi duka biyu kamar ™aramin yaro me koyon tafiya, haka ta"

"dinga janshi ta na tafiya da baya-baya harta cimma ™ofar wani Waki, buWe ™ofar ta yi da ™afarta sannan ta shiga har lokacin bata saki hannuwanshi ba, a gaban baby bed guda biyu ta tsaya tare da dafo kafaWunshi ta juyar da fuskarshi ta na faWin."

"""Yanzu lokacin farin ciki da godiyar Allah ne da ya azurta mu da wannan gagarumar kyautar wacce"

"muka daWe muna jira, ga makwafin yaranmu da muka rasa Allah ya dawo manah da su, MUBARAKA da MARYAM sun dawo gare mu, kallah!!! kallafa!, kalesu Alhaji."""

"Ta yi maganar ta na Wago da jariran yaran Waya bayan Waya ta na nuna ma shi, fuskarta faWaWe da"

"yalwatacen farin ciki, wanda ya kasance na gidoya ga Allah da ya ake azurtata da ´a´a mata waWanda ta ke fatan su kasance ma ta sanyin idaniya, kuma su mamaye wawakeken ramin da ke zuciyarta na rashin ´a´anta da ta yi, waWanda ba mutuwa sukai ba, kawai ™addarace da jarabawa ta Ubangiji ta nesanta"

tsakaninsu.

"LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI."

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI .

5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5Ø
Ü 5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ

LABARI ME CIKE DA

"BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, "

"KUNCIN CUZIYA, "

"SADAUKARWA, "

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.

WRITING BY

MARYAM STAR

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*

THE NOBLE WRITER'S TEAM

PAID BOOK 500 ONLY

BOOK TWO

CHARTER 10

EJ-1D' FE-1D' 'DDG E3(

"Dur™ushewa ya yi akan gwuiyoyinsa, yayinda kuka da dariya suka haWe ma sa lokaci Waya, sai kuma yakai"

"hannayensa cikin bed Win ya tattaro yaran waWanda keta sharar barci abinsu, ya haWa su a ™irjinsa ya rungume kamar wani zai ™wace ma shi su, sai kuma ya shiga jero addu'o'i ya na tofesu, sannan ya shiga sumbatarsu kamar zai cinye su, bai tsagaita ba sai da Waya ya motsa ta na yamutse fuska kamar za ta yi kuka, sai ya yi saurin mayarda su ya kwantar shi kuma ya kwanta akan lallausan carpet Win da ke"

shimfiWe a ™asa ya na sakin ajiyar zuciya a jere kamar wanda ya kubto daga hannun abin cutarwa.

"Alhaji Umar kenan, shararen gogagen Wan kasuwa wanda manya-manyan ´an kasuwa, gwamnati da"

"al'umaa ke ji da shi, Alhaji Umar sanannen mutumne wanda tauraruwarsa ke haskawa da tsananin haske, haskenda ke tattare a cikin tarin ™addarorin da ya shallake kafin haskakuwarshi a sararin samaniyar duniyar kasuwanci, Alhaji Umar mutum ne wanda rayuwarshi ke cike da tari ™addararo mabanbanta, tun tasowarshi ™addara ke walagigi d rayuwarsa, amma bai sare ba wajen yin tawassali da kuma rungumar ™addarar a duk sa'ilin da ta dumfaro rayuwarshi, yakan tsaya tsayin daka wajen ™as™antar da kanshi a wajen Mahalicci me kowa kuma me komi, wanda ke aika dukkan abin da ya so ba tare da shamaki ba, manzon Allah ya yi gaskiya da ya ce a cikin wani hadisi, ""Allah ya na son bawa me"

"tsoronshi, me wadata""."

Tsoron Allah da kuma ™arfin iymani irinna Alhaji Umar sune suka taimaka ma shi wajen samun Waukaka

"a duniya, Allah ya azurtashi da tarin dukiya wacce shi kanshi bai san iya adadinta ba, sannan kuma Allah ya albarkace shi da farin jini a cikin mutane."

"˜addara Waya ce Alhaji Umar ya kasa ha™uri da dangana da ita, wacce ta ke neman zautar da shi, ya"

"rasa ´a´ansa mata har karo biyu, ba rasuwa sukai ba rasa su ya yi ta hanyar son zuciya da kwadayi irin na"

makusantanshi.

"A hankali Hajiya Sadiya ta dire tray Win da ta Wauko goran ruwa gami da cup a ™asa, sai kuma ta buWe wa"

"ta ´ar jaka ta Wauko kwalin magunguna guda biyu, ta buWe tare da ballawa ta saka a cup Win, haka sauran suma ta saka a cikin cup Win sannan ta zuba ruka kaWan ta dama kamar yanda ake bawa yara magani, bayan ta gama ta aje a gefe tare da gyara zamanta ta Wauki kan Alhaji Umar ta Waura akan cinyarta tare da share ma shi hawayen da ke ta faman silalowa daga kwarmin idonshi, a hankali ta janyo cup Win tare da bisimilla sannan ta kafashi akan busashen bakinshi wanda laSSan suka bushe kamar wanda yai sati Waya ya na tafiya ba tare da ya sha ruwa ba, buWe bakin ya yi ta juye ma shi maganin ya shanye tas, sannan ta kora mashi da ruwa me rangwamen sanyi ta gyara ma shi kwanciya akan cinyarta ta na shafa sumar kanshi a hankali, sai da ta tabbatar da barci me nauyi ya yi awon gaba da shi, sannan ta ja shi da ™arfin zuciyarta ta Waura shi akan makeken bed Win da ke Wakin ta gyara ma shi kanciya sannan ta fice"

daga Wakin.

"Wajen photon ta je ta tsaya ita ma ta na kuka me ciwo ta na shafa fuskokin yaran ta na sambatu, ta"

jima a wajen ta na kuka kamin daga bisani ta rarrashi kanta ta tashi ta koma wajen ´a´anta da ke kuka ta

"rarrashe su tare da shayar da su, kwantar da su ta yi a tsakanin ita da mijinta Alhaji Umar, ta jima a kwance ta na tunanin rayuwa, kafin daga bisani barci me nauyi ya yi awon gaba da ita."

A cikin barcinta ta yi mafarki kamar yanda ta saba aduk lokacin da takai kafaWarta ™asa da sunan yin

"barci, yauma kamar kullum."

"Zaune suke a waje Waya, cikin wani faffaWan fili me yalwar bishiyu da ciyayi, fuskokinsu na kallon juna a"

"zahiri, amma a baWini ba junansu suke kalloba ko wacensu na kallon wani abu daban, su na matu™ar kama da junansu sosai, sai de Waya ta kasance fara tas Wayar kuma me matsakaicin haske, amma baza'a kirata da ba™a ba ko wankan tarwaWa saboda tana da haske dande ba can sosaiba, Yau kuma ba kamar"

"yanda ta saba ganinsu su kaWai ba, yau su biyu ne sannan kuma mazaje guda biyu na gefen kowace."

"Da Salati ta farka kamar kullum idan ta yi mafarki, sosai yau zuciyarta ta tsinke da lamarin, sai ta ji yau"

"kaWai ta na so ta tattauna lamarin da wani, to amma kuma wani wah, waye zai dubeta da idon basira ya fuskanci abin da ta ke nufi ba tare da ya yi ma ta kallon mahaukaciya ba, amma kuma ya dace a duba lamarinan gaskiya, wannan mafarkin ta jima ta na yinshi tun shekarun baya, kuma kullum duniya ta kwanta barci sai ta yi mafarkin, ya kamata ace tasan mi wannan mafarkin nata ya ke nufi."

"Ita kaWai ta ci gaba da zancen zucin, ta na lalubawa kanta mafita, kamin daga bisani ta tsaida tunani da"

"nazarin wacce ta dace da tayi shawara da ita, tasan za ta fuskanceta kuma ta fahimceta, ba kowa ba ce"

face ´ar uwarta Asma'u.

LEGOS.

MUBEENAH.

"Yau satina biyu cif a gidan Alhaji Abdallah me gwalagwala, na murje na yi SulSul abina na ™ara zama"

"cikakkiyar budurwa duda kasancewata me ™aramim jiki da siranta, haske da she™in fatata ya sake daWuwa, ni kaina nakan zauna ina taSa fatata ina jin daWin yanda tai laushi gwanin kyau, ba™in gashin kaina wanda da™yar Mama ke gyara min shi dan sam bana son kitso, yanzu ya sake linka tsayi da ba™i saboda musamman Sulaima ke ware lokaci duk bayan kwana biyu ta gyara min shi tsab, haka nike fitowa kamar budurwar ba'indiya irin masu tashen kyawunan, yanzu kullum zaka same ni cikin ado da kwalliya, ga ™amshin tsadadun turaruka wanda Pahpah da kanshi ya bani kyautarsu, sannan yanzu na yi wani irin sabo da ´an gidan, na saki jikina da su sosai, su kuma kullum cikin yaba min suke da godiya akan yanda nike jajircewa akan Fauzan, wanda yanzu jikin na shi yai sau™i sosai, wannan zafin jikin duk babu shi, kasancewar an canza mashi Waki yanzu, da wannan damar na yi amfani wajen saka matakin tsaro daga dukanin abin cutarwa mutum ko aljan, ™ira'a nike sakawa cikin ™aramin sauti a makeken plasma da aka jingine a bangon Waki, sannan da lokacin azkar ya yi da kaina nike canza channel, hakan ya taka rawa sosai wajen dawo da hankalin su Mommy suma suka shiga neman kariyar jiki da neman tsari daga dukkanin abin halitta, duk maricen duniya zaka same su a Wakin Fauzan su na bin ™ira'ar azkar Win da ake yi a Sunnah TV, haka za ka ga kowa ya zauna yana bin ™ira'ar cikin ™aramin sauti, hatta Pahpah yakan zauna idan ya na gida shima ayi da shi, bayan angama kuma abawa ´an aiki umurnin cike wajen da kayan"

ciye-ciye mu zauna ana fira ana ciye-ciye abin gwanin burgewa.

A duk lokacin da na tsinci kaina cikin farin ciki nakan tuno rayuwata ta baya wacce da ni da dabba bamu

"da bancin, ha™i™a na yi rayuwa me cike da rashin ´anci, kyara da rashin samun sakewa a cikin gidanmu, a"

"rayuwata ta baya babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da Abba ya lakaWa min shege duka ba, sannan"

"ya bini da mugayen kalamai masu kama da ZAFIN WUTA, bani da iko da kaina sai abin da aka gindayamin, ba ni sa zaSin kaina sai wanda aka zaSamin, a wajen mutum Waya nike samun rangwame har in samu"

rarrashi da tarairayar da na rasa samu a wajen mahaifina ita ce Mama ita kaWai ce ke nuna min zallar

"soyayya wacce babu surki, takan zauna da ni domin ta ji matsalata, takan tayani Sakin ciki ko damuwa idan wani abu ya same ni, shi yasa har gobe na kasa cire tunaninta, kasa mancewa da ita, kullum sai na yi"

hawayen kewarta.

"A hankali na saukar da kaina daga kallon jikin miron da nike, cikin nutsuwa na sagala mayafin kayan da"

"na saka, sannan na zira takalmina ina sake daidaita fuskata na fice."

"Har yanzu na kasa sabawa da bugun zuciyarda nike tsintar kaina aduk lokacin da na tunkari Wakin Fauzan,"

"abu Waya ne na kasa sabawa da shi tun zuwana gidan shine, kaifafa idanuwan Fauzan bana sakewa idan ya kafe ni da su ya na kallona, shikuma muddin idanuwansa biyu to ya dinga kallona kenan kamar sabon maye, yanzu haka da nike ™o™arin shiga Wakin sai da naWanyi jimmm a bakin ™ofar tare da Waure fuska sannan na yi sallama cikin ™aramin sauti na tura kaina cikin Wakin."

"Tun sanda na tsaya jikin ™ofar ™amshin turarena ya riga ni shigowa Wakin, da sauri ya buWe idanuwanshi"

"ya na jiran ™arasowata, da yake yau tun safe da na bashi magani ban sake bi takanshi ba sai yanzu d"

nasan kowa na gidan na daf da hallara dan mu zauna kamar yanda muka saba dan gudanar da azkar.

"DaddaWar sautin muryata ne ya ratsa can cikin ™o™on kan majiyar sautin kunnuwansa, a hankali ya sauke"

"nannauyan ajiyar zuciya, wata iriyar kewar sanyin jikina na baibayeshi, sanyin da ke tattare da ni wanda ke samar ma shi da nutsuwa na mamaye Wakin."

"Kamar kullum wai ma bai amsa sallamar a fili ba, amma naga lokacin da jajayen laSSansa suka yi motsi"

"kaWan, da sauri na sauke kaina ™asa tare da ™arasawa wajen shi, ba tare da na kalleshi ba na hau haWa"

"ma shi maganin marice, bayan na gama na gyara zamana tare da fuskantar inda ya ke kwance amma fuskata na kallon gefe, na wani maze sannan na ce."

"""Magana nike so inyi da kai, amma dan hasken musulinci ka daina kallona hakanan, idan kana"

"kallona bazan iya faWin abin da nike so imfaWi ba."""

"Nai maganar ina cuWanya ´an yatsuna, amma koda kuskure ban kalli inda yake ba."

"""Ki na da kyau me fizgar hankali, bazan iya janye idanuwana akan ki ba muddin zamu kasance waje"

"Waya, kallonki na rage min zugi da raWaWin ZAFIN WUTAR da bai gama hucewa a jikina ba, please ki yarjemin kallonki a koda yaushe."""

"Yai maganar cikin salon da ke saka ni jin wani abu ya tsarga tun daga tafin ™afata har zuwa ™o™on kaina,"

"mazewa na yi na daure na hana idanuwa da ke ™o™arin bani kunya akan satar kallonshi, sannan na ce."

"""Ban san iya adadin watannin daka shafe a kwance cikin halin ciwo ba, amma kai nasan za ka iya"

"tuna lokacin, ina so in tunatar da kai yanzu Alhamdulillah ka samu sau™i sosai, sai nike ganin ya kamata ace ka fara ramakon sallolin da aka biyoka, ba dole sai ka yi kamar yanda ka saba yi abaya ba, zaka iya yi a kwance ta hanyar ayyanawa a zuciyarka, sai kaga sanadiyar sallar Allah ya sake baka lafiya"

"mawadaciya."""

"Tun da na fara magana ya kafe Wan mitsitsin bakina da kaifafan idanuwansa, ya na kallon yanda nike zaro"

"magana cikin amon da ke saukar ma shi da kasala, da wani yanayi me wuyar fassarawa."

"Bai ce komi ba amma na jiyo sautin fitar murmushinshi, sai na tsinci kaina da jin haushin shirun da ya yi"

"min, dan harga Allah da wannan kallo da yake min gwara ya dinga yimin magana, saboda ina jin daWin amon muryarsa, sannan ina tsintar kaina cikin matsanancin farin ciki aduk lokacinda ya yi min magana."

5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5Ø
Ü 5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ

LABARI ME CIKE DA

"BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, "

"KUNCIN CUZIYA, "

"SADAUKARWA, "

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.

WRITING BY

MARYAM STAR

YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR

RAYUWAR SAMHAD

DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA

AND NOW

ZAFIN WUTA

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*

THE NOBLE WRITER'S TEAM

PAID BOOK 500 ONLY

BOOK TWO

CHAPTER 11

EJ-1D' FE-1D' 'DDG E3(

"Shirun da Fauzan ya yi min ya saka na tashi tare da rufe maganin nai tafiyata nabar shi, bai san zuciya na"

"yi ba a tunaninshi wani abin zan je inyi, amma sai ya ji shiru ban dawo ba, har kowa ya hallara wajen yin azkar amma ni shiru babu ni babu alamuna, duk wanda ya zo sai ya tambayi ina naje yau ban fito ba, ko lafiya, amma sai Fauzan yai musu nuni da maganin da na kaWa na bari, har suka gama azkar aka hau hira cikin raha da mutunta juna amma bandawo ba, Sulaima har dubo Wakina ta yi danta duba ko wani abu ya"

tsaida ni amma ta je ta iske wayam babu kowa.

"Ni kuma garding Win gidan na nufa wanda ya ke a bayan Wakin Fauzan, can nai zamana ina sha™ar"

"dadaWar iskar wajen me saka nishaWi, ina zaune a wajen na ji wa ta iska me tsananin sanyi ta taso,"

lumshe ido na yi ina sha™ar iskar da kyau ina kuma ™an™ame jikina saboda sanyi.

"A hankali na shiga buWe idona amma mizan gani, sai na ganni a tsakiyar wani tan™amemen teku wanda"

"ke Wauke da ruwa masu haske farare tas gwanin sha'awa, firfito da idanuwa na yi waje ina kallon ruwa kuma ina kallon kaina asaman wani dutse da ke tsakiyar ruwan, wani irin tsoro da tashin hankali ne ya baibaye ni, kafin insan abin yi kawai naga wani abu dun™ulalle na fitowa ta ™asan ruwan da nike, a hankali abin yayo sama gaba Waya sai kuma ya shiga shimfiWe kanshi kamar tabarma, kafin in dawo daga suman mamakin da na yi sai kawai naga wani haske me fitar da tartsatsin ruwa na bayyana akan abin, kafin insan abin yi wa ta zankaWeWiyar kyakkyawar hallita fara sol ta bayyana ta cikin haske, zaunawa ta yi ta na fuskanta ta farar fuskarta faWaWe da murmushi, cikin wa ta irinyar murya me sanyin gaske ta ce"

da ni.

"""MUBEENAH!!! INA MIKI BARKA DA ZUWA FADA TA, MI KIKE SO INSAKA A KAWO MIKI, KI FAŠI"

"DUKKAN ABIN DA KIKE BU˜ATA."""

Ta yi maganar tartsatsin ruwa na fitowa daga bakinta.

"""Wa,,,,,,wah,,,,wa,,wa,, wace,,,,wacece ke!!!!!!."""

Na faWi da ™yar cikin inda-indar murya.

"""NI CE SARAUNIYA ZUBUDIYYA, ³AR SARKIN RUWA, NI ŠIN ME TAIMAKONKI CE, INDAI INA TARE S KE"

"BABU MAHALU˜IN DA ZAI CUTAR DA KE, INA BAKI KARIYA DA ˜ARFIN IKON UBANGIJI, INA TSAYA MA KI TA INDA BAKI TUNANI, NI ŠIN MAI TSANANIN TASAYINKI CE."""

"Ta faWi ta na ziro dogon farin hannunta zuwa inda nike ta shafa kaina, nan take wani irin sanyi me"

"tsayar da numfashi ya mamaye ilahirin jikina, sai na faWi a sume, lokaci Waya ruwan ya Sace Sat, hakan yayi daidai da zuwan Mommy ita da masu aiki wajen ta na kwalla min kira, Wan turus ta tsaya ganina a"

"kwance ™asa ina barci, a hankali ta du™o kaina ta na kiran sunana."

"""Mubeenah! ke Mubeenah lafiyarki ™alau kuwa da za ki zo nan ki kwanta da sanyin marice."""

"Tai maganar ta na ™o™arin Wago da ni ganin na buWe idona, ji na yi kaina yamin nauyi sosai dan haka ban"

"samu damar cewa komi ba na shiga kiciniyar mi™ewa tsaye, ganin ina tangaWi sai Mommy ta taimaka min ta Wago da ni tare da taimaka min muka bar wajen."

"Šakin Hajjo ta kai ni, sai da ta kwantar da ni akan gado ta rufamin blanked sannan ta fice ta barni."

Nannauyan barci ne ya Wauke ni wanda ban farka ba sai ana gab da tada sallar magrib.

"A hankali ya tura ™ofar Wakin jin shirun ya yi yawa, sannan ya kira wayatshi amma bai Waga ba har sau"

"biyar, tsayawa ya yi yana bin Wakin da kallo ganin yanda yaWan hargitse, ga wani wari marar dadi da ke"

"tasowa, da sauri ya ™arasa shigowa ya na faWin."

"""Innalillahi bee mi ke damunka haka, lafiya ™alau fa muka rabu."""

"Yai maganar ya na kai hannunshi jikin Al-hassan, da mugun sauri ya janye hannun jin wani irin"

"azababben zafi da ke fitowa daga jikin Hassan Win, bai daddara ba ya sake mi™a hannu da niyyar birkito da shi, amma sai ya sake jin wani irin zafi wanda yafi na farko, Wago da hannu shi ya yi yana kallon yanda nan take hannun yai jazur alamar ™onuwa, cike da firgici ya ke kallon Wan uwan nashi sannan kuma ya"

"kalli hanunshi, da wani irin gudu ya nufi wajen freezer ya buWe ya shiga jido kwalaben ruwan sanyi, Salle"

"murfin kwalaben ya shiga yi lokaci Waya ya shiga juyesu a jikin Hassan idonshi na tsiyayar hawaye, amma"

"mi lokacin da ruwan ke sauka jikin Hassan wani irin ""Cuuuuuuuuw"" kake ji kamar anzuba ruwa a tafasashen mai."

Cike dafirgici Hussain ya ja da baya ya na fashewa da kuka me tsananin ™arfi sannan ya tashi da mugun

gudu ya fice daga Wakin.

ABUJA.

"""Wannan wace iriyar rayuwace, wannan zalincin yayi yawa, rashin iymanina bai kai nanba, ya kake so"

"inyi da girman ha™™in da ke Wawainiya da ni, anya kuwa akwai sauran SirSishin imani a zuciyarka Lawal,"

"wallahi tallahi ka ji na rantse ba zan sake biye maka inyi abin da zai idasa tarwatsa Wan SirSishin farin cikin da ya ragemin ba, na gaji!!! na gaji Lawan, bazan iya ba."""

Hamsha™iyar matar ta faWi ta na jijjiga kwalar rigar mutumin da ta sha™e ta na masa magana cikin ihu

fuskarta shaSe-shaSe da hawaye.

"Wani makirin murmushi wanda ta kira da Lawan ya saki tare da kai ma ta shura da ™afa, nan take ta faWi"

"akan ™afafuwanta, du™owa ya yi tare da tallabo haSarta ya matse da ™arfi, sannan ciki sanyin sauti ya ke"

faWin.

"""Fatima Abbas, dolene ki idasa abin da aka fara da ke, idan kin san ba za ki iya ba tun farko mi yasa"

"kika fara, na daWe ina maimaita maki cewa duk wanda ya shigo wannan aiki to babu fita, matsawar kuma kika matsa akan za ki bar aikin, to kema kin san makomarki, mutuwa ita ce makomarki Fatima Abbas."" Ya faWa tare da hankaWa ta kan kujera sannan ya bita ya Wora ™afarshi Waya akan hannun kujerar fuskarshi a"

murtuke ya sake faWin.

"""Na baki awanni biyu rak, kar ki kuskura ki ™ara koda minti Waya akai, maza ki je ki haWomin waWancan"

"tsinanun ´a´an da Sadiya ta sake haifawa Umar, al™awari na yi akan muddin ina raye to jinin Sadiya da Umar ba zai taka a doran ™asa ba, sai dai idan na mutu na bar wannan duniyar, kai wallahi koda mutuwa zanyi to sai na tabbatar da naga bayan Umar da dukkan dukiyar da ya tara, wannan al™awarina ne."""

Ya faWa ya na murje yatsun hanun Fatima da ™afarshi sannan na fice ya barta a wajen.

"Wani irin kuka ta ke tare da gwara kanta da jikin ™arfen da aka dasa dan sar™afe labule, jini ne ya soma"

tsatsafowa daga goshinta amma sake gwara kan nata take ta na faWin.

"""Kaicona da wannan ™azamar rayuwar wacce na zaSawa kaina, Allah wadarar rayuwata, gashi na"

"biyewa son zuciyata nayi abin da tsawon shekaru masu yawa ya hanani sakewa, ha™i™a na aikata aikin dana sa ni wanda ya kulle ™ofofin farin cikina, Sadiya ki yafe min, ha™i™a na cutar da rayuwarki cutarwa me muni, na azabtar da ke ta hanyar bin son zuciya d kyale-kyalen duniya, Allah ka Wauki rayuwata kozan"

"huta da wannan ba™ar azabar wacce na janyowa kaina da waWannan hannuwan nawa."""

Tai maganar tana dukan kanta da hannayenta

Please Login or Register in order to submit comment