gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Uwa Ko Ukuba Complt Complete Hausa Novel by M Shakur Chapter 5 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

loves us so much, she did alot of things for us batare datama jira Baba ba, kaga she"

"bought that power bike for you rannan u were so happy, akan zancen school take takura mana ai but if"

you look at it very well is still for our own good nan gaba mune zamu ci moriyan karatun mu not her

"cikeda rigima irin na yaron da ranshi yabaci yace  tell me menene point na takuramana akan school can t she just let us be? Look at Ammi bata takurama Ya Ramla ba and still Ya Ramla graduated with a good grade second class upper, I hate wat Mom is doing to us kinsan how many times kike bani tausayi? Kinsan how many times nake shigowa this room and cry because of you? Allah sa kisami mijima that will take you far away from her ni wlh sometimes I wish Ammi ne ma Mamana not Mom! Daidai lokacin aka bugo kofan dakinsu Mom suka gani atsorace dukansu biyun suka mike tsaye Mom tashigo dakin tareda maida kofan tarufe tasaka key takalli Munir dake kallonta dudda jikinshi na rawa but yaturo baki sosai yadauke kai yaki magana itakuma Asmeey kawai saita boye abayan Munir, Mom ta kalli Munir dake kallonta tace  you feel ka girma you can talk back at me ko Munir? Okay I m here repeat everything daka"

fadi just now inba hakaba yau saidai ubanka ya haifi wani wallahi tallahi .

UWA KO UKUBA

M SHAKUR

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn

EPISODE

"Yanda muryan Mom ke amsawa a dakin har cikin y ayan hanjin cikin Asmeey takeji, duk yanda takai ga"

"tsorota saidataji no she have to help kaninta, daurewa tayi tafito daga bayan Munir ta shiga gabanshi tana maidashi bayanta ta boyeshi tama kasa kallon Mom sabida tsoro da fargaba, muryanta kaman na mai koyan magana tace  Mm& .Mom baice komiba game dake, kawai firanmu muke ko Munir Munir yaki magana kaman da gunki take magana, arude Asmeey tadan kalli Mom dake huci tace  Mom Allah baice komiba maganan mu muk& .. Tassss! Mom ta dauramata mari da saida tayi baya baya kaman zata fadi Mom ta matsar da ita gefe tana hankadata tana kalle kalle a dakin taga igiyan chajin lantern tazaroshi tazo dab da Munir dake tsaye kikam cus kawai yaji zuciyanshi yabushe yagaji da abubuwan Mom, Mom tace  I said repeat everything daka fadi kasa magana yayi jikinshi still rawa yake but yaki kallonta, Mom tadakamai tsawa tace  you called me annoying? Kana cewa Allah sa sister ka ta sami miji that will take her away from me? You wished inama wanchan matan ne maman ka? Gani nan say"

everything to my face talk tadaga wayan wutan zata zugamai da gudu Asmeey tashiga in between them

"kawai ta rungume Munir bulalan sai ajikinshi, tafashe da kuka sosai tace  Mom kiyakuri Munir is a small"

"boy he doesn t know wat he is saying, he said it amman he didn t mean it is just anger ran Mom abace sosai tace  wallahi idan baki saki yaron nan ba zan miki jina jina zan halakaki Asma u! I know kece ke koyamai mugun halin nan, saki yaron nan nace sosai Asmeey ke kuka ta kankame Munir cus tasan Mom duk sanda tayi fushi haka zata iya sumar dakai ita tasaba but not Munir, she knows yanda Munir keda jin kunya Mom tamai duka zai dingajin kunyan su Yusra da Amina, cikin muryan kuka da tausayi tace  Mom kiyakuri please, Munir tell Mommy sorry kaman bada Munir take magana ba yaki cewa uppan, Mom tawani kama rigan Asmeey tajawota Asmeey taki sakin Munir tana kuka sosai bata tabama Mom gardama hakaba sai yau kawai zuciya yakwashi Mom tashiga kaimata duka tako ina da wayan tace  zan kasheki kuwa dan ubanki Munir ko zan kasheki kuma sainaci ubansa shi kanshi Munir kokarin ture Asmeey yake dukan ya sauka akanshi taki sakinsa, Mom ta zagaya danta sami Munir Asmeey tasake zagayawa tana kareshi muryanta so weak tace  Mommy don t beat my brother please Ammi tashiga knocking kofan tana jijigawa daga waje.  Maman Aya! Maman Aya Dan Allah kiyakuri kidena dukan yaran nan da magriban nan dan Allah kekam Asmeey da muryanta ba karfi tace  apologize to Mom Munir cikin kunkuni yana nishi kaman zai fashe sabida zuciya yadaga murya yace  fisabilillahi Annabi yadaki yaranshi ne? Malam bai taba karanta mana a seera Annabi Muhammad SAW yadaki yaransa su Nana Fatima da wayan wutaba or always slapping yaransa ba, anything Mom tace muyi we do it, we obey Mom all the time why will she be beating us kullum especially you? Ke jaka ce? Are you animal dazata dinga duka all the time? We are children we make mistakes is her duty to correct us why will she be beating u and me? Why will Mom be beating me a parlor in front of su Yusra how will my younger ones respect me? I am an adult Mom saita dinga dukana, kuma ni hostel zan koma nabar mata gidan since she s an abusive mother! Lahaula wala quwata illabillahi aliyul azeem yanda maganganun Munir suka daki zuciyan Mom batasan sanda tayo kanshi ba tace  yau saina hallaka ka dan ubanka Munir cikashi Asmeey awani irin zuciye ta fizge Asmeey ta jefar saida Asmeey ta buge da bango sosai ta zube akasa Mom tadaga wayan zata kaima Munir duka yarike wayan gam cikeda zuciya hawaye na fitowa daga idanunshi sosai yana huci yana kallon Mom kaman zai rama Mom tace  au dambe zakai dani Munir?Dambe zakai dani? Fine ga bulalan zaneni tasakinmai wayan dasauri yasaki wayan akasa yana huci Mom tace  nadauka kakai matsayi yanzu since u talk back at me u can beat me eh pick that cane and beat me yaki motsi, Mom ta zubamai mari da saida yayi baya zai fadi tsabagen yanda ya shigeshi, Mom tace  wlh yau idan bakasa hannu ka dakeni ba Munir take out all this anger on me I will not leave here, baka tsaneni this much har kana cewa inama banine na haifeka ba oya beat me kokarin tashi Asmeey take tana kuka sosai tama kasa danta bugu, ganin Munir yaki komi sai huci yake yasa Mom ta fizgoshi da karfi tace  look into my eyes and beat me kaji adult Mr Munir adult, grown up saurayi Munir yaki kallon Mom, mari Mom tasake dauramai tace  fight me, daki mahaifiyarka kaji! Yunkurawa Asmeey tayi da kyar ta taso tazo wajen takama hannun Mom dake wuyan Munir tana wani irin kuka tace  Mom you re hurting his neck please kiyakuri Mommy dan Allah yanda ran Mommy ke baci batasan sanda tasaki Munir ta yankama Asmeey mari a fuska dayasa jini ya barke daga hancinta ba tace  yaushe kikai girman ki kama hannuna kirike waye ke Asma u kaskantacciya dake baya Asmeey tayi zata fadi dasauri Munir yariketa yana daga riganshi yasa asaman hancinta sai alokacin yafashe da kuka yana kallonta yace  stop involving kanki nina mata laifi not you takashe ni is not your business eh, she hates you the most so ke zatafi duka not me just like now, stay out of this Asmeeey girgizamai kai Asmeey"

tayi tace  I will always protect you zuciyan Mom na tafarfasa tace  au Allah okay then kawai ta

tsugunna tadauki wayan Asmeey zata yunkuro abunka danamiji Munir kawai yariketa gam ya kareta ya

"kankameta Mom dukansu take tako ina, ta finciko Asmeey daga jikinsa tashiga jibgarta bana wasaba Ammi kaman zata karya kofan yaran na kuka sosai, wani mahaukacin buga kofan akayi.  Salima! Chak Mom ta tsaya, cikin kakkausan murya Baba yace  kika kashemin yara wlh wlh sai anjimu dake aduniyan nan gabaki daya ba garin nan ba! Yarda wayan Mom tayi takallesu dukansu biyun sun galabaita sosai takalli Munir tace  I m not done with you tawuce kofa tabude Baba ne tsaye gaban kofan sai Ammi ga yaran suna ganin Mom dukansu harda Ramla suka boye abayan Ammi, Baba yama Mom wani kallo taki kallonshi tawuce fuuuu Baba yashiga dakin Ammi biye dashi, ganin Asmeey da Munir kawai Baba yaji kanshi yadauki zafi, ranshi yabaci sosai, Munir yakama kawai yasa ajikinshi daya fashe da kuka sosai Ammi taja Asmeey da jini kebin hancinta tace  Subhanallahi, Subhanallahi, bani ruwa Ramla abayin nan yi maza, kira Dr Alhaji Baba na rike da da Munir dashi ma ya daku amman namiji namiji ne huci kawai yake ba kuka yana kallon Asmeey dakaman numfashi na neman kufce mata, Ammi na share mata fuska Baba yamike yana daga Munir yaron yama kasa tashi da kyau Baba yarikeshi yafitar dashi yakaishi mota ya ijiye yazo shida Ammi suka dauki Asmeey suka fito da ita sukasa a mota muryanshi har baya fita sabida bacin rai yace  ki zauna da sauran yaran lemme take them to nearby hospital gyadamai kai Ammi tayi tawuce yabude baya ya zauna baya kusada Asmeey ya daura kanta kan cinyanshi driver shi ya"

shiga gaba aka jasu sai asibiti.

Mom na zaune akan daddumanta rikeda charbi wuraren 8:30 akai knocking tareda sallama aka bude

"dakin juyowa tayi wani magidanci ne dazaikai Baba manyanta yayanta ne Uwa daya uba daya dasauri ta mike dagakan dadduma tace  ah ah Yaya kaine haka bismillah zauna zauna tanunamai kujera, hannu yadaga mata yace  ba zama yakawoni ba daga asibiti nake both Munir da Asma u na admission a emergency Asmeey har drip ake samata saita gama da drip din za a sallamesu, Salima da kinsan bakison yaran nan da tun randa kika haifesu kin kashesu baki bari suyi girman nan ba su shiga ran kowaba sauke kai Mom tayi akasa, anatse Mom tace  Yaya bahaka bane nasan Baban su ne yakiraka bai tsaya yaji meya hadamu ba, Munir ne yamin rashin kunya har yana gayamin dama kishiyata ce ta haifosa bani ba, maganganu dai dayawa marasa dadi Cikin zafin rai Yaya yace  sai aka gayamiki kuma haka ake hukunta yaro? Salima Allah na jarabtan mu da yara daban daban wasu yara har tsinewa iyayensu suke idan ransu yabaci suce Allah ya isa menene menene, yaro wa axi akemai ba duka ba azamanin nan kace zaka dinga dukan d a ai zai gujemaka ne! Kinyi babban kuskure wlh kinga jikin Asmeey? Salima ko makiyinka bazaima yaranka irin dukan nan ba balle ke mahaifiyarsu eh ? Dan lumshe ido tayi tace  Yaya Asmeey ja da ni tayi na tsani na gayama yaro ga abinda nakeso ya nuna a a, kap dinsu tundaga kan yayyinsu sun sanni I hate nonsense, banson rashin d a da rashin biyayya, waye Asma u? Wacece ita dahar ta isa tacemin bazata bari na daki kanninta ba waye ita? Kaskantacciya da ita, itadin banza itadin wofi, saisa na bata kashi sabida ta shiga taitayinta next time she won t try it again shiru Yaya yayi yana kallonta tun akan Aya da Aisha Salima nada dukan yara yawanci abinda ke hadata fada da Babansu kenan, but akwai wani kalan feeling dayake kokarin yagane game da ita akan Asma u dayakasa ganewa, dan ijiyan zuciya ya sauke saikuma ya sassauta murya yace  Salima zafi da tsorata yaro bashi kesa yaro yamaka biyayya ba, wannan shawara zan baki kodai kidena takurama yaran nan kokuma ki takura musu su kangare miki"

"ki kasa lankwasa su nan gaba dan murmushi Mom tayi tace  hmmm Yaya kenan, bawai zanja dakaiba"

"ne Yaya amman wallahi tallahi ban haifi d a ko y a data isa takijin maganan ta ba kaf dinsu, yau idan"

"nadauki waya nacema ko Aya ko Aisha subar mazajensu wlh wlh Yaya saisun bari! Wai ina maka misali ne harshi Munir din dake takama da taurin kai bai isa inja layi nace kar a tsallaka ya tsallaka shi ba, balle kuma wata Asma u wacce da idanu kawai zanyi magana tasan menake nufi, Yaya na tsaya tsayin daka akan yarana su sun sanni na sansu, su gwammace dukan nan dana musu da fushina wlh, itakuma Asmeey will learn not to ever interfere nace no is no! Nace yes is yes! Na nuna banason abu dole itama taki abun! Na nuna inason abu dole tasoshi ki da ko bataso, na nuna ina fushi da Munir dole itama ta nuna tayi fushi da yaron bata nunamin kaman tafini kaunarsa ba, I will so deal with them according to laifinsu dukansu biyun! Yaya kawai ya kada kai yace  kin dauka yaran yanzu kaman na da ne? Mom tai murmushi tace  Yaya yarana kap dinsu are in my palm, a tafin hannuna suke tanuna hannunta cikeda girman kai da fadinrai tana kada kafafu tace  I control yarana however I want! Babansu Babansu ne amman su sunsan ni kaman God dinsu ne! Billahillazi zasu iya tsallake umarnin mahaifinsu amman banda tawa Yaya yace  nazo ina miki fada kinamin wayan nan maganganun Salima anatse Mom tace  Yaya I know nadakesu dayawa, raina yabaci ne, kasanni banson raini, kayakuri amman Asmeey da Munir sai sunyi dana sanin abinda sukamin yau wlh wlh! Munir will regrets everything daya gaya akaina"

"yau, Asmeey will learn not to ever yi fito na fito dani "

Tashi Yaya yayi yace  shikenan nina tafi Allah ya shiramana yaran gabaki daya  Yaya ka tsaya kaci

abinci  banci yabata amsa kai tsaye yawuce yatafi abinshi takoma kan dadduma ta zauna tacigaba da zikiri abinta ko dar babu atattare da ita.

"Wuraren 10 suka dawo gidan Munir da kanshi yafito anmai allurai an bashi magani, Baba yafito da"

"Asmeey da bata da karfi ko kadan gobe ma ance yadawo da ita asibitin yana rike da ita sukai ciki zaunar da su yayi a falo Ammi ta sauko Baba yace  kawo musu abinci suci ahankali Asmeey tace  Baba banjin yunwa Munir yace  nima haka Baba Ammi tai turus tana kallonsu wlh sun bata tausayi Baba yakalli Ammi yace  kawo musu yoghurt toh su sha babu wanda zai kwanta cikinsu ba komi acikinsu dasauri Ammi tawuce yoghurt takawo Baba ya karba yabude yabama Asmeey daya Munir daya duk suka karba kawai duk sun rike yoghurt din sun kasasha, Baba yace  nace kusha da kyar sukasha ita Asmeey just 2 sip ta iya tayi, Munir ne ya iyashan rabi Baba yakalli Ammi yace  kaita dakinsu ta chanza kayan nan ta kwanta Ammi tace  toh yadaga Munir yace  muje wucewa yayi dashi har zuwa dakin yazaunar dashi kan gado ya zauna gefenshi yace  tell me what happened? Baima Babanshi karya ba yafadi everything that happened, Baba yahade fuska yace  yaushe kadawo mara kunya Munir ban sani ba? Look at the pain kasa sister ka aciki all because of you? Mesa datana cema ka bawa Mamanka hakuri kaki? Fashewa da kuka yayi yadaura kanshi akafadan Baba, jikin Baba yayi sanyi Munir is still a child abinda yayi is just an honest mistake, yara always makes this kind of mistake, kadaki yaro zakaga yaro har azuciyanshi zai dinga cema Maman Allah ya isa, so anything da Munir yafadi bawai he meant it bane is just anger besides ba agaban Mom yafadi ba is just coincidence dataji sanda yake gayama sister maganan, kamata yayi dataji datamayi tafiyanta no need ta nuna tamaji tunda ba agabanta yafadi maganan ba but still Baba saiya shiga mai fada calmly yace  har na girma Gwaggo na dukana sabida tana kano ne gidan Baffan ku zasuzo next week salla zaka gani, amman bantabaji dama ba itane mahaifiyata ba, I know your Mom is hot tempered but she wants the best for you saisa take damunka she wants you to become one"

of the best doctor kaman Yayanku Mustapha eh? Danta mare ka gaban kannenka sai mene ba kanninka

bane? Suma ai idan ya kama zata chasasu agabanka kasan mamanka tanada fushi da zafi but she s very

sweet she can give you anything you want don t ever make that mistake kaji? Gyadamai kai yayi Baba yace  first thing tommorow morning go and apologize okay gyadamai kai yayi Baba yace  kwanta anjima katashi saikai salla kahuta yanzu yazauna kusada shi yana shafa kanshi yaron sai sauke ijiyan

zuciya yake bacci yayi gaba dashi.

"Saida Ammi tasata ta chanza kaya ta kwanta kan gado sannan takashe musu wuta tafita, shiruuu Asmeey"

"tayi gabanta sai fadi kawai yake yau ta batama Mom rai tarasa inda zatasa kanta har 1 nadare takasa bacci tanajin munsharin kowa tashi zaune tayi ahankali saikuma ta mike tana tafiya ahankali tayi wajen kofa tabude tafita da kyar take tafiya har zuwa kofan dakin Mom tabude tashiga babu kowa a falon gabanta sai fadi yake har zuwa gaban bedroom na Mom dayake arufe tai knocking tama kasa sallama jikinta yafara rawa strictly Mom tace  who is there? Kasa fadin itane cus tasan Mom zata koreta sai kawai tabude kofan Mom na zaune kan dadduma da hijabi a jikinta da charbi tazuba mata idanunta da babu glass acikinsu sabida dare gaban Asmeey yafadi sosai tasa kafa zata shigo dakin Mom tace  kada ki kuskura ki shigo dakin nan da kafafunki sai kawai Asmeey ta zube awajen kofan tai kneeling ta rushe da kuka sosai bana wasaba tace  Mom I m sorry wani kallo Mom tamata tace  kada ki kuskura ki sake kirana Mom call me Salima na is far better for me you challenged me today? You challenged my authority? Were you trying to tell me kin fini son Munir? Ke gaki big sister? I keep telling you ki tashi daga gabana ki kaki? Waye ke Husna? Guda nawa kike? Yaushe nadena miki wanka? Yaushe kika fara nono dahar zaki challenging dina? Okay now u have everything danake dashi kema kin isa kija dani right ?Girgiza kai Asmeey kawai take tana kuka, asanyaye tace  kiyakuri Mom wlh bazan karaba I will never challenge you, kene mamana I will always do as u told me, banso ki daki Munir ne saisa nakareshi, I will never challenge you duk randa zanyi ma Allah ya kasheni wani murmushi Mom tayi irin wanda kesa yaro zawo tace  Asmeey kenan Alhamdulillah I have other children masumin biyayya dajin maganata dan ke da Munir kun kini babu komi ai dama bahaushe yace haihuwa da yawa nada rana, kuje dake dashi na barwa kishiyata ku daman ai ita kukeso? Baki taba fita bakije kin mata sallama ba, most of the time she knows your need kafin ni uwarki na sani so tashi kije na yafeki na yafe dan uwanki ma nabarmata ku tahada tarike wani irin kuka Asmeey take kaman tagama kadewa a duniya zatai magana cikin kuka Mom tace  ke! Hadiye maganan tayi, Mom tanuna kanta tana buga kirjinta tace  ban haifi"

"d a ko yarda zataja dani ba, my relationship da abin da cikina ya haifa is nace kiyi kiyi ko kinaso ko bakiso, nace karkiyi karkiyi ko kinaso ko bakiso! You couldn t maitain that kinmin girman kai kinmin gardama"

"dan haka kije na yafeki yanda Asmeey ke kuka idan wani na wajen zai iya tayata sabida ban tausayi Mom tace  kin bashi listening ear sabida kema ina forcing naki kiyi karatu, kin bashi listening ear sabida indirectly he s saying everything dake zuciyanki, na tsaya akanki kinyi school nasa kinyi law, nai making sure kinyi graduating da first class yanzu kuma I m grooming you towards law school dazaki tafi so kema na takura miki ko? Girgixakai Asmeey tayi takasa magana sabida kuka Mom tace  no no no speak up ai yanzu dukanku kun sami freedom kuna iya gayamin kome kukeso, tell me Mom banso na gajeki, tell me I m forcing you! Tell me Mom I never wanted to become a lawyer tursasani kawai kike baki Asmeey tabude zatai magana Mom tace nunata da yatsa tace  kul! Cikin kausassan murya tace  stand up and leave wajen nan dagayau karna kara ganinki ko da a parlor na ne, kada ki kara shigomin side dina, kije wajen uwar dakuke craving tazama taku na barmuku ita cikin wani irin kuka Asmeey tabude baki zatai"

"magana Mom ta daka mata tsawa tace  barmin side dina kafin ranki yabaci, ke din banza! Kaskantacciya"

irinki wacece ke Asma u dazaki gwadamin kinfinison Munir get out of my site dasauri ta tashi hartana

neman fadi tabar wajen tawuce tafita takoma dakinsu ta kwanta agado sai kuka.

Da asuba da Ramla ta farka a zaune taganta idanunta sun suntum dasauri tace  Asmeey you ve been

"crying ko? Girgiza mata kai tayi, Ramla tace  dalla ya isa stop crying Mom zata sauko keda bada ke ake fadaba ke kikaficin duka sai kawai tawuce tafita but har cikin ranta batason yanda Mom kema yaranta wlh."

UWA KO UKUBA?

M SHAKUR

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn

EPISODE

Baba na falo dukansu suka shiga gaidashi yakalli Asmeey yace  meke miki ciwo yanzu? Ahankali tace

" bakomi yakalli Munir yace  kaifa ? Shima ahankali yace  bakomi Baba Baba yace  okay kuje ku gaida Maman ku tana ciki dukansu gaba daya suka wuce kitchen Mom na tsaye cikin kitchen din tana directing yan aiki duka suka shigo suna gaidata she answered dukansu banda Asmeey da Munir, tace  Ramla bring crete na egg from the store Ramla tace  to Mom tawuce store, ahankali Hamda tace  mezanyi Mom kaman bada ita ake magana ba Mom tace  Hannatu sa ruwa a doyan nan wannan yayi kadan ahankali Munir yace  Mom kiyakuri kaman bada ita sukai magana ba Mom tace  yauwa ruwan yayi hakanan hannatu daura akan wuta amma yaran nan tea kuma su Yusra Ramla tafito ta ijiye egg din Mom tace  zaki iya tafiya tawuce ta tafi su suna tsaye Mom tacigaba da abinda ke gabanta kaman bata gansu ba kusan 10min suna tsaye awajen Baba daga falo yace  Asmeey Munir kuzo nan juyawa sukayi suka fito daga dakin sukazo falo Baba yakalli Asmeey yace  jekisa kaya I will take u to hospital kafin naje aiki gyadamai kai tayi tawuce Baba yamike yawuce sama, Mom na tsaye a kitchen din wayanta yayi kara"

takalla  Ki sameni a side naki takaranta sakon Baba.

Anatse takalli Hannatu tace  cigaba ina zuwa tawuce sama falonta tashiga dakinta Baba baya ciki hakan

yasa tawuce dakinshi dake side nata tabude kofan yana zaune akan gadonshi tamaida kofa tarufe

ahankali tace  ina kwana Alhaji ranshi a masifan bace yanunata da hannu yace  Salima akan yaranan

"nan ni da ke wlh wlh zamu samu matsala zan sabamiki sosai! Yarana sune rayuwana you know that! You know how much I love yarana! Why? Akanme zaki dinga azabtar dasu? Munir namijine yanada those manly features in him Is not proper ki dinga dukansa agaban kanninsa, he s not a child he s 20yrs, akwai other ways na hukunta yara not by beating! Mesa kin cika saurin hannu? Kinga tabon da kikama Asmeey a jiki? Wat is wrong with you Salima? Mesa kin cika zafi? For God sake Asmeey is a gurl aure zatayi gidan wani zata haka kikeso aganta da tabo abaya? Me amfani kalan wannan zuciya taki?Kowa yasanki da masifa yaran gidan nan babu wanda baya tsoronki! Ki kiyayen mini yara! Ki kiyayesu! Wlh wlh duk randa kika kara daga hannu kika daki ko Asmeey ko Munir Allah sai kinga tsananin bacin rai na wlh kuwa, idan sun miki laifi give them punishment Munir zaki iya sashi share compound ya wanke all cars na gidan nan I will not talk, Asmeey ma you can give her any punishment, duk randa

Please Login or Register in order to submit comment