gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Uwa Ko Ukuba Complt Complete Hausa Novel by M Shakur Chapter 11 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu Ammi tace  Ramla kutashi kuje kuda su Nana ku jera carpet a

"tsakar gida da kayan abinci anan za aci tashi duk sukayi, Asmeey na shiga dakin hijabin ta cire ta zauna ahankali tana zare nose mask daga falo taji Gwaggo tace  kifo Asmeey an saku aiki tasan aikin already hakan yasa tadauki gyalenta na dakin blue ta yafa akai tadan zazzago dashi tafito slippers data gani so well kept anan side na chair a falon ta zura kafafunta aciki sun mata yawa Ramla dake kallonta tace  jiya da daddare saida nazo na ganki but Ya Twins bansan ko Ya Hamadi ko Hameed bane da zuciya daya Asmeey tace  maisa kwallin? Gwaggo dake zaune ta buga salati tace  Hamadi kike cewa maisa kwalli Asmeey ai gashinan yana jinki ? Dawani irin sauri daga Asmeey har Ramla suka juyo daidai yagama saukowa daga stairs gashi bakajin footstep nashi, arude tajuya zata fice gabanta na faduwa calmly yace  my flops chak Asmeey ta tsaya saita sauke kanta ta kalli kafafunta da sukai dan firit a takalmin, awani irin hankali tajaye kafafunta daga ciki sannan ta sauke kanta sadaf sadaf tafita ahaka Ramla tabita suka shiga warware carpet suna shiryawa a compound din ga pillows sun jefa anyi setting sannan suka tafi backyard su da matan yayansu nafito da abincin da aka dafa daban daban kusan 45mins aikin ya daukesu su Baba kuma an gama gasa musu some part na layyan dasukayi duk akazo aka zauna dan cin"

abinci Mama tace  bari na kira Maman su Aya .

UWA KO UKUBA?

M SHAKUR

EPISODE

KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN

SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???

JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA

GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR

JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA

CHAT ME UP DON SHIGA

wa.me/+2347012181461

EPISODE

Babu wanda yace mata wani abu ta mike ta wuce Asmeey kanta na kasa Ammi da Mamie suka shiga

"serving kowa saiga Mom tafito tareda Mama tasami waje ta zauna tana murmushi da Mama, Baba ya tsareta da idanu she never cared about family nashi bata shiga harkansu, this is the measure reason yasa ya karo aure lokacin, Gwaggo ta watsama Mom harara tace  aikin kenan bakar muguwa wani kallo Abba yamata yasa tace  ai nayi shiru uhmm tunda an hanani magana abincin kowa yakeci banda Asmeey data kasa ci sabida zuwan Mom, dan dago kanta tayi tana kallon Mom she just wish inama zata mata murmushi she loves her Mom amman Mom murmushi take da Maman su Nana, dan karkato da idanunta tayi karaf suka hada idanu da Ya Hamad dake kallonta shima bayacin abinci he s not comfortable, da sauri ta sauke kanta kasa tadebi rice takai baki kadan, Mom ta kallota ganin she s eating abinta ta dauke kai zuciyanta na radadi da suya, Ya Hamad yafara tashi kansa akasa yawuce babu wanda yamai magana yamayi kokari yau yafito cus baitaba fitowa aci abincin tareda shi ba, Gwaggo tace  makiyin abinci mai shegen zurfin ciki da rashin son jama a Ya Mustapa yakalli Asmeey yace  once you finish eating go and put ice a fuskan nan take your drugs and sleep kada kiyi komi gyadamai kai tayi"

Baba yakalleta sai kawai yadauke kai.

Tashi Mom tayi takoma ciki ganin tadena cin abincin Baba yace  jeki dauko ice din kisa saiki kwanta

"gyadama Baba kai tayi ta tashi tawuce, ice ta dauko a fridge tawuce dakin Gwaggo this time tadaura tasaka sosai tasha magani ta kwanta agadon tayi shiruuuuuu ahaka bacci yayi awon gaba da ita."

Babu wanda ya tadata bata farka ba sai around after 4 na yamma tai maza ta fada bayi takalli kumatun

"wow yadan sabe yarage ja tayo alwala tafito tayi salla azabar da la asar tayi shiru zaune kan dadduma she has lot of karatu she suppose to do tun jiya da Baba yasa tawuce wajen lalle bata kara karatu ba gashi yau ba a bari taje side dinba wat will do now? Tashi tayi tahau gadon ta kwanta bawai daman wani danna waya take ba so she s okay, tana kwancen lamo aka bude dakin dasauri takalli kofan Munir ne da"

plate na soyayyen kayan ciki da yaji a gefe tashi tayi zaune ahankali ya maida kofan yarufe yana

murmushi yace  yauwa kin tashi nazo yafi sau biyu kinata bacci Mamie tace kar atasheki maganin dakika

"sha ne, zomuci kayan ciki da zafin shi inason salla wlh yayi maganan yana zama kusa da ita kan gadon ya ijiye plate din databi da kallo saikuma ta kalleshi, her life is so dark da bataga mema takejin dadinshi ba she has typically no one, yayinta don t care about her ko Mom ne kehanasu oho, she has no friends, yanda tai shiruuu yasa Munir yace  you re worried about Mom ko ? Gyadamai kai tayi sai kawai ta matso kusada Munir ta daura kanta akan kafadanshi ahankali tafashe da kuka mara kara cus she learnt kuka mara kara sabida Mom ta hanata kar ajisu, cikin murya tace  Munir I am just tired of everything, I know ankawoni nan sabida Mom karta tabani ne but wlh I feel more worried da tashin hankali ma anan da fargaba compare to inachan side namu, I know Mom is very angry with me, I m scared Munir zuciyana is not at ease is constantly beating tunani nake ko gaishe da Mom banje nayi ba I am a bad daughter, metayi da za a ce nadawo nan? Ramla ce tayi karya akaina da batayiba da bazata dakeni ba, Mom wants wat is best for me, I just want to see Mom smile at me I feel bad anytime nasan nine da reason for her anger, I am a bad daughter Munir ahankali gudun kar ajisu Munir ya girgiza mata kai yace  you re not a bad daughter wallahi, Mom ce is a bad mother dake enjoying giving you pain, giving us pain especially you sabida taga kinada tsoro, sabida you don t speak up bakisan right naki ba, what kind of a mother ce zatama yarta irin abin nan data miki koda yes kinyi laifin da Ramla tace kinyi ne?"

"Look at you rannan salla kalli kumatunki kalli lallen ki eh? Wai tsaya Ya Asmeey bakida saurayine kicemai yafito yazo yaga Baba kiyi aure kibar gidan nan? Dago kanta Asmeey tayi ahankali ta kalleshi irin kallon wannan wace kalan maganan rashin hankali ne, dasauri Munir yace  oh no bakida shi ta inama zaki samu when Mom is in control of your life, inama take bari ki taba waya balle kiyi dawani! I ve never ever seen a Mother kaman Mom dinmu wai wat does she get by hurting you? Wani kalan tsana tamiki ne ahankali Asmeey tace  stop talking about Mom haka bata tsaneni ba nine ke mata laifi nake bata mata rai, the problem is me not Mom Allah kuwan cikeda takaici Munir yace  tayaya? How? How are you the problem Asmeey? You think abinda Mom take miki is okay? How are you the problem tell me ? Munir yafadi cikeda gardama da jin haushi, dan shiru Asmeey tayi trying to remember laifukanta chan tace  kaga nine bana gama files data bani dawuri, courses na law school datake min ban cika ganewa ba, ni Ramla tagayama namata laifi dasauri Munir yace  an so fault dinki ne you re a slow learner? Kowa da kalan brain din da Allah yamai haba mana, in the first place ma was law ever choice naki? She forced you to study law yanda Munir ke magana fuskanshi na nuna so much bitterness akan Mom saitaji kaman tana aikata wani babban zunubi ahankali tace  stop talking about Mom like this please, A mother is the best thing arayuwan d a! Kome Mom tayi mana daidai ne, stop talking about her like this kadena jin haushin Mom Munir  naji yar Mom, I just wished she appreciate wannan son dakike mata, Mtsww let s eat nidai favorite soyayyen kayan ciki nakawo mana da zafi naman ta kalla saita dauki daya tasa abaki tai shiru Munir na kallonta, he loves Asmeey, kofan tare suka taso but he loves Asmeey sama da elder sisters dinshi su Aya da Aysha, he loves Asmeey beyond words he s just being strong for her, suna tare"

bai bar dakin ba saida aka kira magrib yafita.

Tashi tayi tai magriba tana kan dadduma Mamie tashigo da plate na nama da abinci tace  Ma u yaya

"jikin da sauki? Gyadama Mamie kai tayi tai murmushi mai kyau, Mamie ta ijiye plate din takai hannunta ta shafa kumatun daya sabe, jan shima yaragu tace  tuntuni kina daki ci abinci kije ki tayani share dakina"

su Areef duk sun zubamin cincin akasa zaki iya? Dasauri ta gyadama Mamie kai dan tuntuni tagaji da

"zama without purpose, itama Mamie that s why tadan sata aikin, Mamie ta mike tace  bari na koma backyard muna chan idan kin gama kinaso kizo kizo kinji sake gyadama Mamie kai tayi tace  toh naji fita Mamie tayi daga dakin tai shiru tana kallon abinci da batada apatite na ci sai kawai ta ijiye, tashi tayi tadauki blue gyalenta ta yafa tafito babu kowa a falo store ta shiga ta dauko broom da packer tafito tawuce sama daganan bene tanajin muryan maza da dan yawa daga dakinsu Ya Hamad karasa hayowa sama tayi takalli dakinsu kofansu arufe hakan yasa tawuce dakin Mamie, ahankali tabude kofan dakin kamshi mai dadi AC ma a kunne dakin duhu banda hasken dake shigowa ta kofan data bude wanda yake na nan corridor babu any haske a dakin, normally dakin akwai switch tanan gefen kofa but yadena aiki sai switch din wajen gado haka tasaki kofan ta shigo ta ijiye broom da packer kofan ya shiga rufe kanshi kadan kadan itakuma tawuce wajen gadon daidai kofan yakarasa rufuwa kamshin dataji ajikin Ya Hamadi taji awajen amman bata kawo komiba ta mika hannu ahankali ta danna switch din wutan dakin yakawo idanunta suka sauka kan Ya Hamadi dake kwance kan gadon Mamie idanunshi a lumshe yana sanye da wata faran t-shirt na polo da wandon kayan sallanshi da alamu bacci ne yadan sace shi adakin Mamie"

yabar dakin sabida baki dan taji muryan maza datana shigowa.

Faduwa gabanta yayi dummm! Saita dan koma baya dasauri ta tsaya tana kallonshi the way he s

"sleeping peacefully, dogayen bakaken gashin idanunshi sun rufu ruff fuskanshi na sheki kaman me yin skincare, yamata wani kwarjini a idanunta kaman me, kasa koda motsi tayi sai kallon fuskanshi take kirjinta nawani irin racing kaman akwai wani abu dake kama kafafunta yana pulling nata zuwa gaban gadon, taka kafarta tashiga yi daya bayan daya tana zuwa gab da gadon ta tsaya daidai bakin gadon tana kallonshi tai shiru kaman wawiya kaman wacce is confuse akwai wani kalan abun datakeji tunda tai girma tai wayau arayuwanta kullum she s feeling tense at any moment cikin tashin hankali take da fargaba da tsoro both boko da islamiyya da gida gudun Mom tsoronta da gudun karta mata laifi, she don t know what happened yesterday was the first ever time she felt peace azuciyanta the little"

"moment that she shared with Ya Hamadi ganinshi gives her wani internal peace, tafiyan shi, maganan shi, kallonshi, duk yana sa taji wani natsuwa acikinta da bata taba sani ba akwai kalan natsuwar, tarrr Hamad ya bude idanunshi sabida kamshin bodymist nata that s so calming, it s smell s fruity with notes na amber and slight oud, hada idanu sukayi eyes nashi looks freaking wild idan yatashi daga bacci sabida kwallin he looks like wani aljanin misira da mahaukacin tsoro tajuya zata gudu karaf yakama bakin gyalenta bawai yawani rike da karfi bane hakan yasa gyalen yazame daga kanta gashinta suka wani bayyana ta tsaya chak batare data juyoba sai tahau kame kame.  Ummm Ma& Mamie tace nazo na gyara dakin su Areef sun bata bansan kana ciki ba sorry yakai kusan 5secs yana kallon bayanta which is so unlike him dan babu wata mace dayake tsayawa ya kalla arayuwanshi banda Mamin sa sannan yasaki gyalenta yatashi daga gadon ahankali yasauka yadan gyara riganshi ya saukar kasa da kyau, yasaka slippers dinshi dake wajen sannan yazo yawuce ta gefenta yafita tabi bayansa da kallo har saida yafita tawani duka tana dafa kirjinta, wat is wrong with her? Takai kusan 5mins aduke awajen sannan ta mike tsaye tawuce wajen gadon danta gyara sannan tayi shara wayanshi tagani agadon iPhone XR yar karama size na wayan, ko ita 11 pro max take amfani dashi, gently tadauki wayan, wayan kamshi, samin kanta tayi da zama abakin gadon Mamie takai wayan ahankali zuwa hancinta tana shinshinawa wayan smells exactly like him, ijiyan zuciya ta sauke wayan smells exactly like him is so calmling, vibrating wayan yayi"

hakan yasa da sauri ta sauko da wayan ta kalli screen din taga whatsapp message ne from number da

babu suna.  Please talk to me Hamadi saikuma wayan yasake vibrating another message na shigowa

"from same number  I am madly in love with you Hussain! Aneesah ce! Hakanan wani abu Asmeey taji a wuyanta why did she even carry the phone? Maisa wayanshi ba key? Maisa notification nashi aren t hidden? Vibration wayan yasake vibrating another message ya shigo  I was able to trace your house nazo ance kunzo Bauchi salla daci wuyanta yahauyi sosai tana kallon screen din kawai taga ruwa ya diga akan screen din hakan yasa da sauri takai dayan hannunta tadaura saman idanunta taji ashe kuka take daidai an bude kofan dakin dasauri ta dago kanta hada idanu sukayi da Hamad daya hade giran sama da kasa yana kallon wayansa dake hannunta da sauri ta ijiye wayan akan gado tawuce bayin Mamie da gudu ta shiga tana maida kofan tana rufewa, yadan jima tsaye awajen yana kallon kofan cus yaga hawaye kan fuskanta sannan yashigo yazo gaban gadon yadauki wayanshi yaga bata shiga wayan ba but he saw the messages shima, sake kallon bayin yayi na kusan 3secs sannan yawuce yafita yarufo kofan hakan yasa ta fito idanunta sunyi ja gadon Mamie kawai tawuce ta gyara sannan ta share dakin tass tafito da packer da broom sai sunan Aneesa ke yawo aranta kitchen ta wuce ta zubar sannan takoma daki tai sallan isha i ko ina Gwaggo take oho ita kadaice agidan su Ramla ma duk basa ta kanta toh salla ake kowa is happy wake zama adaki sai ita abincin ta dauka spoon tayi tahauci duk ranta abace yake ijiye wa tayi tadauki magungunanta dan kawai tayi bacci ta sha tarasa yanda zatayi ranta sai baci yake sai kawai taja karaman tsaki.  Aneesah sunan ma ko dadi Mtsww taja tsaki sai kawai ta kwanta har Gwaggo tashigo mutane da dama sun shigo duk taki juyowa an dauka bacci takeyi nan ko baccin bai"

dauketa ba sai around 12 nadare.

Wuraren biyar ta tashi daga bacci akan dadduma taga Gwaggo data tsareta da idanu tace  sannu tashi

kije kiyi salla Yayyinki Aya da Aysha duk sun kirani jiya da daddare amman kinyi bacci sunmin barka da salla sunce ki kirasu gyadama Gwaggo kai tayi tawuce bayi brush tayi ta dauro alwala tafito tazo gefen Gwaggo tai dalla data idar tai azkar sannan tajuyo ta kalli Gwaggo ahankali tace  ina kwana Gwaggo washe mata baki Gwaggo tayi tace  jibi yanda kika fara kumari dana dagaki daga gaban uwarki ohh wallahi Asama bakiyi dacen uwa ba sauke kanta kasa tayi tasa hannu ta dauki wayan Gwaggo dake wajen ta mike zatai kofa Gwaggo tace  wayan ne har sai kin fita murmushi tayi tabude kofan tafice

waje tafice tana dialing number Ya Aya da ringing daya taga an katse tana kira back

Wucewa tayi parking space ta boye bayan wani mota tadauki wayan kafin tai magana Ya Aya tace

" Asmeeeey wani irin Asmeey taji zuciyanta yayi she missed her sister Mom ta hanata kiransu sukuma hardly calls hawaye kawai ya sauko daga idanunta da sauri tasa hannu ta share cikin muryan dake nuna tana kuka tace  na am ina kwana shiru Aya tayi saikuma softly tace  cry cry Baby wai har yanzu bakisan kinyi girma ba shiru tasakeyi batai magana ba, dan ijiyan zuciya Aya ta sauke tace  I secretly talks to Munir and nayi magana da Mom ma tasake yin shiru sannan tace  Asmeey Mom has always been like this, Mom nada zafi and she s harsh but duk tana haka sabida mu zama wani abu ne, look at me I m a nurse today ga Ya Aysha kullum kika kunna TVC news zaki ganta, kalleki is all thanks to Mom kika gama Law at 20 yanzu sauranki Law school, look at Munir 400level Medicine Mom raised amazing kids kawai"

"dai approach nata is harsh all of us know this gyadamata kai Asmeey tayi tana kuka mara sauti, Ya Aya"

"tace  ke da Munir should stop feeling kaman Mom hates the two of you, besides the Mom dana sani"

"bata dukan daya wuce saurin kai mari idan tana koya ma karatu bakayi ba ko wani abu data saka highest ta daddakeka ajiki oh tana miki sama da haka? Lumshe idanu Asmeey tayi ita kadai tasan me Mom kemata muryanta nadan cracking sabida kuka tace  a a Aya tace  kingani ya isa stop crying ai yau zanzo Aysha ne bazata iya zuwa ba sai kun dawo daga kauye sabida sunje salla a Abuja tareda family mijinta zanzo yau murya chan kasa dake cracking tace  Ya Aya please take me with you idan zaki koma dan shiru tayi tace  tom nazo i will try again kaman yanda na sabayi but Mom bata bari let s see idan this time zata yarda gyadamata kai tayi ahankali Aya tace  kije ki gaida Mom today wat you did jiya was very wrong and tell her sorry kinji gyadama Aya kai tayi tace  tom ahankali Ya Aya tace  akwai wani abu dakikeson gayamin ? Girgiza kai tayi tace  a a ijiyan zuciya Aya tasauke tace  akwai plenty clothes dana saya miki zan kawo miki yau harda very very fine abayas masu kyau murmushi tayi tace  thank you Ya Aya nakira Ya Aysha? Ahankali tace  no you don t have to I will talk to her, okay Baby Sis bye take care ahankali tace  tom bye zare wayan tayi daga kunne ta kifa kanta akan kafafunta tana kuka but mara sauti batajin dadin rayuwanta at all duk ta tashi daga bacci she feels inama bata tashi ba tai tai bacci haka kawai sabida Mom saukan abu me taushi taji asaman hannayenta dake kan knees din hakan yasa ta dago kanta ahankali wani soft handky ne mai bala in taushi dake kamshi gashi so warm dasauri ta dago kanta bayanshi ta iya gani dan yawuce yana sanye da farin jallabiya ya sanya farin hula na kwankwasa kaji hadisi kamshin hanky kawai taji tasan Ya Hamad ne rike hanky tayi ahankali da hannayenta sannan ta matse takai saman fuskanta wani lumshe idanu tayi feeling super calm and warm dan sanyin asuba dukya hura hancinta kusan 1good minutes tana ahaka sannan tace mike tsaye tafara tafiya ahankali tawuce flat dinsu tabude kofa ta shiga duk yaran basa falo wucewa stairs tayi tana kallon side din Mom gabanta na faduwa tawuce falon Baba tai sallama tareda bude kofan, Baba na zaune tareda Abba duk suka bita da kallo tace  ina kwanan ku Baba da Abba Abba yace  Ya jikin kin tashi lpy  Alhamdulillah ta amsa kanta na kasa ahankali Baba yace  why did u come to this side ? Kanta na kasan tace  nazo na gaisheku ne Baba shiru yayi bai kara magana ba tamike tsaye tafice side din Ammi ta wuce tabude kofa sai alokacin taga duka yaran harda su Nana da Ramla duk suna wajen tayi wajensu Ramla tace  ke baccin lafiya kike tayi jiya murmushi tayi tace  maganin da Ya Mustapa yabani ne daidai Ammi tafito daga bedroom dinta tace  Ammi ina kwana Ammi tayi murmushi tace  Asmeey yaya jikin an tashi lpy ahankali tace  lafiya lau Nana ta kalla tabata wayan Gwaggo tace  tayani kaima Gwaggo tana maganan tamike tayi kofa suka bita da kallo tana bude koda daidai itama Mom na bude kofan side nata suka hada idanu ta ganta tana fitowa daga side din Ammi ta dauke kanta sai kawai tajuya"

takoma dakin tarufe kofan yanda kirjin Asmeey ke bugawa kaman zai dare.

Ahankali take tafiya tai wajen kofan ta tsaya hannuwanta na rawa takasa bude kofan handky na

hannunta ta matsa sannan taji karfi da jarumta yazo mata ta daga hannu tabude kofan ahankali tareda sallama chan kasa Mom na zaune afalonta kan dogon kujera tayi crossing kafa daya kan daya ga table gefenta da sliced fruits ke kai sai wani journal haka data rike a hannu da glasses a idanunta tana dubawa ko nuna alamun da tasan mutum na wajen batayiba maida kofan Asmeey tayi tarufe ta shigo dakin tana tafiya kaman wacce akama kaciya da kyar tazo tsakiyan dakin tana facing Mom tai kneeling ta zube guiwowi akasa ko Baba dasu Abba bata musu kalan gaisuwan nan muryanta na rawa tace  good morning Mom Idan banza tai motsi Mom ma tai motsi next page ma tabude na journal din datake karantawa

"tadauki fork na fruits taci, zuciyan Asmeey harwani girgiza yake, bakinta na rawa tace  Mom dan Allah"

"dan Allah kiyaf& .fe& min, Mommy I am sorry sake bude next page Mom tayi tadauki slice na grape"

"tasaka abaki saida ta cinye tass sannan ta sauke journal din ta ijiye akan kujera tajuyo da kanta tama Asmeey wani irin kallon kaman zatazo ta kasheta har lahira komawa baya Asmeey tayi ta jingina da kujeran wajen Mom tawani kada kafa tafara huci tadaga hannunta ta bugi kirjinta dake wani tense sound tace  ni zaki gani jiya ki zubar Asmeey! ? Dasauri Asmeey ta girgiza kanta arude tace  Mo& .. hannu Mom ta daga mata hakan yasa ta hadiye magananan, Mom tace  ni uwarki dana dauki cikinki wata tara na raineki kawowa yau zaki kalla ki zubar Asma u! Ina kwana, good morning bai hadani dake jiya ba rather you went and join my enemies Mom tayi wani dariya tana karkada kafa tana kallon Asmeey tasake dukan kirji da karfin gaske tace  Asam u dangin Babanki da kikasan basa sona da akwai yanda zasuyi tundaga kan makiran tsohuwar dayake kira da uwarsa da yayinsa Abubakar da shi dayan Kawu da munafukar matarsa maman doctor da tuni sun fitar da ni, mutum daya ke sona kap dangin su itace Maman su Nana amman shine kikaje cikinsu aka rikeki ana kula da ke ana baki magani an saki cikinsu ana gulma dake, opportunity da basu samu jikin yarana na amana Aya da Aysha shine yanzu ke sun samu ajikinki, ubanki ma ya jonasu yau rana na biyu bai kulani ba baikuma shigo dakina ba hmmmm tasake murmushi tana kada kafafu tace  wallahi wallahi kome zakuyi saidai kuyi kinga gidan nan zama daram banga uban daya isa ya fitar dani ba wlh nasha karfinku gabaki daya ai ba tun yau akeso a kadani ba tun kafin ahaifeki to nasha karfinku kinganni nan nan gani nan bari, dake da su kuma karo wasu su jona

Please Login or Register in order to submit comment