You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanta ba,
duk lokaci bayan lokaci sai ya saka an masa bincike
akan zuwan su saraniya Lashmin sansanin uwar
dodani.
A yanzu yana zaune a cikin turakarsa ya zuba
tagumi yana cikin tunani kawai sai ya ji ana
qwanqasa qofar, nan ya bada izinin shigowa kawai
sai ganin Bokakuljabu ya shigo fuska a haxe ganin
haka sai sarki Dambola ya miqe cikin hanzari yana
dubansa cikin hanzari yace masa “Lafiya kuwa ya
kai dirka Hindu?”
97

Sarauniyar daji

Boka kuljabu ya girgiza kai yace masa “Ina
lafiya yanzu ina bincike a cikin qwarya tsafi ya
bayyanar mun cewar su Sarauniya Lashmin da
xanka Ashtar sun nufi sansanin uwar Dodani domin
xauko takobin su sarki Amjadu” Sarki Dambola ya
taqarqare ya qwala ihu wanda yasa sassan ginin
gidan soma girgiza jama’ar cikin gidan suka ruxe
suka soma guje-guje cikin firgici yana sauke wani
huci na fusata yace wa Boka kuljabu.
“Mene yanzu mafita?” Boka Kuljabu ya amsa
masa da cewar.
“Mafita xaya ce shi ne mu haxa runduna mu nufi
can sansanin Uwar Dodani mu jira su, idan sun
samu nasara sun xauko takobin sai mu taresu mu
qwace, mu yanki gashin kanta sai ka halakar da ita”
Jin wannan shawarar sai sarki Dambola ya yi na’am
da wannan shawarar take ya baiwa Boka Kuljabu
uwarnin aje a haxa runduna ta zaratan mayaqa
domin yin hawa zuwa ga sansanin Uwar Dodani.
Boka Kuljabu ya amsa cikin girmamawa ya fita
yana mai motsa hannun qarfensa.
Shima sarki Dambola ya soma shirin yaqi shima.
Ba a fi mintina talatinta ya fito cikin shigar yaqi ai
kuwa yana fitowa qofar fada sai ya tarar da runduna
zaratan mayaqa sun haxu baka jin komai sai iface98

Sarauniyar daji

iface da ihun sadaukai. Boka kuljabu ya matso
gaban sarki Dambola ya yi gaisuwa, daga nan sarki
Dambola ya bada izinin tafiya nan take dakaru suka
juya suka xauki hanyar zuwa sansanin uwar Dodani.
**
A lokacin da aljanin daya xauko su Sarauniya
Lashmin zuwa sansanin Uwar Dodani, sai ya
kasance yana tafiya cikin azama baya yada ko zango,
bayan ya shafe aqala awani shida yana wannan
tafiyar sai ya soma rage gudu a sararin samaniya,
sannu a hankali kuma ya soma yo qasa har ya sauko
da akan wani dutse dake tsakiyar daji.
Suna sauka akan dotsen sarauniya Lashmin ta
gane ko wanne dotse ne kuma a wanne daji suke,
nan take suka dirgo daga bayan aljanin suna ma su
gyara makamansu, Yarima Ashtar ya dubi Sarauniya
Lashmin fuskarsa cike da mamakin yadda aka yi
tunda suka soma tafiyar nan har suka sauko ba tare
data cira kai ta dube shi ba.
Yana shirin buxe baki ya yi mata Magana sai
yaga ta suri makamanta ta soma gangarowa daga
saman dutsen zuwa qasa, ya bi bayanta da kallo cike
da mamaki kafin shima ya bi bayanta. Suna
gangarowa qasa suka yi arba da wani katafaren gida
wanda aka yi sa da baqaqen duwatsu suka tsaya
99

Sarauniyar daji

suna kallon ginin cike da mamaki zuwa wani xan
lokaci sai kawai Yarima Ashtar gani ya yi Sarauniya
Lashmin ta kutsa kai cikin gidan.
Lokacin da sarauniya Lashmin ta kutsa kai
izzuwa cikin wannan gida tana shiga sai tayi arba da
wasu irin macizai masu kauri kamar bishiyar kuka.
ai suma macizan suna ganinsa sai suma suka taso
musu lokaci guda da zumar su turmushe su kowanne
ya yagi rabonsa.
Ba tare da fargaba komai ba Sarauniya Lashmin
da Yarima Ashtar suka tunkari macizan har ya
zamana cewar tsakaninsu da su bai wuce taku uku
ba, sai macizan suka kewaye su suka saka su a
tsakiya kamar an ajiye qwayar gero a tsakiyar gona,
nan take suka wangame bakuna suka kawo musu
sara.
Wohoho! Nan fa sarauniya Lashmin ta daka wani
wawan tsalle kamar an janyeta da majajjawa sai gata
ta dirge akan xaya daga cikin macizan, kafin tayi
yunquri tuni sarauniya Lashmin ta caka takobinta a
tsakiyar kanta. Tana zare takobin sai ga jini ya yi
fitar burtu kamar an fasa qatuwar randa wacce take
cike da ruwa, nan take macijiyar ta sulale qasa
matacciya, kafin ta qarasa qasa tuni ta sake daka
tsalle ta dirge akan wata itama ta hallakata.
100

Sarauniyar daji

Haka shima Yarima Ashtar ya shiga wasa da
makami a tsakiyar waxannan macizan kawai sai dai
kaga rabin jikin macijiya ya tashi sama, kafin ya
faxo qasa yana tsartuwar kakkauran jini.
Haka dai Sarauniya Lashmin ta riqa tsalle tana
dira akan macizai tana kashe su cikin matsanaicin
zafin nama na ban mamaki, kafin cikar daqiqa xari
shida da tamanin har sun gama kashe gaba xaya
macizan sun zama gawa, jini kuwa ya riqa Malala
da gudu a cikin xakin. Sai wannan lokacin ta xaga
kai ta dubi Yarima Ashtar suka haxa ido na xan
taqin lokaci kafin ta juya ta nufi wata qofa dake
fuskarta ta, tana zuwa ta turata ba tare da fargaba ko
tsoron komai ba ta sa kai cikin xakin, shima Yarima
Ashtar ya biyo bayanta, suna shiga cikin xakin sai
suka cika da mamaki suka kama kalle-kalle tamkar
xan qauye ya shigo birni.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsintar
kansu da suka yi a cikin wani qaton birni mai yawan
dogayen gidaje masu benaye hawa-hawa shi dai
wannan birni cike yake da mutane kala-kala, wato
jinsi-jinsi wasu farare, wasu baqaqe, babban abinda
ya xaurewa su sarauniya Lashmin kai shi ne gaba
xaya waxannan mutane suna ta aikin wahala ne iriniri wasu qere-qere suke yi, wasu kayan amfanin
101

Sarauniyar daji

gona suke gyarawa suna zubawa a cikin buhuna
suna xinkewa. Waxansu aikin fasa duwatsu, wasu
gini, wasu haqa ramuka kai a taqaice kowa da irin
aikin da yake yi kuma mazansu da mata yara da
manya a cikin wannan halin hidimar suke.
Koda shigowar sarauniya Lashmin da Yarima
Ashtar cikin wannan birni sai suka zamo abin kallo
ana al’ajabinsu tamkar waxannan mutanen ba su
tava ganin baqi ba, babban abinda ya ba su mamaki
duk da mutanen suna kallonsu amman ba su fasa ci
gaba da aikinsu ba, kuma aiki suke yi tuquru tamkar
akwai dakaru a tsaye akan su suna bugunsu alhalin
babu kowa, duk wanda su Sarauniya Lashmin suka
nufa da zumar yi masa Magana sai suga ya sunkuyar
da kansa qasa ya ci gaba da aikinsa ya daina
kallonsu.
Cikin mamaki sarauniya Lashmin ta dubi Yarima
Ashtar tace “Me ka fahimta a wannan lamarin?”
koda jin haka sai Yarima Ashtar ya saukar da ajiyar
zuciyta yace.
“Ni abinda na fahimta shi ne waxannan mutanen
gaba xayansu fursunoni ne kuma aikin dole suke yi
anan don babu yadda za su yi kuma ga dukkan
alamu a matuqar tsorace suke amma me zai hana mu
tambayi xaya daga cikinsu mu ji abinda ke faruwa
102

Sarauniyar daji

tunda waqa tafi daxi a bakin mai ita” koda jin haka
sai Sarauniya Lashmin ta tunkari wata tsohowa
ramammiya wacce da qyar take dakon qasa a kanta
tana kaiwa cikin wani rami mai faxi da zurfi tana
zubawa, koda tsohuwar taga sarauniya Lashmin ta
durfafeta kai tsaye sai jikinta ya kama karkarwa,
fuskarta ta sauya launi izuwa tsananin tsoro tamkar
za ta fashe da kuka, al’amarin daya baiwa su Yarima
Ashtar mamaki amman duk da haka sai suka qarasa
koda suka je sai sarauniya Lashmin tace da ita
“Yake wannan tsohuwar ina dalilin wannan aikin
wahalar da kuke ta faman yi haka?”
Maimakon tsohuwar ta buxe baki tace wani abu
kawai sai ta turnuqe da matsanancin tari, tun tana
tsaye bisa qafafunta sai da ta durqusa qasa bisa
guiwoyinta, kawai kuma sai ta kama aman jini, cikin
hanzari sarauniya Lashmin ta ruga ga tsohuwar
domin kai mata agajin gagawa kafin ta isa inda
tsohuwar take durqushe tuni tsohuwar ta vingire
qasa ta zama gawa. Al’amarin da ya firgita su
Sarauniya Lashmin Kenan taja da baya kafin ta dubi
Yarima Ashtar tace masa “Haqiqa ba shi da amfani
mu sake yiwa wani Magana, tabbas wannan duk
shirin su Boka kuljabu ne, don haka mu ci gaba da
tafiya har mu qarasa wajen da kabarin mahaifina
103

Sarauniyar daji

yake mu ciro takubban su” Tan agama faxin haka
sai suka qara kunna kai cikin garin.
Lokacin da suka yi nisa a cikin gari suka iso wata
unguwa inda basu ga ko mutum xaya ba a waje.
Duk da cewar da tsakar rana ne, unguwar ta yi tsit
tamkar babu wani mahaluki a cikinta, gaba xaya
gidajen unguwar a rufe suke tamkar wata masifa ce
a waje wadda ta hana kowa fitowa. Al’amarin daya
qara ba su mamaki suka tsaya cak a waje xaya suna
nazarin unguwar. Gaba xaya gidajen unguwar iri
xaya ne, kuma girmansu da tsawon su iri xaya ne,
bayan sarauniya Lashmin da Yarima Ashtar sun xan
jima a tsaye suna nazarin unguwar sai Ashtar yace.
“Yanzu mene abin yi?” Ta kallesa tace masa.
“Ai bamu da wani abin yi face mu shiga cikin
gidajen nan xaya bayan xaya muga a wanne ne
kabarin mahaifina yake” Yarima ya gyaxa kai
alamar gamsuwa.
“Amman abinda nake gani wanda zai sauqaqa
mana wahala shi ne ko wanne mun sai ya shiga gida
guda xaya, hakan zai saka mu yi saurin duba
gidajen” Koda jin wannan shawara sai Sarauniya
Lashmin ta aminta da ita kai tsaye ita ta nufi gida na
farko shi kuma Yarima Ashtar ya nufi gida na biyu.

104

Sarauniyar daji

Sarauniya Lashmin tana zuwa qofar gida na
farko koda zuwa sai ta saka qafarta ta banke qofar
gidan duk da qofar ta kasance qatuwa mai kaurin
gaske sai da ta jijjige ta rufta ta faxi qasa, nan take
ta kuna kai cikin gidan ba tare da shakkar komai ba.
Da shigarta cikin gidan sai ta tsaya cak ta kama
kalle-kalle kuma taji kamar ta juyo da baya amma
saboda dakakkiyar zuciya irin ta sadaukai sai tsaya.
Abu na farko daya soma yiwa sarauniya Lashmin
marhabin da shiga gidan ba komai bane sai wani irin
gurnani mai yawan gaske mai amo da cika dodon
kunne wanda ta kasa tantancewa na dabbane ko na
dodani. Da farko gidan dumxum yake da duhu ta
cikin duhunne wannan gurnani ke fitowa daga can
kuma sai gidan ya gauraye da haske na ban mamaki
sai ga waxansu irin kuraye manya-manya sun yiwa
Sarauniya Lashmin qawanya.
Tunda sarauniya Lashmin ta zo duniya bata tava
ganin kuraye irin waxannan ba, girman ko wacce
xaya daga cikin kurayen ya kai a cure giwa guda
biyu a waje guda,duk wacce ta wangame bakinta
kuwa sai kaga kamar qofar bakin gari aka buxe.
Nan fa kurayen suka fara zazzaro harsunansu
waje yana kwanciya a qas tamkar an shimfixa
doguwar darduma mai faxi, ya yin da saraniya
105

Sarauniyar daji

Lashmin taga waxannan kurayen suna matsowa
gareta sai itama ta falfala da wani azababen gudu
kansu, tana zuwa ta daka tsalle sama kamar
tsuntsuwa ta soma kai musu sara da zumar raba
gangar jikinsu da kawunansu amma bisa ga
mamakinta duk kurar data sara sai ta ga ko gezau
bata yi, gaba xaya ma sai suka tsaya cak! Tana
saransu amman kamar susa take yi musu, faruwar
hakan shi ya tabbatar mata lallai makami ba zai tava
tasiri akan waxannan tsafafun kurayen ba don haka
sai ta mayar da makaminta.
Ai koda faruwar haka sai wata kura ta zaburo
kanta baki buxe, tana zuwa sarauniya Lashmin tayi
wuf ta cafi bakinta nan take ta vara kan kura gida
biyu tayi jifa da gawarta, nan ta hausu da duka da
naushi tana sura qafafun wasu tana bugu da su, duk
wacce tayiwa naushi xaya sai kaji qarar karyewar
qashin jikinta ta sulale qasa matacciya.
Kafin wani lokaci babu kura ko xaya dake
numfashi duka ta mayar da su gawarwaki. Ta
duduba ko ina a cikin gidan bataga kabarin
mahaifinta ba don haka sai ta juya ta fito daga cikin
gidan.

106

Sarauniyar daji

Shi kuma lamarin Yarima Ashtar lokacin daya
shiga cikin gida na biyu, yana shiga sai yaja ya tsaya
turus! Ba komai ne ya saka haka ba face arba da ya
yi da wasu girqa-girqa qanti su sama da hamsin
kowannensu babu komai a jikinsu face warki wanda
ya rufe al’aurarsu kuma dukkansu suna riqe da
muggan makamai iri-iri wasu takubba wasu
majaujawa wasu gatari kai wasu makaman ma
mutum bait ava jin irin su ba.
Su waxannan samarin sun kasance dogaye masu
tsawo gami da kauri kuma suna da qwanji manyamanya tamkar ginasu aka yi da qasa, kallo xaya
mutum zai yi musu ya tabbatar suna da qarfi. Ba
tare da shakkar komai ba sai Yarima Ashtar ya zare
takobinsa ya shige cikin gidan yana mai ratsa
tsakiyar waxannan qartin yana kallonsu ta cikin
wutsiyar idanu yana jiran kawai yaga wani daga
cikinsu ya yunquro, haka ta ci gaba da ratsawa ta
tsakiyar waxannan qarti su ba su afka ma ta ba,
itama ba ta afka musu ba har dai ta iso tsakiyarsu.
Kawai sai ji ya yi wani abu mai nauyi ya daki
bayansa ya tafi taga-taga kamar zai faxi amman ya
daure lokaci guda ya juyo ya kalli wanda ya daki
bayansa, cikin tsananin fushi lokaci guda ya yi
xauki akansa suma suka taso masa suka yi masa
107

Sarauniyar daji

rufdugu aka garqame da azababben yaqi. Wahoho!
Idan jarumtaka ta haxu da sadaukantaka dole ne a ga
abin al’ajabi, duk da cewar sarkin yawa yafi sarkin
qarfi amma sai Yarima Ashtar ya zama tamkar wani
shaixani a tsakiyar waxannan qarti domin an rasa
koda mutum xaya wanda zai koda lakaci jikinsa,
amman babban abinda ya tayarwa da Yarima Ashtar
hankali duk lokacin daya sari jikin waxannan qartin
sai dai kawai yaga qura ta tashi daga jikinsu ko
qwarzane ba sa yi. Don haka sai Yarima Ashtar ya
mayar da makaminsa cikin gidansa ya gyara
tsayuwa ya fuskance su sosai nan suka kacame da
wani azababben dambe da kokawa suna dukanshi
yana dukansu.
Duk wanda Yarima Ashtar ya nausa sai ya karya
masa qashin baya ko na wuya, nan fa ya shiga
karkarya su wani ya karya masa qafafu wani hanaye,
kafin wani lokaci gaba xaya ya karairaya su ya
barsu kwance suna iface-iface na wahala nan ya
tsallake su ya fito abinsa ai koda fitowarsa sai ya
iske itama Sarauniya Lashmin ta fito daga cikin
xakin data shiga na farko kallo xaya ya yi mata ya
san ba qaramin fafatawa ta yi ba.
Ya matsa gareta yana shirin yi mata Magana
kawai sai ganin tsohon mutum wanda shekarunsa
108

Sarauniyar daji

sun haura xari yana sanye da waxansu yagaggun
tufafi na qasqanci qafarsa ko takalmi babu, yana da
sanqo a kansa xan ragowar gashin da yake kansa da
saje duka sun zama fari fat, tsohon yana dogara
sanda yana tafiya da qyar kamar zai faxi domin
qafafunsa karkarwa suke yi basa iya xaukar nauyin
jikinsa koda Sarauniya Lashmin ta yiwa tsohon
kyakkyawan kallo sai ta kauda kai ta nufi qofar gida
na uku zata shiga, bisa ga mamakinta sai taji tsohon
ya yi mata Magana yace.
“Dakata ‘yan mata kar ki shiga cikin wannan
gidan?” Jin haka sai mamaki ya kamata su duka
suka tsaya suna dubansa kafin suka qarasa garesa
“Me yasa kace kar na shiga wannan gidan? Kuma
me yasa kai kayi mana Magana shin kai baka tsoron
Uwar Dodani?” Tsohon ya yi murmushi yace musu.
“Me yasa zan ji tsoronta alhalin ina tare da
ubangijin musulunci a cikin zuciyata, kawai nasan
Allah ya jarrabeni ne da zama qarqashin uqubarta
amman sababin kuvuta ta yana nan zuwa, yanzu
kam na yi Imani kune za ku kuvutar da ni. Don haka
kuyi sani cewar abinda kuke nema baya cikin
wannan gidan na uku yana cikin gida na huxu anan
za ku riski uwar dodani tana gadin kabarin
mahafinki samun nasarar ku akan wannan muguwar
109

Sarauniyar daji

matsafiyar uwar Dodani mu kuma shi ne zai kuvutar
da ni da jama’ata daga wannan azabar da uqubar da
muka shiga ta dalilin savawa ubangijin.
Jama’ar qasata sun shagala ga barin sallah da
azumi da sauran ibada, suka kasance basu da aiki sai
caca da zinace-zinace, don haka wani shaihun
mallami ya kasance dare da rana yana yi musu
wa’azi amman suka qi ji. Qarshe suka yi masa kora
wulaqanci lokacin daya tashi barin qasar sai ya yi
wa jama’ar qasar addu’ar kasancewa cikin uquba da
bauta a qarqashin wata matsafiya kuma ba za mu
tava kuvuta ba har sai ranar da wani saurayi da
budurwa sun zo xaukar takobin mahaifinsu dake
jikin kabari a soke. Tun daga wannan lokacin muka
samu kamu cikin bauta ga uwar Dodani har zuwa
yau xinan” Koda jin wannan lamari sai mamaki ya
kama su Sarauniya Lashmin nan dai suka yiwa
tsohonan godiya suka nufi gida na huxu.
Suna zuwa suka samu qofar gidan a buxe, cikin
jarumtaka suka kutsa kai cikinsa ai kuwa suna shiga
sai suka samu wata jibgegiyar halitta mafi muni a
cikin duk abubuwan da suka tava gani na halite, ita
dai uwar Dodani hannunta guda huxu ne haka kuma
rabinta yafi kama da bil’adama haka rabinta kuma

110

Sarauniyar daji

kamar doki haka take, koda ganinsu sai suka tsaya
suka yi carko-carko kamar zakaru suna duban juna.
Ba tare da Uwar dodani tace musu komai ba ta
zaburo kansu cikin tsananin fusata baki a buxe
dalala yana zubar da yawo, ganin haka suma suka
taso mata takubban su a zare, nan suka kacame da
wani azababben yaqi amman abinda ya ba su
mamaki koda suka sara mata takubban su gaba xaya
sai suka karkarye suka zube a qasa.
Faruwar haka ya saka uwar dodani bushewa da
wata irin dariya mai amsa amo wacce ta cika musu
dodon kunuwa, nan ta sake zaborowa kansu tana
zuwa ta saka hannunta ta make Yarima Ashtar
kamar an xauki karmami haka ya tafi ya gwari da
wata dirka ta gini ya baje a qasa yana numfashi
xaixai.
Ganin abinda uwar dodani ta yi wa Yarima
Ashtar ya saka sarauniya Lashmin ta yi xauki kanta
da wata fusata, tana qarasawa kanta tayi tsalle sama
kamar an jefa mashi da zumar xane kanta, amman
kafin ta qarasa tuni ta saka hannuwanta guda huxu
ta cafeta, lokaci guda ta matsata da hannuwa guda
uku ta soma yi mata rufdugun duka da hannu xaya
kafin wani lokaci tuni ta jigata sarauniya Lashmin
da dukan da take mata ta ko wanne vari.
111

Sarauniyar daji

Ganin irin dukan da take yi mata yasa, Yarima
Ashtar ya soma waige-waige a cikin xakin ko zai
gano wani abinda zai yi amfani da shi, ai kuwa sai
idanunsa suka kai kan kabarin sarkin Amjadu da
matarsa Rasina, yaga takubban da suka zo nema
suna soke a jikin kabarin, nan fa cikin fushi na
fusata ya tunkari wajen yana zuwa kan kabarin sarki
Amjadu ya saka hannuwansa duka biyu ya zaro
takobin, ai faruwar haka keda wuya sai suka ji wata
maxaukakiyar qara ta cika ilahirin gidan take uwar
dodani ta jiyu kansa a fusace.
Amman ta rigaya ta Makara domin tun daga nesa
Yarima Ashtar ya daka wani tsalle sama, ya kai
mata sara a hannun da take riqe da sarauniya
Lashmin take ya sare hannun ya faxo qasa yana
tsartuwar jini.
Ganin haka yasa Sarauniya Lashmin itama ta
miqe cikin azama itama ta zaro takobin mahaifiyarta
tayi xauki kan uwar dodani. Suna zuwa Yarima
Ashtar ya kai mata sara ta qasa take ya guntule mata
qafafunta, uwar dodani ta saki wata razananiyar
qara ta yi qasa luuu da zumar faxuwa kafin ta
qarasa faxuwa Sarauniya Lashmin ta saka takobi ta
sare mata kai.

112

Sarauniyar daji

Nan jini ya soma gudana da vulvula ta gurbin da
suka sare suka tsaya suna maida numfashi na huce
gajiya. Sarauniya Lashmin ta kalli Yarima Ashtar
tace masa.
“Zama ba namu bane domin akwai sauran aiki a
gabanmu” Ya gyaxa mata kai.
“Duk yadda kika ce haka za ai” Nan take suka
fito daga cikin gidan da zumar kama hanyar zuwa
birnin Hindu. Ai kuwa kamar daman su Boka
Kuljabu da Sarki Dambola jiransu suke suna fitowa
su kuma suna qarasowa nan fa aka tsaya aka yi
carko-carko ana duban juna, bayan wani lokaci kafin
Boka Kuljabu ya zaburo ya fito yana dubansu kafin
yace musu.
“Ya ke qasqantacciya ki yi sani cewar tabbas yau
xinan sarki Dambola zai samu damar cika burinsa
na kawo qarshen zuri’arku a duniya. Domin a yau
xinan zai kashe ki ya kuma cika yi hawa zuwa ga
qasarki ya rusheta kamar yadda ya aikata a waccan
lokacin” Koda jin haka sai sarauniya Lashmin ta yi
murmushi cikin xaga murya tace masa.
“Ai kun riga kunyi sake xan zaki ya girma,
tabbas lokacin qirga adadin numfashinku ya yi,
xayanku baya barin wajenan a raye face ya zama
gawa. Ina so ka sanar da wannan tsohon azzalumin
113

Sarauniyar daji

wanda zalluncinsa bai bar xansa na cikinsa ba, ka
shaida masa cewar idan har ya cika sadauki to ya
fito muyi gaba da gaba da shi duk wanda ya yi
nasara akan wani shi Kenan ya halaka shi” Koda jin
abinda tace sai sarki Dambola ya zaburo tsakiyar fili
yana gurnani kamar wani mayuwanci zaki yace
mata.
“Ahir xinki yarinya, tabbas yau kin taro ruwan
dafa kanki, domin ba zan gushe daga wajenan ba sai
na kawo qarshen zuri’arku” Jin haka kafin
Sarauniya Lashmin tayi Magana sai Yarima Ashtar
ya yi caraf yace.
“Ai zallunci baya tava nasara akan adalci, don
haka idan hark a yadda za ka yi gaba da gaba da
Sarauniyar Daji, to nima na amince zan yi gaba da
gaba da wannan tsohon munafikin bokan naka”
Koda Boka kuljabu ya ji haka sai ya xaga hannun
qarfensa sama yana murmushi tare da faxi a cikin
ransa yauce ranar xaukan fansa na, yauce nake da
damar da zan rama abinda sarki Dambola ya aikata
mun, tabbas idan na kashe Yarima Ashtar duk da
sarki Dambola baya qaunarsa amman zai ji zafi a
cikin zuciyarsa tunda jininka naka ne.
“Na amince da buqatarka” Ya amsa cikin hanzari
sarki Dambola ya dube shi kamar zai yi Magana
114

Sarauniyar daji

amman kafin yace wani abu tuni Boka kuljabu ya yi
fitar burtu ya yi xauki kan Yarima Ashtar. Nan fa
suka cure da wani azababen yaqi, tabbas gwanigwani ne nan fa suka riqa nuna salo-salo na bajinta
da nuna sadaukanta kala-kala sai da suka xauki
tsawon mintina talatin ba tare da wani ya samu koda
damar tava jikin xan uwansa da makami ba.
A vangaren su sarki Dambola da Sarauniya
Lashmin suma haka lamarin ya kasance, domin
tunda suka ruga da gudu kan juna, suka gauraya da
azababben yaqi, sai ya zamana suna kai sara da suka
da bugu da qafafunsu. Wani salon faxa suke mai
ban mamaki. Haka suka tafiyar da tsayin lokaci suna
wannan gabzawa zuwa wani lokaci can sai
sarauniya Lashmin ta shammace shi ta kai masa
wani sara da zummar sare masa kai ya yi zafin nama
domin gocewa amman ya makara domin sai da saran
ya same shi a ido take ya tsiyaye xaya idon nan fa
sarki Dambola ya shiga ruxani ya qwala wani ihu a
cikin razana.
Ya yadda takobin ya dafe idon cikin tsananin
ruxani, duhu ya mamaye masa ganinsa idon qarfen
ya ci gaba da wulqitawa shi xaya. Nan ya qara sura
takobinsa ya soma kai sara da suka ba tare daya san
115

Sarauniyar daji

wanda yake kaiwa sara ba. Koda gimbiya Lashmin
ta fahimci haka sai ta soma tsalle-tsalle a sama ta
sauya wani salon faxan, can ta qara saka takobi ta
sare masa hannunsa na hagu nan ya sake wata qara,
kafin ya rufe bakinsa ya sare xaya hannun na dama
dake riqe da takobinsa Boka Dambola ya rikice ya
gigice.
Ya zube a qasa yana ihu da hargowa wannan
ihun nasa ya saka Boka kuljabu dakatawa da yaqi ya
juyo domin ganin abinda yake faruwa ga Sarki
Dambola wannan juyowar da ya yi kafin ya qara
juyowa ga Yarima Ashtar sai jin sukar takobi a
qirjinsa ya yi kafin ya saki numfashi tuni Yarima
Ashtar ya soke shi a jikin wata bishiya, sai
qafafunsa ne suke reto nan take jini ya soma
malalowa Boka Kuljabu ya ci gaba da ihu yana
qoqarin zare takobin amman ya kasa, haka ya ci
gaba da wutsul-wutsul har ya zama gawa.
Sarki Dambola ya zube qasa yana gurnani, na
azaba jini ya ci gaba da fitowa daga gundulmin
hannunsa. Sarauniya Lashmin ta tsaya akan sa tana
kallonsa cikin isa tace masa.

116

Sarauniyar daji

“Yau shi ne qarshen zalluncinka, za ka mutu ba
tare da burinka ya cika ba” Ya yi wani gunji na
azaba kafin yace mata.
“Yarinya ko yanzu ai burina ya cika na bar miki
tabon da ba za ki tava mantawa da shi ba” Sarauniya
Lashmin ta yi dariya kafin tace masa.
“Amman kuma ai zan dawo da zuri’armu ta
tsatsonka, domin ni da xanka Yarima Ashtar za mu
yi aure kuma za mu samar da zuri’a mai yawa
waxanda za su zama mashahurai a duniya, shin a
cikin mafarkinka baka ga haka ba?”
Sarki Dambola yace “Kar ki kashe ni, Xana
Yarima Ashtar ka nema mun afuwa a gareta bana
son mutuwa” Yarima Ashtar ya girgiza kai.
“Ka cancanci mutuwa, wannan shi ne qarshen
zallunci” Yana maganar hawaye suna zubowa daga
idanunsa.
Sarauniya Lashmin ta dube shi sai taji tausayinsa
ya kamata, amman data tunano irin kisan gillan da
ya yiwa iyayenta sai ta xaga takobinta da duka
qarfinta ta soka masa ita a qirjinsa, sarki Dambola
ya saki wata qara ta azabar fitar rai nan ya zube
yana shure-shure har sai daya zama gawa.
Daga nan suka haqa musu kabari suka jefa su a
ciki. Yarima Ashtar ya xauki takobin mahaifinsa ya
117

Sarauniyar daji

tsaya akan kabarin sannan yace masa “Ni ne
mamalakin wannan takobin taka” Ya juya ya
miqawa Sarauniya Lashmin takobin mahaifinta.
Lokacin data amsa ta haxasu waje xaya sai hawaye
suka soma zubo mata.
Ganin wannan al’amarin daya faru duka dakarun
sarki Dambola suka zube a gaban su Sarauniya
Lashmin suna ma su yi mata mubaya’a. daga nan su
duka suka xunguma zuwa qasar Hindu. Bayan sun
qarasa an nutsa sosai an huta aka tura su sarkin yaqi
Amjan suka taho tare da mahaifiyar Yarima Ashtar.
Koda suka qaraso nan gari ya kacame da bushebushe da kaxe-kaxe na nuna murna da burin
taryarsu aka kwana ana shagali. Don haka sai
sarauniyar Daji ta nemi ganawa da su Yarima Ashtar
da sarkin yaqi Amjan da mahaifiyar Ashtar bayan
sun zauna sai sarauniya Lashmin ta numfasa tace.
“Abinda yasa na kirawo ku shi ne domin na sanar
da ku cewar na yanke shawarar zan naxa Yarima
Ashtar sarautar birnin Hindu ya kasance ya gaji
mahaifinsa sarki Dambola, ni kuma da jama’ata za
mu koma zuwa tsohon birni wanda iyayena suka
gina za mu gyara shi mu ci gaba da gudanar da
mulki” Koda Yarima Ashtar ya ji haka sai ya miqe
118

Sarauniyar daji

cikin azama yana duban Gimbiya Lashmin yace
mata.
“Ni bana buqatar na zama sarki, don haka ki zavi
wani tsakanin sarkin yaqi Amjan da kuma
mahaifiyata, ni na fi son na kasance dake a duk
wajen da kike a halin farin ciki ko na baqin ciki” Jin
haka sai mahaifiyarsa ta yi murmushi ganin haka sai
sarauniya lashmin ta dubeta tace mata.
“Me ya sa naga wannan murmushin a fuskarki
alhalin ban tava ganin irinsa ya bayyana a gareki
ba?” Mahaifiyar Yarima Ashtar ta sauke ajiyar
zuciya tace mata.
“Yanzu ne na samu qwarin guiwar lallai burin da
mahaifinki ya mutu akai zai cika a wannan lokacin
domin kuwa xana Yarima Ashtar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment