You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Sarauniyar daji

SARAUNIYAR

DAJI

ABDULAZIZ SANI MADAKIN GINI
07064081880

1

Sarauniyar daji

SARAUNIYAR DAJI
Haqqin mallaka (H) M. Kwalisa
Shekarar bugu:- 2022
Shekarar bugu na biyu:-2023
Bugu na uku:- 2024
GARGAI
Ba a aminta wani mutum, ko wani kamfani ya
sarafa wannan littafin wajen juya shi ta hanyar
wasan kwaikwayo ba tare da neman izinin
marubucin ba.

2

Sarauniyar daji

SARAUNIYAR DAJI
ABDUL-AZIZ SANI

3

MADAKIN-GINI

Sarauniyar daji

SARAUNIYAR DAJI

R

ana na daf da faxuwa, mutane na ta
qoqarin haxa kayayyakinsu a cikin
qaramar kasuwar garin, shi dai wannan
garin wani yankine dake sashin qasar
Hindu da ake kira Mawardi.

Gaba xaya mutane garin ba su wuce mutum
xari uku ba mazan su da matansu, dukkanin
jama’ar wannan gari sun kasance mafarauta don
haka ba su da wata sana’a wacce tafi farauta.
Gaba xaya dazuzukan dake cikin wannan yanki
na su sun laqance su ainun kamar yadda suka
laqanci sana’arsu.
Asalin mutanen garin mawardi basa zama a
waje xaya ko da yaushe a cikin yawon daji suke
suna shiryawa kansu gasa ta farauta kala-kala,
duk wanda aka shiryawa gasa shi za a tattarawa
duka dukiyar da aka samu a dajin a bashi
wakilcin siyar da ita a can babbar kasuwa ta

4

Sarauniyar daji

cikin birnin Hindu don haka duk ribar da aka
samu sai kason shi yafi na kowa yawa.
Mutanen qabilar mawardi sun kasance ‘yan
kaxan a qasar ta Hindu kuma suna da sa’a da
nasibi a duk abinda suka sa a gabansu shi yasa
suka fi sauran qabilun nasibi a kasuwanci siyar
da fatun dabobbin daji da kuma duk wani
vangare na sassan jikin dabobbi da ake buqata
don yin magani ko tsafi hakan yasa arziqin
mutanen ya riqa havaka kuma a dalilin hane yasa
suka kafa wani gari a wannnan yanki dake can
bayan birnin Hindu suka daina nisanta kansu da
birnin sosai.
Ko shekara ba su yi da kafa wannan gari na
mawardi ba sai fatake da attajirai manya ‘yan
kasuwa suka mayar da garin babbar cibiyar ta
kasuwanci fatu dabobbi daji, ya zamana anata
gine-ginen manya gidaje kuma ana qawata shi da
abubuwa irin na zamanin waccan zamanin.
Sarkin wannan garin na mawardi ya kasance
matashi wanda shekarunsa ba su wuce arba’in ba,
kuma ya gaji sarautarne a wajen mahaifinsa yana
da matan aure guda xaya me suna Rasina kuma

5

Sarauniyar daji

suna da ‘ya guda xaya ‘yar shekara bakwai ana
kiranta da Lashmin.
Tun Lashmin bata wuce shekaru huxu a
duniya ba mahaifinta ya fara koya mata yadda
ake yin farauta a daji, kuma ya rinqa bata horo
na jarumtaka da cire mata tsoron daji da duk irin
hatsarin da take cikinsa, ai kuwa tana cika
shekara bakwai ta rinqa yin abubuwan ban
al’ajabi wanda shi kansa mahaifinta bai tava yin
kamarsa ba a lokacin da yake da shekarunta
kamar nata. Tana da shekara bakwai take
sulalewa ta shiga daji ita xaya tana yin farauta,
sai dai aganta ta dawo janye da matacciyar
damusa ko vauna wacce ta kashe da hannnunta
tun tana yin farautar yini xaya har ya zamana
cewar tana iya shafe kwanaki uku ita kaxai a
cikin daji tana yin farauta kuma ta dawo gida
cikin qoshin lafiya.
Koda mahaifin Lashmin ya sami labarinn irin
gagarumar bajintar da take yi sai ya qaryata
al’amarin ya buqaci da su tafi daji tare shi da ita
domin idanunsa su ga yadda take yin tatta
farautar.

6

Sarauniyar daji

Bisa wannan shirin su uku wato har da
mahaifiyarta suka xauki guzuri suka hau
dawakai guda uku suka fice daga cikin garin
mawardi suka nausa cikin daji cikin nishaxi da
farinciki.
***
A can Babban Birni Hindu kuwa sarkin da
yake mulki a wannan lokacin ya kasance
qasurgumin azzalumi ana kiransa da suna
Danbola.
Sarki Dambola ya kasance kamar annoba a
qasar gaba xaya domin kuwa hatta manyan
fadawansa tsoronsa su kaji saboda a su kansu
baya xaya musu qafa wajen karva harajinsu
kuma idan kana da mace me kyau da zarar ya
qyallara ido ya ganta zai qwaceta. Idan kuma ka
yi qoqaron hanashi ita zai kashe ka ne ya gaje
komai naka. Hakane ya saka sarki Dambora ya
tara matan aure har xari da sittin da uku.
Wani babban abin mamaki shi ne duk yawan
waxannan mata mace xaya ce jal ta haihu da shi,
itace uwar gidansa wacce aka yi musu auren
saurayi da budurwa ana kiranta da sunan shanina.

7

Sarauniyar daji

Abinda shanina ta haifa xan shekara goma sha
xaya ana kiransa da suna Ashtar.
Barewa bata gudu xanta ya yi rarrafe, sarki
Dambola ya kasance gawurtaccen jarumi wanda
ya yi shuhura a qasar Hindu gaba xaya, bai gaji
sarautaba da qarfin tsiya ya kashe sarkin dake
kan karagar ya karvi sarautar alhalin ya kasance
xan bawa.
Ashtar ya gado mahaifinsa a vangaren
jarumtaka sosai amma kuma ko kaxan shi baya
zallunci kuma baya son zallunci hakane ya janyo
rashin shaquwa a tsakaninsa da sarki Dambola
harma ya daina janshi a jikinsa.
Kisa qwace ba komai bane a wajen sarki
Danbola amma Ashtar ya tsani hakan idan ma
yaga sarki Danbola ya aikata irin wannan
zallunci sai ya yi ta kuka, koda sarki yaga cewar
Ashtar yana da raunin zuciya sai ya hanashi
zuwa fada kuma ya aiyana a ranshi cewar bashi
da magaji.
Wata rana da daddare sarki Dambola na
kwance a cikin turakarsa shi kaxai yana bacci,
sai ya farka a firgice cikin tsananin ximauta, nan

8

Sarauniyar daji

fa ya miqe tsaye ya koma kai kawo a cikin
alamun tsananin tashin hankali, al’amarin da ya
janyo bacci ya qauracewa idanunsa kenan haka
dai ya kasance zaune ko tsaye har gari ya waye.
Da sassafe tun kafin rana ta fito sarki
Dambola ya tura aka kirawo babban bokan qasar
Hindu wanda ake kira da suna Kuljaru. Boka
Kuljaru ya amsa kira ya bayyana a gidan sarauta
aka yi masa iso izuwa wani babban xaki inda
sarki Dambola yake ganawar sirri da manya
mutane masu daraja.
Lokacin da sarki Dambola da Boka kaljaru
suk kaxaita sai sarki ya buxe baki da nufin ya yi
magana amma sai kaljaru ya xaga masa hannu
ya tsaida shi sannan ya dube shi a cikin nutsuwa
yace.
“Ya kai sarki mai daraja ta xaya ka yi sani
cewar tuni nasan abinda kake so ka sanar dani,
jiya ka yi mafarki a cikin mafarkin naka kaga
wata bishiya mai qafafu kuma rasa bishiyar
hannaye ne da yawa haka ne?” Sarki Dambola
ya jinjina kai alamar haka ne Boka karjalu yaci

9

Sarauniyar daji

gaba da cewar “Wannan bishiyar ta ratso har
cikin wanna birni namu ta kashe gaba xatan
mayaqanmu kuma ta riske ka har cikin turakarka
ta tsire maka reshe a cikin jikinka ya volo ta
gadon bayanka ka zamo gawa haka ne?” Sarki
Dambola ya sake amsawa da haka ne duk abinda
ka faxa haka na gani shin wannan mafarki zai
faru ne a gaske?”
Boka kurjalu ya yi shiru kuma ya miqe tsaye
ya yi ‘yar tafiya taku uku sannan ya juyo ya dubi
sarki Dambola yace.
“Tabbas babu makawa sai wannan al’amari
ya faru a gaske, idan kuma bai faru ba to ka
xauki matakin yanke wannan bishiyar da take
tofowa a yanzu uma ka qoneta qurmus yadda ba
zata ci gaba da rayuwaba” Koda jin wannan batu
sai sarki Dambola ya miqe tsaye zumbur cikin
tsananin fushi har fuskarsa ta kama yin gatsine
ya dubi Boka kurjalu yace.
“A ina wannan bishiyar take naje duk inda
take na sassarata gunduwa-gunduwa kuma na
saka a qoneta qurmus sai ta zama toka” Boka
kurjalu ya yi ajiyar zuciya yace “Ita wannan

10

Sarauniyar daji

bishiyar ta kasance mutum kamarka. Yarinyace
qarama wacce ba tafi shekara bakwai ba a
duniya, yanzu haka tana iya shiga daji tayi
farauta ta kwana uku kuma komai hatsarin dabba
tana iya yin gumurzu da ita kuma ta samu
nasarar kasheta saboda ta kasance basaudaukiya
kuma jarumar gaske” Sarki Dambola ya tari
numfashi Boka karjalu a lokacin da jikinsa ya
kama tsuma ya xaga murya yana mai cewa.
“A ina wannan yarinya take ka faxa mun
yanzu naje na qarar da duka zuri’arta da
qabilarta gaba xaya” Boka qarjalu yace ‘Ai ba a
nesa suke da kai ba, tana cikin qabilar mawardi
waxannan tsirarun mutanen da suka gina
birninsu a yamma da wannan birni namu sunan
yarinya Lashmin kuma ta kasance ‘ya ga
sarkinsu Amjadu, idan har ka bari wannan
yarinya ta girma har ta cika shekara goma sha
takwas to zata zama sarauniyar dukanin
dazuzukan dake cikin wannan qasa tamu to daga
nan ne kuma za ta yi harin karagarka zata shigo
har cikin gari ta ci mu da yaqi kamar yadda ka
gani a mafarki”Koda Boka Karjalu ya zo nan a

11

Sarauniyar daji

maganarsa sai Sarki Dambola ya bushe da
dariyar mugunta sannan ya dubi Boka Karjalu
yace “Haba ya kai abin dogaron Hindu ta yaya
zan bari wannan abin kunya ya riskeni shin ka
mance cewar gaba xayan mutanen garin
mawardi basu wuce su xari uku ba, na rantse da
kabarin babana a yau xinan zan kashe gaba gaba
xayan mutanen garin mawardi mazansu da
matansu sannan nasa a qone komai na garin har
sai ya zama to9ka kai ko ciyawar garin ba zan
bari ta sake tofowa ba”.
Nan take sarki Dambola ya yi shirin yaqi ya
xebi wasu zaqwaquran mayaqansa guda dubu
xaya suka xebi makamai suka hau dawakai suka
nufi hanyar da zata kaisu can birnin na mawardi
kai kace yaqi za su yi da wata babbar qasa.
**
A can birnin na Mawarda kuma rana na shirin
faxuwa mutane na ta harhaxa kayansu a cikin
kasuwa domin komawa gidajensu. Baqin ‘yan
kasuwa kuma waxanda su ka zo daga sauran
biranen qasar Hindu tuni sun haxa na su ya nasu
sun soma fita daga cikin gari a wannan lokacin

12

Sarauniyar daji

sarki Dambola da dakarunsa su ka zo bakin
qofar birnin mawardi, suna zuwa bakin qofar sai
ma su kwari da bakansu suka harbe ma su gadin
qofar garin ko da ganin haka sai jama’a suka
saka ihu aka hau guje-guje.
Kaico!Nan fa aka soma qurewa mutane gudu
ana soke su ana saransu suka riqa zubewa qasa
matattu. Ihun mutane ya cika wajen jini ya riqa
falatsi da kwarara a qasa abin takaici kan mai
uwa da wabi suke yi babu qaramin yaro babu
mace, kai idan aka sari mace xauke da goyo a
bayanta tana zuwa qasa sai kawai a saka mashi a
soke jaririn nata shima ya zama gawa.
A can qarshen mawarda jama’a ba su san
abinda yake faruwa ba, kuma gashi a wannan
lokacin sarki Amjadu tare da mai xakinsa da
kuma Lashmin sun yi nisa a cikin daji domin yin
farauta.
A daidai lokacin sarki Dambola suka isa
tsakiyar garin suna ta kashe mutane, sai ihun
mutane ya yawaita haniniyar dawakai da qarar
makamai sai cika kunen jama’a sautin yaqi ya
cika garin sai a lokacin kowa ya farga da abinda

13

Sarauniyar daji

yake faruwa, kowa ya shiga ximuwa mazaje
dake cikin jarumta suka soma xauko makamai
domin maida raddi domin su kare birninsu,
amma da yake sarkin yawa yafi sarkin qarfi sai
qoqarinsu ya zama mara amfani domin karkaxe
su ake yi kamar ana jijiga reshen bishiya busasun
ganyayen dake kai na zubowa.
Sai da aka kashe gaba xaya jama’ar qasar
mawardi ya zamnana sai wani jarumi guda xaya
jal ya tsira da rayuwarsa. Shi dai wannan
matashin sunan shi Aryan kuma ya kasance qani
ga sarki Amjadu uwa xaya uba xaya.
Aryan gwarzon jarumine sosai me dakakkiyar
zuciya kuma Allah yah ore masa baiwa ta qarfin
gudu. Ko da doki ya kasa tsere sai ya bashi rata
me yawan gaske shi kadai ne yake da irin
wannan baiwa ta gudu na ban al’ajabi a cikin
jaruman birnin mawardi.
Lokacin da su sarki Dambola suka shigo cikin
garin mawardi Aryan na can qarshen gari yana
wanka a cikin wata qorama, kawai sai ya fara
jiyo ihun mutane daga can cikin gari, da gudu
Aryan ya fito daga cikin qoramar ya yi sauri ya

14

Sarauniyar daji

saka tufafinsa ya xauki makamansa na yaqi ya
falfala da azababban gudu izuwa hanyar da zata
kaishi cikin gari yana cikin wannan gudune ya yi
tirjiya hankalinsa ya tashi ainun,takaici da baqin
ciki suka kama shi bai san sanda ya soma zubar
da hawaye ba, ba komai ne ya saka shi haka ba
face hango gawarwakin mutanen garinsu birjik a
qasa, maza da mata yara da manya. Kai ko kazar
garin guda xaya bai hango a raye ba, kawai sai
yaga tawagar sarki Dambola sun nufo wajensa
sarki Dambola da Boka Kurjalu ne a gaba bisa
dawakai, koda suka hango shi tsaye can nesa da
su sai sarki Dambola ya zubi wasu zaratan
jarumai wanxanda suke bisa wasu qosassun
dawakai na musamman yace musu “Ku ruga ku
yiwa waccan jarumin kisan wulaqanci ku ciro
kansa ku kawo min nan”Dakaru huxu suka risina
suka ce an gama ya sarkin Indiya nan take
dakaru huxun suka zaburi dawakansu suka nufi
wajen da jarumi Aryan yake tsaye koda yaga sun
nufo wajen da yake sai ya juya da gudu ya
falfala da azababen gudu izuwa cikin daji nan fa
suka kasa tsere sai gashi xan hakkin da suka

15

Sarauniyar daji

raina ya tsone musu ido duk da cewar dawakan
nasu na musamman ne da su ma ake gasar tseren
gudu a qasar indiya sai gashi mutum ya fisu
kaifin gudu al’amarin da yai matuqar xaure
musu kai Kenan amma sai suka ci gaba da bin
jarumi Aryan domin su cimmasa har suka sake
yin nisa a cikin daji.
Al’amarin su sarki Dambola kuwa lokacin da
suka ga zaqaquran mayaqansu guda huxu sun bi
jarumi Aryan da gudu izuwa can cikin daji har
sun vace musu da gani sai suka yada zango a
wajen domin su jira su ga dawowar dakarun
huxu xauke da kan jarumi Aryan. Cikin sauri
aka kafawa sarki Dambola tanti suka shiga ciki
shi da boka kurjala suka zauna a ciki aka kawo
musu ruwa suka sha. A sannan ne sarki Dambola
ya dubi Boka yace masa.
“Ya kai dirka mutanen Hindu shin ka mance
ne mun zo kasha yarinyar dana gani a cikin
mafarkina, gashi mun kashe gaba xaya munaten
garin kuma na lura da duka gawarwakin mutanen

16

Sarauniyar daji

banga sifar yarinyar daka siffanta mun ba”Koda
jin haka sai Boka kurjalu ya numfasa yace.
“Ai kuwa ni na yi kuskure ni ya kamata tun
farkon zuwa garin na yi bincike na gano inda
yarinyar take mu risketa mu gama da ita amma
sai kawai muka kama kashesu. Yanzu dai mu jira
dawowar su sadauki Darwaz su kawo mana kan
wannan jarumin me gudun tsiya sai mu bincika
mu gani ko yarinyar da muka zo dominta tana
raye ko ta mutu” sai sarki Dambola yace “A’a a
bari ya huce shi yake kawo rabon wani, maza ka
duba ma halin da yarinya take ciki yanzu-yanzu
nan”Boka kurjalu yace.
“An gama ya shugabana” Nan take ya xauko
wani madubinsa na tsafi ya karanta wasu
xalasimai ya tofa ya shafe shi kawai sai suka
hango sarki Amjadu tare da matarsa da yarinya
Lashmin a cikin wani daji suna farauta. A
lokacin yarinya Lashmin tana riqe da wasu
wuqaqe a hannunta tayi gaba da gaba da wata
murgujejiyar kura suna kallon-kallo sarki
Amjadu da matarsa suna tsaye nesa kaxan a
bayan wata bishiya suna kallo su ga irin

17

Sarauniyar daji

gumurzun da za’ayi a tsakanin kurar da ‘yarsu
Lashmin, kamar haxin baki sai kura da Lashmin
suka zaburo a lokaci guda izuwa kan junansu.
Saura taku biyar su haxu sai kura ta daka tsalle a
sama bakinta a buxe ta kawowa Lashmin
wawura. A cikin baqin zafin nama itama lashmin
ta daka tsalle sama kamar daga cikin baka aka
harbota, cikin zafin nama lashmin ta wurqila
jikinta kamar katantanwa ta haye samanta ta
luma mata wuqaqe guda biyu a cikin
kunnuwanta, wuqaqen suka lume a cikin
kunnuwan kurar a lokacin da suka yo qasa tim!
Sai ga lashmin ta yi zaman dirshan akan gawar
kurar.
Boka kurjalu ya shafi madubi hoton komai ya
vace, sarki Dambola kuwa ya miqe tsaye cikin
fusata yace “Ashe ma aikin banza muka yi da
muka kashe gaba xaya mutanen garin mawardi
tunda bamu kashe gimbiya lashmin ba, maza
muje wannan dajin inda suke”Kafin sarki
Dambola ya rufe baki sai suka hango dawakan
dakaru sadauki Darwaz guda huxu sun nufo
garesu suna xauke da gawarwakin, al’amarin

18

Sarauniyar daji

daya matuqar girgiza su kuma ya basu mamaki,
boka kuljalu ya shiga gaban dawakan yana xaga
musu hannu sai daya rage sauran taku xaya tak
dawakan suka tsaya cak, dakarun dake can nesa
suka qaraso da gudu suka dudduba gawarwakin
sai suka ga Darwaz ne kawai bai qarasa mutuwa
ba, amma yana gargara mutuwa cikin hanzari
suka xauko shi suka kawo gaban sarki Dambola
suka ajiye shi yana numfashi da qyar sarki
Dambola ya dube shi a fusace yace.
“Ta yaya ku huxu kuka kasa kasha wannan
yaron me azababban gudu alhalin kuna kan
dawakai na musamman” Sadauki Darwaz ya
dubi sarki Dambola yana mai buxe baki da qyar
yace “Ya shigabana a iya rayuwata da dukkanin
yaqe-yaqen da naje ban tava haxuwa da jarumi
mai zafin nama kamar wannan magujin da muka
bi ba, saboda zafin namansa da muka ga
dawakanmu sun kasa sai muka harba masa
kibiyoyi, amma ba tare daya waigo ba sai kawai
muka ga ya zuro hannuwansa biyu baya yana
café kibiyoyin da muka harba masa yana
zubarwa a qasa, har da kibiyoyin namu suka

19

Sarauniyar daji

qare gaba xaya koda yaga mun daina harba masa
sai ya fahimci sun qare, kawai sai ya tsaya cak
ya juya ya fuskance mu, koda muka ga haka sai
mu duka huxu muka zare takubbanmu muka
qarawa dawakanmu qaimi muka durfafeshi
sauran taku kaxan mu haxu da shi, sai kawai
muka ga ya dako tsalle sama kamar tsuntsu, a
sama ya yi shawagi akanmu kamar fuka-fuki ne
a jikinsa ya kaftawa ko wannen mu mummunan
sara a jikinsa ya dira bisa qafafunsa ya juyar da
dawakanmu muna kai suka dawo da baya zuwa
nan da muke”Darwaz na gama faxin haka sai
numfashinsa ya sarqe idanuwanshi suka qafe ya
zama gawa. Koda ganin haka sai sarki Dambola
ya daddage ya qwala wani uban ihu cikin
tsananin baqin ciki ya dubi Boka karjalu yace.
“Daga nan zuwa wajen da su sarki Amjadu
suke mene ne nisan tazararsa?” Boka kurjalu
yace “Ba zai wuce tafiyar awani shida ba” yace
“Kenan sai dare ya tsalla sosai za mu riskesu,
shin baka ganin za su baro dajin da suke yanzu
su dawo izuwa birninsu?” Boka kurjalu yace.

20

Sarauniyar daji

“Ai dole su yi qoqarin dawowa gida kafin
wata safiyar ta riskesu” Sarki Dambola yace ‘Mu
yi gaba mu riskesu ba zan iya jiran dawowarsu
ba, kwanciyar hankalina kawai naga na kashe
gimbiya lashmin tun yanzu zuciyata ta fara
tafarfasa tunda gashi an kasha mini zaqaquran
mayaqana guda huxu, a maimaikon jinin ko
wanne a cikinsu sai na zubar da jinin mutum
dubu a qasar nan maza ayi sabon shiri na tunkara
su Gimbiya lashmin yanzu nan”Kafin sarki
Dambola ya rufe baki tuni dakaru sun soma
tattara kaya domin ci gaba da tafiya.
Wannan shi ne abinda ya faru ga rundunar
yaqi ta sarki Dambola bayan sun kashe gaba
xaya qabilar mawardi ya rage sauran mutum
huxu kacal wato sarki Amjadu sai matarsa
Rasina da ‘yarsa Gimbiya Lashmin sai kuma
jarumi Aryan.
A can daji da su sarki Amjadu suke yin
farauta kuwa bayan jaruma lashmin ta kashe
wannan qatuwar kura sai farin ciki ya kama sarki
Amjadu ya durqusa bisa guiwarsa guda biyu ya

21

Sarauniyar daji

buxe hannayensa yana yiwa lashmin murmushi,
lashmin ta ruga da gudu izuwa gareshi ta faxa
kan qirjinsa ta rungume shi tana dariya, kafin ta
janye jikinta daga nasa tace “Ya kai Abbana shin
yanzu ka gamsu na gajeka a jarumtaka?”Amjadu
yace “Qwarai kuwa ‘yata kinma fini domin ni
banyi irin abinda kika yi ba a lokacin da ina da
shekaru kamarki, don haka ina son ki jajirce
wajen baiwa jama’armu kariya kuma kiyi musu
mulki na adalci bayan raina, duk wuya duk rintsi
kar ki bari qabilarmu ta gushe a bayan qasa. Idan
kika ga sarki Hindu zai cutar da su kiyi yunqurin
janye jiki daga cikin gari ku koma cikin daji ku
ci gaba da rayuwa har ki zamo sarauniyar daji ta
dukkanin dazuzzukan dake cikin qasarnan, ina
mai tabbatar miki indai a cikin dajin zaku yi
rayuwarku to babu yadda za’ayi wani sarki ko
wasu mayaqa su iya ganin qarshenku. Gargaxin
da zanyi miki na qarshe kar ki kuskura kice zaki
yaqi sarkin qasar Hindu a yanzu face sai kin cika
shekara goma sha takwas a duniya”Gama faxin
haka ke da wuya sai suka jiyo takun sawun
mutum a bayansu an tunkaro wajen da suke da

22

Sarauniyar daji

gudu, cikin hanzari sarki Amjadu da Rasina da
Lashmin suka zare makamansu suna jira suga
wanda zai bayyana.
Kawai sai suka ga jarumi Aryan ne,Aryan ya
qaraso garesu cikin tsananin jigata yana uban
haki kamar ransa zai fita ya kife qasa a gabansu.
Abinda ya yi matuqar dugunzuma hankalinsu
Kenan su duka, sarki Amjadu ya yi saurin
sunkuyawa ya tashe shi zaune.Rasina tayi saurin
ta xauko ruwa ta baiwa Aryan yasha xan kaxan
sannan ya dawo cikin hayyacinsa.
Sarki Amjadu ya dubeshi cikin nutsuwa yace
“Ya kai sarkin yaqin mawardi bani labarin
menene ya faru tabbas duk abinda ya koro vera
daga rami ya faxa wuta to yafi wutar zafi.
Tabbas abinda ya saka gudu ba qaramin bala’i
bane a iya sanina da kai daga quruciya zuwa
yanzu baka tava juyawa musifa baya ba sai dai
masifa ta juya ta gudu ta barka” Aryan ya buxe
baki da qyar yace.
“Ya shugabana mu gudu mu bar wannan
dajin mu tafi wani daji can nesa sa qasar Hindu,
idan ba haka ba kuma qabilarmu za su gushe a

23

Sarauniyar daji

doron qasa yaddda ba za a sake tunawa da mu
ba” Sa’ar da sarki Amjadu, Rasina da Lashmin
suka ji wannan batu sai hankalinsu ya sake
dugunzuma fiye da ko yaushe Amjan yaci gaba
da Magana “Duka jama’armu sun mutu tabbas
sarki Dambola da dakarunsa sun kawo mana
harin mamayar bazato”Koda sarki Amjadu yaji
haka sai ya kurma uban ihu kuma ya fashe da
matsanancin kuka na baqin ciki, nan take Rasina
da lashmin suka rungume shi suka kama yin
kukan.
Sai da suka shafe kusan sa’a guda suna yin
wannan kuka sannan suka yi shuru sarki Amjadu
ya miqe tsaye ya dubi gabas da yamma, kudu da
arewa sannan ya dubi Aryan yace “Kai da matata
da gimbiya lashmin ku qara gaba daganan kada
ku tsaya anan har sai kun dangana da bakin
iyakar qasar Hindu da birnin kanad”Koda jin
haka sai hankalin Rasina dana Gimbiya Lashmin
ya tashi Rasina ta dube shit ace.
“Ya za ai mu tafi mu barka anan dajin muyi
gaba alhalin munsa cewar ga maqiyanmu nan
zuwa gareka, ai gwara mu tsaya da kai mu yaqi

24

Sarauniyar daji

abokan gaba idan ya so mu mutu tare da kai,
wannan shi ne abin alfaharinmu” Sarki Amjadu
ya girgiza kai yace.
“Ku mutu tare dani ba shi ne abin alfahariba.
Babban abin alfahari shi ne ku tabbatar cewar
qabilarmu ta ci gaba da wanzuwa a duniya ba a
shafe tarihinta ba, ku sani lokacin dana zama
sarki mawardi na xauki alqawari kuma na yi
rantsuwa da girman iyayenmu da kakaninmu
cewar zan tsare jama’a da dukkan qarfina duk
wuya duk rintsi sai dai na rayu tare da su kuma
na mutu tare da su, ni nan zan tsaya na yaqi sarki
Dambola nasan zan mutu amma kafin na mutu
na rantse da kabarin babana zan kashe mayaqa
ma su yawa na yiwa qasa ado da ajininsu”Sa’ar
da sarki Amjadu ya zo nan a maganarsa sai
matarsa Rasina ta gashe da kuka tace.
“A ranar da muka yi aure tare da kai munyi
alqawarin cewar mutuwa ce kaxai zata rabamu
da kai, ta yaya yanzu zan iya tafiya na barka
anan”Sarki Amjadu yace ‘Idan kika tsaya nan
mutuwa za ki yi ni kuma daman burina na mutu
tare da jama’ata”Rasina tace.

25

Sarauniyar daji

“Ni kaine jama’ata kaine rayuwata, kuma
kaine uwata da ubana, yanzu an kashe duka
iyayena da ‘yan uwana a wannan yaqin mamayar
bazato da aka kawo mana, kuma an kashe
dukanin daginka bamu da wani sauran dangi face
Aryan da Lashmin idan har babu kai babu wani
sauran jin daxi a rayuwar duniya farin cikina
mun bar lashmin wacce zata gaji karagarka anan
gaba, idan Aryan ya tsira zai auri wata matar nan
gaba xansa ko ‘yarsa jinin qabilar mawardi ne,
haka itama Lashmin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment