You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba zai ji
abinda za su fax aba Dambola ya dubi Kuljabu
yace masa.

51

Sarauniyar daji

“Yanzu ya Kenan za mu yi? Kasan duk
wanda ya qera waxannan abubuwan guda biyu
kashe shi za mu yi, don kada sirrinmu ya
bayyana, kasan ba zan iya kashe xana guda xaya
tilo a duniya ba duk da cewar bana qaunarsa
kuma ba zai tava gadataba”Boka Kuljalu yace.
“Ai ba zamu kashe shi ba, ka tuna duk cewa
duk faxin qasarnan babu wanda yasan abinda ya
faru damu sai Abnash, yanzu sai muyiwa
Abnash gargaxi kar ya sake ya sanar da shi
lalurar data same mu, tabbas ba zai sanar da shi
ba kawai zai bashi umarni ya yi aikinsa, ana
kammalawa sai mu kawar da maqeri Abnash
tunda shi ne kaxai yasan cewar mun sami
wannan naqasa” Koda jin wannan shawara ta
Boka Kurjalu sai sarki Dambola ya aminta da ita
suka dawo inda maqeri Abnash yake tsaye suka
yi masa wannan gargaxi sannan sarki Dambola
ya xauko dinare me yawa ya bashi ya sallameshi
akan cewa yaje ya kawo masa ido hannun
qarfenan da tsawon kwana bakwai kacal, nan
take maqeri Abnash ya yi godiya ya yi tafiyarsa.
**

52

Sarauniyar daji

Tun sa’ar da Abnash ya baro gidan sarauta sai
hankalinsa ya sake tashi ya shiga saqe-saqe a
zuci babban abinda ya tashi hankalinsa yasan
halin sarki Dambola mutum ne wanda ko kaxan
baya son asan sirrinsa. Wannan aiki daya bashi
na yin ido da hannun qarfe saboda ya voye
naqasar data same shi shida boka kuljalu.
Tabbas idan ya gama wannan aikin shima
kashe shi za ayi don kar anan gaba ya sanar da
wani wannan sirrin, wai shin yanzu yaya zanyi
Kenan? Yanzu idan nace guduwa zan yi sarki sai
ya saka an nemoni da qarfin sihirin tsafi an
kashe ni, to ko dai kashe kaina zanyi ayi biyu
babu buqatarsu bata biya ba tawa ma bata biya
ba.
Haka dai maqeri Abnash ya yi ta wannan
saqe-saqen har ya iso gidansa, da isowarsa qofar
gidan sai zuciyarsa ta buga da qarfin tsiya
sakamakon ganin wanda yake zaune a qofar
gidan yana yi masa murmushi, ba wani bane face
yarima Ashraf koda suka haxa ido sai ya fahimci
lallai maqeri yana cikin yanayi natsananin
damuwa. Ashtar ya miqe tsaye ya taho ga

53

Sarauniyar daji

maqeri Abnash ya tareshi suka rungume juna
sannan Ashtar ya janye jikinsa daga cikin nasa
ya dubeshi yace.
“Ya shugabana bani labari shin mene ya faru
a tsakaninka da mahaifina, tun xazu na zo nan
baka nan kuma matarka ta shaida mun sarki ne
ya aika kaje da gaggawa yana son ganinka”
Sa’ar da maqeri Abnash ya ji wannan tambayar
sai ya yi shiru ya sun kuyar da kansa ya kasa
cewa komai. Koda ganin haka sai Ashtar ya
kama hannunsa ya ja shi suka shige cikin gida
har sai da suka isa cikin turakarsa suka zauna. A
sannane matar Abnash ta shigo cikin turakar
xauke da abincin kalaci ta ajiye a gabansu.
Macece wacce shekarunta sun kai kusan
hamsin kuma ta kasance doguwa me matsakaicin
kaurin jiki, ana kiranta da masirat, kallo xaya ta
yiwa mijinta tasan yana cikin tashin hankali, har
ta juya zata tafi sai ta tsaya tace “Ya mijina ka
sani cewa ni idan ka voyemun abinda yake
damunka ba laifi bane saboda ba zan iya
taimakon ka da komai ba amma ina mai baka
shawara da kada ka voyewa yarima Ashtar

54

Sarauniyar daji

damuwarka saboda shi zai iya taimakonka koda
kuwa al’amarine daya shafi rayuwarka, ka sani
cewar Ashtar yarone mai sa’a da nasabi bisa duk
abinda ya sa a gabansa kamar yadda ka
sani,kuma ya xauke mu tamkar iyayen da suka
haife shi, ka sani cewar shi ne magajin karagar
mulkin qasarnan amma sai ya haqura da sarauta
ya dawo gidannan da zama ya qasqantar da
kansa ya koyi sana’ar qira” Masirat na gama
faxin haka sai ta juya ta fice daga cikin xakin ta
barsu a zaune.
Tsoho Abnash ya dubi Ashtar ya yi doguwar
ajiyar zuciya sannan ya kwashe labarin duk
abinda ya faru a tsakaninsa da su sarki Dambola
ya zayyana masa ya qara da cewar “Ya kai xana
kayi sani cewar muna hattama wannan aikin na
qera ido da hannun qarfe sarki zai sa a kasheni
kai kuma tunda baya qaunarka zai iya sakawa a
voyeka a wajen da babu wanda zai sake ganinka
har izuwa qarshen mulkinsa” Lokacin da tsoho
Abnash ya zo nan a zancensa sai Yarima Ashtar
ya yi murmushi sannan ya dubi a cikin nutsuwa
yace.

55

Sarauniyar daji

“Ya kai sarkin maqera kayi sani cewar ubana
na jini shi ne sarki Dambola amma kuma kaine
ubana na rayuwa, na so ace na kasance jininka
don jaka kasani cewar zan kare rayuwarka ta
kowacce hanya ko wane hali koda kuwa zan rasa
rayuwata, tabbas za mu qera wannan ido da
hannu na zinare amma ba mu za mu kaiwa sarki
ba, a lokacin da wannan aikin namu zai isa
gareshi mu tuni mun fita daga wannan nahiyar,
sarki ya baka kwanaki bakwai ka sani mu a cikin
kwana huxu zamu kammala aikin, muna
kammalawa za mu bar garinnan a sirrance kuma
aikin sai a ranar kwana na bakwai zai isa ga sarki
ni da kai da matarka za mu bar qasar” Sa’ar da
tsoho ya ji wannan maganar sai ya dubi yarima
Ashtar cikin matuqar mamaki yace.
“Ta yaya duka waxannan abubuwan za su iya
faruwa?” Ashtar ya yi murmushi yace “Kai dai
kawai ka zuba mun idanu zaka sha mamaki”
Ashtar ya miqe tsaye ya dubeshi yace “Abbana
tunda na kawar maka da damuwarka yanzu sai ka ci
abinci ko? Nima zan shiga ciki wajen umma na ci
nawa abinci” Yana gama faxin haka ya juya ya fice

56

Sarauniyar daji

daga cikin turakar sannan kuma sai ya buxe abincin
ya xauki loma guda ya kai bakinsa.
Yarima na barin turakar Abnash sai ya wuce kai
tsaye izuwa turakar masirat ya sameta a zaune tana
cin nata abincin. Tana ganinsa fuskarta ta cika da
annuri ta dubeshi tace “Lalle marhabin xana zo ka
zauna na xauko maka abincinka” Ashtar ya zauna a
kusa da ita yace.
“Ummina ai yau tare dake zanci abinci bana son
naci ni kaxai” Al’amarin daya matuqar baiwa
masirat mamaki Kenan saboda bai tava cin abinci
tare da it aba sai yau.masirat ta yi murmushi sannan
ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa suka ci gaba
da cin anbinci tare, suna cikin cin abinci ya dubeta
yace mata.
“Shin kin tava fita daga cikin qasar Hindu?”
Koda jin wannan tambayar sai ta dakata da cin
abinci ta dubeshi hankali a tashe tace “Gayamun
gaskiya hijira za mu yi” Ashtar ya yi ajiyar zuciya
yace.
“Qwarai kuwa ki soma shirin haxa kayayyan kin
mu daga yau xinnan, hijira zamu yi nan da kwana
huxu idan idan ba haka ba kuwa zaki rasa

57

Sarauniyar daji

maigidannan kuma nima za ki rasani” Koda jin haka
batu sai hawaye ya zubowa masirat tace.
“Shi Kenan mafarki nay a tabbata gaskiya”
Ashtar ya kama hannunta ya riqe yace “Wanne irin
mafarki kika yuine yake ummata?” Masirat ta rufe
idanunta tace “Nayi mafarki ni da kai da mijina
munata gudu a cikin daji ba tare da sanin inda zamu
ba, wata guguwa ce ke binmu duk abinda guguwar
ta riska walau bishiyoyi ko duwatsu sai ta tattakesu
gudu mukeyi iya ranmu amma mun kasa tserewa
guguwar kuma ita guguwar ta kasa cimmana gashi
muna shan baqar wahala muna samun raunika a
jikinmu” Ina cikin wannan mafarki na farka daga
bacci na gani sharkaf jike da zufa ina ta haki kuma
qafafuna sun gaji liqis tamkar gudun da nayi a
gaskiya nayi shi ba’a mafarki ba. Na firgita ainun da
wannan mafarki don haka ko shi mijina ban bashi
labarin mafarkina ba don kada hankalin say a tashi”
sa’ardda masirat ta zo nan a cikin labarin mafarkinta
sai shima Yarima Ashtar ya kamu da tsananin
mamaki bisa jin cewar masirat na farkawa daga
mafarki ta tsinci kanta a cikin zufa da haki gami da
tsananin gajiya tamkar a zahiri tayi wannan gudu
ba’a mafarki ba.

58

Sarauniyar daji

Kawai sai ya ayyana a cikin ransa cewar nan
gaba idan ya haxu da wani babban boka ko masanin
fassara mafarki zai tambayeshi ma’anar wannan
mafarki na masirat, nan dai Ashtar ya kwantarwa da
masirat hankalinta da maganganu masu taushi da
rarrashi harma ya bata dariya suka ci gaba da cin
abinci tare har sai da suka qoshi. Wannan shi ne
abinda ya faru a cikin birnin Hindu bayan sarki
Dambola da Boka kurjalu sun dawo gida.
**
Al’amarin sadauki Aryan da gimbiya lashmin
kuwa bayan sun fita daga cikiun iyakar birnin Hindu
sun faxa cikin iyakar karnad sai suka ci gaba da
tafiya a cikin daji ba sassauci suka tunkari hanyar da
zata kaisu cikin birnin karnad, suna cikin tafiya sai
Aryan yaga Gimbiya Lashmin taja linzamin dokinta
ta tsaya cak.
Al’amarin daya bashi mamaki Kenan shima ya
tsaya da nasa dokin ya dubeta ya risina cikin
girmamawa yace “Shugabata ina dalilin tsayawarki
anan wajen? So nake mu hanzarta isa cikin birnin
karnad domin mu sami masauki mu huta sannan
muyi tunanin yadda zamu ci gaba da gudanar da
rayuwarmu kafin lokacin da zamu koma

59

Sarauniyar daji

mahaifarmu yayi” Koda jin wannan batu sai
gimbiya Lashmin ta girgiza kai tace.
“Ba zan iya rayuwa a cikin gari ba ya kai sarkin
yaqi kayi sani cewa nafi jin daxin rayuwata a cikin
daji don haka mulkina kaso casa’in cikin xari a cikin
daji zan yi shi ina mai tabbatar maka da cewar nan
gaba nice sarauniyar da za a rinqa yiwa kirari da
sarauniyar daji, lallai sai na adabi dukkanin
azzaluman sarakuna na duniya sai sunana ya zamo
abin xaukaka kuma abin tsoro ga azzaluman, ni da
kai mafarauta ne kuma a cikinta iyayenmu da
kakanin mu suka mutu muma a cikinta zamu mutu,
bamu da wani wurin zama wanda yafi daji don haka
a cikin daji zamu zauna baza mu shiga cikin garin
karnata, lallai ina son mu voye asalinmu don kada
kowa yasan ko mu su waye ko kuma daga inda
muka fito, yanzu mu soma neman waje inda zai fi
dacewa da mu, muci gaba da farauta muna kai fatun
dabbobi da sassan jikinsu cikin gari muna siyarwa
muna siyo kayan abinci da sauran kayayyakin
amfani na yau da kullum”
Sa’adda gimbiya lashmin ta zo nan jawabinta sai
sadauki Aryan ya yi murmushi yace “Tabbas kin
tabbata ‘yar baiwa domin a qarancin shekarun nan
naki bai kamata ace kina iyayin wannan tunanin ban
60

Sarauniyar daji

a basira da hangen nesa to ammafa kuma akwai
matsala guda xaya” Lashmin tace.
“Mece ce matsalar?”
“Da zarar mun soma farauta mun soma kai
hajarmu cikin gari muna siyarwa cikin qanqanin
lokaci zamu tara arziqi me yawa, da zarar mun samu
wannan arziqin wajen da muke zai zama gari da
kasuwa a sannane hankalin sarkin qasar karnad zai
dawo kanmu, ina da labarin sarkin qasar karnad
baqin azzalumi ne kamar sarki Dambola na birnin
Hindu don haka shima ba zai qyale mu ba sai yayi
qoqarin kawar damu don mallake duk abinda muka
mallaka” Lokacin da Gimbiya Lashmin taji wannan
batu tayi murmushi tace.
“Ai ko wacce cuta tana da magani kuma ana iya
yi mata rigakafi, tunda harka faxamnu wannan
matsalar yanzu zan san hanyar da zanbi nayi
maganinta kafin a cimmana, tabbas yanzu ne ma
zamu hau kan tafarkin da burinmu zai cika na dawo
da zuri’armu ta mawardi amma sai na fara zama
sarauniyar daji tukuna” Lashmin na gama faxin
hakan sai ta kaxa linzamin dokinta ta nufi wani
vangaren daban na daji shima sadauki Aryan sai ya
bita da sauri.

61

Sarauniyar daji

Haka dai sukayi ta yawo a cikin daji har sai da
suka zo wani wuri mai ni’ima inda yake da wata
babbar qorama wacce ruwa ke gudu bisa kan
duwatsu sannan ga bishiyoyi da dabbobin daji
qanana kala-kala, suna ganin wannan wajen
Gimbiya Lashmin taja linzami ta tsaya cak! Ta
waigo ta dubi Aryan cikin murmushi tace.
“Anan zamu zauna”Aryan ya mayar mata da
martanin murmushi yace.
“Qwarai kuwa wannan wuri yayi kyau sosai
kuma akwai ni’ima to ammanfa akwai ayar
tambaya” Lashmin tace.
“Me kake son kace?”
“Ni dake mun san sirrin daji sosai, a duk wajen
da aka samu irin wannan babbar ni’ima dolene a
samu mafarauta ko fatake suna yada zango a wajen,
amma me yasa bamu ga haka baa nan? Ko dai akwai
manya miyagun daji a wajen ko kuma akwai ‘yan
fashi, wata qila kuma sarki karnad ne ya kafa doka
akan wannan wurin ya hana kowa zama a wajen”
Lashmin ta xaga kai tana murmushi tace.
“Koma mene a tattare da wannan wurin zamu
zauna a cikinsa kuma zamu tunkari kowanne irin
qalubale”Tana gama faxin haka ta sauka daga kan
dokinta ta xaure dokin a jikin wata bishiya sannan ta
62

Sarauniyar daji

sauko da jakar tafiyarta ta buxeta ta fito da gatari ta
dubi Aryan tace.
“Maza ka sauko ka tayani saro itatuwan da za mu
gina gidanmu” Sadauki Aryan ya yi murmushi yace
“An gama ranki ya daxe”.
Ba tare da vata lokaci ba suka je suka saro
itatuwa kuma suka yanko xanyu dogayen jijiyoyin
bishiyoyi suka kama aikin gina gida, sai da suka
kwana suka yini suna wannan aikin sannan suka
kammala. Sun kewaye gidan da Katanga ta ice ya
zamana cewar tsawon katangar ya kai tsawon
mutum koma sun xebi haraba mai xan faxi xakuna
uku ne kacal a cikin gidan sai kewaye guda xaya da
madafa, gidan ya yi kyau sosai kai kace a cikin birni
aka yi shi kuma qwararun magina ne suka yi shi.
Bayan sun kammala ginan suka zauna daga
wajensa suka qura masa idonuwa suna mamakin
yadda suka yi shi yayi kyau sosai kamar haka.
Lokacin da Gimbiya Lashmin ta qurawa gidan idanu
sai ta faxa cikin kogin tunani inda nan take ta tuna
rayuwarta ta baya tare da iyayenta a cikin gidansu
lokacin da sarki Amjadu da Rasina suke renonta tun
batafi shekara huxu ba a duniya da yadda suke nuna
mata tsananin soyayya, qauna da kulawa da kuma
yadda sarki Amjadu ya riqa koya mata yaqi da
63

Sarauniyar daji

farauta a daji. Haka dai taci gaba da yin wannan
tunanin har izuwa ranar qarshe data rabu da su a daji
lokacin da Aryan ya tafi da ita don kada sarki
Dambola ya kasheta.
Tana gama yin wannan tunanin hawaye ya zubo
mata a lokacine sadauki Aryan ya kira sunanta ta
dawo haiyacinta yace.
“Ya shugabata na sani cewar kin da tuno da
iyayenkine nima haka na tuno da iyalina waxanda a
halin yanzu duk an kashe su babu ko xaya a raye.
Dukkanin jama’armu sun mutu ni dake kaxai muka
tsira da rayuwarmu, ki sani cewar burin mahaifinki
shi ne mu dawo da zuri’armu ta mawardi don haka
ina son ta kowane hali mu rayu domin mu cika burin
mahaifinki”
Koda sadauki Aryan ya zo nan a maganarsa sai
zuciyar Gimbiya Lashmin ta karaya hawayen
tausayi ya zubo mata. Tausayinsa ya kama Gimbiya
Lashmin ta faxa kan qirjinsa suka rungume juna
suna ci gaba da kuka sannan Lashmin ta janye
jikinta daga cikin nasa ta goge hawayen idanunta ta
dubeshi tace.
“Daga yau kaine uwata da ubana kuma za mu
haxa qarfi da qarfe domin cika burin mahaifina”
Sadauki Aryan ya risina yace.
64

Sarauniyar daji

“Ya shugabata ki sani ba zan tava maye gurbin
mahaifanki ba, amma zan shuxe a matsayin sarkin
yaqinki lallai zan jure da raina da jikina domin
ganin burin mahaifinki ya cika, yanzu yaushe za mu
shiga daji farauta domin samo hajar da za mu kai
cikin birnin karnad?” Lashmin tayi murmushi tace.
“Ai da zafi-zafi akan bugi qarfe gobe da sassafe
za muje muyi wannan farautar kuma a goben zamu
shiga cikin birnin karnad yanzu mu shiga cikin gida
mu huta kuma mu ci abinci” Tana gama faxin haka
sai ta miqe ta nufi cikin gidan da suka gama ginawa
da itatuwa, shima Aryan sai ya miqe ya bita.

**
Bayan Gimbiya Lashmin da sadauki Aryan sun
ci abinci sun zauna suna hutawa kuma suna yin hira
sai kowai suka jiyo sukuwar dawakai daga gabas da
yamma, kudu da arewa an durfafo wannan gida nasu.
Kai daji kasan cewar dakaru ne masu yawa suka
kawo hari.
Cikin zafin nama Lashmin da Aryan suka miqe
suka debi kayan yaqinsu suka rugo izuwa cikin
harabar gidan na su suka tsaya. A daidai lokacin
65

Sarauniyar daji

wasu dakarun ‘yan fashi suka qaraso daf da gidan
suka yi musu qawanya.
Adadin waxannan ‘yan fashi ya kai dubu biyu
kuma dukkansu suna sanye da baqaqen tufafine sun
rufe fuskokinsu idananunsu kaxai ake gani,
dukkansu suna xauke da mugayen makamai, sannan
sun kasance zaratan jarumai ma su kwarjini da ban
tsoro, bayan waxannan dakarun ‘yan fashin sun
gama kewaye gidan Gimbiya Lashmin da sadauki
Aryan, sai dakarun dake gaban qofar gidan suka
dare suka samar da wata hanya a tsakiyarsu,
shugaban ne ya ratso ta hanyar akan dokinsa tufafin
jikinsa ya bambanta da nasu domin shi fararen
kayane a jikinsa kuma fuskarsa a buxe take amma
ya shafeta da jan shuni kuma ya rataya wata baqar
takobi a bayansa.
Rigar jikinsa mai yankakken hannuce don haka
ta bayyana hannayensa masu kaurin cike da qwanji
da jijiyoyi kai da ganinsa kasan cewar sadaukine nag
aske, shugaban ‘yan fashin ya qaraso daf da qofar
gidan nasu Lashmin sannan yaja linzamin dokinsa
ya tsaya cak aka yi kallon-kallo a tsakaninsa da
Lashmin da Aryan sannan ya dubesu yace.
“Su waye ku harda zaku zo inda muke hutawa ku
gina gida ku zauna? Kuyi sani cewar nine sarkin
66

Sarauniyar daji

varayin wannan nahiyar gaba xaya wannan wurin
qarqashin ikona yake kuma ina biyan haraji ga sarki
karnad, lallai kun aikata babban laifi kuma kun
karya mun dokata, za ku fuskanci hukunci me
tsanani, zan kwace wannan gidanaku da dukkanin
abinda kuka mallaka sannan na kamaku na kaiku
cikin kurkuna ku zauna tsawon shekara
biyu,bayanan kuma zan maishe ku bayi kuyita ta
mun bauta har qarshen rayuwarku” Koda sarkin
‘Yan fashi ya zo nan a bayaninsa sai yaga Aryan da
Gimbiya Lashmin sun dubi juna kuma sun fashe da
dariya, abinda ya baiwa sarkin varayi da jama’arsa
mamaki.
Lashmin ta murtuke fuska ta dubi sarkin varayi
ido da ido tace.
“Ya kai wannan tsohon azzalumin kayi sani
cewar sunana Gimbiya Lashmin kuma nice
sarauniyar daji, dukkanin dazuzzukan dake cikin
nahiyar nan a qarqashin mulkina suke, duk wani abu
dake cikin daji walau mutum ko dabba ko qwari a
qasan ikona suke, daga yau kai da jama’arka kun
zama yarana kubi umarnina ku zauna lafiya ko kuma
ko wannen ku ya xanxana kuxarsa” Koda Gimbiya
Lashmin ta zo nan a maganarta sai sarkin varayi ya
taqarqare ya bushe da mahaukaciyar dariya, ai kuwa
67

Sarauniyar daji

sauran yaransa suka kama yin dariyar sautin dariyar
tasu ya cika dajin gaba xaya babu daxin ji har sai da
shugaban nasu ya tsuke bakinsa sannan suka yi
shuru.
Sarkin varayi ya dubi lashmin a fusace yace
“Yake wannan ‘yar qaramar qwaruwar louo samo
cewar dake da wannan mutumin dake tare dake koda
kun kasance aljanu yanzunan zan sa ayi muku kisan
gilla, ina son ku nuna mun iyakar abinda kuke
taqama da shi har da kuka riqa yi mun rashin kunya
haka”Yana gama faxin haka sai ya xaga hannunsa
sama ya yi wata inkiya faruwar haka ke da wuya sai
gaba xaya dakarunsa suka zaro kibiyoyi suka xana
akan baka suka saita Lashmin da Aryan.
Koda ganin haka sai Lashmin da Aryan suka zare
takubansu kuma suka xaga garkuwarsu sama suka
gyara tsayuwarsu suna masu jingina da bayan juna.
Sarkin varayi na sauke hannunsa qasa sai gaba
xayan dakarun nasa suka sakarwa su Lashmin
ruwan kibiyoyi.
Wohoho! Wanda Allah ya baiwa jarumtaka zafin
nama da kaifin horon yaqi y agama hutawa. Nan
take sarkin varayi da jama’arsa suka ringa ganin
abin al’ajabi da basu tava gani ba a rayuwarsu. Duk
kibiyar data doshi inda Lashmin da Aryan suke sai
68

Sarauniyar daji

aga suna tareta da garkuwarsu da takobinsu, sai dai
kaga kibiyoyi suna zubewa qasa ko xaya bata tava
jikinsu ba.
Nan fa dakaru suka yi ta zaro kibiyoyi suna
sakawa cikin kwarinsu suna harba musu, sai da aka
shafe rabin sa’a ana ta harbawa, Lashmin da Aryan
waxannan kibiyoyin sannan kibiyar kowane
badakare ta qare amma duk Lashmin da Aryan sun
kaxesu sun zube qasa a gabansu, qwaya xaya bata
soki jikinsu ba.
Shi kansa sarkin varayin sai daya diro daga
dokinsa qasa saboda tsananin mamaki aka sake
kallon-kallo a tsakaninsa da su Lashmin, su kuma
dakarunsa ji suka yi kamar su juya da baya su gudu
amma sai suka tsaya saboda tsoron fushin
shugabansu.
Gimbiya Lashmin ta dubi sarkin varayi ta yi
murmushi tace ‘Ya kai wannan shugaban ‘yan fashi
ka sani kun taka rawarku muma yanzu lokacin mu
ya yi, ina mai umartaku daku tattaro dukkanin
makamanku na yaqi ku yi mubaya’a a gareni a
matsayin sarauniyarku” Sa’ar da sarkin varayi yaji
wannan batu sai ya bushe da mugunta sannan ya
dakawa Lashmin tsawa yace.

69

Sarauniyar daji

“Ke yarinya quruciya tana xibanki, don haka
qaryarki tasha qarya yanzunnan zan sa ayi muku
kisan gilla ayi gutsu-gutsu da sassan jikinku a
watsawa dabbobin ruwa su cinye, dakaru maza a
afka musu” Kafin sarkin varayi ya rufe bakinsa
sama da dakaru xari uku sun zare takubbansu sun
sakarwa dawakansu linzami zuwa cikin gidan suka
rushe suka shiga ciki ganin haka Lashmin tace wa
Aryan.
“Mu kare kanmu amma kar mu kashe su mu
karairaya su” yace “An gama ya shugabata”.
Nan take wuri ya hargitse qura ta turnuqe qarar
qarafa da ihun mazaje ya yawaita saboda qurar data
turnuqe wajen sarkin varayi da sauran yaransa basa
ganin abinda yake faruwa amma ihun da suke
juyowa na jama’arsu sai hankalinsu ya daxa tashi
sun fahimci ba sune suke samun nasara ba.
Sai da aka shafe sama da daqiqa xari uku da
sittin ana wannan baqin gumurzu sannan aka ji an
daina yaqin ba a jin komai sai sautin koke-koke na
dakarun ‘yan fashi, a sannan ne qura ta lafa kawai
sai sarkin varayi da sauran yaransa suka gag aba
xaya dakarun nasu da suka afkawa Lashmin da
Aryan suna kwance a qasa magashiyan waxansu

70

Sarauniyar daji

qafafunsu a karye waxansu hanayensu. Lashmin da
Aryan na tsaye qiqam ko qwarzane babu a jikinsu.
Koda ganin wannan al’ajabi sai sarkin varayi da
jama’a suka firgita ainun, sarkin varayi ya xauko
jakar dukiyarsa ya taka da qafarsa yaje har gaban
Lashmin ya jefar da jakar sannan ya kwanto
takobinsa daga gadon bayansa ya jefar da ita a qasa.
Kawai sai ya durqusa a gaban Gimbiya Lashmin
bisa guiyoyinsa biyu ya sunkuyar da kansa qas yace.
“Na miqa wuyana ga sarauniyar daji daga yau ni
da jama’ata mun zama jama’arki sai abinda kike ce”
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya kama
Lashmin da Aryan suka kama yin murmushi.
Nan take gaba xaya rundunar ‘yan fashi suka
sauko daga kan dawakansu suka xebo kayayyakinsu
da makamansu suka kawo gaban Gimbiya Lashmin
suka zube kuma suka durqusa qasa a gabanta suka
yi munaya’a kamar yadda sarkinsu yayi.
**
A can babban birni na Hindu kuwa kamar yadda
Yarima Ashtar ya tsara haka al’amarin ya kasance
wato cikin kwanaki huxu shida sarkin maqera
Ashtar suka hattama qera wannan ido da hannu na
qarfe.

71

Sarauniyar daji

A wannan ranar tsakar dare Ashtar ya xauke
tsoho Asnar tare da matarsa masirat suka fice daga
cikin birnin Hindu. Abinda ya xaurewa Asnar da
Masirat shi ne Ashtar ya fitar da su ne ta cikin wata
varauniyar qofa dake cikin qarqashin qasa a cikin
wani tsohon xakin bauta wacce basu tava saninta ba.
Kawai sai gani suka yi sun fito tsakiyar daji duke
can qarshen birnin, suna fitowa suka iske
dawakansu guda biyu da kuma guzuri. Dawakan na
xaure a jikin wata bishiya. Abnash ya dubi Ashtar
cikin tsanan in mamaki yace.
“Ya aka yi ka samo wannan varauniyar hanyar
wacce mutum zai iya fitowa daga cikin birnin Hindu
ta qarqashin qasa kuma yaushe ka xauko
dawakanmu da guzurinmu ka kawo su nan?”
Lokacin da Yarima Ashtar ya ji wannan tambayoyin
sai ya yi murmushi yace.
“Shin bana baka labara cewar nima ina yin
mafarki shigen irin wanda matarka ke yi ba” Abnash
ya gyaxa kai yace “Tabbas ka tava gaya mini
hakan” Yarima Ashtar yace.
“To ai tundaga wannan lokacin jikina ya bani
cewar lallai akwai lokacin da dolene muyi hijira
daga cikin birnin Hindu asirrance, daga wannan
lokacine na fara tunanin samar da hanyar voye
72

Sarauniyar daji

wacce za mu yi amfani da ita. Wata rana na shiga
cikin tsohon gidan bauta wanda rabon da mutum ya
shiga cikinsa an kai shekaru arba’in ina cikin dubedube kawai sai naga mage ta fito daga cikin ramin
sai naga ashe ramine me zurfi da faxi wanda
mutumn ma zai iya shiga cikin ramin kawai sai na
kunna kai cikin ramin na kunna wutar ice na soma
tafiya a cikinsa har tsawon irin tafiyar da muka yi
yanzu kawai sai gani na yin a fito cikin wannan
dajin.
Da gudu na koma cikin gari na rufe ramin da
katako na zuba qasa akansa na rufe wajen, ina ganin
asalin wannan ramin mutanen dane suka yi shi don
samar da voyayyiyar hanya ta fita daga gari daga
baya kuma suka gine ramin amma sai yau da gobe ta
saka ya sake buxewa.
Dawakanmu kuwa da guzuri tun daren jiya na
fito da su ta wannan ramin na kawo su nan wajen na
ajiye, yanzu abinda nake so daku shi ne ku hau
dawakanan kuyi tafiya har sai kun je iyakar birnin
Hindu da birnin karnad sannan ku jirani na iso na
same ku, ni zan koma domin na kaiwa sarki
abubuwan da muka qera masa guda biyu wato ido
da hannun qarfe” Sa’adda tsoho Abnash ya ji abinda
Yarima Ashtar ya tsara sai hankalinsa ya tashi.
73

Sarauniyar daji

Itama masirat sai ta fara kuka tace “Shi Kenan
mun rabu da kai Kenan har abada domin idan kaje
ka kaiwa sarki waxannan abubuwan ba zai qyaleka
ka fito ba kuma zai saka ayita gana maka azaba ne
har sai ka faxi wajen da muke”Ashtar ya yi
murmushi gami da girgiza kai yace.
‘Ku kwantar da hankalinku hakan ba zai tava
faruwa ba, na yi muku alqawari nan da cikar sa’a
biyu zan zo na riskeku acan bakin iyaka” Yana
gama faxin hakan sai masirat ta rungume shi tana
kuka, shima Abnash sai ya rungume Ashtar yana
zubar da hawaye nan dai Yarima Ashtar ya lallavasu
suka hau dawakansu suka yi gana suna waigensa har
suka yi nisa sannan shima Ashtar ya juya da gudu
izuwa cikin wannan ramin domin komawa cikin
birnin Hindu.
**
A can gidan sarauta Hindu kuma lokacin da gari
ya waye sai fada ta cika da fadawa da jama’ar gari
saboda yau kwana huxu Kenan tunda sarki ya dawo
daga yaqi daya fita bai zauna akan karagar mulkinsa
ba.
A yaune akace sarki zai fito ya yi bayani akan
yaqin dayaje da kuma dalilin daya saka bai yi zaman
fad aba har tsawon kwanaki huxu. Tuni sarki
74

Sarauniyar daji

Dambola ya shirya yadda zai fito ya yi wannan
bayani ga al’umarsa bisa shirin cewar zai voye
fuskarsa ne don kada a ga cewar ya rasa idonsa guda.
Bayan fada ta cika ta batse hakimai da dakatai
duk sun hallara daga garuruwan qasar gaba xaya
sarki Dambola na cikin turakarsa yana shirin fita
fada sai ga matarsa shanina mahaifiyar yarima
Ashtar ta shigo cikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment