You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan ta girma tayi aure
xanta jinin qabilar mawardi ne kaga Kenan
burinmu ya cika farin cikina na mutu tare da kai
don haka zan tsaya anan na tayaka wannan yaqi”
Koda sarki Amjadu ya ji haka sai ya dubi Rasina
ya yi mata murmushi yace mata.
“Macen mawardi guda xaya tafi namijin
Hindu guda dubu saboda zuciyarta dakakkiyace,
ya kai Aryan sarkin yaqina kuma xan uwana na
bar maka lashmin amana ka kula da ita har zuwa
girmanta domin zuri’armu su ci gaba da yaxuwa
a doron qasa maza ka xauketa ku hau
dawakanmu ku bar yanki qasarnan gaba

26

Sarauniyar daji

xaya”Koda jin haka sai Gimbiya Lashmin ta
rungume sarki Amjadu da Rasina ta fashe da
kakan baqin ciki na rabuwa tace.
“Shi Kenan na rasa iyayena ina da quruciyata
kuma shikenan har abada bazan sake ganinku
ba”Tausayinta ya kama sarki Amjadu da Rasina
suma suka qanqame lashmin a jikinsu suna
zubar da hawaye.sarki Amjadu ya janye jikinsa
daga na Lashmin ya kama hannun Rasina suka yi
gaba. Shi kuma sarkin yaqi Aryan sai ya kamo
dawakan biyu ya xora gimbiya lashmin akan
xaya shima ya hau xayan suka zaburi dawakan
da gudu suka bar wannan dajin.
Su sarki Amjadu da Rasina kuwa tunda suka
juya basu qara waigowa ba sai da suka zo wani
waje mai faxi a cikin daji, Amjadu da Rasina
suka dubi gabas da yamma kudu da arewa na
wajen sannan suka dubi junansu suka yi
murmushi tace masa.
“Anan ne muka tava yin yaqi da rundunar
‘yan fashi na kwana guda da yini guda lokacin
ina xauke da cikin Gimbiya Lashmin, yanzu
shekaru goma Kenan”Sarki Amjadu ya yi

27

Sarauniyar daji

murmushi yace “Mutum nawa kika kashe
awannan yaqin?”
Rasina tace “Mutum xari biyu da arba’in na
kashe”.
“Ni kuma mutum xari biyar da huxu na kashe,
Aryan kuma mutum xari uku da goma sha shida
ya kashe, amma ki sani tarkon da muka xanawa
‘yan fashin shi ne yasa muka samu wannan
gagarumar nasara”Rasina tace “Yauma irinsa
nake son mu xanawa waxannan maqiyan namu,
lallai ina son kafin a kashe biri to biri ya yi
varna”Sarki Amjadu ya yi murmushi yace “Ina
alfahari dake matar sarki mawardi, maza mu
soma xana tarkuna kafin maqiyanmu su zo lallai
yau qasa zata sha jinni ta qoshi, ni dake za mu
babbar mutuwa irin ta manyan jarumai”Nan take
Amjadu da Rasina suka zare wasu wuqaqe masu
kaifin tsiya daga cikin jikinsu suka hau kan
bishiya suka fara saro rassa suna fiffiqesu kuma
suka rinqa yanko jijiyoyin bishiyoyi masu kauri
suka shiga haxa mugayen tarkuna suna
bibbinesu a cikin qasa,wasu kuma akan bishiya

28

Sarauniyar daji

suka riqa xana su suna boyesu a cikin ganyayen
bishiya masu duhuwa.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face
yadda sarki Amjadu da Rasina suka laqanci haxa
waxannan tarkuna kuma suke gane wuraren da
suke binnesu da voyesu yadda ba za su tava yin
kuskuren taka inda tarkunan suke ba.
Kafin cikar sa’o’in da su sarki Dambola za su
qaraso tuni su Sarki Amjadu sun gama xana
dukkanin tarkunan su waxanda sun fi guda dubu,
wata hikima da suka yi shi ne ba’a waje xaya
suka xana tarkunan ba. Suna ba tazarar aqala
taku ashirin tarkunan kala bakwai ne kuma
kowanne ya bambanta da sauran.
Bayan sun kammala aikin haxa tarkunan sai
sukaje can gaba suka hau kan wasu bishiyoyi
dogaye guda biyu suka yi zamansu akai cikin
duhuwar ganyaye wanda koda za’a haskosu da
kowanne irin haske ba za’a iya ganinsu ba
saboda ganyayen bishiyar manya-manya ne falafala waxanda za su iya lulluve mutum.
Suna nan wajen a zaune har kimanin sha biyu
da rabi, a lokacin dare ya tsala, baka jin motsin

29

Sarauniyar daji

komai face qwari sai kuma kukan tsuntsaye, ko
ganyen bishiya ne ya faxo qasa mutum na iya jin
qarar faxuwarsa a daidai lokacin Rasina ta soma
gyangyaxi a lokacin kuma su Sarki Dambola
suka qaraso wajen da suka xana tarko, sarki
Amjadu bai san cewar Rasina ta soma bacci ba
don haka kawai sai yaga ta zame daga kan
bishiyar da suke zaune zata faxo qasa. Cikin
zafin nama ya cafo hannunta ya dawo da ita kan
bishiyar sautin zamewarta yakai kunnuwan sarki
Dambola don haka sai sarki Dambola ya ja
linzami cak, hakan ne ma ya saka kowa ya tsaya
cak! Sarki Dambola da Boka kurjalu suna tsaye
kafaxa da kafaxa suka kalli junansu.
A wannan lokacin sauran Dakarun suna riqe
da fitilun itatuwa, kurjalu yace “Ya shugabana
shin baka jiyo sautin motsi ba daga can
gabanmu”Yace masa.
“Na ji mana amma mene abin tsoro ga mutum
da ba su fi huxu ba, tunda mun kashe sauran
gaba xaya shin baka faxamun daga sarki da
matarsa sai kuma ‘yarsu Lashmin”Boka yace.

30

Sarauniyar daji

“Hakane ya shugabana amma ka sani
waxannan mutanen da muke nema ko wanne
xaya a cikin su daidai yake da mutum dubu a iya
yaqi da jarumtaka don haka za su iya yi mana
mummunar varnar da ba ma zato,ka sani cewar a
nahiyar nan gaba xaya babu wanda yafi mutanen
garin mawardi iya xana mugayen tarkuna a cikin
daji sannan kuma sunfi kowa laqantar dukkanin
dazuzzukan dake cikin qasarnan, abune
mayuwanci ayi yaqi da su a cikin daji a samu
nasara akansu” Cikin fushi sarki Dambola yace.
“Indai hakane kayi amfani da qarfin tsafinka
ka gano duka tarkunan da suka xana mana a
cikin dajin nan mana”Boka karjalu yace “Ai da
hakan zai yuwu da tuni nayi,babu wani tsafi da
zai iya yin tasiri a kan mutanen mawardi indai
suna cikin daji sai dai a cikin gari inda yake
akwai gidaje da mutane”Sarki Dambola yace.
“Shi Kenan yanzu a tura mutane hamsin suyi
gaba muga abinda zai faru”Nan take kuwa sarkin
yaqi shargal ya nuna mutum hamsin daga cikin
dakarun suka zaburi dawakansu da gudu suka yi
gaba.

31

Sarauniyar daji

Kaico! Tsautsayi baya wuce ranarsa, mutum
hamsin xin kuwa suna yin gaba kamar da taku
goma sai akaga wasu fiqaqqun itatuwa suna
fitowa daga cikin qarqashin qasa suna soke
dawakansu da su kansu. Wani kaga ice ya soki
qeyarsa ya fito ta gadon bayansa. Wani ta gadon
bayansa zai sokeshi ya vollo ta qirjinsa da su da
dawakan nan take suka zama gawa. Al’amarin
dayai matuqar razana sauran Dakarun Kenan
suka firgita ainun suka soma ja da baya kamar za
su gudu. Ganin haka sai sarki Dambolo ya zare
wuqa yace “Duk wanda ya yi yunqurin guduwa
ni zan qure masa gudu da kaina na kashe shi,
sarkin yaqi maza ka sake tura dakaru xari su
sake yin gaba”Shargab ya dubi dakaru xari ya
basu umarni bisa dole sumna suka sakarwa
dawakansu linzami suka zabura da gudu izuwa
gaba.
Tabbas dole idan ajali ya yi kira dole sai an
amsa, lokacin da waxannan dakarun suka tunkari
gaba sai wasunsu suka kare fuskokinsu da
garkuyinsu saboda tunanin cewar itatuwa za su
sokesu a fuska ko a wuya maimakon hakan ta

32

Sarauniyar daji

faru sai akaga itatuwan daga sama cikin
bishiyoyi suka rinqa zabowa qasa suna soke su.
Kaifin cikar daqiqa xaya gaba xayan waxannan
dakarun xari suka zama gawa har dawakansu
kuwa. Haka dai sarki Dambola yasa aka ci gaba
da tura dakarun suna ta mutuwa har tsawon
rukuni bakwai ya zamana cewar an rasa dakaru
dubu xari bakwai da hamsin al’amarin daya
karya zukatan ragowar dakarun dubu xari biyu
da hamsin Kenan har aka yi musu tsawa sau uku
akan su qara gaba amma suka qi suka
gwammace sarki Dambola ya kashesu da
hannunsa.
Koda ganin haka sai zuciyar sarki Dambola ta
kama tafarfasa kamar zata qone kawai sai sarki
Dambola ya zare takobinsa ya karvi garkuwa ya
riqe koda ya motsa zai yi gaba sai boka kurjalu
yasha gabansa ya tsaida shi yace ‘Ya shugabana
da dai ka mutu anan wajen gwara gaba xayanmu
nan mu mutu kai kaxai ka tsira, ni zan soma
wucewa gaba idan kaga babu abinda ya sameni
sai ka biyoni a baya”Yana gama faxin haka sai
shima ya zare takobinsa ya yi gaba, sai da ya yi

33

Sarauniyar daji

taku goma babu abin daya sameshi sannan sarki
Danbola ya bishi a baya, hakkane yasa sauran
dakarun suka biyosu.
Duk wannan abu da yake faruwa sarki
Amjadu da matarsa Rahina suna can nesa kan
bishiya suna ganin sa murmushi suke na farin
ciki bisa ganin nasarar da suka samu ta na kashe
abokan gaba ki manin dari bakwai da xari koda
suka hango sarki Dambola da boka kurjalu da
ragowar tsirarun dakarun sun tunkaro inda suke
sai Amjadu ya dubi Rahana yace.
“To yanzune fa za’a fara wannan yaqin ni zan
tari sarki Dambola ke kuma ki tari Boka kurjalu,
sauran dakarun kuma kawai ‘yan tsakine a
garemu qwaf xaya zamu rinqa yi musu, ina son
mu taresu kafin su qaraso wajenan”Yana gama
faxin hakan sai shi da Rahina suka janyo
waxansu dogayen jijiyoyin bishiya faruwar
hakan ke da wuya sai fitilun itatuwa sama da
guda xari biyar suka kunna kansu a jikin
bishiyoyi gaba xaya dajin ya haskake da
haskensu tamkar rana, su sarki Dambola suka
kama kalle-kalle suna mamakin yadda aka yi aka

34

Sarauniyar daji

kunna waxannan fitilun a lokaci guda. Kawai sai
suka hango sarki Amjadu da matarsa a suna
sakowa daga kan wata doguwar bishiya ta jkikin
dogayen jijiyoyinta duka su biyun sun yi
gagarumar shiga ta yaqi.
A wannan lokacin su sarki Dambola sun tsaya
cak suna kallonsu kawai. Bayan sun duro qasa
sai aka tsaya aka yi kallon-kallo na tsawon yan
daqiqu sannan sarki Dambola ya dubi sarki
Amjadu a fusace yace “Ina ‘yar taka
take?”Amjadu ya yi murmushi yace “Har abada
ba zaka tava samun nasarar kasheta ba,kuma
itace zata kasheka, a yanzu gimbiya lashmin ta yi
nisa da barin wannan yanki tana daf da shiga
iyakar qasar karnad, kafin ku gama da mu tuni ta
shiga yanki qasar karnad, to amma idan kana
ganin zaka bi mutum biyu rak qasar to ka bisu,
ko yanzu muka mutu anan ni da matata mun bar
abin alfahari tunda munyi muku mummunar
varna kuma mun hanaku cika burinmu” Boka
kurjalu ya tari numfashin sarki Amjadu yace.
“Qarya kake yi yakai talakan sarki me mulkin
tsirarun mutane, ka sani cewar buqatarku ba zata

35

Sarauniyar daji

biya ba kamar yadda zamu kasheku yanzu haka
zamu bi bayan sarkin yaqinka da ‘yarka mu
riskeku kafin su shiga nahiyar da ba tamu ba,
shin ka mance indai za su shiga gari da mutane
da gidaje tsafina sai ya yi tasiri a kansu, to kamar
yadda za mu kashe ku haka za mu riskesu da
qarfin sihiri mu kashe su kaga shi Kenan babu
sauran irin tsatsonku a doron qasa’Caraf sai
Rasina ta tari numfashin Boka kurjalu tace.
“Qarya kake yi yakai tsohon munafuki wanda
yaci amanar marigayi sarkin Hindu. Da kai sarki
Danbola ya haxa kai ya karve karagar mulki da
qarfin tsiya alhalin babu abin arziqin da
marigayi sarki bai yi maka ba, ya kai Dambola to
kayi sani cewar wannan boka baa bin yarjewa
bane, duk yadda kuke da shi bai kai na yadda
suke da marigayi sarki ba amma yaci amanarsa,
shin kaima baka tunanin zai ci amanarka anan
gaba?”Koda jin haka sai sarki Dambola ya yi wa
boka kurjalu wani irin kallo koda yaga haka sai
yace “Ya shugabana kada ka yadda da maganarta
kawai so take ta karya maka zuciya ka kasa

36

Sarauniyar daji

aiwatar da abinda yake gabanka” Sarki Dambola
ya yi guntun murmushi yace.
“Abinda ta faxa kuwa gaskiya amma kasan ni
sarki Dambola bana fara abu naqi gamawa dashi,
na riga na qarar da zuri’ar mawardi sauran
mutum huxu don haka dole na qarasa cikon
aikina dakaru a afka musu”Sarki Dambola na
gama faxin haka sauran dakarun da suka rage
suka ruga da gudu izuwa kan Amjadu da Rahina
aikuwa sai Rahina da Amjadu suka taho da gudu
suka taresu aka ruguntsume da azzababen yaqi,
nanfa qarar qarafa da ihun mazaje ya yawaita.
Jinni kuwa ya rinqa tsartuwa da fallatsa a
sama yana zuba a qasa, nanfa Rahina da Amjadu
suka rinqa sara da sukan Dakarun suna zubewa a
qasa matattu tamkar suna sassabe a gona. Duk
inda suka ratsa sai dai kaga maza na zubewa
babu abin daya baiwa su sarki Dambola mamaki
face ganin irin zafin naman Rasina da kuma iya
yaqinta gami da zafin nama da kuma jarumtaka
irin nata manyan sadaukai. Kafin cikar rabin sa’a
ita da sarki Amjadu sun kashe dakaru xari biyu
koda ganin hakan sai sarki Dambola ya fusata

37

Sarauniyar daji

ainun ya falfala da gudu yana mai xaga
takobinsa sama, kawai sai ya daka tsalle sama
kamar da majaujawa aka harbashi ya kaiwa
Rasina mummunan sara a wuya da nufin ya
cisge mata kai, amma sai takobin sarki Amjadu
ta kare saran a lokacin da shima ya daka tsalle
sama suka duro qasa a tare kuma suka
ruguntsume da azababban yaqi ya zamana cewa
suna kaiwa junansu sara da suka cikin qwarewa
da bajinta. Kai da ganin wannan baqin gumurzu
a tsakanin sadaukan kai da ganin wannan baqin
gumurzu a tsakanin sadaukai biyu kasan cewa
za’ayi baqin gumurzu kafin xayansu ya kai
xayan qasa. Shima Boka kurjalu sai ya ruga da
gudu ya afkawa Rasina suma suka kacame da
masifaffan yaqi.
Wohoho! Duk sa’adda zaratan jarumai suka
fara gumurzu qasa ma sai data koma, bishiyoyi
kuwa sai dai kaga suna rangajin dole, qoramu na
kaxawa duwatsu na motsawa kamar zasu
farfashe ana fara yin wannan baqin gumurzune
ragowar tsiraron dakarun da suka rage suka cika
wandonsu da iska suka bar wajen tamkar sunyi

38

Sarauniyar daji

layar zana, sarkin yaqi Dambola kaxai wato
sadauki shargal ya tsaya. Koda yaga Boka
kurjalu da Rasina suna yin baqin artabu ya kasa
cutar da ita sai ya ruga ya kai masa xauki suka yi
wa Rasina rubdugu bisa mamaki sai shargal yaga
Rasina na iyawa da su biyun.
Maimakon ta sami rauni kuzari sai ya zama
kamar ma an qara mata qarfi da zafin nama, ba
zato ba tsammani sai ta shammaci shargal tayi
tsalle sama ta doki qirjinsa saboda qarfin dukan
sai ya yi sama da baya ya faxa kan reshen wata
bishiya mai tsini. Take reshen ya tsireshi ta
gadon bayansa ya vollo ta cikinsa ya zama gawa.
Koda ganin haka sai Boka kurjalu ya kurma
uban ihu ya afkawa Rasina da dukkan qarfinsa ai
kuwa sai ya sami nasarar yankarta a damtsen
hannunta na hagu. Take wajen ya dare jini ya yi
tsartuwa. Rasina tayi ihu ta durqushe qasa bisa
guiwarta guda.
Kurjalu ya sake kawo mata wawan sara ta
kauce daga inda take ya sari qasa, saboda qarfin
saran sai da takobinsa ta nutse a cikin qasa
amma kafin ya zaro takobin tuni ta yagi gefen

39

Sarauniyar daji

rigar jikinta ta xaure raunin dake hannunta don
tsaida jinni kawai sai ta dako tsalle sama daga
inda take ta kaiwa kurjalu sara a gadon bayansa.
Cikin sa’a kuwa kaifin takobinta ya ratsa bayan
nasa wajen ya dare shima ya kurma uban ihu
sakamakon tsananin zafin dayaji amma sai ya yi
wuf ya xauko wani garin magani a cikin jikinsa
ya manna akan raunin take jini ya daina zuba
shima sai ya cisge rawaninsa ya xaure bayansa
inda raunin yake ya miqe tsaye zumbur suka yi
kallan-kallo kowannansu na tunanin irin sabon
yaqin daya kamata ya yi.
Acan vangaren sarki Amjadu da sarki
Dambola kuwa al’amarin ya qazanta babu kyan
gani, bambancin a bayyane yake sarki Dambola
yafi sarki Amjadu girman jiki karfin damtse da
iya yaqi amma shi kuma sarki Amjadu yana da
tsananin juriya da naci. Sai da sarki Dambola ya
yanke shi sau shida a sassan jikinsa jinni na zuba
amma saboda baqin naci bai faxi qasa ba yana
daxa kai masa sara da suka gami da kare hareharensa ana cikin hakanne shima sarki Amjadu
ya shammaci sarki Dambola ya zaro wata

40

Sarauniyar daji

siririyar wuqa mai tsinin tsiya ya soka masa a
cikin idonsa na hagu. Wuqar ta lume a cikin
kwarmin idon sarki Dambola ya kurma uban ihu
a lokacin da jini ke zubowa shima sai ya
shammaci sarki Amjadu ya zaro tasa wuqar
wacce ta kai tsawon kamu huxu ya soka masa ita
a qirji sarki Amjadu ya kurma uban ihu ya
durqushe qasa bisa guiwoyinsa jin ihun nasane
yasa Rasina ta juyo ta kalleshi, damar da boka
kurjalu ya samu Kenan uya soka mata takobi a
gadon bayanta ta vollo ta cikinta Rasina ta
durqushe qasa bisa guiwoyinta biyu iyama ya
kurma ihu tana kallon mijinta wanda kecan gaba
da ita kaxan durqushe bisa guiwoyinsa yana kan
gargara mutuwa. Hawaye ya zubowa Rasina a
lokacin da jini ya vulvulo daga cikin bakinta, Ita
da sarki Amjadu suka qurawa juna idanu sai taga
Amjadu yana yi mata murmushi duk da cewar
yana yin aman jini, boka kurjalu ua matso kusa
da Rasina yana yi mata murmushin mugunta ya
xaga takobinsa sama da nufin ya falle mata kai
kawai sai sukaga ta sunkuya ya sari iska kafin ya
kawo mata wani harin ta xauki takobinta ta sare

41

Sarauniyar daji

masa hannunsa na dama. Fit! Hannun ya cire ya
yi sama ya qwala ihu jini ya soma vulvulowa ta
cikin dungulmin hannun Boka kurjalu ya kama
hargowa.
Sarki Dambola ya rugo gareshi ya cire
rawaninsa ya nanaxe dungulmin hannun don
tsayar da jini, a sannane shima ya zare wuqar
dake cikin ramin idanunsa ya jefar da ita qasa
kuma yayi sauri ya toshe ramin idon da tsumman
rigar sa daya yaga. A wannan lokacine Rasina ta
dubi sarki Amjadu ta maida masa martanin
murmushin sannan ta vingire qasa matacciya.
Take shima sarki Amjadu ya soma kakarin
mutuwa sarki Dambola ya taka ya qara yace
masa “Yanzu gashi kai da matarka kunje qasa,
ita ta zama gawa kai kuma yanzu zaka zama
gawar mu kuma daganan zamu qara gaba mu
riski ‘yarka Lashmin da sarkin yaqinka mu kashe
su, wacce riba kuka ci kai da jama’arka a
wannan yaqin?”Sarki Amjadu ya buxe baki da
qyar yace.
“Munci babbar riba guda biyu, riba ta farko ni
na mayar da sarkin Hindu musaki ya zama me

42

Sarauniyar daji

ido xaya, matata ma ta mayar da bokan Hindu
musaki ya zama mai hannu xaya, ku xinan a
musakai za ku mutu kuma baku isa ku goge
tarihin wannan ranar ba, riba ta biyu burinmu zai
cika zuri’ar mawardi za su ci gaba da yaxuwa a
duniya don ba zaku tava risker Aryan da
Lashmin ba kuma indai da rai da rabo Lashmin
zata girma kuma zata shigo har cikin fadarka ta
kashe ka...” Kafin Amjadu ya gama rufe bakinsa
tuni sarki Dambola ya saka takobinsa ya fille
masa kai, kansa ya yi sama ya gangara can gefe
xaya amma gangar jikin na tsaye a durqushe bata
faxiba. Mamaki ya kama sarki Dambola ya dubi
gangar jikin Amjadu sannan ya dubi boka
kurjalu yace.
“Tabbas sarki Amjadu jarumine na qwarai
saboda shine mayaqi na farko a tarihin rayuwata
wanda ya sami nasarar lalata mini idona guda
xaya, matarsa ta cika jaruma ta gaske wacce ba
za a tava mantawa da ita ba tunda itama ta
cirewa durka Hindu hannunsa guda xaya, dole
mu yi musu kabari anan mu bar shaida akan

43

Sarauniyar daji

kabarin domin su zama a cikin tarihin jaruman
duniya”Boka Kurjalu yace.
“Anya ba zamu yi nadamar yi musu wannan
kabarin ba”Sarki Dambola yace.
“Ba za mu yi ba, saboda kabarin nasu ne zai
janyo abokiyar gabata ta kawo kanta cikin
qasata”.
Ba tare da vata lokaci wani lokaci ba Boka
kurjalu ya taimakawa sarki Damboka suka haqa
kabari guda biyu suka jefa gawar sarki Amjadu
data matarsa Rasina a ciki. Dambola ya xauko
kan sarki Amjadu ya cila a cikin ramin suka
mayar da qasa suka rufe suka soka takobin sarki
Amjadu da ta Rasina a ciki, har sarki Dambola
ya miqe zai bar wajen sai ya lura anyi wani
rubutu a jikin qotocin takobban amma da yaren
mutanen birnin sin ne, ya juya ya qurawa
rubutun idanu sannan ya dubi takubban da kyau
ya juya ya kalli Boka Kurjalu yace.
“A
ina
ake qera
irin waxannan
takubban?”Boka Kurjalu yace “A qasar sin aka
qera su”.

44

Sarauniyar daji

“To me aka rubuta a jikin kowacce
takobin?”Ya matsa sosai ya dubi takobin yace
“A jikin ko wacce an rubuta sunan me
mallakarta, sunan Amjadu dana Rasina a jikin
kowace takobin”Sarki Dambola ya yi murmushi
yace “Hakan ya yi daidai zo mu tafi
gida”Mamaki ya kama Boka kurjalu yace
“Bangane mu tafi gida ba, ai kamata ya yi mu bi
bayan Aryan da Lashmin mu riske su kafin su
fita daga cikin yanki qasarmu tunda za mu iya
riskarsu da qarfin sihirina da zarar sun shiga
wani gari”Sarki Dambola yace.
“Kai kayi Imani da tsafinka ni kuma nayi
Imani da qaddarata, inda zan sami nasarar kashe
wannan yarinyar a wannan lokacin da bata sami
nasarar guduwaba. Yanzu zan sanar da kai wani
abu wanda baka sani ba, kana zaton kai kaxaine
kasan da wannan mafarkin na bishiyar data shigo
har cikin fadata ta kashe ni, to ba kai kaxai bane
a wannan mafarkin sai dana tashi manzani guda
uku a sirrance na aika da su qasar sin, qasar
Romaniya da kuma qasar Askandar suka gana da
manya bokaye na qasashen uku waxanda babu

45

Sarauniyar daji

kamarsu, suka sanar da su wannan mafarkin suka
fassara musu kamar yadda kaima ka fassarashi
amma shi bokan sin ya tabbatar mini da cewar
bazan iya kashe lashmin ba dole sai bayan ta
cika shekara goma sha takwas, kuma dole sai an
yanko mun gashin kanta na vangaren qarqashin
qeyarta da wannan gashine kawai za a iya haxa
sinadarin makamin da zai iya kasheta” A lokacin
da sarki Dambola ya zo nan a maganarsa sai
mamaki ya kama Boka kurjalu ya yi shiru yana
kallonsa kawai kuma ya tambayi kansa a cikin
zuciya yace ashe dama sarki ba da ni kaxai ya
dogara, indai hakane ba zan tava cika burina
akansa ba, don haka ya zama dole nima nasan
hanyar da zanbi nima na cika babban burina na
duniya.
Nan dai sarki Dambola da Boka kurjalu suka
saka magani a cikin raunikansu. Sarki Dambola
ya xauko wani baqin qyalle mai siririyar igiya a
jikinsa ya rufe ramin idonsa dashi. Ba tare da
vata wani lokaci ba suka hau dawakansu suka
juya da baya suka nufi qasar Hindu.
**

46

Sarauniyar daji

A lokacin da sarki Dambola da Boka Kurjalu
suka iso cikin fadar Hindu alfijir ya keto amma
kuma gari da duhu bai haske ba. Duk su biyun
sun lulluve jikinsu da fuskokinsu gaba xaya su
kansu dakarun da suke gadin qofar gidan
sarautar da dawakansu suka shaida su da kuma
makamin yaqin dake jikinsu sannan suka buxe
musu qofa suka shiga. Maimakon su rabu ko
wanne ya wuce zuwa wajen iyalinsa sai suka
wuce kai tsaye zuwa turakar sarki suka zauna a
babban falon da sarki ke ganawa da baqinsa.
Bayan an kawo musu abinci da kayan
marmari dana shaye-shaye sai sarki Dambola ya
dubi Boka kurjalu yace “Kasan dalilin daya saka
na taho da kai nan cikin turakata kuwa?”Kurjalu
yace ‘Ban sani ba ya shugabana sai ka sanar
dani” Sarki Dambola yace.
‘Bana son duniya tasan na rasa ido xaya kai
kuma ka rasa hannu xaya, don haka ta yaya za
mu iya voye wannan naqasar?” Boka kurjalu ya
yi shiru yana nazari har zuwa wasu ‘yan lokuta
yace “Hanya xayace za mu iya voye wannan
naqasar ka tura a kirawo mana sarkin maqera a

47

Sarauniyar daji

qera mana abubuwa guda biyu, kai a qera maka
ido na qarfe wanda za a ga kamar kana gani da
shi, ni kuma a qera mun hannun qarfe mai yatsu
wanda yatsun na iya motsawa, ta hakane kawai
za mu iya voye wannan naqasar tamu”Sarki
Danbola ya yi murmushi yace.
“Tabbas sarkin maqera zai iya wannan aikin
to amma kuma ai shi yasan sirrinmu Kenan?”
“Yana gama aikin sai mu sa a kashe shi a
sirrance xansa zarhas ya gaje sa don shima ya
iya qira zai maye gurnbinsa” Sarki Dambola ya
rungume Boka kuljalu yana mai cewa “Kana da
matuqar basira gami da hangen nesa shi yasa
bani da kamarka a duniya” Kurjalu yace a cikin
ransa ‘qarya kake tsohon abokina inda baka da
kamata da ba ka yi mu’amala da sauran Bokayen
duniya ba babu komai zan jira lokacin da burina
zai cika akanka’
Kamar yadda Boka kuljalu ya bayyanar da
shawara haka al’amarin ya kasance kashe gari da
sassafe sarki Dambola ya tura aka kirawo masa
sarkin maqera Abnash wani dattijo ne wanda

48

Sarauniyar daji

shekarunsa sun haura saba’in kai tsaye aka kai
Abnash har cikin turakar sarki Dambola, yana
shiga ya samu harda Boka kurjalu a zaune
hidimin daya raka shi ya fita ya barsu su uku.
Yana fita sai sarki Dambola da Boka Kurjalu
suka rufe duka tagogi da qofofin xakin abinda ya
razana Abnash ya yi zaton ko kashe shi za su yi
sarki ya dube shi cikin murmushi yace.
“Kwantar da hankalinka ya shugaban maqera,
kayi sani cewar mun kiraka nanne domin kayi
mana wani aiki na musamman”Yana gama faxin
haka sai ya cire qyallen daya rufe idonsa koda
Abnash yaga ashe sarki ya rasa ido guda sai yaja
da baya ya razana shima Boka kurjalu sai ya fito
da yankaken hannunsa guda. Abnash ya qara
firgita kuma ya kumu da tsananin mamaki ya
durqusa bisa guiwoyinsa biyu a gaban sarki
Dambola yace.
“Ya shugabana garin yay aka rasa idonka
guda xaya shi kuma boka kuljalu ya rasa
hannunsa xaya?”Sarki yace.
“Sanin haka bas hi ne mai muhimmanci ba
yanzu, abinda muke da buqata daga gareka shi

49

Sarauniyar daji

ne kayi muni do na qarfe wanda mutane za su
kasa gane cewar na rasa ainahin nawa shi kuma
kurjalu ka qera masa hannu na qarfe me yatsu
wanda yatsun za su riqa motsawa yadda ba za a
gane ya rasa hannunsa guda ba” Koda jin haka
sai sarkin maqera Abnash ya yi ajiyar zuciya
kuma ya gane lallai a wannan yaqin da suka
fitane suka sami wannan naqasa kuma basa so
duniya ta sani. Abnash ya dubi sarki Dambola
cikin girmamawa a lokacin daya miqe tsaye daga
durquson daya yi yace.
“Ya shugabana tabbas zan iya wannan aikin
amma aqala sai ya xauke ni kwana bakwai”Sa’ar
da sarki da kurjalu suka ji haka sai suka dubi
junansu, sannan kurjalu yace.
“Shin ba zaka iya gama wannan aikin a cikin
kwana uku ba? Shin kai xaya za ka yi ko da
mutanenka” Sarkin maqera yace.
“Ba zai yiwu a gama wannan aikin a cikin
kwana uku ba, kuma mutum xaya ne zai tayani a
cikin wannan aikin shi ne xana yarima
Ashtar”Koda jin haka sai mamaki ya kama sarki
Dambola yace “Saboda me sai sai xana ne zai

50

Sarauniyar daji

taimaka maka, shin me ya haxa xana da harka
qira”Maqeri Abnash ya yi ajiyar zucita sannan
yace.
“Ya shugabana ai tun daga ranar daka hana
yarima Ashtar zuwa fada sai yaji babu abinda
yake so sama da harkar qira don haka kullum
yana gidana yana koyon wannan sana’ar wani
abin mamaki shi ne duk abinda na koya masa
kafin sati xaya ya zagayo sai naha ya fini
qwarewa akan abin, sannu a hankali sai nake
ganin yana qirqiro abubuwan da ni kaina ban
tava tunanin samar da su ba, a halin yanzu yafi
xana iya qira da qirqira ni kuma ina xaukar
darasi ne a wajen yarima Ashtar ko shakka bana yi
idan naje masa da wannan maganar zai iya qera
waxannan abubuwan guda biyu da kuke so, babu

mamaki shi ya iya qera su a cikin kwana uku
maimakon kwanaki bakwai dana ce”Lokacin da
sarkin Maqera Abnash ya zo nan a maganarsa sai
hankalin sarki Dambola ya tashi ya ja Boka
Kuljabu izuwa gefe xaya inda Abnash

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment