You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turakar yana ganinta sai ya
xaure fuska yace.
“Ke kuma mene ya shigo dake cikin turakata yau?
Kina sane rabon dana buqace ki tun ranar dana kori
xanki daga cikin fada” A lokacin ya juya mata baya
don haka bataga abinda ya sami idonsa guda ba
kuma dama fuskar tasa a rufe take cikin baqin
rawani. Shanina ta risina a gareshi tace.
“Ya shugabana banzo gareka domin komaiba sai
domin na nemi alfarma guda xaya a wajenka” Sarki
Dambola yace “Maza ki faxi buqatarki domin na
sallameki ki barmun xakina saboda idan ina kallon
fuskarki zan iya cutar dake bisa qiyayyar xanki ya
shafa miki” Shanina taji wani baqin ciki ya shigeta
ta tuna cewa itace fa kaxai a cikin matarsa wacce ta
Haifa masa magaji amma gashi yayi mata tsanar da
babu wacce ya yi wa kamarta a cikin matansa.

75

Sarauniyar daji

Kawai sai taji hawaye baqin ciki ya zubo mata
amma sai tayi sauri ta share hawayen, ba tare da ta
xago kai ta dubeshi ba sai tace.
“Ina son kayi mini izini naje gidan sarkin maqera
domin na gana da xana Yarima Ashtar saboda yau
wata uku Kenan bai ganni b anima ban gansa” Yace
mata.
“Na amince kije ki gana da xanki idan kin so ma
ki zauna a gidan iya tsawon lokacin da kike so
domin kuyi bankwana saboda kwanannan zaki rabi
da shi kuma rabuwa ta har abada” Koda jin wannan
batu sai alamun firgita su ka bayyana akan fuskarta
shanina tayi ajiyar zuciya sannan tace.
“Godiya nake ya sarkin duniya kuma ina
nemawa xana afuwarka” Tana gama faxin haka sai
ta juya ta nufi hanyar fita koda ta iso daf da qofar
fitar sai ta tsaya a gaban wani masaki na zinare
sannan ta juya ta kalli sarki Dambola sai taga har
yanzu bai juyo ya kalleta ba yana ta xaura wannan
baqin rawanin a kansa, cikin hanzari Shanina ta
xauko wata jakar fata daga cikin rigarta ta xorata
akan wannan masakin sannan ta fice da sauri daga
cikin gidan sarautar gaba xaya.
Shi kuwa sarki Dambola bayan ya gama naxa
baqin rawani ya zamana cewar bakinsa da hancinsa
76

Sarauniyar daji

ne a waje kaxai, idanunsa kuma ba’a gani amma shi
yana ganin komai sai ya zauna akan gefen gadonsa
nab arci ya xauko takalmansa ya sanya, ya xauko
sandarsa ta mulki ya riqe bayan ya yafa alkyaba
kawai sai yaje gaban madubi ya tsaya yana kallon
kansa, koda yaga cewar ba’a ganin idanunsa sai
hancinsa daya kwanta ya juya ya nufi qofar fita daga
cikin turakarsa sai ya tsaya caky a juya ya kalli cikin
masakin zinare, bisa mamaki sai yaga baquwar jakar
fata akan wannan akushi na zinare.
Ya dubi jakar yace a cikin ransa ko a jiya babu
wannan jakar a nan wajen koma bansan da zamanta
ba a cikin xakina, waye ya kawota ya ajiye? Ba
wani bane ya kawo jakarnan face matata shanina
kuma yanzunnan da zata fita ta ajiyeta. Bari na buxe
jakar naga ko mene a ciki, nan take ya buxe koda ya
yi arba da abinda yake ciki nan take hankalinsa ya
dugunzuma, ba komai ya gani a ciki ba face ido da
hannun qarfe.
Nan take sarki ya qwalawa wani hadiminsa kira
da qarfi hadimin ya shigo a gigice ya faxi qasa a
gabansa, sarki Dambola ya dubeshi yace.
“Ayi sauri aje a kirawo mun boka kurjalu, kuma
a haxamun runduna ta mayaqa guda dubu” Hadimin

77

Sarauniyar daji

ya miqe tsaye yana mai cewa “An gama ya
shugabana”.
Sarki Dambola ya koma ya sake zaunawa a gefen
gadonsa a lokacin da zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata qone, fuskarsa ta kama yin gatsine
kamar zata zazzago qasa. Jim kaxan da fitar
hadiminsa sai ga Boka kurjalu ya shigo cikin turakar
a cikin sauri-sauri gudu-gudu da zuwansa ya risina
yak washi gaisuwa yace.
“Ya sarkin duniya menene ya faru kayi mini
kiran gaggawa haka?” Maimakon sarki Dambola ya
bashi amsar wannan tambayar sai kawai ya miqa
tsaye yaje wajen wannan jakar fatar ya zura hannu a
cikinta ya fiddo ido da hannun qarfe ya nunawa
Boka kuljalu ya miqe tsaye zumbur cikin hanzari
yace.
“Ta yaya Abnash da Ashtar suka gama qera
wannan idon da hannun qarfen a cikin kwanaki
huxu rak, kuma ta yaya abin ya zo nan?” Sarki
Dambola yace.
“Duk yadda kake zaton xana Ashtar ya wuce nan,
shi ne ya qera abubuwan nan guda biyu kuma shi ne
ya baiwa mahaifiyarsa kayan yanzunnan ta shigo da
su ta ajiye su ban sani ba, tabbas ya gane za mu
kashe sarkin maqera don haka ya xauke shi tare da
78

Sarauniyar daji

matarsa suka gudu, bama iya sub a harda matata
shanina mahaifiyarsa ya xauketa daga cikin gidan
sarautarnan sun gudu tare, don haka ina son kayi
sauri ka saka hannunan naka na qarfe ka gwada mu
gani idan na yi ina son kaje ka xauki dakaru guda
dubu ku bi bayan su Ashtar, lallai ina son kafin nan
kafin faxuwar rana ka dawo mun da su cikin gidan
sarauta”.
Koda jin haka sai Boka kuljalu ya yi sauri ya cire
rigar dake jikinsa da hannunsa xaya mai kyau
sannan ya xauki wannan hannun qarfe ya sokashi a
cikin yankakken hannunsa. Take hannun qarfen ya
zauna daram a cikin dungulmin tamkar da shi aka
halliceshi yana motsa hannun sai yaga yatsun qarfen
ma suna maotsawa cikin farin ciki suka dubi juna
shi da sarki Dambola.
Boka kuljalu yace “Aikin xanka ya yi kyau duk
da cewar ya ci amanarmu, yanzu nan zanje na dawo
maka da su su duka, yana gama faxin haka sai ya
juya da sauri ya fice daga cikin turakar yana fita sai
shima sarki Dambola ya xauki nasa idon na qarfe ya
xorashi akan fuskarsa, idon ya rufe kwarmin idon
yadda ba za’a tava gabe cewar idonsa guda ya lalace
ba wasu ma zata za su yi wani nau’i ne na ado ko
kuma na tsafi.
79

Sarauniyar daji

Sarki Dambola jaye gaban madubi ya kalli kansa,
koda yaga yadda idon qarfen ya yi masa kyau sai ya
bushe da dariya mugunta yace.
“Lokaci ya yi da zan fara kafa tubulin cikar burin
rayuwata” Yana gama faxin haka sai sarki Dambola
ya haxe fuska yace “Ta yaya shanina zata iya
vacewa daga cikin gidanan lokaci qanqani haka,
duk yadda aka yi yarima Ashtar ne ya shirya mata
komai domin babu wanda ya fishi sanin sirrin
gidanan, wannan shi ne babban kuskurena na farko a
rayuwa.
Sarki na gama wannan zancen zuci a fili sai ya
juya ya fice daga cikin turakar tasa ya nufi fada kai
tsaye domin yaje ya yiwa fadawa jawabin da suke so
suji.
**
Al’amarin shanina kuwa tana fita daga cikin
turakar sarki Dambola sai tabi wata hanya wacce
zata kaita izuwa inda kwatar gidan sarautar take tana
tafe cikin sauri tana waigen bayanta don tabbatar da
cewar babu wanda ya biyo bayanta. Da isowarta
inda ruwan kwatar yake wucewa ta cikin wani
bututu na qarfe sai ta saka hannunta ta qwanqasa
bututun sau uku, faruwar haka ke da wuya sai ga

80

Sarauniyar daji

Ashtar ya shigo ta cikin ruwan kwatar a cikin wani
xan qaramin kwale-kwale.
Shanina tana ganinsa ta ruga ta shige cikin
kwale-kwalen suka juya da baya da sauri suna tuqa
kwale-kwalen da gudu, asha can qasan wannan
kwatar wani kogine mai zurfin tsiya kuma gashi da
girma da yawa.
Suna iso wa wannan wurin sai Yarima Ashtar ya
yi sauri ya rungume mahaifiyarsa ya juyar da ita don
kar ta firgita bisa ganin zurfin kogin da za su faxa.
Ai kuwa sai kwale-kwalen ya faxa da su cikin kogin.
Ashtar ya yi sauri ya sake rufe idanun
mahaifiyarsa da hannunsa, ita dai taji kamar a
sararin samaniya take shawagi sai bayan daqiqu
masu xan yawa sannan taji sun faxo cikin kogi
tsundum! Da su da kwale-kwalen suka nutse izuwa
qasan ruwa, Ashtar bai saketa ba sai ya ci gaba da
linqaya a cikin qarqashin ruwa har suka iso can
bayan kogin suka fito saman ruwa suka kawo bakin
gaba.
Sun jiqe sharkaf da ruwa, Shanina ya waigo baya
ta dubi nisan tazarar dake tsakanin can sama da suka
faxo sai ta cika da mamaki nan ma ta dubi girman
kogin ta qara cika da mamakin yadda suka yi
ninqaya cikin qanqanin lokaci har suka iso bakin
81

Sarauniyar daji

gava ba tare da sun jigata ba. Har ta buxe baki zata
yi Magana sai taga Ashtar ya kama hannunta ya jata
da gudu sun bar wajen.
Ai kuwa suna barin wajen sai ga dakarun sarki
Dambola sun zo wajen su kimanin xari uku a bisa
dawakai, suka kama dudduba ko ina a wajen, abinda
ba su sani ba tuni Ashtar da mahaifiyarsa sun shige
cikin duhuwar ciyayi sun nausa daji da gudu, ta
cikin dajin ne suka bi wata hanya ta kai su har zuwa
cikin tsohon gidan bauta, da gudu suka shige cikinsa
suka isa wajen da raminnan yake na qarqashin qasa
da zuwa sai yarima Ashtar ya buxe ramin suka shige
ciki ya janyo qofar katakon ta sake rufe ramin.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga Boka kuljalu
tare da dakaru ma su yawa sun shigo cikin tsohon
gidan bautar akan dawakai, Boka kuljalu ya xaga
hannu kowa ya ja linzamin dokinsa aka tsaya cak
kuljabu ya sauko daga kan dokinsa ya kama kallekalle a cikin gidan yana dube-dube sai daya duba ko
ina da ina baiga alamar su Ashtar ba, sai ya juya da
baya ya nufi wajen da dokinsa yake har ya kama
dokinsa zai hau sai ya tsaya ya juyo ya dubi inda
qofar ramin nan take na qarqashin qasa.
Ba komai ne ya ja hankalinsa ba face hango wani
fure na kanshi guda ya faxo qasa, shi dai wannan
82

Sarauniyar daji

furen babu ma su amfani da shi sai matan sarki
kuma suna yin adone da shi akan gashinsu, hakane
ya saka ya gane cewar shanaina ta shigo cikin
wannan tsohon gidan bautar. Kurjalu ya durqusa
qasa ya xauki furen yakalleshi sannan ya kalli qasa
inda ya xauki furen kawai sai ya saka hannunsa na
qarfe ya qwanqwasa wajen sai yaji alamar katako,
kawai sai ya saka hannunsa na qarfe ya daki katakon.
Ta ke katakon ya vurme sai ga rami ya baiyana
zururu a wajen gaba xaya ya juya ya dubi dakaru
yace.
“Ga hanyar da Ashtar da mahaifiyarsa suka bi
don guduwa daga cikin garinnan ku zo mu bisu da
sauri mu qure musu gudu kafin su isa iyaka” Yana
gama faxin hakan sai ya faxa cikin ramin ya falfala
da gudu , ai kuwa sai suma dakarun suka bishi da
gudu izuwa cikin wannan ramin.
Lokacin da Ashtar da mahaifiyarsa suka fara
gudu a cikin wannan ramin sai shanaina ta fara
gajiya, kawai sai ji ya yi tayi tuntuve a bayansa ta
faxi qasa. Cikin hanzari ya tsaya caky a juyo ya
xauketa ya goyata a bayansa ya falfala da azababben
gudu a cikin ramin saboda yasan cewa a koda
yaushe za’a iya gano inda suka shiga a biyo bayansu.

83

Sarauniyar daji

Haka yaci gaba da wannan gudu yana goye da
mahaifiyar tasa har ya iso qarshensa ya fito saman
daji ya iso inda ya ajiyewa sarkin maqera dawakai,
suka iske doki guda xaya nan ya xora mahaifiyarsa
akai ya yi tsalle ya hau gaba yace ‘Umma ki
ruqunqumeni” Ba tare da wata gardama ba kuwa ta
ruqunqumeshi ai kuwa sai ya sakarwa dokin linzami
ya zabureshi da gudu, ai kuwa sai dokin ya kama yin
wani irin azababben gudu na ban al’ajabi.
Shi dai wannan dokin tun yana qarami Yarima ya
rene shi don haka shi ne ya bashi horo na gudu da
jure wahalar daji data yaqi da kansa. Babu wanda
yasan cewar wannan doki babu mai qarfin gudunsa
a cikin dukkanin dawakan birnin Hindu face Yarima
Ashtar shi kaxai.
Lokacin da Boka kurjalu da dakarunsa suka fito
daga cikin ramin sai suka hango yarima Ashtar a can
gabansu ya basu tazara mai yawan gaske wacce ba
za su iya cimmasaba tunda ya basu tazara me yawan
gaske koda ganin haka sai Boka kurjalu ya yi tsafi
nan take wasu baqaqen dawakai ma su yawa suka
sauko qasa daga sararin samaniya kuma ko wanne
doki akwai siddi da linzami a jikinsa.

84

Sarauniyar daji

Cikin hanzari kowa ya kama nasa dokin ya hau
suka bi bayan Yarima Ashtar a guje cikin azababben
gudu bisa qarfin sihirin tsafi.
**
Yarima Ashtar tare da mahaifiyarsa shainana na
bisa doki guda suna ta faman tsala gudu kawai sai
suka jiyo sukuwar dawakai da yawa a bayansu masu
yawan gaske, Ashtar ya juya yaga ashe su Boka
kuljalu ne suka biyo su kuma tsakaninsu bai wuce
taku xari ba, al’amarin da ya yi matuqar ba shi
mamaki, ta yaya su kuljalu suka riskesu alhalin ya
tabbatar da cewar tazarar da suka basu ba kaxan
bace.
Nan fa hankalin Ashtar ya tashi ainun yace
“Yake Ummina nayi iyakar qoqarina domin na
kuvutar dake daga sharrin sarki amma gashi qarfina
ya qare, nan da xan qanqanin lokaci boka kuljalu za
su riske mu su kamo su mayar da mu ga azzalumin
mahaifina” Koda jin haka sai tace masa.
“Kwantar da hankalinka ya xana ai dawakan da
suka Boka kuljalu suka hawo na tsafi ne, yau ni
kuma zan nuna maka nawa qarfin tsafin wanda ban
tava jarraba aiki da shi ba, juya kaga abinda zai
faru” Gama faxin haka sai shainana ta juyo ta
hurawa su Boka kuljabu iskar bakinta. Nan take
85

Sarauniyar daji

iskar bakinta ta zama wuta, wutar ta tafi da gudun
tsiya ta feshe dawakan da su Boka kuljabu ke kai,
nan take dawakan na su suka qone qurmus suka
zama toka.
Boka kuljabu da dukanin dakarunsa suka faxo
qasa cikin galabaita, amman wutar data qone
dawakan bata qone su ba, suna ji suna gani Yarima
Ashtar suka tsallaje iyakar birnin Hindu suka faxa
cikin qasar karnad.

SHEKARU NA SHUDEWA. ZAMANI NA
SAUYAWA.
SARAUNIYAR DAJI:-Ta qara girma.
YARIMA ASHTAR:- Shekaru sun qaru
SARKI DANBOLA:-Na jiran Lashmin ta cika
shekaru goma sha takwas.
Shekaru na shuxewa zamani na sauyawa har aka
sami shekara goma sha xaya da faruwar wannan
al’amarin. A wannan lokacin Gimbiya Lashmin ta
zama cikakiyar budurwa kyakkyawar gaske kuma ta
zama gagarumar mayaqiya mai mulkin dukkanin
dazuzzukan dake cikin qasar karnad har ta kai cewar
hatta sarkin qasar karnad tsoronta yake ji don haka
86

Sarauniyar daji

duk abinda take buqata daga gareshi da rawar jiki
yake yi mata.
Wata rana sai sarauniyar daji sarauniya Lashmin
ta shirya gagarumar gasa ta jarumtaka a qofar
gidanta na sarauta. A wannan lokacin garin nata ya
bunqasa da arziqi saboda kasancewarsa babbar
cibiyar kasuwanci na siyar da fatocin dabbobi da
sassan jikinsu. Baqi suna shigowa garin sosai ana
samun maqudan kuxaxen shiga.
Yanayin wannan gasar shi ne duk jarumin daya
iya kai sarauniya Lashmin qasa ko kuma ya iya yi
mata rauni zata ba shi babban matsayi a fadarta
gami da dukiya mai yawan gasket un safe aka fara
wannan gasar har la’asar tayi ba’a sami jarumi gudu
xaya ba wanda ya sami nasarar kai sarauniya qasa
ba ko yi mata rauni alhalin ta fafata da mazaje guda
saba’in da biyu.
Duk jarumin data fafata da shi cikin ‘yan daqiqa
take kaisa qasa an gama da shi Kenan, kafin mutum
ya shiga wannan gasa sai ya biya dinare dubu goma
don haka manyan kuxaxe sarauniya Lashmin ta tara
a dalilin wannan gasar.
Bayan Lashmin ta sami nasara akan jarumai
saba’in da biyu sai ta fito daga cikin filin gasar da

87

Sarauniyar daji

nufin ta shige cikin gidan sarauta, fadawa sun
kewayeta domin yi mata rakiya.
Kwatsam sai aka jiyo muryar wani jarumi daga
can nesa yana mai xaga murya yana cewar “Ga
baqon jarumi da zai kai sarauniya qasa ya zo, ina
sarauniyar take ta dawo mana mu fafata ko kuwa ta
tsoratane dani” Koda sarauniyar taji wannan kurin
da wannan baqon jarumi yake yi sai ta juyo a fusace
ta qura masa idanu a lokacin da ya tunkaro qofar
gidan sarautar bisa doki.
Shi dai wannan jarumin ya kasance matashin
saurayi wanda shekarunsa ba za su wuce ashirin da
huxu ba, kyakkyawa ne na kwatance kamar
sarauniya kuma yana da cikakkiyar sura irinta
manya sadaukai shigar yaqi ya yi irin ta mafarauta.
A wannan lokacin sarkin yaqi Aryan na can gefe
xaya a tsaye ya fara tsufa yana ganin wannan jarumi
sai ya tuno da fuskar sarki Dambola take zuciyarsa
ta buga da qarfi a zuciyarsa yace anya wannan ba
shi ne Yarima Ashtar ba xa ga sarki Dambola, to
amman shi Yarima Ashtar an koreshi daga fada tun
yana yaro kuma sarki Danbola ya tsane shi harma ya
so kashe shi kamar yadda ya samu labara daga
wajen fatake. Don haka tabbas idan shi ne ba zai zo
domin cutar da kowa ba.
88

Sarauniyar daji

Baqon jarumi ya iso qofar gidan sarauta ya sauka
daga kan dokinsa yaje ya biya dirhami dubu goma
kuxin shiga gasa, sannan ya shiga cikin tsakiyar filin
gasar ya tsaya yana murmushi kuma ya qurawa
sarauniya Lashmin idanu yana jira ta qaraso cikin
filin gasar.
Koda ganin hakan sai sarauniya Lashmin ta taho
da sauri cikin tsananin fushi gami da mugun nufi,
tun kafin ta qaraso cikin filin gasar ta zare takobinta
ai kuwa sai ta falfalo da gudun gaske izuwa kan
baqon jarumin ta daka tsalle sama ta kai masa
wawan sara a kafaxa da nufin ta tsargashi gida biyu.
Cikin wani irin baqin zafin nama jarumi ya zare
takobinsa yak are saran data kawo masa, nan fa suka
ruguntsume da azababban yaqi na ban al’ajabi
wanda ba a tava ganin irinsa ba a garin. Wani irin
yaqi suke yi na nuna tsagwaron jarumtaka, qwarewa
da zafin nama gami da kaiwa juna naushi da bugu da
hannu da qafa, sai da suka shafe sa’a uku cur suna
baqin artabu. Gashi dai suna kaiwa junansu sara da
suka amma babu wanda ya sami nasarar koda
yakushin jikin xan uwansa haka kuma duk irin
naushi da bugun da sukewa juna ko wannensu na
shanye dukan sunqi yarda suje qasa a haka suka
haxawa junansu jini da majina har ya zamana sun
89

Sarauniyar daji

jigata ainun amma saboda baqin naci sunqi faxuwa
qasa jama’a yan kallo kuwa sai ihu suke yi suna
qara musu qaimi.
Manya attajirai dake wajen kuwa sai suka fara
yin caca kowa nasa kuxaxe masu yawa da ba’a tava
sakawa a wannan gasar kowa na burin cewar
gwaninsa ne zai cinye wannan gasar.
Suna cikin wannan gumurzun ne suka kawowa
juna sara da takobi a lokaci guda ta kubban na sun a
haxuwa sai suka manne kowannensu ya fara qoqarin
danna abokin faxansa qasa da dukkan qarfinsa
amma aka rasa me nasara sai dai aga sunyi baya sun
yi gaba a lokacin sarauniya Lashmin ta dubi baqon
jarumin tace.
“Waye kai kuma daga ina ka fito” Ya yi mata
murmushi yace mata.
“Sunana Yarima Ashtar daga qasar Hindu na
fito” Tana jin haka sai ta fusata ainun suka sake
ruguntsumewa da da masifaffan yaqi dayafi na farko.
Suna cikin wannan fafatawar sai takubban na su
suka karkarye suka zubar da suka sake kaurewa da
kokawa suna dukan juna da gware a haka sai da
suka xauki sa’ani uku kafin lokaci guda su duka
biyun suka yanke jiki a tare suka faxi qasa a sume.

90

Sarauniyar daji

Ganin haka sarkin yaqi Aryan ya rugo da gudu
ya xauki sarauniya ya nufi cikin gidan sarauta da ita,
shima Aryan fadawa suka xauke shi daga tsakiyar
filin.
Bayan aqala sa’a uku sannan sarauniya Lashmin
ta farfaxo daga suman data yi, koda ta buxe
idanunta taganta akan gadonta sai ta yi zumbur ta
miqe zaune ta soma qoqarin qara surar makaminta
da zumar komawa filin fama.
Ganin haka sai sarkin yaqi Aryan ya yi saurin
shan gabanta yace mata “Ya kamata ki kwanta ki
huta” Ta xaga idanu cikin tsananin fushi tace masa
‘Ta yaya zan huta alhalin xan maqiyina yana qasarta,
tabbas a yau xinan sai na saro kan Yarima Ashtar
daga nan kuma na zarce har zuwa birnin Hindu na
saro kan mahaifinsa” Koda jin haka sai hankalin
sarkin yaqi Aryan ya dugunzuma.
“Kar kiyi gagawa ya shugabata” Ta tsare shi da
idanu.
“Shin ka mance abinda mahaifinsa ya aikata
mana? Ka mance gisan gillar daya yi wa zuri’ar mu?
Har ka mance da iyalinka daya halaka?” Sarkin yaqi
Aryan yace mata cikin tafarsa zuciya da vacin rai na
tuna abinda ya faru.
91

Sarauniyar daji

“Ban mance ba” A hankali yace mata.
“To matsa na je na saro kan abokin gabana…”
Kafin ta qarasa Magana sai taji wata siririyar murya
ta ratso cikin tsakiyar xakin tana cewa da ita.
“Ba za ki iya kashe Yarimya Ashtar ba, kamar
yadda shima ba zai iya galaba akan ki ba face ku yi
ta ragas” Koda jin haka sai su duka suka soma
waige-waige a cikin xakin Gimbiya Lashmin suna
son ganin mai wannan maganar amma ba su ga
kowa ba. Bayan daqiqa biyu sai aka yi dariya aka
qara cewa da su “Ba za ku tava ganina ba face na
bayyana a gareku” Ana gama maganar sai shainana
ta bayyana a tsakar xakin.
Ai koda sarkin yaqi Aryan ya ganta sai ya qura
mata idanu ya kasa xauke idanunsa daga kanta, haka
itama Sarauniyar Lashmin ta zuba matai do ta kasa
xauke idonta daga gareta. Ba komai ne ya haifar da
haka ba face ganin kamani sak da suka yi da
mahaifiyarta Rasina, koda ganin irin kallon da suke
yi mata sai Shainana ta yi murmushi tace.
“Sunana Shainana mahaifiya ga Jarumi Ashtar”
Koda jin haka sai fuskar Sarauniya Lashmin ta qara
murtukewa ta so zaburowa kanta. Amma sai sarkin
yaqi Aryan ya tareta ya dubeta cikin girmamawa
yace mata “Ita xin qanwar mahaifiyarki ce, jinin
92

Sarauniyar daji

mawardi mutum ta uku data rage a jikin mawardi
data rage a duniya” Koda jin haka sai takobin dake
riqe a hannun Sarauniya Lashmin ta suvuce ta faxi
qasa hawayen farin ciki ya soma zubo mata.
Shainana ta matsa gareta ta kama hannunta a
hankali ta zaunar da ita akan gadon, suka yi shiru
zuwa wani xan lokaci kafin tace mata “Duk abinda
ya faru na samu labara, kiyi sani cewar ni lokacin
dana bar cikin daji na koma birni da zama a lokacin
da muka kai fatin daji ni da mahaifiyata birni domin
siyarwa anan sarki Dambola ya soma ganina wata
rana ya shigo kasuwa tun daga nan ya saka fadawa
suka xaukeni ya saka aka xaura masa aure dani,
wannan shi ne abinda ya rabani da dangina da ‘yar
uwata Rasina. Duk tsawon wannan lokacin bai daina
bibiyar duk abinda yake faruwa ba ga jama’ar
mardawa. Musamman na saka aka je har birnin sin
aka samo mun wata bokanya aka kawo mun ita ta
riqa koya mun alqaluman sihiri, yanzu haka da nake
baki wannan lamarin na bunqasa a duniyar
Bokanci” Ta sauke numfashi tana kallon Sarauniya
Lashmin kafin ta qara cewa da ita.
“Abinda yasa yanzu ma kika ga na zo, lokacin
zuwan nawa ne ya yi domin cikawa mahaifinki da
yayata burinsu na ganin zuri’ar mardawa bata qare
93

Sarauniyar daji

daga doron qasa ba, domin sarki Dambola yana
shirin fitowa nemanki domin kashe ki, amma shi da
kansa yasan ba zai samu nasara akan ki ba face ya
samu gashin qeyarki an haxa masa wani tsumi, haka
nan kema ba za ki samu nasara akan shi ba face kin
mallaki takobin mahaifinki da mahaifiyarki wanda
sarki Dambola ya soke su a jikin kabarinsu bayan ya
halaka su, ki sani wannan takobin xaukota daidai
yake ya tunkara yaqi da rundunar duniya.
Domin tuni Boka Dambola ya bayyanar masa
cewar ba za ki samu nasara akan shi ba face kin
mallaki waxannan takobin don haka ya saka
Bokayen duniya suka samar da wani sansani na
tsaro wanda uwar dodani take yi, kafin ki qarasa
wajen da take sai kin bi ta wasu xakuna guda biyar
wanda dukansu suna tattare da nau’ikan bala’i da
masifa kala-kala” koda jin haka sai jinin jikin
Sarauniya Lashmin ya soma tafarfasa jijiyoyin kanta
suka mimiqe cike da jarumtaka ta miqe tana faxin.
“Ina rantsuwa da kabarin iyayena da kakanina
babu abinda zai hanani kaiwa ga kabarin mahaifana
kuma na xauko takobin mahaifana domin kashe
azzalumin daya yi musu kisan gilla” Shainana ta
miqe a hankali itama kafin tace mata.

94

Sarauniyar daji

“Amma wani hanzari ba gudu ba dole kina
buqatar taimakon xana Yarima Ashtar, domin shi ne
kaxai zai iya zare takobin mahaifinki sarki Amjadu
daga cikin kabarinsa” Sarauniya Lashmin ta yi shiru
tana duban Shainana tana furza da fushi na zuciya,
koda sarkin yaqi Aryan ya fahimi halin da take ciki
sai ya yi saurin matsowa kusa da ita, a hankali ya
dafa mata kafaxa yace mata.
“Dole kina buqatar taimakon Yarima Ashtar
yanzu a wannan gagarumar tafiyar da za ki yi, kiyi
sani cewar shima mahaifinsa nemansa yake domin
kashe shi, abu na biyu kuma shi xin akwai jinin
mawardi a jikinsa” Waxannan kalaman na sarkin
yaqi Ashtar sun taimaka sosai wajen kwantar wa da
sarauniya Lashmin zuciya a hankali tacewa shainana.
“Na amince za mu yi wannan tafiyar da xanki
Yarima Ashtar”.
Ai kuwa tana faxin haka sai gani suka yi Yarima
Ashtar shima ya bayyana a cikin xakin yana
murmushi, yana sanye da kayan yaqi koda sarauniya
Lashmin ta kalle shi sai ta xauke kanta. Ganin haka
sai mahaifiyarsa shainana ta yi murmushi tace musu
“Idan kun shirya yanzu na saka akai ku can gidan
uwar dodani wajen da ta yi sansani domin gadin

95

Sarauniyar daji

takobin sarki Amjadu da matarsa Rasina” Take cikin
haxa baki suka ce “Mun shirya”.
Nan take shainana ta yi wata tsatsuba ai kuwa sai
wani aljani ya bayyana a cikin xakin take ta basa
umarni ya xauke su ya kai su sansanin uwar
aljanu.aljanin ya amsa cike da girmamawa su
sarauniya Lashmin da Yarima Ashtar suka haye
bayansa Aljanin ya luluqa da su cikin gajimare da
zumar kai su can sansanin uwar aljanu.
**
A can qasar Hindu kuma tun lokacin da boka
kuljabu ya komawa sarki Danbola da baqin labara
na tsafi da matarsa Shainana ta aikata sai mamaki da
baqin ciki mai tsanani ya mamaye masa zuciya.
Mamakinsa shi ne yaushe har matarsa shainana
ta koyi tsatsuba, baqin cikinsa shi ne yadda bai samu
nasara kashe su ba. Tun daga wannan ranar ko sau
xaya Sarki Dambola bai qara yin murmushi ba.
Kullum yana cikin qidayar kwanaki da watani
domin jiran ranar da zai yi hawa na musamman
domin kawo qarshen maqiyarsa sarauniya Lashmin.
A duk shekara sai ya saka an nemo masa manyamanya bokayen duniya ya musu bayyani halin da
yake ciki da kuma neman mafitar hanyar da zai bi

96

Sarauniyar daji

domin ganin ya samu nasara akan sarauniya
Lashmin.
Amma dukan su abu guda suke faxa masa, dole
sai ya mallaki takubba guda biyu dake soke a jikin
kabarin iyayenta, wanda suka basa tabbacin duk
duniya babu waxanda za su iya xauko takobban
daga cikin kabarin face mutum biyu xansa Yarima
Ashtar da kuma sarauniyar Daji Lashmin. Jin
wannan bayyanin na bokayen duniya ya saka
bokayen suka samar masa da tsaro na gadin
takobban. Tunda dole sai sarauniya Lashmin ta
mallake su kafin ta samu nasara akansa to idan
kuma bata mallake su ba shi Kenan dole ta qyale shi.
Amman duk da wannan tsaron da sarki Dambola
ya samar, hakan bai saka hankalinsa ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment