You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kyalkyala dariyar maganar da Nenne ta gama yanzunnan, kafin tace.
“Ai wato Nenne sun fito fa da farko, tun ina 13 years, Ummace ta bige su da muciya, lokacin da suka fara fitowa ta samu muciya ta karanta addu’ar da bansan me ta karanta ba tace "Ya Allah ba yanzu ba, sai ta kara girma", sai ta buge su da bakin muciyar, daga lokacin suka koma”. Nenne ta kasa rike dariyarta, don ita bata taba jin inda akai haka ba, kai Hajiya Zainab sai a barta, saida ta gama dariya mai isarta kafin tace.
“to ita kuwa Umma meyasa tayi hakan ai girma dole ne ga diya mace, fatan dai shine Allah ya taya mu akan tarbiyyarku, har mu mika ku gidan mazajenku. Fara kirgen dangi da wuri ba abinda zaisa ba abinda zai hana in lokacin aure ya zo wa mace. Sabida shi aure lokaci ne dashi ga kowacce mace ba sai sanda ta shirya ba”.
Siddiqah tace “ai Ummana bata so ayi min aure da wuri, ga Babana yayi alkawarin da wuri zai min aure, saboda ya samu jikoki da wuri tuda shi bashi da’ya’ya da yawa, ita kuma Umma tunda nikadai ke gareta, sai bata son auren wuri gareni, shine dalilin data komar da kirgen dangin lokacin da ya soma fitowa, tace itama Goggonta Allah ya jikan rai haka tayi mata kuma suka koma, don in Abbana ya gani zai ce ai kawai na isa aure”. Kai yau cikin Nenne har kullewa yayi don dariyar da Aisha ke bata, tace “kuma sai gashi hakan bai hana auren yazo miki da wuri ba, Allah kenan! Mai yin yadda yaso a lokacin da yaso”.
Ita kuwa Siddiqah sai yanzu take jin takaicin abinnan da Umma tayi mata, da yanzu tana cancada gayu kamar su Fatima, don gani take ko kwalliya tayi bata kyau kamar yadda su Firdausi ke cika idon mai kallonsu, suna juya jikinsu yadda ransu yake so.
Tun daga ranar Siddiqah ta cire kyankyamin abincin yarbawa, ta bude ciki tana cin ire-iren abincin da akeyi a gidan, irinsu ‘Afang Soup’ da ‘Ewedu Soup’ da ‘Oka (brown amala), ga Iyan (yam flour/pounded yam) da 'ékuru' da akeyi da wake’. Duka abinciccika ne masu gina jiki da kara kuzari. A gefe kuma ga kamun da Nenne ke yi mata da kanta kullum da yamma bata mantawa har cikin dan lokaci ya fara bin jikin Siddiqah.
**** ***** ****
THE PRINCE
Bayan ya koma Qatar baifi da sati biyu ba aka turashi consultation na aiki a Abu-Dhabi Kamfaninsu ‘Qatar Refinery’ ne ya tura Engnr. Abdulrasheed consulting wani aiki na sati biyu a (Abu-Dhabee National Oil Company) don haka yau da safe ya kira Nenne a waya, don ya sanar da ita, yaso kwarai a satin da za’a shiga suzo masa hutu Qatar yadda ya riga ya tsara tunda farko, lokacin da Abdulrasheed ya kirata ko fitowa Nenne bata kai ga yi daga dakin barcinta ba don safiya ce sosai a wurinsu Dade kuma ya jima da fita jogging.
Bayan sun gaisa yadda suka saba shi da mahaifiyarsa, kasancewar baya yiwa Nenne kowanne yare sai fulatanci, don yasan shi tafi so su dinga yi mata musamman in shi da ita ne, yarbanci wannan saisu Fatima, sam basu cika yin fulatanci ba sai harshensu na gado. Aunty Taiwo kuwa dama maganarta duka rabi turanci ne ita saboda mijinta Toufeeq da yaranta su Kiki shi suka fi yi a junansu.
Yace da Nenne cikin fulatanci “Nenne inata dokin son ku zo wannan watan gabadayanku keda twins, har Hakeem, muyi hutun Easter dinnan tare duk da babu Kiki. Itama naso ince ta samemu anan don ta kusa Hutu.
Amma tafiyar aiki ta sameni unexpextedly zuwa Abu-Dhabee sai suka rushe min plan, sai idan na dawo in sha Allah sai kuzo”.
Nenne tace “to sarkin kanne Uban Hakeem da Kiki. Sune kawai ababen kulawarka iyali ko oho. ‘Allah hokku sa’a ko ayahi dabbutugo Albarka Annabijo" wato (Allah ya bada sa’ar abinda aka je nema albarkar Annabi), Ya kuma dafa muku”, sannan ta nisa tace.
“Hammansu bazamu zo ba wannan Easter Holiday din, saidai kai kazo. Am not feeling fine da zan iya hawa jirgi nan kusa”.
Amma Prince ya riga ya sakawa ransa nan kusa shikam nan kusa bai zuwa Lagos ko Ilorin, ba don komai ba sai don gujewa fushin Baffanninsa.
Yayiwa Nenne alkawarin zai zo amma sai bayan wani lokaci. Yayi mamaki da bata yi masa korafin Baffanninsa sun bude mata wuta akan rashin zuwansa ba yadda ta saba.
Sunyi waya da Aunty Murja ma duka a ranar, wadda ke can cikin bacin ran Nenne ta hanata sanar dashi maganar aurensa har yanzu, balle ta san yadda ya karbi al’amarin ta bangarensa.
Da yake bakinta nata kaikayi saida tace masa “Kehinde!” Yace “Na’am” ta sake cewa “Prince! Sau nawa na kiraka?” Yana dariya yace “Taiwo! Kin kirani sau biyu, wani abu?”.
“Ka daure kaje gida immediately daka gama aikin da zaka je dinnan”.
Ya nemi karin bayani dalilin kalmar immediately din, don yaji seriousness sosai a kan muryarta, sai kawai ta kashe wayarta ba tare data bashi amsa ba.
To haka su Fatima ma baki nata kaikayi, kamar sun ci bawon Doya, musamman Princess Fatima uwar tsegumin gidan bakidaya, komai a bakinta Taiwo ke ji. Har hotunan Siddiqah ta tura mata.
Amma wane mutum a gidannan Nenne tayi umarni yayi fatali dashi? Ko tasa kara mutum ya tsallaka? Ko basa so zasu bi. Don kowa na gudun bacin ran Nenne Sappa.
Da wuya tayi bacin rai a cikin iyalinta amma in tayi shi basa ji da dadi, don bata sauka ta sauki sai kowa yaji a jikinsa.
Yau da ba don Nenne uwarsu bace kuma itace da kanta ta hada auren nan na Prince da Aisha, da Murjanatu tace an kwari Kehinde dinta, an zubar masa da class a inda bazai kwasu ba, da aka aura masa Aisha.
Ta fadi hakan ne lokacin data ga hoton Aisha Siddiqa a wayarta.
Ba wai Siddiqah din ba kyakkyawa bace, a'ah don kyau Masha Allah ko makiyinta ya san ta kere sa'o'inta a kyawun sura. Amma a ganin Aunty Murja kyawun ba shi Prince yake bukata a halin yanzu ba da shekarun girma suka riskeshi.
A yadda Prince ya kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure a ganin ta cikakkiyar mace kuma kilalliya wayayya preferably ‘yar kabilar Yoruba ce ta dace dashi in har ba Haseenah ba, mace 'yar shekaru akalla Talatin wadda zata kula da komai nasa, ta tarairayeshi ba hijabin kunya, sannan ta jiyar dashi dadin aure da ya jima bai sani ba, amma ba dai shi Prince a halin yanzu yayi zaman rainon ‘teen’ ba.
A yadda Fatima ke fasalta mata abubuwan da Siddiqa keyi a gidansu na kauyanci da kuma hotonta data gani ba maraba da ‘yan tallan nono a kasuwar Gombe. Don haka zamu iya cewa, from Day 1, Aunty Taiwo bata yi na’am da dacewar Siddiqah da Prince ba a matsayinta na mafi kusanci dashi data fi kowa sanin likes and dislikes dinsa.
Ko dalilinta ya isa dalili? Ko kuma na son zuciyarta ne bazan iya cewa ba.
Dan adam din kenan, har kullum halinsa sai shi. Marar godiyar Allah marar tuna baya. In banda haka sai muce ko dai Aunty Murjanatu ta mance yawan shekarun dan uwanta Prince Abdulrasheed dinne? Da dadewarshi yana Polo babu aure, kuma har gobe bashi da niyyar yi?
Maimakon Taiwo tace dan uwanta ya tsinci dami akala, na samun yarinya danya sharaf (in her teens) wadda bazai sha wahalar tankwarawa zuwa duk yadda yake so ba. A ganina, Aisha-Siddiqah ce za’a ce ta kwaru da auren Prince Kehinde, wanda a haife sai mu ce ya haifeta, ko mu ce ya kusa haifarta da yayi aure a farkon samartakarsa, amma ba Prince za’a ce an kwara ba a logical reasoning. Taiwo-Murjanatu, bata duba duk wannan ba, ji tayi kamar ta fashe don haushi da taji cewa matar da aka aurawa Prince ma wai ko sakandire bata gama ba, sannan ba ‘yar kowa bace a Gombe, kawai haduwar kan titi ne ita da Nenne. Sai taji fit! Matar Prince bata da muhallin kima a gunta. Wani abunda zai baka mamaki a lokacin ma sai Haseenah ta dawo ranta. Wadda a lokacin suna tare a gidanta ta kawo mata ziyara har Lancashire. Wannan ba shine zuwan Haseenah na farko gun Aunty Murja ba. Don haka a wurin Aunty Taiwo ma kamar danginsu na Ilorin, zamu iya cewa Siddiqah bata samu maraba ba, amma ba yadda zasu yi tunda zabin iyayensu ce.
Taso kwarai ace da Prince bai auri Haseenah ba, to zama ya auri wadda zata iya kula dashi, wadda ta fi Haseenah komai na kyau, ilmi da wayewa, Uwa Uba babbar nasaba ta sarauta da da zasuyi tinkaho da ita a cikin dangi tunda akan nasaba ne Nenne taki Haseenah, kuma mace mai cikar halitta da Kehinde zai iya jerawa da ita a ko’ina, amma ba wadda ko a shekaru da matakin ilmi bata kai ya jera da ita ba.
A cikin watanninta na uku tareda iyalin Abdulrasheed, sai ga Siddiqah ta fara cikowa, jikinta na faman murmurewa a hankali yana glowing, fatar jikinta tayi lukui-lukui, ta zama wata danya (fresh) wanke hanu ka taba sakamakon zaman waje daya, sanyin iya kwandishan da shan fruits (kayan marmari) da ake yi a gidan kala-kala ya fara huda fatar jikin Siddiqah, hatta farcenta na kafa da hannu wani irin jazur ya koma, kumatunta luwai-luwai sumul-sumul dasu fatar bakinta ta koma wani irin soft, pinkish da ita. Kugunta ya shiga wani irin budewa a hankali ta zama kamar kwalbar nan ta coca-cola daga kasa. Siddiqah zuwa yanzu ta zama kamar an barota daga cikin kwai don kyau da kyawun fasali, sulbin jikinta har daukar ido yake.
Madallah da kulawar uwar miji irin Nenne Sappa, madallah da kyawun abincin yarbawa mai inganci da gina jiki (freshy Yoruba food), ga kamun gero da cukwi din Nenne, tabbas yana aiki ba kakkautawa a jikin Aisha-Siddiqah.
**** **** ****
CIKA ALKAWARI
Yau dai Nenne ta cika alkawarin data daukarwa mahaifin Siddiqah, domin kuwa ta shigo dakinnta ta sameta ne tana gyaran kumba, sai ta mika mata littafai da uniform harda takalmi da jakar makaranta, ta gaya mata gobe in Allah ya kaimu zata fara zuwa makarantar da Kiki tayi.
Har ila yau, ta sanar da Siddiqah cewa ta shirya an daukar mata malama da zata dinga yi mata lesson Asabar da Lahadi akan jarrabawar WAEC din dake gabanta.
Hakan yasa Siddiqah ta kwana cikin zullumin wayewar garin, maimakon farin ciki, wanda shi ya kamata ace tayi, don samun damar karasa karatunta data yi cikin sauki kamar yadda Nenne ta dauki alkawari tuntuni ga iyayenta, ba kuma don komai ta shiga zullumin ba sai wani tunani daya tsirga mata babu gaira babu dalili.
Wai gata dai yanzu ta tsinci kanta dumu-dumu a garin Yarbawa ta dalilin auren da bata shiryawa ba, duk wannan bai isa ba, yanzu gashi gobe zata fara cudanya da dalibai suma yarbawa, ta tabbata duka daliban makarantar Yarbawa ne tunda su suka fi yawa a garin Lagos, kuma cikinsu za’a kaita tsundum a barota suyi tayi mata yaren da bata son ji dinnan, in a gida ana ragewa sabida ita. Shin ko yaushe hakkin Bisola Akanbi zai barta ta huta? Ta tabbata shiyake ta bibiyarta har yau.
Kabilanci yaki sakin ranta ta sarara, kullum tana tunanin ko ta koma Gombe. Gabadaya rayuwarta ta dawo cikin yarbawan data raina matukar rainawa, takewa shagube da mockery yadda ranta yake so, Allah kenan. Yau dai gata tsundum a cikinsu da sunan zama na dindindin har inda bata taba mafarkin shigowa koda ziyara ba (masarautar yarbawa).
Babu ko shakka alhakin Bisola ne ya tsundumota cikin kabilar yarbawa, ya hanata samun rayuwar fulani yadda ta yi mafarkin samu, ta kuma yi burin samu tareda wanda takeso, saurayin bafillace dan uwanta, wanda ya san ciwonta da darajarta, suke harshe da yare guda (Ishaq Nafada).
Sai Allah ya jefo ta duniyar yarbawa data ke yiwa wani kallo-kallo da shagube. Yanzu idan taje makarantar itama daliban suka yi mata irin abinda take yiwa Bisola fa a matsayinta na bahaushiya ita kadai?
Duk sai taji zancen karasa makaranta ya fice mata aka, gara ta cigaba da zamanta a gidan tunda su suna raga mata, Fatima ce kadai bata raga mata in taga ba iyayensu a wuri ma da gayya ma take suburbuda yarbanci, da zata iya da tace da Nenne bata so kawai a kyaleta. Ta hakura da zana WAEC din don dam aba wani jami’a take son zuwa ba. Dan ilmin data samu na karatu da rubutun hausa ya isheta ya wadaceta Allah ya amfana. Don ko turanci ba wani iyawa tayi can acan ba, tana dai ji in an yi mai sauki amma ko na su Fatima ba duka take ganewa ba.
Da wannan damuwar Aisha-Siddiqa ta kwana yau, wadda ta saka mata kewar FGC Billiri, ta hadu da kewar Umma data gang members dinta su Amintako, Ramatu da sauransu.
Ga Ishaq dinta masoyi na hakika data kwallafawa burin rayuwa tare dashi ya mata nisa yanzu, ta tambayi kanta ko zuwa yanzu Ishaq ya gama NYSC? Rabon ta dashi har ta manta.
Kowa nada wayar hannu a gidan nan banda ita, don Nenne tace makaranta zata fara, nan kuwa bata so Siddiqah ta dinga yiwa Ummanta kuka a waya ne, don kusan kullum ta hada su waya a gabanta sai Siddiqah tayi kuka da ta ji muryar Umma, saidai ta kai yanzu Nenne ta dade bata hadasu gaisawa da Haj. Zainab ba.
Yau kam da yake cikin tension da takurar zuciya take, saita nutsu, tana sauraron zuciyarta, shiga tunane-tunanen abubuwan da suka dace suka kuma shafeta, ciki har da tunanin wai shin ma wanene shi wannan Hammansu Firdausi din da ake kira Hamma Prince???
Ko meye matching dinta dashi da har yasa iyayensa suka ga kamatar su katse mata rayuwa a kansa, ta hanyar hadasu wannan makalallen aure haka bagatatan bata shirya ba, kawai daga haduwar Umma da Nenne a hanyar Munna, alhalin sun san ba sonta yake yi ba shanyata zai yi a garin yarbawa?
Ai ko ba'a fada ba zuwa yanzu ta gane kamar ma baisan da auren ba, don kusan duk wayarshi da Nenne dasu Firdausi ta kan ji jefi-jefi, bata taba jin wani cikinsu yayi masa zancenta koda da subutar baki ne ba.
Kamar ma boye masa suke, me hakan ke nufi? Anya Umma ta san zaman kashe wando da take yi a Lagos ba a gidan Prince din takde ba?
Haka kawai an raba ta da mai sonta bayan shi ba son ta yake ba baima da lokacin zuwa kasar Nigeria, me yasa iyayenta zasu takurata a yi aurennan don kawai su farantawa Nenne dake cikin damuwa akan danta. Ita ba'a damu da nata feeling din akan kabilar yarbawa ba. da gaske take tanada kabilanci da ethnocentrism ba da gangan gtake yi ba. amma aka tashi aka aura mata Bayerabe da bata ko taba gai ba shima kuma baya sonta.
Ta tabbata da yana son ta, da tuni ya zo, ko bai zo ba, da wani cikinsu ya gaya masa batun auren su da zaman jiransa data ke yi. Gashi har ana neman fita watanni uku. Shi wanda aka ce zaman shi take yi a gidannan bai zo ba, bazai wuce shima bakin bayerabe bane kamar kowanne bayeraben mutum data sani, kuma irin katoto dinnan ya tsa tsagu ba kamar Ishaq ba. Kodayake taga cewa Dade baida tsagu, kuma indai irin kalar su Fatima ne kuma Nenne ce ta haife shi da gaske to ba lallai yayi muni ba.
Ai kawai data rasa takamaimai tunanin daya dace tayi, ta kuma ga cewa tunaninta ya fara fita daga saiti, sannan ta kuma ji ta na dokin ganin Prince Abdulrasheed (just to quench her curiousity about him) sai ta karkace ta cusa kai a kasan pillow ta tsinke da kuka ita kadai, irin kukannan na banida tsumi bani da dabara. Ba tareda ta san mawuyacin halin da al’ummar gidan suka kwana a ciki ba.
Ashe ita kukan samun wuri takeyi.
Kwana sukayi Nenne na suma tana farfadowa cikin murmukususu na azabar ciwon ciki. Don haka cikin daren akayi asibiti da ita. Sai da asubahi taji ana buga mata kofa, dama barcin nata ba wani nisa yayi ba, ba kuma dadinsa take ji bat un bayan daya sureta, tana dai kwance ne kawai, nan da nan ta bude ido tana mutstsika shi sai taji ya kumbure suntum. Ta mike ta bude, sai taga Femi tsaye cikin damuwa.
“Aisha ki sauko falo Dade na kiranki”.
Gabanta saida ya tsinke ya fadi, amma bata tambayi Femi komai ba ta dauko hijab ta dora akan kayan barcin ta cikin kidimewa tabi bayanta zuwa downstairs.
A falon kasa ta tadda Dade a tsaye yana jiranta, Fatima da Firdausi basa gidan suna Ilorin bikin cousin sister dinsu ‘yar wajen Malami Uban Doma. Da girmamawa ta hau kokarin gaisar da shi, amma ko daga fuskarsa ta ga damuwa, Dade yace mata cikin Hausa
“Aisha biyoni, Nennenku ce babu lafiya tun cikin dare muna asibiti, and she’s calling you”.
Iyakar firgita da rudewa Siddiqa ta shigesu. Ta bi bayan Dade zuwa mota a sukwane, Seun direba ya ja suka tafi asibitin da Nenne ke zuwa wato Lagoon.
Suna tafe a hanya Siddiqah na jan hasbunallahu wani’imal wakeel saboda ko daga damuwar da Dade ya nuna a fuskarsa ka san jikin na Nnnne ya matsa, ta na jin sa yana waya da Hammansu Firdausi, akan hanyarsu ta isa Lagoon Hospital. Dade na magana kamar cikin hassala yana cewa.
“Kehinde na rantse maka zaka hadu da fushi na, na ga alama baka san zuru ba, na rantse in ban ganka gobe ko jibi ba zaka sha mamaki na, aiki da hawa doki yafi ahalinka ko? Yau watan ka nawa rabon ka da gida saboda Baffanninka? To in kaga dama yanzu ai ka zo, in kana da rabon ganawa da mahaifiyarka dake kwance rai kwakwai, mutu kwakwai tun jiya.
Gata nan kwance rai a hannun Allah amma da yake har kullum kana ranta bata fasa kiran sunanka ba.
Ka tabbatar ka bar duk abinda kake yi ka nemi jirgi mafi kusa ka taho Lagos”.
Ya danyi shiru, da alama rokonsa Prince yake ta daya bangaren, kan ya fadi masa ko me ya faru da mahaifiyarsu Nenne?
Dade sai da ya nisa kafin yace.
“Wai ashe Hajiya Sappa ta jima da 'renal stones' har 'cyst' ya fito a ‘kidney’ dinta, tana treating ni ban taba sani ba saboda zurfin ciki irinnata?”
Da haka Dade ya kashe wayarsa, ba tareda ya jira amsar Hamma Abdulrasheed Prince ba, ya koma ya jingina da allon kujerar motar, ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali yana kiran sunan Allah As-Sattaru, yana rokonsa ya tashi kafadar matarsa abar son sa uwar ‘ya’yansa Nenne Sappa.
Itama Siddiqah ta tsorata sosai da jin halin da Nenne ke ciki. Tuni ta fara mata addu’ar duk da tazo bakinta.
Sanda suka isa asibitin Nenne ta sha allurai ta samu barci mai nauyi amma bata san wanda ke kanta ba, motsin da bakinta ke yi ya nuna salati take yi da hailala wanda daman baya rabo da bakinta koyaushe.
Gari na kara wayewa likitoci sun gama shirinsu na shigar da Nenne tiyata. Dade yayi shahada kan ba yadda zai yi yasa hannu, aka wuce da ita dakin tiyata.
Shi da Siddiqah suka koma suka zauna a dakin da aka bata, kowannensu yayi tagumi da hannu bibbiyu yana kissima irin girman rashin da zaiyi, it will be (irreplaceable loss) rashin Nenne a tare dasu.
Idan Nenne bata fito da rai ba, dukkansu rayuwarsu ta durkushe suna addu’a suna kuma hawaye, Siddiqah har da kuka wiwi amma Dade ko umh bai iya yace mat aba balle ya lallasheta shima fama yake da kansa, da zai iya shima fashewa da nasa kukan zaiyi yadda ta yi ba kananan hawaye ba amma dai ya jure yanata hailala da carbinsa yana tsane ruwan ido.
**** **** ****
Koda Dade ya kashe masa waya. The Prince was shocked, hankali a tashe ya zubar da komai da yake yi a lokacin, yanada tournament din da zai halarta swannan satin a Argentina amma ya kansile shi nan take, haka yayi ta kansile duka scheules dinsa na sati yana bada excuse, ya soma neman jirgin da zai kawo shi Lagos ido rufe.
**** **** ****
Sosai Siddiqah kewa Nenne addu’a kafin fitowarta dakin tiyata da carbin da da Dade ya ciro a aljihunsa ya mika mata, yace tayi masa shiru haka, kafin isowar Femi da kayan karin kumallon su.
Amma ko kallon kwandon abincin babu wanda ya iya yi a cikinsu, kuma Dade ya ki kiran kowa nashi daga Ilorin ko nata daga Gombe don ya sanar da su, don yasan da ya fada za azo a cika asibitin. Ya dai kira Fatima da Firdausi yace su bar bikin su dawo gida maza-maza.
Bai kuma basu damar tambayar ba’asi ba ya kashe wayarsa amma sun tsinkayi damuwa a muryarsa.
Wajen karfe sha biyu na rana aka fito da Nenne daga theatre room. Cikin ikon Allah an yi aikin lafiya, an cire stones and cyst, aka kawo abubuwanda aka ciro din aka nuna wa Dade, Dade sai hamdala yake yana godewa Allah, Siddiqah ta rungume hannu a gefe tana hamdallah, aka fito da ita tana barci akan gado aka gungurata zuwa dakin hutu.
Sai lokacin Dade ya samu ya fita ya tafi gida don ya dan kintsa, ya bar Siddiqah tana jiran farkawar Nenne. Ta
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500