ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata don a lokacin kanana ne stones din likita na tunanin zai iya treatment dinsu ba tareda surgery ba.
Daga baya ta manta da zancen don bata fama da kowanne ciwo ga yawan sabgogin iyali dana al’umma dake kanta.
A check-up na karshe da Hajiya Sappa ta je Morocco aka tabbatar stones tana bukatar surgery don a ciresu gabadaya ta huta. Kaninta Abdulmajid baisa was aba yajaddada mata cewa da zarar ta dawo ta yi shiri ta sake dawowa ayi aikin. Amma Nenne tunda ta dawo kuma tanacikin koshi lafiyarta sai bata sake bi ta kan lalurarta ba.
Daga ita sai Dr. Abdulmajeed Ahmadu Jalloh Omar, suka rike da wannan zancen na kidney stones dinta a tsakanin junansu, wato kaninta mai binta a haihuwa wanda likitan Koda ne dake aiki a babban asibitin Koda na kasar Morocco, su biyu kadai suka san da wannan al’amarin.
A can baya da take yawan zuwa Morocco da sunan ziyarar Abdulmajid da iyalinsa a rashin sanin Dade da yaranta ana treating dinta ne, don samun lafiyarta.
Daidai lokacin data dago daga sujjadarta, jikinta ya soma dan bari da karkarwa na shigar zazzafan zazzabi, bata taba jin zazzabi irin na wannan lokacin ba tun saninta da ciwon nata. Zafin jikin Nenne ya karu, har ta kai ga ta bar abinda take yi a kitchen ta koma dakin mijinta ta kwanta a gadon su na alfarma.
Nenne ta dauki waya ta kira Abdulmajid, yana jin muryarta sanda suke gaisawa ya san jikin ya tashi sosai, yace “Adda kiyiwa Allah ki yarda ayi miki aikinnan kowa ya huta, ina amfanin zama da ciwo? Kuma kin hanai fadawa kowannensu har yau” Nenne tace “Abdul tsoron aikin nake ji, gara idan tafiya ce in tafi salin alin ba tare da an farke ni ba, ina rokon ka kara rike min sirri na, ban yarda Dade da Hammansu da Nani Oummana su ji wannan maganar ba…”. Abdulmajeed ya katseta cikin damuwa “Adda na gaji! Na gaji da wannan boye-boyen da muke yi, mara amfani, Adda boyewar nan bata da wani amfani, su dinnan duka musulmi ne Adda, musamman miji da mahaifiyarki, koba komai zasu yi miki addu’a ayi aikin nan a sa’a. shikuwa Abdul ai namiji ne shi yafi kowa dacewa ya san halin da kike ciki, ki sanar da ko Abdulrasheed da Murjanatu ne kadai su rako ki ayi aikin, in har bazaki bari Dade dinsu ya sani ba saboda hawan jininsa, su ya kamata su sani”.
Nenne tace “ko zan sanar dasu ba yanzu ba sai na shirya, akwai abinda ke gabana yanzu, zan cigaba da shan magungunana da na bar sha kwana biyu. Tunda na samu cikar burina da raina akan Hammansu (Abdulrasheed) to Alhamdulillah!”
Abdulmajeed Yace cikin damuwa da hukuncin ganganci na ‘yar uwarsa, “amma Adda idan kika mutu kina musu wannan boye-boyen ba tareda sun san jinyar da kika dade kina yi ba, suka kuma ji da hadin bakina, na rantse daga ni har ke bazasu taba yafe mana ba!”.
Nenne tace “bazan taba saka sunanka cikin maganar nan ba Abdulmajeed, amma zan duba yuwuwar na sanar da Abdulrasheed shikadai, amma dai don Allah ka kara min lokaci Abdul, har Abdulrasheed ya karbi matar dana aura masa daga hannuna”.
Abdulmajeed ya rasa me zai ce mata da zai sa ta dauki al’amarin lafiyarta da muhimmanci sama da zancen auren danta. Yace a hankali “Adda!” Nenne Sappa ta katse kanin nata cikin kulawa.
“Abdul, Ko Allah hoddiri fe’an be tagu fe’an!”.
(Abinda Allah ya riga ya rubuta zai faru ga bawa ba makawa sai ya faru)!”
***** **** *****

ROUQAYYAT-KIKI
K
iki (Ruqayyat) zuwa yanzu an zama manyan ‘yanmata, shekafun ta zasu kai sha bakwai da watanni tara. A bana ne ta kammala karatun sakandire. Can na hangota cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan gayu amma kuma wadda bata nuna tsiraici a tare da itaba, irin dai shiga ta yaran musulman Yoruba, rashin saka lullubi ko a kafada aka ya nuna ita din ba cikakkiyar bahaushiya bace, cikin wani hamshakin supermarket take shawagi a (Santa Monica) din birnin Los Angeles.
Dana leka kwandon da Kiki take sayayya a ciki sai na ga cewa kanta take zabar ma ‘brazier’ da ‘panties’ da ‘undies’ da kuma ‘nighties’ ‘yan ubansu-ubansu, kasancewar a gobe ne zata koma hutu na farko gida Ilorin, tun bayan zuwanta kwas din Computing a Los- Angeles, sai wani tunani ya fado mata, kasancewar kome take yi Uncle AK baya barin ranta.
Mai zai hana tayiwa Kawunnata gudunmuwa dasu shima idan aurensa ya tashi ya baiwa matarsa? Sabida a idanunta nighties dinnan da undies din duka unique ne, da kyawunsu da tsadarsu ya kai ya kawo. Kiki na nan ‘yar lukuta haka duma-duma kamar buloras, doguwa mai garin jiki kamar na mahaifiyarta, Taiwo.
Da ‘yan yatsunta da suka sha adon bangles da zobban zinare ta latsa tsadaddiyar wayar hannunta wadda Uncle AK dinne ya mallaka mata (yadda take kiran Prince har inda yau ke motsi watau Uncle Abdulrasheed Kehinde) a ranar da yazo bikin graduation dinta na sakandire daga ‘Greensprings School’ dake jihar Lagos, alkawari ne da ya dade da yi mata cewa sai ta kammala secondary school da kyakkyawan sakamako sannan zai mallaka mata wayar hannu kuma a ranar ya samu ta cika shi. Musamman kasancewar Kiki tayi kokari sosai a jarrabawarta.
Yana kwance cikin ‘sofa’ a ranch house dinsa atsakiyar babban birnin kasar Argentina, a jiya yazo kasar daga Qatar wani babban tournament.
Dawowarsa kenan a matukar gajiye ko Polo Helmet din kansa da chukka boots din kafarsa da socks bai samu ya cire ba. Da chukka boots da safa da komai dake jikinsa ya fada akan Sofa-bed din, yana matukar son zuwan su Nenne a satinnan kafin lokacin tafiyarta aikin Hajjin bana yayi, don ya jima shi bai je ba. Idan kuwa har yayi irin wannan jimawar bai je gida ba irin haka Nenne kan tarkato kan kannensa Princess Fatima da Princess Firdausi, da ‘ya’yansa Hakeem da Kiki su zo su yi masa sati.
Daidai lokacin yana tunanin mikewa don wucewa bedroom dinsa yayi sallah, ko ya samu yayi barci sosai, ya huta gajiya don rabonsa da barci tun daren shekaranjiya wato kafin su fara tournament din da ya kawo shi, wayar ‘yar rigimarsa Kiki ta shigo masa.
Da kyar ya mika hannu ya daga idanunsa a lumshe saboda gajiya. Amsawar kawai yayi cikin dushewar murya ba tareda yace mata komai ba.
Tace “Uncle AK size nawa zan daukar mata na backward da frontward?”
Abdulrasheed ya yunkura ya mike zaune cikin yamutsa fuska yace “Kiki! Where are you now? What sheet are you talking about?”
Kiki ta rangwadar da kai gefe irin na yaran da ke jin duniya akan tafin hannunsu tace “Uncle AK, lefe zan fara hada maka, in duba wata hadaddiyar Baby haka anan ajinmu in yi mata tallanka, Uncle nagaji da ganin ka kai kadai a gida, Uncle nagaji da ganin ka a cikin Dawakai ba ‘ya’yan ka ba”.
Idanun Abdulrasheed suka dan bude kadan don mamaki, har an kawo wannan lokacin da ‘yar cikinsa ma ta damu da rayuwarsa har haka, da kyar ya iya ya hadiyi miyau, yace.
“Kiki are you alright? Ko kin fara shaye-shayen zamani ne?”
“Allah ya sani ban sha komai ba. Mamana ta hanani sauraron samari saboda kai, ina dalili? Akwai BF dina dana ke matukar so Mama ta hana ni ko magana dashi wai sai kayi aure, rannan fa cewa tayi wai bana jin kunya in shige gidan miji in barka a zaure?” Kiki ta karasa harda kirkiro ajiyar zuciyar damuwa, yadda take maganar kadai zaka san bilhaqqi take yinta cikin gabunta.
Wata ajiyar zuciyata subucewa Prince, shikansa bazai iya tuna rabonsa da yin irinta ba, in ba yana magana da Kiki ba baya tuna yawan shekarunsa. Ita kadai ke iya saka shi dariya a kowanne lokaci koda bai shirya ba.
“Idan na fahimceki daidai Kiki, kina so in yi aure ne don a baki dama kema kiyi aure?”
Kiki tasa hannu daya ta rufe ido daya tana dariya don kunya, kamar Abdulrasheed na ganinta, shikuwa kallon mamaki yakewa kan wayarsa, har yaushe ‘yar cikinsa Kikin da yake sawa ‘diaper’ ta girma haka?
“Alright Kiki, nina tsufa da aure, zan wa Taiwo magana kada ta kara fadin haka gareki. Ta baiwa mai kaunarki dama ya iso gida. Kiki har kayan dakinki na gama hadawa suna nan kulle a gidana na Qatar.
Kuma ni zaki fara kawowa boyfriend dinki din kafin kowa. Sai nayi na’am dashi zaki kaishi ga Daddynki. Yaya sunanshi?”
Don farin ciki Kiki kamar bakinta ya yage don murmushi tace “You know I love ko Uncle AK? Nayi alkawarin bazan taba sauraron saurayi ba sai kayi aure? Sunansa “Abdul-Nasir Oluwatosin”.
A kwance Prince yake amma bai san yaushe ya tashi zaune ba. ya rike wayar hannunsa sosai yace “Tosin Abdulnasir, a footballer?”
Kiki ta gyada kai tana jin kunya, kamar Uncle AK yana kallon idonta. Shi kuma yace “Kiki iyayenmu bazasu taba bari ki auri footballer ba, sai dan sarauta, ni nasan iyayenmu sarai, ki cire ni a gefe kan batun aure. Maybe your Uncle is not destined to marry in his life. Amma akwai mata fal a aljannah ai kin sani ko Kiki? They are called hurul’eeni, who knows ko mata na hudu suna cikinsu?
Don haka ki daina damun kanki a kaina kinji. If you really-truly love this Guy, I will stand by you Kiki. AbdulNasir was a football celebrity. Me ya hada ki da dan ball? A ina kika hadu dashi?”
Kiki ta labarta masa haduwarta Tosin AbdulNasir sun je kallon wasan da Inter-Miami tayi da LA Galaxy a California itada kawarta Badriyya.
“Amma Kiki ban hanaki bin kawaye yawo ba? Ban ce daga makaranta sai makaranta ba? wato har kallon ball kike zuwa?”
“Kayi hakuri Uncle AK, wallahi ba inda nake zuwa banda shopping, ranar ma Badriyyah ta matsa muje ne don taga AbdulNasir a fili, tana matukar son wasansa, na gaya mata ka hanani zuwa ko’ina, tace daga ranar bazasu kara zuwa yin wasa Los-Angeles ba, and she don’t want to miss seeing her favourite footballer in reality (bataso ta rasa ganin dan ball din data fi so a fili), sai na yarda muka je, tun a ranar ya nuna kaunarshi gareni muke waya, ban taba gayawa kowa ba sai Mama, shine ta bani waccan amsar cewa bazan taba sauraron kowa ba sai kayi aure”.
Abdulrasheed yayi ajiyar zuciya ya ce “Kiki count me out kinji? Bani lambar yaron kuma ki bar ni da Taiwo”.
Kiki ta dage itafa bata so itama, in Abdulrasheed naso tayi aure ko ta saurari maso sonta to ya barta ta hada masa lefe.
Dariya yake yi a yanzu. Yace “Kiki! Daga hada lefe sai me? Na baki dama kiyi tayi. Kudi ne dake. Ki sayi kome kike son saya kiyita tarawa gaibu, amma bada kudina ba bana cikin shirme kinji?”
“Yo dama Uncle ai ban ce ka turomin ko sisin kwabonka ba. Zai zama cewa tawa gudunmuwar kenan ta aurenka, saya maka akwatin (undies and night wears) dinta. Kawai cewa nayi ka gayamin frontward and backward size din matar ka”. Kan Abdulrasheed ya shiga duhu da shirmen Kiki, yace “meye kuma front and back?” Kiki ta hau dariyar shakiyanci sabida yadda Uncle Prince yayi maganar cikin yamutsa fuska dole ya baka dariya tace “brazier da panty dinta nake nufi, gani gaban wasu masu azabar kyau, amma bansan size dinta ba”. Da karfi Prince yace “Kiki! If I don catch you….” tayi maza ta kashe wayar don kamar zai fasa kunnenta da ihu. Itama ta san da a kusa suke yau ko Taiwo bata isa kwatarta hannun Uncle ba, in ya murde kunnenta.
Ya kashe wayarsa yana fadin “Oh my God! Kiki ta girma, har ta fara raina shi, don ya maida kansa abokinta.
Ya koma ya kishingida, amma barcin da yake so yayi yaki zuwa sam. Sai juyi yake gefeda gefe akan sofa-bed, maganar Kiki ta jefashi cikin wani yanayi na begen yayi auren don yasan yana missing wata rayuwa da bait aba shiga ba har shekarun girma suka riskeshi, sai kuma bacin rai ya biyo baya da wani tsohon tunani y gilma masa…
A can baya shekaru masu dama da suka gabata ya taba sayawa Haseena brazier da Panty da hannunsa, itace da bakinta ta gaya masa size tace ya sayo mata, a lokacin ne ma ya taba sanin wani abu brazier, da wannan tunanin dana kadaitacciyar rayuwarsa wadda bai nemi komai ya rasa a cikinta ba sai macen aure kadai, alhalin yanada tabbacin cikakkiyar lafiya ta kowanne dan adam a tare dashi, idan kuma by now ya rasa mazantakarsa ne duk ba mamaki, watakila yawan shekarunsa yasa ya rasa feeling na manhood dinma gabadaya, har gashi ‘yar da ya haifa ta isa aure, da wannan tunanin mara dadi kuma mai sosa zuciya barci mai nauyi ya dauke shi.
Yana fadawa ransa da zuciyarsa cikin barcin da ya debe shi mara dadi, mai wani irin nauyi; hatta matan aljannah (hurul eeni) in aka bashi zai ce baya so! Ko kuwa yace ya yafe!! He is not destined to experience that kind of life!!
**** **** ****


1/RABI’UL THANI HIJRIYYAH
P
rince Abdurrasheed Idris Akanni, yana wannan barcin mara dadi agareshi kife da ciki (rub da ciki) akan ‘sofa-bed’, irin kwanciyar da bai san ma yayi ba don tun suna kanana Nenne ke gaya musu bata da kyau ga musulmi, mafarkai barkatai masu alaqa da aure da ‘ya’ya na ratsawa ta cikin barcin nasa mara dadi. Daidai lokacin da Turaki of Ilorin (mai bin mahaifinsa a haihuwa) ya mikawa Malam Barau Hamza (madaurin aure Aisha-Siddiqah) wato wan mahaifinta sadakin Abdurrasheed na dankwala-dankwalan sarkokin zinare a cikin battarsu, ga “Aisha-Siddiqah Yunus”.
Aka daura auren nan da nan, bisa tsari da koyarwa irin na addinin musulunci, bayan an shafa fatiha, kalilan din shaidu kuma sun shaidah, masarautar Gombe data Ilorin da dangin Uwa da na Uban Siddiqah duk sun shaida domin kowanne bangare ya bada wakilai da suka shaida, aka fara musabiha a tsakanin iyayen wadanda suka kasance Yoruba da fulanis, daga kowanne bangare na farin ciki bayan kam]mala daurin auren mai albarka.
Abinda zai baka mamaki shine ko a kafar sadarwa daya ba’a sanar da wannan daurin auren na Prince ba, wannan kuma ya faru ne bisa umarnin Emir, daga nan aka wuce fadar Uban kasar Gombe inda za’ayi reception na bayan daurin aure tsakanin dangin Siddiqah maza, dangin Nenne da kuma Akanni’s dake nan har lokacin.
Sun kwashe akalla sati guda kenan a garin Gombe suna gudanar da komai cikin nutsuwa har alkawarin Allah ya tabbata a yau Juma’ah daya ga watan Rabi’ul Thaani da Siddiqah ta tabbata matar Abdurrasheed.
**** **** ****
“
An daura!”.
Dade ya gayawa Nenne, fuskarsa fal murmushi kamar tana kallon shi, ya kara da cewa “sai ki daukota ki dawo da ita Gombe toh, kin kama musu ‘ya kin rike daga zuwa asibiti, at least tayi sallama da iyayenta ko, in yaso su kawo ta da kansu”.
“Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Kawai Nenne ke maimaitawa a fili.
Nenne ta shigo dakin da Siddiqah take da wani irin annuri a kyakkyawar fuskarta irin wanda Siddiqah ko wani dan adam ko ‘ya’yanta babu wanda ya taba gani a tare da ita, zuwa yanzu alamu na raunin ciwo sun dade da bayyana a tare da ita, tana dai daurewa ne tana kuma karfafa jikinta da son ayi biki a gama lafiya kafin ta tafi Morocco ayi mata surgery, sai ta tadda Siddiqah tana hada kayanta a trolley dinta hajaran majaran, fuskarta fal damuwa da ci da zuci.
“Siddiqan Nenne yaya dai? Kayan menene haka aka dannawa a jaka ba ko ninki? Ko mun miki laifi ne za’a yi mana kaura?”
Cikin damuwa Aisha-Siddiqah ta dago ta dubi Nenne tace “Gida nakeso zan tafi, baku yimin komai ba Nenne sai alkhairi, na duba date ne a kalanda naga gobe za’a koma makaranta shiyasa nake hada kaya na, kinga har na cinye hutun ma a nan, ban ma Ummana ko kadan ba”.
Nenne ta karaso cikin dakin ta dafa kanta cikin tausayi da wata sabuwar kaunarta, tace “babu laifi Siddiqah munyi waya da Umman naki ma, tace goben dama zaki koma saboda makaranta”. Siddiqah ta hau murna.
“Allah Nenne ba tsokanata kike ba gobe zan koma Gombe?”
Sai ga Siddiqa tana far’a tana dariya kamar ba itace yanzunnan cikin damuwar data sameta ciki ba.
Nenne tace “wannan ‘mood swing’ haka Aisha ai sai kisa inyi tunanin mu din ba kya jin dadin zama damu ne, ko nida ahalina bama kyautata miki a kan guiwa kike”. Siddiqah ta rufe ido tana jin kunya, sai ta kara fadada far’arta, tana “a’ah Nenne ba haka bane, nayi kewar Umma na ne da yawa, kin san ban taba zuwa ko’ina na kwana ba banda makaranta, sai nan, ko gidan ‘yan uwanmu na Kumo muka je da sallah bana yarda in kwana”.
A washegarin ranar Nenne da kanta ta maida Aisha Gombe. Kai tsaye suka zarce zuwa gidansu Aisha kafin ko’ina. Nenne bata ko jima ba tasha kunun zaqi da cincin da aka sauketa dashi don basu samu Umman Siddiqah a gida ba sun fita da Baba Yunusa sayayyar wasu daga kayan auren Siddiqah duk kuwa da Emir yace a gaya musu yarinya kadai zasu dauka zuwa Ilorin. Sai ‘yan uwan Ummanta fal gidan. Ganin suna neman fallasawa a gabanta ta hanyar kiran Siddiqah da “amarya oyoyo!” Da ake tayi don haka suna gaisawa aka sauke kayan Siddiqah Nenne da direbanta suka juya a gurguje zuwa gidan Sarkin Gombe, suna tafe suna waya itada Haj. Zainab. Inda Nenne tace da ita a shirya amarya gobe-gobe zasu dauketa su wuce Ilorin bisa umarnin Maimartaba. Haj. Zainab ta kawo uzurin cewa a kara musu kwanakin tarewa su gama shirinsu a nitse, Siddiqah tayi sallama da danginta su kuma samu su lallasheta akai, tayi mata shirin aure kuma da ya dace. Nenne tace.
“Kada ki damu da wannan Zaynaba nima Uwa ce, uwar kuma ta ‘yaya mata, nasan me kike nufi, in lokacin tarewar yayi zan yiwa Siddiqa abinda ko su Murjanatu ban yiwa lokacin aurar dasu ba.
Zuwa yanzu dai Ilorin za’a isa da ita ga Emir da dangin mahaifin su. Kin gama mana alfarma ai tunda kin bamu diya kun gama komai, ku dai yi kokarin sanar da ita da lallashinta daga yau zuwa gobe”.
Da haka sukayi sallama Haj. Zainab da Nenne, itada direba suka karasa fadar Gombe.
Umman Siddiqah kuma ta gayawa Malam Yunus isowarsu bayan sun gama waya da Nenne, don haka a gurguje suka karasa sayayyar abinda suke yi suka koma gida.
Kukan Petel tun daga soron farko shi ya fara bakuntar kunnuwansu.
Daidai lokacin da suka sawo kai tsakar gidan, sai suka ji muryar Addar Kumo, sarkin kankanba wato kanwar Malam Yunus Magajiya da tazo daga Kumo tana ce da ita.
“Shin wai laifi ne don su Hasssilo sun kira ki amarya? To ko kina nufin baki san an daura aurenki bane tun jiya, da Dan Sarkin Yarbawan Ilorin take ko Ibadan??”
“Sun jika mana aiki!” Inji Umma cikin bacin rai, tana karasawa cikin gidan da sauri har zanin ta na kuncewa. Siddiqah na ganin shigowar Ummanta ta hau ja da baya a firgice, idonta cikin na Umma tana tambaya.
“Umma wai da gaske ne?”
Umman ta mika hannu zata rikota sai ta goce. Ido fal hawaye tace “ki gayamin Umma da gaske suke? Wai an yimin aure bada Ishaq ba? Umma wai da Bayerabe? Shiyasa kika kaini gidan Yarbawa na zauna dama Umma?
To makarantata kuma fa Umma? Don Allah kada kuyi min haka!”
Umma na isowa don ta rike Siddiqa dake kuka tana mazari sai gani tayi yiiip! Aisha-Siddiqah ta fadi kasa ta mimmike mata.
Umma cewa take “ku bani inhaler”. Addar Kumo na fadin “ki nutsu Zaynaba, ki gane wannan ba tashin Asma bane, shidewa ce (suma) ne”. Malam Yunus na karasowa bai ce komai ba, sai kawai ya kinkimi Aisha a kafadarsa zuwa motarsa, sai asibitin da take da file wato FMC Gombe.
**** **** ****

A can gidan Sarkin Gombe kuma su Nani Oummana abin nema ya samu, shirin biki ya kacame ka’in da na’in, bikin jikan da aka jima ana jiran zuwan ranar aurensa a zuri’arsu Nenne Sappa, duk da Nenne tace bata son biki, sabida bata jin dadin jikinta. Uban kasa yaki amincewa, yace ta kwanta a daki ta huta ta barsu suyi. Abdulrasheed ne, dole su yi biki kona kwana uku ne, tunda dangin ubansa ma zasu yi irin nasu a Ilorin.
Yayinda can gidansu amarya hankula ba’a kwance suke ba suna asibiti tun faduwar Aisha suke asibitin a hannun likita Umar. Ko a lokacin Haj. Zainab sunyi waya da Nenne ta gaya mata ga akori-kurar kayan abinci nan an taho saukewa sabida bakin da suka zo biki, komai na al’adar bikin gidan Sarkin gombe an hado musu dashi rankatakaf.
Hajiya Zainab bata gaya mata Petel dinma tana asibiti ta rikice musu da sambatu ba. Don kada hankalinta ya rabu biyu, ko daga jin muryarta ta fahimci Nenne bata da lafiya, sai Haj Zainab ta roki alfaramar Nenne, tunda itama bata jin dadi kan cewa suna so a daga daukar amarya zuwa kwana uku don a samu a sanar da ita ko me ake ciki a kuma samu a lallasheta.
Nenne ta amince da hakan inda ta sanar da ita matan ‘yan uwan mijinta masu daukar amarya zasu zo daga Ilorin, zasu hadu da nata ‘yan uwan su dauki amarya. Likita Umar

Please Login or Register in order to submit comment