You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
shine likitan asmar da Petel take gani tuntuni shi suka samu nasarar gani a hannunsa Siddiqah take, kuma yana kula da ita yadda ya dace don dama sun saba sosai shi da ita, yace ba asma ce ta tashi ba, suma tayi dan firgici, ya bata (bed-rest) na kwana daya don yanaso yayi counseling dinta tunda Haj. Zainab ta gaya masa aure ne aka yi mata bagatatan.
Koda ta farfado ma bin su Ummanta take da ido ta dauka asma ce ta kawo ta asibiti ta manta shaf da abinda ya faru din.
Duk yadda Likitan ya iya lallashin Siddiqa don ta gaya masa abinda ya firgitata da bakinta yau Siddiqah shiru tayi masa, tace ya tambayi Umma don ita ta manta. Umma dake gefe tace. “Likita ba abinda aka yi mata rigima ce irin tata daga dawowarta bata ko ganmu ba, ta tsinci magana a wajen ‘yan uwanta shikenan ta fadi ta sume min.
Umma ta kara da cewa “Petel dina, ai kinsan daga ni har Abbanki masu son farin cikinki ne, ba abinda zai daga miki hankali ba”.
Sai a lokacin Siddiqah ta tuno exactly me ya faru daga shigowarta gidansu daga Lagos. Da sauri Siddiqa ta katse Umma hawaye nan da nan ya cika idonta. “Umma! Kuna son farin ciki na shine kuma aka aura min Bayerabe da ban ma san shi ba?
Umma kinfi kowa sanin yadda bana son yarbawa”. Dr. Umar wanda mahaifiyarsa ‘yar kabilar Yoruba ce, bai san sanda ya kufula yace da Siddiqah.
“shi Bayerabe ba mutum bane Aisha?”
Ta yi maza ta sunkuyar da kai, hawaye ya zubo mata tace “amma ai inada miji, kuma ban gama makaranta ba”.
Abban Siddiqah da Baba Barau tare suka shigo lokacin, suka ja kujera suka zauna ta gaban gadon Siddiqah aka cigaba da lallashin tare dasu. Muryar Abbanta abin tausayi yace “Aishah-Indo Siddiqah, to uban Ishaq din yace bazasu aureki ba tunda kinada cutar numfashi”. Aisha ta zaro ido daga kwance, Baba Barau ya gyada kai ya gyada mata kai cikin tabbatarwa, yace “to su kuma wadanda kikewa kabilancin son ki suke da asmar taki, da dukkan zuciyarsu sun karbeki cikinzuri’arsu, Ubanki kin ganshi sabida ya faranta miki ya kuma fita hakkinku don yasan kinason yaron nan shima yana sonki da gaske sai da ya yi tattaki ya isa ga mahaifin Ishaqa, amma bawan Alllahn nan ya wulakanta mu, don haka ya rage naki ki nemawa kanki mutunci kije inda ake son ki ko ki tsaya shirmen banza a inda ba’ayi dake saboda lalurarki.
Hajiya Sappa Uwa ce da kowane Da zai so ta za uwarsa. Ke ya kamata ki bada wannan shaidar, kowadanne iyaye zasu so hada zurri’a da ita saboda karamcinta da girmama dana dam da halin tawali’u, ai dai kin dan zauna da su zuwa yanzu ya ci ace kin san ko su su waye.
Inna kara jin Kalmar “Bayerabe” ta fito a bakin ki wallahi sai na kumbura miki shi, don dama yayi miki kadan”.
Suka taru su duka har likita Umar suna tausarta, likita yace “Aisha kibi zabin mahaifinki nina gaya miki in sha Allah bazaki nadama ba, a cikin biyayyar iyaye babu nadama kin ji?
I am a Yoruba man by maternal tribe, ina tabbatar miki mun iya rikon aure mun iya tattalin matanmu da girmama su”. Umma tace “wallahi wallahi bamu yi miki zaben tumun dare ba duk da ban san shi ba ban kuma ganshi ba ko a hoto, zuri’ar Hajiyar Lagos ba yarbawa ba ko inyamurai ne zan basu ke albarkacin ta da addu’ar da naji tana yi a filin Arfah, tunda dai kalmar shahada ta hada mu bakidaya.
Ni bansan ina kika koyo wannan kabilancin naki ba, ni dai baki taba jin na ce wani da ba bahaushe ko bafillace ba daban yake da sauran mutane ba”.
Ko ta ina sun rufu a kanta basa ko bari ta ce uffan, wannan ya koro nashi wannan ya cafe. Baba Barau yafi kowa zafi, shi baya hadawa da lallashin ma. Cewa yake ta kara fadin Kalmar yarbawa ko bayerabe yanzu ya kumbura mata baki. Malam Yunus shi ke lallashinta, yana gaya mata kaddadar kenan data hado Hajiya Zainab da Hajiya Sappa a aikin Hajji, wato kaddarar aure a tsakanin ‘ya’yansu.
Kaddara mai kyau, wadda aka kullata a gaban Ubangiji a dakin Allah kan dutsen Arfah mai alfarma.
Domin Umma ta gaya musu addu’ar data ji Haj. Sappa nayi a kan dutsen arfah. Ta ce tun a lokacin ta fada a ranta baiwar Allah inama zai amince da Petel dina! Ko ba komi addu’arta da tsarkin zuciya tayi ta, kuma sai ta riga ni furtawa kafin ni in furta nawa fatan.
Ina kara fada miki cewa ban ganshi ba, ban taba ganinsa ba ko a hoto ban kuma taba jin muryarsa ba, amma shi na zaba miki a matsayin miji Petel”.
Aisha ta saka kuka tana cewa “Umma karatuna, Umma makarantata shikenan bazan gama aji shidda ba?”
Malam Yunus yace “Aishatu ni malamin makaranta ne kin fi kowa sani, na san muhimmancin ilmin diya mace, ko bana raye bazan bari a aurar dake a inda za’a tauye ki ta fannin ilmi ba. Ki bari ki samu lafiya ki barwa Allah komai, shi zai iya miki kinji ko?”
Har dare suna kanta, kuka da sheshsheka har da jijjiga don kuka. Hawaye ya hade da majina. Saida likita Umar yayi mata allurar barci suka samu lafiyarta.
Washegari da safe data tashi nurses suka bata maganin ciwon jiki da Panadol ta sha. Umma ta hada mata tea mai zafi da kauri shima ta sha. Wajejem karfe sha biyu na rana yace zasu iya tafiya gida sannan yace da Siddiqah ita kadai.
“Babanki ya bani tausayi Aisha, ki duba yadda ya damu da halin da kike ciki, jiya ya sameni a ofis ya gayamin yafiso yayimiki abinda kikeso amma yana ganin kimar wannan baiwar Allah, kiyi hakuri kiyi masa biyayya kinji bazaki tabe ba”.
Ya kara da cewa “one more albishir, Yarbawa fa sun fi Fulani iya soyayya Siddiqah”.
Siddiqah ta harareshi sannan ta gyada kai, tana tsane hawayen idonta, Umma kuma na can tana tattara ‘yan kayansu batasan me Dr. Umar ke fadawa Siddiqah ba wanda shi fisabilillahi an yi masa riga malam masallaci ne tuntuni yana matukar son Siddiqah, amma da yaji ko sakandire bata gama ba shiyasa ya dakata, don shi kadai take gani a matsayin likita duk sanda tazo FMC. Umma tazo inda suke sukayi sallama da likita ta kamata ta sakko daga gadon suka wuce zuwa mota inda malam Yunus ke zaune cikin motar shi Toyota Corolla yana jiransu.
Ko kafin su iso gida, an sauke buhunhuna da katon katon na kayan abinci daga gidan Sarkin Gombe. Siddiqah ta wuce uwar dakin Ummanta ta kule a karshen gadon Umma bata ko kula kannen iyayenta dake tsokanarta ba, wai ciwon aure take yi ai normal ne. Addar Kumo da yake mijinta bai jima da rasuwa ba, tabi Siddiqah har dakin Umma tace da ita, “to ni ki bar min Bayeraben mana? Shashasha jikan uban kasar Gombe ne ta fannin uwa, ni inasonsa tunda ba wani tsufa nayi ba”. ta kara da cewa (cikin jin takaicinta) “Su Indo! An tako arziki ana kokarin fatali da shi da gangan”.
Siddiqah kasa shiru tayi tace “Adda wallahi Allah na bar miki bayeraben dari bisa dari kuma da zuciya daya, koda Ishaq ba zai aureni ba ai na fi karfin auren bayerabe jikan oduduwa”. Sai jikake gab! Umma data shigo ta gabje bakin nata.
“Inace dazunnan Babanki Barau yace kada a kara jin kalmar nan ta kabilanci daga bakinki?”
Siddiqah kuka ya koma sabo, bazata iya tuna (when last) Umma ta kai hannu jikinta ba sai yau. Itace ta fari itace auta tsakanin ta da Umma sai soyayya. Sai yau akan Bayerabe dan kawarta. Tayi kuka-tayi kuka ta gode Allah bata kara tankawa kowa a gidan ba. Daga bisani kuma barci ya dauketa.
Data farka da la’asar da kyar Addar Kumo tasa ta tayi wanka shima duk rabi ita ta cuda mata baya Siddiqah na rufe kirjinta wai kada Adda ta gani. Wannan abu ya kara kular da Siddiqah don tayi tayi Addar ta fita ta bata wuri tayi wankan da kanta taki, tace na san biji-biji zaki yi, gara in cuda ki da kaina, da aka haife ki ma ni dinnan nina cude ki, har yaushe kika yi girman? Ina abin yake da zan gani wai maye ya ci jinjiri kirji kamar ‘ya’yan goriba? Haka in kin haifo mana jikan Uban Kasa ni zani har kasar Yarbawa in sake wanke ki fes da runhu da ganyen darbejiya”.
Kabakin abinci iri-iri aka dinga fiddawa daga gidan su Siddiqah da soyayyen naman Sa zuqu-zuqu akai, wanda aka saka cikin abincin ya wadata. Lemuka (soft drinks) kamar a wanke tsakar gidansu Aisha dasu. Surutu iri-iri a Jeka da fari, don basu bayyana neman auren ba sai bayan daurin auren aka bayyana kowa yaji.
Wasu ma sun ce Uban kasa ne da kansa wato Yayan Nenne Sarki mai ci a yanzu Abdul Yasar Jalloh Umar ya auri Aisha-Siddiqah. Duk kuwa da cewa ana kishin-kishin wai sarkin Ilorin ne da kansa ko babban dansa. Shaci fadi iri iri musamman daga gidansu Ishaq. A lokacin shi Ishaq yana can Abia state yana bautar kasa babu wanda ya sanar dashi daga gidan su.
A kwana biyun Aisha ta dan kwantar da hankalinta, amma bata fitowa daga daki. Adda tayi mata kwalliya amma iyakata uwar dakin Umma. Ko falo bata zama. Musamman da Malam Yunus jiya da daddare yazo har dakin Umma ya sameta, ya bata kunshin balangun da ya shigo mata dashi mai zafi da ruwa-ruwa, don yasan ko abinci ba sosai take iya ci ba, sai Umma ta zauna ta bata a baki, shima loma uku take yi tace ta ko shi.
Malam Yunus ya zauna a gefen gadon da Aishah take kwance, yace da ita “kwantar da hankankalin ki kin ji Indo?
Dazu nayi Magana da Hajiya Sappa kan makarantarki, ko zasu mana alfarma su bari ki karasa kafin ki tare, tunda term biyu kadai ya rage miki? Tace kada in damu, gtana sane da wannan, zasu wuce dake gidanta a Lagos ne daga Ilorin, in an kai ki kin ga dangin mahaifinsa, Kakansa ya ganki yasa albarka, amma a gidanta zaki zauna har sai kin zana WAEC da NECO zaki bari ki tare a gidan mijinki”.
Wannan albishir ya dan faranta ran Siddiqah.
Ba’a tashi drama da Siddiqah ba sai a washegari da ‘yan daukar amarya suka iso da hantsi ido na ganin ido daga masarautar Gombe, tareda hamshakan dangin Abdulrasheed mata daga Ilorin. Matan Baffanninsa ne su duka tara da dangin marigayiya kakarsa Olori Murjanatu, wadda ta haifi Waziri Idrisu, su uku suka zo daban, suka hade da mutanen Ilorin suka taho Jeka da fari a manyan motoci Hummer Jeep bakake wuluk masu tinted.
Raba Aisha da Ummanta kadai abin kallo ne domin wani ‘show’ ya koma, don saida aka boye Umman aka iya fitarda Aisha daga gidansu zuwa fadar Gombe, tare da Goggonninta su Addar Kumo, da Baba Barau da kansa a gidan gaban motar a matsayin uban aurenta kamar yadda yake a al’adar su dole a yi mata uban aure.
Nasiha iri iri babu wadda iyaye da ‘yan uwa da baba Barau basu yiwa Aisha-Siddiqah tun daren jiya ba. ko ta dauka ko bata dauka ba dai ta ji su.
A gidan Sarkin Gombe a dakin Nani Ummana wato Kakar Abdulrasheed data haifi Nenne Sappa aka kai amarya da iyayenta, Nani duk da ta tsufa sosai amma kasancewar 'ya'ya na kula da ita ga rike ibadah tsufa baisa ta rikice ba, tsaf take, cikin nutsuwarta, ita ta amshi amarya da iyayenta inda aka wadatasu da nau’I nau’I na kayan abinci na alfarma da abin sha gwargwado. Daga bangaren matan Sarki na yanzu wato Yayan Nenne Uban Kasa Abdulyassar wanda shi ya gaji mahaifinsu duk an kawo kabakin abinci iri-iri na sarauta.
Da daddare ne aka kai Aisha har turakar uban kasa yayi musu addu’a mai tsayi, inda yace da ita suna mata maraba da shigowa masarautar Gombe. Suna mata fatan alkhairi mai yawa da fatan bada jimawa ba ta cika musu gida da 'ya'ya.
Sun kwana a gidan Sarki karkashin kulawar Nani Ummana da hadimanta sai washegari Nenne da wasu daga ‘yan uwanta da iyayen Abdulrasheed mata da suka zo daga ilorin suka dauki amarya suka wuce Ilorin da ita ta jirgin sama, don a kaita ga Emir, da kuma dangin mahaifin sa da da yawa basu ma san da zancen auren ba. Abinda zai baka mamaki hatta Taiwo bata san komai ba. Nenne da Dade suna ta boyewa, Taiwo itace kunnen Abdulrasheed shiyasa suka boye mata kada su bata musu shiri, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya kira ta a kan maganar don ta tafi UK tare da mijinta bayan y agama hutunsa.
Da yawa cikin family din su ma basu sani ba, banda matan baffaninnsu da suka je Gombe dauko amarya.
Princess Fatima da Princess Firdausi kuwa suna can gida Lagos, basu san meke gudana ba, sun dauka Nenne ta tafi mayar da Aisha wajen iyayenta ne kawai, daga nan zata ga gida ta dawo, basu san ana can ana bidirin auren Hamma (Prince) da Aisha a Gombe ba tare dasu ba.
Duk abubuwa na al’adar su na karbar amarya an yi wa Aisha-Siddiqah a Ilorin, aka kuma kaita ga Emir. Sarki Abdulrasheed dan Abdullataeef Akanni, ya dade yana musu addu’a itada Kehinde ya kuma baiwa Aisha kyautar zoben zinare mai daraja a cikin battarsa, kyauta ce ta bajinta da sarki ya dade baiyiwa kowa ba. domin kuwa zoben na marigayiya Olori Murjanatu ne da ya gada.
A kofar fitowarsu daga turakar Emir ne mayafin Siddiqah ya dan zame, fuskarta ta bayyana sai a idon Bisola. Bisola ta cika da mamaki, wannan kamar abokiyar fadanta Siddiqah Yunus. Ta tambayi ta kusa da ita aka tabbatar mata daga Gombe aka aurota. Bisola sai da ta san yadda tayi ta kutsa cikin mutane ta isa har jikin Siddiqah wadda ke rike cikin hannun Adda Magajiya, ta sunkuya daidai kunnenta ta ce “an fadi ba nauyi. Aisha Sadiqqah! Kece kuma kika bige da auren dan sarkin yarabawa?”
A firgice Siddiqah ta dago sai taga Bisola Akanbi. Bisola ta kyabe baki ta ce “dama an ce mutum bai san inda ranarsa zata fadi ba. Sai a koyi kiyaye harshe acan gaba”. Ta murguda baki ta kada ido ta wuce cikin ‘yan kallo.
Kafin su wuce Lagos kusan duk masarautar Ilorin sun samu labarin auren. Masu mamaki nayi masu jin haushi da takaicin an rasa wadda za’a baiwa Prince duk cika da batsewar masarautarsu sai diyar fulanin arewa na yi, kuma wai ba ‘yar sarauta bace diyar malamin sakandire ce, ko daga nan Aisha Siddiqah bata samu wani maraba sosai daga dangin mahaifin Prince ba.
Musamman da ba wani shahararren biki aka yi mata ba irin wanda aka saba yi a gidan, ba kuma angon, kuma babu danginta masu yawa da suka nuna ita mai yawan dangi ce, sannan kowa ya tabbata Prince Kehinde, bai san ma ana yi ba. Rabonshi da kasar shi an doshi watanni uku kwarara yanzu.
Sai bayan sun koma gida Lagos ne an kai Aisha dakinta na da, an kai mata duk abinda zata bukata sannan Nenne ta samu nutsuwar zama ta kira babbar diyarta Taiwo a waya, dake Lancashire a lokacin tare da maigidanta.
Bata san cewa kafin ta kira ta tuni Fatima ta kira Aunty Taiwo din cikin tsegumi da mamaki, wai Anti Bisi (matar Uncle dinsu Malami Uban Doma) ta gaya mata sunje Gombe dauko amaryar Hamma Prince, amma meyasa Nenne bata saka su a ciki ba. Me hakan ke nufi?”
Taiwo (was like) irin bata yard aba wasa ake yi, hakan ba mai yuwuwa bane a yiwa Kehinde dinta aure babu saninta. Wane irin aure ga Prince haka bagatatan kamar wasan yara? Ita din ai daga mahaifiyarsu wato Nenne, sai ita a mutane masu matsayi cikin rayuwar Prince, kuma ta ya za’ayi masa aure babu sani da amincewarsa sai kace wai saurayi ko karamin yaro? Don ko jiya sunyi waya dashi lafiya-lafiyar Allah sukayi sallama bai ce mata komai ba, mai nuna ya san zancen.
Tana kashe wayar Fatima don tsananin haushi ta kasa cewa komai, sai ga kiran Nenne na shigowa, kamar jira take Fatima ta gama tseguminta sannan ita kuma ta kira.
Taiwo ta amsa wayar mahaifiyarsu ba tareda ta nuna jin haushinta na tsameta da tayi daga al’amarin ba. Nenne ta kwashe komai ta gayawa Taiwo, tun haduwarta da Hajiya Zainab a tafiyar filin Munna, da yadda taji sha’awar karbawa Abulrasheed auren diyarta bai ko sani ba, ba don komai ba sai don ita kadai taga ta dace dashi. Yarinya ‘yar masu mutunci sannan mai addini da tsarkin nasaba. Amma ina! Hankalin Taiwo yana kan Haseenah da labarin data zo har UK ta bata akan abinda ya faru tsakanin ta da Tokumbo, cewa daga baya ta gane magani Tokumbo yasa mata a lemo a gidan Prince, yayi raping dinta a dakinsa shine har Prince ya zo ya gansu basu sani ba. Da sauran maganganu very sensitive na kare kai, da yasa ta daina ganin laifin Haseenah kwatakwata.
Ai daga jin Nenne tace daga Gombe ne ta karbawa Hamma aure, nan take Taiwo ta tuna da zancen yarinyar nan ‘yar siririya da Fatima ke bata labari kullum, wadda tace Nenne ta dauko a Jeka da fari tana zuba musu fi’ili a gida har da kyamar abincinsu.
Babban abinda ya bata ran Taiwo da aka yi abinnan babu sanin ta, ba kuma ita ta tsara komai ba. ba karamin buri ta ciwa auren Kehinde dinta ba duk ranar da yazo. Amma wai an yi an gama babu ko saninta.
Taiwo nada son girma, wannan halin a ciki jininta ne, wanda ta tashi dashi a matsayinta na babbar Yayarsu tun suna yara tanada son seniority. Hakannan tanada son duk wani sha’ani in dai ya shafi Prince Kehinde ya kasance kacokam a hannunta. Kuma wai yarinyar da aka ce kyamar kabilarshi ma take yi, koba itace akace wai bata iya cin abincin gidansu ba. Me Kehinde zai yi da karamar yarinya haka (teen) mara exposure? Ai ko Haseenah da ya so ta baiwa shekaru 22 baya a lokacin, kuma tana ajina uku a jami’a a turai, duk da shi ya saka ta. Ta tabbata Prince ba zai taba yarda da wannan zabin ba ita kuma har kullum tana bayan abinda yake so ne.
Ita a wurinta Prince har gobe yana son Haseena bacin rai ne da kishi, wanda tayi alkawarin sulhunta su. Nenne bata taba yin wani hukunci da ya bata ran Taiwo irin na wannan lokacin ba. Don ta katse duk wani hanzarinta na shirin sulhunta Haseenah da Kehinde. Kafin Taiwo tace komai, Nenne ta soma gargadinta kan cewa bata yarda Hammansu Fatima ya ji komai akan maganar auren shi daga bakinta ba, ta kyaleshi har zuwa ranar da yayi niyyar zuwa don kansa, bata yi mishi aure don ta takura shi ba, ita da kanta zata sanar dashi ta hanyar da zai fahimceta, don yanzu makaranta ma zata mayar da Aisha abin bana gaggawa bane, zata ta zana WAEC da NECO kafin lokacin da yaga damar zuwa don radin kansa.
Taiwo was speechless. Har suka gama magana da Nenne, bata yarda ta ce uffan ba don bacin rai, ita bata yarda bama ba’a mafarki taji zancennan ba. Wasa kawai ake yi hakan ba mai yuwuwa bane Haseenah da Kehinde zasu komawa juna da taimakonta. Don a halin yanzu ma suna tare da Haseenah a UK, wadda tayi tattaki ta sameta har gidanta a Lancashire ta gaya mata komai na hanyoyin da Tokumbo yabi ya yaudareta ya rabata da Prince.
Ita kuma kamar wata Rakumi da Akala duk tabi ta hau kai ta zauna. Ita ta san zuciyar Prince har gobe Haseenah take so, don soyayyar da yayi mata irinta ce ake kira soyayya ta gaskiya da babu material attachement, tunda kuwa a kanta ne ya guji dukkan ‘ya’ya mata.
Haseenah ta gaya mata cewa ta dade da barin kasar Japan, wato bayan kammala karatun digirinta, tana aiki da bankin Barclays a yanzu haka a garin Leicester. Har gobe aure ya gagareta, ba don batada masoya ba, a cewarta sai don Prince kadai take jira ya huce.
Yadda Nenne ta sanar da Taiwo haka ta gayawa Firdausi da Fatima, cewa kada su sake su sanar da shi sai ya zo don gigin kansa.
Taiwo ta rasa me yasa ta yarda da duk abinda Haseenah ta gaya mata, har hakan yasa kwanannan take jin kewar rashin Haseenah cikinsu a ranta, ji take babu macen da ta kwanta mata a matsayin partner ga dan uwan nata irin rainonta HASEENAH AMBURSA! Yo waye yake sama da aikata kuskure ma? Haseenah ‘yar adam ce kamar kowa, mai sexual feeling at her very age a lokacin, Nenne kuma ta hanasu aure itada Prince, don haka ta dauko uzuri saba’in ta yiwa Haseenah tun sanda ta sanar da ita asalin komai da ya faru ta daina tsangwamarta a ranta.
Sai ma ta koma ganin beken dan uwanta kan ya fiya kullata. Abu baya taba barin zuciyarsa ya wuce. Shi Kehinde din zai ce a tsayin rayuwarsa bai taba kusantar kowacce mace bane? Musamman in akayi la’akari da inda yake zaune, a matsayinsa na namiji mai cikakkiyar lafiya da arzikin rayuwa mai albarka irin wannan?? Saidai idan da gaske ne da ake kishin – kishin din cewa, bashi da lafiya ta auratayya ko aljana ta shafeshi.
A ganinta Haseenah ce kadai ta dace da bukatun Prince, ita kadai zata iya baiwa Prince kulawar aure da ya dade yana bukata daga mace, ba wannan yarinyar kamar ‘yan tallan nono ba.
Fatima ta tura mata hoton Aisha Siddiqah ta waya ba tareda Aisha ta san lokacin data dauketa ba, tun ranar da sukayi discussion a kanta, kyau kam akwai shi tareda Aisha-Siddiqah Yunus itama ta shaida, ko makiyin Aisha zai shaida wannan farat daya, gashinan har neman zuba yake inji zuciyar Aunty Murjanatu, ga cikar sumar kai, ta gira data ido masha Allah, amma kuma nakasunta shine ba exposure (ba wayayyen kai) da zata jera da Prince matsayin matarsa.
Har ila yau kamannin Siddiqah sun nuna innocent looks dinta, babu sanin me duniya take ciki ko dabarun zama da namijin duniya irin Prince Kehinde.
Uwa Uba babu dressing a tareda Aisha-Siddiqah irin wanda zai dauki hankalinsa a matsayinsa na celebrity, ba cikar kirji balle na mazauna kamar ma yanzu ne ta soma balaga, Ya Ilahi ga mazansu na Yoruba da son mata masu manyan abubuwa, gatanan dai a hoton irin (typical Fulani girls) na garin Gombe. Wadda babu abinda take
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500