You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
mara nasabar sarauta, marar ajin rayuwa irin nasu zata iya zama mata ga Hammansu Fatima.
Ya Allah kanwarsa Fatima da ‘yar uwarsa Taiwo ma ya aka cika dasu wajen kasaita balle kuma shi kansa? Ita sau dubu gara mata Ishaq da yake bahaushe/bafillace ba dan kowa ba akan Bayeraben Prince din. Darajar idon Nenne kadai ya hanata cewa don Allah in ya tafi kada ya kara dawowa.
Tafi jin dadin rayuwa cikinsu da ya bar gidan. Don a dan zuwan Prince gidan hatta numfashi wuyar shaqa ya koma yi mata. Kwarjininsa ya bi ya cika kowanne sako na gidan Engnr. Idris Akanni.
Dade kadai ne ya san cewa Siddiqah murna take da komawar Prince, don yafi kowa lura da reactions dinsu ita da shi, don lokacin Nenne bata gama samun kanta ba, so bata ta tasu ta lafiyarta take, amma shi yana hankalce da motsin kowannensu, shi kansa Prince ya takaitawa kansa magana cikin ‘yan uwansa a wannan zuwan da yayi ba kamar yadda ya saba ba.
Daga irin kalaman bakin Nenne na yanzu Dade ya fahimci ta fidda rai akan al’amarin, wato ta fidda ranta akan auren Prince da Aisha. Jira take, Allah-Allah take Siddiqah ta gama WAEC ta maidata Gombe, akalla zata cigaba da rayuwa da mahaifiyarta a gefenta. Ita kuma ta fita zargin kanta na cewa bata kyautawa Siddiqah ba.
Don haka Dade ya fara nasa shirin shima don ruguza na Nenne. A wurinsa Aisha tazo cikin ahalinsa kenan. Aure tsakaninta da Abdulrasheed anyi kenan, ko yace yanzu aka fara daga nan har gaban abada, bazai yi saken da Siddiqah zata bar Abdulrasheed ba no matter ho worst things are becoming.
Hasalima bada sanin ita Nenne ba shi da mahaifinsa maimartaba sarki sun riga sun yi shawara, ji da Emir yayi Abdulrasheed yazo har ya tafi bai nuna bukatar daukar Siddiqah ba yace lallai jikan nasa sai an fito masa ta bayan gida, Emir ya gayawa dansa Engnr. Idris yadda za’ayi da Prince, yace in ma aljanar ce tare dashi da macen aure ta shiga gidansa alkadarinta ya gama karyewa, wato sunada yadda zasuyi maganinta cikin sauki.
Don haka yasa Dade ya fara shirin abinda ya dace akan Prince da Siddiqah.
Satin Kiki biyu tare dasu ta koma gidan iyayenta a Ilorin, bata tafi ba sai da tayiwa Nenne dadin bakin da yasa ta baiwa Aisha kan waya don a baya tace sai ta gama WAEC zata bata. A cewar Kiki ta yaba da hankalin Aisha tana so zata dinga kiranta akai-akai don neman shawara. Kuma bai dace a dinga hadata waya da Ummanta ta wayar Nenne ba a barta ta dinga kwana tana hira da Ummanta tunda yanzu bata kukan. Kuma dai Aisha bata da `BF’ a cewar Kiki da zai ke distracting karatunta da zancen soyayya.
Nenne ta kalli Kiki tana hararar ta wai bata da kunya, amma maganganun Kiki suka sa dole ta baiwa Aisha waya tsadadda, ta yarda Kiki na son Aisha.
Su Siddiqah sun fara jarrabawar gwaji wato mock kusan kullum suna waya da Ummanta da Abbanta suna binta da addu’ar samun nasara (albarkar Annabi).
**** **** ****
Watarana Kiki ta kirata tsakar dare daga Ilorin.
“Siddiqah ko kin san addu’ar rufe bakin mutum ya kasa magantuwa akan wani abu?” Dariya sosai Aisha tayi tace “Kiki wa kuma za’a rufewa baki dungurungum? Wane mai tsautsayinne ya shiga komar yar gatan Uncle dinta?” Kai tsaye Kiki tace
“Mamana! My Mum. Oh! My Mum is annoying.
Aisha tayi maza tace “akul! Kiki daina fadin haka gareta tun kafin mala’iku su rubuta” Kiki tace “To ya zanyi da Mum dina? Tosin yace zai zo Ilorin, musamman don ya gabatar da kansa gareta ya gaisheta ya kuma gaida Emir, amma ina tsoron gaya mata, don nasan bazata yarda ba, yanzu zata hau cewa sai Uncle AK yayi aure, bayan Uncle da kansa ya bani go ahead, har Tosin yaje ya sameshi a Qatar ya ganshi ya kuma amince da shi.
Amma ita sarkin tagwaitaka ta nace sai yayi aure zanyi, sabida Allah Aisha Mum bata kwareni ba idan ta janyomin na rasa Tosin? Abinda na sani ina son AbdulNasir sosai. Kuma Uncle din nawa ya amince dashi. Haka kawai Mum zata yimin sakiyar da babu ruwa. Bata san yawan ‘yammatan dake son Tosin bane”. Muryar ta yanzu gwanin ban tausayi cikin damuwa. Aisha ta san bayan wauta da gata da suka yiwa Kiki yawa, still da gaske tana neman shawara da mai hankalin da zai sa ta a hanya.
Ta san ko ta girmi Kiki to da kadan ne, amma hankalinsu da wayonsu ba iri daya bane. She’s so much infatuated akan Tosin AbdulNasir. Har tana ganin laifin mahaifiyarta akan saurayi.
Irin Kiki duk abinda wada suka yarda dashi ya fada musu dashi zasu yi amfani ba tareda wani dogon tunani ba. Siddiqah ta nisa, a hankali tace da Kiki cikin kwantar da murya.
“Kiki ki dinga addu’ar neman zabin Allah kin ji? Don’t be obsessed with him, ki bi mahaifiyarki akan duk abinda takeso wallahi zaki ga alfanu a gaba.
Kuma ko a kan son da kika ce min Uncle dinki na yi miki zaki iya yi masa solidarity ki jikirta baiwa zuciyarki abinda take so kamar yadda Mum take so sabida shi, da gaske baza taso ki yi aure ki haihu alhalin shi bai yi ba, baki son soyayyar twins ga junansu bane musamman in opposite sex ne (mace da namiji).
Nima bana son zaman gidannan, bana son zaman Lagos at all, amma yana iya? Dole na yiwa iyayena biyayya kuma ina kan yi. Na san ko bajima ko ba dade zan tsinci wannan biyayyar dana yi musu a gaba ko a kan ‘ya’yana ne.
Ke kinji dadi ma kina tare da ita har gobe (mahaifiyarki) an kuma barki kin gama karatu kafin ayi miki aure kuma ga dukkan alamu wanda kikeso za’a barki ki aura …..”.
Sai bayan ta fadi hakan ta tuno cewa ta saki layi. Kiki bata san wacece itaba har yau a gidannan. Bai kamata Kiki taji daga gareta cewa tana da auren Uncle dinta daga bakin ta ba, idan har Nenne da Aunties dinta babu wanda ya ga dacewar ta sani din ita akan me zata fada?
Amma ina! Aka ce magana zarar bunu ce ta riga ta fita, ta kuma shiga kunnen Kiki-Ruqayyat.
Kiki tayi dan jim, kafin tace.
“Kina nufin kina da aure? Ko kin taba yi kenan sister Aisha?”
Ta girgiza kai da sauri tana cewa “Kiki chapter closed, kiyi ta istikhara kina addu’a idan Tosin rabonki ne, kuma akwai alkhairi a tarayyarku, Allah ya kawo auren Uncle dinki kurkusa kamar yadda Mum keso, idan hakan ne kwanciyar hankalinta. Kada kimanta kullum tafi Tosin muhimmanci agareki”.
Kiki ta ja numfashi tace “Sister Aisha, my Mum is annoying, wadda take so Uncle ya aura fa ba wata bace Aunty Haseenah ce, his ex Haseenah Ambursa, koda yake ya so ta acan baya, amma wallahi yanzu baya sonta, ban dai san abinda ya raba su ba amma anfi ten years da rabuwarsu, rana daya naga ta dawo jikin Mum dina sun koma shiri, ni nafi Mum sanin Uncle dina, bakina da nasa yace min shi matansa Hurul eeni ne suna aljannah, me Uncle zai yi da Haseenah yanzu? Don kawai ya taimaketa?
Tsintacciya ce fa as in ‘yar gidan marayu bata da iyaye shiyasa Nenne bata so.
“Ho Kiki! Shafa labari Shuni!”
Duk da Kiki bata san me kalmar shafa labari shuni ke nufi ba, ta san yana nufin dai kamar ta faye surutu ko fadi ba’a tambayeki ba. Ta hau dariya tana cewa “da gaske nake duk abinda na gaya miki ni bana karya, ke nafi ganin dacewar Uncle ya aura kuma zan je har Qatar in sameshi akan hakan”.
Siddiqah tace da karfi “Kiki! Ni nace miki banida wanda nake so toh? Ba kyau cin naman mutane ki daina zancen wata budurwarsu. Is better you mind your business Kiki, ki rabu da sa damuwar kowa a ranki. In Allah yayi matarsa ce tunda Mum naso, sai kiga anyi”.
Kiki tayi maza tace “ba amin ba! Because my Uncle has a pure heart, I assure you he’s pure and clean, with a golden heart! Allah bazai bashi mace wadda ba mai tsarkin nasaba ba. Bazai taba auren mara asali ko lalatacciya ba in sha Allah”.
Amma ko bayan gama wayar su da Kiki, Aisha sai tayi jimm! Tana jin maganganun a ranta. Ashe shiyasa bata samu reception a wurin Aunty Taiwo ba, akwai wadda ta dade da yiwa dan uwanta tanadi.
Banda haka bata ga me tayi mata ba da ko gaisuwarta sama-sama ta amsa kuma a shaqare.
“Umh! Su suka sani” inji Aisha. Babu wani Bayerabe data saka a ranta balle damuwarsu ta dameta.
Sati biyu bayan nan su Aisha suka fara zana WAEC, wadda zata dauke su tsayi sati hudu suna zanawa.
Watarana Siddiqah ta fito dakin jarrabawa ta tadda Seun yana jiranta zai dauketa zuwa gida, suka kamo hanyar gida, sai taga Seun ya karkace kan motarsa ya tafi wani wurin da ita. Saida suka isa wurin ta fahimci ko’ina ne, wata ma’aikata ce ta shige da fice a jihar Lagos (immigration office).
Da ta tambayeshi ko’ina zasu je yace “tayi hakuri Dade zai dauka. Suna isa ta hango dade a nesa yana jiransu, sai ya karaso jikin motar tana kokarin fitowa cikin girmamawa don ta gayar dashi, yace ta biyoshi zuwa ciki.
Tare suka shiga ciki yasa aka mata hoto da finger-print. Seun ya dauko su zuwa gida gabadaya. A kan hanya Dade na tambayarta yaya jarrabawar tana gaya masa ita bata da matsala har suka iso gida.
**** **** ****
BAYAN SATI HUDU
MURFIN LITTAFI NA BIYU
“Dade har ka kwanta ne?”
Nenne dake karasowa gabansa ta tambaya, ganin shi a kwance, ido a lumshe kamar baya jin dadi, sai ta zauna gefensa ta dora hannu akan goshinsa, zafi rau.
Dade ya bude ido da suka kada yayi mata murmushi, kafin yace “masassara ke son rufe ni tun dazu” “sannu Dade, to tashi ka sha magani”. Ya yunkura ya mike zaune akan gadon ita kuma jiki na rawa ta doshi (first aid box) dinsu don dauko maganin.
Dattijan biyu na matukar kula da junansu, kullum kamar sabon aure haka suke mu’amalarsu, ta ballo maganin kan hannayenta ta bashi ya kora da ruwa sai ya koma ya sake kishingida. Nenne ta yi amfani da wannan damar ta zauna a jikinshi ta soma magana.
“Dade nace dama gobe ne Aisha zata zana final paper, ina so jibi in maida ita Gombe in Allah ya kaimu”.
A kishingide Dade yake, amma bai san lokacin da ya taso zaune ba, yace “zata je ganin gida ne? Har yaushe aka yi auren Hajiya Sappa? Ko dai Nani Ummana zaku je ganowa?” Girgiza kai Nenne tayi, tace “Dade, in ta tafi ta tafi kenan, Allah ya gani na yi nadamar hada wannan auren, na bata muhimmin lokacina a kansa, don zuwa yanzu na yarda da gaske Abdulrasheed baya bukatar mace a rayuwarsa.
Na yi nadamar rabo yarinya da iyayenta. Da na san in ya ganta bazai karbeta ba da koda wasa ban fara ba”.
“Dama ana nadamar aikata alkhairi ne ga haularka Hajiya Sappa?”
Dade ya tambaya idonsa a kanta. Ba tareda ya jira amsarta ba ya cigaba.
“Kada ki karaya, kada ki sare tun yanzu kada ki maida alkhairinki baya. Wanda zashi sama ya taka tsauni ai yayi kokarin azo a yaba.
You truly made it my dear. Tunda har kin aura masa ya san da zancenta ya kuma ganta ganin idanunsa, ya kuma san tana zamansa. To kin gama naki, ki barni inyi nawa nikuma.
Da wannan Dade ya lallashi Nenne kan kada ta mayar da Aisha gida, ya soma yi mata bayanin abinda ya dade yana shiryawa wanda shima Emir ne ya bashi idea din hakan.
“Yana hutun karshen shekara (Annual Leave) a gidan sa na kasar Argentina currently”.
Mu karasa a littafi na uku.
Tare suke.
Taku har abada SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORIN TAKORITES).
10/04/2024
(MASOYA LITTAFAN TAKORI INA FARIN CIKIN TALLATA MUKU JAKADIYAR KAYAN KAMSHI NA ORIGLAME HAJIYA AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
-Takori Sumayyah Abdulkadir
April, 2024
Downloaded From https://arewanovels.com
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500