gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading MASARAUTAR QAMAR Sirrin Sarauniya Book 2 By Khadija (KMU) Chapter 20 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani murmushi yayi yace my stubborn little maid saboda ai little ce don inda yayi auren wuri rayuwarshi kilan da first born dinshi ta kusa girmanta saboda he s about 40





Khalifha kam tashi yayi tareda nufa dayan dakinshi wato secret room yana shiga ya cire kayanshi ya daura farin towel ya lumshe idonshi Toilet ya shiga sannan ya kunna cold shower ruwan yana shiga kota ina na jikinshi wani irin sanyi ke ratsa shi wanda ya taimaka wurin kwashe duk wata gajiya tashi.







Hurriya kam bacci ta rinkayi mai rai da lafiya don saida tayi baccin sauke gajiya don duk saida gajiyarta ta sauka sannan ta tashi ahankali ta bude idanunta sannan ta kalli dakin Khalifha wanda banda kamshin shi ba abinda dakin yake





Hurriya kamshin Khalifa ne yake dawainiya da duk jikinta don kamar shine a kusa da ita takeji frowning face dinta tayi sannan tace wannan kamshin fa ?ganin batada amsa ne ya sanya ta tashi da niyyar shiga toilet ahankali ta tashi Saida kafarta taji tadan amsa ahankali tace what caused this sai a lokacin ta tuna abinda duk ya faru gabanta ne ya fadi don wani fargaba da tsorone ya cikata don tuna halin da take ciki





Sai a lokacin tagane cewar Khalifha ne tagani ba mafarki tayi ba daman she wondered why would she saw him in her dreams while he s nothing to her cizon lebenta tayi tareda tashi ta shiga ciki toilet din wanka tayi da ruwa masu zafi sosai sannan ta fito daure da bathrobe dinshi cikin sauri take komai Amman komai yana tafiya da natsuwarta bataga ta zama ba yau ya kamata duk wata hanya tabi yanda zata tsere ma wannan bakar masarautar don ga dukka alama sun shirya mata sosai don sam baza su barta ba, don haka gwara taje tayi facing abun kuma tayi fighting dinshi bazata mika kai ba sai tabar masarautar nan safe and sound ahankali ta kalli sama tace In Sha Allah don lokacin da tana a Heral babanta yakan ce insha Allah acikin magana watarana ta tambayeshi ma anar insha Allah aiko yayi mata bayani da kuma nuna mata girman hakan kuma da tabbatar mata cewa indai tace Allah zai mata abinda takeso kalmar ta fado mata a rai tareda fatan Hakan ya tabbata





Kayan khafha ta sanya masu kyau kuma designers ko mai bata shafa ba ta fito ta nufi dakinsu aiko tana zuwa su Bintu suka taso da wasba da sauri ta kauce ma kowa acikinsu don ta tabbatar rungumeta zasuyi nan da nan suka fara tambayar lafiyarta lau ba abinda ya sameta ko ?daga masu kai tayi wasba ce ta share Hawayenta tace don Allah kada ki kara tafiya ki barmu kinji daga mata kai Hurriya kawai tayi Don tunanin da takeyi yanzu yanda zata bar masarautar nan









Sarki Faizan sai kai da komowa yake da jin zancen Khalifha ya dawo hankalin shi kwata kwata ba a Daidai yake ba ga tunanin yarinyar nan da baisanta ba da yabi ya dami kwakwalwar shi abubuwa da yawa duk sun hade mashi ya rasa miye yake mashi dadi







Galadima ne ya shigo jikinshi na wani irin rawa yana bar bar don shi kadai ne ba a tafi dashi ba cikin mutanen dake wurin don kaf harda su jakadiya an tafi dasu gidan yarin Khalifha abinda ya sanya bai tafi dashi ba chief of security saboda alakar dake tsakaninsu da sarki Faizan da kuma Khalifha shi yasa ya kyale shi amman Dukansu suna prison



Sarki Faizan yana ganin shi yasan cewar ba alkhairi bane tattare dashi don yadda ya shigo a kidime aiko hakan ta faru bakaken labarai ne ya fada mashi guda biyu daya na dawowar Khalifha da kuma yanda ya sanya aka tafi da dogarai da security s din shiru sarkin yayi don ya rasa abinda Zai fada kafin ya dawo daga tunanin ya kara daga mashi hankali da sakon boka don yace duk yanda za ayi su nemo yarinyar nan ciki kwanakin nan idan ba haka ba akwai matsala





Shiru yayi don ya kasa tunani sarKi Faizan don yasan bai isa acigaba da nemanta ba Khalifha na cikin masarautar nan



Galadima ne yace Allah ya taimake ka ga wata yar shawara tawa mu gwada mugani ko zatayi daga mashi kai sarKi Faizan yayi wani irin murmushi yayi sannan yace mai zai hana kawai Khalifha yayi aure kamar yanda ta rinka faruwa dashi da



Shiru sarKi Faizan yayi sannan yace Aa kasan duk wadda ya aura ranar take cewa saidai ya saketa Amman bazatayi auren ba ka canza wata shawara







Galadima shiru yayi yace wannan ita kadai ce shawarar idan akayi auren da an fara shagali hankali mutane yadan dauke sai mu cigaba da dubata ana shagali ana dubawa.







Sarki Faizan duk yanda yaki yadda saida Galadima ya rinka insisting har dai yace akai ma Khalifha takarda da sauri Galadima ya daga kai ya fita akayi rubutu ya kawo ma sarki yayi stamp yakai part din Khalifha









Khalifha yana zaune a falo kafa daya kan daya yana amfani da iPad dake hannunshi don duka hankalin shi nakan iPad din saida akayi ma chief of security iso sannan ya shigo hade da sallama





Galadima sallama ya karayi mashi Khalifha ba tareda ya dago ko bare ya kalleshi ba ya amsa sallamar shi bayan sun gama gaisawa wanda Khalifha cike da tsantsar mulki yake maganar don har lokacin bai kalli inda Galadima yake ba





Galadima cikin yar kyarma don duk yanda kake kazo wurin sai kaji dar don powerful aura dinshi duk ta cika wurin , fara karanta takardar da sarki ya sanya akawo mashi yayi inda yake cewa gobe akwai daurin auren Khalifha da za ayi bayan azahar kuma mata hudu zai aura





Khalifha bai ko kalleshi ba ya tashi yabar parlon don ba abinda ya dameshi idan an tashi adaura mashi mata dari ya san cewar a ranar kowacce acikinsu zata nemi sakinta zasu gudu baisan miye ake turo mashi ba Amman koma miye bai damu ba sune suke auren kuma sune suke raba auren





Galadima kam ya shaka lokaci kawai yake jira zai bama kowa mamaki acikinsu daga sarki Faizan din har Khalifha duk zasu dawo atafi hannunshi lokaci kawai yake jira.









Koda dare yayi inna hanne tazo taga Hurriya ba karamin dadi taji ba ganin ba abinda ya faru da ita don ta saki jikinta Sosai tunda gashi tana kallonsu Bintu sunata cin abinci kowa yayi shiru baya yin magana inna hanne murmushi tayi don tasan aikin Hurriya ne zama tayi itama bayan sun gama cin abinci suka taba yar hira sannan tayi masu Bankwana ta tafi ta kwanta







Saida ta tabbatar Bintu ta tafi ita kuma wasba tayi bacci sannan ta tashi ahankali ahankali ta fita don ganin ko akwai inda zata iya samu ta gudu





Cikin sanda takeyin komai har tazo taron wasu yan iskan dogarai suna zaune suna shaye shaye aiko suna ganinta suka taso kowa acikinsu a buge yake yana cewa ina aka samu wannan kyakkawar yarinyr





Hurriya kallonsu tayi don kyankyamin su Dukansu takeyi wani acikin su ne ya kawo hannu zai taba mata gashi ne aiko yaji an rike hannunshi Hurriya kallon wanda ya rike mashi hannu tayi shiru tayi tareda zuba mashi idanunta masu kyau wanda ke kara jefashi cikin kaunarta da sauri ya janye idanunshi daga nata sannan ya kalli dogarawan yace ku wuce ku bama mutane wuri,da sauri Dukansu suka bace a wurin



Kumurci kasa kallonta yayi ita kuma kallonshi kawai takeyi





Cikin natsuwa yace mata kinason fita ne Hurriya saida ta dauki lokaci as always sannan ta daga mashi kai murmushi yayi ganin ji da kanta har yanzu yana nan ba wanda ashe ya ladabtar da ita.







Kallonta yayi sannan yace muje na taimaka maki Hurriya daga mashi kai tayi sannan suka fara tafiya duk inda suka gifto da anyi mashi magana sai yaje wurin ma aikatan ya basu wani Abu sai su wuce saida suka zo Daidai bakin wani gate din da zai iya fiddasu palace din tace na manta wayata





Kumurci kallonta yayi da mamaki ganin tana Neman komawa bayan duk wahalar da suka sha ahankali yace mata kiyi hakuri da wayar mana.Girgiza mashi kai kawai tayi sannan ta juya ta koma saida tayi tafiya mai nisan gaske ta fara hango dakunansu ga dare





Kunnenta akwai ji don tana tafiya daga nesa taji ana waya ana cewa dole mu nemo yarinyar nan gobe ko a ina ta makale cikin masarautar nan don boka yace duk wanda ya sameta zaiyi sarauta ko dai na aureta kona kasance da ita



Ai saboda auren Khalifha da za ayi ba zai zargi kowa ba ko yayi tunanin Akwai Abu ke faruwa a masarautar don haka ba wata matsalar da za a samu

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: Masarautar Qamar



61





Bintu shiru tayi tana kallom yanayin Hurriya Mai tsoratawar don idanunta sunyi sanyi kamar banata ba kodai batada lafiya ne shine abinda Bintu take fada aranta cikin kulawa tace sannu Hurriya naga kamar bakida lafiya ne shiru Hurriya tayi mata ta tashi ta fita Bintu murmushi tayi saboda hakan ba bakon abu bane a wurin Hurriya wasba ma shiru tayi don sai taji wani iri da taga Hurriya cikin wani yanayi Dukansu zama sukayi sukayi shiru suna kallon juna







Hurriya kam inda take wanki da can taje ta zauna tana wasa da icce tana kallon nature a masarautar masu sanya mutane nishadi ahankali ahankali ta saki ranta she believe that they will never get what they want from her after all ita fa jikar Hamood ce





Rashin mutumci kawai su Galadima sukeyi don da manya manya Guards wadanda suka kasance abun shakka ko wanne da bindigu acikinsu sai dogarawa wanda hannun su ke rike da zabgegiyar dorina fuskarsu babu wani annuri bare alamar sauki





Sai manya mata wadanda suka kasance suke yawo tare dasu wanda suma dai babu sauki a tattare dasu koda ga kallonsu , su jakadiyya sune ke wani irin bincike mata tareda wulakanci da rashin sanin darajar yan mata don sai mutum ya cire kayanshi dagashi sai zani sannan a duba bayanshi agaban mazan daman bayan kawai ake dubawa don boka ya fadi inda za a samu zanen ajikinta saidai ya kasa ganin fuskarta don wani irin bishi bishi takeyi mashi ta yadda koda shine bokan da yafi kowa iya tsafi bazai ganeta ta haka ba.







Galadima wanda sun gama da dakin bayi ne don haka Hurriya ce ta fado mashi arai wata dariyar mugunta yayi don yasan yanzu ne zai iya zuwa ya dauki fansanr abinda tayi mashi,





Har sun kama hanyar wani daki yace masu bana nan zasuje ba yace ga inda zasuje.ba wanda ya musa mashi haka suka jero kowa idan ka kalla acikinsu sai yan hanjin cikin mutum ya kusa kadawa





Basu wani sha tafiya ba Sosai saiga su adakin su Hurriya wanda yake sosai da mutane aciki saidai tun kafi a ida yi masu iso kowa acikinsu ya natsu ya shiga taitayinshi





Dakin shiru yayui don kamar babu numfashin biladama aciki





Kallon matan yayi yace ku fara aikinku da kakkausar murya .Daya daga cikin dogarawan yace suyi layi ba musu suka jera layi





Cikin sauri aka rinka zuge rigar uniform dinsu ta baya ana dubawa don da an duba naki sai ki koma gefe haka aka rinkayi hadasu bintu da wasba akan layin ba wani bata lokaci suke komai wasu kam hada mari matan ke kai masu







Galadima shiru yayi tareda mamakin rashin ganin Hurriya a wurin don ga dukkan alama gashi har an kusa gama searching bata nan saidai tun kafin yagama tunanin da yake yaji wata acikin matan da yazo dasu ta bude Baki tana kallon kofa tace wacece wannan aiko kamar hadin Baki suka juya suna kallon yadda take tafiya in all her mighty





She looks fierce and confident don wani jeans ne jikinta shima crazy wandon duk ya fashe saidai shi ba kamar wanda ta sanya rannan bane don wannan gwiwar ne yafi fashewa gashin kanta kitso ne guda hudu gashin ta nanadeshi ba karamin kyau kitson ya karayi mata ba don ya sanya ta kara looking very unique and classy yanda take tafiya kanshi abun kallo ne with so much mighty don kamar tana da sarautar rabin duniyar haka take takawa she s beautiful tana da asalin kyau wanda idan akace ta zana kanta iya abinda zata iya yi ma kanta kenan inda ace zata fito gasa kyau toh tabbas Akwai 100% possibilities din dazata iya ci Because her beauty is beyond perfection







Kamar an dauke wuta an kawo haka ta haska wurin kallonta kawai sukeyi they were all in awe don cikin mazan harda matan suma sun kasa janye idonsu daga gareta .







Cikin wani irin confidence ta iso wurin saidai idan zaka bude zuciyarta fargaba ne fal da tsoron makomarta saidai tasan ta riga tazo bazata iya juyawa ba saboda sunanta Hurriya Faisait Hamood ba abinda ke firgita ta bare ya tsorotata jikar sarki Hamood ce fa.





She knew that she would never allowed anyone of them to touch her with their dirty fifthy hands saidai batasan mi zatayi ba.







Jakadiya kallon tafiyarta da izzarta tagama how could they not see that tuntuni ai basai an fada masu ba wannan Hurriya itace yarinyar da ake magana daga Heral palace why are they so blind that they couldn t see that since, tafiyarta cin abincinta miskilancita rainin wayonta yayi solving equation din it s not a coincident she must be the girl they ve been searching for







Galadima gabanshi banda faduwa ba abinda yake yi irin tunanin jakadiya ne shima ya darsu a zuciyar shi sadai dayar zuciyar shi tafi rinjaya da haba ba ita bace bazata taba zama jikar sarki hamood ba duk da alamamomin a bayyane suke Zata iya zama jikar tashi.





Da sauri manya manya matan sukazo zasu taba Hurriya kallonsu Hurriya tayi tareda dage gira babu alamun tsoro bare kuma fargaba kallon su tayi ahankali sannan tace cikin muryarta mai dadi tace mi kukeso wani acikin dogarin yayi karaf ya amshe tareda cewa ubanki mukeso shegiya yar matsiyata,Hurriya ahankali ta dan ciji bakinta sannan tace ubana kakeso kallonshi tayi cikin idonshi idanunta cike da rashin tsoro da kwarjin tace ubana yafi karfin kaskantaccen mutum irinka sakarai wawa irinka har ka gama rayuwarka baka isa ka taka inda mahaifina yake ba sannan tace ko karen mahaifina baka isa ka bashi ruwaba bare kuma gugar takalmi har ka kai inda zaka ganshi kace shi kakeso raising brows dinta Tayi in a mocking way tace bawa kamar ka bai isa ba ta ida maganar cikin mulki gadara da jan aji





Wurin kamar ita ake jira ta fara magana don har wani extraordinary shiru ya kara dauka wurin sosai har takai aya muryata kawai take fita cikin sautin amo mai dadi da kuma iya shirya kalamai



Cikin zafin bakin ciki da kufula dogarin yace ni kike gayawa wannan maganar yau zaki gane waye matsiyaci tsakani na dake ,kallon matan da suke duba bayan yan matan yayi yace kuyi maza ku cire mata rigar ya matso saitin su hannunshi rike da bulala abinda ya Sani yau mai rabashi da Hurriya yau sai Allah don sai ya wulakanta ta ya kaskanta mai muni cikin bainar jama a don yanda tayi mashi maganar banza sai ya huce akan jiknta don yanzu ya daukar ma kanshi alkawarin bazai iya Bacci ba idan baiga bulalarshi akan jikinta ba.





Galadima yasan mi dogarin yake shirin yi amman bazai hanashi ba saboda shima cike yake fam da yarinyar she always gets on his nerves don shi baiki ta wulakanta ba wulakanci mafi muni







Dogarin ya kallesu yace wai mi kuke jira tsoronta kukeyi manya matan masu duba bayan yan matan suka kalli guards da sauran dogarawan daga masu kai head of security din yayi alamar kuyi aikin ku kada ku fasa shima haka galadima ya nuna saidai kallo daya zakayi ma Hurriya kasan cewar batayi na am da wani ya taba mata jikinta ba don wani irin kallo take watsa masu in a warning way wanda kallon cike yake da gargadi da kashedi









Galadima kallonsu yayi yace mi kuke jira dallah ku dubata muyi mu tafi akwai sauran inda zamuje aiko yana gama maganar sukazo zasu taba Hurriya da zafin nama ta ture daya daga cikinsu da tayi sa ar sanya hannunta saman wuyanta wani irin fury bacin rai kawai ke fita daga fuskar Hurriya



Basu daddara ba mutum biyu suka karu suka cike hudu sukazo suna kiciniyar cire mata riga jakadiya acikinsu Hurriya wani irin murda takai ma hannun jakadiya da sauri ta saketa how dared you touch me with your stinky hands inji Hurriya ta fada tareda turesu wanda cikin muryarta zaka iya jin zallar bacin rai da kuma bakin cikin hakan da akayi mata



Tunda tabar Heral palace bata taba samun ranar bakin ciki irin ta yau ba wasu matsiyata kazamai suke kokarin su tabata not just to touch her ma they re trying to undress her this is unforgiving itace Hurriya Faisait Hamood nobody dared to touch her even in their palace except for 3people that was her father,her mother and her grandfather except them,nobody would tried that because they knew the outcome don bata da sauki don a Heral palace ace mistakenly cousin dinta ya matso kusa da ita da niyyar ko kai hannu kan yatsanta don ta daukeshi da mari sannan akawo mata ruwa agabanshi ta wanke hannunta ba komai bane,





Sai a masarautar Qamar wanda basu kai ta hada hanya dasu ba ma wadanda ba blood relatives dinta ba sune suke tabata da kazamin hannunsu if her grandfather is were to hear this tasan da kilan yau masarautar Qamar tazama labari don kilan sai ya sanya an rusheta







Cikin kulewa Galadima kuma ba tareda tunanin abinda zaije ya dawo ba yace ma Guard din su cire ma Hurriya riga now ya buga masu tsawa,



Hurriya kam ba karamin gajiya tayi ba don sarkin yawa yafi sarkin karfi sosai don bataci abinci ba duk yau ga abinda ya faru itakam batada karfi don karfin daya rage mata kadan ne







Fargaba ne da tsoro fal acikin ranta saidai bazaka iya ganewa ba saboda bacin rai daya rufe mata fuskarta,Dogarin da ta gama gaya ma magani shine ya kutso kai tareda jan rigarta Hurriya kam ta riga ta hakura tayi nata fadan yanzu saidai ta zuba ma sarautar Allah ido saboda karfin daya rage mata kadan ne da wani irin zafin nama da bakar keta yaja rigar saidai ji kake tass tass





Sakin baki kowa yayi tareda kallon saitin Khalifha sanye yake cikin wasu hadaddun suits na Hermes wanda suka amshe shi tareda fito mashi da haiba da kwarjini he looks so dangerous and scary don aura dinshi da ta cika wurin mutum bai isa yagane yanayin fuskar shi ba,







Hurriya wadda take neman faduwa idonta har rufewa sukeyi da sauri ya tallabota ta fada jikinshi yana mai riketa gam



Kowa kallon shi yake da mamaki yanda akayi ya iya ganeta yana makaho da yawa a wurin suna cikin fargaba da tashin hankali saboda basu san Khalifha ba sai dai suna jin labarin shi don duk wanda ya kwana ya tashi masarautar yasan labarin shi wanda ako dayaushe cewa ake baida dadi sam.



Rungume yake da Hurriya sannan ya juya ya kalli cheif of security yace mashi take care of them



Wurin ba wanda baiji hantar cikin su ta kada ba don ba kowa ke son shiga harkar shi ba.













********************** + **************************

********** Ai Hausa Novels ****************

*************************+ **********************



DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.



Visit > https://www.aihausanovels.com.ng



Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.



Email > aihausabooks@gmail.com



******* FOLLOW US ******



Facebook: Ai Hausa Novels



Twitter: Ai Hausa Novels



Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



WhatsApp Number: 08138873799





Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.



********************** + **************************

*************** Ai Hausa Novels ****************

********************** + **************************



MASARAUTAR QAMAR NA KUDI NE CIGABANSA



Naira dari uku kacal300



3139107983

Khadija Mustapha first bank



Ko kuma katin mtn ta wannan number 08029520062



Ku tura screenshot ta a wannan number 08029520062



Saimun hade a paid group kasaitattun Mata masu ci da guminsu



>7<
@&=E<
@&


Downloaded From https://arewanovels.com


Please Login or Register in order to submit comment