gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading MASARAUTAR QAMAR Sirrin Sarauniya Book 2 By Khadija (KMU) Chapter 2 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idonka tayi maka daidai abinda kayi mata Amman dai ba ruwan ta da kowa kawai miskila ce ta karshe and don t talk behind her back saboda Allah ya bata wani irin ji sosai kilan shine baiwarta Don tana iyajin magana daga nesa Sosai wadda nisanta ya wuce tunani Amman cikin ikon Allah zataji lokacin da bata ma iya hausar ba Sosai don ko magana taso ta fada ma mutum marar dadi to ba lallai yaji mi take cewa ba saboda she s using British and Amacharic Amman yanzu idan ta yanko maka magana kamar daman asalin yaren hausan takeji don duk kalmomi mararsa dadi ta iya amfani dasu.



Bintu kam har ta jika masu garin tanata jiran Hurriya din tazo domin susha suyi sallah su kwanta Bintu ta kalli Hurriya tace ina kika tsaya ahankali tace waje tasan bata cika san magana ba don ta tsani unnecessary zance don haka Bintu taja Bakinta tayi shiru



Tare suka sha garin don ita Hurriya a hankali take sha don har tagama shanye nata Hurriya bata shanye ba tanajin waka tana kada kanta Bintu murmushi tayi sannan ta fita ta wanke kofin tayo alwala sannan ta kabbara isha i tana gama sallah tana lazimi saiga sallama

Hurriya idonta lumshe Amman duk abinda Bintu suke cewa tanajin su Bintu ta kalli Hurriya tace Hurriya na tafi baba ya dawo yace a kirani tana goge dan hawayen da ya zubo mata Hurriya tayi shiru kamar bataji mai Bintu take cewa ba sannan Bintu ta fita tana dan gyara ma Hurriya labule.



Bintu na isowa kofar gida gabanta ya fadi don batasan mi zata tarar ba a gidan a hankali tasa kanta a soron Gidan tana tafiya kamar munafuka lalu da suka shirya abunsu da larai daman yasan dole zata dawo gida shiyasa ya tsaya zaure ya tarbeta saboda ya lalubi rabonshi



Daidai inda take yazo yana wani munafukin dariya yace wa naka ma matsowa ya farayi tana matsawa baya yana Dariyar har saida ya kawota karshen bango riketa yayi gam yana dariya yellowing hakoranshi suna bayyana kugunta yarike yana kokarin sanya mata hannu cikin riga tureshi tayi yayi baya ya kalleta sannan yace ni zaki ture to yau Mai rabani dake sai Allah kugunta ya rike aiko suka fara kokowa karfinta ne ya fara karewa sosai



Hurriya da take kallon ikon Allah zuwa tayi daidai inda yake ta dauke lalu da mari a harzuqe ya dago da niyyar sauke ma kowaye ya mareshi ruwan tijara saidai da kyar ya iya hadiya maganar shi da kuma yawun dake bakinshi kallonta yakeyi da yar crop top din da ko cibi bata rufe mata ba sai bakin wandon dake jikinta gashin kanta kam ba a daure ba tunda lalu yake bai taba ganin halitta mai kyan mahnoor ba saidai kyawawan idanunta da Allah ya basu matukar kwarjini Hurriya ta janye bintu daga wurin lalu tana mashi wani irin banza kallo da kyawawan idanunta cikin muryarta mai dadi da tace duk randa na karajin wani Abu makamancin haka ya faru sai kaji a jikin ka sakarai mai karamar kwakwalwa



Bintu kallon Hurriya tayi sannan tace nagode Hurriya kam baka iya karantar yanayinta don ta kwarai wurin shutting emotions dinta



Tare suka shiga inda suka tarar abbanta na kwasar tuwo larai na kusa dashi Larai na lura da shigowar su ta saki wani munafukin murmushi Abbanta da ya kula dasu aiko zumbur ya taso da hannunshi duk miya zai mari Hurriya cikin sauri ta rike hannunshi tana rikewa ta saki don kamar ta rike kashi tana kallonshi Abba da ya harzuka yace daman kina wurin wannan shedaniyar marar tarbiya marar addini.



Hurriya a kalleshi sannan tace babban shedani ya wuce bayanka wanda har zai tsallake kafa ya tafi gantali ba tare da tunanin halin da diyarshi zata fada ba a hannun kishiyar uwa bakasan mi taci ba bakasan mi tasha ba baka san wazai lalat maka diya ba kallon Larai da tabata fuska tana kallonta tayi sannan tace koda yake ba abin mamaki bane tunda duka jikin ka daure yake da asiri.



Rashin addinina da Rashin tarbiyata duka dauka nayi a wurin wanda baisan hakkin diyarshi ba ido cikin ido tace sakarai wawa mijin tace Bintu da take kallon komai tasan a haka Hurriya na ganin mutuncinta tasan idan tayi wani abun ba zataji dadi ba.



Hurriya ta kalli Bintu sannan tace ai baki jin yunwa ko Bintu ta daga mata kai tace muje dakinki Hurriya na gaba Bintu na baya har suka zo dakin kallonta tayi mata da ido ta shiga kuka take shirin yi Hurriya ta nuna mata alama da tai shiru.



Abba da Larai kam sunsan halin shegiyar Hurriya ldinan da ta zame masu karfen kafa a cikin garin nan don bata da mutunci



Hurriya tazo ta kallesu sannan tace idan har naji ko harar Bintu kunyi to zan kira maku hukuma ta kada kai ta bar gidan lalu da yake boye yana kallon su duka ya fito yana kallon Larai yace wacece wannan Larai ta kalleshi tace fitacciyar marar kunya kenan don haka duk abinda tace to ba mamaki zata iya aikata shi.

[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: <Masarautar Qamar



By Khadija (KMU)



Page 7&8



Gida Hurriya ta koma tana shiga ta kwanta a katifar tana tunani bata gama tunanin ba bacci ya dauketa sai karfe bakwai ta tashi ruwa ta dan kashe sannan ta juyeshi cikin bucket tayi wanka kanta ta fara wankewa sannan wanka tayi alwala saida ta sanya gashin kanta saitin fan ya bushe tukunna scissors ta duba inda take ajewa bata gani ba dubawa tayi sosai bata gani ba tsoki tayi ta gyara gashinta ta daureshi kawai don taso ta yankeshi saboda gashin ya fara yi mata yawa wani dan karamin box ta fiddo can cikin kayanta ahankali ta bude tana kallon sarkoki guda biyu masu masifar kyau Rufe box din tayi ta maida sannan ta fiddo wani jeans blue ne sosai Amman yanada dan fadi kasan shi sai tsagar dake a cinyoyin wandon da gwiwar wandon shiryawa tayi cikin wando ta sanya bakar riga yau kawai taji tanason ta sanya dan kwali don haka ta zaro wani blue and black vintage scarf ta daura ma kanta saida tagama shiryawa tsaff sannan ta dan murza dan oil turaren ta mai saukin kudi

Saida tagama komai sannan ta kabbara sallahr asuba don har takwas da mintuna tayi da sauri tagama komai ta nufi gidan mai anguwa .



Tadan makara yau wurin aiki tana shiga laminde tace kina raina Hurriya yanzu nike da niyyar daman In sanya a Duba ki ko lafiya Hurriya ta share tambayar da tayi mata tace ina kayan murmushi laminde tayi ta fiddo mata kayan yau cikin sauri take komai saboda yau zata kwashi adashenta kuma tanaso ta siye kaya saida ta tabbatar tagama komai don ko laminde ko Bankwana batayi ma laminde ba ta fito



Hurriya kam saida taje gida ta fiddo asusunta har ta maida wurin maida asusun ne wani dan box = ya fado a hankali ta bude tana kallon sarkoki guda biyu da banda kyalkyali ba abinda sukeyi maidawa take kokarinyi kawai sai a ranta tace bari ta sanya it s been a long time a hankali ta warware sarka guda daya wadda plain ce kawai Amman gold ne a sarkar ta sanya Kallon dayar sarkar take wadda kamar diamond ce Amman stone din anyi mashi carve da H Maidawa tayi a box din sannan ta sanya shi a aljihun wandonta Emotions din da taji ya fara taso mata ne ya sanya kawai ta cire kudin asusun wanda suka kama dubu takwas ta tafi gidan Asabe wadda ta kasance uwar zubin adashen Hurriya ba sallama ta shiga gidan a tsakar gida ta iske asabe tana shan rake

Asabe saidai ganin mutum tayi a kanta don ta tsoro ta matuka Hurriya ta kalla daga sama har kasa tace Nagode ma Allah kece cikin gidanan namu da ace bake bace da sai anjimu dake yau Hurriya kallon Asabe tayi fuskar ta babu alamun murmushi ko daya tace nazo kwashe kudina

Dariya Asabe tayi sannan tace oh kece fa kwasar karshe kusan kowa yasan halinki shiyasa duk angama maki zubin adashen ki tun kafin ma kizo ta ida maganar da dariya hurriya batace mata kala ba saidai ta jawo kujerar dake kusa da Asabe ta zauna



Asabe tace kinga bari na dauko maki kudin ki labule asabe ta daga ta shiga daki sai gata tafito da yar lalitar tsaff ta kirga ma Hurriya dubu sha biyar da dari takwas tace ga kudin ki kece daman zaki ida zubin yau shine zai kama dubu sha shida kenan Hurriya amsar kudinta tayi daman hannu biyu tayi zubin na wata biyu kenan kuma itace kwasar karshe ta hada da dubu takwas din da ta fiddo daga asusun ta wanda suka kama dubu ashirin da uku



Amsar abunta tayi ba tare da tace ta gode ba asabe har zata wuce asabe tace yawwa Hurriya ga fa irin kayan da kike sawa gwanjo ki duba Hurriya alama tayi mata da ta miko cike da murna asabe ta shiga daki don tasan indai Hurriya ce sai ta siye kayan kusan dubu biyar indai tanason Abu zata siya gashi ita bata taya kaya duk yanda aka batasu saye takeyi



Kulli guda asabe ta fitoda kayan tana nuna ma Hurriya murmushi tayi tare da bude kayan tace kalla Hurriya kallon da Hurriya take ma kayan kawai zai tabbatar maka da cewar sun burgeta a hankali ta fara zabar kayan masu kyau har kusan kala goma sai hula kala uku Asabe ce ta kalleta sannan tace Hurriya gafa wata jalabiya zatayi maki kyau ki hada da ita Hurriya kallon jalabiyar tayi sannan tace ta sanya mata da murmushi asabe ta sanya hada wani dan kwali Mai silbi sai hijab Mahnoor kallonta tayi sannan tace nawa ne duka kudin kayan Asabe ta gyara tsayuwa sannan tace dubu shida Hurriya ba tare da bata lokaci ba ta kirgo dubu shida ta bama asabe

Asabe kam dadi kamar ya kasheta daman tasan Hurriya bata da bakin ciki indai tanason Abu zata siya yadda ka batashi leda ta dauko ta kwashe ma Hurriya kayan sai zuba kam godiya take da addu a Hurriya bata bi takanta ba ta fito daga gidan ta nufi gidan mai unguwa cikin aljihun wandonta ta sanya kudin tabo aljihun tayi kawai sai taji dan karamin box dinta tsoki tayi ta maida kudin a dayan aljihunta



Da isowar ta kofar gidan mai unguwa taga kofar gidan cike da motoci fararen bus ne na hias masu kyau ga yara da iyayen yara shake a wurin

A hankali Hurriya ta kutsa kai gidan mai anguwa samudawan dogarai ta gani sai mazurai suke da idanu frowning face dinta tayi ganin su da wasu uniform ga kuma rawani daure a kansu hango laminde da Hurriya tayi ne ya sanyata kutsa kai har inda take ganin ta , Duka wurin kallonta suke ba tare da ko kyaftawa laminde kam kallonta take tana mata alama da ta fita Amman Hurriya ba tare da ta kula kallon da ake mata ba ta iso har inda take fuskar ta sai fidda wani irin kyau take Amman kwata kwata babu murmushi ko sauki a fuskar ta laminde ta kalla sannan tace namanta ban amshi kudin aikina ba laminde tace oh oh bari na dauko maki



Mai unguwa kallon Hurriya yayi cike da tausayinta saboda ya tabbata baza ta koma gida ba yau don kallon da dogarawan kadai ke mata ya isa ya baka amsa laminde ta fito da Dari biyu ta bata tana kallon ledar hannunta da kuma wuyanta gaban laminde ne ya fadi ganin sarkar gold din da ta fito baro baro a wuyanta tasan zalincin dake masarautar Qamar don haka a hankali tazo saitin Hurriya gabanta na faduwa saboda kada wani ya lura da abinda zatayi itadai Allah ya Sani tana kaunar Hurriya har cikin ranta duk da ita bata nuna wata alamar girmamawa amman a haka take kaunarta a hankali tazo ta gyara mata wuyan riga tare da zurma sarkar cikin riga Hurriya kam wani irin kallo take mata murmushi laminde tayi sannan tace kada ki yadda wadanan dogarawan suga sarkar dake awuyan ki a hankali tayi mata magana yadda ko mai unguwa da yake nesa dasu bazai iya ji ba ki kula da kanki

Hurriya .



Hurriya a daga kai tayi tana rike da ledar kayan ta ta doshi hanyar fita wata tsawa aka daka mata Daidai ta kai kofar akace ke yar matsiyaciya ina zaki

Hurriya cigaba tayi da tafiyar ta wata tsawa ce aka kara daka mata ke kaskantarciyar karuwa ina zaki Hurriya bata taka ba kuma bata juya ba tsaye tayi tana jiran isowar ko waye da yake mata tsawa har haka don tun lokacin da ya fara tasan da ita yake



Salati laminde takeyi ta kalli mai unguwa dake gefe sannan tace ka taimakeni ka rufama yarinya asiri kasan halin Hurriya Daidai take da duk wanda ya kwana ya tashi kasan masarautar Qamar basu da imani mai unguwa shiru yayi



Kowa ma shiru yayi yana kallon ikon Allah Hurriya da take tsaye fuskar ta blank baka iya cewa ga yanayin ta Kumurci yazo saitin ta sannan ya daka mata tsawa wadda saida ta girgiza kusan kowa a wurin Amman Hurriya ko gezau duk da saida yan hanjin cikinta saida suka kada Amman tayi kokarin gyara tsayuwarta tana frowning fuskar ta Mai fidda zallan kyau tana kallon cikin idanun kumurci



Kumurci kallonta yake da mamaki sannan cikin daga murya yace kaskantaciya yar gidan matsiyata wadda tarbiya gabaki daya bata wadata iyayenki ba har suka baki ba yana magana cikin hargagi da wulakanci yana kallon ko ina na jikinta



Hurriya tace Are you mad kana hauka ne cikin zazzakar muryata mai dadi da dadin sauraro saboda yanayin maganarta hankalin kowa ya dauku ya dawo kanta tarbiya bata wadata iyayena ba kai kuma jahilci ya wadata naka iyayen tunda gashi kana juya abinda suka koya maka cikin doddar kwakwar ka Animal Asshole

Kumurci banda radadi ba abinda zuciyar shi takeyi don ba a taba maida mashi martani irin yau ba kuma cinkin mutane daga hannunshi yayi zuciyar shi banda tafarfasa ba abinda takeyi zai sauke a fuskar shi Hurriya ganin marinta zaiyi da sauri ta cire dankwalin da tadaura yau cikin sa a ta sanya dankwalin ta rike hannunshi tana rikewa tayi sauri ta saki kamar ta kama kashi kowa kallonsu yake itama tana kallon cikin idonshi tace Kana hauka ne ?sai tadan tsotsi bakinta kadan



Kumurci kam kallonta yake har baya kyaftawa tunda yake baitaba ganin mace mai kyaun ta ba don lokacin da take mashi magana ya kura mata ido har gold din dake ratsin hakoranta biyu saida ya gani saboda irin kallon da yake mata Hurriya kam lura da hakan yasa tayi shiru tana kallon tsakiyar idanun shi Kumurci kallon dogon sumar gashinta yake don baitaba ganin wani da irin gashinta ba ko subira da take take takama da kyau da gashi Hurriya ta fito don nata cike yake ga tsawo ga yawa wannan yarinyar dole ya tafi da ita masarautar Qamar Hurriya daukar ledarta tayi tace wawa dan akuya sannan ta kama hanyar kofa



Kumurci kam daya saki baki yana kallon ta Sauran dogarawan kam kallom Kumurci sukeyi don ya kasance Azzalumi kuma marar Imani Amman yau wata yar matsiyaciya yar talaka kuma karawu zata zauna ta Gaya mashi magana



Laminde kam tsoro da fargaba ya cika mata ido tanason Hurriya bata kaunar wani abu ya sami yarinyar dama bata zo ba saboda ta sani sarai bazasu barta lafiya ba.



Kattin dogarawan dake tsaye gefenta ne suka tare mata hanya a hankali ta dan ja baya jin saukar wata azababbar dorina ya sanya ta juyowa wasu ta gani guda biyu dukan ta suka farayi ba ji ba gani da wani irin rashin imani suke dukan ta laminde kam kuka take don duk bulala daya idan akayi mata sai ji takeyi kamar ita ake duka mai unguwa saidai dauke kai yayi

Hurriya kam tana durkushe don tun bulala daya da sukayi mata ta durkusa ta dukar da kanta ta hade kafafunta da gwiwowinta dukanta suke ba ji ba gani duk wanda yaga Hurriya sai ya tausaya mata don idonta sun kada sunyi jawur kukan zuci take wanda yafi ko wani kuka zafi da radadi fargaba da tsoro duk ya cikata laminde matar Mai unguwa kuka takeyi kamar ita ake bugu kasa jurewa tayi ta rugo ta wurin saitin masu bugun ta dan ture Hurriya aka zabga mata bulalar Ai laminde fitsari ne kawai bata saki ba saboda azaba Hurriya dago jajayen idanunta tayi ta saukesu akan laminde kukan da Hurriya zata iya cewa rabon da tayi shi har ta manta ne yazo mata laminde kallonta tayi ta girgiza mata kai ta daina kuka



Bulalar suka kara zuba ma laminde Hurriya zuwa tayi ta ture ta tana masu wani kallo Mai unguwa ne ya kalli dogarawan sannan idonshi na taruwa da kwalla yace don Allah kuyi hakuri ku taimaka kuyi hakuri ta gane kuskurenta yanzu Saminu ya kalli Kumurci wanda yake kallonsu yana kallon Hurriya wadda tayi ligis Kumurci yace sharadi dayane zamu baku Mai unguwa yace ka fadi koma wani irin sharadi ne zamu cikashi In Sha Allah murmushi yayi sannan yace ko matarka ta bimu masarautar Qamar ko kuma wannan matsiyaciyar ya nuna Hurriya shiru Mai unguwa yayi Hurriya da idonta sukayi jajir ta dago tana kallonshi wani murmushin mugunta yayi mata laminde tayi sauri tace ni zanje wallahi ku kyale yar marainiyar yar nan ku taimaka don Allah Hurriya kallon laminde take wadda banda kuka ba abinda take matar ta sota duk da hali na kin kulawa da take bata Amman bata taba gajiyawa da ita ba laminde ta kalli maiunguwa da idon shi sukai ja tace ga Hurriya nan don Allah ka kula da ita Maiunguwa cewa yayi laminde tare zamu tafi mubar Hurriya a garin nan ni zan biki murmushi tayi tace idan mun tafi kuma mubar ma wa ita? Hurriya da zuciyarta tagama karewa ta bude baki kamar tana tsoron magana tace I will go with them cewa tayi banji Mai kikace ba Hurriya tace zan bisu Kumurci wani murmushi ya saki yace da kin taimaki tsohuwar da take tsugune tana rokona Don wannan matar idan har ta bimu sai na sanya ta Zama baiwa mafi kaskanci a masarautar Qamar kuma sai na tabbatar da ko wani kaskantar bawa ya kusanceta yayi dariya Hurriya kam idonta kadai inda ka kalla zakasan tana cikin zallar bacin rai ga galabaitar da duk tayi laminde girgiza kai kawai take tace ba inda zaki ni zan tafi tana kuka tana girgiza kai Hurriya kam abinda bata tabayi ba shi tayi lallashi don bata iya ba ma kwata kwata Amman daga jin yanayin muryarta zakasan kokari ne take tana magana zan dawo zan kira shine abinda tace Kumurci kam kokarin turata ya farayi juyawa tayi ta kalleshi tace kada ka sake ka taba ni da kazamin hannunka a irin yanayin da tayi maganar zaka san ba abinda bazata iya ba idan har ya kara Kumurci kallonta yayi yaga yadda idonta ba wani abu wai shi tsoro shiru yayi sannan yace yarinya zaki gane kurenki a masarautar Qamar don karnukan suna da yawa ya fada a zuciyar shi.



Hurriya jikinta duk ya mutu saboda dukan da akayi mata laminde kuka kawai takeyi don abun yafi karfin ta Jikinta sai kyarma yake ledar dake yashe ta kayanta ta dauka



Kumurci ya kalli mutanen da dogarawan yace su fito su tafi kamarshi ake jira aka tasa kyayar samarin suna turasu kamar jakuna



Hurriya gashinta duk yayi budu budu saboda bata maida dankwalin da ta cire ba lokacin da zata rike hannun Kumurci shikam Kumurci da ya juyo ya kalli yadda take struggling yakejin gabanshi na faduwa saboda yadda yakejin zuciyar shi ya kosa su isa masarautar su Mai cike da zallar zalincin he can t wait to have her in his bed



Cikin hiace din emirates din ake ta tura maza saida aka cika mota guda uku Hurriya dai tana tsaye bata matsa ba saboda duk duniya ta tsani taji jikin wani kusa da ita gashi duka marmatse suke saidai fa ko zata mutu a wurin bata shiga motar nan don waye ma baisan Hurriya Faisait hamood ba duk wanda yayi gigin tabata da hannunshi saidai yaji saukar mari



Daya daga cikin dogaren ne yazo ya zuba mata bulala ke yar matsiyaciya shiga banza tayi dashi don wani bansan kallo tayi mashi bata ko daga baki ba ballantana yayi tunanin zata bashi amsa kara mata wata bulala yayi har tana durkushewa kasa da kayanta shegiya matsiyaciya ki wuce ki shiga Dukanta ya fara kamar Allah ya Aiko shi yana zagin Hurriya da ta shiga motar Amman shiru tayi saidai fa ba hawaye amman idonta sunyi ja saboda radadi da azabar da take ciki Kumurci ne ya buga mashi tsawa yace shaho ya isa hakanan shaho badan ya gaji ba ya daina dukan ta ya lura wata isa gareta alhalin ita din ba kowa bace face kaskantarciya Kumurci ne yazo saitin da take yace Mai kike jira da bazaki shiga ba banza tayi dashi kamar batasan da ita yake magana ba kara tambayar ta yayi banza Hurriya tayi dashi har cewa yayi zai kira shaho ya kara mata still bata ko motsa ba Hurriya kam taki ko matsawa kowa mamakin Kumurci yake da aka ga yana lallabata saboda waye baisan Kumurci ba saida Hurriya ta mula sannan tace ban iya zama kusa da kowa cikin motar I want to seat alone kallon yadda take magana yake fuskar ta a daure kuma kamar tana bashi order abun ma dariya yaso ya bashi Amman da yake Kumurci ne yayi saurin murtuke fuska ya kalli motar da duk maza ne a ciki sannan ya fitoda mutum biyu yace ta shiga da kyar take tafiya Hurriya saboda dukan da tasha ,har ta kawo wurin cikin motar kayanta gam a hannunta kamar daman sune rayuwarta kusan duka mazan saida suka juyowa suna kallonta saboda kyaunta ga gashin dake yawo a bayanta tsawa Kumurci ya buga masu dukansu suka shiga taitayinsu Hurriya bayan ta zauna ta fara sauke ajiyar zuciya tunani take yanzu to ina rayuwa zata kaita lokacin da bata tsammani haka ya faru da ita saidai duk inda zata tana fatar Allah ya bata ikon jurewa don ga dukkan alama sun nuna ba wurin jin dadi bane a hankali ta duka ta nemo safa cikin kayanta ta sanya dukar da kanta tayi yadda ba wanda zai iya ganinta ta cire sarkar dake wuyanta da kuma dayar sarkar ta sanya su cikin safarta harda kudinta duka ta sanya su wayarta ce kadai ta bari a aljihunta tafiya ne suka fara Sosai don tunda ma aka fara tafiyar Hurriya wani bacci ya dauketa tafiya sukayi sosai don kusan tafiyar awa biyar sukai don lokacin har amfara kiran sallah la asar shine suka tsaya domin yin sallah



Hurriya jin hayaniya ya sanya ta bude idonta a hankali nan taga sun tsaya masu gyada nata tallah masu rake panke awara duk da sauransu cikin rashin kuzari ta sauko Amman jikinta yayi mata mugun tsami don da kyar take tafiya wasu panke manya guda biyu ta siya aka bata canjin ta sannan ta koma chan gefe ta zauna ta fara cin abunta



A hankali take ci ba don dadi ba sai don yunwa Hurriya taji ankira ta da mamaki ta dago kanta sai taga Bintu.

[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: <Masarautar Qamar



By Khadija (KMU)



Page 9&10



Mika ma Bintu fanke daya tayi kato cikin jin dadi ta amsa tace nagode Hurriya ,shiru Hurriya tayi tana kallon yadda Bintu ke cin panke a hankali ta kara kiran mai fanken cikin muryarta Mai dadi kara mika mashi kudin tayi tace ya bata na dari guda biyu ya kara bata mika ma Bintu tayi amsa tayi tace inason ki Hurriya sannan ta rinka cin fanken kamar bata taba cin abinci duniya ba Girgiza kai Hurriya tayi Bintu ce tace ma Hurriya kalli abinda dogarawa can keyi Hurriya mun bani Hurriya kallon saitin

Please Login or Register in order to submit comment