gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading IBTISSAM Murmushin Da Ya Canza Rayuwa BY MSSLEE Chapter 5 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sauri Abla ta girgiza mata kai “ Azumi nake “, sakin baki ilham tayi, itama Abla manyan idanuwanta ta lumshe mata , gudun karta ‘kara wata maganar yasa tace “kiyi sauri bamu da lokaci”, da Sauri kuwa ilham ta soma cin biscuit d’in, saida ta cinye manyan biscuit d’in kafun ta soma ajiyar zuciya , da sauri kuma ta tattara ledojin biscuit d’in ta Mayar cikin ledar data ‘boye cikin wani fasash shen gini daya lalace. Cikin sand’a suka fito daga d’akin gabaki d’aya ajiyar zuciya suka sauke ganin su Zinariyya basu fito ba, uban kayan wanke wanken da aka ‘bata masu shegen yawa su Abla suka fara had’a ita da ilham, basu suka kammala wanke wanken nan ba sai wajan karfe 12, lokacin da su Zinariyya suka fito kowa yana hamma acikinsu . Kallan su Abla Zinariyya tayi kafun ta ja wani dogon tsaki “ matsiyata kawai “, acikin su babu Wanda ya tanka mata saida suka kammala komai , sai alokacin fargaba ta soma kama su Abla , musamman da ilham ta tuna mata kiran ta da Uwar karuwai take , Jim kad’an Abla tayi kafin ta kalleta cikin ‘kasa ‘kasa da murya “ mu gudu sai mu dawo anjima “ da Sauri ilham ta girgiza mata kai cike da tsoro” a’ah Abla Nidai ina tsoro wallahi”, kama hannunta Abla tayi “ idan bamuyi hakan ba kinsan me zatayi miki idan kika shiga d’akin? Ko kin manta lokacin datasa kawayen ta su danneki tana ‘ko’karin farka miki kaya Allah ya ceceki daga cikin zaluncinta ?” Ajiyar zuciya ilham ta saki, ganin hakan yasa Abla taja hannun ilham Suka gudu, sunzo fita daga gidan Zinariyya ta hangosu, duk yadda taso taresu abun yaci tura saida suka gudu, tsaki zinariyya ta saki tana taunar le’ben kasan bakinta.

✨✨✨✨✨

UNITED STATES

karfe 6:30pm motocin Bobo Suka shigo cikin harabar building d’in gidan ,gabaki d’aya soldiers d’in kowa yashiga taitayinsa , Adil na jin durar motocin ya zabura zai gudu uncle iron man ya mayar dashi kan kujerar da karfi ya dam’ki hannun uncle kuwa , Adaidai side d’in building d’insu motocin nan sukai parking tsawan mintuna biyu da bud’e masa mota da akai kafun ya fito cikin takun manyan sojoji masu ta’kama da izza , yana fito wa daga cikin motar gabaki d’aya sojojin suka sara masa , basu ba hatta wa’yanda suke nesa dashi gaba d’aya kowa sai da ya sara masa , ganin yanda fuskarsa take a had’e ne yasa kowa ‘kara shiga taitayinsa, daga hannunsa na dama wani farin bandage ne daya zagaye tafin hannunsa dashi, a hankali ya soma taku kamar bayasan taka ‘kasa, duk daku d’aya da zaiyi da bugawar zuciyar Adil da gabaki d’aya ya dure, yana zuwa daidai bakin kofar shiga wani green d’in abu ya haska kafun ya fara kiran sunan “Bobo is back”, . Kara damke hannun uncle , Adil yayi gabaki d’aya tausayinsa ne ya kamasu shida prince ganin lokaci d’aya yana neman rikicewa , Bobo na shigowa cikin falon ya tarar dasu su uku a zaune da Sauri ta saka hannunsa me bandage d’in a aljihu, dukda yadda ransa yake a had’e hakan be hana yasassautashi ba , cike da girmamawa ya gaishe da uncle d’insu batare da ya kalli inda prince da Adil suke ba , cikin yar in ina prince ya furta “ welcomed back yaya bobo “, batare da ya kalli inda prince yake ba ya d’an jinjina masa kai, Adil ma kamar zaiyi kuka magana a rarrabe ya furta “Ya..Ya Bo…” be karasa maganar saba ya had’iye halamansa sabida kallan da bobo ya jefa masa kafun ya nufi inda Elevator d’insu yake . Fashewa da kuka Adil yayi ganin Bobo ya sharesa,gabaki d’aya rarrashinsa su uncle suka fara cikin sakin yalwataccen murmushi uncle ya furta “ Banasan wannan kukan , kaje ka basa hakuri kawai”, kallansa Adil yayi “Amma uncle fushi fa yake dani”, girgiza masa kai prince yayi “ kamanta abunda yaya bobo ya koya mana , idan munyi lefi mubada hakuri? Just kaje babu abunda zai maka kaji?”, kallan uncle da prince yayi lokaci d’aya suka d’aga masa kai, da sauri yanufi elevator shima, Daidai part d’in bobo ya tsaya ya’ki shiga, har zai juya sai kuma yasaka turn print d’insa take a Wajan kofar wajan ta bud’e babban falonsa me shegen kyau da ‘kayatuwa ya bayyana , kamshin freshener d’in lavender cedar leaf linen ne ya doki hancinsa, cikin sand’a Adil yasoma tafiya sabida kar aji ‘karar tafiyarsa, babu kowa a falon, kofar da ya gani a bud’e ya nufa bakinsa d’auke da sallama, da Sauri bobo da ke dressing d’in hannunsa yasaka hannun cikin aljihu yana bun fuskar Adil da kallo, sallama yayi Bobo ya amsa masa yana binsa da kallo, a mara rai ce Adil ya furta “ Yaya bobo kayi hakuri kaji?” ‘Dan harararsa bobo yayi ,” ni babu ruwana tunda baka jin magana , idan mesu ya dawo sai kayi masa bayani”, da Sauri Adil ya shigo cikin d’akin “ Dan Allah yaya bobo na, kawai nayi missing d’insane fa , shine naje na kallesu “, tausayin Adil , Bobo yaji ganin yana ‘ko’karin yi masa kuka “ fine , idan ka ‘kara rashin jinka kuma ni babu ruwana, lokacin sallah ya kusa “, ka hakura ? Adil ya tanbaya , gyada masa kai bobo yayi , da Sauri yazo zaiyi hugging d’insa bobo ya dakatar dashi “ idan na fito sai ayi hugging d’in, lokaci yana tafiya”, toh kawai Adil yace masa tare da barin d’akin fuskarsa a washe tunda bobo ya hakura, hannunsa me ciwo bobo ya ciro yana ‘kara bin yankan da kallo, ko da wasa yasan bazai bari Adil yaga wannan ciwanba, shiyasa ya ‘karasa dressing d’insa , kafun ya shirya cikin wasu Lious Vuitton d’in kaya riga da wando, daga jikin rigar akwai tanbarin VL me shegen kyau d’aya ‘karawa farar rigar jikinsa kyau , damtsen hannunsa sosai ya fito cikin farar jigar jikinsa, yalwataccen ba’kin gashin kansa duk ya kwanta masa a ‘keyarsa kasantuwar baya tara gashi sosai akansa . Kiraye kirayen sallar magariba ne yasa ya fito daga d’akinsa, lokacin gaba ki d’aya su Adil suna tsaye suna jiran sa, yana fitowa masallacin gidan suka nufa , kamar ydda suka saba kullum jam’i suke bi tare da musulman sojojin, wa’yanda ba musulmai bane sukuma suna kula da tsaran gidan. ‘Ka ida idan suka shiga sallahr magrib basa fitowa sai anyi sallar isha’i, suna idarwa Bobo tare da wasu sojoji manya manya suka nufi wata hanya , Adil zai bisu uncle iron man da prince suka dakatar dashi, zaiyi magana uncle iron man ya katse shi “ banasan musu Adil, dare nayi lets go “, girgiza masa kai yayi ya rike hannun uncle na hagu, dayan hannunsa kuma prince ya rike masa . Suna shiga prince ya nufi dinning daman bashi da jumurin yunwa , shima Adil dinning d’in suka nufa shida uncle , James ne yafito yayi serving d’insu , ko wannansu favorite food d’in sa yasoma ci, Adil ne kad’ai be soma cin abincin saba , prince ne ya kallesa “ me yasa baka cin abincin ka ?” , spoon d’in sa Adil ya d’auka “ ina jiran yaya bobo ne “, ‘karamun tsaki prince ya saki tare da ci gaba da cin abincin sa, kallan Adil, uncle yayi “ kaci abincin ka , idan ya dawo zan sashi yaci okay?” , kamar wani ‘karamin yaro ya mikawa uncle ‘karamin d’an ya tsansa alamar Alkawari, shima uncle yatsan nashi ya miko masa suka d’aure waje d’aya alamar promised.


A bangaran Bobo wani d’aki suka nufa me duhun gaske , kamar wani ‘karamin kurkuku haka d’akin yake , ga wasu chains da yawa a ciki , ‘kofofi uku ne a cikin d’akin, d’akin tsakiya Robert ya bud’e masa , nan ma wani duhu ne a wajan sai wani d’an haske kad’an daya haska d’akin, wani abu Robert ya danna take haske ya haska cikin d’akin . Wasu samari guda biyu ne a cikin d’akin ko wannensu da kunburarriyar fuska , suna ganin Bobo suka mi’ke tsaye , d’aya daga cikin sune ya kalli bobo murya bata fita sosai ya soma magana “ mun fad’a muku komai da kuke so ku sani , akan me za Kuzo ku kullemu anan “, be ‘karasa maganar saba sabida naushin da captain ya d’auke fuskarsa dashi, ‘kara ya saki sosai tare da dafe bakinsa da Jini ya fara zuba , kujera robert ya ajje wa bobo, yana zama suka koma bayansa shida captain suka tsaya , da hannu yayi wa samarin alama dasu zauna Bashiri suka zauna , cikin kausash shiyar murya bobo ya soma magana “ Tanbaya d’aya , Amsa d’aya , suwanene suke baku umarni akan kwayoyin da aka shigo dasu, matan da aka samu abuge cikin maye and ko waccen su anyi raping d’inta su wanene sukayi musu haka ?” A zabure suka kalli junan su , gabaki d’aya tsoro da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu, saurin kallan suna suka kafun su had’a bakin wajen furta “ mu babu Wanda ya samu”tsakanin captain da Robert babu Wanda yace musu komai sai ma fita daga Wajan da Robert yayi, Bobo kuwa tun bayan tanbayar da yayi musu be ‘kara d’ago kansa ya kallesu ba sai ma wata tsadaddiyar waya da yake dannawa hankali kwance, mintuna biyu Robert ya dawo cikin d’akin hannunsa d’auke da wani madaidaicin box me fad’in gaske black colour , kallan juna samarin sukai ganin Robert ya ajje Box d’in a gabansu, numbers guda uku ya saka box d’in ya bud’e , a ido mutum sai ya d’auka ba shi da girma , amma daga cikin sa waje ne me steps uku a jiki, ko wanne kuma da wasu ‘kananan makamai a cikin su kamar na operations , Wani ring cutter Robert ya d’auko tare da kama d’an yatsan d’aya daga cikin guys d’in , a tsorace guy d’in ya soma kuka yanaso ya kwaci hannunsa amma Robert ya rike hannun gagam, a daidai d’an yatsan sa ya saka abun fuska a cunkushe ya kalle su, “ 1…, 2….” Wanda aka rike wa d’an yatsane ya kalli d’aya da shima gumi da tsoro ya gama bayyana a fuskarsa amma taurin kai ya hanasu magana , Robert na furta “3”, Ring cutter d’in da yake hannunsa ya danna take a Wajan ‘karamin finger d’in guy ya cire , gigitacciyar ‘karar a zaba ya saki tare da zubewa wajan a sume, d’ayan da ya fara futsari a wando Robert ya kalla , amaimakon d’an yatsan hannunsa shi d’an yatsan ‘kafarsa Robert ya kama , da sauri ya fara girgiza kansa , cikin ‘kin’kina ya soma magana “ Me .. me zakuyi mun, me nayi muku , kuyi hakuri , please kuyi hakuri “ shima Robert be saurare saba ya yanke masa ‘karamin d’an ya tsan ‘kafa, kasan turar da turanci suke maganar yasa guy d’in sakin ihu shikansa be san me yake furtawa ba sabida azabar da ya ratsa masa ‘kafa “ Wayyo d’an yatsana, zafi, kuyi hakuri , na fad’amuku babu abunda muka sani , Wayyo , Wayyo ‘kafata “, d’an d’ago da fuskarsa bobo yayi kadan tare da kallan Robert, da Sauri Robert ya kalli guy d’in , finger dinsa yasaka guda d’aya alamar yayi masa shiru , da Sauri kuwa ya kama bakinsa ya ri’ke sai faman zazzare ido yake, Wanda ya suma Robert ya kalla kafin ya d’auko wani ‘karamin robber , me cike da gishiri da wasu abubuwa a ciki, d’an kad’an ya dauka ya barbad’awa mutumin cike da mugunta, azabure kuwa ya farka sabida rad’ad’in azabar da ya fi na d’azu zafi har cikin kwanyar kansa , kamar wani ‘karamin yaro ya fashe musu da kuka , kallan da Robert yayi masa ne yasa cikin sauri shima ya kama bakinsa yana nishi azaba, wani fingers d’insa Robert ya kama da niyar yankewa yasaki bakin nasa , cikin kuka ya furta “ ku tsaya zanyi magana , kuyi hakuri zanyi magana , zanyi magana “, shima d’ayan cikin kuka yadunga d’aga kansa, “susu uku ne “, ya furta da’kyar Sabida zafin da ‘kafarsa ke masa , shima Wanda aka yanke wa hannun jinjina kansa yayi alamar Hakane da ‘kyar ya furta “ Logan ,Dylan,Nicholas” a zuciye Robert ya ‘kara rike d’an yatsan sa daniyar yankewa guy d’in yayi saurin furta “ Logan d’an Governor, Dylan dan mayor , and … and “, ya kasa ‘karasa cikon na ukun, Gigitaccen mari Robert ya d’aukesu dashi , lokaci d’aya suka furta “Nicholas d’an matemakin shugaban kasa “, sai kuma suka fashe da kuka suna bawa bobo hakuri. Wayarsa Bobo ya mayar cikin aljihu , kafin ya mi’ke tsaye , ko kallan inda suke beyi ba ya bar d’akin su captain suna Goya masa baya har zuwa building d’insu, yana shiga captain da Robert suma suka shiga cikin wata ba’kar mota, bayansu kuma wata mota ce guda biyu da manyan karatan sojoji a ciki sukabar gidan.

ME BU’KATAR KARANTA IBTISSAM ZAI BIYA KU’DINSA TA WANNAN ASUSUN 2681892316
AISHA UMAR , ZENITH BANK , sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581. https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA


IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee

PAID BOOK:

littafin Ibtissam na kudine akan 300kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai tuntubeni ta wannan number tawa :07041879581.
Ko aturo kud’in book d’in ta wannan bank d’in: 2681892316 Aisha umar, sai a turo mun shedar biya ta wannan number : 07041879581.


Dedicated this page to the family of MAI INGILA , love you all my parents 💞💞💞.

💞💞__ All praises are due to ALLAH, the forgiver and concealer of fault, The Guide to Repentance, The one who responds to duas . AMEEN 💞💞__.


__BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM __


BOOK 1
( The beginning)

Season__6

ABUJA STATE , NIGERIA .

Tun da su Abla suka fita daga gidan karuwai gabaki d’aya barin unguwar sukai, sai da sukayi tafiya mai Nisan gaske kafin su zauna suna hutawa , ilham kamar zatayi kuka ta kalli Abla “ yanxu Abla kinga abunda muka jawo wa kanmu yanxu me kwatar mu a wajan shegiyar matar nan sai Allah”, kallanta Abla tayi kafin ta d’an ta’be bakinta ,cikin siririyar muryarta me dad’in gaske kamar sarewa ta furta “kome zatayi mana Allah na tare da mu ai , kuma ita bata isa tayi mana abunda Allah be nufa ba, kwanda ma ki kwantar da hankalinki”hawayenta ilham ta share duk da har yanxu akwai tsoro a tattare da ita “ Abla kinsan halin matar nan, bata da Imani musamman ke da ta fi nuna wa tsana , bansan Sharrin da Zinariyya zataje ta ‘kulla mana ba , shegiya kanta kamar duwawun d’an buri”, dungure mata kai Abla tayi “ kar ki wani dasu, ki tashi muyi abunda zamuyi kafin yamma tayi, kina an fara kiran sallar‘karfe d’aya , damun idar zan ‘karasa layin Formella , idan basu gama karatun suba , na saurara ko Allah zaisa na iya wasu abubuwan, Allah yasa Malam Sule yayi Tarihi yau”, shiru ilham tayi kamar me tunani kafin tace “ Amma Abla me zai hana yau muje kasuwar kubwa ,ko kayan kwanjone mu siya”mi’kewa tsaye Abla tayi , tare da zubawa ilham manyan dara daran milky eyes d’inta, dukda tana cikin halin rayuwa amma babu abunda ya canza daga kyawunsu,daga cikin idanuwanta har wasu d’igon tauwadane guda biyu da suke ‘kara Haska kyawun kwayar idanuwanta da suke zara Zara kamar wacce ta saka kwalli a cikin idan, ‘kara ‘kiftasu tayi akan ilham take a Wajan dogan gashin idanunta suka soma sama da ‘kasa ba’ka’kye Wuluk kamar tasaka , cikin daddad’ar muryarta me kama da na sarewa ta cewa ilham “idan kika kashe su ranar da kike bu’katan kudin ya zakiyi kenan? Karki manta su kad’aine dake duk duniya yanxu, na d’auka zakice zakisi wani abu ki kwada siyarwa? Ni kam babu ruwana babu wani kubwa da zanje, kinga biyu ta kusa ki taso muje muji karatun malam sule , banaso tarihin Annabi ya wuceni yau” Amma abla idan bamu je kasuwar ba Wana irin abu kikeso musiyar?” Soma tafiya Abla tayi ilham tabi bayanta da Sauri “ Allah zai haska mana ai, Kema kuma kinsan akwai sana’a sosai da mutum zai iya farawa , Nidai yanxu damuwa ta, kar agama karatu banjiba, ga tarihin da nakeson ji, ki bari zan fad’a miki Wana irin kasuwanci zamuyi kinji?” Jinjina mata kai ilham tayi tare da kama hannunta suka soma tafiya , saida suka ‘karayin tafiya me Nisan gaske kafun suzo wata makarantar Almajira da ke cike da maza, can gefe dasu Ilham da Abla suka ra’be suna sauraran karatun Malam suke dayake ‘karawa almajiran, ganin lokacin sallah yayi ne suka samu wani guntun ruwa sukayi alwala da sallarsu, kafin su ci gaba da sauraran karatun. Karfe 3:00 daidai Malam sule ya dakata da karatun ya soma yi musu tarihin annabi yusuf, gabaki d’aya nutsuwa Abla tayi tana sauraran tarihin, ita kadai sai faman murmushi take , 4:00 ya dakata musu, d’an ‘karamin tsaki Abla taja tare da kama hannun ilham suka bar wajan” wallahi Malam sule wani lokaci bashi da M, saida na nutsu ina jin tarihi zai katse mana “, dariya ilham ta saki daman tasan za a rina , duk lokacin da zasu zo jin karatun Malam sule a’karshe sai tayi complain musamman idan tarihi ake yi lokacin , Kiraye kirayen sallar la’asarne yasasu tsayawa daidai gefen wani masallaci, saida suka tabbatar sun shiga sallah kafun su samu suma suyi Alwala da ragowar ruwan butocin wajen, can gefe da masallaci su bi jam’i suma , ana idar da sallah muma suka tashi suka soma tafiya , wani dakali da Abla ta hango ta nufa, itama ilham zama tayi a gefenta, cikin nutsuwa suka soma karanto adduar safe da maraice, duk inda ilham tayi kuskure sai abla ta sake gyara mata , har suka gama sai lokacin ilham ta fara ri’ke cikinta “ Abla wallahi yunwa nake ji,”duk da itama Ablan yunwa take ji sai bata nuna hakan ba ita , cikin tsokana ta ce wa ilham “ toh taho mu koma kurkukun mu”, tsallan data ga ilham tayi ne yasata ‘kyal’kyalewa da dariya da har dimple dinta na both side suka lo’ba, “ wallahi Kema kinsa in muka koma zamu san sauran balalle ma musamu abinci ba, ga me awaracan dan Allah ko na d’ari musamu muci”, ‘karar da cikin abla yayi ne yasa ilham ‘kara kallanta “kinga Kema yunwa kikeje, karkimun musu kawai ki taso muje muci awaran”, batayi mata musu ba kuwa suka tsaya wajan me awara saida suka ci ta d’arinsu suka kora da ruwa kafin su fara tunanin komawa gida , wata bishiyar KARARA Abla ta hango da sauri ta nufeta ilham na binta abaya , saida suka ‘karaso wajan ilham ta zaro ido “ Abla me zakiyi da karara kinsan ‘kai’kayine dashi fa sosai, dariya mugunta abla ta saki kafun ta samo wasu manyan ledoji guda uku, biyu ta saka a hannunta,d’ayar kuma ilham ta rike mata ,tsabar mugunta irin na abla wad’an da Suka bubbushe ta tsutstsunka, sai da ta tara masu yawa sannan ta dakasu da dutse , ilham gabaki d’aya ta tsorata batasan me abla zatayi dasu ba , saida ta tabbatar ya mata yanda take so kafun suka nufo hanyar gida lokacin magariba ta kusa, a farkon layin suka hango husna ita da wani a tsaye daga jikin bango sai wani mammanne mata yake, tana ganin su Abla ta d’auke kai,kamar Abla zatayi mata magana sai itama ta shareta, hannunta ilham ta kama “ Abla ki ‘kyalesu, duk wanda yace baya bu’katarki a rayuwarsa Kema ki rabu dasu, kinyi iya kokarin ki akansu amma basa ganin haka “, d’an murmushi Abla ta sakar wa ilham kafun ta furta “insha Allahu “ . Kid’an da Abla ta somajine yasa ta girgiza kai, haka suke tun farkon magariba suke sa kid’a har isha’i, a Wajan gidan kuwa kamar yadda tayi tsammani mata da maza ne kowa tare da ‘yan matansa, wasu kuma matane kawai, ko wannen su da ‘yar iskar shiga , suna shiga Sukatar da abun yafi worse ma dan gabaki d’aya daga wacce zaka ganta kwance jikin namiji sai wanda suke kiss da shafe shafe ba ko kunya, kauda kanta Abla tayi tana neman tsari daga sharrinsu, da Sauri ta kama hannun abla kada su Zinariyya su gansu, suka nufi store d’in da ya zama kamar d’akinsu, karo suka ci da Aneesa dake ‘ko’karin fitowa daga d’akin cikin wata doguwar Riga , mamaki ne ya kama su Abla dan basu ta’ba ganin ta da irin wannan kayan ba “ Anee?” Cewar Abla , itama Aneesa murmushi ta sakar musu , cike da murna ta furta “ tun d’azu nake tanbayar inda kuke akace ba’a san inda kuke ba , Aushe zan ganku dai kafun na fita “, kallan ban gane ba Abla ta bita dashi, fahimtar hakan Yasa Aneesa bud’e wata swag Jakarta itama da Alama sabuwa ce ta Fito da ma’kudan kudi tana nuna musu “ A ina kika samo wannan kudin? Karkisa na fara zargin ko sata kika fara ?” Dariya Aneesa ta saki” haba Abla ki dunga mun kyakkyawan zato man, inda naje ne nasa mu wannan kudin kyauta , kinga tun jiya kaza da lemo nake sha sai abunda yayi mun yanxu na dena kwanan yunwa , zan dunga samun kudi” atare suka had’a baki wajan furta kamar ya”, bata damu ba itama ta soma musu bayani” kawai fa hotel zakuje, Wanda aka had’a ku dashi ya d’an shash shafaku,shikenan fa”, da mamaki Abla ta furta “ kina nufin karuwanci?” Girgiza mata kai Aneesa tayi “ ni ba karuwanci nayi ba , nace miki shash shafa ni yayi yana mun wasa da breast d’ina , ni kuma yace na sha masa…”, bata ‘karasa ba Abla tayi Saurin daka mata tsawa “ ya isa haka Aneesa bana bukatar jin zancenki , Allah ya shiryeki, banga anfanin mu’a mala da me irin halinki ba “, daga bayan ta taji an furta “ sai me idan bazaki yi mu’amala da ita ba ? Ko kina ba’kin cikin kudin da ta fara samu bakamar ke da kike a wahale ba? Gabaki d’aya maida kansu sukai wajan wacce tayi maganar , Husna ce tsaye sai faman harararsu Abla take , babu Wanda ya tanka mata tsakanin ilham da Abla, Hakan sai ya ‘kara ba’kanta mata musamman ydda Abla ta sakar mata murmushi tayi wucewarta, itama ilham wucewarta tayi batare da tace musu komai ba , tsaki husna taja dan ba haka taso ba “ Alhaji sammani yace na fad’a miki yana waje yana jiran ki, karki saurari maganar su? Ba’kin ciki suke miki dan sun fara ganin kin fara samun kudi, da suke cewa karuwanci, me kikayi a ciki dan kawai an shafa ki? Ki rabu dasu nima ke nazo kira daman Zinariyya tace mun akwai wani Alhaji da yake jira na, zo mu tafi “ ta kama hannun Aneesa sukabar wajan gudun kar Abla ta fito ta hana ta zuwa.

Suna shiga d’aki Shuru Abla tayi kamar me tunani, dafata da ilham tayi ne yasata sakin ajiyar zuciya “ na fad’a miki kidena sa damuwa aranki,ki duba kiga abunda husna take miki, gaskiya bana jin dad’i” Abla bata tanka mata ba sai ma murmushi da ta sakar mata,Inda suka bo’ye ledarsu ilham ta nufa Amma wayam babu ita babu alamar ta da sauri ta kalli Abla “,Abla banga ledar da na ajje anan ba , ko kin sauya Mata waje ?” Kai Abla ta girgiza mata alamar ah’ah suka shiga bincikar d’akin ga baki d’aya ko zasu ganshi amma wayam babu ,kamar zatayi kuka ta furta “ yanxu Abla ya zamuyi kenan Haka zamu zauna kenan?Ni ina tunanin ko su husna ne ma Suka d’auka “, zato zunubi koda ya kasance gaskiya , ki kyautata musu zato, sannan idan kika yarda da ‘kaddara sai kiga Allah ya baki sama da hakan Kinji “ cewar abla “ naji Abla Amma kinsan su Zinariyya bazasu taba bamu abinci ba ,”

Please Login or Register in order to submit comment