You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
bacci shiyasa bobo ya rage masa sanyin Acn dakin . Big boss na tsaye a falon hannunsa sanye cikin aljihu haka bobo kamar yadda yasaba kullum saida ya tabbatar da lapiyar komai na gidan kafun ya dawo cikin falon har lokacin big boss na tsaye ko gajiya da tsayuwar bayayi , sai da yaga shigowar bobo sannan ya juya zai bar Wajan , cike da tsokana bobo yayi saurin karaso wa inna yake “daga ganina kuma sai kajuya ? Hira fa zaka zo muyi “, big boss bai tanka masa ba sai hannun sa d’aya daya daga ya kaiwa bobo naushi, cikin azama bobo ya kauce yana dariya “ba’a banza ba little ya iya mugunta ba fa” cewar bobo yana kashe wa big boss ido d’aya alallai sai ya nemi rigima dashi , dauke eyes dinsa big boss yayi tare da soma takawa zuwa elevator har ynxu bobo na biye dashi , sai da ya shiga ciki tukunna lokacin da bobo yazo shiga big boss ya hanka dashi baya ya kulle bayan wani irin kallo da ya jefa wa bobo , har yanxu bobo dariya yake masa musamman yadda yaga ya hade rai . Gabaki d’aya light din ya kashe ya bar dum tukunna ya koma part d’insa , ba jima ba ya kwanta shima .
Big boss kuwa yana komawa part d’insa system dinsa ya janyo ya soma operating dinta cikin kwarewa kamar ba dare ba Sabida yadda ko damuwa da ya kwanta ba yayi , ya dau tsawan lokaci yana operating akan system din nan sai wajan karfe 4 ya kashe system din , still be kwanta ba sai da ya kara komawa part din su little wannan karan har dakin bobo ya shiga , duk da yadda bobo ya girma hakan be hana big boss gyara masa blanket ba kamar yadda ya sabayi masa, sai da ya tabbatar shima he’s okay tukunna ya koma part dinsa. Daidai Wajan balchony ya tsaya yana shakar daddadar kamshin wajan ko damuwa da yadda dare yake karayi bayayi ga sojoji da suke yawo ta ko ina . Yana tsaya akai kiran sallar Asuba , saida aka gama kiran salla ya bar wajan , cikin kankanin lokacin ya kara Shiryawa cikin wasu cotton kaya farare tas dasu , yau gashin kansa a nannad’e be tufkeba, ga kamshin turaransa ta ko ina da ya kama dakin. Tun kafun ya sakko down stairs prince da little suka fito falo, yau sun ruga kowa tashi daga bacci dan wallahi big boss ya Riga su fitowa suma sun san sauran shiyasa duk lokacin da yake gida suka saka alarm, Allah ya temakesu tun 6pm na yamma jiya prince ya saka musu alarm , uncle da bobo ma kusan lokaci d’aya suka fito suna jiran fitowar big boss. Saida suka kara kusan 10 minutes tsaye a wajan tukunna ya fito gabaki d’ayansu suka nufi masallaci dakaga fuskar little zai baka tausayi Sabida canjin face dinsa yau ko fara’a bayayi so yake yaya ya kulasa amma gabaki d’aya babu Wanda ya kula a cikinsu har suka tafi masallacin.
🍃🍃🍃🍃🍃
ABLA
Da ido ta fara bin dakin da kallo tana Tuna’nın ta yadda za’ai tayi sallah, batasan ya zatayi ba tunda ko kwakkwaran motsi bata iyayi da gabbanta, sun cutar da iya iya cutawa da bazata ta’ba yafe musu ba , da’kyar ta iya jan jikinta ta jingina da bango tana lumshe eyes dinsa da hawaye suke sakko mata , yunwa take ji ba kadan ba tun safe bata saka komai a cikin taba gashi har yamma tayi bata ci komai , jinta take kamar ‘ya’yan cikin ta zasu fito waje , tunanin yadda zatayi sallah kawai take cikin ranta da tayi kokarin mikewa zataji jiri na neman kayar da ita , bata da wani zabi face tayi niyya cikin zuciyarta ta rama sallolinta. Sai wajan karfe 8 aka kara bude kofar dakin da take , wannan karan ba a shigo ciki ba sai ledar bread da aka jefo mata tare da pure water guda d’aya aka sake kulle ta , dukda tsananin yunwar da take ji ko kallan inda bread din yake batayi ba ta kara silalewa a kasa ta kwanta cikinta har wani yaji yaji yake mata na yunwa , a haka wani irin wahalallan bacci ya d’auke ta . Binta shagala kuwa daga waje ta bada umarnin ajefawa Abla bread da ruwa dan bil hakki lokaci d’aya taya taji wani irin tsoran Abla ya shigar mata zuciya babu abunda yafi tsoratarda itama kar ace Abla tana da aljanu dan dukan da Abla tayi mata har yanxu bata dena shakkar tava , gani take Aljanun Abla ne suka tashi shiyasa bata kara tun karan ko inda dakin yake ba .
PAY YOUR 300 into dis Account 2681892316 Aisha umar, zenith bank.
Sai a tura shardar biya ta wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now * IBTISSAM*.
💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
S____17💞
Karfe 10 : 30 na dare wani irin azababben yunwa ya tayar da Abla daga baccin wahalar da ya d’i beta , Sabida yadda takejin yayan cikin ta kamar zasu tar watse sabida yunwa ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai , ganin da wuta a d’akin yasa cikin birgima ta Soma lalubar bread da ruwan da aka jefo mata , kamar zata fita daga cikin hayyacinta haka ta dauki bread dinnan ta dunga turawa cikin bakinta , sai da taga tana kokarin kwarewa ne yasa ta Soma ci a hankali amma duk da haka cikin Sauri sauri take tuttusa bread din da take ji ko ma’kogwaranta baya kai mata , gabaki d’aya sai da ta cinye guntun bread din da aka jefomata , a haka kuma ta sha pure water da take ji kwata kwata be ishetaba sai ma tasar mata da wani saban kishir ruwan da yayi amma ba yadda zatayi Haka tayi zamanta, sai alokacin ta soma jin karfin jikinta kadan a tattare da ita , gabaki d’aya abunda ya faru dazu ne ya soma dawo mata cikin kwakwalwarta, lokaci d’aya ta fashe da wani saban kuka , cikin shash shekar kuka take furta “ shikenan Arwa, shikenan yanxu kin mutu kin tafi kin barni?” Ita kadai take faman surutunta ga kuka tanayi lokaci d’aya, wani abun ma gabaki d’aya ita kanta bata san me take cewa ba dan kamar wacce ta fice daga cikin hayyacinta haka Abla ta dawo , bata dauki dogon mintuna 7 ba a wajan nunfashinta ya soma fisgewa , da kyar take iya jansa sabida yadda kirjinta yake mata zafi, take a Wajan ta fadi jikinta ya saki bata ko motsi.
4:00am Daidai aka bude d’akin , sai alokacin binta Shagala ta shigo cikin dakin amma tana daga baya baya ta tura yaranta gaba gaba , suma duk Wanda ka kalla fuskarsa zaka alamar tsorata a tattare dashi, d’aya daga cikin yan matan da ta shigo da ruwa a hannunta ta mikawa d’ayar, kafun ta karba sai data daidaici kofar fita kafun ta watsawa Abla ruwan. Lokaci d’aya Abla ta ware idanuwanta da ya ‘kara firgita su sun d’auka har yanxu Aljanun da suke cewa tana Dashine suka kara tashi. Gabaki d’ayansu zabura sukai lokaci d’aya suka bar d’akin, da kallo kawai take binsu ganin lokaci d’aya sun firgita . Ko mintuna biyu ba’a ‘karaba kuma suka kara dawowa cikin dakin, a wannan karan su 5 ne ragowar mata guda biyun ko wannansun sanye yake cikin ba’ka’ken kaya fuskokinsu a rufe , batare da wani tsoro ko shakkar yadda Abla take kallansu ba suka fara nufota, Abla bata soma jan jikin taba sai lokacin da taga d’aya daga cikin matar ta dakko wata allura cikin jakarta, da Sauri Abla ta soma jijjiga mata kai, gashi bata da karfin da zata gudu ko ta ce zata gudun ma babu hanyar guduwa , da karfi d’aya daga cikin matan da suka kulle face Dinsu ta janyo Abla tare da Matse mata ma’kogaro kamar zasu cire shi d’ayar kuma ta dauki Allurar da ta fito da ita batare da ta duba jijiya ko wani waje da ya kamata ayi wa Abla allura ba ta buga mata ita a kafadarta. Zafin da Abla taji ne yasa ta ware muryarta da tayi mata saura ta saki wani irin azababbiyar kara Sabida yadda taji allurar na shiga cikin jikinta , lokaci d’aya zafi da kaikayi ya rufeta, ji take kamar ana ‘kona mata naman jikinta, cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta fice daga cikin hayyacinta sai faman shure shure take sabida yadda take jin allurar cikin jikinta. Su binta shagala gabaki d’aya basu damu da yadda Suka ga Abla ta koma ba sai ma hanya da ta basu lokacin da suka ja Abla a kasa kamar wata kayan wanki, kanta na buguwa haka suka dinga janta har zuwa wata bakar mota da suka shigo da ita, haka suka jefata cikin voot suka tayar da motar tare da barin layin, Abla na cikin mota gabaki d’aya sai taji komai na jikinta ya tsaya bayan idanuwanta da take iya motsawa babu wani abu na jikinta da take iya d’aga wa , cikin wata bakar jaka yan matan nan da suka kulle face Dinsu suka mikawa Binta shagala kudaden da Suke ciki, cikin Sauri kuwa ta amshesu tana boyewa cikin rigarta, motar da aka saka Abla ko minti biyu cikakku basuyi ba suka tada motar a guje tare da barin area din gabaki d’aya .
🍂🍂🍂🍂
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
Koda aka idar da sallar asuba babu Wanda ya ‘bata lokaci tsakanin prince da little , cikin kankanin lokaci ko wannansu ya shirya cikin sport dinsa na training , musamman yadda suka ga big boss be shigo cikin gida ba , hakan ya basu tabbacin ko minti d’aya suka kara zasu gamu dashi . In ka kalli face din little yau zaka ga gabaki d’aya babu walwala a tattare dashi, daga big boss har bobo suna sane da halin da yake ciki, shi bobo yayi masa shirune sabida big boss yayi masa magana , big boss kuma izza da miskilanci ya hana ya kulasa. Cikin Sauri gabaki d’aya suka shirya tare da fitowa , cikin kankanin lokaci suka nufi wajan training, Wanda suka ganine yasa suka sha jinin jikinsu ganin sa a tsaye yayi folding hannayensa , zasu soma magana ya zuba musu rikitattun eyes dinsa da yasa ko wannansu yin shiru . Hatta sojojin da suke cikin wajan kowa cikin kwarewa yake motsa jikinsa dan idan tsautsayi yasaka kayi mistake babu ruwan big boss wai kai sojane, sawa zaiyi a rataye masa kai na 2 hours shiyasa ba karamun mugun shakkarsa suke ba . Cikin sunkuyar da kai suka nufi main dakin da suke motsa jiki, suna shiga Suka tarar da ba kowa a ciki shiyasa wani irin dadi ya kamasu , prince harda buga tsalle ganin bobo baya ciki yasan da wuya shima big boss ya shigo shiyasa ko wannansu ya d’auko abun motsa jiki mara sa wahala . Shi little da yafi kowa ma wani mat na training ya shinfida tare da daukar babbar balloon da ake motsa jiki da ita , prince Kuma skipping rope ya dauka shima , a tunaninsu big boss bazai shigo ciki bane shiyasa suka d’auki ‘kananan abubuwan nan ,prince yana cikin skipping dinsa juyawar da zaiyi kawai idanuwansa ya sauka kan big boss da yaya bobo dake gefensa, shi kansa besan lokacin da ya kusa hantsulawa ba , da Sauri ya yardar da I giyar shi little gabaki d’aya be kula da yanayin da Prince yake ciki ba sabida kulle eyes dinsa da yayi , kallan da big boss yake bunsu Dashi kadai ma yasa hantar cikin sa kad’awa , da Sauri prince ya ta’ba little , shima yana bud’e eyes dinsa yayi saurin mikewa tsaye , cikin rawar murya ya furta “ yaya please kuyi hakuri kunji?” Ya karasa da niyar matsowa inda bobo yake sabida yadda yake tsoran Kallan side din big boss , shima bobo kallan da ya jefa wa little ne ya hanashi motsawa daga inda yake , big boss be ce muku komai ba sai juyawa da yayi ya bar wajan, shima bobo kallo d’aya yayi musu kafun ya furta “ follow me” yaya please ka bashi hakuri , we’re sorry “ cewar prince , amaimakon bobo ya bashi amsa sai ma cikin kakkausar murya ya furta “ 2 minutes kawai na baku” yana kai karshen zancansa ya juya yabi bayan big boss , cikin rud’ewa prince ya fara furta Innalillahi wa inna ilaihi raji’un , little please ka bawa yaya big boss hakuri please” shima little kamar zaiyi kuka ya furta “ fushi yake dani fa, ni tsoro nake ji” bai karasa maganar da zaiyi ba shida prince suka bar dakin a guje sabida minti biyun da bobo ya basu har yayi . Kamar yadda suka sani wajan horan sojojin da suka je jiya zasu nufa , shiyasa kai tsaye cikin ‘kan’kanin lokaci suka karasa wajan , yaya big boss baya wajan shiyasa gabaki d’aya suka saki ajiyar zuciya duk da kasan zuciyar su fall tsoran hukuncinsa suke ji, inda bobo yake a tsaye wani waje ne me kamar tiles ,yadda Wajan yake kyalli zai tabbatar maka da abun santsi sojoji Suka zubawa a Wajan , kallan kallo prince da little sukai kamar zasuyi kuka dan sun gane me zasuyi shiyasa tun kafun bobo yace su cire takalmansu Suka ciresu tare da tsayawa a Daidai sai tin wajan , wasu sojoji guda biyu Suka karaso Inda suke tare da wani fork a hannu saida suka rike fork din sosai kafun sojojin su saka musu kwai a kai , duk abunda yake faruwa bobo na kallansu bayasan ganin yadda face Dinsu take , shiyasa yadan daure face dinsa kadan “ you can start , duk Wanda ya fadi a cikinsu zai fara daga farko , duk Wanda egg din fork dinsa ya fadi zai gane kurensa , you can start “, cewar bobo, prince yana saka kafarsa a wajan yaji yana kokarin sullu’bewa, da Sauri ya ja baya da yasa egg dinsa fashewa,” ^2” cewar bobo, shima little yana shiga yaji yana kokarin faduwa , saura kadan ya fadi shima amma Allah ya temakesa, saida yazo Daidai tsakiya ya su bale kwansa ya fadi, kamar zasuyi kuka haka ya kara dawowa farko , shima prince da yayi nisa santsi yake d’ebarsu suke faduwa , sunfi 20 minutes suna abu d’aya amma sun kasa karasa zuwa inda zasu ajje kwan, akan idan bobo duk abunda yake faruwa , gwanda shi yayi musu hukunci akan big boss yayi musu , idan ba hakaba ba karamun jigatasu zaiyi ba , yadda santsi yake kayar dasu ba karamun dariya da tausayi zasu baka ba , hatta little cikin faduwar da yayi saida ya Bige hannunsa amma ya ki bari bobo yagani shiyasa ya cigaba , ga zafi da hannunsa yake masa amma hakan ya cigaba da shiga cikin santsin yana fad’uwa , tun yana kokarin dannewa har ya soma hawaye , , shikansa bobo da yake kallansu ba dadin abin ya ke jiba , a ka’ida punishment 4 zaimusu amma ba xai iya ba shiyasa ya dakatar dasu ya bar wajan , Allah sarki little yadda fuskarsa tayi jajawur ba karamin tausayi zai baka ba , dakyar suka taka Suka koma cikin part Dinsu , babu kowa a cikin falourn kai tsaye d’akinsu suka shiga sukai wanka , shi prince sabida yadda ya gaji kai tsaye lapiyar gado yabi, little kuwa kasa kwanciya yayi Sabida tunanin yayansa da ya’ke shiyasa ya nufi part d’insa , ko da yashiga kasa tun karar dakin big boss yayi shiyasa ya kwanta akan sofa a takure , yasan bazai fito yanxu ba Sabida yanxu ne lokacin baccinsa , shiyasa shima yayi kwanciyarsa kan sofa , sai da ya dau kusan 20minutes kafun wani irin wahalallan bacci ya daukesa. Tun lokacin da ya shigo big boss ya gansa , amma miskilanci da izza ta big boss ta hana yace ya shigo d’akin, tsawan wannan lokacin yana zaune kan sopa yayi crossing legs dinsa , tun lokacin da little yake kwance kan sofa da yadda ya takura har yayi bacci duk a kan idan big boss , lokaci zuwa lokaci yana lumshe kyawawan idanuwansa sabida yadda yaji kansa yana sara masa , saida ya ‘kara d’aukar 10 minutes zaune a wajan tukunna ya mike ya nufi palourn da little yake a kwance, gabaki d’aya eyes dinsa ya zuba masa yana bin kyakkyawar face dinsa da tayi ja kadan da kallo, a hankali ya soma takawa har ya karaso inda yake a wance , hannunsa da yasa cikin aljihu ya fitowa dasu tare da daukar little kamar Wanda ya dauki wani jariri ya nufi d’akinsa dashi, akan lallausan king size bed dinsa ya kwantar da little tare da d’auko wani unique roba d’an ‘karami, hannun little dayaga ya d’anyi ja ya shafawa a hankali gudun karya tashesa daga baccin da yake yi , saida ya tabbatar maganin yayi masa yadda yakeso kafun ya ja masa Duvet dinsa sosai sabida yadda sanyin Ac ya karad’e ko ina . Ya jima zaune a inda little yake yana bin kyakkyawar innocent face dinsa da kallo , lokaci zuwa lokaci kuma yana lumshe idanuwansa da suka fara canza launi kad’an, idan mutum ya kallesa yaga yadda yake lumshe idanuwa sai ya dauka wani izzar ya’ke kara nunawa , amma gabaki d’aya sabida saramasan da kansa yake masa ne yake lumshesu, a wannan lokacin kamata yayi a ce yana kwance , amma ya hana kansa haka sabida little da yasan zai shigo d’akin. Yanxu ma saida ya tabbatar baccin little yayi nisa sosai kafun ya koma d’ayan side din ya kwanta.
A ‘bangaran bobo ma saida ya shirya cikin wani saban wankan kananan kayan kafun ya nufi d’akinsu little , yana shiga ya tarar da babu kowa a ciki sai prince da yake bacci a gajiye , ‘karasa shigowa ciki bobo yayi , dan karamin maganin hannunsa ya bude tare da shafawa prince a gwiyarsa shima da tayi ja , har wani ajiyar zuciya yake saukewa cikin baccin, yana gama saka masa ya gyara masa duvet dinsa ya bar d’akin. A falo ya tarar da uncle yauma hannunsa dauke da jarida, suna had’a ido da bobo ya hararesa, shi kuma bobo sai ya mayar masa da martanin murmushi yana sunkuyar da kansa kasa “ dole kasun kuyar da Kai masa mana , tunda kun gama cin zalin bayin Allah “,
Ynxu ma murmushi bobo ya saki tare da zama kan d’aya daga cikin kujerar kusa da uncle “ uncle ba haka bane bafa , as big as they’re sun shiga training room suna shashan cinsu cos basuyi tunanin zuwan muba , they’re very stupid shi prince skipping rope wai yake yi sai kace wani yaro , little kuma mat ya shinfida gefen sa ball, in ba so suke big boss ya gwada harbi akan suba “, murmushi uncle ya saki “ shine dan mugunta ka sakasu abu me wahala , taya zaka saka a saka abu me santsi a tiles sannan ka basu kwai cikin fork? Muguntar tayi yawa fa”, cewar uncle , a wannan karan dan dariya bobo ya saki “ uncle ai gaka gashi, kasan big boss lokacin da kake ce masa no toh alokacin zai mayar da abun yes , thank god ma a waje na suka sha hukunci ba a Wajan sa ba”, harararsa uncle yayi “ Menene banbancin naku? Ba duk mugaye bane ku? Musamman wancan wan naka idan ya d’aure fuska sai ka dauka ba’a ta’ba saukar da wani abu murmushi ba a Inda yake “, tun be kai karshen maganar saba bobo ya kyalkyale da dariya sabida wani abu da ya tuna , sai da yayi dariyarsa sosai kafun ya kalli uncle “ uncle har ka tuna mun wani abu, a kwai wani ma’aikaci da ya dunga washe baki a wani meeting da akai, tun lokacin da big boss ya shigo ciki kowa ya shiga taitayinsa banda guy din cos lokacin ne meeting dinsa na farko, yadda yake murmushin ne ya bata wa yaya rai shiyasa yasaka ayiwa mutumin abinda zai sa shi dariya yana zaune kan chair sannan ga shocking yasa a kunna , duk lokacin da guy din ya kuskura yayi dariya zai bada umarnin a kunna shock, that guy har yau idan yaji sunan big boss sai ya firgita Sabida amaimakon ya dunga dariyar kuka ya soma , and at last kasan me yayi ? That his red lips ya ta’be ya bar wajan “, shima sosai uncle yayi dariya yasan kad’an daga cikin aikin big boss , zaiyi abunda yafi haka ma , shiyasa kowa yake tsoran shiga gonarsa.
“ uncle lets eat , yau yaran naka bacci suke” hakan kuwa ya faru su kadai sukai breakfast Dinsu , yau hatta Prince da yafi kowa san cin abinci shima baccin yake yi, saida suka kammala cin abincinsu uncle yaga bobo ya nufi hanyar kitchen , cikin shock da mamaki uncle ya furta “ me zakayi kuma a nan?” ‘Dan murmushin bobo ya saki yana kallan hanyar “ its long time now ! Na dad’e ban girka masa abinci da kai na ba”, yanxu ma cikin dan zaro ido uncle ya furta “ who ? Are you serous ?” Fasa tafiya bobo yayi ya kalli uncle yana dariyar reaction dinsa “ uncle kai ma kasan yayana zan girkawa abinci ko?”, yau ba fita ?” Uncle ya kara dakatar dashi, juyawa bobo yayi kafin ya furta “ he’s more important than my work ! Yau zan girkawa big boss abinci ne with my own hands kafun tom and Jerry ( prince da little ) su tashi daga bacci .
✨✨✨✨✨
GERMANY
A hankali sauban yake sakkowa daga stair case, yana tafiya yana duba agogon hannunsa Sabida bayasan lokaci yaja masa , daga gefensa kuma Fanan ce take sakkowa da wani unique travel bag madaidaiciya , daga nesa da shi ta d’an tsaya tana facing Mamey dake binsu da kallo “ yaya sauban yanxu shikenan wai tafiya zakayi da gaske? Mun kusa komawa makaranta fa, bazaka ‘kara kwanakiba kafun na tafi? Wallahi zanyi missing dinka”, girgiza kai kawai mamey tayi , dan halin fanan sai ita wani lokacin , shikansa sauban d’an hararar ta yayi kafun ya furta “ zakiyi missing dina ko zakiyi missing kudina da kikeci?” Dariya Fanan ta saki a wannan lokacin “ Haba yaya sauban kasan kai nafi missing amma kudin naka ma nayi missing dinsa kaga mun kusa komawa makaranta” ta karasa tana kashe masa ido, sai kuma tayi saurin dafe bakin ta sabida pillow din da ya jefa mata a baki “ kud’i dai nawane ba naki ba sai naga me baki ai “, Haba yaya cewar Fanan tana kallan mamey , “ kima dena kallona dan babu abunda zance muku, anjima kuzo ku bani kunya “, sim sim Fanan ta karaso Wajan ta “ mamey babu wani kunya da zan baki kawai kibi bayana , kinga yanxu yaya sauban ya rage sona kawai ki fad’awa Abbu a aurar da shi nima nagaji da ganin sa ba aure”, yadda ya nufo kanta da saurine yasa ta arta a guje cikin daga murya ta furta “ Allah yaya sauban ka kawo mun aunty ta , ni bazan tsaya ka kamani ba , Allah ya tsare hanya , all the best Fleet Admiral,” bata jira cewarsaba Sabida karyace zai kamatan, girgiza kai kawai yayi yana kallan mamy “ wannan yarinyar taki mamey ta rainani , ranar
Book Chapters
Chapter 20
Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51