You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
cikin gidan sabida headache din da yake fama dashi ga idanuwansa da sukayi mugun red sai faman lumshe su yake .
WASHE GARI
Ana kiran sallar asuba gabaki d’aya suka fito falourn , yau abun mamaki kowa ya fito kamar yadda suka saba fitowa amma banda big boss , sun dad’e suna jiran fitowarsa amma basu ganshi ba , little har ya damu yana ‘kokarin zuwa part d’insa bobo ya hanasa sabida sallah da ake ‘ko’karin yi , haka gabaki d’ayansu suka nufi masallacin banda shi , dan kuwa abune me matukar wuyane xai hana sa fitowa kowa kuwa rashin lapiya yake yana fitowa sallah dukda shima rashin lapiyan da wuya su gane bashi da ita . Ana idar da sallah tun kafin kowa ya fito daga masallacin bobo ya nufi part d’in Big Boss dan yasan ba lapiyar sa kalau ba tunda be fitowa sallaba, yana shiga part d’insa ya kulle door din ta ciki ta yadda ko su little sun saka turn print d’insu bazai bud’e ba, gabaki d’aya ko ina da duhu , cikin Sauri bobo ya tura ‘kofar bedroom d’insa da yaga alamar hasken fitula, yadda yaga Big boss a zaune ne yasa yayi saurin ‘karasawa inda yake , yana kokarin ta’basa big boss yayi saurin hankad’asa baya “ don’t touch me” shine kadai abunda ya iya furtawa, Bobo bai damu ba yakara yunkurin ta’basa big boss yayi saurin bige masa hannu, Allurar da yagani akan center ne yasa gabaki d’aya mamaki ya kamasa , xai d’auki allurar big boss ya ‘Kara bige masa hannu, wata allura ya janyo xai yiwa kansa bobo yayi saurin ri’ke hannunsa sai alokacin yaji yadda jikin Big boss yayi mugun zafi, zai ta’ba masa goshi big boss ya kara bige masa hannu , cire hannun bobo yayi yana ‘ko’karin yin allurar cikin Tashin hankali bobo ya kai hannu zai fusge amma ina tuni big boss ya yi allurar , cikin Sauri Bobo ya fita daga d’akin, be jima ba ya dawo d’auke da babban ruwan roba me shegen sanyi, gashin big boss gabaki d’aya ya rufe masa fuska a Bobo na kokarin ta’basa big boss ya hanasa hakan , tunda ya sunkuyar da face d’insa kasa be katta dawo da ita ba sabida yadda jijiyoyin wuyansa suka tashi sosia , idanuwansa sunyi jajawurrr ba kad’an ba , lokaci bobo ya kalla da Sauri ya bude ruwan nan duk da yadda yake da mugun sanyi haka ya fara tuttulawa big boss akansa…..
PAY YOUR MONEY INTO 2681892316, Aisha umar zenith bank sai a turo shardar biya ta wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨
Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*
💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.
O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to the besieged😭😭.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏…
S____23💞
Lumshe idanuwansa yayi sosai sabida ruwan da bobo ya watsa masa me shegen sanyi da har cikin gashin kansa saida yaji sa , a karo na biyu bobo ya ‘kara bud’e wani saban ruwan ya tuttula masa har farar shirt dinsa sai da ya ji’ke , daga inda mutum yake xai iya hango white singlet d’insa da farin fatar jikinsa. A maimakon bobo ya rage ‘karfin Acn sai ‘karawa ma dayayi, a hankali ya Mayar da kansa baya ya jin gına da jikin sofa d’in da yake , sosai jijiyoyin kansa suka mi’ke, wata allurar ya janyo batare da ya bud’e eyes din saba , da Sauri bobo yayi saurin d’auketa yana ja baya “ why please? Kanaso kaji wa kanka raunine? Please kabar allurar nan haka “, ko ta kan maganarsa Big Boss be biba sai ma hannun sa d’aya da ya sake wa dressing ya mi’kamasa “ Give it back !” Cewar Big boss , Baya bobo yayi kad’an “ am sorry gaskiya bazan baka ba “, Lokaci d’aya big boss ya bud’e idanuwansa da sukai mugun yin jaa sosai , yadda idanuwansa sukai jaa sai ya ‘kara fito da kyawun idanunsa kamar ya saka kwalli, “ kasan illa kake ‘ko’karin yiwa kanka , me yasa duk lokacin da ranka yake a’bace bazaka iya dannewa ba sai kayi wa kanka wannan allurar ? Please !”cewar Bobo, yanxuma hannunsa Big boss ya mi’ka masa a d’an zuciye ya furta “ Give it back “, shima bobo a zuciye ya furta “ Bazan bayar ba ! So kake kayi wa kanka illah ? Wazai kula da little? Prince? Uncle? Please ka rage zafin zuciyar nan taka please “, cikin cool voice big boss ya furta “Get out of my room “, bobo zai ‘kara magana cikin zafin rai Big boss ya ‘kara furta “ I said get out of here “, girgiza kansa kawai bobo yayi batare da ya ajje allurar ba ya sata cikin aljihunsa tare da barin part d’in . Yana fita Big Boss ya lumshe idanuwansa da sukayi ja sosai, ya dad’e zaune a wajan jikinsa a ji’ke , kusan 10 minutes sai kuma ya tashi ya nufi toilet d’insa .
Bobo yana sakko wa ya tarar dasu little a tsaye duk sunyi sarko sarko suna jiran sakkowansa , murmushin da ya sakar musu ne yasasu ajiyar zuciya “ why kuka tsaya anan ? Ku dena damun kanku babu abunda ya sameshi , kunsan yanzune lokacin baccinsa , anytime ya tashi zaku gansa ya Fito okay?” A d’an shagwa’be little ya furta “ yaya ko zanje na dubasa? Tunda ya fita jiya ban ‘kara ganin saba fa “ hannunsa bobo ya kama suka nufi kan kujera “ little banda rashin ji kuma kasan yayanka ayyuka sun masa yawa ko?” Kansa little ya d’aga masa “ then allowed him to relax jiya be dawo gida da wuri ba ! Kaga yau ko training baza muyi ba , Nima guduwan training din zanyi “ da Sauri prince ya matso kusa dashi “ Dagaske kake yaya bazayı ba?” Daman a cikin su babu Wanda yafi tsanar motsa jikin nan kamar prince shiyasa bobo yana amsa masa har da wani juyawa yayi na farinciki “ hannunsa d’aya ya dunkule tare da furta “ yessss”. Yaya “ little ya ‘karakiransa , shima amsa masa bobo yayi yana kallansa “ yaya please yau munasan zuwa siyayya kaji “ tell me what you want sai a kawo muku har gida “ da Sauri little yace “No yaya wannan siyayyar little sister ne , kaga ya kamata ta za’bi kayan da take so ko? Please just say yes and bata iyacin abincin mu bafa “kumatunsa bobo ya shafa “ Are you happy?” Yes yaya sosai , be bari bobo ya kuma magana ba ya furta “ yaya ina farin ciki sosai, I also have a sister now , inaso na sata farin ciki itama , bata da family , ni kuma ina da ku my only family, and now we are 6 not 5, okay ?” Kaifa fi’ilinka ya maka yawa tunda ka samu sister kake behaving sai kace wani babba ….” Uncle bai’karasa maganar da yakeso yayi ba Sabida ‘kamshin turaran Big boss da suka ji daga sama , gabaki d’aya cikin sauri suka kalli direction d’insa , yana tsaye daga bakin elevator d’in da ya fito fuskarsa gabaki d’aya babu fara’a , ba kamar ko da yausheba yau face d’insa tafi ta ko Yaushe had’ewa shiyasa lokaci d’aya little da prince Suka shiga taitayinsu , uncle da bobo kuma idanu kawai suka zuba masa. Kamar ko da Yaushe sanye cikin wasu white d’in kayan Hermes farare tas dasu riga da wando said’an jikin rigar da aka yiwa ado da d’an ba’ki kad’an, Sabida yadda rigar ta kama damtsen hannun sa sosai muscle dinsa suka fito farare tass da su , ‘kafarsa sanye take cikin black d’in Nike Air Max din ta kalmi ,yau hatta gashin kansa be tufkeba kamar yadda ya saba sai nannad’e shi da yayi , hakan ya bawa farar kyakkyawar fuskar fitowa sosai ga Diamond necklace d’insa da kullum baya rabuwa da shi, sau d’aya ya kalli ko wannansu yana d’auke kansa , dan gabaki d’aya yaji maganganunsu, yadda su uncle suke binsa da kallo ne yasa ya ‘kara had’e face d’insa yana takowa a hankali kamar bayasan taka ‘kasa , har ya ‘karasa sama akan white sitter suna binsa da kallo, ko sau d’aya be d’ago ya kallesu ba sai yayi kamar ma baisan da zaman suba, “ Morning yaya” cewar prince da little da suka had’a baki kusan a tare , bai amsa musu da baki ba sai lumshe eyes d’insa da yayi kad’an alamar amsawa , gabaki d’aya falourn shiru ne ya biyo ba , sabida mamakin fitowar Big Boss a wannan lokaci , dan yawancin lokuta a wannan lokacin ne yake bacci , d’ago da eyes d’insa yayi ya zubawa little , cikin Sauri little yayi masa fiki fiki ido, d’an motsa lips d’insa gefe d’aya big boss yayi da hakan ya bawa dimple dinsa lotsawa , gabaki d’aya sai suka tsaya kallansa duk da abunda yayi baza’a kirasa murmushi ba sannan baza’a kirasa ya’ke ba , ganin yanda suka wani kallesa ne yasa ya tsuke face d’insa , cikin cool voice d’insa kamar bashi ba ya furta “ You are happy because of that thing ( Abla 😂) ryt”, yadda ya kira thing d’inma kamar Wanda aka saka dole , da farko little begane wa yake nufi ba saida yaga kallan da prince yake masa , da Sauri ya furta “ yes yaya”, hannu d’aya big boss ya saka ya shafa girarsa da take a tsage kamar ba zai kuma tanka wa ba sai kuma ya ‘kara furta “ you all want to leave with her ?” Ya ‘karasa yana kallan prince da little , cikin Sauri suka furta “ yes yaya” dan ko magana yayi bayaso ayi masa knodding , sannan bayasan ‘bata lokaci koda kuwa sai yi hour kafun yayi magana . Kansa yayi knodding a hankali, shi kansa bobo kasa magana yayi yasan tunda ya fara kiran Abla da thing ba lalle inuwarsu tazo d’aya ba , bai kai ga ‘Karasa maganar zucin saba sabida saukar muryar big boss da ya ‘karaji “ bring her here”, lokaci d’aya gabaki d’aya Suka zaro masa ido, little kuma cikin sauri ya nufi d’akin Abla , “ Ba ka yadda ta zauna ba ?” Cewar bobo dan har ga Abla Bayaso big boss yayiwa Abla komai , amma ganin ya sharesa ba tare da ya tanka masa ba ne yasa yayi shiru shima yana jiran yaga me zaiyi, uncle kam sarautar Allah ya zubawa ido shi kansa ya kasa magana dan besan me Big boss zaiyi ba . Ko cikakken 3 minutes little beyi ba suka sakko shida Abla da wani irin masifaffen ‘kamshin turaranta ya do’kosu dukda ko kwatan kamshin turaran big boss beyi ba , kanta a ‘kasa cikin shigar doguwar rigar da tayi purple colour da yayi mata kyau sosai sai veil d’insa da ya ‘kara haskota, tun kafin su ‘karaso cikin falourn bugun zuciyarta ya fara da Sauri Sauri, hannunta har ya fara rawa duk da bata d’aga Kai ta kalli mutanan falourn ba amma ta gane masifaffen ‘kamshin turaran jiya da ta dad’e tana ji cikin hancinta, lokaci d’aya taji kayan cikinta sun juya sabida tsoro dukda bata d’aga fuskarta ba Sabida shakkar d’ago da face d’inta da take , hatta tafiyarta saida ta canza sai faman hard’e ’kafa take , suna shigowa cikin falourn ta d’an d’ago kanta da niyar gaishesu, idanuwanta basu sauka ko ina ba sai a kan face d’insa da ya lumshe , lokaci d’aya ta fara ‘ko’karin birkicewa har wasu kwallane da ita kanta batasan dalilin fitowarsuba suka tarar mata cikin idanuwa, cikin sauri ta d’auke eyes d’inta , muryarta har rawa yake wajen furta “ ina.. ina.. kwana…” gabaki d’aya sai suka ‘kara kallansa sabida sunsa da shi take amma kamar Wanda akai magana da gunki, akaro na biyu ta ‘kara furta “ ina… kwana “ be amsa mata ba , shi kansa little a tsure yake dan gabaki d’aya ya manta be fad’a mata kada tayi Hausa ba, koda ace bata iya turanci ba zai fi mata alkairi akan tayi Hausa a gaban big boss dan yana d’aya daga cikin abunda yayi mugun tsana shiyasa duk lokacin da yake gida basa amfani da Hausa, lokaci d’aya Abla ta fara shash she’kar kukan da bata san dalilin fitowar sa ba, prince har da dafe kai ganin tana ‘ko’karin janyo musu wani hawan ruwan, rai a ‘bace ya bud’e eyes dinsa da sukai mugun ‘kad’awa na ‘bacin rai, wani irin mugun kallo da ya zuba mata lokaci d’aya tayi kneeling dan sosai wani irin tsoran sa ya ‘kara shiga cikin zuciyarta , ita kad’ai bakinta sai rawa yake sabida tsananin tsoran da ya kamata , d’an ta’be bakinsa yayi kad’an yana d’auke eyes dinsa zuwa na little da yayi tsutsu dashi kamar mara gaskiya , akaro na biyu ya ‘kara bud’e bakinsa cikin tsantsan American English d’in da ya zauna masa ya ‘kara furta “ duk kun amince da zamanta ?” Da Sauri cikin turancin prince da little suka basa amsa , direction din bobo ya kalla da ido , wani murmushi bobo ya saki kafun shima ya furta “ yeah “, the same amsar da uncle ya basa kenan, wani irin murmushin gefen baki big boss yayi da yayi mugun basu mamaki ba kad’an ba , banda Abla ta sunkuyar dakanta ‘kasa tun bayan tsugunnawar da tayi, bakad’an ba tsananin mamaki ya kamasu dan abune me mugun wuya kaga ‘karamun murmushin gefen bakin big boss . “ she will stay”… cewar Big boss yana katsemusu tunaninsu, cikin murna little ya fara gode masa “ thank you so very much yaya” hannu kawai big boss ya d’aga masa lokacin da ya zubawa Abla narkakkun idanuwansa da yasa tayi saurin ‘kara sunkuyar da kanta ‘kasa ga hawayen da suke sakko mata suma , hannunta sosai yake rawa haka bugun zuciyarta ma da take ji kamar zata fito waje , “ My orders !” Ya ‘kara furtawa a gajarce dan bayasan magana me tsawo gabaki d’aya , shuru falan yayi lokaci d’aya kowa yana jira yaji me zai kuma fad’a , sai ya d’auki good 1 minutes kafun ya iya bud’e bakinsa kad’an kamar me ciwan baki “ from today kece sabuwar me aikin Simba”, cikin cool voice bobo yayi saurin furta “ big boss please!” Big boss bai saurareshi ba ya cigaba da maganarsa “ 7:00am zaki kaiwa Simba abinci , 3:00pm for his lunch and 8pm for his dinner , in fact komai nashi ke zaki kula dashi” ya ‘karasa da d’an ‘karfi , cikin sauri cike da tsoro Abla ta furta “ Toh…”duk da bawani turanci ta iya sosai ba tana jin me ake cewa mayarwane bata iya ba sosai amma dukda haka ta gane maganganun da dukda yadda turanci yake fitowa , bobo zai sake magana Big boss ya ‘kara bud’e bakinsa , “ 7:00am for the training time ko 1 minutes kika ‘kara , zaki gane kurenki, anytime idan zan dawo I need my coffee and also dis is your job , idan kika kuskura kika kwana without my coffee… “ bobo zai ‘kara magana ya furta “ kin yarda ko baki yardaba “ yadda ya fad’a cikin d’an tsawane yasa Abla tayi saurin furta “ Na Aminci” dukda yadda little yake girgixa mata kai amma aikin gama ya gama tunda tace masa ta amince, be kuma cewa komai ba ya mi’ke tsaye tare da zuba hannayensa cikin aljihu “ Daga yau na ‘karajin wannan banzan yaran naki ki tabbata sai na mugun sa’ba miki” yana kai ‘karshen maganarsa ya nufi hanyar fita , cikin Sauri bobo ya mi’ke zai bisa uncle yayi saurin ri’ke masa hannu , da French uncle ya furta “ No bobo karka bisa kasan yanzu kana masa magana akanta zai ‘kara nunka mata wani aikin, thank god kad’an ya bata yanxu amma kana sake yin magana zai ‘kara ninkamata and ta riga ta amsa da ace bata amsa bane da abun yazo da sau’ki” , ajiyar zuciya bobo ya sauke cike da tausayinta ya kalli direction d’in da take , suma little da prince gabaki d’aya idanuwansu suka zuba mata musamman little da yake ji kamar yayi kuka, ita kuwa Abla gani take zata iya yi musu ko wana irin aikine tunda har zata zauna a cikinsu, gani take ai aiki me sau’ki tunda simba kawai zata dunga yiwa abinci, ita gabaki d’aya ta d’auka simba mutum ne da zata dinga kaiwa abinci safe zuwa dare sai kuma coffee d’inda zata dinga kaiwa wanda ganintake ba aikine masu wahala ba , abu d’aya ne ya sakata cikin tsoro da damuwa , rashin turancinta sosai tunda ya fad’a idan ta sake Hausa sai ya ‘bata mata , a tausha she little ya furta “ me yasa kika yadda zakiyi aikin nan ?” Murmushi me ciwo kawai Abla ta sakar masa sabida tuna rayuwarta a gidan karuwai da tayi “ wannan ai bame wahala bane na saba yin aikin da suka fi wannan yawa ma “ , shiru little yayi Sabida abinda tace , a hankali ya ‘kara furta “ kinsan wanene simban ?” Itama Abla amaimakon ta basa amsa sai ta ‘kara sakar masa murmushi tana d’aga masa kanta alamar Eh , cikin daddad’ar muryarta ta furta “ Shima ba d’an uwanku bane ?” , sakin baki sukai gabaki d’aya suka zuba mata ido , gabaki d’aya tunaninta ta d’auka Simba mutum ne Kenan , Tashin hankali” cewar prince cikin zuciyarsa , little “ Innalillahi “ kawai yake maimaitawa ganin bata san wanda zata dunga yiwa aiki ba “ shi kansa bobo da uncle sun tausaya mata ganin bata fahimci Wana irin aikine zata dunga yi ba , maganar turanci duk me sau’kine ko su little zasu iya koya mata . abu me wahalar yadda zata dinga kula da simba , ganin lokaci na tafiya sosai bobo ya dakatar dasu gabaki d’ayansu “ let’s it first “ hakan ne kuwa ya faru gabaki d’aya suka nufi dinning , yau babu James Sabida bobo ya hana sa zuwa sabida gabaki d’aya sun fahimci Abla tana tsoran sojoji Wanda dolene ta dena jin tsoransu tunda batasan Inda ta shigo ba . Little da prince ne sukai serving d’insu ba lefi yau ta d’anci wani abun dukda ba sosai ta iya ci ba sai Youghurt data sha sosai . Har suka kammala cin abinci babu Wanda yayi magana , tsakanin little da prince kowa tunanin yadda zai temaka mata yake shiyasa suna kammala cin abincinsu suka Jata zuwa office d’in prince banda bobo shima da ya fita , uncle ma part d’insa ya koma dan babu yadda za’ai su hana big boss , wasu manyan books suka fito dashi duk a ciki zasu fara koya mata turanci, a hankali a hakali little ya fara kowa mata ‘kananan kalmomi Marasa wahala , cikin sau’ki kuwa Abla ta soma fahimta tunda duk abinda ya koya mata sai yayi mata bayanında da turanci yanda zatafi saurin fuskanta.sun fi ‘karfin 2 hours suna koya mata ‘kananun words , suna yi suna janta da hira , kiran sallar azahar ne ya katse musu karatun da suke , yanxu itama Abla ta gane hanyar komawar ta d’akı shiyasa lokacin da suka nufi masallaci itama ta koma d’akin, da ta kulle idanuwanta husky voice d’in Big boss ne yake mata kuwwa cikin kunne, kyansa , muryarsa, da kuma idanuwansa , shine abu uku da ya kasa
’bace mata , gabaki d’aya ita ta manta da zancan kaiwa simba Abinci dan yadda sanyin Acn yake huro mata har wani irin bacci take ji yana fusgarta, ko mintuna 30 batayi ba little ya kwankwasa mata ‘kofa tana bud’ewa ya sakar mata murmushi “ let’s it lunch”, itama martanin murmushin ta sakar masa dan yana d’aya daga cikin ‘kananun abunda suka fara koya mata shida prince “ okay yaya little”, murmushi kawai little yayi mata suka sakko ‘kasa , yanxu su uku zasuyi lunch d’insu, a wannan karan ma little ne yayi serving d’insu , shima abincin kad’an ta ci ganin bazata iya cıbane yasa little d’auko mata fruits masu yawan da zata sha sai kuma Youghurt wannan karan strawberry ya d’auko mata sai da suka kammala cin abincinsu zaku koma falo idanuwan prince ya sauka kan agogo da ‘karfi ya furta “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” da Sauri little ya jiyo ya kallesa , a gogon ya nunawa little shima cikin sauri ya zabura ganin saura 2 minutes 3 tayi , cikin wani irin Sauri ya ja hannunta gudu gudu sauri suka fito daga cikin part d’in , tun kafin su cigaba da tafiya tayi wani irin jan burki da saura kad’an ta fad’i ’kasa sabida yadda taci karo da sojoji ta ko ina , cikin tsananin tashin hankali fara girgiza musu kai jikinta har ya fara rawa lokaci guda Sabida sojojin da ta gani, “ oh my god “ shine abunda little ya furta , zata juya prince yayi saurin dakatar da ita “ No sister , babu abunda zasuyi miki ki kwantar da hankalinki, 3 ta kusa idan baki bawa simba abinci ba da matsla babba , kawai ki kwantar da hankalinki , ina Abla gabaki d’aya ta tsure , so take ta samu hanyar guduwa amma prince na ‘ko’karin tare mata hanya , yadda take mugun tsoron sojoji ko kallansu bata san yi shiyasa a duk lokacin da ta gansu jikinta ya ke d’aukar rawa , ganin sun hanata wucewa ne yasa ta fashe musu da kuka dan Allah kuyi hakuri ni bana san mutanan nan tsoro suke bani , kuyi hakuri dan Allah ni zan bar muku gidan kuma amma dan Allah ku dena kirawo wad’an nan mutanan , shima little cikin Tashin hankali ya furta “ babu abunda zasuyi miki sister ki kwantar da hankali , gida fa kawai suke bawa tsaro kin manta zaki bawa simba abinci by 3 ? Ko so kike yaya big boss ya dawo ? Dan Allah ki nutsu “ sai a lokacin ta d’an dakata cike da tsoro Sabida ambatan Big boss da little yayi amma duk da hakan jira take ace tak ta saka gudu yadda take ganin sojojin nan da bindigu ta ko ina , da ‘kyar da ‘kyar little da prince suka saka Abla ta wuce shima sai da suka sakata a tsakiya sabida yadda tayi mugun furgice lokaci d’aya , tanayi tana wai gan sojojin sabida kar wani ya biyosu, har suka ‘karaso Inda gidan simba yake , ita Abla gabaki d’aya bata san inda suke nufa ba Sabida yadda hankalinta gabaki d’aya yana kan sojojin gidan da take faman bi da kallo cike da tsoro , suna zuwa wajan gidan simba suka tarar da Victor a tsaye hannunsa d’auke da wani bucket da Alama abincine a ciki, anan ma Abla ta so guduwa saida su little suka dunga ro’karta tukunna ta tsaya , hanya Victor ya bud’e musu suka shiga yana gaba suna binsa A baya Daidai d’akin Simba ya ajje bucket d’in tare da tsaya wa , little xai d’auka Victor yayi saurin dakatar Dashi dan umarnin Big boss ne kar a barsu su shiga , little kamar zaiyi kuka sabida yasan dole sister ta firgita da ganin simba tunda ba saba ganinsa tayi ba , kamar zaiyi kuka suka tsaya
Book Chapters
Chapter 29
Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51