You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
yana mugun shakkanta, Hawwa bazata taba iya soyayya da wanda ta girma ba Khaleel kuma
wanda yake ba addininta ba, saikuma na karshe sauran samarinta“ anatse Ammi tace “Ibrahim Hawwa
na can be everything, stubborn, mafadaciya da sauransu amman Hawwa na ba mazinaciya bace! Dudda
ta dade batai aure ba bata taba kallon zina as solution na matsalolinta ba, duk ina maka bayanin nan
sabida ni uwa ce bazanga ana so akashe auren y’ata naja baki nai shiru ba, duka sakon nin nan karya ne
Khaleel koda bakai trusting Hawwa ba trust me ni mahaifiyarta, I will never lie to you kaji”.
Sosai Khaleel yake kallon Ammi natsuwan da tun jiya yakasa samu bayan yaga sakonnin nan sai Ammi
tabashi natsuwan in just few minutes ya yarda and he believed her, gyadama Ammi kai yayi ahankali
yace “I know! Deep down I know my wife is not like this, kawai bansan mesa zuciyana keta zafi yana
radadi ba bayan na karance messages din” yasan inda Hawwa yar iska ce da bazata taba tsanan halinshi
ba, sabida batayi saisa she despise his way of life, dan murmushi kadan Ammi tayi tace “sabida kana
sonta ne saisa kakejin haka!” Tsare Ammi Khaleel yayi da ido jin tace yanason Hawwa bayan shi yasan
baya sonta he just wants to show her he can have her idan yanaso, ahankali Ammi tace “Khaleel aure
dole agina foundation da trust, you have to trust matarka, itama matarka have to trust you, ta hakan ne
zaku iya strengthening bond naku ta yanda babu any makiyi dazai iya zuwa ya jijjigaku kaji” gyadama
Ammi kai yayi ahankali Ammi tace “tashi kaje gida kai wanka Ni’ima zanje har gidansu naga
mahaifiyarta” gyadama Ammi kai yayi baiso yagayama Ammi what he’s planning dan zata iya hanashi
but Ni’ima zatasan she messed with the wrong person this time, tashi yayi yawuce haryakai kofa
saikuma yajuyo hada ido sukayi da Ammi kai yadan sosa yana sauke idanunshi kasa ahankali yace “thank
you Mom for guiding me” yana maganan yawuce yafita Ammi tai shiru tana kallon inda yabari saiga
hawaye ya sauko daga idanunta daidai Malam na zuwa zauren ahankali Ammi tace “Malam ina alfahari
da wannan miji dakama Hawwa hakika Hawwa tai sa’a! Hawwa tai dace” ahankali Baba cikeda damuwa
yace “nagode Zainabu da babu ke da bansan yanda zanyi handling issue din nan ba, me Ni’ima ta turo a
sakon”? Karantama Baba sakon tayi tass sannan suka tashi suka wuce dakin Hawwa tana zaune ganinsu
yasa ta tashi ta taho wajen Ammi tace “Ammi wlh ita tazo wajena an off…….” Tassss! Ammi ta yanka
mata mari mai kyau da lafiya Baba yace “nagode Zainabu!” Hawwa ta dafe kuncinta dasauri, wani irin
feeling Ammi keji aranta, irin after much struggles da wahala da kata katan rayuwa da gori, habaici
maganganun banza, gulman makota da mutanen gari, kasamu ka aurar da diyarka wata yar iskan kawa
na kokarin kashema yarka aure, cikin murya mai rauni Ammi tace “Hawwa magani Ni’ima tabaki a abinci
kikaci da bazaki iya rabuwa da ita ba ko me? What did I tell you about that girl ranan nan? Ni da
mahaifinki nan mun gayamiki Ni’ima bata kaunarki kona miskala zarratin, ta tsaneki, kukanta kukan
mazuru ne, kukan karyane da yaudara, so tabiyoki jiya office kika bari tazo, kinsan cewa Ni’ima ta dauki
wayanki a sace ta kwashi number mijinki?” Hawwa dake dafe da kuncinta tana kallon Ammi da mamaki
tabude baki in disbelief, tace “Ammi karya yamiki kawai ya tsani Ni’ima ne” “kinci mai garinku Hawwa
kaniyanki” Baba yamata dakuwa yatsunshi kaman zasu shiga kwayan idanun Hawwa yace “mijinki kike
kirada makaryaci”? Sauka kanta tayi kasa ahankali, Ammi tace “ta aikama Ibrahim sako cewa DIG oganki,
Abraham da duk duka samarinki dasuka gudu jikinki kike basu suna amfani dake” dawani irin sauri
Hawwa takalli Ammi, Ammi tace “tayi amfani da wayan masu bara jiya at exactly 2:15 ta tura” shiru
Hawwa tayi basu wani dade da rabuwa ba aka tura sakon, Ammi tace “he tracked the number masu bara
sukai kwatancen ta da motarta you are lucky bai sakeki ba Allah yaga zuciyanki yabaki miji mai sonki da
tsaya miki haka” Ammi ta nuna kanta tace “idan har ni Ammin ki Zainabu na kai mahaifiyarki na isa dake,
dagayau namiki iyaka da Ni’ima baki ba ita! Ko wayanta kika kara dauka ban yafemiki ba Hawwa!” Sosai
Hawwa ke kallon Ammi, Baba yace “nima idan na isa nakuma kai matsayin mahaifi agareki namiki iyaka
da Ni’ima har abada! Ni’ima bata kaunarki! Ta tsaneki, bakin ciki take dake, idan Ni’ima tasami hanyar
kasheki zata kasheki Hawwa, dan haka bassss! Bassss! Enough! Bake ba ita, da raina bazan bude idanu
inga kawa na neman kashema y’ata auren da ba’a riga an kai daki ba, tundadai an baki hutu awajen aiki
dagayau na ijiye dokan kada ki kara fita daga gidan nan unless shi mijin naki ne yazo yanaso yafita dake,
sa hijabi muje gidansu Ni’ima Zainabu”.
[10/6,
7️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣7️⃣
5️⃣
Koo kadan jikin Hawwa ba karfi jin abubuwan da su Baba suka fadi, dafe katifa tayi tazauna ahankali tai
shiruuu tana tunani, duka abubuwan da Ni’ima tamata abaya she kind of give her excuse sabida Aliyu
duk shi yaja da sauransu, so tasan ba kowa ya iya handling kishi ba, kuma tasan yanda Ni’ima ke mugun
son Aliyu, so tamata excuse dudda she goes as far as tana zagin iyayenta tana tonamata asiri, but this!
Yaushe ta dauki wayanta harta dauki number Khaleel dabatai saving ba? Takasa yarda still, kodai
Khaleel sheri yayi mata da karya sabida ya tsaneta? Sai kawai ta tashi da sauri ta dauki wayanta takira
Abraham ringing daya ya dauka tace “Abraham I remember kataba cewa kasa wani invincible CCTV
camera an office dina right?” Dasauri yace “yes Miss Hawwa” ahankali tace “can you send me footage na
jiya at about 1Pm zuwa 2pm” Dasauri yace “sure give me 3mins” ta katse wayan ta zauna tana kada kafa
she really don’t wanna believe Ni’ima did all this dasu Baba suka fadi noo! Ni’ima tai nadaman
everything datayi abaya, she’s a changed person, kishin Aliyu yasa tayi all those things ada.
3min basu cikaba Abraham yaturo mata video ta watsapp dasuri tashiga downloading yana gamawa
tabude dasauri tashiga kallo gabanta na mugun faduwa tana cewa kanta No No Ni’ima can’t do this to
her, aiko saiga Ni’ima na daukan wayanta tana daukan number tana kallon kofa atsorace, wani irin
runtse idanu Hawwa tayi murya araunane dake cikeda mamaki tace “Ni’ima!” Ijiyan zuciya ta sauke ta
fuzar da iska mai dumu ta ijiye wayan a gefe, she’s really hurt dudda bataga text dinba but for Ammi to
slap her this hard that means she said alot tabata mata suna, dole Khaleel yaji ba dadi zaiga tana
crucifying nashi on something da itama tanayi, fuzar da iska tayi bataso tayi kuka akan Ni’ima yau but
zuciyanta namata wani iri kaman ma idan tai kuka zaifi rage mata zafin dayake mata yanzu.
Hawwa na zaune a wajen idanunta sunyi ja almost 1hr dafitan su Baba da Ammi taji ana bude kofanta
dasauri tadago kai, ganin Khaleel again saida gabanta yafadi da sauri taboye wayan dake hannunta na
video akasan bedsheet sabida karya ga video, yana shigowa babu wata wata kawai yazo inda take zaune
tana kallonshi, hannunshi yasa yakamata yadagata yajata turjewa tayi tace “stop touching me ina zaka
kaini kuma”? Cikin bacin rai Khaleel yace “i want to show you wacece wacce kikai considering as true
friend” kawai yajata takalmi tasaka sukai waje takasa kwace hannunta Salman yabude musu bayan mota
ita tafara shiga sannan shima ya shiga aka rufe motan aka ja, to her biggest suprise hanyar office nata
taga sunyi, dasauri takalleshi tace “ina zaka kaini?” Banza yamata yaki amsata har office nasu, parking
yayi yana rikeda hannunta suka wuce ciki har zuwa office na DIG kai tsaye Khaleel yabude office din
batare dayama yi knocking ba, DIG Hawwa tagani tareda Abraham duk zaune, DIG na ganinshi da sauri
DIG yatashi yace “Mr Ibrahim I……” hannu Khaleel yadagamai strictly yace “did you bring her here yes or
no?” Rai abace DIG yace “not just she duk ma wani wanda ke gidansu cus I will never take this
defamatory statement likely” yakalli Abraham yace “bring everyone in” wucewa yayi yafita chan saiga
wasu manyan yan sanda guda biyu sun shigo da Mama da Ammi sai Baba da Ni’ima dake sanye da
doguwan rigan atampa dukansu sunyi zuru zuru dan duk suna zaune suna magana agida wasu yan sanda
sukazo sukace ana inviting nasu to police station dukansu haka suka taho, Baba na ganin Khaleel da
Hawwa yace “Ibrahima me kukeyi anan? Munje gidansu yarinyar nan ana cikin magana saiga yan sanda
akace muzo chaji opis” ahankali Khaleel yace “nina turasu Baba” hannun Hawwa yasaki gently yasa
hannu ya karbi karafunan Baba ya zaunar dashi a kujeran wajen yakalli Ammi yace “Mom sit” zuwa
Ammi tayi ta zauna, gaban Mama dana Ni’ima suka shiga bugawa especially gaban Ni’ima dabatasan
meke faruwa ba gabanta sai fadi yake cus su Baba dasukazo cewa sukayiwa Mama basuson yarta tareda
Hawwa basuce komiba, kawai faduwa gabanta yake dudda bata kawo text messages na jiyaba dan
batajin za’a iya gano ita bane, Hawwa takalla cikin makirci tace “Best is everything okay? Why did you
call us here”? Wani daci Khaleel yaji aranshi yanda take kiran matarsa wani best azafafe yace “wlh kika
amsa that beast sai ranki yabaci” yafadama Hawwa dake kallon Ni’ima jikinta yagama sanyi da Ni’ima
sosai, faduwa gaban Niima yayi itama Hawwa tadauke kai kawai Ammi saitaji wani son Khaleel ya
lullubeta.
Anatse DIG yakalli daya daga cikin yar sandan mata dake taredasu Mama, ba zato ba tsammani Ni’ima
taji saukan bulalaaa akafanta dayasa kawai ta zube akasa tace “wayyooo Allah na” dasauri Hawwa ta
juyo jin karan bulala da dukan Ni’ima, Yar sandan tace “mai laifi kneeling yakeyi ba tsayuwa ko zama ba a
police station” rawa jikin Mama yafara dasauri ta duke itama kusa da yarta, DIG yakalli Ni’ima da
kafafunta ke bari sabida zafin wayan inji yace “kece Ni’ima?” Gyadamai kai Ni’ima tayi tace “eh yallabai
nice” gyadamata kai yayi yace “an shigo da karanki office dina daga Mr Ibrahim akan kinyi defaming
matarsa, dakuma ni, da yaron aiki na” yanuna Abraham dake tsaye ransa abace yana kallon Ni’ima, DIG
yace “No body ya isa yabata min suna, idan kowa na dakin nan yabarki ni bazan barki ba!” Faduwa sosai
gaban Ni’ima yake tace “yallabai bantaba ganin ka bama, saidai wanchan na sansa ta dalilin Hawwa
amman me dalilina dazaisa nabata maka suna wani sherin aka kulla min ne? Best something yafaru ne”?
“stop calling matana da Best!” Khaleel yafada aharzuke kowa ya kalleshi har Hawwa dasauri dan kaman
zai rufe Ni’ima da duka, DIG yace “calm down Mr Ibrahim” rike kansa Khaleel yayi kirjinshi na tafarfasa
yayi punching air, DIG yace “jiya wuraren 2:16 kin tura sakonni marasa dadi zuwa wayan Mr Ibrahim”?
Faduwa sosai gaban Ni’ima yayi ta zaro idanu tareda dafa kirjinta Mama na kallonta hankalinta atashe
Ni’ima tace “Yallabai an ina zan sami number sa har na turamai sako? Ni kuma? Sheri akamin” Dan
murmushi DIG yayi yakalli Abraham yace “play the first evidence” saramai yayi yace “yes sir”.
[10/6,
8️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣8️⃣
5️⃣
Wucewa Abraham yayi yana connecting laptop nashi to office television sai kawai ga video Ni’ima sanda
take kwashe numbers daga wayan Hawwa, Hawwa na kokarin shigowa ta ijiye wayan da gudu, Mama
tace “na shiga uku na lalace Ni’imaaaa” yanda kirjin Ni’ima ke rawa zaka dauka an sokashi da electricity
ne, Hawwa ta tsareta da idanu just looking at reaction dinta, Ni’ima da sauri ta kalleta tace
“Bes…..Hawwa I can always take anything daga wayanki, baki tabamin shamaki da wayanki ba, kaman
yanda ban miki da nawa ba, ba lallai number Khaleel na dauka ba ai, abinda na kwafe daban fa number
Ammi na dauka inaso namata sako na bada hakuri naga bata hakura ba” Baba yace “shegen karya
kaman bokanya! Yau za’ayi maganin ki” DIG yadagama Baba hannu Ammi tace “kai shiru Malam” Baba
yace “raina sosuwa yake ne Zainabu Amman nayi” DIG yace “bring in the second evidence” fita yan
sandan sukayi chan sai gasu sun shigo da beggars din nan su biyar duk jikin su na rawa, Ni’ima jikinta
yafara bari sosai data gansu, Hawwa kawai saitaji Hawaye yazo idanunta zuciyanta ya tsinke ganin
reaction na Ni’ima so ita ta tura text din, DIG yace “zaku iya nunamin acikin dakin nan matar datazo tayi
amfani da wayanku jiya bayan karfe biyu” dawani irin sauri dukansu sukai wajen Ni’ima dake susunnar
dakai suna cewa “gata nan gatanan itace tabamu dubu biyar bayan tagama” DIG yace “fita dasu a
sallamesu” sutafi ficewa dasu akayi.
Ni’ima jikinta yahau rawa, in her wildest dream bata taba tunani abinda tayi jiya will backfire like this ba
before 24hrs like this is just 11 na safe, tadauka ma dazu dasu Ammi sukazo sunzo suce an fasa auren,
Khaleel ya saki Hawwa ne fa, sai kuma taji suna magana kan arabata da Hawwa. Dasauri Ni’ima tashiga
jan guiwa tafashe da kuka tana zuwa wajejen da Hawwa take tace “Hawwa wait I can explain, wlh wlh
sherin shedan ne kuma harda naji haushi dakika ki kiramin Baban Yaseer…………” Tasssss! Aka dauketa da
mari da saida ta kwanta flat akasan wajen tanaji kaman kunnenta yafita, Hawwa takalli Khaleel daya
sauke mata mari yana huci da mugayen idanu tama kasamai magana, Mama ta dago Ni’ima dasauri
dataki dawowa daidai tana jijjigata, DIG yataba kansa yana kallon su Baba da Khaleel yace “Baba, Mr
Khaleel ni mahaifine, dudda ban haifi kaman Hawwa ba but I have a daughter of 24yrs, ni father figure
ne all mata na office din nan I consider them y’ay’ana, bazan taba having wani abu dawata ba, an sanni
my record is clean, mata basa gabana, matana daya aduniya rak 25yrs of marriage, as for Abraham data
kira sunansa zan iya tsayawa Hawwa in tsayama Abraham, Hawwa y’ace da kowa a office din nan fara
tundaga yan gate sunsan tanada kamun kai, infact Hawwa itace one officer namu da baka ganin
murmushinta anyhow! This is police station fa kace zaka bama wani kanka ai saika dawo abincin kowa,
the only relationship between Hawwa da Abraham is strictly work and will always be work!” Yakalli
Ni’ima dake kuka sosai tadawo daidai yace “zanyi maganinki dagayau zakisan akwai freedom of speech
but shin akwai freedom after the speech? Zan barki da question din dazaki amsa kanki da kanki daga
baya” wasu takardu yashiga signing gaban Hawwa yashiga faduwa sosai ganin stamp din daya daga
dasauri tace “Sir!” Atare daga DIG har Khaleel suka mata ihu. “Wat!” Dan kowa ransa abace yake, Ni’ima
Hawwa takalla dake kuka sosai sannan takalli DIG ahankali tace “Sir tun dazu nasa Abraham yaturomin
CCTV footage na office dina nagani, I knew ita tamin, I already have it a heart dina is over between us na
bar Ni’ima har abada, amman dan Allah Sir karka turata prison, she’s a mother, banda haka ita ke kula da
mahaifiyar ta, karka turata prison kaji Sir” wani kallo Khaleel kema Hawwa kaman ya dauketa da mari
yakeji hakama Baba da Ammi tahanashi magana amman kana ganinsa kasan ashar yakeso ya durama
Hawwa, DIG ransa abace yace “idan ke kadai tama laifi saiki yafe mata, this lady tayi making so much
accusation ciki harda process na promotion namu tai mocking, she played with my name! I! Ni DIG! Da
ma’aikatana You and Abraham my asset, government asset! Hawwah zan wurgata gidan yari tai kaman
1month kafin law yayi taking cause nashi, ashiga kotu abata proper punishment na defamation of
character na mutane uku datayi, gidan yarin nan dazata zauna na wata daya punishment ne na ambato
sunayenmu wanda nine nake mata shi kafin punishment na asalin law” daga Mama har Ni’ima fashewa
da kuka sukayi jin abinda DIG yace, Mama tace “yallabai amata rai, amata rai, kumin rai nima, namuku
alkawari ko hanyan da Hawwa zatabi Ni’ima bazata karabi ba Billahil Azeemu, dan girman Allah kuyakuri
sherin shedan ne” mtsww DIG yayi tsaki yawani buga stamp a paper dayasa Hawwa tace “noooooo” DIG
yamikama yar sandan takardun yace “akaita prison now now ku jefar da ita” Ni’ima tarungume Mama da
karfi tana ihu sosai. “Mama Mama karki bari su tafi dani, Mama na shiga uku na lalace, Mama karki bari
su tafi dani, Hawwa, Hawwa kiyafemin Hawwa is me fa, kiji tausayina Hawwa, kimin rai, kituna su Yaseer
da Yasmeen, Hawwa tare muka girma, muka taso and did everything together, Hawwa tundaga Abuja
nataso nazo kano graduation ceremony dinki na yar sanda ko Baba baizo wajen ba sai ni sai Ammi”
Afusace Baba yace “sabida kafana ne banje ba badan banso najeba kinji makira mai bakin hali,
annamimiya algumguma, shi ramin mugunta dama kurarre ne idan baka hakashi ahankali ba kaine ke
fadawa cikinsa, gashinan ai abinda kikama kanki, kinso kashe ma y’ata aure amman kalli kece kika kwana
ciki, wannan saiya zama darasi da ishara agareki, adinga sara ana duban bakin gatari, kikaje gidan yari
kiyita tofama kanki da Alhamdu ko Allah zai yaye miki bakin cikin nan, da kishi, da hassada azuciyanki
kinji makir……” muryan Hawwa na rawa sosai tace “Babaa!” Shiru Baba yayi Hawwa ta share fuskanta
Ni’ima tabata tausayi, bawai sabida tana sonta or anything ba as a human being kawai tana tuna
yaranta, ahankali muryanta na rawa tace “Sir Ni’ima made a mistake okay, wlh nabarta har abada No
more friendship amman please don’t send her to prison” DIG ya dauke kai kaman baijitaba, saikawai
tajuyo takalli Khaleel idanunta sunyi jaa sosai cikin raunin murya tace “dan Allah Khaleel kayakuri
please” dauke kai yayi tareda juya mata baya, zagayowa Hawwa tayi ta gabanshi takasa daurewa tafashe
da kuka tana kai hannunta ahankali ta kama hannunsa tace “if you loook at it she lost everything
already, yara, aiki, the only thing takeda shi is her freedom please Ibrahim don’t take it away from her,
do it for the sake of two innocent yaranta for her kids and her poor Mom look at her” tanunamai Mama
dake kuka gwanin ban tausayi, gabaki daya zuciyan Hawwa yayi breaking ta kankame hannun Khaleel
tana kuka tace “please Khaleel, I know you are a good man kaji” zuciyan Khaleel na kuna ganin yanda
Hawwa ke kuka yana kallonta yace “this crazy woman defame you! Haryau akwai tabon data miki a
hannu, she almost killed you at the hospital! She insulted Baba! Ta zagi Mom, she booed you! She called
you whore Hawwa! Takirana matana karuwa kai!” Khaleel harwani jijiya ke fitowa agoshinsa kawai yama
Hawwa ihu yace “tayi maganganun banza akan matata! My wife! Zuciyana is not as good as naki i will
not forgive her! She will pay for abinda tamiki all of it, nooo bazan hakura ba bazany……….” Hawwa bata
taba sanin willingly zata iya rungume Khaleel ba sai this moment kawai rungumeshi tayi tashige jikinshi
Khaleel yakasa karasa maganan dayake yi, tai placing fuskanta a wuyanshi tafashe da kuka mai tsuma
zuciya akuma hankali ta yanda shi kadai da itane zasu iyaji, kowa ya sauke kai daga kallonsu a office din
ganin yanda Hawwa tai hugging mijinta, cikin murya mai bala’in rauni dake shesheka awuyanshi Hawwa
“Pleaseeeeee Husbyyy!” Wani irin automatic mutuwa jikin Khaleel yayi, Hawwa tace “dan Allah kayakuri
kaji My Ibrahim Khaleel! Kanada sunan daya daga cikin annabawan Allah, show mercy, ina matarka
bazan iya rokonka abu kamin ba”? Tafashemai da kuka dakawai yaji jikinshi na sanyi, gently yadago
hannunsa shi yadaura kan bayanta yashiga patting yana moving hannun up down abayan ta, murya chan
kasa yace “there’s nothing bazan iya miki ba, okay stop crying now” gyadamai kai tayi gently, yakalli DIG
still holding her yace “for the sake of my wife that pleaded on her behalf tayi one week a prison din
daganan i will decide idan zanyi charging nata to court ko zan yafemata” Hawwa tadago kanta dasauri
zatai magana Khaleel yace “kome zaki cemin idan kinga dama ma kihada da kukan jini this is the least I
can do, taje tayi kwana bakwai gobe ta kara gwada messing da matana taga abinda zan mata from now
duk wanda zai tabaki must have to go through me” yan sanda suka shiga bambare Ni’ima daga jikin
Mama tana ihu tana kiran Hawwa akai waje da ita Hawwa zata bita Khaleel yarike mata hannu tana kuka
sosai yawuce da ita su Baba suka tashi da Ammi suka bisu abaya Mama aka barta tana kuka awajen.
Agabansu aka jefa Ni’ima dake ihu cikin motan da akekai mata gidan yari, Hawwa sai kuka take taji
tausayin Ni’ima, Ni’ima tabata tausayi, suke suka wuce suka shiga mota Khaleel na rike da Hawwa data
kasa daina kuka abin tausayi.
NI’IMA TABANI TAUSAYI HARDA DAN KUKANA😭
[10/6,
0️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣0️⃣
5️⃣
Har tsakiyan kanta Hawwa taji kanta yafara kararrawa bell ringing tafara gayama kanta is Khaleel, Pops
boy kemiki all this abubuwa, karfi taji yazo mata yana kokarin taba boobs nata ta iya daga hannunta
takama hannunshi tarike gam, Khaleel ya kalleta da idanunshi da sun kankance, kasa magana Hawwa
tayi sai kallonshi datake tarike hannunshi gam kirjinta na bugawa ba kakkautawa, murmushi Khaleel yayi
kaman karya barta ta tafi haka ya keji sai kawai yayi hugging nata so tight batare daya karbe hannunshi
data rikeba, sugar jikin Hawwa tayi yana mata wlh, kawai zaki jikinta keyi addu’a tashiga yi takasa
tureshi,
bakinshi saitin kunnenta cikin mugun tsokana yace “if Lee wants to have Kulu he will have Kulu can you
see that now? I can shut you up anytime naga dama, I’m not just any regular bad boy, I’m a bad police
officer’s boyfriend, I’m dating you! We are couples! Remember Khaleel can have any woman daya ga
dama you’re no difference” dagata yayi ahankali yakoma yazauna agefe bangon wandonshi yatashi
harda na bala’i amman ko kokarin boyewa baiyiba yakama hannunta yadauki paper bag din yasa aciki
yace “you can go girlfriend Kulu” dasauri Hawwa tabude kofan tafice jikinta kaman ba nataba tana tafita
kaman zata tashi yabita da kallo saida yaga ta shiga cikin gida sannan yabuga kofan Umar ya shigo yaja
motan suka fice yana kallon gaban shorts nashi dake atashe yaja yar gajeren tsaki he’s so horny sabida
yanajin nauyin Baba ne da wlh saiyaci yarsa a kofar gidansa.
Sosai gabanta ke faduwa, what just happen now? How was that boy able to shush her up? What is the
meaning of abinda jikinta yamata? Ahaka ta shiga gidan Ramla ta taho da gudu tace “Ya Hawwa kinga
shopping danayi dayawa harke nasayoma abu kuma bodyguard dinshi baicemin ya isa ba har Baffa na
nasaima abu shine yanzu Ammi kemin fada wai yayi yawa” kirjinta har lokacin bugawa yake tadaiyi
murmushin yake da kyar Ammi dake daki tace “Hawwa!” Dasauri Ni’ima dake zaune da Hawwa bata
lurada itaba tace “Hawwa!” Dasauri Hawwa tajuyo takalli Ni’ima jin muryanta, kusan 20secs Hawwa na
kallon Ni’ima itama haka Ammi taleko daga net ranta abace tace “Hawwa bakiji ina kiranki bane” firgigit
Hawwa ta kalli kofan tace “toh Ammi gani nan” tai wajen kofan kai tsaye daidai zata bude ta shiga Ni’ima
takama hannun Hawwa tarike gam cikin wani irin murya mai rauni tace “Hawww…….waaaaa!” Kawai
hawaye Hawwa taji sunzo idanunta tadai daure tahanasu zubowa takalli Ni’ima data rike mata hannu
tace “yanzu kuma mena miki Ni’ima kikazo nemana?” Daidai lokacin Baba na bugo sallama yana shigowa
tareda Aminu suna hira ganin Ni’ima tarike hannun Hawwa yasa ya kirne fuska suka kame awajen, cikin
sanyin murya dake nuna nadama Ni’ima tace “Hawwa banda words to justify whatever I did to you and
your family, Hawwa bansan meya shigeni ba, I couldn’t believe nine ke yunkuri inacewa zan kasheki da
gaske kaman aka banni zan iy…..iya….” Muryanta yashiga rawa takalli Ammi dake kallonta ta kofa tajuya
takalli Baba tace “nama magabatana kuma iyayena maganganu marasa dadi I’ve lost everything, Hawwa
Baban Yaseer yasakeni tun ranan hospital din nan ina gidanmu har yau” ahankali Hawwa ta kalleta
tausayinta na ratsata da rashin jin dadin news din, gyadama Hawwa kai tayi Ni’ima tayi ganin taga
tausayinta akan idanunta yasa cikin sanyin murya tana kuka tace “ya kwashe yaranmu bansan ina
yakaisu ba nakira school ance basa zuwa” tafashe da kukan damu da rashin gata Hawwa taji zuciyanta ya
tsinke awani irin hankali Ni’ima tace “yau an koreni daga wajen aiki Leadway sun tura video abinda
namiki to NMCN anyi revoking license dina! My hospital fires me” Runtse idanu Hawwa tayi she knows
what nursing means to Ni’ima, shine kadai profession datake so aduniya, cikin muryan kuka Ni’ima tace
“idan bakiso nakashe kaina Hawwa ki yafemin ki manta da abinda namiki komi yawuce I’m sorry, I’m
really very sorry” tafashe da kuka sosai zatai kneeling da sauri Hawwa takai hannunta ta tareta kaman
abinda Ni’ima ke jira kenan ta shige jikin Hawwa ta rungumeta ta kankameta tana kuka Hawwa ta tsaya
turus paper bag dake hannunta yafice yafadi akasa idanunta suka cicciko da hawaye dago idanunta tayi
tahada idanu da Ammi data mata mugun kallo kawai tasaki labule takoma cikin daki abinta, Baba ma
yakada kai yajuya rai abace kawai yayi zaure Aminu yabishi, kaman jira Hawwa take tasaka hannayenta
abayan Ni’ima ta hugging nata back murya chan kasa tace “it’s okay stop crying ya isa, kinsan anytime
kikai kuka haka yana saki ciwon kai”
Book Chapters
Chapter 24
Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33