You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kira ko dai kunnena ne jama'a? Sanisa dai da duka muka sani?" Cikin kuka Badiyyah tace "Wallahi ita ce ta hada mu, Malaminta ne shi yake mata aiki a Zaria" Salati Mama Ladi ta saki bayan ta ajiye maficin hannunta tana tafe hannu cikin kidimewa tace "Malaminta kuma?" Maheer kam kallon Badiyya kawai yake babu ko kiftawa kamar yanda Abba da Usman dake tsaye bakin kofa ma suke kallonta, Cikin rawan murya Badiyyah tace "Dama bayan an fasa auren Mayraah nace mata ina son Musharraf din ya dinga kulani, shine ta hadani da malamin wai ya iya aiki, shikenan mu ka fara waya da shi na fara tura masa dubu hamsin sai watarana yace in je Zaria zan amshi wasu turarruka da zan dinga amfani da shi, ni kuma sai nayi ma Hajja karya zan je Bichi sai na tafi Zaria wajensa" Tana kai wa nan ta kara rushewa da kuka, Mama Ladi dake ta zare ido tace "Sai aka yi yaya?" Cikin kuka sosai Badiyyah tace "Wallahi ni ban taɓa iskanci ba Haseenah ce ta hadamu da shi, kuma yace min shi ne ma yayi mata aiki har ta auri Ya Maheer, sannan ya bata asiri da ta kai dakin Ammi wai don Ammi taji ta tsani Mayraah, ita ma kuma ai tana zuwa wajensa a zaria sai da tayi aure ne ta daina zuwa wajen sa" Mikewa Mama Ladi tayi ta dafe gwiwa tana kallon Hajja da hawaye ke sauka ta gefen idonta tace "To Allah ya sa dai kunnuwanki basu samu matsala ba kina jin duk abinda marainiyar ki ke cewa, mu dai sai dai mu ce Allah ya isa lalata mana zuri'a da za ayi da shege, yau ga dai Badiyyah da cikin boka" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta rike kanta, Ammi ma kukan take sosai wani bakin ciki da takaici na taso mata a zuciya, ita dai Aunty Mariya shock ya sa ko motsi ta kasa yi a inda take zaune sai kallon Badiyyah take, shi kansa Abba kallon Badiyyah kawai yake ko kiftawa babu, can ya girgiza kai ya mike kawai ya fita daga parlon, Usman ya juya ya bi bayansa, Maheer ya kusa minti biyar tsaye parlon da tunani iri iri a ransa, can ya nufi kofa ya fita shi ma, Ammi ta mike ta bi bayansa da sauri har a sannan tana kukan takaici, tsayawa yayi har ta karaso inda yake cikin rawan murya tace "Yanzu Maheer ta yaya za ayi a cire cikin nan? Ya za mu yi yanzu ya fita Maheer?" Da mamaki Maheer ke kallonta yace "A cire fa kika ce Ammi?" Ta fashe da kuka tace "To me zance Maheer? da wani ido za mu kalli duniya? Wannan abun kunyar har ina Maheer? Badiyyah ta cuce mu, ta cuce mu wllh" Maheer ya girgiza kai yace "Ai in ma wani ya kawo shawaran a cire cikin ke me hanawa ne Ammi" Muryar Mama Ladi suka ji da karfi tana cewa "Ashe baki da kai Ammi? Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka bane? Wani cikin za a cire? So kike Allah yayi fushi da kaf zuri'ar mu? Ga laifin zina sannan ga na zubar da ciki, to wallahi babu ruwana sai inyi ta kaina in fita daga zuri'ar nan in shiga duniya kamar yanda Mera tayi, babu zunubin shegiyar da zai shafeni ban ji ba ban gani ba, ai tunda taje ta yo cikin dole sai ta haifesa a ba Hajja ko kuma a baki ku yi raino don nasan Mariya bazata amsa ba, ni ma kuma ba ruwana wallahi, da ana canza ma tuwo suna wallahi a yau din nan da na canza pamily bakina alekum na koma wani pamilyn, yanzu zancen da nake maki wllh kunyan Mamuda nake ji tun dazu na kasa hada ido da shi" Ammi dai kuka take ta kasa cewa komai ta nemi dakali ta zauna, Maheer ya fita daga tsakar gidan kawai, a kofar gida ya tadda Abba tsaye alamar dai lamarin nan ya girgiza sa ba kadan ba, shi dai Usman na tsaye jikin gate din gidan har sannan bai ce komai ba, shi fa bai yi mamaki ba ko kadan yasan akwai ranan da za a zo wanna gaɓar in har Hajja ta ci gaba da biye Badiyyah to gashi nan kuwa an zo, Abba na kallon Maheer bayan ya fito yace "I won't decide for you Maheer, duk hukuncin da kaga ya kwanta maka a zuciya game da matarka zaka iya yankewa but... Ka tabbatar baza kayi hakan ba sai kana da kwakkwaran hujjoji da zaka gabatar ma danginta don Badiyyah ba abun yarda bace, a yau na gama sarewa da lamarinta sannan na zame hannu a duk wani abu da ya shafe ta babu ruwana, sannan zan gaya ma mahaifiyarku daga yau bana son Badiyyah ta sake takowa cikin gidana" Abba na kai wa nan ya shiga motarsa ya wuce. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba tana azkar dinta idonta a lumshe ta jingina da bango, wayarta ne ya fara ring ta bude ido tana kallon wayar cike da mamakin wanda ke kiranta by this time, Dr Khalil ta gani jikin screen din, ta sake duba agogo taga karfe shidda, picking call din tayi ta kai kunne hade da sallama, ya amsa yace "Good morning, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah, ina kwana" yace "Lafiya lau, i just want to let u know ba sai kin shigo hospital yau ba MD na da meeting, but just make sure karfe tara na yi ki tafi gidan Ummi mu hadu a can" Mayraah ta ɗan yi shiru, yace "Are u there?" A hankali tace "Eh ina ji" Yace "Good! Zan kira in ji ko kin tafi anjima nima sai rana zan shiga asibitin" Tace "Toh" Katse wayar yayi ya juya yaga Zainab tsaye kansa tana masa wani kallo, bai ma san ta fito parlorn ba, a fusace tace "To kar ta kuskura ta sake kai kafarta gidan mahaifiyata don wallahi zan mata rashin mutuncin da bazata taba mancewa a rayuwarta ba, ka nemi wani wajen da zaka kai ta amma in har tayi mistake din zuwa gidanmu yau din nan to zata ga ikon Allah, halan ita arniya ce da bata da iyaye har zata shigo garin Abuja namiji ya dinga accommodating dinta, kuma ko bata da iyaye ai bazata rasa yan uwa ba ko yawon bariki ta shigo yi a Abujan ne dama" Dr Khalil dai kallonta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, tace "Naga rainin hankalin ya kai rainin hankali yanzu, wato har kiranta kake da asuba ka gaya mata kar ta ma je asibiti saboda baza ka je ba, duk kwanan nan dama ina ta lura da take taken ka, ga wani gidan Ummi da ka tsiri zuwa kullum tunda ka kai ta can, an mayar da ni wata shashasha to my patient is finished, kuma ka sani babu yarda tsakanina da kai yanzu" Ya mike tsaye yace "Listen Zainab...." Ko sauraronsa bata tsaya tayi ba ta wuce daki kamar zata tashi sama, ya sauke ajiyar zuciya bai ma san yanda zai mata bayani ta fahimci babu komai tsakaninsa da Mayraah ba sae Kasancewarta er uwar sa musulma da baxai so ganin ta fada halaka ba, gani yayi ta fito daga daki da akwati kamar dama ta hada akwatin ta ajiye gefe abinda take jira kenan, da mamaki yace "Ina zaki Zainab?" Ko tsayawa bata yi ba ta bude kofa ta fice daga parlon, ya kalli dakin da twins dinsu ke ciki suna bacci, komawa yayi ya zauna don yasan ko ya bi ta tunda har taki tsayawa a nan ta sauraresa to a wajen ma bazata sauraresa ba sai ma dai kawai su tona ma kansu asiri, he definitely knows ba gidan Ummi zata ba gidan Aunty Rabi'ah zata dama ita ke zugata always. Tara da yan mintuna Mayraah ta fito daga gida bayan Dr Khalil ya sake kiranta yace kawai ta taho asibiti ba sai taje gidan Ummi ba kuma, wajen karfe sha daya ta shigo asibitin ta gaisa da nurses din da ta gani reception ta tafi sama zuwa office dinsa, hijab ne jikinta bata saka uniform ba, zaune ta samesa office din da twins dinsa sun cika sa da surutu shi kuma yana ta aikin gabansa, tun da ta hadu da su a supermarket ranan bata sake ganinsu ba sai yau don bata taɓa ganinsu gidan Ummi ba, ko kilan an kai su bata nan bata sani ba, ta karasa tana murmushi tana kallon kyawawan yaran tace "Su ma sun zo aiki yau ne Dr?" Shi dai kawai yayi murmushi yana ci gaba da abinda yake yace "Ya hanya?" Tace "Alhamdulillah" tace "Ya sunansu?" Yace "Fatima and Khadija, ana kiransu Ashnaah and Ashfah" Tace "They are so cute" yace "Dama zan fita, ke nake jira so u can stay with them here" Mayraah tace "Ohk, Maminsu fa?" Yace "Bata jin dadi ne" Mayraah tace "Toh Allah ya sauwake" Yace "Ameen" Yana kallon girls din yace "Za ku zauna tare da Aunty zan je in dawo yanzu kun ji? Ga cartoon zan kunna maku sai ku yi kallo, do not disturb Aunty" Ashnaah da Ashfah suka kalli Mayraah a tare, dukawa tayi tana masu murmushi ta kamo hannunsu tace "Hello cuties, yanzu Daddy zai dawo, i will keep u company" Dr Khalil ya dau makullin motarsa bayan ya sa masu cartoon a tv dake office din ya kalli Mayraah yace "Ga cornflakes dinsu da abinci a jaka if they need" Mayraah tace "Ohk" fita yayi daga office din zai tafi gidan Aunty Rabi'ah don ya kira Zainab ya fi a kirga bata daga kiran, Da ya kira Ummi kuma normally suka gaisa nan ya gane ba can taje ba kamar yanda ya zarga kawai sae bai ce ma Ummi komai ba, Mayraah bata san yaran are sharp haka ba, don cikata suka yi da surutu ta rasa wanda ma zata amsa cikinsu, bayan tafiyarsa da kusan minti talatin Ashnaah tace "Aunty i want cornflakes" Mayraah tace "Ohk" Ashfah tace "Me too" Murmushi Mayraah tayi ta tafi inda ya nuna mata jakar ta durkusa tana dubo cornflakes din a ciki, bude office din aka yi ta juya da sauri, sosai gabanta ya fadi ganinsa amma lokaci daya ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, tana ji ya shigo office din yaran suka je da gudu suka rungumesa ya duka ya ba ko wannensu peck yana kallonsu yana murmushi yace "Where is papa?" Ashnaah tace "He is gone" Yace "And he left u 2 all alone?" Ashfah ta nuna masa Mayraah da ta mike tsaye, ya juya suna hada ido ya wani sha kunu kamar ba shi ke murmushi ba ya mike tsaye ya jefa files din hannunsa kan table din Dr Khalil, tayi gathering courage zata gaishesa taga har ya fice daga office din daga ita har yaran suka bi sa da kallo, tabe baki tayi ta zagayo ta mika ma yaran bowl din cornflakes da ta hada masu. Sai kusan azahar Dr Khalil ya dawo, duk yaran sun yi bacci ta kwantar da su kan kujera, yana shigowa ya ajiye car key dinsa ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yayi kasa da murya yace "Me yasa baki gaida MD ba da ya shigo office din nan dazu, Why pls Mayraah?" Hade rai tayi tace "Ni gaskiya Dr bazan iya aiki a asibitin nan as far as wannan mutumin yana nan, ya tsaneni, how will i greet someone that just disappeared daga gani na, he is just too rude for my liking, sannan ya fiye nagging" Dr Khalil yace "Let me tell u something, in fa kina karkashin mutum dole za kiyi hakuri a rayuwar nan, mu ma nan duk hakurin mu ke, MD is nyc but he have anger issues sannan baya son wasa baya son raini, he is a man of principle, mun yi degree tare da shi ne shi yasa har muka ɗan saba yake daga min kafa a abubuwa da yawa" Da mugun mamaki tace "To asibitin sa ne nan din with his principality?" Murmushi Dr Khalil yayi yace "Ba nashi bane, amma he is the second in command, he is a braniac Mayraah yasan aiki sosai, i think his dad is also a Dr in the US yanzu haka, and he is an only son, dole sai kinyi hakuri da shi, ni ina maki sha'awar son ace kin zama staff a nan saboda zaki ga advantage din hakan nan gaba" Daukar jakarta tayi tace "Tun da ka dawo ni zan tafi" Yace "No, i spoke to him now, zai yi interviewing dinki, he is less busy a office yanzu" Sosai gabanta ya fadi tace "But i am not ready Dr" yace "Dole ayi inputing data dinki yau Mayraah, don gobe me asibitin nan will be around saboda next workshop da za mu je, kin ga idan bai baki employment din ba u are not a staff, sannan babu vacancy, and they will be none anytime soon" Mayraah da taji hankalinta ya tashi tace "To amma wani irin interview zai min, i don't have knowledge of how it is..." Dr Khalil ya katse ta yace "Just compose ur self, u are not dull Mayraah, i know u can do it" Bude drawer yayi ya ciro farin takarda ya mika mata yace "Apology letter, in kinje kin gaishesa sai ki basa hakuri da baki respectfully sannan ki mika masa wannan" Sake baki Mayraah tayi tana kallon takardan, can tace "Apology letter for what? Are we in secondary school?" Dr Khalil ya daure fuska yana kallonta, da tasan stress din da yayi going through yau duk a kanta da bazata ci gaba da stressing dinsa ba ita ma, first yaje shawo kan matarsa duk a kanta, secondly ko gamawa da matar tasa bai yi ba sai ga kiran MD babu abinda ya mance bai gaya masa a waya ba, yana shigowa asibitin yanzu yaje ya samu MD after almost 30 minutes of persuasion ya shawo kansa har ya yarda yayi mata interview din yau and she is here trying to complicate issues the more, Mayraah ta amshi takardan, on a serious note Dr Khalil yace "Mayraah ko zaginki yayi kice kin gode, kuma kar ki kuskura ki fito office din duk ma me zai ce maki" Ta ɗan yi murmushi kawai ta juya ta fita, ya zauna ya sauke ajiyar zuciya a yanda ya lura ma ta fi MD din girman kai amma bata sani ba, Mayraah na tafiya sama ta tsaya kofar office din MD din tana kallon sunan dake manne jikin kofar daga sama.
[7/25, 7:04 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah tayi knocking din office din a hankali ta koma gefe ta tsaya, jin ba a amsa ba bayan some seconds ta sake knocking, Sai da tayi knocking sau uku sannan taji ya bada izinin shigowa, ta bude kofar a hankali suna hada ido tun kan ta saka kafarta cikin office din yayi saurin cewa "I am occupied Madam, leave and come back tomorrow 8am prompt" yana fadin haka ya ci gaba da sipping juice dake hannunsa yana operating laptop, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa, a karo na farko tun barin ta gida Musharraf ya fado mata a rai, don last day da ta je kai masa project work dinta a office dinsa da yanda yace ta tafi ta dawo 5:30pm prompt ne ya shiga rotating a kanta, ganin bata bar bakin kofar ba ya daga kai ya sake kallonta ya hade rai yace "Are you daft?" Wani tsinannen kallo ta jefa masa, wanda hakan yasa ya ajiye juice din hannunsa ba tare da yasan yayi hakan ba cause he was taken aback by her reaction, tuni ta kulle kofar office din ta bar wajen fuskarta daure, har ta sauka second floor ta kasa kauda tunanin Musharraf da ya mamaye ranta wanda hakan yasa kuzarinta ya ragu, office din Dr Khalil tayi knocking ta shiga bayan yayi mata izini, da mamaki yake kallonta ya mike tsaye yace "What happened again?" Ta kirkiri murmushi tace "No, na samesa yana cin abinci ne, shine yace in bari gobe karfe takwas na safe idan Allah ya kai mu" Dr Khalil yace "Are you sure Mayraah?" Ta gyada masa kai tace "Da gaske fa, yace gobe da safe in sha Allah" Dr Khalil ya koma ya zauna yace "Ohk" Daukar handbag dinta tayi tana kallonsa tace "Na gaji, ina son in tafi" Yace "Toh ki gaida su Ummi, inna dai na gidan Baffan su Mimi, cousin din Zainab zata yi aure next week" Tayi murmushi tace "Allah sarki, pls idan twins sun tashi kace masu sai mun sake haduwa i will miss them" Yace "To zan gaya masu" juyawa tayi ta fita daga office din ta sauka downstairs, sallama tayi da Nurse Hafsat sannan ta fita haraban asibitin, zaunawa tayi karkashin wani bishiya ta ciro wayarta a jaka, a hankali ta fara dialing number Musharraf da ake samunsa not his private line dake kulle, tafi minti uku tana kallon numbers din ta runtse ido kawai ta goge ta maida wayar cikin jakarta ta mike walking slowly ta fita daga asibitin, tana taran adaidaita sahu ta gaya masa inda zai kai ta sannan ta shiga, after many minutes ride yayi parking inda tace ya tsaya sannan tace "Don Allah ka jira ni zan amshi sako ne sai ka kai ni wani wajen daban" Yace "Toh" Karasawa tayi ta shiga shagon Aminu, gaisawa suka yi da fara'a yace "Ya makarantar Hajiya" Tace "Alhamdulillah ya kasuwa?" Yace "Lafiya lau wallahi, kin ga na kwana biyu ma ban shiga Sulejan ba ni" Tace "Allah sarki, don Allah SIM card nake son zan kara siya" Yace "Toh wani network kenan?" Tace "Ko wanne, sai ka hada min da katin dubu daya" Dauko mata yayi ta ciro dubu biyar a jakanta ta basa tace "Ka saka katin waya da sauran canjin" Godiya ya mata sosai bayan ya amsa, tayi murmushi ta yi masa sallama ta koma cikin adaidaita sahun dake jiranta. Mayraah na sauka kofar gidan Ummi bayan ta ba mai adaidaita sahun kudinsa ta shiga gidan, Ahmad na zaune compound making a phone call, kawai ta ɗan masa murmushi not wanting to distract him ya bi ta da ido har ta shiga gidan, karime kadai ce a gidan bayan sun gaisa karime tace "Ai ko awa daya yan gidan basu yi da fita ba in gaya maki, kinsan aminiyar Hajiya ke aurar da er ta, to can Hajiya ta tafi da Mimi, gobe asabar ne daurin aure ranan lahadi kuma ayi taron biki, ina jin ranan lahadin za su dawo, Hassan da Hussaini kuma sun je gidan baffansu tare da Inna tun jiya, Baffan zai aurar da er sa satin nan da za mu shiga" Mayraah dake zaune parlon tana danna wayarta tace "Allah sarki" Karime tace "Ai gobe baki da aiki ko?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ta ɗan yi murmushi, Karime tace "Sai mu je gidan bikin kawai tare, Hajiya ta ce in je gobe, ina jin bata san za ki dawo ba tunda mun san can Suleja kike weekend dinki" Mayraah tace "Zan je aiki goben in sha Allah" ta fada haka ne ba don tana da intention din zuwa asibitin gobe ba sai don kawai bata son bin karime gidan bikin, Karime tace "Allah sarki, to bari in zubo maki abinci" Daga haka ta mike ta shiga kitchen Mayraah ta bi ta da kallo, Karime zata yi shekara kusan arba'in da biyu, kuma ta fi shekara bakwai tare da Ummi sai dai taje ganin yaranta da iyayenta a kauyensu ta dawo don ta zama kamar wata er uwar Ummi, Karime na kawo mata abincin ta ajiye Mayraah tace "Nagode sosai" Karime tace "Kin ga da daddare ba sai mun yi girki ba, tun da akwai burodi kawai soya kwai za mu yi mu sha shayi don shi yallabai dama shayi yake sha da daddare" Mayraah dai ta ɗan yi murmushi ta dau plate din abincin ta fara ci, sama sama take biye karime da ta cikata da hira a parlon don duk ta kagu ta wuce daki ta saka sabon sim card da ta siyo, kiran la'asar ya sa Mayraah ta mike ta tafi kai plate din kitchen ta wanke sannan ta dawo ta tarar har Karime ta shiga daki ita ma zata yi sallah, Mayraah ta dau jakanta ta wuce nata dakin da take sauka a gidan, alwala tayi, bayan ta idar da sallah ta dau sabon sim din ta saka a wayarta, ganin ya hau ta loda katin, dialing din number Musharraf tayi da sabon Sim card din, tana ji ya fara ring sai da gabanta ya fadi, ta daura goshinta saman knees dinta har sannan zuciyarta na bugawa tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa taji ya daga, shiru tayi shi ma yayi shiru bai ce komai ba, after few seconds taji ya katse wayar, murmushi tayi don tasan dama bazai ce komai ba in dai bai san number ba haka yake, sake dialing number tayi duk da a ranta tasan ba lallai ya sake dagawa ba ai kam har ya gama ringing bai daga ba, kawai ta kashe sim card din cikin wayar ta ajiye wayar ta kwanta. Mama Ladi ce zaune gefen Hajja dake jingine da bango tana zaune kan shimfidar da aka mata a parlonta wajen karfe biyar na yamma, Mama Ladi na washe baki tace "Alhamdulillah jiki ai ya fara kyau, gashi har kin kusa shanye shayin, tun jiya fargabana ta ina zan fara jinyarki idan shanyewar barin jiki ya sameki, wallahi hankalina yayi matukar tashi bazan boye ma kowa ba" Ammi dai na zaune parlon tana kallonsu, Aunty Mariya kuma na kitchen tana dama ma Hajja kunu, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Ke fa nace maki ki tashi ki tafi gida kar Mamuda ya ga rashin hankalinmu ya sake tabbatar da mu kananun mutane ne, tun shekaranjiya fa kike nan ko mutuwa aka yi ya ci ace kin koma dakinki barin ma ga Hajja har ta fara tashi zaune ga kuma shayi tana sha, nima zuwa anjima in sha Allahu zan taho sai Mariya ta zauna tayi jinyar Hajjan da me laulayin can, don gaskiya bazan iya jure ƙarnin aman da Badiyyah take kirba mana ba, in tayi aman ƙarnin har nan malam, to a kan me, ɗa ba ɗan sunna ba ta dinga cutar mu da ƙarni, bazan iya ba wallahi" A karo na farko Hajja ta bude baki a hankali tana girgiza kai tace "A fitar min da ita daga gidana dama jira nake in gama shan shayin inyi magana, a tafi da ita duk inda za aje da ita, in ko ba haka ba in bi Mariya mu tafi kaduna ta sauke ni gidan yahanasu" Tana magana ne hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "A fita da ita a kai ta ina Hajja? Ko dai baki gane wa nake nufi ba, Badiyyah fa nake magana, Badiyya guda fa taki" Hajja na gyada kai wani bakin ciki na kara tokare mata makogwaro tace "Ita Ladi, bazata kwanar min a gida yau ba ta tafi duk inda za ta, ni ma kaduna zan tafi gun yahanasu" Ammi tayi kasa da murya tace "To ina za ta Hajja? Da dai kin yi...." Dakatar da ita Hajja tayi cikin rawan murya tace "Wallahi tallahi bazan kwana da Badiyyah gidan nan ba yau kun ji har na rantse, dama ina ta addu'ar in samu karfin yin magana tun jiya Allah bai bani iko ba sai yanzu, to Allah ya isa tsakanina da ita, Allah ya isa, Allah ya isa wannan abun gorin da ta ja min har karshen rayuwata, duk soyayyar da na nuna mata saboda tausayin maraicinta duk jan ta jiki da nayi don kawar mata da maraici a rayuwarta sakayyar da Badiyyah zata min kenan, da haka zata saka min? ta cuce ni, ta ja min abun kunya, ta

Please Login or Register in order to submit comment