You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

doki banza babu wanda ya dau mataki kema yau haka zan dokeki in doki banza babu abinda zai faru wallahi...." Mayraah na jin haka ta fara kokarin cire Hijab dinta don baxata bari haka kawai Badiyyah ta doketa ba, Badiyyah tayi using wannan opportunity din ta shakota da Hijab din ta fara dukanta ta ko ina tana cewa "Yau sai dai wata ba ke ba wallahi" Haseenah ta koma gefe tana kyalkyala dariya tana kallonsu tana hailing din Badiyyah, Sai da Mayraah ta san yanda tayi ta fizge Hijab din daga jikinta ta fara retaliating dukan da Badiyyah ke mata, nan suka fara kokuwa suna kai ma juna duka ta ko ina, Haseenah ta ga alamar at anytime Mayraah zata iya kai Badiyyah kasa ashe Badiyyar ba wani karfi ne da ita ba, kawai Haseenah ta shige kitchen da gudu ta kunna gas ta dau fry pan ta zuba manja ta daura kan wuta ta yanka albasa ciki sannan ta cika wutan gas din sai da taga ya fara hayaki sosai kitchen din ya turnuke ita kanta tari take sannan ta fito da fry pan din parlor ta nufo inda suka damben, Mayraah taji numfashinta ya fara tsarkewa ta fara struggling to breathe saboda manjan da Haseenah ta fito parlor da shi tana zagaya su, Badiyyar ma tari take amma hakan bai hanata dinga kai ma Mayraah duka ba har sae da ta kai ta kasa duk da yanda taga numfashinta na kokarin daukewa bata fasa dukanta ba, Haseenah na ganin haka ta ajiye fry pan din hannunta bayan kujera ta gudu daki ta dau wayarta tayi dialing number Maheer yana dagawa ta fashe da kuka tace "Baby kana ina ne don Allah? Ka bar ko me kake yi ka dawo gida ba lafiya" Maheer da fitowarsa kenan daga asibiti ya rage sautin karatun Alqur'ani da ke tashi a motarsa yace "Me ya faru???" Cikin Muryar kuka Haseenah tace "Wallahi ina zaune ko minti ashirin ba ayi ba Badiyyah ta zo wai shekaranjiya ta mance charger dinta zata dauka, to zata tafi kenan sae ga Mayraah ta dawo ita ma zata shigo parlor, kawai sai Mayraan ta bangajeta a bakin kofa, ni dai kawai sai gani nayi suna dambe, daga haka kuma numfashin Mayraah ya fara sama sama...." Katse wayar Maheer yayi, Haseenah ta koma parlor da sauri, zaro ido tayi tana kallon Badiyyah da ta mike tana huci tana kallon Mayraah dake kwance kasa kamar bata numfashi, Haseenah ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kamar bata numfashi fa Badiyyah" Badiyyah ta dau Hijab din Mayraah da sauri ta saka don tuni shegun kayan jikinta suka yage kaca kaca, ta dau handbag dinta da wayarta da gudu ta bar gidan, rikicewa Haseenah tayi ta nufi windows din parlon da sauri ta bude labule don hayakin manjan ya fita, ta kure fanka ta buda Ac sannan ta dau fry pan din shima da gudu ta kai kitchen ta zubar da manjan a sink ta fara wanke wanke, gaba daya a tsorace take, ta kara dawowa parlor tana kallon Mayraah that is lying almost lifeless a kasa, jikinta na rawa ta kara daukan wayarta tayi dialing number Maheer amma bai daga ba, da gudu ta tafi kitchen ta debo ruwa ta fara zuba ma Mayraah tana jijjigata, gaba daya ta tsorata ba kadan ba, ta fita a guje tana kwala ma Musa mai gadi kira tana cewa "Musa zo ka duba min kaddai mutuwa tayi" Musa na shiga parlon shima ya kasa karasawa ya dinga "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Tuni Haseenah taji hanjin cikinta ya kada ta daura hannu a ka ko ina a jikinta na rawa tace "Ta mutu ne Musa??" Dai dai nan Maheer ya shigo parlon, shi kansa bai san ta yaya ma aka yi ya iso gidan ba, dukawa yayi inda Mayraah ke kwance ya dagota yana kiran sunanta cikin tashin hankali, ganin she is unresponsive ya fara mata Chest Compressions da sauri, daga bisanni ya bude bakinta ya hade da nasa giving her mouth to mouth resuscitation, duk da tashin hankalin da Haseenah ke ciki sai da ta hade rai tana kallonsu ganin abinda yake ma Mayraah, nan da nan ta nemi fargaban da take ciki ta rasa, ganin bazata iya ci gaba da kallonsu ba ta fito balcony ta tsaya fuskarta a daure. Haseenah ta fi minti biyar tsaye a balcony taki shiga parlon, sai a sannan kuma ta fara addu'ar Allah ya sa Mayraahn ma ta mutu kawai, tana tsaka da wannan tunanin ne Maheer ya fito dauke da Mayraah ya nufi motarsa dake waje da sauri, Haseenah ta wani kyabe baki ta bi Mayraah da kallo ganin idonta a rufe suke ta fara wishing dinta mutuwa, can dai kuma ta bi su har kofar gidan da sauri, cike da damuwa kamar gaske tana yarfe hannu tace "Maheer hope she is breathing now? Hope kayi reviving dinta?" Ko sauraronta Maheer bai yi ba ya shige driver seat ya tada motar ya bar unguwan with speed, wani murmushi Haseenah tayi ta juya ta koma ciki tana ci gaba da yi ma Mayraah fatan mutuwa. Maheer na zaune ward din da aka kwantar da Mayraah wajen karfe tara na dare, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, kana ganinsa zaka san he is not himself, ba a jima da cire mata oxygen ba don breathing din nata ya dawo normal, lkci lkci yake tashi ya dubata a kan gadon, Usman ne ya shigo ward din, direct gadon da Mayraah ke kwance ya nufa ya tsaya yana kallonta babu ko kiftawa, Kamar yanda bai ce ma Maheer komai ba haka Maheer ma bai ce masa komai ba, ko minti ashirin Maheer bai yi da kiransa ya sanar masa da abinda ke faruwa ba, don ko Ammi bai gaya ma ba har sannan, after standing for almost 5 minutes yana kallon Mayraah, Usman ya juya ya kalli Maheer for the first time yace "Me ya kai Badiyyah gidanka har tayi mata haka?" Maheer dai bai ce komai ba, juyawa Usman yayi ya nufi kofa ya fice daga ward din Maheer ya bi sa da kallo. Usman na fita ko minti sha biyar ba ayi ba Mayraah ta bude idonta, Maheer ya mike da sauri ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace "Mimi how are you feeling?" Hawaye ya gani a idonta, lkci daya jikinsa yayi sanyi ya ma rasa abinda zai ce mata.... Badiyyah na kwance Hajja na gasa mata hannu da ruwan zafi sai ihu take duk ta cika gidan tana cewa wayyo mamana kamar gaske don babu abinda ya samu hannun, dama tana dawowa gida ta sanar ma Hajja karya zalla wai Mayraah ta rufeta da duka a gidan Maheer da kyar Haseenah ta kwace ta, daga dai Mayraan taga wannan lecturer din da ya fasa aurenta yana kula ita Badiyyar a school, ta dai yi fabricating lies ba kadan ba tayi feeding din Hajja da shi, wanda nan da nan Hajja ta kira Ammi tana vibrate, abinda ta manta ne kawai bata fada a wayar ba don in ance ma ta tsine ma Ammi ba mamaki, Hajja ta tafi ta dafo ruwan zafi ta hau gasa ma Badiyyah hannunta da tace ya goce, a cikin ihun da take ne take cewa Hajja ita Bichi kawai zata tafi, Hajja tace "Ki tafi ina a haka? Ae wallahi in har Hajarah bata dau mataki a kan wannan abinda aka maki ba sai dai ta nemi wata uwar kuma ba ni ba, saboda ta nuna min iyakata shine ta sa Maheer ya tafi da yarinyar gidansa, to wllh yau za ayi ta ta kare, su zabi ko ni ko yarinyar nan, ae ita ke da iko da Maheer ba shi ke da iko da ita ba...." Hajja na kai wa nan ta mike tana huci ta shiga daki zata dauko man zafin da zata shafa ma Badiyyah amma ta neme sa ta rasa, fitowa tayi ta dau gyalenta tace "Bari in amso man zafi nan makota in dawo" Badiyyah na ganin fitar Hajja ta mike da sauri ta shige daki ta dau karamar jakarta ta saka kaya kala biyu da kayan shafe shafenta ta zuge jakar har wani rawa jikinta yake don ita gani ma take kamar za a kira ace Mayraah ta mutu, da ta tuna yanayin da ta bar ta sae gabanta ya fadi, tana fitowa parlor ta nufi kofa zata bude aka riga ta budewa, duk a tunaninta Hajja ce amma tana daga kai taga ba haka ba, a cikin minti biyar zuwa shidda ya gama mata abinda ya kawosa ya bar ta kasa ko kwakkwaran motsi bata yi tsabar duka, ya fice daga parlon.... Maheer na tsaye kan Mayraah dake zaune kan gado wajen karfe goma, tun dazu yake lallabata ta gaya masa menene ya faru dazu amma taki cewa komai, a haka Usman ya shigo ward din ya same su, Maheer ya dinga kallonsa don ko ba a gaya masa ba ya ma san daga inda yake, Usman ya nemi kujera ya zauna as if everything is okay, Maheer ya kalli Mayraah dake kallonsa, sai a sannan ta bude baki a hankali tace "Aunty Haseenah ce da sis Badiyyah" da wani expression Maheer ke kallonta, can dai yace "Haseenah?" Mayraah ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, juyawa yayi ya fita daga ward din.... Haseenah na zaune parlor tana cin Indomie din da ta dafa, zuwa yanzu har ta gaji da addu'ar Allah ya kashe Mayraah, banda ma ta gigice ai da taga ta shiga comma kamata yayi ace ta dau throw pillow ta danne mata fuska da shi da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, ta kyabe baki tana cin Indomienta da soyayyen kwai, tun da taga har goma da rabi tasan Maheer ba lallai ya dawo ba kenan tunda kanwar uwarsa na kwance asibiti, tana cikin tunanin nan ya bude kofar parlon ta daga kai da sauri, ganinsa ta mike ta nufesa da damuwa tace "Baby ya jikin nata, har na gaji da kiranka a waya baka dagawa, kaga tun dazu sai yanzu na iya dafa Indomie zan ci...." Takardan dake hannunsa ya jefa mata ya juya ya fice daga parlon, ta dinga kallon takardan gabanta na wani irin faduwa, da kyar ta durkusa ta dauka ta warware tana duba content din, wani ihu ta fasa ta bi sa a guje tana cewa "Maheer ka sakeni saki daya kamar yaya??? ban gane ba Maheer, ni din ka saka?" Amma tuni ya shige motarsa ya bar layin, shi dai mai gadi sai zare ido yake.



MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788



*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/2, 6:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya kalli agogon wrist dinsa dake nuni da karfe sha dayan dare sannan ya kalli Usman dake danna wayarsa yace "It's getting late, baza ka tafi gida ba?" Usman ya daga kai ya kallesa yace "I should be asking you that kai da kake da iyali a gida" Maheer yayi shiru bai sake ce masa komai ba, lkci lkci yake kallon Mayraah da ta koma bacci tun dazu, ganin har sha biyu Maheer ya mike ya dau makullin motarsa without looking at Usman yace "Sai da safe" Usman yace "Allah ya tashe mu lafiya" Bai ce masa komai ba ya fice daga ward din ya kulle kofar... Through out night din Usman bai yi wani bacci ba, he kept a close eyes on Mayraah dake ta bacci just to make sure is okay, karfe biyar saura na asuba aka bude kofar ward din ya daga kai ya ga Maheer ya shigo, Ajiye ledan hannunsa me dauke da hijab din Mayraah da toothpaste and brush yayi, sannan ya ajiye takalmanta a kasa kusa da gadon ya juya ya fita daga ward din, sai da aka kira sallah Usman ya fita shi ma. Da safe karfe bakwai da rabi aka yi discharging din Mayraah daga asibitin, suna isa parking space da brothers din nata taga ko wannensu da motarsa a nan, tsaye tayi gefe daya not knowing motar wanda zata shiga cikin su, Usman dai ya bude motarsa ya shiga ya tada ya bar su tsaye wajen yayi wucewar sa from the hospital, Mayraah ta bi motarsa da kallo sannan ta bude motar Maheer a hankali ta shiga ta zauna. Kusan a tare suka isa gida sai dai Usman ya riga su shiga cikin gidan, Maheer na gaba tana biye da shi suka shiga gidan, zaune suka tadda Usman a parlorn downstairs tare da Mama Ladi dake cusa lafcecen kwai cikin biredi tana dannewa, ga cup din shayinta a gefe tana cewa "Wallahi yanzu haka wai suna asibiti, ko wani asibiti ne oho, wa ya sani ko gantalinta zata je mota ya kade ta, tun karfe hudun asuba Ammi ta bar gidan nan har yanzu babu ita babu alamarta inji Saliba me aikinku, ni dai nace sai na ci na koshi kafin inje ko ina babu ruwana da lalacewa inje yunwa yayi min lahani ayi min hisabi da yan hanjin cikina ranan gobe kiyama" Shigowan Maheer da Mayraah yasa ta daga kai tace "Yauwa Mashir wai me ke faruwa haka ne? Saliba tace min Ammi tun asuba ta bar gidan nan" Maheer ya karasa ya zauna kan kujera yace "Sabira dai ko, ina kwana..." Mayraah dai tafiya take a hankali ita ma tana kallon Mama Ladi, Mama Ladi ta yagi kwai da bread ta kai baki tana cewa "Ni jiya da wuri nayi bacci bayan na ci abinci ban san kan komai ba wllhi, ita Salibar ke gaya min an kai Badiyyah asibiti" Bata rufe baki ba Ammi ta shigo parlon rike da basket din flask da kayan shayi, Maheer da Usman suka juya suna kallonta haka ma Mayraah da ta nufeta zata amshi basket din hannunta tace "Sannu da zuwa Ammi" Ammi bata ce mata komai ba kuma bata bata basket din hannunta ba ta wuceta ta karasa cikin parlon tana kallon Maheer da Usman tace "Ina jiranku a sama...." Daga haka ta ajiye kayan hannunta ta wuce sama, duk suka bi ta da kallo, har Mayraah da ke tsaye inda Ammi ta bar ta, Mama Ladi na kora bread dinta da shayi tace "Ko kudi za a harhada na trintment din Badiyyar tunda dai duk mun san dangin ubanta matsiyata ne, tun tana karamarta Ammi ke mata komai sai Mamuda da Hajja da ni, sai kuma ku da ku ka kawo karfi yanzu, ku dai je ku ji, iyaka ku bada dubu daddaya ta rabaku da kowa lafiya tunda ba wani ya aiketa ba...." Usman ya fara mikewa ya wuce sama, Maheer ya tashi ya bi bayansa shi ma, Mayraah dai ta kasa karasawa cikin parlon ta zauna, Mama Ladi ta mike ta dau shayinta da bread tace "To ya ma za a bar ni a nan sai kace wata bare..." Sai kuma ta kalli Mayraah tace "Zo ki dau min shayin nan mu tafi sama kar garin hawa benen nan in barar in shiga uku ance milo ya kare, duk an wani watse a bar mu kamar mun ci mutum" Mayraah da gaba daya jikinta yayi sanyi ta rasa dalilin hakan, ta karasa gun Mama Ladi ta dau mata shayin suka wuce sama a tare. Usman na shiga parlon Ammi ya ga Haseenah zaune kan kujera da hijab dinta har kasa sae counter din carbi a hannunta, duk da yayi mamakin ganinta ya gaisheta a takaice ya shiga dakin Ammi, Maheer ya shigo Parlon few seconds later, he was very very surprise to see Haseenah sitted in Ammi's parlor, ya dinga kallonta, suna hada ido ta kauda kanta ta wani daure fuska tana daddanna counter din hannunta, lkci daya yaji wani mugun ɓaci rai ya zo masa, but ya dai yi calming kansa down bai ce mata komai ba ya wuce dakin Ammi, tsaye ya ga Ammi bakin window duk tana jiran su, kallo daya Usman yayi mata bai ma karasa can cikin dakin ba ya tsaya daga gefen kofa cause her facial expression isn't giving, Maheer ne yayi karfin halin karasawa ciki yana kallonta shi ma, daga shi har Usman babu wanda ya iya bude baki ya gaisheta don basu ma ga fuskar yin haka ba, Mama Ladi ta shigo parlon Ammi Mayraah na biye da ita, buda baki tayi ta koma baya da sauri ganin Haseenah, cike da mamaki tace "Ke kuma daga ina matar nan? Ko dai ba da ke aka tafi jiya ba?? Ni fa na raka ku har mota, garin yaya haka na ganki a nan?" Haseenah dai ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi ta nufi dakin Ammi tace "Yau ni naga ikon Allah" Mayraah bata bari sun hada ido da Haseenah ba ta ajiye Shayin hannunta a kasa sannan ta zauna kan carpet din parlon, tun da Haseenah tayi mata wani matsiyacin kallo ta kyabe baki ta kauda kai tana girgiza kafa.... Maheer yayi gathering courage yana kallon Ammi yace "Ina kwana Ammi" A fusace Ammi tace "Ban kwana ba, nace ban kwana ba..." Kallonta kawai Maheer yake yayi shiru, Ammi na nunasa cikin bacin rai tace "Before going into my main point ina son ka maida matar ka immediately first..." Maheer ya sunkuyar da kansa, Ammi ta masa tsawa tace "Are you deaf, ko baka ji na ne?" Ya dago kai a hankali yace "I have done that" Mama Ladi da ta shigo dakin ta buda baki tace "Wai me yake faruwa ne kike daga murya haka? Me ke faruwa ni Ladiyo? Wace matar za a mayar?" Ammi bata ko kalleta ba tana kallon Maheer tana gyada kai tace "Sai yanzu na fahimci inda Hajja ta dosa all this while, sai yanzu na gane abinda take son ta fahimtar da ni na kasa ganewa, i now fully understand Mimi is nothing but a nuisance in our midst now, she is beginning to cause nothing but chaos in this family, kai ka saki matarka da ko sati uku ba kuyi da aure ba duk a saboda ita, shi kuma ɗan uwanka ya sake komawa for the second time yayi ma Badiyyah dukan tsiya duk a kanta ba tare da yayi binciken abinda ya faru ba, a saboda yarinyar nan har yau mahaifiyata bata ɗaga wayata, ko naje inda take babu maganar arziki tsakanina da ita all because of Mimi, is that how she wants to pay us by destroying us? Toh all this is going to end now" Cikin daga murya Ammi tace "Maheer from today henceforth she is not staying in ur house any more, bazata sake zama a gidanka ba nace...." Maheer couldn't believe this is really coming out from Ammi's mouth, ji yayi kansa ya wani sara masa yana kallonta cike da karfin hali yace "Where will she stay then?" A takaice Ammi tace "I don't know, and I don't care Maheer, idan ma kai da Usman za ku dawo hankalinku ku dawo, baku hada komai da ita ba, i repeat babu abinda ku ka hada da ita in any way, she is not ur blood, and because of her bazan zuba ido zumunci ya lalace ba, Ita Badiyyar da ku ka mayar makiyiyarku ita ce dolen ku duk inda za a je kuwa, ita ce er uwarku ta jini, sannan baza ka taɓa hada matar da kake aure da ita ba, matar ita ce dolen ka ba ita ba" Usman ya dinga kallon Ammi da mamaki babu ko kiftawa, jin maganganun nata yake kamar a mafarki, Mama Ladi dai sai zazzare ido take duk da turanci yafi yawa a maganganun amma sarai ta fahimci komai, salati ta saki tayi zaman dirshan a kasa tana girgiza kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Hajaru yau kece kike wannan munanan kalaman akan Mera? Me suka baki kika sha a asibitin Hajaru, yau mun shiga uku mun lalace, ina ake son Marainiyar ta sa kanta taji dadi kenan?" Kawai sai ta fashe da kuka wiwi, Maheer dake ta kallon Ammi ganin zata fita ta bar masu dakin, a hankali yace "Ohk then, tunda kince babu abinda muka hada da ita, sannan ita din ba jininmu bace yanzu na yarda kuma na amince da hakan, as at before i was still doubting that, don bamu ji kin gaya mana hakan da bakin ki ba duk abubuwan da suka faru, it was hard for us to assimilate Mimi isn't our blood all this while, but after saying this today naji na yarda da hakan har cikin raina, saboda haka ni zan auri Mimi in samar mata gidan da zata zauna to bring an end to all this...." Juyawa Ammi tayi da sauri tana kallonsa kamar yanda Usman ma ya daga kai yana kallonsa, Ammi na kallonsa da kyau tayi wani murmushi tace "Ba da yawuna ba, in kuma gaban kanka zaka yi i assure u baxa ka taɓa ganin dai dai ba..." Juyawa Usman yayi ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Mayraah na zaune parlor kanta a kasa duk tana jin abubuwan da ake yi a dakin, banda murmushi babu abinda Haseenah take tana kallon Mayraah kasa kasa dom everything was clear kamar a gabansu ake yi, Mama Ladi dake rusa kuka ta mike tana kallon Maheer tace "Kawai ta hado kayanta mu tafi karaye Mashir, dama ka taɓa ganin inda barewa tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe??" Bata jira amsarsa ba ta fice daga dakin ta koma parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi maza ki tattaro kayanki" Sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Mama Ladi da manyan idanuwanta, cikin daga murya Mama Ladi tace "Baza ki tashi ba sai kin ga tana watsar maki da kayanki titi" Mayraah ta mike tsaye, Mama Ladi tace "Fita mu je, ai naga akwai sauran kayanki a gidan nan tattaro su gaba daya kawai ki zuba a akwatina" bin bayan Mama Ladi Mayraah tayi suka fita daga parlon zuwa dakinta, Mama Ladi ta bude inda sauran kayan Mayraah suke ta dinga kwasowa tana zubawa a akwatinta, ita dai Mayraah na tsaye tana kallonta kamar statue, Maheer ya shigo dakin looking so weakened and confused, Mama Ladi ta dago bayan ta gama cusa kayan a akwatin tana kallon Mayraah tace "Shikenan abinda zaki bukata kin wani tsaya kamar gunki kina kallona, ko baki ji abinda ke faruwa a gidan bane" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kallonta take, it seems like it's taking her too long to absorb the reality of what is happening, Maheer na kallon Mama Ladi a hankali yace "Tana da jarabawan da zata yi Mama" Yana fadin haka ya karasa ya kama hannun Mayraah suka fita daga dakin kawai, ita dai bin sa kawai take har suka sauka downstairs, Balcony ya fita da ita ya sa ta zauna, shi ma ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya tsaya cak ganin abubuwan yake kamar a mafarki ya rasa wani tunanin zai yi, ita dai Mayraah kallonsa kawai take, can ya dago ya kalleta ganin yanda take kallonsa ya kama hannunta yace "Mimi" sauke idonta tayi ta amsa, yaji wani tausayinta har cikin ransa, seeing her dry eyes ne ya kara daga masa hankali don yasan taji duk furucin Ammi tunda kofar dakin a bude yake ya kuma san ita din me saurin kuka ce amma ynxu bbu ko digon hawayen a idonta.... Haseenah bata taɓa shiga farin ciki irin na yau ba ko aurenta da Maheer bata ji irin wnn mugun farin cikin ba, gaba daya ta kasa tsaye ta kasa zaune a part din Ammi don murna, babu kowa sai ita kadai a part din, aka bude kofar Parlon juyawa tayi da sauri ganin Abba

Please Login or Register in order to submit comment