You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don surutunta kara masa ciwon kan da yake ji yake, a takaice Abba yace "Nayi waya an saketa" Mama Ladi ta fashe da sabon kuka tace "Allah Ubangiji yayi maka albarka, in ba kai din ba wallahi sai dai ta kwana cikin barayi a self, tana kuka fa basu ji tausayin tsufarta ba suka dinga figarta har kofar gida, kuma ba kowa ya ja mata ba Badiyyah" Maheer ya shigo parlon da sallama, ya nufi Abba yana kallonsa ganin yanayinsa amma ya kasa cewa komai, Abba ya mika masa takardan hannunsa yana kallonsa ya girgiza kai sounding so pained yace "Ur mother failed me" Daga haka ya wuce sama, ita dai Mama Ladi sai zare ido take tana bin takardan hannun Maheer da ido, Sai da kan Maheer ya sara yana fara karanta first 3 lines din takardan kuma yaga writing din Mayraah, ya ji kafafuwansa sun kasa daukansa ya zauna kan kujera zuciyarsa na bugawa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta zaro ido a tsorace tace "Lafiya, takardar mecece Mashir?" Kasa bata amsa yayi ya rike kansa. Hajiya Fauziyya da mukarrabanta dake cikin mota za su koma asibitin da aka kwantar da Haseenah bayan ta tabbatar mai gidanta ya bada order din kada a bada belin Hajja sai an kama Badiyyah tukun wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin mai gidan nata ne ta daga tace "Abban Ikram muna hanyar asibitin yanzu haka, don Allah ka kara jaddada masu kada a bada belin matar nan sai an kamo matsiyaciyar yarinyar" Mai gidan nata yace "Ai ina jin fa kawai hakuri za kuyi ayi sulhu Fauziyya, don yanzun nan wani officer da nake jin nauyinsa don gaba ma yake da ni gun aiki kawai dai na fi sa sanin Officers dinmu ne ya bugo min wai surkar abokinsa ce ita matar da yan sandan suka kama, yana kuma neman alfarman a rufe case kawai aje gida ayi sulhu" Hajiya Fauziyya na huci tace "Ban gane ba Abban Ikram, kana nufin an doki er mu an fasa mata kai a banza kenan? Wai kai kaga uban raunin da ta ji mata ne kuwa? Ko don ban dauka a hoto na turo maka ba?" Yace "Na dai gaya maki, ayi hakuri a je ayi sulhu don gaskiya ina bala'in girmama Mutumin nan kuma ina jin nauyinsa, don haka ni har na kira Dpo din division din nace masa a saki matar kawai....." Cikin daga murya Aunty Fauziyya tace "In mun yarda shegiya nake, in mun yarda Allah ya tsine mana, wallahi baza mu yarda ba, a tura mu kotu kawai alkali yayi mana Shari'a...." Katse wayarsa yayi, Aunty Farida tace "Lallai Baban Ikram, a saketa fa yace??" Aunty Fauziyya na huci tace "Kyaleni da shi kawai, a tura mu kotu a kwatar mana hakkin er mu kawai, babu wani sulhu da za ayi a gida, idan ko ba haka ba idan ban kira Yaya Abdurrahman soja an kai Badiyyar barikin sojoji ba sun kakkarya mana shegiya ku ce ba ni bace......." Haka Ammi ta dinga yawon police stations tana neman Hajja, in ta hau wannan adaidaitan ta sauka ta hau wannan a haka dai har Allah ya kai ta division din da aka kai Hajja, Hajja na zaune gaban yan sandan sai zare ido take, tana hango Ammi ta fashe da matsanancin kuka, Ammi ta nufeta ita ma ta fara kuka, wata police woman tace "Ku tun dazu an kawo tsohuwar nan station amma babu wanda ya biyota kamar bata da gata kusan awa biyu kenan......" Ammi na kallonta cikin kuka tace "Tun dazu na fito wllhi, nayi ta duba stations don ban san wanda aka kawota ba, da muna gidan ai sai dai ko ni a tafi dani baza mu bar haka ta faru ba" Police woman din ta taɓe baki tace "To za ku iya tafiya kawai an rufe case din, wai ku je gida ku sulhunta kanku" Ammi tace "Toh mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ammi ta kama hannun Hajja dake kuka har sannan saboda takaicin wai yau ita ce a motar yan sanda har police station, adaidaita sahu Ammi ta samar masu, ta dinga bata hakuri amma Hajja ta ki daina kuka don kamar ma dada tunzurata take, cikin rawan murya Hajja tace "Kar ma ki maida ni anguwan nan don yanxu ban san da idon da zan kalli yan anguwan ba wannan abun kunya har ina? Da tsufana da mutuncina a min wannan cin mutuncin Ammi, wallahi ko yarinyar nan kadai ta rage a duniya Maheer bazai zauna da ita ba" Ammi ta rasa ma me zata ce jin furucin Hajja na cewar kar a maidata gidanta, to yanzu ina zata kai Hajja, da ace da ne dama gidanta kawai zata tafi da ita amma yanzu ba da bane, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi ta rasa tunanin da zata yi kuma, tana kallon mai adaidaita sahun kawai ta gaya masa unguwan Maheer tace "Can zaka kai mu kawai" kafin su karasa ta kira Maheer, yana dagawa tace "Kana ina ne?" Maheer da har a sannan ya kasa motsi yana rike da takardan da Abba ya basa cike da karfin hali yace "Gida" Ammi tace "Wani gidan, mu gashi muna hanyar gidanka da Hajja yanzu tace bazata koma gidanta ba, ya za ayi da makulli?" A hankali yace "A bude gidan yake" Ammi ta katse wayar, wato bazai ma tambayeta ya aka kare ba, a haka suka isa gidansa ranta a bace, babu wanda ya nuna concern din abinda aka yi ma Hajja daga shi har uban nasa, suna shiga parlon Hajja ta zauna kan kujera ta fashe da sabon kuka, cike da damuwa Ammi tace "Don Allah kiyi hakuri Hajja" Cikin kuka Hajja tace "Ni abinda ya ban takaici da aka ki bin ba'asin ma abinda ya hadasu tun asali, wllhi da muka shigo nan da Ladi shake Badiyyah matar tayi tana neman kasheta har Allah ya ba Badiyyar sa'a ta bugata da bango, da kuma Badiyyar bata yi haka ba da ta dade da mutuwa a hannunta wllh, yanzu da ita matar ce ta kashe Badiyyar sai ace yaya? Ban shiga uku ba idan hakan ta kasance me zance ma dangin ubanta daga sun bar min amanar yarinya? Ashe matsiyaciya ce matar Maheer duk bamu sani ba tace Mayraah kaza, Mayraah kaza, Mayraah ta zageta, Mayraah ta ci mutuncinta, Mayraah ta tara mata kawaye a gida ita da kawayen su yi ta shewa, bayan ni dai nasan ba tarbiyyar da muka yi ma Mayraah ba kenan, yarinyar da kowa ya shaida nutsuwarta amma azzalumar matar nan ta dinga mata sharri tana kawowa kunnenmu, to wallahi Maheer ya gama zama da ita har abada kuwa, muna zaman zaman mu lafiya ta shigo ta tarwatsa mana Pamily, ta lalata komai, ashe ita ce ibilishiyar cikinmu daga aurota ko wata uku ba ayi ba ta tarwatsa komai, idan an bibiya wllhi ita ta dinga zuga Badiyyar ma take ta kawo wasu mugayen maganganu kan Mayraah, don da ai ba haka Badiyyah take ba, to yaushe ma ta zauna dindindin a kano balle ta shiga sabgar Mayraah har tace ta mata wani abu, tsakaninsu fa gaisuwa kawai ba wani shiga harkan juna suke ba duk mun sani, suna zaune lafiya kuma, Tun a sannan sai abun yayi ta daure min kai don nasan Mayraah dai da na sani a baya ba haka take ba, amma sai nake tunanin canzawa tayi kawai don ta gano ba mune asalin jininta ba bari ta gwada mana halin ɗan Adam, ashe shegiyar matar Maheer din nan ce duk ta hada komai, duk ita ce ta hada fitinar nan ta rikita mana komai, to da yake Allah me gafara ne sai gashi cikin gaggawa asiri ya tonu tun bamu shiga hakkin Mayraah ba, to wallahi sai Maheer ya saki annobar nan, ya rubuta mata takardanta kawai a gadon asibitin ya bata ba sai ma anje da nisa ba, a duk duniya babu cin mutunci da ya wuce wanda dangin Haseenah suka min yau don har in koma ga mahaliccina bazan manta ba wallahi, da mutuncina da girmana wai yau ni aka saka cikin motar yan sanda" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta ci gaba tana cewa "Wai fa a haka Allah ya rufa mana asiri an dauke Mayraan daga nan gidan bata kasheta ba, a yanda naga ta shake Badiyyah wllhi zata iya kisa matar, Allah dai shi yasan dalilin faruwan komai wallahi" Ammi dai kanta na kasa duk tana sauraron Hajja, lokaci daya hawaye ya kawo idonta, Hajja na share idonta tace "Duk ma abinda kika ma Mayraah ai er ki ce halaq malaq babu me ce maki don me tun da ba shi ya maki rikonta ba ya sha wahala da ita har zuwa yau, kuma 'ya bata fushi da uwarta koma me zata mata dole dai uwarta ce bazata canza haka ba, nakudarta ne kawai baki yi ba amma babu wanda ya kai ki sanin zafinta, ba kuma wanda zai nuna maki ya fi ki sonta daga 'ya yan naki har uban nasu, shi kuma Mamuda dama can da niyyar aurensa kece kawai baki sani ba, a yawace yawacensa ya samo Bazawararsa suke tadi ke kina gida kin saki baki, shine da ɗan matsalan nan ya faru yayi maza ya aureta ya fake da matsalar, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yana da niyyar auren ya dai rasa yanda zai gaya maki ne, ni fa ba yarinya bace" Ita dai Ammi bata ce komai ba kuma har sannan bata dago kanta ba, hawaye kawai ke zuba idonta, Hajja ta cire dankwalinta ta share hawayen fuskarta tace "A samo min ruwan zafi in je inyi wanka in hadiyi panadol, wallahi duk jikina ciwo yake" Ammi taji baza ma ta iya shiga kitchen din ba, banda lalura me zai kawota gidan matar Maheer har ta zauna, rabonta da gidan tun ba a gama gini ba almost a year ago da ya kawota ta gani, ta dau wayarta ta mike ta fita balcony hawaye na sauka idonta ta sake dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga, sai da tayi controlling kanta sannan ta iya cewa "Ka taho da Mayraah" Duk da Maheer ya ji ta ya kasa ce mata komai, kuma yana dai dai gate din gidansa ta kirasa, bude gate din yayi Ammi na ganinsa ta katse wayar, zata juya ta koma parlor kira ya sake shigowa wayarta ta duba taga Abba ne ke kiranta, sai da gabanta ya fadi don wata daya kenan rabon da kiransa ya shigo wayarta, ta daga kiran ta kai kunne ba tare da ta ce komai ba.
[7/15, 5:30 PM] Khaleesat Haiydar💖: Abba yace "Na kira ne in sanar maki burin ke da danginki ya cika a kan Mayraah, You and ur relatives have succeeded into pushing her, dama duniya ae kuke so ta shiga ko? To hakan ya faru sai ku zuba ruwa ƙasa ku sha..... amma ina son ki sani, idan wani abu ya samu yarinyar nan a duk inda take bazan taɓa yafe maki ba, i will never forgive u, duk halin da ta shiga ke da danginki ne sila saboda selfishness dinku, alhaki a kanku kuma ina me tabbatar maki Allah bazai bar ku ba....." Abba na kai wa nan ya katse wayarsa, Ammi dai ta ƙame a inda take tsaye as if trying to assimilate all what Abba is saying, after few second da katse wayar da Abba yayi ta juya a hankali tana kallon Maheer da ya iso balcony din, Har a lokacin bata cire wayarta a kunne ba, tana kallon Maheer ko kiftawa babu cikin karfin hali tace "Ina Mayraan?" Maheer bai yarda sun hada ido da ita ba ya mika mata takardan hannunsa, Ammi ta amsa da sauri tana duba takardan, lokaci daya ta juya ta koma parlor gun Hajja ta durkusa gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta gigice ta mike tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, lafiya? Me kuma ya sake faruwa?" Takardan hannun Ammi ta amsa a rikice tana jujjuyawa tace "Ko sakin ki Mamudan yayi??" Ammi dai ta kasa cewa komai sai kuka take uncontrollably, Hajja ma ta fashe da kuka gashi ita ba iya karatu tayi ba balle ta karanta takardan taga na menene, cikin tashin hankali tace "Ki bude baki kiyi min magana don Allah, sakin ki Mamudan yayi wai??" Ganin Maheer ya shigo Parlon Hajja ta nufesa da sauri jiki na rawa tana nuna masa takardan tace "Maheer takardan meye wannan din?" Maheer yayi shiru yana kallonta da farko, can yace "Mayraah ce ta rubuta" Hajja tace "Mayraah kuma? Na meye to?" Maheer yace "Ta tafi" Hajja ta zaro ido tana kallonsa tace "Ta tafi? Ta tafi ina?" Maheer bai bata amsa ba ya juya ya fita daga parlon ya koma balcony ya tsaya, Hajja ta dawo da sauri tace "Ina wai Mayraahn ta tafi Ammi?" Cikin kuka Ammi tace "Allah ya gani ko 'ya yan cikina ban gwada masu son da nake ma Mayraah ba, ban taɓa mata kallon ba ni na haifeta ba tunda Allah ya bani ita, kallon jinina nake mata, soyayyar uwa da ɗan ta nayi mata....." Ta kasa ci gaba saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajja ta zauna kan kujera ta rasa abun cewa, can ita ma ta fashe da kukan ta daga hannu sama tace "Allah mun gode maka, wannan wani irin fitina ne ke ta billo mana ni Sadeeyah daga wannan sai wannan? Wa ta sani a duniyar da har zata ce ta tafi? Ta tafi ina? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya tsine ma wannan mata ta Maheer duk ita ta jagwalgwala al-amarin nan, muna zaman mu lafiya ya auro annoba ta tarwatsa mana farin cikin mu, yanzu ita kanta Badiyyar bamu san inda ta tafi ba bamu san wani hali take ciki ba, ga Mayraah ma wai ta tafi, ta wa ta sani da zata ce ta tafi?" A ranan Abba ya maida Hajiya Amina sabon gidansa da ya gama ginawa har yayi furnishing not long ago a Miller road, he wanted to take Ammi by surprise, don ko su Maheer basu san da gidan ba balle ita, kawai rana daya yayi niyyar ce masu su shirya za su fita kawai sai ya kai su gidan daga nan kuma sai tarewa ba lallai ma su koma tsohon gidan ba, don shi ma a yanzu yana son barin anguwan da ya taso ya koma area with full security ya zauna, tsohon gidan nasa kuma ya saka cousin dinsa da matansa uku don kar gidan ya kasance babu kowa, Chalet kuma dama wani makocinsu dake biyan kudin haya da kyar don yawanci shi ke biya masa kudin hayan ma duk shekara, to shi yayi niyyar ba ma chalet din da matarsa da yaransa su zauna, to a yanzu kam ya ji zaman gidan ya fita ransa, tafiyar Mayraah ba karamin daga masa hankali yayi ba da distablizing dinsa, he wish zata canza tunani ta dawo gida don bata da wani gata a duk inda ma zata je yanzu, ya kuma san he tried his best, yayi bakin kokarinsa na ganin she wasn't traumatized or felt dejected with all what was happening, yayi iya kokarinsa all through the Saga but all his effort prove abortive, yasan da Ammi bata mata abinda tayi mata ba koma me zai ci gaba da faruwa bazata bar gida ba, baya jin zai iya yafe ma Ammi da ahalinta gaba dayansu, ba don yaranta ba babu abinda zai hanasa tura mata text kar ta dawo masa gida don har cikin ransa yaji baya ma son ganinta, amma bazai yi hakan ba ko don albarkacin su Maheer, don haka gwara kawai ya bar mata gidan kawai, daga ita har yaran nata. Karfe bakwai da rabi bayan gari yayi duhu Maheer ya kai Hajja gidanta, Throughout hours din da suka yi gidan Maheer kuka kawai Ammi take regretting so many things, kana ganinta kasan ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, she never expect things to go this way, ba kowa ya ja mata duk wannan abun ba sai Hajja da take kokarin ganin ta rabu lafiya da, pressure din Hajja duk shi ya ja mata wannan abu, she was only trying to please her mother in so many ways kar su samu matsala, Hajja kam ba bakin magana amma ta tsine ma Haseenah ya fi a kirga, ta rantse ta kuma rantse Maheer bazai ci gaba da zama da annoba, Abincin da ya fita ya siyo masu ma duk basu ci ba saboda babu kwanciyar hankalin ci, Maheer na maida Hajja gida ganin Ammi zata sauko daga motar Hajja ta kalleta tace "Ina kuma zaki kike kokarin saukowa?" Cike da karfin hali Ammi tace "Me zan koma gidan in yi Hajja? Babu amfanin komawata kawai" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Hajja tace "Ni kuma me zaki shigo min nan kiyi, ni fa ina ji a jikina babu inda Mayraah ta tafi in ma zaki kwantar da hankalinki, ki kwantar da hankalinki ki dukufa da addu'a ba ji ba gani wallahi zata dawo, babu abinda kukan nan zai kara ki da shi sai ma ki ja ma kanki wata cutar dama ke ba lafiyayya ba yanzu, kwanaki ma ba haka ta dinga yi ba da aka fasa auren kuma daga baya sai ta dawo, duk bacin rai ne da rashin madafa ba wai wani abu bane yasa tace ta tafi, tunda ita kanta tasan bata da inda za ta, bata da kowa da ya wuce mu, ai yarinya ce me hankali Mayraah, ina da tabbacin kilan gidan kawayenta ta tafi ta samu nutsuwa na ɗan lokaci, amma in sha Allahu zata dawo komin dare, ke kin taɓa ganin inda ɗa ya guji iyayensa komin laifin da suka masa? To ki sa ma ranki salama ki koma dakinki ki samu kuyi shawaran yanda za a fara cigiyarta a gun yan makarantarsu ke da mai gidan ki, wannan kawar tata da kika kira daxu ai ba ita kadai bace kawarta, kilan wajen wata daban taje, kar ki biye abinda Mamuda ya maki ki samesa a san na yi tun dare bai tsala ba, in sha Allahu Mayraah tana nan gun kawayenta, nima yanzu ina shiga zan buga lamban yan bichi in ji ko Badiyyah ta je can ko hankali zai kwanta, amma Mayraah kam nutsuwarta da sanin ya kamata ma bazai sa ta tafi wani waje ba, tana nan kusa da mu in sha Allah" Hajja na kai wa nan ta bude gidanta dake bude har sannan ta shiga ciki a hankali tana cewa "Wai ni yau da mutuncina da girmana aka kai Caji opis" Sai kuma ta fashe da kuka ta kulle gidan. Maheer ya bar anguwan bayan sun ajiye Hajja, tun dazu ko magana bai yarda ya hadasa da Ammi ba balle ya bata hakurin kukan da take, to me ma zai ce mata.
Wajen karfe tara Mayraah ta farka daga baccin da take, it was still raining but not heavily, zuwa sannan zazzabi ne sosai jikinta, ta daure ta sauka daga kan gadon ta lallaba ta bude jakarta ta ciro wani hijab ta saka sannan ta dau Atm card dinta, tana tafiya a hankali ta bude kofar dakin ta cire makullin sannan ta fita ta kulle kofar ta sauko kasa, reception din hotel din ta nufa cike da karfin hali tana kallon receptionist din tace "Plss where can i locate...." Kasa ci gaba tayi ta dafe kanta, receptionist din ta zagayo inda take da sauri ta riketa ganin tayi baya zata fadi tace "Are you okay Madam?" colleague din receptionist din shi ma ya taho da sauri suna mata sannu, Mayraah dai gyada masu kai kawai, receptionist din ta karasa da ita inda kujera yake ta xaunar da ita kan kujera tana kallonta, sauran ma'aikatan wajen ma duk suka taho suka tsaya kan su, Receptionist din tace "Amma baki da lafiya ko?" Mayraah ta kasa bata amsa sbda sarkewa da breathing dinta ya soma yi, nan duk suka rikice aka fara mata fifita duk da sanyin gari, wata worker din wajen na cewa ko dai a tafi da ita asibiti don babu wani tanadi incase of such emergency a hotel din, Wani mutumi ne ya shigo Reception from upstairs zai fita waje, ya tsaya ganin yanda ma'aikatan hotel din suka taru waje daya sai fifita suke ma Mayraah, ya karasa inda suke yace "Hope all is well?" Wani ma'aikaci yace "Bata da lafiya ne muna jiran za a dauko makullin mota a tafi da ita asibiti" Yace "Subhanallah, why not mu tafi asibitin since i am with my car key, i am going out now" Yana fadin haka ya tsaya gaban Mayraah yana kallonta yace "Sannu, are you Asthmatic?" Mayraah bata ma san yana yi ba don zuwa sannan double take ganinsu gaba daya, da sauri ya kalli receptionist din yace "Ku fito da ita kawai, mu tafi asibitin" Yana fadin haka ya fita in a haste don tada motarsa dake parking space, receptionist din suka tafi da Mayraah motar tasa, ya bude masu back seat, ma'aikaciyar hotel din daya ce ta shiga motar tare da Mayraah za su tafi asibitin bayan ta amshi Atm din Mayraah dake hannunta kar ta yar, makullin dakin kuma ta ba colleagues dinta su mayar cikin hotel din, tuni ya ja motar suka bar haraban hotel din bayan an bude masu gate. Mutumin na driving din ya kira wani abokinsa yana dagawa yace "Hello Dr kana hospital ne?" Sai kuma yace "Ohk, to dama emergency ne, wata baiwar Allah ce bata da lafiya muna hanyan asibitin yanzu" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah ta bude idonta after an hour a asibitin, ido hudu tayi da receptionist din dake zaune ward din ana jiran tashin Mayraah don ta kira yan uwanta kafin ma'aikaciyar ta koma hotel bakin aikinta as instructed by the hotel manager, matar ta sakar ma Mayraah murmushi ta mike tace "Sannu fa" Mayraah ta mike zaune da kyar tana bin ward din da kallo, it's so big and clean, daga gani kasan ba karamin asibiti bane ko daga gadon da take kwance zaka gane hakan, Receptionist din tace "Bari in masu magana ince kin tashi...." Daga haka ta fita daga babban ward din, Mayraah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Cctv camera dake ward din, maida dubanta tayi kan drip da aka makala mata a hannu, dai dai nan aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, wani mutumi ne ya shigo tare da wani dake biye da shi a baya with white lab coat da stethoscope a wuyansa, ita dai duk kallonsu take har suka iso bakin gadon da take, mutumin da ya fara shigowa dakin ya ɗan duka ya dafa gadon yana kallonta yace "Baiwar Allah ya jikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Likitan ya karaso ya kara gudun drip din kafin shi ma ya kalleta yace "Hope you are feeling much better now?" Tace "Sure" Yace "To Maa sha Allah" Receptionist din tace "Manager yace ta kira yan uwanta sai ni in koma bakin aikina" Sosai gaban Mayraah ya fadi, likitan yace "Eh gaskiya ne, ai kun ma yi kokari for such hospitality" Sai kuma ya kalli Mayraah yace "Ki kira yan gidanku yanzu ki sanar masu kina asibiti" Da sauri tace "Ai wayar na dakin hotel din" Mutumin da ya kawota hospital ya ciro wayarsa ya mika mata yace "Za ki iya amfani da nawa" Sosai gabanta ya fadi, ta amshi wayar tana tunanin yanda zata yi, nan da nan dubara ya fado mata tayi dialing din layinta dake kashe ta sa handsfree, duk suka dinga kallonta jin switch off, a hankali tace "Number Abbanmu ne, bari in kira yayana" Daga haka ta sake dialing other line dinta nan ma aka ce switch off, Mayraah ta kalli receptionist din tace "Za ki iya tafiya, Nagode sosai, nasan zuwa anjima zan samesu a waya" Receptionist din tace "Toh Allah ya kara lafiya, ga Atm

Please Login or Register in order to submit comment