You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya halicceka, in mutum ya sa wannan a rai to babu ta yanda za ayi masa mugun abu, ke kawai baki da aiki sai zuwa gun makaryatan banza marasu tsoron Allah" Mama Ladi ta saki baki tana kallonsa, a fusace tace "Kar ka sake gaya min maganar banza Mashir, kai wawa ne baka san komai ba baka san me duniya ke ciki ba, kuma laifina ne don wannan zancen ma ba da kai ya kamata in yi ba don kai ba sa'ar magana ta bace, tsinanniyar matar nan taka dai ita ta saka wannan mugun abu a dakin Ammi, shi yasa duk abubuwa suka cakude haka" Maheer ya kai hannu zai dau layan ta janye parkern da sauri tace "Rufa mana asiri, ni nasan inda zan kai sa, ni kaina bazan bari hannuna ya taɓa ba" Can dai yace "To meye manufar layan da aka sa kasan gadon kenan?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "A rabata da Mera ta tsaneta taji bata sonta kwata kwata, sannan kuma a tarwatsa mata gidanta ta dawo bora, kaga kuma yanzu tsakani da Allah wanne ne bai faru ba? Rabata da Meran ko tarwatsa gidan? Wai ma ina Mamuda don na tambayi Ammin tace min bata sani ba dazu" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ya koma can wani gidan da ya gina da matar" Mama Ladi ta gwalo ido ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani gidan da ya gina? Amma ga dukkan alama matar ma matsiyaciya ce shaidaniya, zuwa kawai tayi ta mallakesa ta rabasa da Ammin, kai shegu dai sun yi yawa wallahi a duniya, yanzu ka gaya ma Ammin suna wani gida da katuwar matar?" a hankali yace "Ban gaya mata ba" a hankali Mama Ladi tace "To ka ja bakinka kayi shiru kar hankalinta ya sake tashi don naga ɓatan Mera ya gigitata gaskiya, kar ka kuskura ka gaya mata" Wayarta ta kunce a ɗan kyalle da ta cusa cikin hulan kanta ta mika masa tace "Kira min Mamudan" Maheer ya dinga kallonta, a fusace tace "Kira min shi mana" Amsan wayar yayi, yayi mata dialing number Abba sannan ya mika mata, ta amsa ta kai kunne, yana fara ring Abba ya daga, da karfi tace "Mama Ladi ce Mamuda..." Gaisheta Abba yayi, tace "Don Allah ina son ganinka yau na shigo garin" Yace "Toh sannu da zuwa Mama, zuwa gobe kenan idan Allah ya kai mu" Mama Ladi ta girgiza kai da sauri tace "Wani gobe? A yau nake son ganin ka Mamuda" Yace "Toh zan sa Maheer ya kawo ki inda nake" Mama Ladi tace "O'o ba ruwana gaskiya kawai ka shigo mota ka taho ina nan gidanka yanzu haka gani ni kadai zaune a parlor ba kowa" Abba ya dan yi shiru, sai kuma yace "To gani nan zuwa" tace "Yauwa ina jiranka" Daga haka ta katse wayar tana kallon Maheer tace "Ai kaga ni ba er banza bace da zan je in samesa a wani sabon gida bayan yayi watsin ruwan tsarki da 'ya ta" Shi dai Maheer bai ce komai ba. Maheer na barin gidan da minti arba'in Abba ya shigo wajen karfe tara da rabi kenan, Har sannan Mama Ladi na zaune parlon tana jiransa bayan ta gama cin abincin da Maheer ya kawo mata daxu, Abba na shigowa ya gaisheta da ladabi sannan ya zauna kan kujera yace "Ya hanya Mama?" A hankali Mama Ladi tace "Kai yanzu Mamuda so kake ranan gobe kiyama ka tashi da shanyayyen ɓarin jiki? So kake duk mu tafi aljanna kai kana wuta? Auren da har yanzu bamu gama na'am da shi ba a zuciyarmu shine har ka fara rashin adalci a cikinsa Mamuda? Ita Ammin ka gama cin moriyarta ta zama bola kenan yanzu kake nufi?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Ko me Ammi zata maka a duniya bata cancanci walakanci daga gareka ba Mamuda, balle baiwar Allahn bata taɓa maka komai ba sai biyayya da girmamaka tun kana talakan ka, sai yanzu don kaga ka rasa yanda zaka yi da kudi sai ka canza hali ka kasa hakuri da ɗan kuskuren da ta maka? Ko ka mance ɗan adam ajizi ne? Ammi ta taɓa maka wani gagarumin laifi duk zaman ku tare tsakaninka da Allah?" Abba yace "Yanzu tace maki na mata wani abu ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Kayi mata mana, sai ta fada sannan za a san ka mata? don me za ka dau bazawarar da ka aura sama ta ka, ka kai ta sabon gida ku tare a can Ita kuma ku bar ta a nan?" Abba yace "Ai ni ban san tana gidan nan ba ma" Mama Ladi tace "Kai dai kaji tsoron Allah kaji tsoron kamun Allah Mamuda, wallahi kaji tsoron Allah ina gaya maka" Abba yace "Yanzu tun da nasan tana gidan duk ranan kwananta zan shigo gidan in kwana a bangarena" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Haba Mamuda, don Allah kayi hakuri.... wallahi ni kaina nasan Ammi tayi kuskure nasan bata kyauta ba amma duk sharrin shaidan ne, kai shaida ne mutuniyar kirki ce Ammi, babu sa wa babu hanawa, kar ka yi mata mummunan hukunci saboda wnn ɗan kadɗarar ya fada mata, wallahi kaddararta ce wannan, amma kai kanka kasan duk bamu fi ta son Mera ba, kayi hakuri ka dubi halin da take ciki ka ja ta jiki ka maida komai ba komai ba har Allah ya dawo mana da gantalalliyar yarinyar nan da ta tafi inda bamu sani ba dama kuma ta saba shiga duniya da er matsala ta faru, Wallahi Ammi na cikin mawuyancin hali yanzu a kan batar yarinyar nan, da wanne kake so ta ji, ga kishiya ka dankara mata Mamuda?" Abba dai yayi shiru bai ce komai ba, Cikin lallami Mama Ladi tace "Nasan ka da hakuri da kauda kai Mamuda, kayi hakuri yanzu ka tafi sama ka duba halin da take ciki sai ka ga ta samu nutsuwa a ranta, babu bawan da ke wuce kaddararsa wllhi, babu tsimi fa babu dubara sai wannan abu ya faru Mamuda" Abba yace "Shikenan Mama, zan duba ta" Mama Ladi tace "Yauwa ko kai fa ɗan albarka, ai haka ake son babba ya gaya ma yaro magana ya ji, ni wallahi ka gama min komai wannan mutunta ni da kake yi" Mama Ladi tace "Yanzu sai ka tashi ka tafi sama ka dubata, ni kuma zan je kitchen in nemi abinda zan ci kar yunwa ta kasheni" Mikewa Abba yayi ya wuce sama zuwa bangaren Ammi.
[7/17, 10:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari da safe Mayraah ta sake komawa gun me pos din a tasha, kamar jiya ma yau Nose mask ta saka don gaba daya a tsorace take da Abujan gani take kawai zata yi jamming wanda ta sani, wajen karfe goma da rabi ta isa shagon nasa, bayan sun gaisa yace "To yanzu zan bar yaron shagona ya jire min shagon sai mu kama hanyar sulejan ki ga gidan Hajiya...." Mayraah tace "Toh shikenan, nagode" Mayraah bata yi tunanin haka Sulejan ke da tafiya daga cikin Abuja ba, don har bayan minti arba'in bata ga sun isa ba, though is not as if she cares about the distance tunda babu abinda ma zata dinga shigowa garin Abujan tayi, at last dai suka iso garin Suleja ya tare masu adaidaita sahu suka tafi anguwan da yace mata gidan yake, anguwar dai ba laifi amma duk yawancin gidajen unguwan na average class ne har ma da lower class, suna isa gidan da aka kama mata bayan ya shiga da ita ko ina tare da wani agent sun nuna mata suka fito compound din gidan yace "Toh ya kika ga gidan ya maki kuwa Hajiya?" Mayraah da bata da choice kawai tace "Eh yayi" Agent din ya bata makullin gidan da reciept din payment ta saka a handbag dinta, bayan ya tafi Mutumin da ya kawota yace "Kin ga ai anguwan bata da hayaniya ko? Ga shi kuma a cike yake da jama'a" Mayraah tace "Haka ne, yayi kam" Yace "Kuma gidan kin ga sabo ne dal bai da matsala" Mayraah tace "Eh duk na gani, amma kasan abinda zai faru? Don Allah idan baza ka damu ba ina son in baka list din wasu abubuwa ka taimaka min ko a kasuwan garin nan ne ka siyo min, gobe nake son zan dawo gidan gaba daya" Yace "Toh babu matsala kamar me da me kenan kike bukata" Nan Mayraah ta zayyane masa duk abubuwan da zai siyo mata a kasuwa na bukatar gida har da kayan abinci, ta mika masa Atm card dinta yace "Aa Hajiya, da dai kawai ki min transfer" Tace "Kar ka damu, bana iya transfer ne shi yasa" Yace "Toh amma fa mantuwa gareni, kyau kawai muje kasuwan tare Hajiya" Ta ɗan yi shiru tana nazari, sai kuma tace "Toh shkkn mu tafi" Tricycle suka samu zuwa kasuwan. kafin yamma Mayraah ta siyi duk wasu abubuwan da tasan zata bukata a gidan tare da mutumin da yace mata sunansa Aminu, har gas da few kitchen utensils sai da ta siya, da labule da aka dinka masu sharp sharp a kasuwar suka siya da karafen labulen, wajen karfe biyar da rabi tana kallon Aminu bayan ya gama saka mata labulen karshe tace "Gaskiya Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajiya, amma yanzu abinda zai faru ya kamata ki ɗan shiga makotanki ku gaisa su sanki ki ce masu ke daliba ce, yau kika dawo unguwan, kinsan yanzu yan sa ido sun yi yawa a duniyar kar su yi zaton ko zaman kanki kike a nan bayan basu san karatu ya kawo ki garin ba" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace "Haka ne, zan shiga in sha Allah amma sai gobe idan na dawo nan din gaba daya, yanzu na gaji ina son mu koma Abuja ne in hutu sannan in harhada kayana na can" Yace "To ba laifi Hajiya, in dai da wani abu da kike bukata ko na aike koma na menene kawai ki buga wayata, in kin dawo nan din gaba daya har iyayena zan hada ki da su da matana duk da dai gaskiya anguwansu da nisa daga wannan anguwan, sai a dinga zumunci" Mayraah na murmushi tace "Toh shkkn, in na dawo din duk sanda kake da lokaci ko kuma in ka shigo garin sai ka hadani da su" Yace "In sha Allahu kuwa, Allah kuma ya baki sa'an abinda kika zo nema" A hankali Mayraah tace "Ameen nagode" Sai kusan shidda da wani abu suka shiga garin Abuja, Mayraah tayi tayi da shi ya tsaya ta ciri kudi a wajen wani me pos ta basa yace mata wllhi wanda ta basa ma ya isa saboda Allah yayi mata, taji dadin hakan har ranta, she really appreciate him, ta samu adaidaita sahu da ya maida ta hotel don duk ta gaji. The next day Mayraah tayi check out daga hotel din ko kwanakin da aka biya mata bai cika ba ta koma sulejan wajen karfe sha daya na safe, zaunawa tayi a gefen gadon dakin tana bin ko ina da kallo, tun barin ta gida sai yau kawai taji tunanin yayyinta ya cika zuciyarta, ita kanta tasan tana kewansu, this made her feel so down tun safe take jin ranta babu dadi, lokaci daya ta ba kanta courage ta shiga kitchen ta dafa Indomie wanda har ta mance rabon da ta ci Indomie, kamar yanda Aminu yace mata gidan kam da wuta don har suka gama abubuwan da suke yi jiya ba a dauke wuta ba yanzu ma gashi da ta zo ta tarar da wuta, ta jona wayarta a caji sannan ta saka hijab ta fito zata yi yanda Aminu yace mata, karamin gidan dake gefen nata ta fara kwankwasa gate din aka bude, matar gidan na kallonta daga sama har kasa tace "Sannu da zuwa" Mayraah tace "Ina kwana" Matar ta amsa still tana kallonta irin ban sanki din nan ba, Mayraah tace "Ni neigbor dinki ce, jiya na dawo wancan gidan..." ta fadi haka tana nuna gidan, Matar tace "Ayya, Allah sarki, bismillah sannu da zuwa baiwar Allah, ai ko naji yan anguwa sun ce an tare a gidan ni dai ban ga kowa ba, ashe kuwa da gaske ne" Mayraah dai ta bi ta har cikin gidan ta zauna kan kujera a karamin parlon ta kara gaisheta, matar ta amsa da fara'a tace "Sannu da zuwa anguwanmu, ya sunanki?" Mayraah bata san sanda tace "Ilham, sunana Ilham.... ni daliba ce ina karatu ne cikin garin Abuja, shine aka samar min daki a nan in zauna" Matar tace "Allah sarki, toh Allah ya baki sa'a Ilham, ai ko zaki ji dadin zama cikinmu wallahi duk bamu da matsala, ni ana ce min Maman Hanan, yanzu zan zaga dake duk sauran gidajen a san juna" daga haka ta mike tace "Bari in dauko maki ruwa ki sha sai mu tafi" Mayraah dai sai kallon yarinyar dake kwance da bazata wuce shekara 8 ba tana numfashi ta baki take, har matar ta dawo Mayraah ta kalleta tace "Bata da lafiya ne yarinyar can?" Matar ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi Hanan ba lafiya yau kusan sati daya ko makaranta bata zuwa, tun dazu ma nake ta goge mata jiki da ruwan sanyi don naji zafin yau na daban ne da sauran ranaku, gashi zazzabin baya sauka wallahi" Da mamaki Mayraah tace "Kuma ba a kai ta asibiti ba har yanzu Aunty?" Maman Hanan tace "Baban magunguna ya siyo mata a chemist ake ta bata, wanda ya fara siyowa har sun kare ya sake siyo wasu" Mayraah couldn't stop looking at the woman with surprise, a ranta tana mamakin me yasa wasu iyayen ke irin wannan sakacin ace yaro bai da lafiya critically amma sai a wani je chemist a siyo masa magani, mikewa tayi ta tafi kusa da Hanan din ta durkusa tana kallonta don ko rufe baki bata iya yi kamar warce mura yayi ma mummunan kamu, and she is breathing noisily, Mayraah ta bude bakinta tana duba ciki, lokaci daya ta mike tana kallon Maman Hanan tace "Ya kamata a tafi da ita asibiti yanzu Aunty" Da damuwa Maman Hanan tace "Ko?" Mayraah tace "Gaskiya, a nemo adaidaita sahu a tafi asibitin kar a bata lokaci" Wani irin numfashi Hanan din ta fara yi, Maman Hanan ta maza ta dauketa tana jijjigata tace "Haka fa take yi tun dazu sai numfashin yayi kamar zai dauke wllh sai ya dawo, bari in kira baban nasu" Mayraah tace "Mu je kawai asibitin idan mun je can sai ki kirasa" A tare suka fita gidan, Maman Hanan duk ta gigice ko kulle gidan bata yi ba suka nufi titi, Mayraah dai bata karbi yarinyar a hannunta ba, a haka suka samu adaidaita sahu, wani Asibiti nesa da Sulejan Maman Hanan ta sa mai adaidaita sahun ya kai su, duk tunanin Mayraah zata ga babban asibiti saboda taga wajen da ɗan tafiya daga suleja, kawai taga clinic, though ba laifi kamar clinic din sananne ne don taga patients da yawa amma bata tunanin the clinic is well equipped suna isa entrance din clinic din basu fara karo da kowa ba sai Dr Khalil yana kokarin fitowa rike da makullin Motarsa, kallon mamaki yake ma Mayraah kamar yanda ita ma take kallonsa da mamaki, Maman Hanan ta saki ihu don taga kamar numfashin er yayi sama bai sake dawowa ba, Dr Khalil ya saka makullin motarsa a aljihu da sauri ya amshi Hanan din a hannunta ganin condition din da ta shiga ya juya ya koma cikin asibitin sauran nurses suka nufosa, Mayraah ta bi bayansa da sauri har ta isa dai dai wajensa tayi kasa da murya tace "I think it's Diphtheria, symptoms din ne..." Da sauri ya juya ya kalleta, ya kalli yarinyar hannunsa, amma saboda babu lokacin batawa kawai ya shiga da ita emergency dake reception wani likita da ya fito office ya bi bayansa da sauri, Mayraah ta koma gefe ta tsaya Maman Hanan kuwa sai kururuwa take a reception din nurses na bata hakuri, Dr Khalil na shiga emergency din kawai abinda Mayraah ta fada yasa hankalinsa bai kwanta ba ya saka safar hannu, da few protections sannan ya fara gwaje gwaje, nan ya tabbatar da abinda Mayraah ta fada haka ne, Likitan da ya shigo wanda shine me asibitin shi ma ya koma baya closing his nose with nose mask ya buda ido sosai yace "Diphtheria, wannan sai dai a tafi da ita Abuja Dr.... Babu facilities a nan" Dr Khalil bai cire protective gown din jikinsa ba ya dau yarinyar ya fita daga emergency din, kawai ya nufi motarsa Maman Hanan ta bi sa a guje tana cewa "Ina za a kai ta Dr?" Ya kalli Mayraah dake tsaye ta kasa cewa komai yace "Ki taho da ita asibiti can Abuja" Daga haka ya shiga motar da likitan suka zuwa cikin Abuja, Mayraah har gajiya tayi da lallashin Maman Hanan a hanya har suka karasa Abuja, bata mance sunan asibitin ba wanda is so popular duk da asibitin masu kudi ne, suka hau adaidaita sahu ya kai su har asibitin, Sun fi minti ashirin zaune a katon reception din hospital din, bakaken fata da fararen fata sai kai koma suke a reception din, everywhere is just so organized kamar a kasar waje, suna kuma da lokacin zuwa duba mara lafiya ba anyhow ake shigowa ba, Mayraah ta kalli Maman Hanan for the countless time tace "Maman Hanan kiyi hakuri da kukan nan addu'a kawai za kiyi mata, in sha Allah zata samu lafiya kin ga nan babban asibiti ne" tausayinta kawai Mayraah take don ta san ko da an kwantar da Hanan to ko ita baza a bari ta zauna da ita ba sbda infection din is contagious, don su inda ake kwantar da masu cutar ma daban ne ba kowa ke shiga ba sae ma'aikatan asibitin, After another 20 minutes wata nurse sanye da cute uniform dinta ta nufosu tana kallon Mayraah da turanci tace likita na bukatarta a office, Mayraah ta mike tana kallon nurse din ita ma da turanci ta tambayeta ina office din, Nurse din tace "First floor, office number 1, Dr Khalil" Mayraah tace "Ohk" Maman Hanan ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Tare za mu je?" Mayraah tace "Aa ki jira yanzun nan zan fito ai" Daga haka ta wuce sama ta isa har office number din da nurse din tace mata tayi knocking, sai da aka mata izini ta shiga, the office was large and organized, ko ina fes fes ga Ac a kunne, yana zaune kan office chair dinsa ya canza kaya alamar har yayi freshen up, ta karasa har front din table din ta zauna tana kallonsa tace "Dr ya jikinta?" Ya kalleta yace "Ina mance sunanki, pls remind me" A takaice Mayraah tace "Ilham" Yace "Ilham, how did u know it's Diphtheria?" Ta ɗan buda ido thinking of what to say sai kuma da sauri tace "Na taɓa koyon aiki a wani karamin asibiti" Yace "Really, kina da experience kenan in haka ne" Ta ɗan yi murmushin karfin hali bata ce komai ba, yace "Kin samu hostel din?" A hankali tace "Aa ina wajen aunt dina a suleja" Yace "What about ur parent" Tayi shiru tana kallon sa, kawai ta samu kanta da cewa "They are late" Ya ɗan sauke kansa sai kuma yace "Allah ya ji kansu" Tace "Ameen" Yace "But idan baki samu hostel ba ai akwai off campus da zaki samu cikin gari, isn't suleja too far for you? Yayi nisa fa zuwa school din" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi shiru da ya tuna ba fa kowa ake haifa da silver spoon ba barin ita da tace iyayenta sun mutu, probably bazata iya affording off campus ba, can yace "Wani course aka baki admission yanzu?" Mayraah ta rasa ma me zata ce masa, can dai "Microbiology" Ya gyada kai yace "That's good, i guess ur Aunty isn't financially stable ko?" Nan ma kawai tayi murmushi, ya sauke ɗan ajiyar zuciya yace "Mu kinga nan ba a daukan health workers sai da Qualified medical certification, infact ba mu da vacancy ma yanzu haka, we are dealing with just qualified medical staffs don wasu daga likitocin mu ma turawa ne da indians, so i will see if it will be possible in san yanda zan yi inyi attaching dinki ko during weekend ne as an auxiliary Nurse don ki samu ki dinga fending for ur self kar ki sakar ma mutane burden dinki su gaji da wuri" Mayraah kallonsa kawai take da mamaki and she couldn't believe her ears, aiki a babban asibitin nan?? can tace "Zan ji dadi idan ka min haka" Yace "But fa dole sai ta bayan gida zan yi maki wannan abun don we have strict orders a asibitin nan...." Mayraah tayi shiru tana kallonsa, Calmly yace "Kar ki damu, i will try my best zaki fara aiki a nan in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sa, but i am sorry about that admission da nace na samu da naje makarantar ba haka bane" Yace "I don't get you" Ta sunkuyar da kai tace "An ban admission din da dadewa ne, sai yanzu muka tara kudin makarantar ban san ashe ba a haka ba, da naje makarantar shine suka ce anyi cancelling admission din long ago" Yace "Subhanallah" Daga haka bai sake cewa komai ba, ita dai kallonsa kawai take, yayi kasa da murya yace "Kar ki damu Ilham, zaki fara aiki a nan, and the salary is good sai kiyi ta saving ki sake sabon jamb ki nemi wani admission din" Ta ɗan yi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen" Da sauri tace "Plss ya jikin yarinyar??" A hankali yace "She is late already, before we could do anything" Mayraah da gabanta ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Yace "Ya ku ke da matar?" Nan da nan hawaye ya kawo idon Mayraah tace "Neigbor dinmu ce a Suleja" Yace "Sai hakuri, yarinyar ta rasu" Ta masa wani kallo tace "Shine tun dazu baka gaya min ba??" Mikewa tayi tana share idonta ta nufi kofa yace "Wait Ilham" Ta juya ta kallesa yace "Ce mata za kiyi nace ta bada number baban yarinyar ita kuma ku tafi gida a kawo ma yarinyar abinci, so i will communicate with the father, bama son ta hada mana commotion a nan" Cikin sanyin murya Mayraah tace "Sai dai nurses din su gaya mata ni bazan iya ba" Ya dau waya yace "I will tell dem now" Kiran nurses din yayi downstairs, Mayraah kuma ta fita a sanyaye.
[7/18, 8:04 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na tsaye gefe wata Nurse tayi ma Maman Hanan bayanin da Dr Khalil yayi mata a waya na cewar ta bada number mai gidanta sannan ta koma gida ta dauko ma Hanan kayan sa wa, ko minti daya Maman Hanan bata kara asibitin ba bayan ta bada number mijinta bata bi ta kan Mayraah ba ta fita da sauri zata koma gida, Mayraah dai ta bi ta da kallo ciki da tausayinta, tana tafiya a hankali ta nufi kofar fita reception din ita ma, Dr Khalil ya sauko downstairs kenan ganin Mayraah zata fita ya bi bayanta har suka fito haraban asibitin yace "Na kira mijin nata suna hanya yanzu haka..." Mayraah ta gyada kai tace "Toh, Allah ya ji kanta, Allah ya basu hakurin rashi" Yace "Ameen, haka yawanci wasu mutanen suke sai yaro ya jigata ake kawo sa asibiti..." Mayraah tace "Na fa shiga gidan ne nayi insisting mu tafi asibiti amma bata da intention din kai ta asibiti don tace mijin ya siya mata magani a chemist" Dr Khalil yayi murmushi yace "Yanzu ina kika nufa?" Tace "Zan koma gida" Yace "Ohk, bari in baki transport naga ko jaka babu a hannunki" Sai a sannan Mayraah ta lura ashe empty handed ta fito, ta kalli Dr Khalil, sai kuma ta
Book Chapters
Chapter 44
Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63