You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa gaban motar, har lokacin fuskata Wauke da annashuwa da farin ciki, cike"

"da Wauki na matsa gaban motar ina jiran ya buWe min da mota itace ™arshen abin da nike son hawa a rayuwata, ina bala'in son inganni a cikin mota, amma babu halin hakan, iyakata da ita sai gani daga nesa."

"Tun da muka fara shiga cikin tsararriyar unguwar bugun zuciyata ya sauya salo, numfashina na yau shirin Waukewa"

"amma ban bashi damar Waukewarba nike janyo shi da sauri, wato malam duniya da arzi™i su na inda suke, tsayawa baku labarin yanda unguwar ta kai ™arshe a haWuwa Sa ta lokacine, sai dai kawai ince kugi imagin."

Daidai wani ™aton get na alfarma wanda ya lashe ma™udai wajen kafuwarshi Yaya Hashim ya tsaya da motar tare da

fito da wani card ya mi™awa Waya daga cikin jibga-jibgan jaruman escort Win da ke zagaye da get Win.

"Bayan am bamu damar shiga cikin gidan ta hanyar buWe manah wannan makeken get Win, kai tsaye Yaya Hashim ya"

danna kan motar cikin makeken ™eraren gidan wanda yakai ™arshe wajen haWuwa.

"""Mu™u™ut, ma™wat."""

"Abba da ya hangame baki tare da karkace kai ke ta faman haWiyar yawu, lissafi da kwancewa kawai ya ke a kwanyarshi, tare sa wasu irin tunanika da ke bijiro ma shi."

Ni kuwa sake rakuSewa nai ina ™ara kallon yanda aka narke dukiya wajen gida wannan gida me kama d aljannar

"duniya, tun da nike ban taSa ganin gida wanda ya kama ™afar wannan wajen haWuwa da tsaruwa ba."

BANANA ISLAND.

"Zazzaune suke su huWu akan lallausan carpet, gabansu an cike shi da kayan break fast na alfarma, kallo Wa ya zakai"

musu ka gane basu cikin walwala.

Nisawa kamulallen mutum yai tare da cigaba da maganar da yake wacce ta saka sauran nutsuwa.

"""Wallahi hajjo inda kika ga mutumin ba za ki ce ba mutum ba ne, saboda kamala da dattako irin na shi, ya"

"tabbatar min da idan har muka samo wacce ta amince zata yi wannan aiki to babu makawa Fauzan zai warke ya samu lafiya kamar kowa, abin da ke bani tsoro yanzu Waya ne, shin ta yaya zamu samu wacce za ta amince da aikin alhalin ko mu da muke iyayenshi ba komi zamu iya yi ma shi ba, ni kaina jiya da na kusanci inda ya ke sai da na ™one wallahi."""

Yai maganar ya na kallon hannunshi da yai jazur ga kuma alamar konuwa ta tashi a hannun na shi.

"""Ya Allah gareka muka dogara, Allah ka bamu mafita akan yanda zamu shawo kan ciwon wannan bawa naka"

"wanda yake cikin matsanancin hali."""

Hajjo tai maganar fuskarta na jimamin lamarin.

Mommy ce ta Wan muskuta tare da gyara kishingiWar da tai ta buWe baki cikin ™arfin hali ta na faWin.

"""In sha Allah za'a dace dan kuwa jiya na yi magana da wannan yaron Hashim me wanki da guga akan ina so ya"

"binciko min yarinya me hankali da nutsuwa a can cikin unguwanin talakawa, ya amsamin da in sha Allah za'a samu,"

yanzu haka na tabbatar da su na hanya dan kuwa munyi waya yau da asuba ya sake tabbatar min da ansamu kuma

"΄ar uwarshi ce, ya na da ya™ini akan zata iya, to na bashi umarni akan ya Waukominsu yanzu da safenan kafin anjima Mu'allim ya zo."""

"Jinjina kawuna sukai a zuciyoyinsu su na addu'ar Allah ya sa a dace, indai kuWi za su yi aiki to a shirye suke wajen"

ganin sun salwantar da ko nawa ne dan samun lafiyar sanyin idaniyarsu.

"Bayan isowarmu da kamar mintuna goma, amma shiru babu wanda ya le™omu, mamaki, gidadanci gami da ™auya ci sun gama daskare man kawunanmu ni da Abba, idan Abba ya kafe abu Waya da ido tofa ba zai janye idonsa ba har"

"sai ya gamsu da bayanin da kwanyarshi ke ma shi na adadin kuWaWen da abun ya lashe kafin wanzuwarshi, duk da iskan AC da fankoki ma su wurwurawa da tsanani gudu hakan bai yi nasarar hana gumi tsatstsafowa Abba ba, duk bayan sakanni sai ya kai hannunshi ya shafce gumin da ke barazanar ji™eshi, sai zare jajayen koWaWWun idanuwansa ya ke ya na shege lafiya, lissafi tun ya na yinshi ya na tafiya daidai har busy yaiwa brain Winshi yawa ta daina bashi haWin kai saboda yanda ya takurata da lissafe-lissafe."

"Tsinewa rashin siyo calculator ya saka a cikin aljihu saboda irin haka da yayi yafi sau shurin masa™i, ni kuwa tun"

"lokacin da akai mana iso zuwa wannan dan™areren Wakin na alfarma wanda ya ke cike da kayan ™awa da more rayuwa jikina yai sanyi, sai na soma tunanin anya kuwa a cikin duniyar mutane mu ke, ko dai duniyar aljannu Yaya Hashim ya kawo mu, tun ina kallon kayan ™awa da more rayuwar da aka wadata Wakin da su cikin tsoro, mamaki gami da al'ajabj, har na ware ina bawa idanuwana abinci nima nabi sahun Abba wajen buWe idanuwana ina kallon kayan ban mamaki, wato malam arzi™i na inda yake, talaka bawan Allah inji hausawa sukace Talaka buzun banza indan ta mutan gari sai ya mutu."

"Sa™e-sa™e da lissafe-lisafe babu wanda banyi ba, amma sam hankali da brein Wina sun gaza lissafo min adadin yawan"

ma™udan kuWaWen da aka narka wajen gida wannan gida.

"Wa ta dattijuwar ma ta ce ta shigo da kayan uniform a jikinta, a bayanta matasan ΄an mata ne suma sanye cikin"

"uniform kalar na ta, sai Yaya Hashim da ke biye da su waya kare a kunenshi da alama waya ya ke."

Cike da fara'a matar ta ™araso inda muke tare da bawa ΄an matan umarnin ajiye treyn da ke hannuwansu wanda ya ke sha™e tab da kuloli da jug na alfarma.

"Gaishe mu tai tare da ™are manah kallo ganin irin shigar da ke jikinmu, duk da ba kallon raini ko ™as™anci tai mana"

"ba amma sai naji duk na muzanta, musamman dana Waga kai na kalli yanda kayan uniform Win jikinta suka sha guga suka kwanta kuf, sannan fatarta luwai gwanin kyau dan harda siririn glashi a idonta, ya™e kawai nai ma ta ina sinne kaina ina jin wani iri, atamfar jikina na kalla wacce tana Waya daga cikin kayan da nike ji da su, Yaya Sumayya ce ta bani ita a wani zuwa da sukai Katsina biki suka dawo da kaya ni™i-ni™i wanda ΄an uwan Umma suka basu, shine ta Waukota ta bani saboda rigar ta yi daidai da ni, saboda bani da ™iba sam sai dai inada cikar jiki da ™ira me jan hankali."

"Janye ™afafuwa nai tare da ™udundune su a cikin hijabi, dan ina Wago kai naga matar ta kafe ™afafuwan nawa da ido,"

"ba tun yau ba nasan Allah yai mani halitar ™afa me kyau da tsari, sautari idan na ina ina zaune da Mama takan janyo"

™afafuwa ta Waura a kan cinyarta ta na shafawa wai burgeta suke.

"Abbana yai saurin saukowa ™asa bayan ya amsa gaisuwar matar cike da fara'a kamar bakinshi zai yage, bayan ta"

"gabayar mana da waWanan kuloli wanda na tabbata cike suke da abinci na alfarma, godiya Abba ya shiga zundumawa kamar sabon maro™i, nannaWe hannun riga ya soma yi tare da haWiyar yawu ji kake ""Ma™wat""."

"Kiciniyar buWe food flasck Win ya soma amma ya kasa, gudun kar ya je yai Sarna ya sa ya kalle ni tare da faWin."

"""Ke Mubeenah sauko ki buWe mana coolar muyi mu ci kafin mutan gidan su fito, dan wallahi Allah cikina ya kwakware kamar ban taSa cin komi ba, dama dai Wan ruwan kunu ne wanda Umma ta dama kuma kinsan halinta da ba™ar ruwar tsiya Wan kaWan ta sammin."""

"Banja da nisa ba na sauko, dan nasan halin Abba tsaf zai dalle ni maruka babu ruwanshi dan yasha faWi da"

"bakinshi cewa shi abin kunya gaba ya bashi ba bayaba, iskanci da abin kunya gadonshi sukai."

"Da ™yar na iya buWe food flask Win waWanda suke ta faman Waukar ido da walwali, zazzafan peper soup ne"

"wanda ke ta faman tashin ™amshi me tado tsohuwar yunwa, Wayar kuma soyayyen dankalin turawa wanda aka soya da kwai, jug Win kuma kunun madara ne fari sol sai da™™uwa yakemin, ban san sanda nima na bi sahun Abba wajen haWiyar yawuba."

"Abba bai jira na zuba a plate ba ya suri cinyar kaza ba tare da yayi bisimilla ba ya dirar ma ta, ganin haka ya saka"

"nima nai maza na zanyo plate na warci ™irji da fuffuke na saka tare da Wan tattare hijabina gudun kar ta Saci nai bisimilla tare da far ma ta, lokacin da WanWanon naman ya ratsa kwanyata sai da nai hooking na wucin gadi, idan ma rantsuwa nai to bazanyi kaffara ba tunda nike ban taSa cin kaza me makamancin Wadin wannanba, ga shi ta dahu luSus tai taushi gwanin Wadi wajen ci, ina ci ina jinjina kwarewar wacce ta sarrafa wannan girki, ba maki Wari ba ni dai har maki dubu Wari na bata wallahi."

"Jug Win kunun na janyo na tsiyaya a ™aramin cup, tare da zuba dankalin shima a plate Win da nike cin kaza, harga"

"Allah ina da karah da kawaici amma banda wajen abinci, ina bawa cikina muhimmanci sosai, bare nasan idan na tsaya sanya tsaf Abba wai wawure abincinan tas ya barni da haWiyar yawu, shi yasa nima ban tsaya cutar kainaba na saki jiki na cika tunbina tsaf."

"Abin mamaki duk irin mugun cin Abba sai da ya gaji ya ture kazar nan ya koma kan kunun madara, shima ya WaWWaka sosai amma bai shanye ba, yo ta ina zai iya shanye wannan kayan gara waWanda ™amshinsu kaWai ya isa ya ™osar da"

"mutum bare ace ya ci, wani abu Waya da na hasaso shine, tabbas idan dai Sangaren masu girki za'a Waukeni aiki zan zage in koyi irin waWanan abubuwan dama na daWe da burin zuwa koyan girki amma sai Umma ta sakamin mugunta, har makaranta abokin Abba ya taSa samomin ni da Wiyarshi amma ta shiga ta fita ta hanani zuwa sai aka ™a™abamin zaman shago cikin yare."

"Duk abin da muke Yaya Hashim na zaune a gefe yana kallonmu, kunya gami da takaicin halin Abba duk ya cikashi,"

dama yasan za'ayi haka shi yasa koda wasa bai taSa nuna ga irin gidan da ya ke aiki ba dan yasan dole wa ta rana irin haka za ta faru.

"Bayan na gama ne na suWe hannuna tas kaWi da lashe pink lips Wina kamar banci komi ba, sai lokacin hankalina yakai wajen Abba wanda ya wani bararraje kamar gidanshi, duk ya Wiga musu miya a jikin carpet da gabanshi rigarshi da"

ya Sata kamar wani ™aramin yaro.

"Kunya ce ta kama ni ganin yanda tai, ina tunanin inda zan samo ma shi ko da tsumma ne ya goge jikinshi kafin masu gidan su iso, amma kash na makara dan kuwa ban gama tunanin mafita hancina ya sha™omin wani irin sanyayyen daddaWan turare me saukar da nutsu "

"IN SHA ALLAH SAURA ONE PAGE MU KAMMALA FREE, SABODA HAKA MAZA-MAZA KU HANZARTA BIYAN KUŠINKU"

DOMIN SAMU DAMAR KARANTA WANNAN LABARI.

9136291920

MARYAM UMAR OPAY.

KU SAKA SHIADAR BIYA A WANNAN LAYIN

09136291920

Only watsapp

TAKU HAR KUKLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.

MARYAM STAR

ZAFIN WUTA

Follow the 5Ψ@ά5Ψ4ά5ΨEά5ΨLά5Ψ4ά5Ψ@ά 5ΨFά5ΨGά5Ψ4ά5ΨEά 5ΨLά5Ψ4ά5ΨEά 5Ψ5ά5Ψ4ά5Ψ<ά5ΨJά5Ψ4ά5ΨEά 5Ψ=ά5Ψ4ά5Ψ=ά5Ψ<ά5ΨEά5ΨGά5Ψ4ά5ΨGά5ΨGά5ΨHά 5Ψ;ά5Ψ4ά5ΨHά5ΨFά5Ψ4ά 5ΨAά5ΨBά5ΨIά5Ψ8ά5Ψ?ά5ΨFά 5Ψ6ά5Ψ;ά5Ψ4ά5ΨAά5ΨAά5Ψ8ά5Ψ?ά channel on

WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

5Ψά5Ψά5Ψά5Ψά5Ψ
ά 5Ψά5Ψά5Ψά5Ψά

LABARI ME CIKE DA

"BAN TAUSAYI, "

"MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, "

"SADAUKARWA, "

ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.

WRITING BY

MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR

RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI

A DAREN AURENA AND NOW

ZAFIN WUTA

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341

&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*

"_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ™asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau™i_. "

"""Jajirtattu mu ne ™arfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faWuwa. Mu ne tarihi"

"da ake ginawa!"" "

THE NOBLE WRITER'S TEAM

( DEDICATION IS OUR STRONG )

Typing...

PAID BOOK 500 ONLY

CHAPTER 50-55

.EJ-1D' FE-1D' 'DDG E3(

"Me saukar danutsuwa gami da nishaWi, kafin ingama tunani akan daWin ™amshi turare wa ta matashi wacce ta"

"™awatu cikin uban ado kamar wacce za ta je gasar kyau ta bayyana a parloun, gayu iya gayi ta yi shi amma kuma kallo Waya nai ma ta na tabbatar da ta na tare da matsananciyar damuwa, fuskarta fayau babu komi akanta sai man leSe me she™i, idanuwanta duk sun zurma can ciki da alama tayi rashin lafiya saboda sautari akan samu irin wannan ramarne wajen wanda yai rashin lafiya, ko me fama da matsananciyar damuwa."

"Siririyar sallama ta yi idanuwanta na akanmu, amsa ma ta na yi ina janye idanuwa daga kallonta, kallon secons biyu"

"tai mana sannan ta Wauke kai zuwa inda Yaya Hashim ke zaune, cike da girmama ya zamo daga kujerar tare da faWin. ""Ranki ya daWe Hajiya Sulaima barka da wannan lokacin."""

"A ta™aice ta amsa tare da bashi umurnin mu biyo bayanta, babu Sata lokaci yai manah inkiya akan mu taso da sauri."

"Hakanan kawai na ji gabana ya tsananta dokawa da tsananin ™arfi, sannan kuma kasala ta baibaye ni da ™yar na"

samu na mi™e akan ™afafuwana.

"Abbama tuni ya mi™e ya na ta faman sakin gyatsa da buWaWWiyar muryarshi. Rufawa Yaya Hashim baya mukai har zuwa wa ta ™ofa ta glass wacce akaiwa ado da kalar gorlding, sai Waukar ido ta ke, bayan wannan wacce Yaya Hashim ya kira da Sulaima ta shiga muma muka rufa ma ta baya ni da Abba fuskokinmu fal mamakin irin wannan dukiya da aka narka, a wani ™ayataccen makeken parlou wanda ya gaji da gaWuwa muka Sulla, su uku ne zaune akan ™ayataccin kujerun alfarwa waWanda aka ™awata wajen da su, Dattijuwa ce zaune kusa da wa ta mata wacce taWan jingina da jikin Dattijuwar, sai wa ni kamulallen mutum zaune a kujerar kusa da su, kusa da mutumin wacce aka kira da Sulaima ta nufa tare da zaunawa ™asan ™afafuwanshi."

"Cike ca fara'a Dattijuwar ta ke mana sannu da zuwa, yayin da na sake shiga wani irin yanayi marar misaltuwa ga"

"zazzaSi da ke shirin rufar ma ni nan take, a ™as™ance muka rakuSe ni da Abba, mu na jinmu wani iri ganin yanda muka samu mutanen wajen kamar sarakuna saboda ado da kwalliya, mu kuma sai na dinga ganinmu kamar bayi du™e a gaban sarki ko yarima."

"Abba kamar zai taune harshe wajen gaisarda su,ni kuwa cike da nutsuwa na gaidasu ba tare da na kallesu ba."

"Mommy ce ta Wago a hankali ta na gyara zamanta tare da kafe ni da ido kamar me kokonto a kaina, sai kuma ta kalli Pahpah wanda shima dai idonshi a kaina ya ke, ita kuma Hajjo hankalinta na wajen Abba wanda ke ta faman"

"zare idanuwa ya na ™arewa duk abin da idonshi ya sauka akanshi kallo, idan ya kalli abu sai ya lissafi idadin kimanin kuWaWaWen da abin zai iya lashewa sannan ya jinjina kai ya koma wajen wani abun, bayan kamar min tuna biyu da zamanma Pahpah ya kalli Yaya Hashim tare sa gyaran murya sannan ya ce."

"""Masha Allah, Hisham wannan ita ce ™anwar ta ka ko? gaskiya na yaba da hankalinta sosai, kuma ina da ya™ini"

"akan za ta iya, nutsuwarta da kamalarta sun burge ni ainun, sannan ina fatan itace za ta zame mana abin alfahari anan gaba."""

"""Dararammm"" ™irjina ya doka da tsananin ™arfi, yayinda zuciyata ke kokowar fitowa saboda razani da fargabar da"

nike tsintar kaina a gaban waWanan mutane.

"Aje numfashin Pahpah ya yi daidai da tabbatuwar lissafin da zuciya da kwanyar Abba ya haWe waje Waya, tare da"

"gamsar da kanshi wannan ita ce sakayyar yanda gobenshi da ta iyalanshi za ta kasance, dan haka sai ya aro bargon nutsuwa ya yafawa kanshi, tare da ™o™arin hana idanuwanshi kalle-kallen abubuwan da suke neman caza tunaninshi."

Nutsuwarshi ta yi daidai ta kallonshi da Pahpah yai tare da fara yi ma shi magana ya na karantar yanayinshi.

Babban abin da ya burge bai wuce yanda naga Abba ya kame kamar ba shi ba ya na zayyano zantuka masu ma'ana

"da dattako, sai na ji wani sanyi da farin ciki ya baibaiyane yau Waya Abba ya Soye hallayarshi a gaban mutane."



BAYAN AWANNI BIYU.



"Zaune nike akan mafefen royal bed Win da ya mamaye Wakin, ya yinda idanuwa ke zubarda hawaye wanda ni kaina"

"bansan na minene ba, amma zuciyata ta tilasta ni amincewa sa lallai Abba baya so na, ban taSa kawo afkuwar irin wannan lamarin nan kurkusa a rayuwata ba, ban san mi yasa a kaina Abba ya ke kasancewa me son kanshi ba, muddin lamari ya shafe ni to babu makawa sai Abba ya nuna son kai akaina."

"Šaure fuska na yi tare da furta ""Abba kenan, ina mai tabbatar maka daga wannan karon rayuwata ta canza,"

"Abba daga yau bazan sake kasancewa cikin ba™in cikin abubuwanda kake yiminba, daga yau zan tsaya tsayin daka wajen ganin na inganta rayuwta kamar ko wace mace."" Na yi maganar kamar Abban na gabana ko ancemin ya na jin abin da nike faWa."

"Rigar da aka aje kusa da ni marar nauyi na Wauka, sai da na tabbatar da babu me kallona sannan na shiga warware"

"™aton towel Win da aka kawomin wai in Waura idan zan shiga wanka, a jikin ™aton madubin da ke sha™e da kayan kwalliya na kalla, ina sake ™arewa surar jikina kallo ta cikin gashin, wani irin daWi ne da sanyi ne ya baibaye ni domin kuwa ni kaina nasan Allah yayimin baiwar tsarin zubin hallitta me Waukar hankali, sai na ji zuciyata na min wasu sa™e-sa™e aiko nai saurin yin A'uziyya tare da hanama kaina sake yarda da yin makamancin wannan tunanin, cikin sauri na zura rigar tare da mulke jikina da lallausan losion wanda naga an jera, ban tsaya jiran komi ba na Wauki veil Win rigar na Waure kaina da shi, sai na kawo hijabina na saka, kallon kaina nai a madubi sai naga na yi wani irin kyau na musamman wanda zan rantse ban taSa yin irinshi ba, tunawa da wannan matar wacce na ji sun kira da Mommy ta ce inyi sauri ta na jirana, ya saka nai hanzarin juyawa dan infita, sai de kuma na mance inda ™ofar ta ke, duk inda na taSa sai inga ashe ba ™ofar ba ne, tashin hankali ne ya baibaye ganin ™ofa ta Sacewa ganina, da ™yar na rarrashi kaina banyi kuka ba, amma kuma daf ni ke da rafka ihu ko za'a samu wanda zai kawo min Wauki idan ya jiyo ni."

"˜arar buWe abu na ji, cikin sauri na Waga kaina dan ganin minene, sai na sauke udanuwa akan wacce na ji an"

"kira da Sulaima, ajiyar zuciya na saki ina godiya ga Allah da ya kawo min Wauki."

"Guntun murmushi ta sakarmin tare da ™arasowa inda nike ta na min magana da turanci, aiko gaba na sake tsallen"

"bugu, dan harga Allah nasan ina jin turanci amma da na ji yanda ta ke nata turancin cike da kwarewa da iyayi sai na kasa fahimtar mi ta ke nufi."

"""Oh sorry, Mubeenah ko! dama Mommy ce ta ce ki zo muje idan kin ™arasa, tun Wazu muke jiranki amma shiru"

"baki fito ba."""

"Zurum na mi™e tsaye ba tare da na yi magana ba, dan sai na tsinci kaina cikin tsoron buWe baki inyi magana kar inyi"

ba daidaiba in kwafsa.

"Ganin na mi™e tsaye ya saka ta Wauke kai daga kallona da ta ke, a ranta ta ke yabawa da irin kyawun da Allah yai min,"

"sai de rashin gyara da ™arancin wayewa ya disashe ™yalin kyawun nawa, amma duk da haka kallon farko za'a sakani a cikin jerin kyawawa."

Bin bayanta ni ke kaina a ™asa har muka isa wani Wan ™aramin parlou wanda babu komi a cikinsa saga na'urar Ac sai

"™aramin fridge me kyau da tsari sai kujeru masu taushi. ganinmu ya saka Mommy da Hajjo mi™ewa tsaye, bayan mun ™arasa na zame na sake gaidasu ta hanyar yin jimla."

Bayan sun amsa Hajjo ta matso kusa da ni tare da kama hanuna ta na faWin.

"""Mu je jikata yarinyar kirki, Allah ya albarkaci rayuwarki ya haskaka ki da saiken alkairi."""

Amsawa na yi a cikin zuciyata ina yaba karamci irin na waWanan mutanen.

"Mommy ce gaba sai ni da Hajjo da Sulaima a bayanta, sai da tai Wan jimmm sannan ta tura ™ofar glashin tare sa Bisimilla ta tura kanta ciki, haka Sulaima ta rufa ma ta baya, yayinda Hajjo ta tura kanta tare da janyo hanuna nima"

na shiga.

"Wa ni irin mummunan bugu ™irjina yau, wanda saura ta™i Waya rak ya ragewa zuciyata ta wuntsilo ta ma™ogarona"

"zuwa waje, ban san lokacin da na du™e a wajenba na shiga maida numfashi da tsananin sauri, hannunawa dafe da ™irjina, dokawar da zuciyata ke yi na barazanar toshe magudanar numfashina, yayin da wa ta iriyar zufa tare da sanyi suka lulluSe ni lokaci guda, juyowar Mommy da du™owar Hajjo a kaina ta na jijjigani ya yi daidai ta isowar Pahpah wajen, cikin hanzari ya matso kusa da ni fuskarshi na bayyanar da annuri gami da tausayina a lokaci Waya, kafin kowa ya samu damar cewa komi Pahpah ya du™a tare da kamo hannuwana ya mi™ar da ni tsaye, sai da ya tabbatar da na samu nutsuwa sannan cikin taushin murya gami da rarrashi ya ke faWin."

"""Ki nutsu! nutsu kinji mah doughter, ki tausayawa halin da Wan uwanki musulmi, kuma wanda ke amsa suna miji"

"a gareki yanzu ya ke ciki, ke kaWaice za ki iya ceto rayuwarshi da taimakon ubangijinmu, na baki yardata 100% a karo na farko a cikin rayuwata da na yarda da wani mutum na daban har na yi marabada shi a cikin familynah."""

"Duk da yanda ™afafuwana ke rawa su na barazanar kayarda ni, amma sauraren kalaman da suka ci gaba da fitowa"

"daga bakin Pahpah, wanda nike wa kallon mutum me daraja da karamci, sai na ji zuciyata na bani kwarin gwuiwa, hakan ya saka na shiga gyaWa ma shi kai, ban san wane zaren ™addara bane ya janyo ni zuwa cikin waWannan ahali masu karamci, ban san cewa amincewar da na yi ba zai zama mabuWin buWe ™ofofin ™addararon rayuwata, haka kawai nike ji a jikina daga yau kuma yanzu rayuwata ta sauya, sauyi sosai wanda ya banbanta da irin faWi tashi da tarin ™alubalen da na fuskanta a rayuwata."

"Cike da tausaya Pahpah ya janyo hannuna zuwa ainahin cikin Wakin, wanda shigata cikinshi ya zaftare abubuwa da"

"dama daga ratuwa da burukana, Wakin da ya zama wajen da zan kafa tarihin wa ta rayuwa me cike da rikitattun al'amurra."

"Duk ta™o Waya da zanyi, ina aje ™afata ne tare da bugawar zuciya me tsananin ™arfi, sannan kuma ina jin wani irin"

"ZAFI me kama da ZAFIN WUTA ya na fuskanto ni, a daidai lokacin da na sauke takona na ™arshe, a lokacin ne zuciyata ta tsaya cak da bugawa, gangar jikina ta kafe akan ™afafuwa, a sa'ilin da idanuwa suka sauka abin abin da ya nemi hargitsa duniyata a lokacinne kwanyata ta shiga maimaitomin tariyar mafarkan da suka addabe ni a cikin barci musamman kwanakinnan "

"ALHAMDULILLAH YAU DAI ALLAH YA AMINCE NA KAMMALA FREE PAGE, YANZU ZAMU SHIGA AINAHIN CIKIN"

LABARIN BA TARE DA ATA LOKACI BA.

DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNAN

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment