ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saleem yakashe motan yasauko abinsa yadan bi jikinsa da kallo 3 quarter ne ajikinsa da bakar singlet da sarka da dan kunne, Marwan yazo yadan kallesa saiya zare t shirt na jikinsa ya mika masa yace  put this on cikeda Iskanci Saleem yace  why? Kana tsoro bakaso nai breaking heart din Abbanka? Yana maganan yawuce abinsa yabar Marwan da riga a hannunsa maida rigan Marwan yayi yasaka yabi bayansa su Mami na zaune aka bude kofa Saleem yafara shigowa Marwan biye dashi Abba yabi Saleem da kallo tundaga kan wani dundumemen canvas dake kafansa da gajeren wando crazy ayayyage dawani shegen dan iskan singeleti da sarka a wuyansa da dan kunne, Saleem yakalli Mami da itama ke kallonsa jikinta ba karfi yace  Hi Mams Mami tama kasa magana jikinta yayi la asar wlh ganin Saleem yakoma gogaggen maraji, Abba yamike cikeda fada yanuna Saleem from head to toe yace  what is this Saleem? What is this? Me wannan a wuyanka? Mace kakeso ka koma? Kasan cewa Allah ya tsinewa namiji maisa kayan mata?"

"Meya hadaka da sarka da dankunne, jibi yanda kake warin giya eh Saleem? Irin yanda niggas ke behaving yawani bude hannu yajuyo yakalli Marwan dake bayansa yace  yooo! You see why I don t wanna come back, you see now ? Cikin tsananin fushi da bacin rai Abba yawani fizgosa ya juyo dashi yace  ba magana nake maka ba wai kana dan musulmi gaba da baya kake shiga haka kaman kafiri? Cikeda takaici Saleem yace  yooh wai menene aibun dressing dina Yays eh Wlh wlh Abba try his best to control his anger amman yakasa wai wato Yaya ne ma Yays yanzu, hannu yadaga a fusace zai dauramai mari dasauri Marwan yashiga gabansa Marin yasauka akan gefen wuyansa da side na kunnensa, Saleem ya kalli Marwan idanunsa sunyi ja Mami tace  Alhaji dan Allah calm down ba a gyara kuskure da fushi takalli Saleem tace  kuwuce kuje ku kwanta Saleem gobe zamuyi magana wucewa azuciye Saleem yayi yace  okay Mams Marwan yabi bayansa, sukai sama instead of Saleem yashiga dakinsa dake gaban na Marwan kawai yabude na Marwan ya shiga Marwan yayi dan jimm saiya shigo baice komiba, yamaida kofan tarufe Saleem yashiga cire kayan jikinsa yana jefarwa duk inda yaga dama yarage dagashi sai boxer yafada bayi, dukawa Marwan yayi ya kwashe kayan nasa tass dake wari shaye shaye ya tattara yakai Landry basket yazuba sannan yawuce yafita daga dakin koda yakoma kasa su Mami basanan anma kashe wuta sunje sun kwanta kitchen ya shiga yahada lemon tea yana warware hangover nasu giya da shaye"

"shaye, sai yayi frying egg guda 4 Yayi toasting bread yadauki karamin bottle water duka yahada a tray"

sannan yakashe komi yafito yataho sama har dakinsa yabude kofa har lokacin wanka yake normally yana

"dadewa a bayi, ijiyemai abincin yayi kan study desk dinsa inda ka top nasa yake da folders daya kawo daga hospital na patient, ya ijiye wani kati na kwayan magani guda daya shima yana kara flushing toxins daga jiki, yadauki pen yarubuta eat and drink this, yakashe wutan dakin ya kunna mai wutan study desk din dake haska abincin sannan yakunna mai wutan closet kafin yajuya yawuce gado ya bala in gaji ya kwanta yana cire glasses nasa ya ijiye kan side drawer dake gefensa yayi addu a yashafa ajiki ya kwanta"

ko 2min ba a dauka ba yayi bacci dan yagaji sosai lokaci was already 2 nadare.

Wuraren 2:15 Saleem yafito ya tsaya yana kallon abincin daya hadamai a study desk yakallesa yana gado

"yarufa da bargo sai kawai yawuce closet, pajamas dinsa yadauka yasaka yafito ya shinfida dadduma yayi magrib da isha i yatashi yazauna akan kujera yana kallon rubutun dayamai yakalli kwayar maganin wanda baisan na menene ha amman yabude kawai ya jefa abaki yasha yana daukan tea ya kurba, yadauki spoon yadebi egg yakai baki saiya tsaya yayi wani dan tsuki yana murmushi daya wani irin karamai kyau yace  what a terrible cook saikuma ahankali yace  is after 2 I m hungry I have to eat it like that shaye shaye nasa kaji yunwa, he knows Marwan yasan da hakan saisa ya ijiyemai abinci tass ya cinye komi dan shi yanada cin abinci, yadauki tea yashiga sha idanunsa suka sauka kan folder ahankali yakai hannunsa yace  let s see wani case kebama yaron nan headache cus any folder daya kawo g1da means one thing the case is intriguing and he needs to study more or dig more yabude file din yanabi da kallo yanashan tea, Aminatu Adamu, born 2004, an kawota akace autism& .. saida yabi komi ya karanta down to treatment da Marwan yamata yau zuwa sanin Babanta ne yakawota asibiti she was agrressive ta cije baban dariya yayi yace  woww wat a fiesty little girl, inason yara haka, aida kin yayyaga old man dinki da kumba, if I ever see you I will tell you how to handle all this trouble some old"

"niggas, mine too is disturbing my life Yayi maganan yana rufe folder kawai ya ijiye."

Yamike tsaye ahankali yayi murmushi yace  Aminatu Adamu Daddy s biter yadauki wayansa yawuce

"zuwa gado yahau gadon ahankali harzai kwanta saiya kunna touch nasa ya haska Marwan dake bacci ya kalli wuyansa dayayi ja sai yadanji wani iri yace  bakasan yanzu mun girma ba when will you stop taking beating for me foolish boy, he s just too caring, i thought by now he will realize not everyone deserves it"

especially me cus gobe still sainaje club ya kwanta yanandago bargo yarufa sai bacci.

Wuraren 5 Marwan yabude idanu da kyar shima kawai dan jikinsa yariga yasaba da tashi around that

"time ne for subhi, ahankali yamika hannu yadauki glasses naaa yasaka sannan ya yaye bargo yatashi zaune yana addu an safiya kafin yamike yawuce yafada bayi saida ya gyara bayin sannan yayi wanka yafito yashiga closet nashi ya shirya yafito cikin wata milk jallabiya yasa faran hula yana kamshi yazo gadon ya bubbuga Salim yace  Saleem, Saleem, Saleem da kyar Saleem yayi motsi yace  if I have the chance stitches your mouth Marwan ahankali yace  tashi muje muyi salla saika dawo ka koma bacci, tashi tashi kafin Abba yazo Sarai yasan yayansa ruwan sanyi zai zuba masa hakan yasa yabude idanu da"

kyar yaki motsi yace  I can t feel my body dagasa Marwan yayi yawuce yashiga bayi yadauro alwala

yafito jallabiyan Marwan yadauka daga closet yasaka yafito yana hamma ya ballama Marwan harara

dake kallonsa yace  mugu murmushi Marwan yayi suka fito suka wuce mosque.

JAMA A GA SALEEM GA MARWAN!!!

ME KUKE GANI ZAI FARU??

KUN TABA GAN0N KANIN DA SHIKE KULA DA YAYA?

AGANIN KU WA AMIRAH ZATA AURA??

EPISODE

Miemie sosai take buga kofa tana kuka sosai tana kwalama Ammi kira amman shiru kuma babu yanda

"za ayi ace kap gidan nan ba aji ihunta ba dan harta window taje ta tsaya tana ihu tana kiran su Maman Baby amman shiru, dasauri tai wajen wayanta dake kan gado tadauka jikinta har rawa yake tashiga dialing number Umar, a ringing na farko bai dagaba ana biyune ya daga, cikin kuka sosai tace  Ya Umar kana ina? Dadan damuwa yace  menene kike kuka meya sameki? Gani a gareji cikin kuka Miemie tace  dan Allah kazo gidanmu yanzu ka shigo har side namu dadan tashin hankali yace  wait why are you crying like this? Dasauri tace  zan fadamaka kazo kashigo ciki ahankali yace  ya za ayi na shigo cikin gidanku babu izini tasan gaskiya yafada hakan yasa tace  Ammi ta sume ne kuma kanta yabugu ni ina daki a kulle kuma babu kowa dazai budeni nabata taimako you are the only one I could think of, dan"

Allah kazo Ammi first we will deal with koma menene later ahankali yace  okay gani nan zuwa tana

tsaye awajen jikinta rawa kawai yake bini bini tana share hawayen dayake saukowa daga idanunta

hankalinta atashe batamasan meke mata dadi aduniya ba ina yakai Amirah?

Wani matashin saurayine dazaikai shekaru 30 haka aduniya kakkarfa bafulatani yayi parking Wayyo

"kudina a kofar gidan yana sanye da kayan gajere dan bakaniken mota ne yaciro wayansa yayi dialing number dayasa my wife ajiki ringing daya Miemie tadaga jin tana kuka har lokacin yace  waiba nace kidena kuka ba, nothing will happen to Ammi, gani awaje cikin kuka tace  to kashigo flat dinmu ne na karshe ai kasan flat din ko rannan dakuka zo ganin Daddy ahankali yace  eh nasani katse wayan yayi ya kalli gate din dudda he s feeling uncomfortable amman haka yabude gate din yashiga luckily babu kowa a tsakar gidan yawuce flat nasu sallama yayi yadaga labule yashiga yana hango Ammi akasa flat ga jini agoshinta daya kumbura yace  Subhanallahi yayi wajen jin muryansa yasa Miemie ta jijjiga kofan tace  Ya Umar ina nan budeni kofan ya kalla sai yayi wajen ya murza key dake jikin kofan yabude Miemie data saka hijab dinta har kasa tayi wajen Ammi da gudu tarushe da kuka tana dagota tana jijjigata.  Ammi, Ammi Ammi, Ya Umar Ammi na ta mutu ne ? Dasauri yace  don t say that yamike cup ja ruwa daya gani akan table yadauka yazo wajen yadan debi kadan ya yayyafa ma Ammi a fuska amman ko gezau batayiba Miemie tarude jijjiga Ammi kawai take kaman mahaukaciya duk takara daburta Ya Umar the only thing dayazo kansa is.  Bari nakira keke mukaita asibiti Miemie tace  kafadamin gaske ta mutu ko shine bazaka fadamin ba Ya Umar yace  waiba nace kidena magana hakaba cikin tashin hankali tace  to maisa bata farfadowa bayan mun watsa mata ruwa inba mutuwa bane, idan Ammi na ta mutu nima saina bita Ya Umar ganin yanda kaman ta haukace saiya duka kusa da ita abinda baitabayi ba yayi yakai hannunsa yakama kuncinta yace  Maryam put yourself together babu abinda ya_am1 Ammi we will take her to hospital dole ke zaki tsaya mata so kudawo hayyacinki kina jina gyadamai kai tayi yamike dasauri"

yafita.

Ko 3min bai bataba yadawo suka shigo da keke yabudema Keke gate aka shigo Miemie tasama Ammi

hijabi yashigo dakin shida Miemie suka kamata suka fito da ita daidai Maman Baby na zuwa wajen tace  Au karuwanci kika fara kike kiran saurayin naki har gida dukansu biyu babu wanda yabi ta kanta sukasa Ammi a keke keke yafice Unar ya sauka a waje yahau machine nasa yabisu abaya.

Wani karamin primary health care center sukaje suna zuwa aka karbi Ammi dasauri Miemie tazauna

tana kuka shiya biya kudin komi da yan kudaden dayake dashi sannan yadawo yazauna gefenta yayi shiru yana kallonta tabasa tausayi wlh yanason Maryam sosai bata taba fadamai anything akan family ta ba but zaman tare yadan lura da yan abubuwa from rannan dayazo tambayan aurenta Babansu baice komi akan Miemie ba amman yanda yadinga kiran Amirah da mahaukaciya dakuma yanda yadinga kaskantar da Ammi agabansu he knew something is going on just like that yasan Ammi bazata fadi

"hakaba Miemie kuma a kulleta adaki ba sannan baiga Amira ba, he knows something is going on"

ahankali yace  Maryam dago rinannun idanunta tayi tace  uhm ahankali yace  ina Amirah? Tsare

"Umar tayi da kallo wani kuka nataso mata kawai saita shiga rerama Umar kuka tama kasa magana but kukanta said a lot tace  bamusan inda Daddy yakaita ba Ya Umar yayi shiru saikuma cike da tausayi yace  ya isa stop crying kar zazzabi yakamaki, kika fara zazzabi ina zansa kaina eh kinaso nakasa aiki ne? Girgizamai kai tayi yace  okay we will do this first thing first, muji da Ammi yanzu dake gabanmu muji ta farfado, tunda Amirah natare da Abba zamu nemeta okay gyadamasa kai tayi ahankali, yazaro handkerchief mai kyau daga aljihu yabata yace  wipe your friends mujira Dr I m here for you okay, you are not alone Wifey wani sanyi Miemie taji aranta Umar nada kirki sosai baida wani kudi tasan kwanan nan he s working times 3 sabida yahada kudin aurensu yana hada akwati akwai dan karamin filin dayake dashi daya daha ginin gadan gadan dan awajen yakeso su zauna gashi duk yakashe kudi anan sai yabata tausayi ahankali tace  nagode Ya Umar Allah kara buda maka dasauri yace  inhar zaki godemin da gaske godiyan danakeso is kidena kuka sabida dagamin hankali yake share fuskanta tayi tass yace  to yima mijinki murmushi kadan murmushi tayi tadanja hijabinta tana boye fuskanta yayi murmushi yace  Alhamdulillah baison abinda sai taba Miemie ko kadan, suna zaune awajen Dr yafito dasauri Umar yatashi yace  stay here zama tayi yawuce wajen Dr dasauri, Dr yace  jikinta yahau sosai that s abinda yayi contributing dayasa takasa farfadowa amman she s out of danger mun mata allurai mun dinka mata kan, tana bukatan full circle na sleep so bazata tashi ba sai zuwa gobe da safe zuwa rana haka amman Alhamdulillah no need to worry again Dasauri Umar yace  Alhamdulillah Alhamdulillah thank you Dr thank you Dr yace  zaku iya shiga ku ganta yanzu za a maidata ward tahowa wajen Miemie yayi data tsaya tana kallonsa murmushin dataga yanayi yadan kwantar mata da hankali yace  Ammi is fine yanzu amman Dr wai yamata alluran bacci sai zuwa gobe zata farfado muje ki ganta zasu maidata ward daga emaergwncy room din Gyadamai kai tayi tabisa sukaje har ward ne inda kusan patient goma suke kowa akan gadonsa suka gaida mutane sannan sukaje gadon Ammi dake bacci ga drip nabin jikinta da gudu Miemie tawani rungumeta ta kankameta Umar yabita da idanu, da yanada kudi dabazai jira 4 months da aka deba musu ba kawai aurenta zaiyi yahuta da wutan sonta dake damunsa sai yanzu hankalinsa ya"

kwanta ganin tadena kuka dazu world dinsa was crumbling because of yanda take kuka.

"Ahankali yazo wajen 10k ya dunkule ya ijiye kusa da ita yace  ga wannan incase wani abu come up, bari"

nakoma gareji anjima zan dawo da yan abubuwan da kuke bukata dago kanta tayi takallesa saita gydamai kai akunyace tace  thank you Ya Umar Allah kara budi da arziki ahankali yace  promise bazaki kara kuka ba sauke kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace  tom murmushi yayi yace  take care and take care of Ammi bye yawuce yafita yan ware din na kallonsu machine dinsa yahau

yabuga sai gareji.

Miemie na asibitin har magrib ta ari dadduman wacce ke next to bed nasu tai salla har akai isha i ma

"haka 8 daidai Umar yayi sallama yashigo Miemie tadan dagokai ta kallesa yana gaida marasa lafiyan yan dakin yana sanye da shadda blue mai kyau yasa hula sai kanshi yake hannunsa duka biyun rike da abubuwa sannan yazo wajen gadon ya ijiye basket din yace  Umma tace akawo miki Allah kara sauki gobe zasuzo dubiya ya ijiye dayan ledan wanda yan shopping ne yamata, Miemie da kanta ke kasa tace  an gode Allah amfana zama yayi akujeran daya bata yakalleta yace  bude kula ki debi abinci kici Dan kallonsa kadan tayi ganin ba wasa fuskansa saita sauka saga bakin gadon tabude kulan dafadukan shinkafa aka dafa musu da nama da zobo mai sanyi tadauki spoon da plate ta deba tadan kalli matan dake bata Aron dadduma ta kusa da su tace  ga abinci muna kwarya matan tace  ahh Alhamdulillah an gode dawowa tayi tazauna tafara ci duk kanta akasa Umar sai kallonta yake, haka take ta gansa taita kunya ko yazo zance awaya ne take bude baki tamai magana, today is the first day datake ganinsa in reality tayi magana shima sabida rudewan Ammi ne, cinyewa tayi tasha ruwa sannan ta ijiye plate din, Umar yamike yace  bari naje to gud night akwai sock da zanin gado kisa ki rufa da kyau sabida sauro gyadamai kai tayi tace  nagode agaida Umma dan kallonta yayi yace  muje kirakani akunyace ta sauke kanta kasa wucewa yayi yay gaba sannan tasauka tasa takalmi tafito awaje ta samesa wajen wani bishiya inda akasa kujeran zama haka tawuce wajen tana tafiya ahankali ya tsareta da kallo taje saita zauna amman tabar dan gab between them, sukayi shiru sai chan yace  Maryam dago kanta tayi takallesa, ahankali yace  how are you? Tambayan ya sosa zuciyanta sosai baki tabude zatai magana kawai saita daura hannayenta akan fuskanta kaman yar yarinya tafashe da kuka, she just feel alone, she feels ayanzu right in this moment batada kowa sai Umar, ba Ammi ba Amirah, mikewa Umar yayi saiyazo ya tsaya agabanta kafin yaduka gabanta ahankali yace  Miemie is this the promise dakika min? Yakikeso nayi da raina? Do you want to kill me eh Miemie, bakiso na ko? Girgixamai kai takeyi tana shesheka irin yanda yara sukeyi hancinta harda majina tace  Ya Amirah batada lafiya, bataci abinci ba nasan har yanzu dare yayi bazataci ba tunda bataganmu ba, jikinta was hot, bansan wani hali yar uwata ke ciki ba, Ammi gata itama a hospital banda kowaaa tana kuka numfashinta har neman daukewa yake Umar baimasan"

mezaiyiba sai kawai ahankali yajawota for the first time tunda suka san juna yayi hugging nata.

EPISODE

"Batasan metakeba kawai kankamesa sosai Miemie tayi back, Umar yafara patting bayanta yana mata"

"magana a kunne,  Maryam do you also want to loose me too? Cus kukan ki zai iya halakani kinga saiki"

"zama ke kadai aduniya uhn kankamesa Miemie tayi tana girgiza masa kai, ahankali yace  komi yayi zafi"

"maganinsa Allah, rayuwan nan babu wanda baya cikin wata jarabawa, I just want you kisan cewa Allah baya bacci, ki karfafa imaninki, kome ke damunki ki fuskancesa kiyi addu a, kima Amirah addu a wherever she s Allah ya tsareta ya kareta yakuma bata lpy, yadawo da ita lpy, sannan Allah yabama Ammi lafiya, everything is going to be okay I promise you, kinji, I m right here fa, I will always support you and be there for you no matter what kinji ?Gyadamai kai tayi tanajin wani natsuwa da karfi a zuciyanta, ahankali Umar yace  I love you so much be strong for me okay gyadamai kai tayi, cirota yayi daga jikinsa saita kasa kallonsa kuma ta sauke kanta kasa shima yatashi yakoma gefenta ya zauna saukai shiru sai chan ya kalleta yace  bari natafi uhm, saida safe tashi ki koma ciki tashi Miemie tayi da sauri kanta akasa tace  saida safe uhm nagode Ya Umar tawuce dasauri yabita da kallo yadanyi murmushi dan hug dasukai sharing nadawomai greasy azuciya yashafa kansa yamike ahankali yawuce yahau"

machine dinsa yabar asibitin.

**

"Wuraren 10 na safiya Ammi tashiga bude idanunta ahankali, dasauri Miemie dake gwfenta tawani"

"zabura tace  Ammi kin tashi, gani nan Ammi kina ganina ? Bude idanunta Ammi tayi ahankali tana bin ko ina da kallo kafin tasauke idanunta akan Miemie dake kanta, Miemie tace  Ammi murya chan kasa mara karfi Ammi tace  ina ne nan Miemie? Meya kawoni nan ? Ahankali Miemie tace  kanki ne yadan fashe tun jiya kike nan shiru Ammi tayi nan da nan abinda yafaru jiya yadawo mata dawani irin sauri tazabura ta mike zaune zata sauka daga gado Miemie tariketa tace  Ammi tsaya kinji dan Allah Ammi da zuciyanta yashiga bugawa dumdumdum tace  Miemie ina Amirah? Babanki yasa mazan nan sun tafi da ita? Ahankali Miemie ta gyadama Ammi kai, gaban Ammi yayi wani mummunan faduwa sai kawai ta kalleta tace  kira Dr a sallameni, bazan iya zaman asibiti bansan wace duniya Amirah take ba, kome zai samen ya samen gyadama Ammi kai Amirah tayi batare datai gardama ba tawuce tafita takira Dr sai gasu, Dr yace  Hajiya kibari agama miki treatment BP ki is very high maisa kikeso a sallameki cikin dauriya dan daurewa kawai Ammi take tace  nabar diya mara lafiya agida, lafiyanta shine gabana likita banawa ba dan Allah ka sallameni sauri nake, ganin yanda Ammi take magana sai kawai Dr yaji tabasa tausayi yace  okay amman ki dinga zuwa duk say1 sati dan mu dinga managing BP naki sannan you need to sign this discharge against medical advice form gyadamai kai Ammi tayi tai signing komi, Miemie tashiga hada kaya tass Mamie tazira hijabi ance subiya 5k suka biya suka fito Ammi bamatajin karfi"

jikinta amman tafiya kawai take har titi suka tare keke sai gida.

Shiga gidan sukayi bakowa agidan babu motan Daddy bangaren Maman Baby ma a kulle alamun

"batanan, Ammi kawai tafiya take tana shiga flat nasu koina tabi da kallo kafin tafada ban daki ta dauro alwala tai sallolin da ake binta dan Allah ne fark1 before anything saita shiga kiran Daddy wayansa na ringing baya dagawa, da kyar tasamu akaro na kusan 20th call aka dauka, muryan Maman Baby taji tadauka tace  dan Allah kadauki wayanta kar bakin ciki ya kasheta sweetheart muryan Daddy Ammi taji"

yace  tunda kin rokan mata ai hikenan yasa wayan a kunne yace  yi maganan ki da sauri dan tuki nake

Zainabu dakewa Ammi tayi tana rike abinda ke zuciyanta saita kalli Miemie dake gwfebta tace  bani

wuri Miemie ki rufomin kofa ta ashi Miemie tayi jikinta asanyaye tafita daga dakin tarufo kofa amman saita kasa wucewa ta tsaya tareda jingina kanta jikin kofan.

Da kyar Ammi tadaure tace  Baban Baby ina Amirah? Wani dan dariyan shakiyanci yayi harda shewa

"yace  har abada bazaki san inda Amirah takeba idanma abinda yasa kike kirana kenan gwara ki kashe dan bazan gayamiki ba wani abu Ammi taji yazo mata wuya ahankali tace  Baban Baby dan Allah dan darajan sa, kaduba girman Allah kagayamin inaka kai mini Amirah, karaman yarinya ce dabai kamata tana inda maza sukeba, idan suka keta mata haddi fa, ba hijabi ba takalmi ba hula jikinta, Amirah batasan komi akan rayuwa ba batada wayan kara kanta idan suka mata wani abu fa, katuna akwai Allah yarinyar nan marainiya ce, kafadamin ina ka kaita tsaki Daddy yaja yace  ai saikuma kiyi keda ganinta har abada dan wlh wlh wlh kinji na rantse miki mahaukaciyan nan bazata kara dawowa cikin gidana ba har abada wlh kuwa ki mutu idan zaki mutu munyi tafiya sai nan da yan kwanaki zamu dawo ya katse wayan Ammi tace  Baban Baby Babban Baby tai maza tasake dialing number taji akashe takira Number Maman Baby shima akashe duk dauriya irin na Ammi kawai saitaji kuka yazo mata tafashe da kuka sosai"

dayasa Miemie tadaura hannunta akan bakinta tana rushewa da kuka itama.

Takai morethan 20mins ahaka saita daga wayanta tai dialing wani number ringing daya aka daga wani

"dattijon namiji ne yace  Zainabu Abu muryanta adan shake tace  Yaya ina yini kai tsaye jin muryanta yace  meyasameki muryanki yake haka ahankali cikin sheshekan kuka tace  Yaya zankai Abban yaran nan kara a police station one thing he knows about his sister is she s a very very peaceful person ga hakuri hakan yasa yace  Subhanallahi meya faru haka Zainabu? Ina zuwa tsaya nasa kati na kiraki katse wayan yayi within one minute sai gashi yakira Ammi back tadaga yace  what happened Zainabu? Meya batamiki rai haka dahar zakikai mijinki kara police station eh ? Duk yanda Ammi taso ta daure takasa sai kawai tafashe da kuka tahau gayamai komi tace  idan wani abu yasameta fa? Wlh batada lpy, jikinta zafi kaman wuta, me mukamai ya tsaneta haka? Nagaya maka batun yau ba mutumin nan ba kaunata yakeba gadon yakeso yaci yasa ya aureni sabida komi yadawo

Please Login or Register in order to submit comment