gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading A Wani Gida Complete Hausa Novel by Nabeelert Lady Chapter 2 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace muyi hakuri da duk abinda za'ayi mana. Kaga nima yanzu girki Mama tasani, Faisal yace zauna bazakiyi ba.

Bugo kofar dakin akayi, suna daga kansu sukaga Mama ce, wajen da Faisal ya bigeta har yayi baki gaba daya zagayen idon. Kallon Fatima tayi tana fadin bazaki tashi kidora girkin ba sena sa kema an zaneki? Ai ni wallahi naji dadi.

Daga yanzu bazan kara bata bakina akanku ba, tunda Allah yasa yarana sun kawo karfi sune zasu cigaba da rike gidan nan, kuma dani kuke magana, kujira dawowar Malan. Ke kuma kada kije kidafa abincin.

Fita tayi tana masifa, tashi Fatima tayi tana kuka, rikota Faisal yayi yana fadin wallahi ba zakije ba, ko kinje kinyi aikin seta hadamu da Malan, gara ki kiyi tafada da hujja. Fatima tace nide Yaya ina tsoron Malan, kuma kaji tace zatasa adukeni. Kwace hannunta tayi ta nufi kitchen. Kara fashewa Faisal yayi da kuka, yana matukar tausayin Fatima.


Zaune suke gaba dayansu afalo, Mama se kuka takeyi tunda Malan yashigo, gashi yaga idonta yayi ja kuma gefen yayi baki, tambayar abinda akayi mata yayi, Farida ce tace Yaya Faisal ne ya nausheta a ido dan tace ina zeje.

Saurin kallon Faisal Malan yayi, shima ga bakinshi nan afashe. Cikin kuka Mama tace tunda nake da kai ban taba bata maka rai ba, narike maka yara tsakani da Allah, amma yau nice yaranka zasu hade ma kai, shi Faisal ma hada naushi na.


Ita kuma Fatima na sata aiki tace bazatayi ba. Allah yasani nayi iyakar yina, bazan iya zama ana cimani mutuncina da girmana ba, domin nima na haifa, kuma babu wani Dan da zega ana dukar Uwarshi ya kyale.

Badan ina zaune da yaranka lafiya ba, Allah kadai yasan abinda zaka dawo ka iske a gidan nan, domin nice na raba fadan da akai tsakanin Fahad da Faisal, domin Fahad baze iya ganin ana dukana ya kyale ba, shima Farouk dan na hanashi ne.

Amma wai har Fatima tasan tashigar ma dan uwanta, wannan wace irin rayuwa ce haka, gaskiya idan har baka dauki mataki ba wallahi sena bar maka gidanka, idan yaso seka zauna da yaranka ni kuma in koma gidanmu.

Malan yace haba Hauwa meyayi zafi haka? Ai ko dabba inde ta gidan nan ce zata iya bada shedar yanda kike zaune da yaran nan, kuma ni ba sakaran Uba bane, bazan lamunci irin wannan rashin tarbiyar agida na ba.

Kallon Faisal yayi yace kaji abinda tace, anyi haka ko ba'ayi ba? Mama tace karyata ni kake ma? Malan yace niba karyataki nakeyi ba, inso ya amsa da bakinshi ne. Ina tambayarka? Shiru Faisal yayi hawaye ne kawai suke zuba a idonshi.

Cike da bacin rai Malan ya wanke shi da mari, tashi yayi yadauki dorinarshi, haka yakama Faisal da Fatima ya zanesu, Fatima se kuka takeyi tana boyewa bayan Faisal, shiko se kara kareta yakeyi.

Malan kuwa dukansu yake yana fadin yara kanana daku har kun isa ku raina matata, wato Uwarku taje wajenku tayi maku mummunar hudu ba, shiyasa da kuka dawo kukazo da sabon rashin kirki.

Ada ai ba haka kuke ba, se yanzu da taje wajenku, to wallahi zan iya maido ku Day ba damuwata bace, bazan zura ido ina gani abata mani yara ba. Ganin dukan da yake masu yasa mama tace kabarsu haka nan ai sun daku.

Wurgar da bulalar yayi yana fadin gobe ma ku kara. Sosai suka bama Farouk tausayi, domin yasan ba gaskiya Mama ta fada ba, kawai de baze iya karyata ta bane. Sosai jikinsu ya fashe, Fatima se shashsheka takeyi.

Mama tace kayi hakuri nasa ranka yabaci, abun ne naga kada yayi yawa shiyasa na fada maka, amma ba wannna bane karo na farko da suke mani rashin kunya, kawai banason yawan kawo karar sune, domin suma yarana ne.

Amma na yau yayi yawa shiyasa na fada maka, gashi nan ranka ya baci abanza. Malan yace ke zan bama hakuri, kuma daga yau bance ki kara boye mani duk abinda sukayi maki ba, shi icce tun yana danye ake lankwasa shi.

Nan gaba bamusan abinda zasuyi ba, nagode da irin kaunar da kike nuna mani. Kuma zan kira Alhaji Mansur ince yajama matarshi kunne, idan kuma taki zan maidosu Day. Kutashi kubani waje, yaran Banza kawai.

Ruwa Mama takawo mashi tana fadin dan Allah kasaki fuskarka, banaso ina ganin bacin ranka, da na san haka ne ma daban fada maka ba. Murmushi Malan yayi yace shikenan yawuce, amma zamuje chemist aduba mani idonki, dan banzan yaro ze bata mani fuskar mata. Murmushi Mama tayi tana fadin ai yarinta ce, aranta tana fadin burina yacika tunda ka dokesu.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/3, 5:38 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
😭😭😭

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Part 55 ⏩ 60

Malan kasa kiran Alhaji Mansur yayi, domin yana matukar jin nauyinshi, zama yayi ya tsara mashi message ta yanda ze fahimci abinda yake nufi cikin ruwan sanyi, dan yana tsoron yayi mashi rashin mutunci kuma aikinshi ya samu matsala.

Assalamu Alaikum.

Ya gida kuma ya aiki, nasan zakayi mamakin wannan sako dana rubuto maka. Bawani dalili bane se dan inaso in toshe wata matsala da take shirin fitowa daga gidanka.

Kamar yanda kasani ni tsohon mijin matarka ne, kuma akwai yara guda biyu atsakanin mu, matarka tayi matukar kokari wajen raba tsakanina da yarana.

Kwata kwata yarana basa sona saboda mahaifiyarsu, bayan mun rabu da ita daga lokacin nafara samun soyayyar yarana. Amma yanzu sena samu labarin tafara bibiyarsu tana so takara raba tsakaninmu.

Kuma zuwan datayi wajensu tabbas naga sauyi daga wajensu, domin sabuwar hudubar datayi masu tashiga zuciyarsu, kuma tayi matukar tasiri, yanzu dariyar da suke mani ma sun dena, basa zama kusa dani.

Basa son sauran 'yan uwansu, babban abinda yafi daga mani hankali shine abinda Faisal yayi. Kamar Faisal har yasan yayi fada da mata ta, wallahi da za kazo da kaga yanda ya nausheta a ido.

Nasan yanda Hauwa take matukar sona shine ya hanata kai Faisal wajen 'yan sanda, bakaga yanda idonta yayi ja ba. Ita kanta Fatima da take karama idan ta sata aiki batayi.

Wannan abu yayi matukar tada mani hankali, shiyasa nace zan maka magana domin kajama matarka kunne. Wallahi Alhaji ina matukar ganin girmanka shiyasa nakasa kiranka.

Da ace wani ne ba kai ba Allah kadai yasan matakin dazan dauka, da zaka tambayi mutanan unguwar mu na Mani zasu fada maka halina. Amma kai kana da girma a idona bazan iya maka rashin kirki ba.

Kuma matarka taci darajarka,kuma bata isa inkirata muyi maganar ba, kawai na fada maka dan kaja mata kunne. Kada takara zuwa wajen yarana, abinda nake siya masu ya ishe su.

Kuma ina matukar kokari akan yarana, babu abinda suka nema suka rasa. Idan kuma taki daukar maganata, to zan iya cire duka yaran daga makarantar in maidosu nan kusa dani suyi Day, idan nayi hakan nasan bazata iya tasowa tazo gidana wajensu ba.

Ina fatan zaka fahimci abinda nake nufi? Nagode.

Principal,
Science Faskari.
Malan, Bature Mani.


Malan ya karanta message din da yayi yafi so 5 kafin ya tura, domin bayaso ya rubuta wata kalma marar dadi wadda zata batama Alhaji rai, domin shide aikinshi yakeji.

***** *****

Lokacin da message din yashigo Alhaji yana kwance kusa da Inne suna fira, Inne ce ta miko mashi wayar tana fadin gashi anyo maka message. Alhaji yace nifa bana son duba message, yanzu haka campany ne.

Amsar wayar yayi ya bude, saurin tashi zaune yayi ganin wanda ya turo mashi sakon. Murmushi yayi yace Innen yara ga mutuminki yayo mani sako.

Inne tace to akaranta mana muji. Alhaji yafara karanta mata tana sauraro, seda yagama sannan ya juyo yana kallon Inne. Hawaye ne suke zuba daga idonta. Murmushi yayi yace wannan kukan kuma na meye? Kara fashe tayi da kuka.

Lallashinta ya farayi yana fadin haba Innen Yara, meye abin kuka anan? Daga ganin yanda ya rubuto wannan sakon kema kinsan yana jin tsoro.

Kuma tunda baze iya kirana ko yazo yasameni muyi magana baki da baki dashi ba ai yayi abanza. Kuma babu wata shari'a data raba tsakanin Uwa da 'ya'yanta, koda kuwa basa tare da Ubansu.

Kuma wannan maganar banza ce yake fadi, sede kamar yanda yabani girmana, kuma ya nuna yanajin nauyi na, nima bazan bada kai naba. Kiyi hakuri da hukuncin dazan yanke yanzu.

Kamar yanda ya bukaci kidena kula mashi yara dole zamu samo wata mafita, domin ya gane baki zuwa wajensu, sede kuma ba kamar yanda yafada abun ze kasance ba.

Zan tura mashi message na ban hakuri, kuma zance inde nine mijinki bazaki kara zuwa wajensu ba. Sede zamu sake salon kai masu ziyara, haka kuma zamu jama su kunne akan kada su sake su fadama kowa kina zuwa.

Idan zakije ganin Fatima gidan Principal zamuje kamar munje wajenta, kinga zata sa akira Fatima tazo gidanta batare da Farida ta sani ba. Na Faisal kuma me sauki ne, domin babu wanda ze fada mashi kinje.

Kiyi hakuri, duk wannan abun da yakeyi na lokaci kadan ne, da yaran nan sun girma komai zezo karshe, domin ayanzu ne kawai yakeda iko dasu. Ina me tabbatar maki akwai ranar da se yazo wajenki yana rokon kisaka baki domin surika zuwa wajenshi.

Kuma banaso wannan maganar tashi ta dameki, tunda ni yayi ma magana ki bar mani komai a hannuna, domin da dan gari akanci gari. Murmushi Inne tayi tace nagode Alhaji, bansan da wane baki zan gode maka ba.

Alhaji yace kin gama mani komai, domin kin rike mani marayuna tsakani da Allah. Lokacin da mamansu ta rasu kukan da nayi hada na tunanin matar dazan aura, wane irin riko zatayi masu.

Ga sude yara nasan idan ban samu mace tagari ba shikenan rayuwarsu zata shiga matsala, kina ganin se yanzu Ansar zeje secondary, ita kuma Khairat tana primary 4, kinga ko ai za'a kwaresu idan basu hadu da marikiyar kirki ba.

Inne tace ai bakomai, kowa yarike dan wani ze samu lada me tarin yawa, bare kuma marayu, wadan da ko kansu ka shafa kana da lada. Wallahi banajin bakin ciki dan ina rike yaranka da kyau ni kuma nawa ana wulakantansu. Allah yabani ikon cigaba da kula dasu. Alhaji yace amin, kema ai kin kusa sauka. Murmushi Inne tayi.


Faisal gaba daya ya canza agidansu, idan kaga yana magana shida Fatima ne, haka idan yana dariya da ita duk wanda yazo yake denawa, tsakaninshi da Malan gaisauwa ce kawai.

Haka ma Mama gaisuwa kawai take hadasu. Fatima ma sam tadena kula kowa, duk aikin da tasan tanayi bata bari ayi mata magana, tana tashi take yin abunta. Haka idan rana tayi zataje ta tambayi Mama abinda zata dafa.

Sosai Fatima ta iya aiki da girki, domin Mama abincin safe kawai takeyi, amma komai Fatima ce keyi, tun tana nuna mata yanda zatayi har ta dena. Farida kuwa sede adafa taci, bata aikin komai se zama cikin manya.

Ko wankin da Faisal yake ma Farouk yanzu ya dena, shima Farouk din yadena bashi, kuma shikadai ne yake kula su Faisal, kasancewarshi bame son magana ba yasa ba koda yaushe yake masu magana ba.

Fahad kuwa yafi kowa rashin mutunci agidan, Malan kadai yake tsoro, amma baya daga ma kowa kafa hatta da Mama, kuma duk tafi sonshi shida Farida, kuma sunfi kowa rashin kunya.

Bayan kwana biyu Alhaji ya maido ma Malan amsar sakonshi. Sosai Malan yaji dadin abinda Alhaji yace, kuma yaji dadi daya fahimceshi, dama tunda yatura sakon yake cikin zullumi, musamman da yaga anyi kwana biyu be maido mashi da amsa ba.

Mama yakira yace dama nafada maki zan dauki mataki akan zuwan Jamila wajen su Fatima, dazu Alhaji ya maido mani da amsar sakona, kuma yabani hakuri sosai, yace besan haka abun yake ba da be barta taje ba.

Kuma yace baze kara barinta taje wajensu ba matukar shi take aure. Dariya Mama tasa tana fadin yanzu haka shima yafara gano bakin halinta, ina nan da kai ya kusa korota daga gidanshi.

Malan yace ai shima yana da yara, kuma awajenta suke, yanzu haka tafara kokarin rabasu dashi kuma wannan message din danayi mashi shine ze kara haska mashi asalin boyayyen halinta.

Mama tace ai naji dadi, kaga yanzu yaranka zasu dawo kamar da. Malan yace na manta ma ban fada maki ba, kifadama yara nan su shirya gobe zamuje Mani tunda saura sati biyu su koma, Hajiya tana maganar ban kaisu sun gaisheta ba.

Mama tace ai nima abinda naga yafi tunda de ka kusa aje aiki, kuma lokacin da zaka aje aiki Mazan ne kawai suka gama karatu, kawai da anyi hutu murika tafiya Mani, tunda kaima idan akayi hutu ba aiki kake zuwa ba.

Kaga fa tunda suka dawo basuje islamiya ba, kuma ni nafison islmiyarsu ta Mani, gara murika tafiya can, suna komawa hutu semu dawo nan, suma kansu sunfi sabawa da unguwarmu ta can.

Gashi akwai yaran da zasuyi wasa acan, kuma ni nafi yarda da tarbiyar yaran can. Malan yace ba naki taki bane, inajin tsoron su Faisal surika zuwa Mashi wajen Kakanninsu, tunda de yanzu Uwarsu ta bar garin amma akwai iyayenta ai.

Mama tace matukar kaja masu kunne nasan bazasuje ba, kuma yaushe rabonsu da garin, bama zasu iya gane gidan ba. Malan yace yanda kikace haka za'ayi, kawai ki sasu kowa ya hada kayanshi se amaidasu can, idan yaso se mubar namu tunda zamu dawo.

Cike da farin ciki Mama tace nagode. Zuwa tayi ta fadama Yaran suje su hada duka kayansu gobe zasu koma Mani. Wani murmushin farin ciki Faisal yasaki, har seda hakoranshi suka fito.

Ita kanta Fatima seda tasaki dariya, sauran yaran kuwa ihu sukasa hada tsalle. Ido kawai Mama ta zuba ma Faisal, wato yana son akoma can shima, tsaki taja aranta tana fadin kunci sa'a nima inaso murika zuwa saboda ina son garin.

***** ******

Washe gari tunda safe Mama taje yima Zulai sallama ta fada mata nan da sati 2 zasu dawo. Zulai tace kawaide kinyi mana wayau, Mama tace haba ba haka bane, kawai ina kewar gida ne. Zulai tace to Allah ya tsare, ayo mana tsarabar Mani.

Haka suka kulle gidan suka tafi, acikin mota Farida da Fahad se wasa sukeyi suna dariya, Fatima kuwa tana kusa da Faisal yana bata labarin Saleem. Se dariya takeyi, tace ai da mun koma zan fadama Lubna kuna tare da Yayanta, dama ta fada mani Yayanta yana makarantarku. Duk haushi ya gama cika Mama ganin yanda suke labari suna dariya.

Lokacin da suka isa Abba da Saddik suna kofar gida suna wasa, da gudu Abba yashiga gida yana fadin Amira fito gasu Fatima Da Yayanki Faisal. Abinci Amira takeci alokacin, ai da gudu ta tashi tayi waje, duk kiran da Mama take mata tadawo tasaka hijab amma bataji taba.

Su Faisal suna fidda kaya yaji an rungumeshi ta baya ana dariya. Fatima ce tace lah, Yaya Amira ce, saurin juyowa su Malan sukayi suna kallonsu, juyowa Faisal yayi yana dariya ya kama kafadarta yana fadin Amirata ashe kinji nazo.

Sakin baki Malan yayi shida Mama yana kallon yanda Faisal yake wata irin dariya cike da farin ciki, shi betaba ganin farin ciki akan fuskar Faisal irin na yanzu ba. Saddik ne yace Fatima angirma.

Dan kwalinta ta buga mashi suna dariya, acikinsu babu wanda ya kula su Fahad, se murnar ganinsu Faisal sukeyi. Amira tace dan Allah Yaya kada ka kara tafiya ka barni, Faisal yace bazan karaba kinji? Kai ta daga tana murmushi.

Mama ce ta buga masu tsawa tana fadin dalla sakar masu yarinya, ko an fada maka Fatima ce da kuke ciki daya zaka rika taba ta.

Saurin sakin Amira Faisal yayi tare da hade fuska, turo baki Amira tayi tana fadin aide shima Yaya nane. Malan yace haba Hauwa meye haka? Ke bakisan yara ba, kuma bakisan yanayin da Amira take ciki ba.

Mama tace idan ita bata da hankali aishi da hankalinshi, meye amfanin riketa da yakeyi, kai dalla kuwuce yanzu mukazo zakuzo kudame mu. Hannun Amira Abba ya kama tana ta hararar Mama suka wuce, idonta har ya cika da kwalla.

Haka suka shiga da kayan ciki ran Faisal a abace. Fita Malan yayi yana fadin zanje wajen Hajiya nasan yanzu gyaran gidan zakuyi. Mama tace gaskiya kam, saboda yayi kura. Yana tafiya tasa su Faisal da Fatima su share gidan, wani kuma ya goge.

Farouk yace kai Fahad kaje ka gyara mana dakin mu ni kuma in gyara dakin Malan. Mama tace bazeyi ba, ai kanajin wadan da nace suyi aikin shine kai kuma uban iyayi zakace yaje ya maku shara. Farouk yace gaskiya Mama abinda kikeyi baki kyautawa.

Allah fa yana kallonki, yanzu kanar Fahad da Farida ba zasuyi aiki ba, kuma ai Malan yace arika sa kowa aiki. Kuma wallahi idan basuyi ba sena fada ma Malan, juyawa yayi yashige falon Malan ya fara sharewa.

Sakin baki Mama tayi tana kallonshi, yaushe yaron nan yafara rai nata? Wato yanzu bayansu Faisal yakebi kenan? Idan ko haka ne zata dauki mataki. Kallon Fahad tayi tace yi hakuri kaje ka share maku dakin.

Kaji de yace ze fadama Malan, kuma Malan zaneka zeyi, kabari zan kamashi, Fahad yace kaji Mama, to tsoronshi kikeji, nide bazan share ba, sede kishare mana. Mama tace haba Fahad, nima zan gyara mana kayan mu ne, kayi hakuri zan baka naira 100 ka kashe.

Da kyar ta shawo kanshi yatafi yaje yafara sharewa. Haka suka gyara gidan yayi fes, sannan kowa yaje yayi wanka, Malan ya aiko da cefane, haka Mama tasa Fatima ta dafa masu taliya.

Zaune Faisal da Fatima suke agidansu Amira, se wasa sukeyi, Faisal da Amira kuma suna gefe ta dauko mashi littattafanta yana dubawa, sosai yaji dadi ganin yanda Amira ta iya rubutu, kuma tana karanta duk abinda ya rubuta mata.

Maman Saddik da Baba sunji dadin dawowar su Faisal, dan kullum Faisal yana gidansu suna wasa da Amira, kuma yana koya mata karatu, da Maman Saddik ta fada mashi za'a kai Amira Secondary sosai yaji dadi.


Mama sosai takejin haushin zuwan su gidansu Amira, tana so ta fada ma Malan kuma tana tsoron kada yagane tana jin haushinsu ne, hakan yasa ta kyalesu, sede Fatima bata cika zuwa ba, sede idan Mama ta fita, dan ko taje se Mama tasa ankirata tasa ta wani aiki.

Sosai su Momyn Teemah sukayi mamakin girman Faisal da Fatima, domin sunje har gida sun gaishe su, har seda Momyn Teemah ta kira Inne ta hadasu suka gaisa. Ana bama Fatima wayar ta sama Inne kuka.

Duk abinda akayi masu seda tafada mata, hada dukan da Mama tasa Malan yayibl masu seda tafada mata, kuka sosai takeyi tana fadin dan Allah Inne kizo kidauke ni. Itama Innen kuka takeyi.

Haka tarika lallashin Fatima kuma ta fada mata yanda Abbansu yace, kuma tace kada takara bama Farida komai, kuma kada tabari tasan tana zuwa. Fatima tace bazan fada mata ba.

Faisal ne ya karbi wayar, shima seda yayi kuka, Inne tace kanaji ko, kada ka kara fada da Mama, itama Mamanka ce tunda tana kula daku, kaga Farouk da yake maka kirki bazeji dadi ba idan kana ma Mamanshi rashin kunya.

Duk abinda tasaka karikayi, kuma kadena rai nata, wata rana komai ze wuce, kayi hakuri kaji? Faisal yace to. Nan shima tafada mashi abinda Abbansu yace, haka suka yita fira, domin itace ta bugo.

Bayan sun gama gaisawa sukayi sallama dasu, godiya tayima Momyn Teemah. Abinci tasa masu sukaci sannan suka tafi. Suna komawa suka iske su Farouk zasuje gaishe da Hajiya.

Haka Malan yace sutafi gaba daya su gaisheta. Sosai Hajiya taji dadin zuwansu, Mama tace ai Hajiya daga yanzu nan zamu rika hutu. Hajiya tace ai haka yafi, amma ace ya daukeku gaba daya wai se dogon hutu sannan zakuzo.

To ya gidan, kuma ya hakuri da yara? Tabe baki Mama tayi tana fadin Hajiya kinsan ai yanda zama da Dan da ba naka ba yake, sede hakuri kawai, amma inashan wahalarsu Faisal. Kwanakin baya har naushi na yayi a ido.

Kalli wajen har yanzu be gama washewa ba. Hajiya tace shi Faisal din? Mama tace wallahi kuwa, ai da gashi har Fatima sun rai nani, ko aiki na sasu basayi. Hajiya tace ja'irai masu hali irin na Uwarsu.

Kunnan Faisal dana Fatima takama ta murde tana fadin, idan kuka kara mata rashin kunya se nasa Malan ya maidoku wajena, se inga koni zakuyi mani rashin kunyar. Mutanan banza, ko kunyar Diyanta bakwaji kuke mata rashin kunya.

Seda Fatima ta fara kwalla sannan ta sakar masu kunnan. Haka Mama tayita fada mata karya da gaskiya tana kara batasu awajenta. Sosai ran Hajiya yabaci, haka ta yita bama Mama hakuri, kuma tace idan suka kara ta kirata ta fada mata.

Zatasa Malan ya maidosu wajenta. Haka suka wuni aranar, su Farida se wasa sukeyi, shiko Farouk yama tafi wajen abokanshi, Faisal da Fatima jisukayi kamar sutafi, dande Malan yace zezo ya daukesu, ko abincin da aka basu beda wani yawa.

Lokacin da Malan yazo daukarsu haka Hajiya tayi mashi fada akan yarika tsawatar ma su Faisal akan rashin kunyar da suke ma Mama, kuma tace idan suka kara ya maidosu wajenta. Malan yace ayi hakuri Hajiya, nima na nadauki mataki, kuma bazasu kara ba. Haka sukayi mata sallama ta bama yaran Mama kudi tana fadin bazan ba marassa kunya ba, seda Malan yaji ba dadi abinda Hajiya tayi, haka suka tafi.

****** *****

Lokacin da hutu yakare haka Malan yayima kowa provision, har Faisal seda ya siyama wasu abubuwan kasancewar shi basa zuwa da komai na abinci amma seda ya siya mashi sabulun wanka dana wanki da omo, mai hada turare da maclean.

Sosai Fatima da Faisal suke cikin farin cikin komawa warsu, dan Fatima duk ta rame, shima Faisal duk ya yi baki ya rame. Amira kuwa tasha kukan tafiyar Faisal, shima seda yayi hawaye, dan yanda Amira take kuka.

Faisal ya rigasu tafiya dan tare suka tafi da Nura, Baban shine yakaisu Katsina, seda Fatima tayi kuka daze tafi. Su Fahad se dariya suke mashi dansu se ranar lahadi suke komawa, su kuma asabar shida su Fatima.

Kafin Malan yaje yadawo haka Mama ta kwashe kusan rabin kayan Fatima ta karama Farida, kuma ta sama Farida sauran abubuwan data siya mata, babu wanda yasan ta kwashe dan Fatima tana dakinsu kuma sun gama hada kayansu sun kulle komai.

A cikin jakar Farida Mama tasa mata dubu daya tace kada tabari Malan yasan ta bata idan ba haka ba baze kara mata ba. Haka Malan yazo suka saka kaya amota, seda Mama ta rakosu sannan ta bama Fatima dari 200 tace gashi ku kara ko, kema Farida ga taki Dari biyun, se ku kara da wanda Malan ze baku, adage ayi karatu kunji.

Sosai Malan yaji dadi kuma yayi mata godiya, haka suka tafi Farida tana kuka. Lokacin da suka isa malan ya basu dubu dai dai kuma yayi masu nasiha akan su kara dagewa. Kallon Farida yayi yace kada kimanta da addu'ar dana baki, kullum kirikayi duk abibda kikeji zaki dena, kuma kokarinki ze dawo.

Kallonshi Fatima tayi, wato Farida kadai ze bama addu'a banda ita, kwallace ta cika mata ido, shi kuma Malan anufinshi saboda yana tunanin anyi mata asiri. Ita ko Fatima se ta karajin haushin Malan.

Haka yayi masu sallama yatafi, da gudu Lubna tazo ta rungume Fatima tana dariya, itama Fatimar dariya tayi tana fadin ashe kin dawo? Lubna tace tun dazu. Tsaki Farida tayi ta dauki kayanta tana fadin aikin banza.

Zinatu ce tazo tana fadin ga kawata, rungume juna sukayi suna dariya, haka suka nufi hostel. Lubna ce tace Fatima amma rashin lafiya kikayi ko? Kwallar da Fatima take boye wace ta zubo.

Kamata Lubna tayi tana fadin mutafi kada aganki kina kuka, haka suka dauki kayan suka tafi........... Duk abinda Mama tayi masu seda Fatima ta fadama Lubna, sosai Lubna taji tausayin Fatima, har seda tayi mata kwalla.

Hakuri tayita bata, haka suka fara fiddo kaya dansu jera a loka. Tsayawa Fatima tayi tana kallon kayanta, fashewa tayi da kuka tana fadin wallahi ba haka Malan yasiyo mana ba. Mama ce ta kwashe mani kaya, ai dama tunda tace intafi daki nasan kayana zata kwashe.

Lubna tace kiyi hakuri, taje tayi ta kwashewa,

Please Login or Register in order to submit comment