You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tai ahankali tana jinjina kai kafin ta bude baki tace
"Daddy banason komai ya samu My Jan,
Batada lafiya,tanada heart problem Daddy"
Kallan falaq din yayi da sauri yana mamakin yanda akai ta sani
Gyada masa kai tayi tana cigaba da cewa
"Yes Daddy,ta fada mun sbd naga yanka a gurin heart dinta inata tambayanta meya jin mata ciwo a gurin so ta fadamun,
Daddy tayi fama da ciwon zuciya na shekaru masu yawa tin yarinta,
Ta rasa shekarunta na yarinta,
Ta rasa childhood nata,
Ta taso a boye sbd ciwonta,
Ta cire rai daga rayuwa kwata kwata sbd ta kasa samun donor sai a lokacin da time ya qare mata aka samu donor daga wani namiji wanda aka bata zuciyarsa shine Allah ya bata sabuwar rayuwa sbd kwananta be qareba,
Daddy jannah nada zuciya me kyau wanda ban saniba ko zuciyar datake kirjin nata ne amma tin daga lokacin data warke haryanxu bata denawa wanda ya bata zuciya addua ba..."
Yanda hannuwansa suke rawa sosai yana kokarin hana falaq din ganewa sbd yanayinsa dayake sauyawa matsalansa na neman dawowa ya sakasa miqewa yana kasa iya cigaba da saurara ya bar dakin baya ko gani sosai ya nufi palonsa ya shige ya rufe ya nufi bedroom dinsa wanda yana isa kasa iya cire kayan jikinsa yayi sedai ya yagasu da karfin gaske yana jefarwa ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwan dumin da hayaqinsu ke dan fita ahankali suna gauraye toilet din shikuma sosai jikinta ke rawa ya daki bangon toilet din da karfin gaske har saida hannunsa ya fashe amma sam bayajin komai sai masifar dayake ji a cikin kansa da kirjinsa mai tsananin gaske.
Jinin dayake zuba a hannunsa ne yake gauraya da ruwan dayake sauka a qasa daga jikinsa suna sauya kala suna gangarawa.
A duk lokacinda maganar yanda aka raba Ummitah da ranta ta taso yanayinsa tashi yake wanda duk yanda yake ganin likitocinsa many akan hakan yanayin ya kasa rabuwa dashi lokaci daya duk da ya rage sosai amma yanayi me matiqar hadari yake shiga batareda sanin kowa duk duniya ba bayan Sayd.
Trauma din Ammar Zad a bayyane take wanda shi kuma tasa dataci uban ta Ammar din yake a boye sbd yafisa sanin gwagwarmaya da iya taku tareda kwarewa a iya controlling kansa sabanin shi nasa dayake bayyane ga duniya ma kila.
Ya dade a ciki kafin ya samu iya controlling kansa yanayinsa ya fara dawowa daidai ya zari towel ya dauro a qugunsa ya fito bayan ya nade hannunsa dayake dan zubar da jini har lokacin ya shirya a natse yana kallan fuskansa cikin mirror zantukan falaq na yawo a cikin kunnuwa da zuciyarsa har lokacin,
Menene Jannah din take nufi da zuciyar namiji ne a kirjinta?
Boye gaskiar ne takeyi kokuwa iyayen nata da lover boy din nata basu fada mata gaskia ba?
Shin kafin komai ma da saninta kuwa suka raba wata da ranta dan bata zuciya?
Ta Aminta da a raba mace me tsohon ciki da ranta dan ita ta samu sabuwar rayuwa?
Dakatawa yayi daga saka agogon diamond din dayake hannunsa ya zubawa mirror idanuwansa da har lokacin basu qarasa komawa daidaiba abubuwa da yawa ne suke cikinsu suna qonasu.
Karfe goma ya fito dauke da wayarsa yana duba tarin misscalls daga Zaadens wanda babu wanda ya gani bare dauka.
Su mama dake palo dukkaninsu Qamshinsa ya gauraye palon cikin sanyi ya sakasu kallan hanyar fitowansa
Sai gashi ya fito kwarjinsa da kamewansa ta saka su fadilah sauke idanuwansu mama kadai ce bata dauke idanuwanta akansa ba cikin kulawa ta amsa gaisuwansa tana sake tambayar jikin jannah duk da taje ta dubota har so biyu da safen.
Fadilah dagowa tayi cikin girmmawa da wayewa ta gaidasa ya amsa batareda ya kalleta ba ya nufi dining.
Dukkaninsu yau sukai breakfast kaman yanda suka saba hadda falaq sbd jannah nata farfado ba.
Suna gamawa su dr Sameera suka iso shikuma ya fice daga gidan.
Yana ficewa Anny da Mimi tareda saleem da maheer da mommy suka iso gidan sukuma.
Dukkaninsu babu wanda zuciyarsa bata tabu da yanda suka gantaba da yanda ta koma.
Abinda ya dan ragewa Mimi tsananin nauyin da kirjinta yayi shine ganin yanda falaq take kulawa da jannah din sbd koda suka iso ta rage mata kayan jikinta tana goge mata jikinta da lallausan qaramin towel da ruwan dumi sosai ita da Fiddausi.
Hadiye hawayenta Mimi tayi sbd duk gwagwarmayansu akan jannah ta qare a inda masu aiki ne da qaramar yarinta ke kulawa da ita tana yashe a daki batareda anbata taimakon datake buqata ba.
Ga wanda bai taba mahimmancinta da komai na rayuwarsa ba an cutatar dashi ta hanyar hana masa abinda zuciyarsa ke so ita kadai idan Ammar ya samu ya yadda ya fuskanci kowane irin talauci da ukubar rayuwa idan har jannah na tare dashi.
Anny ma sanyi jikinta yayi sbd bata taba dauka jannah zad zata taba dawowa haka ba,
Idan har zaa iya daukan rayukan mutane akan jannah to bata taba tinanin zata taba ganin jannah a irin wannan halinba na daukanta batada mahimmanci ko kadan.
Suna gidan likitocin da suke dubata suka buqaci zaa koma asibiti da ita sbd acan xaa bincika ciwonta dakyau yanda ya kamata.
Kai tsaye Maheer ya nuna rashin Amincewansa da hakan karshe ma ya mama yayi magana da ita da kansa akan suna son tafiya da jannah din sbd tanada likitocinta na musamman da zasu taho dan ita kadai daga wata qasar.
Mimi ma baki ta saka suka buqaci Amincewan maman sbd ita kadaice zata amince su tafi da jannah din AZIZ ya dawo baice komaiba.
Mama ita kanta batason a tafi da jannah din amma yanda mimi tai mata bayanin yanda yanayin ciwon jannah din yake sai tace saita kira AZIZ ta sanar masa.
Kiransa tai yana dauka kai tsaye ta sanar masa tanason ya bari iyayen jannah suje da ita gida likitocin da suka saba dubata su dubata tinda haryanzu bata farfado ba.
Shiru yayi batareda yace komaiba tsawom mintina kafin ta sake maimaitawa ya bude baki a taqaice yace
"Ba damuwa duk yanda kikace mama amma su tafi zan kaita na kaina amma sai likitocin nata sun sauka qasar ina buqatan ganinsu da kaina"
Yana gama fadan hakan ya kashe wayar sbd yasan suna sauraronsa.
Mama kallansu tai sbd sunji da kunnensu idan sun aminta da hakan shikenan idan basu aminta ba itama tafiya da jannah bai kwanta mata bare falaq datake jin kaman zatai kuka zuciyarta da jikinta na sanyi.
Basada zabin daya wuce amincewa da hakan dan haka suka tattara suka koma da jiran saukar su Abraham da Ken Nigeria sbd tin barin Ken Nigeria ya koma yaron Abraham ya zama baturen kansa shima sbd ya tabbatarda idan ba cigaba yayi da binsu ba zai samu kansa a matakin da dr ismail ya taka sbd duk wanda yake cikin wannan sirrin an dade da rife babinsa iya su yanzu suka rage.
Wanna sharadin na AY LIMBA ya saka dole zuwansu Abraham ya dawo a kwana daya dan haka a washe gari ake jiran saukarsu Nigeria.
Ammar ya dawo daidai sedai ciwone yanzu me tsananin radadi yake cin zuciyarsa,
Kewan mahaifiyarsa yake sosai radadin rashinta na dawo masa,
Ya rasa walwalwansa da farin cikinsa gabaki daya bayajin dadin komai na duniyar jin yake inama yabi Amminsa ya huta da abinda yakeji a zuciyarsa da gangar jikinsa.
Hoton jannah dayake dakinsa ya qurawa idanuwansa dasuke masa yaji da radadi sunyi jajir ya bude baki zaiyi magana amma baya iya cewa komai sbd tsananin damuwar datake neman taba kansa.
Mimi da Saleem suke tsananin jin ciwonsa a cikin ransu suna jin tasu zuciyar na cikewa da nauyi da dacin ganinsa a halin dayake ciki sbd ya dena fitowa kwata kwata,
Dad da daddy mahmoud duk yanda suke zaryan zuwa dakinsa sam baya budewa sbd bayason ganin kowannensu sbd idan yana ganinsu Amminsa yake gani a tare dasu dan haka baya son ya tsanesu sbd tsananin kaunar dayake wa Amminsa.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
75
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
***********
Sai dare ya dawo gida shi kadai sbd Sayd yana jos acan zai kwana yaje karbo duk wasu takardu da records na Asibitin Zaadens daya boye bayan wanda suka tabbatarda sun karbe daga hannunsa sbd AZIZ da kansa yayi magana da Matar ismail din sbd ya bayyanar mata da kansa tareda sanar da ita komai dan haka da kanta ta kusa cikin kayan Dr ismail ta samo musu duk wani abi da zai dan taimaka musu ciki kuwa hadda date na ranar aikin da time da akai aikin da record din Ummitah na komai da sukai mata tin a asibitin dr ken tareda copies na transactions da akai musu shi da dr ken da tarin kudaden da suka ringa basu masu yawan gaske.
Koda ya iso gida kusan duka kowa ya shige dan haka kai tsaye Bedroom dinsa ya nufa yayi wanka ya sauya kaya zuwa na bacci masu dan kauri ya fito sanye da slippers a kafafunta.
A kaidar aikin Fiddausi indai yana gari to ko karfe nawa zekai bai dawoba zata jira dawowansa sbd gabatar masa da abinci kokuma tea ko wani abinda zai buqata na ci nara nauyi.
Dan haka ko yanxu ma batai bacci ba suna dakin Jannah itada falaq datai bacci a zaune sbd tsaron jannah,ita kuma tana kokarin goge mata jikinta da son sauya mata kaya taji anbude kofar dakin kai tsaye a natse.
Juyowa Fiddausi tayi a natse taga shine take ta ajiye rigar jannah din data zare tana miqewa tsaye da girmamawa tai masa sannu da zuwa.
Falaq ya kalla cikeda tausayawa yaga yanda itama ta fada kafin ya maida kallansa akan jannah wadda take qara ramewa da sauyawa sosai a kwancen.
Numfashi mara sauti yasauke kafin ya tako a hankali ya rankwafa ya dauki falaq gabaki dayanta ya juya ya fice da ita xuwa dakinta ya kwantar da ita ya rufeta da abin rufa yayi mata addua ya kashe wuta tareda daidaita mata ac ya fito ya rufeta ya koma dakin jannah din.
Koda ya isa Fiddausi ta sauya mata riga mara nauyi tana kokarin fara goge mata jikinta.
Tana ganinsa ta ajiye ahankali tareda ficewa daga dakin gabaki daya ta nufi kitchen ta hado masa lemon tea da sabon cake da aka gasa yau na chocolate sai dabino da madara me dumi ko zai saka a tea din tana ajiyewa ta juya ta fice tareda jan kofar dakin.
Zubawa jannah din idanuwansa yayi tsawon mintina kafin ya zauna ahankali tareda miqa hannunsa ya dauki towel din da baa warwareba ya warware ya saka a cikin ruwan zafin masu tsafta sosai da Fiddausin ta ajiye.
Ahankali ya rage ruwan towel din sosai kafin ya yaye rufar datake jikinta ahankali ya dora towel din da hannunsa a fuskanta yana gogewa.
Cikin nutsuwa da mamakin kansa yake goge mata fuskan harya kammala da fuskan ya gangaro wuyanta ahankali yafara gogewa a natse.
Yana kawowa kirjinta kasa wucewa gaba yayi ya tsaya cak a gurin yana saukar da idanuwansa akan aikin zuciyarta yana jin zuciyarsa na sanyi jikinsa na dumi damuwa da tausayin kansa daya rasa macen dayafi kauna
fiyeda komai a duniyarsa,
Ta tafi bazata taba dawowa ba har abada,ta tafi tabarsa da tabo da ciwon da bazai taba warkewaba na rashinta,
Kaunar Ummitah halitta ce da Allah ya halitta masa a cikin zuciya da jininsa,
Ummitah rayuwarsa ce,ruhinsa ce,jinsa da ganinsa ce,
Ummitah itace asalin ABDULAZIZ AYOUB LIMBA ayau daya rasata gabaki daya ya rasa kansa sbd gashinan ya koma tamkar me ciwon haukar juyewan kwakwalwa a boye,
Ya rasa wani bangare na rayuwarsa da har abada bazai taba dawowa ABDULAZIZ dinsa na asali ba sbd rashin Ummitah,
Kaman yanda take kallansa a matsayin uwa da ubanta da kuma hammanta a garesa shima Ummitah itace uwa da ubansa daya rasa da kuma 'ya da kanwarsa gaba daya itace familynsa datake dauke da matsayin kowa da family ke buqata ya cika.
Wasu hawaye masu tsananin zafin da baisan da su bane suka gangaro suka sauka akan fuskan jannah wadda idanuwanta suka bude tsowon seconds goma da suka wuce.
Idanuwanta da basa gani sosai sbd ciwo da dadewa a kwance ta zuba masa batareda ta iya motsa komai na jikinta,
Bata ganinsa sosai amma dai tasan shi dinne dan haka zuciyarta tai wani irin sanyi cikin damuwa da ciwo hawaye masu zafi sika gangaro da gefen Idanuwanta.
Hannunsa ya motsa ahankali ya dora akan zuciyarta dake bugawa cikin sanyi ahankali da nutsuwa tareda wani irin tsananin sonsa datake jin kaman illa ne ma gareta zuwa yanzu sbd ya gama tabbatar mata da bazai taba sonta ba har abada.
Shiru sukai kowannensu idanuwansu jajir da radadin da zuciyoyinsu suke ciki,
Bugun zuciyarta yake sauraro da tafin hannuwansa yana isa ga tasa zuciyar yana jin kaman ya ambace ta da sunan Ummitah ta amsa masa ko zai samu abinda yakeji a kirjinsa na shekaru ya dan fada masa ko zai iya dawowa cikakke lafiyayyan mutum daya rasa lafiya da cikakken hankalinsa....
Itama nata idanuwan har lokacin gangaro da hawaye masu ciwo da zafi sukeyi batareda ta motsaba dumin tafin hannunsa dake kan zuciyarta yana isa cikin zuciyarta yana qarasa mata illar da har abada tasani bazata taba iya dena sonsa ba sbd jinsa takeyi har acikin jininta ba iya zuciyarta ba,
Batasan wane iri so bane wannan wanda yake sakar mata ciwo da radadi ta kasa ciresa a ranta,
Bazata iyaba duk yanda taso hakan sbd son nasa yai mata mummunan illar da ita tata rayuwar ma ta gama mutuwa akansa, dan haka rufe idanuwanta tayi ahankali tana jin inama ta tafiyarta itama ta huta da wannan radadi da ciwon datake ji kila shima zai samu nutsuwar zuciya idan ta tafiyarta tabar masa duniyar.
Ahaka suka raba dare sosai har saida ta motsa kadan ta bude idanuwanta a wahalce sai alokacin ya dago ya kalleta yaga idanuwanta a bude sunyi jajir da hawayen dataita yi tin dazun.
Hawayen dake gangarowa daga idanuwanta yabi da kallo yana yana dauke hannunsa daga kirjinta tareda xare hannunsa daya dayake cikin nata ya juya ya fice baice komaiba ta bisa da kallo.
Nurse din dasuka dauka ne ya turo mata ita ta dauketa takaita toilet tayi fitsari ta gyaro mata jikinta daqyar sbd babu abinda yake motsi a jikin jannah din bata iya motsa komai nata.
Washe gari tinda safe dr Sameera ta iso gidan koda ta iso yana babban palo zaune tareda mama da sai Fiddausi dake kai da kawon aikin hada dining.
Falaq kuwa farin cikin ganin jannah ta farfado ya saka tinda safen ta saka Nurse tai mata wanka aka saka mata riga da wandon jeans marasa nauyi aka turota a kujera jannah dince ta turota suka fito palo jannah din batada karfi ko kadan magana ma bata iyayi bare iya motsawa sai an taimaka mata a komai.
Dr Sameera kuwa hannun AZIZ din da dr Ashir yayi dressing jiya taxo dubawa dan warwarewa ta duba ciki.
Cikin kulawa ta kallesa bayan sun gama gaisawa da mama a sake ta sake kallansa cikin kulawa tace
"Hannun zan duba naga idan zaa sauya bandage dinne"
Mama kallan hannun tayi tana cewa
"Yarsa ce bata lura da hannun ba da yanxu ta daga mana hankali ai"
Murmushi dr Sameera tayi yana miqa hannunta akan hannunsa daya dora mata akan Hannun sofan dayake zaune batareda ya kalletaba yana duba abu a waya.
Nurse ce ta kawowa Sameera akwatin first aid ta kama hannunsa a hankali zata fara warware bandage din su falaq suka shigo palon da jannah wadda idanuwanta da sukai laushi sosai sbd ciwo suka sauka akan hannunsa da dr Sameera ta riqe da sunan dubawa.
Tsayawa falaq tai tana kallan dr Sameera din zuciyarta ba dadi.
Jin shiru ya sakasa dagowa ahankali idanuwansa akan Jannah data dauke idanuwanta ahankali akan hannuwan nasu suka fara sauka ya zare hannunsa daga gyaran yana cewa ba buqatan wani bandage din abar masa hannun haka.
Falaq kuwa qarasowa tai gurinsa da sauri tana kama hannunsa da kulawa tana cewa meya samesa.
Mama kuwa jannah ta tashi ta qarasa turowa har gefenta tana mata sannu da ido kawai jannah ta iya amsawa zuciyarta ba dadi ko kadan sbd ta riga da ta rasa farin cikinta rayuwarta ta sauya daga jannah zad a yanxu batasan ita wace jannah dince ba.
Bata iya sake kallan inda kowa yakeba rufe idanuwanta tai tana sake zama weak yana lura da yanayinta dan haka da kansa ya maidata daki batareda kowannensu yayiwa kowa magana ba ita a yanzu kallansa ma batason yi sbd shine yake qara azabtar da zuciyarta dan haka ta hakura ta bawa zuciyarta salamar hakura da wanda baya kaunar komai daya shafeta.
Yana ficewa wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata ta rufe idanuwanta tana tsananin son ganinta cikin familynta dake tsananin buqatanta a lafiya da ciwo.
Shi kansa zuciyarsa daci take masa dan haka ko abincin kirki baiciba yace Fiddausi ta hada kayan jannah din a luggage qarama.
Sayd ne ya iso shima a lokacin latif ya daukosa daga airport dan haka tin kafin ya iso gida a waya ya sanar dashi ABRAHAM da KEN sun sauka a abuja Nigeria dan haka ya saka Fiddausin hada kayan jannah.
Da kansa ya daukota tin daga cikin dakinta a hannunsa ya fito da ita xuwa mota da Sayd ya shirya musu.
Da falaq aka tafi dan haka dashi da ita jannah dinne a bayan motar sai falaq a gaba Sayd na tuqa motar suka nufa zaadens baida niyar barinta acan din amma sbd umarnin mama ne kadai zai kaita kuma a gobe zai dawo da ita limbas.
Suna isa limbas gabaki daya familyn jiran isowansu akeyi sbd sunta kira su sanar masa isowan likitocinta amma sam babu wayar wanda ya dauka sedai suka kira Sayd suka sanar masa wanda yana sane da saukar su Abraham din sbd sun saka tsaro sosai akan isowansu.
Ammar da Mimi take riqe da hannunsa sbd yanda yake kasa riqe zuciyarsa akan jannah dago jajayen idanuwansa yayi yana kallan yanda AZIZ LIMBA yake dauke da jannah a gaban idanuwansa ya wuce da ita ciki ta gabansa ita kuma idanuwanta suna kansa tana masa kallan mamaki da bankwana sbd batajin zata iya komawa gidansa ta hakura da auren sbd zuciyarta bazata iya daukan kallan qinta a cikin idanuwansa ba da kuma yanda tsananin sonsa dayake bayyane a idanuwan Fadilah da dr Sameera dan haka ta zabi dawowa hannun familynta ta qarasa mutuwarta a hannunsu idanma ciwon bame barinta bane kenan.
Har bedroom palonta dayake hade da lafiyayyan bedroom dinta yakaita ya ajiyeta ahankali ta tsaya da kafafunta tana kallansa shima ita ya kalla da idanuwansa dake bayyanar mata da wani tsananin zafin hoton da idanuwanta suka sauka akai na Ammar hakama Ammar dinne duk yanda Mimi taso hanasa isa ga jannah din ya kasa riqe kansa dan haka akan idanuwan AZIZ Ammar din ya shigo palon idanuwansa akan jannah zuciyarsa na samun sassaucin azabar dayake ciki..
Wani kallo Daya saka jannah jin idanuwanta sun ciko da hawaye yayi mata ya bude baki tsananin dayake cikin idanuwansa baya boyuwa zaiyi magana ya fasa sbd zai iya loosing control dan haka Ammar din ya juyo ya kalla ya bude baki yana controlling kansa sbd hannuwansa da suka fara wani irin rawa idanuwansa na sauyawa yace
"Ka tabbatarda wannan kallan shine na karshe akan matar da aurena yake akanta sbd nxt kallo da zakai mata irin wannan shine ganinka na karshe sbd saina tabbatarda an saka maka da dabobbi"
Dad ya kalla yace
"Idan aka take mutuncin igoyiyina wannan shine zuwanta na karshe har abada"
Tsit sukai babu wanda ya iya cewa komai sbd rasa abin fada,
Mimi gurin Ammar da hannuwansa ke rawa sosai ta nufa da sauri idanuwansa na cikowa da hawaye masu tsananin ciwo.
Jannah kuwa tinda AZIZ din ya fara magana idanuwanta suka sauka akan hannuwansa dake wata irin rawa batareda kowa ya lura da hakanba,
Wani abu taji yana danne zuciyarta me tsananin nauyi da ciwo,
A iya saninta datake dashi tasan me wane ciwo ne yake samun irin wannan yanayin sbd akan Ammar ta fara sanin hakan,
A idanuwansa ta maida nata idanuwan tana kallan yanda suka sauya hannuwansa na tsananta rawa yana kokarin controlling kansa.
Jin tayi ta kasa riqe zuciyarta daga azababbiyar soyayyarsa data rufe mata ido har ta bari ya tafi a hakan bazaiyi nisa ba zai iya loosing control na kansa kowa ya san halinda yakeji cewan yana tattare da masifaffiyar trauma shima hakama idan har wannan shine haduwarsu ta karshe data yankewa kanta tana fatar ta kasancewa abinda zata ringa tinawa da ita dashi har abada dan haka ko taku biyu baiyiba ta tattaro karfi a jikinta ta riqosa.
Su dad na ganin hakan shi yafara juyawa ya fice....
AZIZ kuwa dayake gap da rasa control da zafin gaske ya juyo idanuwansa jajir sedai ba zato ta kamo wuyan rigarsa ta ta hade bakinta d nasa cikin wata irin nutsuwa.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
76
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
*************
A cikin tsakiyar bakinsa bakinta ya isa direct dumin bakinsu yana haduwa da juna abinda bai taba faruwa dasu su dukanba,
Bai tinda yake bayan kumatu da goshin da hannuwan falaq dayake wa pecks lips dinsa basu taba haduwa da fatar kowaba dan haka shock din dayake ciki ya ninku sbd dumin bakinta daya shiga cikin nasa da kyau yana tayar da duk wata tsigar jikinsa hannuwansa na tsananta rawa ya daga zai janyeta daga jikinsa,
Yana dago hannun ta saka nata tafin hannun a cikin nasa ta riqe hannunsa tana kissing tsakiyar bakinsa da kyau cikin nutsuwa da sanyin daya kashe dukkanin jikinsa wutar ciwonsa na mutuwa sedai tana mutuwa ne da wani sabon masifaffen zafi da tiriri jikin daya sakasa mata wani mugun riqon daya kusan karya qugunta ta bude idanuwanta ta zuba masa ahankali shima ita din yake kalla da
Book Chapters
Chapter 36
Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500