You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
bazai fito da raiba shikenan ya tafi har abada.
Ana shiga shigewa da ismail dr Nico da badashi zaayi aikinba ya kira AZIZ ya sanar masa tareda godiyar wanda suka samu donor din dan musulmi ne ma kuma me iyalai dan haka hakan ba qaramin farin ciki da sabuwar rayuwa zai kai a familyn ba.
Sayd kuwa take ya fara shirye shiyen komawar familyn dr ismail din sbd yasan shikenan komai ya qare.
A lokacinda aka isarwa da familynsa Allah ya karbi ransa yanke jiki matarsa tayi a gurin...
Qaninsa ma tashin hankalin ya shiga sedai daman sun riga sun cire rai daga tashinsa dan haka matar aka fara kokarin cetan ranta cikin gaggawa har aka samu ta dawo daidai zuciyarta tai mata wani irin nauyi kukan ma ta nemesa ta rasa sai ajiyar zuciya datake saukewa idanuwanta sunyi jajir.
Washe gari anan italy akai masa komai aka rufesa sedai acan gida aka fara zaman karban gaisuwa cikin jimami na baqin cikin rashinsa.
Kwanansu biyar a hotel da aka sauya musu sayd ya sakosu jirgi batareda sun taba sanin LIMBA ba ko kammaninsa.
Suna dawowa kuka ya dawo sabo a familyn na rashinsa wanda yaransa hudu maza biyu mata biyu suke cikin baqin ciki da qunci.
Acan italy kuwa suma a ranar da familyn suka bar qasar kwana daya suka qara suka tattara suka koma gida.
Suna dawowa kawai shirin baro kasar suka fara sbd sayd ya kai karshen Wani mahaukacin sabon mansion da aka siya har anyi payment da komai Alh Saad ne da lawyers dinsu a cikin siyansa.
Luxuries din da aka zuba gidan saida ya ringa bawa Lawyers din mamaki sbd Yace duk abinda zaa saka yayi daidai da yanayin rayuwar da falaq ta saba ta taso a cikinta dan hakanne ma aka zuba dukiya iya dukiya kaman ba nemanta akeba debowa kawai ake.
Securities din kwarai aka dauka aka zuba a gidan bayan an tantancesu tareda masu aiki wainda Latif ne a wannan bangaren yake wannan aikin dan tini ya rufe shago jin ubangijinsu the great AZIZ AY LIMBA zai dawo Nigeria,
Shine chief officer na gidan duka maaikanta gidan a karshinsa suke hakama qanansa biyu ya dauko sune drivers na gidan daya hajia mama dayan kuma wanda yafi tsananin kiyayewa da taka tsantsan drivern falaq ne.
*********Kusan wata uku suka share suna shirye shiyen kafin suka siya tickets da komai bayan ya nada sabbin presidents da chairmans da directors na companies dinsa dasuke qasar shikuma zai karba na Nigeria din.
Babban tarkon daya dana wanda shine sanadin da komai zai fara shine Siye dukkanin hannuwan jarin businesses din sauran companies dasuke aiki da Zaadens batareda saninsu ba sbd a iya bincikensa ya tabbatarda sunada power me karfi,
To idan zai kaisu qasa su nema hanyar kabarinsu da kansu to saiya fara rabasu da komai daya bayan,
Duk wani abu dasuke so a duniya saiya rabasu dashi akan idonsu......
JANNAH ZAD itace abinda sukeso fiyeda komai kuma suke komai akanta,
Tsanar da yake mata batareda ya san waye ita dinba ta gama gauraya dukkanin wani digon jinin dayake yawo a jijiyoyin jikinsa....
Itace zaiyiwa mummunan illan da suna gani batareda sun iya komaiba kafin ya karbe abinda yake nasa daga jikinta yabar musu gangar jikinta.
Bazai taba nemansu da kansu yakeson su kawo kansu gurinsa da dukkanin yarda da buqatuwarsu dan haka tashik farko hannuwan jarin daya siye da sunayen Alh Saad da Wasu manyan abokan businesses dinsa ya saka suka ringa janyewa suna cirewa daga business din zaadens wanda cikin qanqanin lokaci arzikinsu yayi wata irin girgizan data sakasu tashi cikin mummunan tashin hankali da tsoro sbd kawai companies dinsu qasa suka fara yi kaman saukan ruwan jiki......
Hakama kusan manyan ma'aikatansu da suke ji dasu take suka ringa ajiye aiki bayan sun satar musu manyan kudaden dasuka qarasa Jijjigasu kuma sata irin tsaftatacciya da babu inda suka bar evidence ko record na fitar kudaden gaske.
Neman zaucewa sukeyi take suka tashi tsaye da neman hanyar tsayar da wannan iftilain kwatsam daddy mahmoud dayake can qasar daga fita aka kira ya samu stroke.
Bp din Dzad daya dena tashi tinda Jannah ta samu lafiya ne ya tashi hankalinsu yafara tashi sedai sam basu bari duniya tasan suna yin qasa ba.
Sbd gudin raba hankalinsu biyu a yanzu da suke cikin crisis dawo da daddy mahmoud Nigeria akai suka hade mansion daya ana jinyarsa a gida kawai aka dauki manyan doctors dake zuwa dubasa kullum.
A ranar da aka dawo da mahmoud Nigeria jirgi daya ne ya saukesu a Nigeria da LIMBAS family wainda motaci suka daukesu zuwa LIMBAS mansion.
#MAMUH
##BESTSTORY
#KALBIM
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
46
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC (kayan mata)
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa niβima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah π₯°ππ»
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1kπ₯ Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4200
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
π£οΈπ£οΈπ£οΈπ£οΈπ£οΈπ£οΈ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALAππ½ππ½ππ½πππ da 6k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata ππ½ππ½ππ½ππKazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadΔ±π800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Na Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 6k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
************
Maheer dayafi mintina arbain yana waya daya a tsaye cikin office dinsu dayake gida,
Dad ne zaune shikuma yana duba tarin reports na acct histories na duka companies dinsu yana ganin yanda suka sauka qasa sosai a lokaci daya kamar aikin asiri,
Cikeda mamaki da tsananin bacin rai da baqin ciki yana duba yakardun duka partnerships masu da aka janye aka barsu.
Ammar dayake can yana nasa wayoyin da binciken cikin tsananin baqin ciki da mamaki babu wani bayani ko daya daya samu na wanda ya siye duka hannun jarin dayake kamfaninsu dan haka ya shigo office din fuskansa ba walwal ya tsaya gaban dad daya dago idanuwansa jajir ya kallesa yace
"Me aka samo??
Ka gano ko waye?
Girgiza kai yayi zuciyarsa na daukan zafi yace
"No dad,
Ko waye ba qaramin Monster bane sedai ko waye shi zamu ganosa sbd he's playing with the wrong people,
Ya taba wutan da zata konasa ko garwashinsa baa samuba"
Maheer daya gama waya cikin damuwa ya kalli Ammar din kafin ya kalli dad yace
"Duk yanda nayi sunriga sun siyar masa kuma baama sansama bare mu fuskancesa da kanmu yasan da waye yake,
Sune a tsaye akan janyewan kwata kwata duk tsawon kwanakin nan babu alamar ko hanya daya da zamu gane waye a bayansu,
Hakama muna cikin tsananin stock market crash sbd komai na sauka rapidly da dole mu dakatar da komai for now mu tsayar da marketing da duk wani aiki a companies namu aje break kafin a gano kan matsalar coz idan aka tafi a hakan babu bata lokaci zamu iya qarasa rasa komai so a tsayar da komai"
Dagowa Dad yayi ya kallesa idanuwansa na jajir sbd dakatar da komai na nufin zasu rufe komai sai sun daidaita..
Ammar ma cikin tsananin kasa yadda da hakan ya kalli Maheer yace
"No,we cant do that,tayaya kake tinanin zamu dakatar da komai namu?
Katsesa Maheer yayi cikin damuwa da cewa
"Dole sai anyi hakan idan har munason cigaba da amsa sunanmu da riqe power dinmu idan ba haka zamuyi zubewanda zamu jima bamu dawoba duk da munada tarin dukiyar da bazai taba iya talautamuba amma karku manta arzikinmu bai taba girgiza ba sai yanzu,
Ya girgiza mana arziki da karfi sbd a cikin kaso biyar mun rasa kaso uku,
To idan bamu tsaya ba muka sauya taku zamu qara zubewan da kaso daya bazai riqemu a rayuwar da muka saba da ita hakama duniya da sauran business partners namu zasu fahimci mun rasa power da muke da ita wadda har abada bazamu bari a san da hakanba dan haka komai zai zama iya sirrin cikin familyn ne,babu wanda zaisan mun girgiza"
Dad dayakejin zuciyarsa na tafarfasa bude idanuwansa yayi ya kalli Maheer yace
"Ka tabbatarda ancigaba da tsananta bin sirrinsu an nemo mana wanda yayi backing komai,
inason a fasa kansa da bullet sbd indai yana duniyar zai ringa alfahari daya girgiza Zadeens hakama ya taba wainda baa tabawa dan haka duk tsanani inason a nemosa dan yayi danasanin wannan abinda yayi"
Gyada kai Maheer yayi Ammar ma gyada kan yayi yana tinanin tayaya zasu ajiye komai suyi me to??
Zaunawa sukai sunayin shiru sbd kosu Mimi da Jannah basusan meyake faruwaba iya mazan abin ya tsaya..
Waya Maheer ya fidda tareda saka kiran Saleem daya kusan zarewa shikuma akan Sabon business dinsu kamfanin motoci da a yanzu shine babban hope dinsu dazai dawo musu sa percents din da suka rasa gashi basu gama bayyanarwa da duniya kamfanin ba dan haka wanda yake wasa dasu bai saniba hakama AY LIMBA da suka fahimci zafin kansa da kuma saar da ake fada yanada ita dole dashi zasuyi business.
Saleem daya shigo da laptop dinsa da takardu a hannunsa ajiyewa yayi ya kalli dad din wanda zuciyarsa ke ciwo Ammar da idanuwansa sukai jajir
Maheer ya bude baki cikin rashin mafita bayan wannan yace
"Dad,LIMBA ne abinda muke buqata a business dinmu yanzu sbd sabon kamfanin nan shine zamu daga ya bamu abinda mikeso,
Muna buqatan aiki dashi gaba dayanmu a yanzu ba Saleem ba"
Dad din bayanan komai AZIZ AY LIMBA ya karba takardun yana karantawa tareda tarin nasarori da asalin dukiyar dayake da ita hakama ga connections na manyan mutanen da baima taba tunanin matashi kamarsa ba suna hulda dashi wanda a taqaice Abokin manya ne shi kansa ya wuce ace shine yake neman wani sedai a nemesa kaman su kenan,
Hanyoyin bullewa ya gano da Yawa ta hanyar AZIZ din dan haka ya ajiye takardun yana sauke ajiyar ya dago ya kalli Maheer yace
"No da kaina zan business dashi dan haka ina buqatan haduwa dashi,
Muna buqatansa a matsayin friend na zaadens,
Damu ya kamata yayi hulda fiyeda kowa dan haka kowa ya tabbbatarda hakan ta faru na samun kusancinsa damu"
Maheer jin wani irin sanyi yayi yana sauke ajiyar zuciya a bayyane sbd tabbas suna buqatan self made billionaire me zafin kai kamar AZIZ AY LIMBA sbd su samu saarsa,
Saleem kuwa dayake kaunar kasancewa da AZIZ LIMBA ba tin yanzu ba jin yayi zuciyarsa tayi sanyi farin ciki na cikesa sbd kaunarsa yake har ransa.
Ammar kuwa jin yayi zuciyarsa na shiga yanayin daya kasa gane farin ciki ne,tsoro ne,fargaba ne ko baqin cikin Zasu kusancesa da kansu batareda yazo garesu ba sbd power dinsu da matsayinsu hakama jin yayi tsananin kishinsa akan zamansa selfmade billionaire sabaninsu da tasowa sukai a cikinta ta iyayensu ce ta gado bawai sune suka tsayu suka samarwa kansu sunan kamarsa ba...
Saleem ne kawai me raayin kirkirawan kansa suna ya gina dukiyarsa da kansa dan yayi bugun gaba da shine ya gina kansa bawai iya alfahari da dukiyar familynsa ba dan hakanne ma yake shaawar AZIZ AY LIMBA wanda akace baida uba a maraya ya taso daga shi sai mahaifiyarsa da 'yarsa daya tak wadda babu wanda ya taba ganin mahaifiyarta dan haka babu wanda yasan rasuwa tai kokuwa rabuwa sukai haryau wannan sirrin shine babu wanda ya sani akansa.
Da wannan shawaran da suka tsayar suka samu sassauci da damar dawowa hayyacinsu suka fito meeting din da kullum sai sunyisa dan neman mafita.
Kowannensu na fitowa kai tsaye Bedroom dinsa ya nufa dan samun nutsuwar da suka rasa ta kwanakin.
Anny da hankalinta ya fara tashi ganin suna neman durqushewa jin an samu mafita daga bakin Maheer din samun kanta tayi da jin dadi da dawowa hayyacinta duk da tasan suna zubewa qasar zasu bari su koma Greece inda suka fito su dasa sabuwar rayuwar rufin asiri sbd girman kansu bazai bari su zauna anaba ana musu kallan sun rage karfin dasuke dashi kwata kwata.
********washe gari gaba daya familyn suna dining room suna breakfast harda daddy mahmoud dayake zaune a wheelchair dinsa sedai baya iya cin komai se abinci me ruwa duk da yafara samun sauki,
Jannah ce ta shigo dining room din a natse sanye da riga da wando daya lafe a cinyoyinta sai rigar Cardigan da qaramar scarf akanta.
Ammar ne tareda ita gefenta qamshinsa da nata ya cakude yana fita a tare yana bada wani kalar qamshin me dan dadi.
Mimi kallonsu tai tanajin ita dai batada nutsuwa idan ba aurensu akaiba duk da tasan yanzu ba lokacin maganar aurensu bane sbd lura kwanakin a kwai matsalar datake faruwa ta aiki duk da baa sanar mata ba ta fahimta kuma itama bata saka baki ba addua kawai tai musu.
Zaunawa sukai bayan sun gaida kowa suka fara breakfast din.
Wayar Maheer ce tai ringing yana dubawa yaga pa dinsa ne
Ajiye wayar yai batareda ya dauka ba saida ya gama breakfast dinsa ya dauki tissue ya goge bakinsa yana miqewa ya saka kiransa.
Cikin girmmawa deen pa din nasa yace
"Goodmorning Boss"
Amsawa yayi yana zaunawa a kan sofa yace
"Any news???
"AY LIMBA yana Nigeria gaba daya ya dawo tareda familynsa a cikin satin daya gabata"
Dan tashi daga jinginar da yayi maheer yayi yana cewa
"A ina??
"A abuja boss"
Wani numfashin farin ciki da samun kwanciyar hankali Maheer din ya sake yana cewa
"Kaje in person kai magana da Personal person nasa Muna neman gayyatarsa na welcoming nasa kafin maganar business gaba"
"Yes an gama boss"
Kashe wayarsa yayi bayan yace a nemo contact na LIMBA din a gurin SAYD.
Dad na zaunawa palon Maheer din ya sanar dashi LIMBA na Nigeria cikin samun nutsuwa.
Shi kansa dad zancen ya sake sakasa cikin kwanciyar hankali sbd da kansa yakeson kulla Kyakkyawar alaqa me karfin gaske da LIMBA sbd baya wasa da billionaires dan haka da kansa zai jagoranci neman kusanci da Limban sbd kada ma su kawo matsala ko daya su 'yayan nasa.
*********Sayd dayake jiran kiran Zaadens din tin ranar da suka dawo Nigeria se yau ya samu kiran daga garesu dan haka cikin rashin basu mahimmanci a natse ya gama sauraron bayanin Deen kafin ya basu damar contacting Limba din kai tsaye wanda Maheer ne ya kira AZIZ da kansa sedai bai daga ba sbd baimasan numbern ba sai kusan bayan kwana biyu daya sake kira kafin Ya daga cikeda iko da nutsuwa da izzansa data saka Maheer jin kishinsa me tsanani ya rufesa sedai kuma yana tsananin son kasancewansu dashi dan haka cikin tasa class din da wayewa tareda dukiya daya taso cikinta da hutu suka gaisa ya gabatar masa da kansa.
Wani irin yanayi me daci ne ya dan tasowa AZIZ din yanajin saukan muryan Maheer din kamar wani yankan rezan dayake yanka zuciyarsa sbd bai taba tinanin zai iya sauraronsu da kunnuwansa masu tsafta ba.
Bude kyawawan idanuwansa da ya dan rufe yana cigaba da sauraron Maheer din wanda ya nuna masa sakewa.
A natse cikin kwanciyar yake dan magana kafin ya amince da gayyatarsu na haduwa bayan yace zai duba proposal nasu da suka turawa sayd insha Allah zaizo da approval nasa na hada business din.
Sallama sukai Maheer na cikin farin ciki da samun cikar burinsu dan haka suka fara shirin tarbonsa a Zad mansion.
##MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
47
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC (kayan mata)
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa niβima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah π₯°ππ»
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1kπ₯ Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4200
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
π£οΈπ£οΈπ£οΈπ£οΈπ£οΈπ£οΈ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALAππ½ππ½ππ½πππ da 6k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata ππ½ππ½ππ½ππKazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadΔ±π800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Na Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 6k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
************
A bangaren LIMBAs komai yana tafiya a familyn daidai sbd falaq bata samu damuwa ko jin rashin dadin qasarba sbd bata taba zuwaba tinda aka tafi da ita gana Nigeria dan haka kamar wannan ne zuwanta na farko bayan data barta dan haka suke tinanin zata iya shiga damuwa da rigimar batason nan din amma kuma a nata bangaren Nigeria din ta zama best gurin da zatai rayuwa me dadi sbd daddynta zai kasance dasu ba yawan tafiye tafiye dan haka hankalinta yake kwance sbd tana tareda familynta duka hakama yanayin duniyar dake cikin gidan yasakata batajin wani banbanci da qasar da suka baro dan haka takejin dadinta kawai hankalinta kwance.
Kwanciyar hankalinta da walwalwanta ya saka gabaki daya gidan suma suke cikin walwala da kwanciyar hankali da farin cikin komai yana tafiya daidai gashi daga mama har Fiddausi suna cikin farin cikin dawowan dan gashi sam bai fadawa mama abinda akaiwa Ummitah ba dan kada ya sakata quncinda baida magani dan haka suke cikin walwalansu gidan.
Baba alhassan ma ya taho yana abujan saiya huta yanda ya kamata zai koma gida dan haka sosai gidan ya zama cikin walwala.
Falaq sosai suke fita yawo da Latif da Fiddausi sbd taga gari da yawon shopping.
Ya karba gayyatarsu ne sbd bazai bari su sukawo masa ziyarar ba dan bayason abinda zai kawosu cikin gidansa da iyalinsa dan haka zai dira a nasu empire din da kansa.
****A cikin qanqanin lokaci ya kasance suna yawan waya dashi harma dashi Dzad din dakansa dan haka ya fara sakar musu hanyoyin businesses da suke buqata sbd su sake jikinsu sosai dashi.
A ranar daya shirya ziyartar familyn da nasa familyn sbd yanda suke son haduwar familyn nasu...
Cikin nutsuwa dukkani familynsa suka shirya suka fito banda Baba alhassan da hutu kawai akeson yayi.
Lafiyayyar RR ce da beymach Baqaqe suna daukan ido suka kawosu mansion din Zaadens da ake jiransu cikin Kyakkyawan tarba wanda suma lafiyayyun motocine a jere harabar gidan dan dukkanin wanda yake gidan yana motan datake amsa sunanta mota shi dad dinma kusan uku ne dashi Maheer ma biyu dashi sauran daddaya ne sbd basason mota da yawa.
Securities din gidan da sauri suka budewa motocinsu gate suka sako kai a cikin gidan sayd na kallan Zaadins din dake fitowa daya bayan daya cikin iko da suke murzawa dan tarban AZIZ LIMBA da basusan balai da masifar rayuwarsu ce suka fito tarba da hannu bibbiyu ba.
AZIZ kuwa idanuwansa ya tsayar akan Dzad dayake fitowa sanyeda kayan alfarma cikin dattako da nutsuwa ta ilimi daya ratsashi da dukiya amma zuciya duk tsatsa sedai yayi masa alkawarin kankare tsatsar zuciyarsa da abinda yafi tsatsan muni.
Parking aka latif ya fito daga mazaunin driver yana budewa mama mota,
Sayd kuwa AZIZ ya budewa sayar motar.
Fitowa qafafunsa ya ziro a natse yana fitowa sanyeda navy blue wata tsadaddiyar cashmere data fidda tsananin haske da kyan fatarsa da hutu ne kawai a bayyane koina na aji.
Gabaki daya sun Maheer zuba masa idanuwansu sikai aura dinsa na cike idanuwansu da kuma asalin nutsuwa da steez dinsa.
Hannu ya miqa a natse ya budewa Falaq mota wadda a duniya ita kadaice yakewa hakan.
Kallan wanda aka budewa mota sukai suna jiran ganin ko matarsa ce suka ga Yarinya qarama ce wadda kai tsaye suka fahimci itace 'yar da babu abinda yakaita mahimmanci kaf rayuwarsa.
Fuskanta dauke yake da murmushi koda ta fito sanye da doguwar riga lilac da mini hijab dinta.
Hannunsa ta kama cmda sauri cikin nata tana murnan sunzo baqon guri sbd tanason shiga mutane sosai sbd ta taso a killace.
Mama da Fiddausi ma cikin walwala suke ganin daga karshe ya yadda zasuyi muamala da mutane sosai tinda gasu a cikin wani familyn sun kawo ziyara wanda sai wanda ya yadda yayi kusanci dasu yake hakan.
Cikeda sakewa da farin ciki tareda bayyanarda shaquwa Maheer ya miqa masa hannu yana cewa
"Welcome to zaadens LIMBA"
Dagowa yayi yana miqa masa hannunsa tareda sakin wani lafiyayyan murmushin daya saka Zuciyar Jannah data sako kai dauke wuta cak tana kallansa idanuwanta na cikowa da hawayen da batasan na meneneba batareda ta qara taku ko daya ba...
Anny data sako kai tareda jannah din itama wutar ta dauke tana zubawa masa dukkanin idanuwanta zuciyarta na ambatar sunan Allah.
Dad cikin sakewa da bayyanarda farin cikin samunsa a gidansu yau din ya miqa masa hannu shika ya miqa masa yana cewa
"The pleasure is mine"
Ammar ma cikin danne abinda yakeji ya sake fuska cikin nuna farin cikinnsa yai masa welcome.
Saleem kuwa da farin cikin ganin AZIZ din yake tin daga zuciyarsa murnan haduwansu ya bayyana masa suna qarasawa ciki.
Mimi datake fitowa daga dining room da aka gama hadawa da farin ciki ta tarbi su mama tana musu sannu da zuwa.
Itama maman cikin sakin fuska take amsawa.
Anny juyowa tayi ta kalli jannah data kasa motsawa jikinta a sanyaye musamman daya rabata ya wuce ciki batareda ya lura da ita dinba a karo na biyi kenan yana mata hakan yabarta da kamshinsa daya saka kanta cakewa tana kasa dauke idanuwanta akansa.
Anny zuba mata idanuwanta tayi tana nazartanta batareda tace komaiba....
Me yake shirin faruwa?
Me jannah ke tinani?
Cabdijam" tafada a fili tana shiga lissafin da idan har hakanne to wlh saita tabbatarda hakan ya faru sbd a yanzu da AZIZ LIMBA yake gabansu to iya business dashi ba shine kadai zai fiddasu ba suna buqatan hada family dashi ta hakan ne zasu shiga dukiyarsa su juya a cikinta su samesa yanda sukeso,
Dan Maheer na buqatan sanin hakan indai neman mafita suke kuma a saukake Lamarin zaizo indai Jannah ta kamu da tsananin son AZIZ din dan haka tayi Alqawarin sakawa jannah din tsananin son AZIZ LIMBA batareda saninta ba sbd kamuwa da sonsa kawai zaisaka familyn su hana aurenta da Ammar su aura mata wanda takeso...
Wani Murmushi ta sake tana kallan jannah din cikin tausayi dan babu alamar Akwai mace ma rayuwar LIMBA bare soyayya...
Taba jannah din tayi ahankali tana cewa
"Cewa Jan muje ko"
Ciki suka nufo Anny din na gaba Jannah na bayanta a natse.
Dad ne dasuke zaune suna magana kowa a cikin wayewa da arziki daya gama hudasu ya kalli jannah yana miqa mata hannu yacewa AZIZ
"Meet the princess of d family JANNAH ZAD my daughter"
Dago Fararen idanuwansa yayi an natse ya saukar akanta daidai itama ta dago tana kallansa bayan ta kama hannun dad dinta ta zauna kusa dashi.
Fuskanta yayiwa kallan Minti daya yanajin wata wuta me zafin gaske tana cin zuciyarsa,
Kallanta kadai qona rahamar idanuwansa yakeyi...
Ahankali cikin nutsuwa ya gangaro da idanuwansa setin zuciyarta dake bugawa ahankali tana dauke idanuwanta daga kallansa sbd yanda idanuwansa ke karya kuzarinta zazzabi
Book Chapters
Chapter 23
Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
β¦500Monthly Support Β· Most Popular30 days of premium access
β¦1,500