You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
airport Alh Saad ya kalli Sayyid wanda kai tsaye kallo daya zakai masa kasan ya sauya daga asalin Sayyid dinsa na baya idan ka sansa.
Har a cikin jirgi bayan sun zauna babu walwala a tattareda Sayyid din dan haka bai takurasa ba ya kyalesa dan yasan zuciyarce ba dadi ko kadan.
******
Lafiyayyan toilet ne dayake da girma sosai komai a tsare,
Qamshi ne me sanyin dadi da nutsuwa yake tashi a cikinsa hakama da dan hayaqin zafin ruwan da ake wanka dasu dayake dan gauraya toilet din yana saka koina a toilet din daukan dumi ahankali.
Wanka takeyi a natse qamshin shower gel dinta me kyau da tsada yana sake tashi harta gama wankan ta kashe shower din tareda miqa hann ta janyo towel ta dauro a jikinta ta fito cikin Lafiyayyar jacuzzi din ta nufo gaban mirror daya kusan cike rabin bangon toilet din ta tsaya cak ta zubawa kanta idanuwanta da suka fara sauyawa ahankali.
Hannunta na dama ta dago ahankali ta dora akan kirjinta seti da zuciyarta dake bugawa ahankali cikin cikakkiyar lafiya..
Tabon dinkin gurin ta shafa ahankali tareda lumshe fararen kyawawan idanuwanta tana sauke numfashi ahankali me dumi...
Tin daga lokacinda ta wayi gari ta samu kanta a sabuwar rayuwa daukeda sabuwar zuciyar datake bugawa a kirjinta tasan duniyarta ta sauya ta dawo sabuwa a daidai lokacinda ta cire rai da rayuwa gabaki dayanta,
Allah ya bata damar cigaba da rayuwa a lokacinda take saka ran ta farko ta samu kanta a duniyar barzahu,
Duk wanda zuciyarsa take bugawa a kirjinta tana masa fatar samun rahamar ubangiji dashi da danginsa a duk inda suke,
Harta bar duniya bazata dena yi masa addua ba sbd sadaukarwansa gareta.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana lumshe idanuwanta tana sake jin bugun zuciyar wadda take tata ayanzu yana ratsata cikeda shauqi da samun nutsuwa da yanayin da bata saniba a baya na bugawar Lafiyayyar zuciya a kirjinta.
Ayau kusan wata hudu da kwanaki kenan da aikinta amma haryanzu ta kasa sabawa da sabuwar rayuwar data samun koyaushe jinta takeyi kamar sabuwar mutum sedai kauna da tsananin son datakewa yan uwanta familynta babu abinda ya sauya saima qaruwa da yayi sbd jajirwansu gareta.
Kaman yanda samun lafiyarta ya sauya rayuwarsu gaba daya a qanqanin lokaci sbd sabon farin ciki da jin dadine tareda sabuwar rayuwa ta dawo musu sabuwa dan haka komai nasu ya dawo tamkar baya kusan ma fiye dan farin ciki da kwanciyar hankalin dasuke dashi yanzu na tafiyar da komai yafi na bayan.
Ta jima a tsaye kafin ta juya ta fito toilet din.
Qamshin dayake tashi a bedroom din nata ne ya shiga hancinta ta dan Lumshe ido tana jinsa yana ratsata sbd komai a yanzu jinsa take kamar sabo gareta.
Gaban mirror ta nufa bayan ta zaro wani towel din tana goge jikinta a hankali kamar batason taba soft fatarta sosai.
Da kanta ayau ta shirya kanta sabanin tinda suka gama jinya a asibiti suka dawo gida Mimi ke tayata shiri sbd batason tayi aiki da jikinta ta gaji sbd sun saba a lokacin ciwonta abu daya takeyi zuwa biyu ta gaji sosai ba kuzari.
Body milk me kyau da qamshi ta shafa tareda Turare mai sanyin qamshi ta miqe ta nufi closet nata ta saka undies kafin ta saka oversize skirt and shirt na Liliana ta saka hula me laushi da rashin nauyi a kanta ta fito da slippers a kafarta sbd yunwa takeji abinci take buqata.
Anty Anny ce ta nufo palon itama sanye da shaking doguwar riga mara adon komai sai kudi tana qamshi fuskanta fresh dan itama gaba daya yinin ranar bata fito daga bedroom ma bare palonsu harta fito zuwa nan sai yanzu data fito neman abincin da zata dan duk da a familyn kowa da nasa bangaren amma a hade suke guri daya babu wani rarrabewa sosai dan kusan duka a guri daya suke kowa baifi kayi tafiyar corridor ba zuwa palo da bedrooms wani hakama duk yanda kowa yake bangarensa a tare ake cin abinci dining room dinsu daya ne hakama chiefs dinsu da masu aikin.
Rayuwar hutu kawai sukeyi mazan gidan ne suke fita aiki suma bawai sammakoba tinda sune masu companies dinsu amma matan kuwa da saleem ma sai lokacinda suka ga dama suke fitowa idanma ba abinci zasuci ba saika wuni a gidan bakaga ko dayansuba sai idan dare yayi ake taruwa babban palon ayita fira da yar hayaniya cikin walwala.
Anny na ganin Jannah ta zuba mata idanuwanta tana kallan yanda take sake warwarewa tana komawa lafiyayyar jannah dinta wadda ita bata saniba a baya,
Wani irin sirrin kyau da kwarjini ne da itama duk da bata gama zama cikakkiyar budurwar data amsa sunanta budurwanba amma haka kawai wani lokacin sai take mamakin saa irinta jannah din kowa sonta yake,
Babu abinda ta nema ta rasa,
Kowa zai iya komai dan bata abinda takeso,
A irin wannan gatan da Jannah din take ciki me zata nema a duniyar nan ta rasa?
Duk yanda familyn suke ganin babu abinda bazasu samar mata indai har tanaso akwai abinda yafi karfinsu shine ikon Allah,
Ita kanta zataso Allah ya kawo abinda Jannah zataso fiyeda komai ko buqata fiyema da zuciyar da aka dauki rayuka da dama akanta amma kaf familyn babu wanda zai bata kuma dukiyarsu bazata taba iya siya musu ba,
Zataso taga wannan ranar sedai batajin tana zuwa dan raine kadai bazasu iya siya mata amma ko rai din da zaace musu ana iya sakawa wani ran wani to tabbas zasu iya sedai Allah bai bada damar hakanba.
Isowan Jannah gabanta ya sakata sake murmushi tana sake kallan Jannah da yanayi na tinani kala kala akan fatan zuwan ranar da jannah zata dandana rashin ba komai ake nema a samu ba.
Da murmushi a fuskanta da kulawa tace
"Hey Jan sai yanzu kike fitowa?
Yaya jikinki?
Ya kikeji yanzu?
Karki manta duk abinda kikaji ba daidaiba ki sanar"
Fararen idanuwanta ta kalli Anny din dasu kafin ta saukar da murmushin kwanciyar hankali a fuskanta tana cewa
"Anty Anny karki damu i dont feel any uncomfortable yanayi,
Am all good"
Gaba tayi anty anny din na bin bayanta tana cewa
"Masha Allah"
Mimi ce itama ta fito a lokacin tana waya cikin walwala da annushuwa tabi bayansu dukansu dining room din suka nufa suka zauna daman dining din baa dauki mintina da yawa da gama shiryasa ba sbd ansan lokacin cin abincinsu na rana yayi kowane time zasu iya fitowa.
Suna zama qamshin Ammar ya doso dakin me sanyi da tsadar gaske tareda rashin hawa kai ko kadan.
Jannah ce taji wani sanyi yana ratsa xuciyarta tareda qamshin nasa ta dago idanuwanta tana kallan kofar daidai da shigowansa sanye cikin black thick riga da wando masu laushi fuskansa fresh da alama bai fita koina ba yau din shima yana gida hutu yake sosai haryanxu.
Kyakkyawan fuskansa jannah take kalla tana jin bazaa samu namijin da zai kai Ammar Zad kyau da kwarjini tareda haiba ba a idanuwanta har abada ba,
Ammar Zad shine mafi kyawun namiji data sani wanda shi kadai take zubawa ido bata gajiya da kalla.
Kallan datake masa ya saka Anny sakin murmushi tana kallansa shima kallan Jannah din yayi yana sake murmushi yana kujera ya zauna yana cewa
"Me Jan Zad take kalla??
Mimi ta kalla kafin ta kalli Anty Anny ta rage muryanta tace
"The one and only Ya Ammar Zad"
Mimi na jinsu farin ciki ya sake cikata tai sallama da wayarta ta kashe ta ajiye tana kallan Ammar din daya zauna kusa da ita yana daukan cup din fresh juice da akai na gida ya kai bakinsa yana cewa
"Mimi barka da rana"
Kafin ta amsa Jannah ma tace
"Sannu da fitowa Mimi"
Anny ma gaidata tai ta hada duka gaisuwar tasu tai musu amsawa daya tana cewa aci abincin tukuna wani zancen.
##MAMUH
#JANNAH ZAD
#AZIZ AY LIMBA
#AMMAR ZAD
#BESTLOVE STORY
#CRAZYLOVE
#BILLIONAIRES WAR
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899
[27/12/2024, 3:20 pm] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
28
*_LADIES COLLECTION AND MORE_*
08169307477
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S COLLECTION AND MORE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
08169307477
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
***********
Da asuba jirginsu ya sauka Sayyid yana a sanyaye baida wani kuzari ko yin abinda ya wuce bin bayan Alh saad sawu kan sawu sbd kansa dayaji yana juyawa samun kansa a baqon guri inda bai taba tinanin zuwaba ko samun kansa ga jajayen fata tako ina suna wuce suna sake saka kansa juyawa amma ya daure babu abinda yake buqata irin ganin ABDULAZIZ LIMBA.
Mota suka hau wadda kai tsaye takaisu train station suka siya ticket din zuwa Milan wanda acan ABDULAZIZ din yake.
A train ma wata sabuwar duniyar Sayyid yake kalla wadda tale sake juyar da kansa sedai ko dagowa bayayi kansa na qasa Allah yasa kayan sanyi ne masu kyau da kauri a jikinsu dagashi har Alh saad dan haka rashin wayewansa da gurin ya boyu shi kuwa Alh Saad dayake gogagge ne a yawon qasashe sam babu abinda ya damesa sajewa ma yayi dasu banda banbancin fatar amma turancinsa dayakeyi hankali kwance cikin qwarewa yana waya da wanda zai kaisa har gidan ABDULAZIZ
Tafiya sukai me dan tsayin data saka Alh saad jin daya sani flight suka sake bi zuwa milan din..
Suna sauka daga train Station daga nan kai tsaye motace ta daukesu zuwa Address din Fash wanda yake abokin karatun ABDULAZIZ tin abaya amma yanzu basa tare amma yasan sabon gurin dayake zama yanzu sbd dukkaninsu sun zama busy kowa ya samu success din dayake nema.
Koda suka isa gidansa cikin sakewa ya tarbesu tareda riqesu sukai sallolin dasuke kansu sukai breakfast wanda daqyar Sayyid ya tura abincin a cikinsa sbd ba cimarsa bace hakama zuciyarsa kwata kwata a sanyaye take ba dadi ko kadan nauyi yakeji a kirjinsa.
Wayar ABDULAZIZ din shima Fash ya ringa kira ko zaa dace amma still bata shiga ba kuma a lokacinda Alh saad ya kirasa baya qasar shima bai dade da dawowa ba dan haka bai samu zuwa ya dubo lfy ba kuma yayi masa gaisuwar babban rashin da yayi wanda duk wanda yasan ABDULAZIZ sanin daya wuce awanni to tabbas zaisan Ummitah itace rayuwarsa,jarumtarsa kuma karfin dayake riqe dashi a duk gwagwarmayar rayuwarsa hakama duk abinda yakeyi a rayuwarsa sbd cigabanta da ingatata yakeyi.
Saida suka nutsu sosai kafin suka fito a motar fash din zuwa gidan ABDULAZIZ.
Tin a mota sukai tsit babu me magana sai fash din dayake dan kokarin ragewa yanayin nasu damuwa da cewa
"Insha Allah lafia kalau sbd LIMBA yana hakan so da dama idan yana son kadaicewa baya son damuwa"
"Ummnh" kadai Alh Saad yace yana kallan hanya sbd baida abin fada.
Sayyid kuwa shiru har lokacin bai iya cewa komaiba hakama ko kallan gari baida Nutsuwar yi.
Shiru Fash yayi ganin yanayin baya buqatan karfafawa shiru kawai kowa yake buqata.
Tafiyar mintina kusan 40 sukai kafin suka isa dogon building din da gidan ABDULAZIZ yake ciki.
Parking fash yayi yana gaisawa da securities din wajen da suka bude musu hanyar shigowa fededen harabar gurin.
Fitowa sukai dukkaninsu fash da Alh saad ne a gaba suna magana
Sayyid dai har lokacin bai iya dago kansa sosai ba bayansu kawai yakebi a natse babu kuzari.
Lift suka shiga zuwa saman Fash na daga wayarsa da ake kiransa.
Suna isa floor din dayake suka fito fash yana kashe wayarsa suka tsaya kofa tareda sauke ajiyar zuciya ya miqa hannunsa ya danna Door bell dake qara mara damuwa da karfi.
Kofar suka zubawa idanuwa dukkaninsu suna jiran fitowansa.
Sake dannawa Fash yayi yana gyara tsayuwarsa.
Shiru babu motsin alamar bude kofar,
Sake dannawa Fash yaci gaba dayi yana shiga mamaki.
Mintina suka dauka a gurin sunata bugawa babu alamar zaa bude din babu ma alamar akwai mutum a ciki.
Saukowa qasa sukai suka nufi gurin receptionist din building din dake qasan
Fash ne ya kalleta yana mata sannu kafin ya sanar da ita gurin wanda suka taho.
Kallansu tayi dukkaninsu da mamaki kafin ta tsayar da kallanta kan fash da shine a gabanta tace
"His family????
"Yes" yafada yana nuna su Alh saad din wanda shima Alh saad din matsowa yayi yana amsa gaisuwarta kafin tace
"Baya nan for morethan 2 month yana asibiti likitansa yazo ya tafi dashi,
Mutuwa yakeyi ciwo yake sosai.......
Kallanta Alh saad yayi da sauri yana juyowa ya kalli Sayyid wanda bayajin abinda suke fada yana dan nesa kadan hakama turancin ba duka ya iyaba.
Fash cikin Yanke zancen yace wane asibiti and the name of the doctor.
Basu tayi cikin sauri sbd basuda tabbacin ko zuwa yanzu LIMBA din ya rasu sbd a yanda aka bar nan dashi batajin ko kwana daya zai qara a duniyar.
*****A ranar kunnuwansa basu gama sauraron maganar Alh Saad ba yaji tsit bayajin komai jinsa na daukewa ahankali,
Ganinsa ma Fara daukewa yayi qafafunsa ma mutuwa suka fara yi suna gaza daukansa hannuwansa da suka dauki rawa suma mutuwa suka farayi harsuna kashe wayar wadda ta zame daga hannunsa ahankali shida wayar suna zubewa agurin paralyse na kamasa a take.
Buguwa kansa yayi da centetable din dayake tsakiyar palon take jini ya feso daga gefen fuskansa datai mugun buguwar idanuwansa da suka mummunan sauyawa a take na kafe akan wayarsa dake gaban fuskansa batareda ya kafta ba.
Zuciyarsa kokarin dena bugawa takeyi sbd mummunan bugun datai wanda ya sakar masa paralys na take,
Wani irin Radadin da baya misaltuwa ne yake ratsa zuciyarsa dake neman bugawa ta dena aiki gaba jininsa na gangarowa daga gefen goshinsa yana shiga har cikin idanuwansa da suka kafe akan waya bai iya motsa ko dan yatsantsa sbd babu abinda yake aiki ajikinsa bayan zuciyarsa datake matsanancin ciwo da radadinsa yake juyar masa da kai kafin ahankali idanuwansa suka rufe ruf ba alamar rai a jikinsa.
A haka ya wuni a gurin kwance babu alamar rai a jikinsa harya kwana a gurin kwance babu taimakon kowa sbd babu wanda yake shigowa building din saida kwakwaran sanin gurin wa akazo hakama ko securities sun san shi kwata kwata baya wani muaamala da mutane hakama baya wani yawo sosai,
A gurin kwance ya farfado sbd sanyin asuba dayake kadowa a hankali daga balcony dinsa dayake bude yana saukar masa..
Jajayen idanuwansa da ganinsu ya dauke ko kadan ya dena ganin komai ya bude suna wani irin radadin da duk azabarsu bayajin komai sbd har Allah ya dauki ransa dayake fata a yanxu bazai taba jin radadin dayake a yanzu yana yanka duk wani tsokar datake kirji da zuciyarsaba azabar daukan raine kadai da baisaniba yake jin zatafi abinda yakeji yana tarwatse zuciyarsa da kwakwalwansa datake dena aiki,
A yanda yaken babu inda yake motsawa a jikinsa har gari yafara haske ya sake somewa a gurin sbd azaba da radadin dayake kirjinsa yayi masa tsananin da baya motsawa amma azabar tayi qarfin datake sumar dashi ya sake ficewa hayyacinsa.
Mai aikinsu shida wanda yake next floor yazo aikinsa aikinsa guraren karfe 9 na safe kai tsaye ya bude kofar sbd yasan code na budewan.
Iskan dayake kadowa daga balcony ne yana ratso palon me tsananin sanyin gaske ya saka Eden nufar hanyar balcony din bayan ya tafi extra room din dayake kaman nasa anan yake ajiye jakarsa da laptop dinsa ta karatu ko kallo ko wani abin idan yazo da ita.
Sauke jakarsa yayi daga bayansa ya ajiye tareda ledar fresh fruits din dayazo dasu me girma wanda Tin jiyan LIMBA ya basa kudin ya siyo idan zai taho yau.
Da ledar ya fito daga dakin ya nufi kitchen ya ajiye ledar ya nufo balcony din dan rufewa sbd sanyin yayi yawa sosai yana mamakin ya akai Mr LIMBA ya bar balcony din a bude sbd bayason sanyi sosai.
Taku biyu yayi idanuwansa suka sauka akan LIMBA din dayake kwance a kife cikin mummunan yanayi ga jini a fuskansa duk ya bushe ba kyan gani babu alamar rai a jikinsa.
Da gudun gaske ya nufesa cikin matsanancin tashin hankali da tsoro yana kiran sunansa.
Birkitosa yayi da karfin gaske sbd nauyin da yay sosai alamar da gasken ba rai a tareda shi.
Ihun gaske ya sake yana sakinsa ya miqe da sauri koina jikinsa na rawar tsoro da firgita,
Kararrawan neman taimakon gaggawa zuwa ga securities da reception na building din ya danna da hannuwansa biyu yana sake daddanawa ba kakkautawa a rikice.
Ganin kaman hakan bazaiyiba sai kawai ya rarumo wayar Limban datake gefe a yashe ta mutu ya nufi gurin caji da sauri yana kokarin sakawa manager da securities suka iso cikin sauri suna buga kofar ya bude da sauri yana jifa da wayar suka shigo da gaggawa suna ganinsa a hakan hankali tashe aka kira ambulance tareda likitansa dayake kamar Abokinsa
Cikin gaggawa Dr Nico yace ayo asibiti dashi.
A cikin nurses da suka taho da ambulance daukansa tin anan aka gane he is paralysed dan haka tin anan suka fara bawa rauninsa taimakon gaggawa aka kwashesa zuwa asibitin.
A asibiti ana isa cikin gaggawa akai cikin emergency dashi sbd zuciyarsa dake bugawa ahankali kaman zata tsaya hakama numfashinsa dan haka hankalin dr Nico ya tashi dan suna buqatan gaggawar dawo da bugun zuciyarsa daidai idan ba hakan ba zaa iya rasashi.
Kamar kar afara basa taimako ya rikice gaba daya kokarin rasashi akeyi dan haka hankalin likitocin gaba daya ya tashi aka saka masa oxygen ana kokarin hana zuciyarsa dena bugawa,
Kokari sukeyi amma kwakwalwansa failing takeyi wanda kwata kwata baa son hakan...
Duk yanda suka ringa kokarinsu babu abinda yake karban kokarin da sukeyi a jikinsa,
Ba yanda suka iya dole aka yaga rigar jikinsa
Dr Nico yace nurses su kawo Defibrillator
Da gaggawa aka kawo tareda sauran abubuwan Dr Nico ya bawa dayar dr din shi ya fara hadawa da sauri
Cikin sauri dr yace su kunna yafara kirga da sauri ya danna a kirjinsa ya basa AED a kirjinsa wanda ya sakasa yowan sama yana komawa ya zube babu alamar rai a tareda shi..
Da sauri ya sake cewa su basa wuta ya sake manna masa yana cewa
"Com on com on com on LIMBA pls pls pls......
Cikin sauri nurse tace "hes Getting it Doctor"
Cikeda fatan ya tashi ya hada na ukun yana danna masa sbd daga shi idan bai tashiba shikenan.
Danna masa yayi yana daukewa Nurse tace "dr the heart.....
Bata qarasa ba ya juyo da sauri yana cewa a basa sauran alluran da zai masa da gaggawa.
Dr Nico ne yai masa alluran sbd bugun zuciyarsa ya dan samu karfi.
Aden dayake wajen Emergency din yana kaida kawo cikin fargaba da rikicewa ya zauna ya tashi ya rasa ya zaiyi sbd tsananin Tausayin yanda A lokaci daya LIMBA ya koma kalar tausayi.
Dr Nico damuwa ce sosai a tattare dashi sbd Bugun zuciyarsa ya dawo daidai sedai babu inda nasa yake motsi sun bincika sun tabbatarda ya samu paralys din da shock ne me girman gaske ya haifar masa dashi wanda zuciyarsa take kasa dauka.
##MAMUH
#BESTLOVE
#BROTHERS LOVE
#RESTINPEACE UMMITAH LIMBA
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
29
*_LADIES COLLECTION AND MORE_*
08169307477
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S COLLECTION AND MORE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
08169307477
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
***********
Duk yanda Dr Nico ya dage sosai cikin tsananin tausayawa yana neman lafiyar LIMBA sam babu cigaba sbd baya karban treatment da ake basa sbd Zuciyarsa data riqe da abinda yake cikinta sai sauki baya samuwa,
A kwance yake ba motsi ba magana ba kuka ba kowane irin reaction da ake samu daga garesa dan haka jikin nasa yake sake mutuwa,
Manyan likitocin da sukeda su asibitin Dr Nico ya sako a case din ABDULAZIZ suka duqufa amma sam sbd bayason ya tashi duniyar yakeson bari shima sai babu sauki a zuciyarsa ko sassaucin tsananin quncin dayake cikinta sai anata magani amma ba sauki.
Aden ne yake kulawa dashi sbd ABDULAZIZ yayi masa abinda baitaba samu daga kowa ba,
Shine ya dauki nauyin karatunsa dana kanwarsa sbd duk inda yaga yaya yana son kanwarsa jin yake yana kauna da Tausayinsu dan haka babu abinda bazai iya yiwa ABDULAZIZ LIMBA ba dan haka yake jinyarsa.
****lokaci yafara tafiya babu wani sauyi daga lafiyarsa,
Wata rama yakeyi sosai tana cinyesa daga kwance tana busar da fatarsa,
Ya tara suma da gashin fuskan har lokacin babu abinda yake motsi a jikinsa,
Asalin qunci da radadin da babu magani ne yake cin zuciya da ruhinsa ko idanuwansa bai cika budewa a rufe suke kusan koyaushe sbd basuda kyan gani suma sun kode sun jeme radadi da qunci kawai kake hangowa a cikinsu tareda cire rai daga duniya da abinda duka yake cikinta.
Aden ne ke dawainiya dashi komai shine yake masa cikin kulawa da fatan samun lafiyansa gashi duk yanda zasuyi contacting familynsa an rasa sbd wayarsa ya rasa inda ya yarda ita an nema an rasa dan haka suke dawainiya dashi shida dr nico wanda yayi iya kokarinsa akan ABDULAZIZ ya sassautawa zuciyarsa dan saiya sassautawa kansa zasu samu lafiyar da ake nema masa tafara samuwa amma hakan baya samuwa dan haka ya hakura yana cigaba da kulawa dashi sedai ahakan ya sani ABDULAZIZ bazai dade a duniyarba zai iya samun bugawan zuciya daga kwancen.
***Aden ya sadaukar da rayuwarsa a watannin akan ABDULAZIZ din wanda suka hakura suka cire rai daga tashinsa sbd ya koma ba kyan gani
Ahankali ahankali yake rasa sauran ji da ganin daya rage masa....
Kuka sosai Aden yakeyi a lokaci da dama idan ya kalli ABDULAZIZ din idan ya tina asalin kamanninsa da haibarsa tareda wani irin aji da kwarjininsa tareda tsarin rayuwarsa datake cike da Class da burgewa amma ayau gashi a kwance komai sai anmasa.
Ahakan ya dauki watanni koyaushe suna jiran ji daga familynsa tinda su sun kasa samunsu.
*************
Motar fash ce tayi parking a asibitin cikin damuwa da shakkar halinda ABDULAZIZ din yake ciki suka qarasa reception suka fadawa nurse din dasuka samu agurin cewa Dr Nicolas sukeson gani.
Kallansu tayi kafin tace dr Nicolas din ya shiga tiyata sedai su jira.
Kallanta Alh saad yayi yana cewa "akwai patient me suna ABDULAZIZ LIMBA mune familynsa"
Kallansa tayi kafin ta kalli Fash da shima itama yake kalla yana jiran amsarta.
Dawo da kallanta tayi kan Alh Saad tana mamakin lokacinda suka dauka basu taho garesa ba duk mummunan halin dayake ciki baida jininsa a kusa.
Numfashi me sanyi ta sauke tana cewa
"AZIZ AY LIMBA?????
yes" suka ce mata dukkaninsu cikin sauri.
Kallan nurse din kusa da ita tayi ta fada mata familyn Patient din dr Nicolas ne LIMBA.
Itama nurse din kallansu tayi d sauri tana ajiye Wayar datake amsawa da mamaki tace amma basusan halinda yake ciki ba ko?
Yes sukace suna cewa ganinsu kawai suke tsananin so a yanzu.
Room number aka fada musu bayan an duba id
Book Chapters
Chapter 14
Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500