gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Furar Danko Part2 Complete Hausa Novel by Billyn Abdul Chapter 8 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yana ganin bayan ya tsigesa mataki na biyu da zaibi a kansa shine bin shawarar amaryarsa akan haɗashi aure da ƙanwarta, dan ya gamsu da bayanin datai masa ya kuma ɗauki shawararta. Sannan ita kanta Dada lokacin gama nata aikin yayi.
      Koda ya koma gidan sai bai cewa Dada komai ba koda ta tambayesa ya batun zuwa asibiti. Sai da ta ƙara maimaita masane ya ce ta saurareshi yana nazari ne. Badan Dada taso ba dole tai shiru ganin ya haɗe fuska. Ummita dake laɓe tana jinsu, sai dai bata so jin Alh. Sulaiman yay shiru ba. A lokacin da duk wannan cakwakiya ke faruwa Smart na can cikin farin cikin samun nasarar cin ƙwallon da sukai tsakaninsu da abokan hamayyarsu ƴan Model Unitet a wannan ranar......

Bayan kwanaki biyu Alh. Sulaiman ya kammala yanke hukunci akan zancen Usman Nurse, sai dai bai nemesa ba sai da ya saka akai masa bincike a kansa tsaf. Inda aka kawo masa bayanai akan tabbatar da cewar karatu ne ya kawo mahaifinsa ƙasar Canada, amma asalinsu ƴan Nigeria ne. Anan Usman ya girma dan yana da shekara kusan goma iyayen nasa suka dawo Canada, sai dai fa yana yawan zuwa ƙasar haihuwar tasa. Usman dai a zahirance baya jin magana sam, dan duk wani ɗani'u na turawan nan yana zubasu musamman neman mata, kuma kamar yanda yake a turai hakan ba komai ba suma iyayensa basu ɗauke sa komai ba. Bai taɓa aure ba amma yanada ilimi mai dan babban Nurse ne shi ɗin. Wannan bayanai sun ƙawatar da Alh. Sulaiman, dan ya nazarcesu tsaf da fahimtar su a yanda makauniyar zuciyarsa ta tabbatar masa. Abinda bai sani ba Usman yarone mai matsanancin kishin ƙasarsa da ma yankinsa na Africa har ma da addininsa duk da waɗan nan rashin jin nashi. Wannan aƙidar tasa tasa ko kullum yake cikin yawo tsakanin Nigeria Da Canada kamar wani ɗan sama jannati. Dan ko aikin ma anan da ƙyar mahaifiyarsa ta samu ya yarda yakeyi, amma duk da haka sai da yaje ainahin ƙauyensu ya buɗe wani ƙwarya-ƙwaryan asibiti ya zuba likitoci da ke aiki a cikin kuɗi ƙalilan wa marasa lafiya. Koda Alh. Sulaiman ya gama tattare abinda yake buƙata sai yay ma Dada wayo akan ta koma wajen Baba, ciki Lulu kuwa su barshi ta haifi abinta kawai tunda dai Dr Olivia ta tabbatar musu akwai matsala. Ba haka Dada taso ba, sai dai bata iyayima ɗan nata musu, ganin kuma ya dawo da passport ɗin Lulun da Ummita ya basu ya sakata jin kwanciyar hankali, dan haka badan taso ba ta shirya ta koma wajen mijinta da al'amarin nata ya sashi fara tsarguwa shima. Sai dai baice mata komai ba tunda ta ce masa wasu kaya zata duba a Canada ɗin dama kafin ta wuce........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣5️⃣



......Ko kaɗan Lulu bata nuna damuwa da tafiyar ta Dada ba duk da kuwa a ƙasan zuciyarta cinkushe yake matuƙa, amma plan ɗinsu ita da Ummita ya sakata dakewa abinta ta nuna komai ba komai har Dada ta wuce. Washe gari shima Tajuddeen mahaifin nasa ya janye ra'ayinsa ta hanyar tura sa Nigeria da saƙo. Ko kaɗan Tajuddeen bai kawo komai a ransa ba ganin shima Alh. Sulaiman ɗin yayi shiri wai zai wuce ƙasar Brazil ne yin wani business, sai dai ɗan nasa na wucewa yayo sau da baya. Sabon gurin daya shirya za'a kai masa su Lulu acan wani ƙauye ko yanki za'a kirashi ma ne oho ya wuce. Wajene tsibiri ne, dan a tsakkiyar wani irin makeken ruwa mara iyakar kallo tsibirin yake. Gidajene kawai na masu zuwa hutawa a wajen da yawon buɗe ido, sai jiragen ruwa ne kawai ke iya kaika cikin tsibirin. Wajen kam a kwai daɗin zama musamman ga wanda suka je hutawa, zaka tabbatar da hakanne ne idan kaga yanda mutane ke nishaɗi musamman ma masoya da masu kuɗi......

Kamar kullum yau ma bata fito ba har sai da Ummita ta kamma kimtsa gidan, yay tsaf abinsa sai tashin ƙamshi da ɗumi mai ratsa ɓargon jiki daya gauraye ko'ina. Wando da riga ne a jikinta marasa nauyi, dan haka matashi cikinta ya samu damar fitowa ɗas da shi. Yau gaba ɗaya kasala takeji, dan da ƙyar ta iya fitowa dan yunwa data addaba mata ya sata fitowa ta samu abinda zata ɗan ci. Kai tsaye kitchen ta nufa inda Ummita keta ɓuruntun dama mata kununta, koda tai sallama kafin ma Ummita ta kai ƙarshen amsawa ita harta isa ga freight, ruwa ta ciro mara sanyi ta sha, tana ajiye bottle ɗin da sauran wanda ya rage ta nufi Ummita. Fuskarta da murmushi take faɗin, “Har yanzu ƙarnin kifin nan da Dada tasa kika dafa mata a gidan nan ya ƙi fita wlhy Ummita”.
         Da mamaki Ummita ta ce, “Kai aunty dan dai baki so ne kawai, amma wlhy ni banjin komai sai ƙamshin fresheners a gidan nan.”
    Cikin ɗan yamutsa fuska da tsaki ta ce, “Wlhy Ummita yanzu ne dai bana so, amma da ai kafin na ci miki nama naci kifi, sai dai yanzu na rasa miya haɗani da shi haka ko ƙamshinsa bana so”. Da dariya Ummita ta ce, “Aikin Unborn ne ai Aunty”. Shiru Lulu tai tana kallonta kamar mai nazari kosan tuna abu, abinda ke ƙoƙarin tuna kam nasa ne a zuciyarta ya zo mata. Tabbas Aliyu bama yancin kifi kwata-kwata idan bata manta ba. A take ta haɗe fuska kamar a ɗan ƙufule ta ce, “Ni shikenan saboda wannan cikin duk abinda baya ci nima na daina ci koda ina sonshi, sannan abinda yake so dole sai na so shi kamar abin asiri?”.
       “Wakenan Aunty?”.
  Cewar Ummita cikin nuna mamakin furucin uwar ɗakin nata. Sai dai maimakon bata amsa sai taga ta juya tama fice a falon tana ɗan dafe kai. Bata kawo komai a ran nata ba game da dafe kan ta cigaba da zuba mata kunun gyaɗar a flaks ɗin da ake zubawa. Ta kammala idonta ya sauka akan sauran ruwan da Lulu tasha ta ajiye, ta san da wahala ta sake shansa. Dan haka ta ɗauka ta shanye ta jefa bottle ɗin a shara sannan ta ɗauki flaks ɗin da ƙaramin kofi tabi bayan Lulu. Ɗan turus tai na mamakin ganinta baje a kujera tana barci kamar ba yanzu ta baro ta a kitchen ba. Sai tai dariya da jin tausayin ta. Ta ajiye flaks ɗin itama da nufin komawa kitchen ta gyara kayan datai amfani da su a aikin itama kanta ya sara, da sauri ta dafeshi tana mai ambatar sunan ALLAH, jin hajijiya na neman yadda ta a ƙasa da bin bango ta fito falon itama, sai dai kafin ma ta kai ga kujera ta zube ƙasa, daga haka bata sake sanin ina hankalinta yake ba itama....
       Duk abinda ke faruwa Alh. Sulaiman na kallo ta camera da ya saka musu kamar yanda Ummita ta zarga dama, wata shegiyar dariyar basanci ya saki sai kuma ya gimtse fuska duk a lokaci guda. Wayarsa ya jawo a gefensa tare da shaƙar cocaine ya wani girgiza kan nasa da wani irin style na ƙwararrun ƴan cocaine sannan ya kai wayar kunnensa. Cike da izza ya furta “Nan da awa ɗaya ku tabbatar su da duk tarkacensu suna a gabana” da ga haka ya yanke kiran batare da jiran an bashi amsa ba da ga can...

      Matuƙa hankalin Lulu da Ummita ya tashi a lokacin da suka farka da ga nannauyan barcin da ya samesu suka ga kansu a inda ba'a nan suka kwanta ba. Cikin matsanancin firgici suke kallon juna kafin su miƙe duk a zabure su fara dube-duben inda suke ɗin. Falo ne madaidaici sai dai akwai komai a cikinsa sai bedrooms guda ɗaya mai ɗauke da gado biyu, sai kitchen. Ko ina a kulle yake ta hanyoyin waje sai dai suna iya hango makeken ruwan daya zagaye ko'ina da ina ta cikin gilashi. Basu iya ganin mutanen da ke kai kawo balle iya jiyo hayaniya saboda gilashin manne da ginin bullet proof ne. Yunwar da Lulu keji dan a yanzu sam bata da jimirinta ya sata fara jin yuuu-yuuu kamar jiri zai yadda ta. Da sauri takai zaune cikin rawar murya tace, “Ummita yunwa”. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa dan haka ta miƙe cikin rawar jiki ta fara dube-duben ko zata ga abinci, cikin aminci ALLAH ta ganshi an ajiye a gefe kan ƙaramin dining table mai kujera biyu. Ɗakko mata tayi, jikin Lulu har rawa yake wajen karɓar abincin ta fara turawa, duk da baya mata daɗi haka takeci ko zata samu nutsuwa. Tan kammalawa ta fara sheƙa amai kamar zata fidda har hanjin cikinta. Ta jigatu matuƙa dan Ummita har da kukan ta, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta canja kaya ta hau gado ta kwanta ta dunƙule a waje ɗaya cikin rawar sanyi, kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Kuka sosai Ummita ta zauna ta dingayi, babban tashin hankalinta shine basu san wanene ya kawosu nan ba kuma. Duk da suna zargin Alh. Sulaiman sai dai zukatansu sun kasa zama waje guda. Sosai Lulu bata da lafiya gaba ɗaya a wannan daren, gasu a rufe balle Ummita ta fita ta nemo musu taimako. Sai da barcin wahala ya ɗauke Lulun ne Ummita ta samu damar tashi zuwa kitchen ta shiga bincike, ta ɗan samu nutsuwa ganin kayan abinci harda kayan tea, sai dai babu gyaɗa, ga shi a yanzu komai Lulu baci take ba da daɗin rai sai wannan kunun....

       Kwanakin Lulu kusan uku tana fama da zazzaɓi kafin ALLAH ya bata lafiya ta dawo dai-dai, duk ta rame sai wani uban haske data ƙara. Kamar ance su dawo nan ciki ya fara girma, ga shi bata samun kunun gyaɗar da take so sai ɗan tea da take sha kaɗan-kaɗan, abincin ma Ummita kan zauna taita lallaɓata har sai taci ko yaya ne, duk da data gama take yin amansa. Wani bai taɓa zuwa musu ba, sai a randa suke cika sati guda ne suka wayi gari suka ga an ajiye musu kayayyakin abinci dana buƙata a falo, ciki harda gyaɗa abin mamaki. Kallon-kallo kawai sukeyi, a ransu sunajin tabbacin duk abinda sukeyi kenan ana sane da su. Murmushi Lulu ta saki a karo na farko, dan dama kawo su nan ya tabbatar mata da hasashenta akan kawun nata kenan. Basu da hurumin cewa bazasuci abinda aka kawo musun ba, sai dai Ummita kan zauna ta tofeshi da addu'oi sannan. Wannan abin da take ɗin ne ya sake sakama Lulu nutsuwa da ita. A hankali shaƙuwa ta cigaba da shiga tsakanin Ummita da Lulu, har takai yanzu Ummita na ɗorama Lulu karatun Alkur'ani da na wasu littattafan addini da take da su kamar yanda Lulun ta buƙata. Sannan cikin dare Ummita kan tashi tai nafilfilinta, tun Lulu najin damuwa da takurar hanata barci da Ummita keyi kasancewar bata saba da zama mutum biyu a ɗaki ɗaya ba har itama ta fara tashi tana sallar. Hakan ya saka Ummita a farin ciki sosai, haka itama Lulun wannan yanayin na sata jin farin ciki da jinta kamar wata sabuwar hallita, dan wata sabuwar nutduwa ce ta sake zo mata. Kullum sai Ummita ta mata addu'a ta bata a ruwa ta sha, sannan takan gaya mata wasu akan ta dingayi tana shafe cikinta da shi. A haka suka cika wata ɗaya a wannan juyayyen waje da basu san inane ba, sai dai hakan bai hana Lulu cigaba da tattara bayanai akan kawun nata ba, ranar da suka cika wata guda sai ga baƙonsu na farko daya fara ziyararsu. Wato Nurse Usman, babu wanda ya ganesa a cikin su Lulu, shi kuma bai nuna musu sani ba ya ce kawai yazo duba lafiyarta. Da taƙi sai yay kiran Alh. Sulaiman. Wannan ce ranar ta farko da su Lulu suka fahimci wanda ya kawo su nan ɗin duk da ita dama Lulu ta gama bama zuciyarta shi ɗinne. Al'amarin ya sake dilmiya Lulu a kogin mamaki game da abinda kawun nata ke yi akanta, sai dai batace komai ba ba kuma ta hana Nurse Usman ɗin yin aikinsa ba duk da tana ɗar-ɗar tana son a na duba mata lafiyar jaririnta kuma, shot note da Usman ya ajiye mata ya sakata sakin ajiyar zuciya. Shima sai yay mata ɗan guntun murmushi. Ya dubata tare da bata magunguna bayan ya tabbatar mata da lafiyar cikin nata. Tai masa godiya ya tafi. Sunyi mamakin ganin bayan ya kammala sai da ya kira akazo aka buɗe masa ƙofar sannan ya fita, hakan na nufin akwai wani a waje da ke gadinsu kenan ma kamar acan inda suka baro. Ganin Ummita zata saka damuwa a ranta Lulu tai mata murmushin kwantar da hankali. Note ɗin Usman ta miƙa mata, sai ga Ummita na murmushi da sauke ajiyar zuwa. Lulu ta lumshe idanunta a hankali ta furta “Yanzu kin fahimci wasan namu ne ko? Karma ki tadama kanki hankali yanzu lokacin tattara bayanai ne, dan haka babu buƙatar cigaba da shiga damuwa kuma farin ciki kawai domin kama tsuntsu mai wayo”.
Ƙaramar dariya Ummita tayi, yayinda a ƙasan zuciyarta tamaji ta fara tsoron Lulu, dan fa ta fahimci atsabibiyar kanta ce ashe.....

Tun daga wannan ranar Lulu da Ummita suka sake sakin jikinsu tamkar basu da wata damuwa, ga ciki nata haɓaka da bunƙasa cikin ƙoshin lafiya. Ganin yanda suka sake jiki da walwala ya saka Alh. Sulaiman bada umarnin a ɗan dinga buɗe su, sai dai yana son duk inda suka saka ƙafa a tsibirin nan yana sani. Dan ya zagayesu da mutanensa kusan goma batare da sun sani ba. A cewarsa yanzu plan zai fara. Kamar yanda itama Lulu take ji a ranta yanzu wasan zai fara........✍️


_🤣🤣Hahaha anayi muna cin gyaɗa mai gishiri🥱🥱🚴_



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣



.......Tun a randa suka fara fitowa Lulu ta fahimci zagaye suke da idon yaran Alh. Sulaiman, amma maimakon ta razana sai ma tayi murmushi. Batace da tacema Ummita komai ba akan hakan, sai ma zunguran Ummita data shigayi game da sanin wacece ita? Da yanda akayi ta yarda ta biyosu Canada. Tuni hawaye suka cika idon Ummita. Bata hanasu zuba ba sannan bata sharesu ba, sai da ta jiƙe gaban rigarta sosai kafin cikin shashshekar kuka ta ce, “Sunana na yanka Fatima. Naci sunan kakata ne shiyyasa ake kirana Ummita. Asalinmu ƴan wani garine ɓagwai a ƙauyen bichi. Anan nai karatun primary ɗina, da ga baya aka kaini boarding school a wata makaranta da ake kira GGASS Ɗan/zabuwa. Naje har js 3 aka cireni na koma cikin garin Kano hannun yayata da ke aure acan sakamakon rashin lafiya data kwanta. Jeka ka dawo na koma zuwa ina kula da yayata a gidan mijinta tsahon shekara biyu harta fara samun lafiya. Tun ban wuce shekara ɗaya a gidan ba mijin yayata ke nunamin wasu abubuwan rashin ɗa'a, sai dai bana kulashi sai da naga abin na neman wuce gona da iri na nuna inason komawa gida dan ban son faɗama yayata na tayar mata da hankali. Amma sai iyayenmu sukaƙi yarda yayar tawa ma harda kukanta, acewarta idan na tafi wazai ringa kulawa da ita da ƴaƴanta biyu kamar ni. Tausayinta ya kamani sosai, dan haka na haƙura na zauna, sai dai na ɗauki matakan kare kaina tako ina har takai mijin nata shima ya daina shiga sabgata ya kama kansa. Ashe lumbu-lumbu yay min, dan sai da ya bari na shagala sannan a wani dare ina gab da kammala ss3 ya bankama yayar tawa maganin barci ya keta mun mutuncina. Maganin daya banka mata yay sanadin barinta duniya, na shiga tashin hankali irin wanda baida misali, sai dai na gagara faɗama kowa asalin al'amarin har akai sadakan uku. Ina murna zan koma gida sai babana yace na zauna tare da gwaggonmu mu kula da yaran harna ƙarasa jarabawar neco da waec da zamu fara. Naso tada hankalina amma akaita tausata, ganin akwai gwaggonmu ya sani jin zan daure ɗin. Mun fara jarabawa ina a cikin yanayin rashin jin daɗin jikina. Haka dai naita daurewa yayinda iyayenmu a bayan fage batare da sanina ba suke shirye-shiryen aurar da ni wa mijin yayata matsayin madadi waina riƙe yaranta. Da farko ya yarda sai dai a randa muka gama jarabawar ƙarshe na kaita a wahalce, tun daga makaranta aka wuce dani asibiti, inda a gwajin farko aka sanarma gwaggona da tazo inada shigar cikin wata biyu. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana, babu bin ba'asi babana ya hau dukana Sakamakon zugar da mijin yayata yay masa akan dama ance ina yawon banza ai, baya son ya faɗa ne ace dan karya auranne yake son zamewa. Iya jijjiga kamalamansa sun jijjigani, yayinda ɓacin rai ya saka baba rantsewa bazan zauna masa a gida ba. Hankalin mahaifiyata ya tashi, amma sanin halin mahaifinmu ya hanata cewa komai, sai shawarar turani Abuja data yanke wajen ƙaninta. Matar ƙanin mamana na samu damar warwarewa komai da ya faru, ranta ya ɓaci matuƙa ita da ƙanin mamana, dan haka suka ɗaukeni muka juya Kano suka shigar da ƙara kotu tare da neman lawyer daya san aikinsa sai aka haɗamu da ke. A lokacin baki jima da dawowa Nigeria ba kamar yanda naji ance, dan hausanki ma ba wani sosai yake fita ba. Kin taka rawar gani a rayuwata ta hanyar tabbatarma mijin yayana MACE MUTUM ce (Rahma Abdull-majeed. Wanda bai karanta littafin nan ba wlhy anyi bashi🥱). Dan sai da kika turashi gidan yari har yanzu kuma yana can. Uncle ɗina bai saurari iyayena ba da suka shiga nadama sosai ya ɗakkoni muka sake dawowa Abuja. Inda ya nema min makaranta na fara. Ga rainon ciki inayi, cikin danai matuƙar tsana a rayuwata har ALLAH ya kaini ranar haihuwa. Sai dai alhmdllh jariri baizo da rai ba. Hakanne ya sani farin ciki na maida hankali a karatuna. Bana zuwa gida saboda gudun zunɗen mutanen ƙauye harna kammala karatu na na samu result mai ƙyau, ina cikin neman aiki ne sai ga Hajiya Shuwa a gidan mu kasancewar tana huɗɗa da aunty na, tana kawo mata turaren wuta. Jin ina neman aikin taimin tayin wannan aikin, sai dai tace aikin na shekara ɗaya ne kacal shiyyasa kawuna ya amince da sauri, ni dai bance komai ba dan banjin zanje ɗin, sai a randa na ganki matsayin wadda za'aima aikinne ya sani yarda da sauri-sauri domin rama alkairi da kikai min nima....”
       Tuni hawaye sun jiƙe fuskar Lulu, jik 10inta har wani tsuma yake kamar wadda ake kaɗama gangi. Lura da hakan ne yasa Ummita kamata suka koma ciki batare da ma lokacin da aka basun ya cika ba.....
         
      _________★

   A ɓangaren Dada tun a washe garin da Alh. Sulaiman yasa aka canjama su Lulu wajen zama yay kiranta cikin tashin hankali da makirci yake sanar mata baiga su Lulu ba, yazo gida ya samu sun gudu. Yasa ƴan sanda nemansu da ga baya suka fahimci sun bar ƙasar ne da taimakon wani dan har note aka bar masa. Hankalin Dada yay masifar tashi har takai ta kasa controlling kanta Baba Garko ya fahimta. Tambaya ya shiga jera mata wadda ta kaita da gaya masa cewar Lulu ta gudu da ga Canada, kuma suna zargin wani ne ya sace ta. Cikin matuƙar mamaki Baba Garko ya ce, “Canada kuma Hajarah, miya kai Mawaddat Canada ko ita da mijin nata ne?”. Wannan kalma ta Baba ce ta dawo da Dada a hayyacinta. Duk kuma sai ta daburce ta rasa abin cewa  har takai Baba Garko ya daka mata tsawa, tasan halinsa baya ɗaukar raini, idan ya juye mata takan rasa gane kansa, kafin yay hakanne akan jima shiyyasa take samun damar iskancinta. Waya ya ɗauka ganin bazata bashi gamsashiyar amsar da yake buƙata ba yay kiran Daddy. Sai dai wayarsa taƙi shiga, yasan hakan nada nasaba ne da yanayin network. Ganin zancen waya ma bazai bashi yanda yake buƙata ba a ranar ya saka autansa namiji da tunda yazo da iyalinsa bai koma Saudiyya inda yake aiki ba ya yanka musu ticket, dan yace yau bazai sake kwana a ko'ina ba sai a Nigeria, saboda ya fahim al'amarin babba ne. Hankalin Dada ya sake tashi, amma tasan a wannan gaɓar bata isa yi masa wani daɗin baki ya dakata ba, dole ta shirya suka wuce a tare.
      Sunma Nigeria ƙasar haihuwarsu saukar dare, hakan sai ya sirranta dawowar tasu suka samu damar isa gida cikin kwanciyar hankali. Kowa ka gani a gidan Baba Garko ma'aikata cikin farin ciki yake da samun lafiyar tsohon abin son kowa. Mai tausayi da son ƙyautata rayuwar na ƙasa da shi, mai jan ɗan aiki jikinsa tamkar ɗan uwa ba bawa ba. Bayan albashinsu da ba'a taɓa tauyewa ba a koda yaushe cikin musu alkairin yake. Ko Zakka ya fitar sukan samu kaso mafi tsoka duk da Dada bata son hakan. Sannan duk abinda ya samu iyalansu ko lafiyar jikinsu yakance su sanar masa dan shine da hakkin wannan. Wannan yasa su jin ƙaunarshi da shiga a tashin hankali a duk lokacin da suka ga yana a cikin damuwa ko farin ciki. Sam hankalin Dada baya a jikinta, suna isowa sashenta ta wuce, layinta na Nigeria ta ɗora a waya sai dai kafin ya gama dai-daita duk ta ƙosa, hakan ya sata amsar wayar mai aikinta domin kiran Daddy. Amma abin mamaki sai ta samu number busy, bata kawo a ranta da mijinta Daddy ɗin ke kiran ba, dan haka ta cigaba da jera masa kira. Shiko Daddy dake waya da Baba Garko ganin baƙuwar lamba ce yasa koda ya kammala bai ɗaga ba, ganin ma za'a damesa ya sashi saka wayar a airplane mode kawai. Haukane kawai Dada batayi ba a wannan dare jin daga baya ma ta daina samun Daddy ɗin. Karo na farko da taji takaicin rashin riƙe number kowa na jikinsa da ga shi sai Lulu. Dan ko Yousuf ita bata da lambarsa. Matarsa kuwa (Mommy) dama ba huɗɗa take da su ba. Barcin kirki dai Dada bata sameshi a wannan daren ba sam. Tana sallame sallar asuba sai kuma ta fara jerama Daddy kira, sai dai har lokacin wayar bata shiga. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kuma kasa zuwa inda Baba Garko yake. Dan gani take kamar yana riga ya gama jin komai da komai. Tayi kiran Sulaiman kuma shima wayarsa bata shiga ba sam...

A ɓangaren Baba Garko ya gama fahimtar akwai matsala, sannan koma minene akwai saka hannun matar tasa a ciki. Yay kiran Daddy kuma dan yaji gaskiyar zance game da zuwan Lulu Canada sai ya samu numbersa busy. Akan Uncle Yousuf ya maida akalar kiran nashi, inda yaji komai da komai, yana gama wayar da Uncle Yousuf ɗin ne kuma kiran Daddy ya shigo masa. Maimakon ya tambayesa kamar yanda ya tambayi Uncle Yousuf sai ya canja kawai suka gaisa ya sanar masa yazo Nigeria, yana son da safe ya samesa a gida da wuri. Daddy yayi farin cikin jin Baba ya samu lafiya, sai dai ya shiga mamakin jin

Please Login or Register in order to submit comment