gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Furar Danko Part2 Complete Hausa Novel by Billyn Abdul Chapter 5 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunkarar mahaifinsu Alhaji Garko da batun yana son aure Mawaddat. Alhaji Garko yayi farin ciki, yayinda Dada tai tsalle ta dire tace sam bata yarda ba. Ankai ruwa rana sosai game da wannan aure, dan an samu rabuwar kai wasu na goyon bayan Dada, wasu Alhaji Garko da Mawaddat. Inda dai daga ƙarshe bayan an cuɗa an cuɗo ALLAH yay wannan aure da babu wanda yasan manufarsa sai ALLAH sai kuma su ma'auratan. Mawaddat ta shiga gidan Daddy da gigiwar izza da gadara, inda daya motsa zai taka mata birki tamai barazana da wannan video recording da maganar kuɗaɗe. Hankalinsa a tashe yake, yayinda Mommy da Uncle Yousuf suka kasa fahimtar halin da yake a ciki lokacin duk da yanda yake son fahimtar da Mommy amma sai kishi ya rufe mata ido ta kasa fahimtar ba dukiya ko wani matsayi bane ya sashi aikata yin auren ma kansa balle biyema iskancin Mawaddat a gidan. (Wannan shine kuskuren Mommy. Mata ya kamata mu dinga sanin kowanne yanayi da mazajenmu suka shiga koda akan mace ne. Mu dinga sassauta kishi a wasu gaɓoɓin rayuwa dan wani abun kanzoma bawa ba yanda ake kallonsa ba.) Daddy yata gwada son sace camara ɗin nan daga wajen Mawaddat sai dai a ankare take da duk wani motsinsa. A magana ta gaskiya a zamanshi da Mawaddat bai taɓa jin sonta ba kona yini ɗaya, dan ko'a harkar auratayya ita ke kiɗanta ke rawarta game da shi. Sai dai yana yin dauriyar sauke hakkinta har ALLAH yasa aka samu cikin Lulu, sanadin cikinne ma yasa shi ɗan fara sassauta zuciyarsa. Hatta da son ƙyautatama Mommy idan yay niyyar yi Mawaddat kan masa barazana, ga shi Mommy taƙi fahimtarsa, a kullum kawai tana kallon yana cutar da rayuwarta saboda ya auri ƴar masu kuɗi ƴar ogarsa. Ana baifi sati guda a haifi Lulu ba a wani dare yana tsaka da barci Mawaddat ta tashesa. Hakan ba sabon abu bane da take masa, sai dai kuma bayan tashinsa cikin ɓacin rai ya fahimci tashin yau yasha banban da wanda take masa a baya. Dan a mamakinsa ma sai gata durƙushe gabansa a ƙasa tana hawaye da neman gafararsa akan duk abinda ta aikata masa. Ta ce, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, nasan na aikata abubuwa masu yawa a gareka tare da tilastaka aurena badan kaso hakan ba. Na kuma azabtar da matarka itama ta hanyoyi da dama. Ba komai ya jawo hakan ba sai ɗunbin so da ƙaunar da nake maka har ƙasan zuciyata. Duk da inajin kishin matarka banso shigowa cikinku ta wannan sigar ba. Sai dai komai ya canja a dalilin wannan video na fyaɗe da kukaima Sultana kai da Ɗan uwana Sulaiman da kuma kuɗin daka salwantar a Companyn mahaifina bisa son zuciya kamar yanda ma samu labari. A ranar da kukaima Sultana abun nan nayi kuka kamar zan mutu tare da jin tsanarku irin wanda ban taɓama wani mahaluki a duniya ba, na saƙa abubuwa daban-daban akan ku a ciki harda shafe numfashinku a bayan ƙasa. Sai dai zuciyata ta gargaɗeni da yin hakan tare da bani shawarar na dafaku da ranku cikin ruwan sanyi. Na fara da kai ne ta hanyar maka barazana harka aureni, tare da nisantaka da matarka da nasan kana matuƙar so da ƙauna. Da farko naso na haɗa harda Yousuf, sai dai nutsuwarsa da hankalinsa yasa naji tausayinsa nama tsaya masa akan ya tafi makaranta dan bana son yaga abinda na tanada muku. Burina sai na gama da kai sannan na koma kan rayuwar ɗan uwana Sulaiman shima, daga ƙarshe na fallasaku a idon duniya ku kunyata. Sai dai duk wannan lissafin nawa ƙaddara ta canjashi Isma'il a dalilin wannan cikin da ya shiga jikina a mistake, sau biyu ina yunƙurin zubar da shi amma hakan ya gagara, a karo na biyun ma sai likitoci suka tabbatar min idan na sake zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Wannan yasa na haƙura na barshi badan naso ba. Sai dai kuma kana naka ALLAH na nashi, tashi kuma itace gaskiya. Wlhy Isma'il a ƴan kwanakin nan inajin kamar barin duniya ke gabatoni. Ji nake kamar bazan yi rayuwa mai tsaho ba. Shiyyasa na shirya faɗa maka gaskiya da neman afuwarka. Tare da baka shawarar kaima ya kamata ka fito ka sanarma iyayenmu gaskiyar al'amurin game da abinda kuka aikatama Sultana kai da Sulaiman koda bazaka faɗi maganar kuɗaɗe ba. Ku karɓi kowane irin hukunci hakan zaifi zama masalaha a gareku da zuri'arku gaba ɗaya”.
Sosai jikin Daddy ke rawa a wannan lokacin, ya kama kafaɗun Mawaddat ya tadata daga durƙushen da take ya rungumeta a jikinsa. Sai kawai ya samu kansa da sakin kuka. Itama saita shiga tayashi. Sosai sukai kukansu kafin su zauna dan bata jurar tsaiwa yanzu. Suna zaune a tsakkiyar gadon suna fuskantar juna hannunsa cikin nata ya ce,........✍️


_🚴🚴🚴🚴Dan ALLAH wazai tayani typing._



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣



.........“Wlhy wlhy wlhy Mawaddat ban aikata komai ba wa Sultana, sannan ban san yanda akai muka rasa kuɗin nan ba a cikin Company, iya bincike kuma nayi amma ban gane komai ba har zuwa yau. Yanda kike kallon al'amarin ba haka yake ba. Kinƙi bani damar na warware miki ne tun farko shiyyasa amma yau zan sanar miki komai. Sai dai dan ALLAH ina son ki fahimceni, sannan kiyi bincike dan ki tabbatar da gaskiya ta. Ina zaune a gida tare da iyalina Sulaiman yay kirana hankali tashe yana kuka. Cikin sauri na shirya na nufi Garko house da yace min yana can a zatona ma wani abu ne ya faru da Baba wlhy, kasancewata ba baƙo ba a gidan yasa kai tsaye aka buɗen gate na shiga, hakan ya ƙara sakani sake shiga ruɗani, bayan nai parking nayi kiran Sulaiman ya sanar min na zagayo ta baya sashen masu aikin gidan yana acan. Na ɗan ji mamaki, amma sai bance komai ba nace masa ina zuwa. Wannan ne karo na farko danai ta wajen, da kwantace na shiga sashen dan alokacin duk masu aikin na can cikin gida suna aikinsu. Na samu Sulaiman zaune yana kuka ga yarinya gefensa kwance ya rufa mata bargo. A lokacin bansan matsayin Sultana a gidan ba, zamma iya cewa ranar ne nai mata ganin farko dan har sannan ba wani shiga gidan nake ba Sosai ai. Cikin tashin hankali da ruɗewar da nake a ciki nima na shiga jera masa tambayoyi. Da ƙyar ya iya sanar min fyaɗe yayma yarinyar. Kuma wlhy shi bada manufar hakan ba a zuciyarsa. Yazo ne wajen yarinyar mai aikinku dan sun saba kasancewa a tare kawai sai ya samu Sultana a ɗakin, kasancewar baya cikin hayyacinsa saboda abinda wai wani abokinsa ya yaudaresa ya basa da kayan maye a ciki kawai ya afka mata dan tana masa gizo ne like yarinyar da yake zuwa wajen nata sai daga baya ya fahimci abinda ya tafka ɗin. Kuka yake riris da roƙon na taimakesa, wlhy idan wani yasan wannan al'amarin to gaba ɗaya farin cikin family ɗin ku zai ruguje. Kai iyayenku ma zasu iya rasa ransu musamman ma Baba. Dan ya ɗauki son duniya ya aza akan Sultana kamar kowa na gidan gashi bata da isashiyar lafiya. Bani na aikata al'amarin ba amma wlhy na shiga matuƙar gigitaccen ruɗani a lokacin jin yarinyar ƙanwarku ce, dan wlhy bamma san sanda hawaye nima suka fara zubomin ba. Shine ya kawo shawaran yana son na taimaka masa mu kaita can waje ta yanda in mu ajiyeta kamar wani ne yay mata za'a fi saurin fahimta a kaita asibiti, muma kuma hakan zai fi bamu damar kaita asibiti da wuri karta rasa ranta. A ɗan gajeren tunanina a lokacin sai na fahimci hakan shine dai-dai saboda a ruɗe nake ni kaina bana iya gane komai dan tashin hankali, inba hakaba kafin a farga anan tabbas za'a iya rasata. Sannan su masu aikin zai zame musu tashin hankali. Ace a sashensu abun ya faru da ƴar masu gida dolene ace su nemo wanda ya aikata. Na biyu tashin hankalin daya tabbatar min Baba da Dada zasu iya shiga koma su rasa ransu. Wannan shine ya ƙarfafani muka ɗakko Sultana cikin duhun magriba muka saka a motata muka kawota ƙarƙashin bishiyar da aka ɗakkota. Bakuma mubar anguwar ba har sai da aka ɗauketa zuwa asibiti. Ban fahimci nayi kuskure babba a bama Sulaiman gudunmawa ba sai da na dawo gida nake bama Kareema labari kamar akan wani abun ya faru. Kalamanta ne sukai matuƙar rikitamin lissafi da zama nayi nazari nima. Matuƙar damuwa na shiga, har na yanke shawarar tunkarar Sulaiman da batun akan magana ta gaskiya mu fito kawai mu sanar da iyayensa gaskiya, musamman ganin yanda aka kama maigadinsu da wasu masu aikin gidan aka rufe kuma da taimakonsa ne koma nace shine ya saka akai hakan. Sai dai mi koda nai masa zancen sai ya shiga roƙona da kalaman da suka sake rikitamin lissafi, ina tsaka da neman mafita ke kuma kikazo da naki kalar salon..”
       Kuka suka sake haɗe kai sunayi, sai da sukai mai isarsu sannan ta ɗakko masa camara ɗin ta bashi, hankalinsa ya tashi da ganin komai, dan tabbas duk wanda zai gani inba yasan gaskiya ba zai ce harda shi aka aikata, sai dai idan kai nazari a yanayin shi akwai sutura jikinsa saɓanin Sulaiman zaka iya fahimtar gaskiya. Laifinsa dai biyewa da yay aka fitar da Sultana a gidan. Roƙo sosai Mawaddat tai masa akan karya bar Sulaiman yasha ruwa a rayuwarsa akan wannan kuskuren har sai ya fito ya tonama kansa asiri, sannan maganar kuɗin Company ya binciki yayan nata sun salwanta ne da haɗin kansa, kuma kuɗin na hannunsa, dan taji suna tattaunawa da yaronsa Malami akan batun, sai dai ba komai taji ba da ƙyau gaba ɗaya. Wannan shine abinda take so ya mata koda bayan ranta. Ya tabbatar mata zaiyi amfani da shawaranta, dan yana son ya samu salama shima a ransa, hakan kuma bazata faru ba har sai ya fidda wannan ɓoyayyen sirrin da neman gafarar su Baba garko. Maganar kuɗi kuwa da tace ya bincika itama tai matuƙar girgiza masa zuciya, har ya fara shiga waswasi akan al'amura da dama game da abotarsa da Alh. Sulaiman ta rana tsaka. Kwana biyu da yin haka naƙuda ta tasarma Mawaddat, a lokacin daya samu Mommy na bata abu harga ALLAH a ruɗe yake, sannan ko Mawaddat ɗin ce tai mata haka a irin yanayin itama zai iya kawo hakan a ransa dan ya fahimci Mommy nada zafin kishi na masifa, shi da yake fuskantar ƙalubalen daga gareta shi yasan wannan saboda a zahiri da wahala ka gane tanada kishi a ƙanƙanin zama da ita. Dan ga wanda bai santa ba bazaice akwai ba, duk da yasan sun cuta mata, sannan tabbas tanada ƙyawawan halaye kishinne mai zafi kawai matsalarta, amma shi laifinta da yake gani shine kasa fahimtarsa da tayi tun farko. Lokacin daya ɗauki hanyar asibiti da Mawaddat cikin kuka dana azaba ta kamo hanunsa ɗaya ta ɗora a kan cikinta da faɗin, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, ka sake roƙamin matarka ta yafemin, ga amanar abinda ke cikina nan na baku, soyayya ta gaskiya daban samu daga gareka ba ina roƙonka dan ALLAH abinda zan haifa in har ya rayu shi ya samu. Kada ka bama kowa daga cikin ahalina abinda zan haifa ka riƙesa a wajenka ciki harda Dada. Idan da hali ma ka nisanta shi da su dan duk sanda Sulaiman yasan gaskiyar lamari kowane irin mataki zai iya ɗauka, kaima ka nisanta kanka daga al'amarin sa, inba hakaba wataran sai kayi dana sani, dan ƙarya yakeyi babu wani abokinsa daya bashi kayan maye da kansa yasha har cocaine yana sha dama, sannan ya jima yana lalata rayuwar masu aikin gidanmu, na taɓa tarar Dada da zancen amma bata yarda ba, sai ma balbaleni datai da faɗa akan idan taji batun a bakin wani saita ɓata min raina. Wannan dalilin yasa kaga na shige masa kamar munfi kowa shiri, amma ba haka bane ba, ina binciken abubuwa ne a kansa dan na jima ina zargin yana safarar miyagun kwayoyi a ƙasashe daban-daban musamman ƙasar Mexico, sannan yanabin hanyoyi daban-daban wajen ɗibar kuɗin baba. Na yi shirin idan na kammala bincikena na bama Baba bayanan ta hanyar gani da ido da zai tabbatar. Dan haka akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a cikin camara ɗin nan da suka shafesa sai kayi takatsantsan dan dama saboda shi na mallaketa...”
       Wannan magana ta Mawaddat ta saka rayuwar Daddy sosai a wani hali bayan rasuwarta, shine dalilinsa na hana ahalinta jaririya daya maidama suna Mawaddat, tare da nuna mata soyayyar data roƙa garesa kuma yay mata alƙawari, wadda harga ALLAH bayan rasuwar tata kuma sai yake jin soyayya mai nauyi a kanta. Sai tausayin yarinyar da ya ringa ɗibarsa kuma shima. Dalilinsa na hana Mommy Mawaddat shawarar da yaji dangin mahaifiyarta na bata ne, hankalinsa ya tashi da jin abinda suka faɗa mata akan marainiyar ALLAH da batama san minene duniyar ba, sai dai ita Mommy bata san yaji ba. Yaso yay mata uziri amma jin itama ta karɓama ƴan uwan nata da cewar ai duk abinda Mawaddat tai mata saita ramashi akan Lulu ya saka zuciyarsa a razani lokacin. Dan baiyi tunanin kishin Mommy zaisa idonta rufewaba ta karɓi shawarar ƴan uwan nata. Wannan dalilan yasa ya sake tsayawa akan al'amarin Lulu ya hana kowa jingina da ita. Sai kuma ga abinda yafi na Mommy ya ɓullo masa, bai san yanda akayi Alh. Sulaiman yasan da camara ɗin hannunsa da Mawaddat ta bashi ba, kawai a wata rana ya samesa da batun a rikice, yace ya bashi camara ɗin Please. Amma sai shi Daddy kansa tsaye yace bazai bada ba har sai Alh. Sulaiman ya sanar masa gaskiyar al'amari game da harkar shigo da kayan shaye-shaye daya tsunduma shi, sannan ya faɗa masa gaskiya akan ya akai kuɗaɗen nan suka salwanta da kuma haikema Sultana a sashen masu aiki bayan kowa ya shaida bata zuwa can ɗin sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Wani banzan kallo Alh. Sulaiman yay masa tare da masa nuni da baida hankali. A kausashe ya ce, “Isma'il kai wanene da zaka titsiyeni? Yaushe ma ka kai inda kake tunanin ka kai ɗin? Kana almajirin gidanmu dan na jawoka kaci arziƙi har kake ganin idonka yay tsaurin sanin abinda ni kaɗai ya shafa. To daga yau ka kama kanka. Camara kuma idan baka bayar ta arziƙi ba zaka bada ta tsiya. Sannan ita wannan yarinyar ka shirya dan dolene na hukunta rayuwarta da laifin mahaifiyarta, dan ni bana yafiya bana kuma barin bashin gaba. Sannan sabo da kaza a wajena baya hanani yankata. Ba ita data zama ɗiyar ƙanwata ba, ko ita ƙanwar tawa da tana raye saina ɗan ɗana mata azabar sanin ainahin Sulaiman, amma duk da haka wannan ƴar tata zata fansheta ne”.
      A lokacin tsawa Daddy ya daka masa, sai dai kafin yace komai Alh. Sulaiman ya bar wajen.
      Wannan ne sanadin komai da zama mafarin ɗauke Lulu daga Nigeria Daddy ya maidata Garmany ya nema mata Nanny da tunanin ya kuɓutar da ita daga sharrin Alh. Sulaiman, shine kuma mafarin duk wani rikicin dake a tsakaninsu, dan har yanzu dai camara na a hannun Daddy duk barazanar da Alh. Sulaiman ke masa yaƙi bashi ita. Ya kuma kasa gayama kowa ciki harda Uncle Yousuf da Mommy dama Baba Garko....

     Wannan kenan.
        

        *_★CANADA★_*

    Zuwa yanzu wata irin nutsuwa ce ke saukarma Lulu maiban mamaki, yayinda girman da cikinta keyi ya fara ɗaukar hankalinta. Da farko ta ɗauka tunbi ta fara tarawa, hankalinta ya tashi ta fara tunanin ko kunun gyaɗar da take shane ya kawo mata haka. Ta yanke hukuncin fara fita motsa jiki kawai da alƙawarin daina shan kumun gyaɗa duk da tasan hakan bamai yiwuwa bane. Sai dai bata san yaya zatai hakan ba dan yanzu hatta security ɗin gidan na ƙofa Alh. Sulaiman ya canja shi, idan zata fita dole saita kira Dada ita kuma ta kirashi sai yasa a buɗe. Gefe guda ga cid ko bodyguard zata kirasu ma ita bata sani ba yasa suna bibiyar al'amarin ta. Ta fahimci hakanne a randa sukai fita yin wani shopping ita da Ummita. Hankalinta ya ƙara tashi, dan zuciyarta zuwa yanzu ta fara ayyana mata abubuwa da dama. Cikin harda tunanin anya kakar tata da kawunta basu da wata manufa a kanta. Wannan shine mafarin data fara natsar da zuciyarta waje guda da hankalinta domin fahimtar abubuwa a matsayinta na lawyer. Abu na biyu shine randa ta amshi wayar Ummita da nufin kiran Daddy a karo na farko. Dan ita nata wayoyin ma ta mantosu a Nigeria tun sanda ta taho, tanata ma Dada naci akan a kawo mata sai taita cewa ta manta. Koda Lulu ta saka number Daddy ta kira sai taji Alh. Sulaiman ya ɗaga. Hakan ya ɗaure mata kai akan miya kawo wayar Daddy hannun Uncle ɗin nata, amma sai ta tsinkayi Alh. Sulaiman ɗin na ƴar dariya da faɗin,........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟

__________________

*3 DAYS CLASS*

Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rararar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rararar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni

Class ze fara gobe jumaa insha Allah

WhatsApp group 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA

WhatsApp 08144147273

_______________

........“Karki cigaba da wahal da kanki wajen kiran kowa da wayar nan Mawaddat, koda kuwa Dada ce. Dan duk wanda zaki kira ni ne zakiji na ɗaga, dan lokacin da zasu san ina kiken baiyi ba”. Da ga haka ya yanke wayar ya barta da baki a sake. Na uku har gida ake kawo mata kayan shaye-shaye sai dai yanzu bata iya sha, kallon magani kawai ma tayar mata da zuciya yake yi, jima take ta tsani koda ganinsu. Na ƙarshe shine rashin dawowar Dada Canada tun tafiyarta kusan wata uku kenan. Idan sunyi waya kuma sai tace mata zatazo uziri ne ya riƙeta. Tajuddeen na zuwa gidan kusan duk bayan kwana biyu. Amma ko kallo bai isheta ba. Dan in yazo idan zai yini mata magana ko a bata furta masa har ya gaji ya tafi. Daga baya ma sai ta koma duk randa yazo kulle kanta take a ɗaki har yabar gidan baya ganinta. Duk da yanda waɗan nan abubuwan ke mata kai kawo a rai sai yanayin canjawar jikinta yafi komai ɗaga mata hankali. Da gaske fa komai nata ya canja, tayi ƙiba hallitun jikinta sun sake cikowa, ga wani mugun fresh da tayi kamar ka taɓata jini ya fito. Sai period ɗinta, duk da dama tun kan tai aure yana mata haka tai wata uku bata gani ba, idan kuma zai zo tasha wahalar ciwon mara. Tasha ganin doctors akan matsalar amma amsa ɗaya take samu shine yanayin halittar tane kawai haka lafiyarta lau. To amma a wannan karon idan fa zatai lissafi kusan watanta biyar kenan batayi ba, sai jinin data zubar na lokacin da su Dada suka zubar mata da ciki. Ganin al'amarin na neman sakata a wani hali ya sata saka Ummita ta kira mata Dada. Dada da har yanzu basu koma Nigeria ba sai dai suna shirye-shiryen hakan cikin mamaki take sauraren Lulu dake mata bayani akan rashin ganin period ɗintan. Amma ganin yanda Lulun ta tada hankalinta sai ta shiga kwantar mata akan ta bari zata turo mata Dr Olivia ko kuma ta shirya suje asibitin su sameta. Ɗan son fita da take ne yasata cewa gwara su sametan to. Sai Dadan tace to bari ta samu Alh. Sulaiman da maganar. Kasa shiru Lulu tai ta jehoma Dada tambaya akan miyasa yanzu komai nata sai Dada tace sai Uncle Sulaiman ya sani. Ita kanta Dada sai hakan ya tsikari zuciyarta, rashin sanin ƙwaƙwƙwarar amsa ya sata faɗin Lulun ta bari har sai tazo zasuyi wannan maganar. Badan Lulu taso ba tayi shiru.
       Sunje asibiti sun sami Dr Olivia, inda akaima Lulu gwaje-gwaje da duk suka dace, babu wani wahala aka gano ciki ɗan watanni biyar a mararta sai dai kwanakin sa sun ɗan koma baya kaɗan, hakan kuma nada nasaba da yunƙurin zubar da shi da akayi kenan. Ba Lulu ba hatta Dr Olivia ta shiga ruɗani, dan al'amarine da bata taɓa cin karo da shi ba. Saboda tabbas ita shaidace sun zubar da cikin Lulu, sun kuma tabbatar da hakan, amma a yanzu ace musu kuma a kwai shi gashi yana rayuwa cikin ƙoshin lafiya. Dada ma da taji al'amarin hankalinta ya tashi, ta kira Alh. Sulaiman a rikice ta sanar masa. Tamkar wani sumamme haka ya daskare a waje ɗaya, har Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen da suke tare a lokacin na tambayarsa ko lafiya? Bai iya cemata komai ba face furzar da wata irin iska mai zafi daga bakinsa ya miƙe ya fita. Kaɗan ta taɓe bakinta tare da binsa da kallo, gaba ɗaya kwanakin nan ta gagara gane kan mijin nata, iya tambaya da lallaɓa tayi shi kuma ya dage mata akan babu komai.....

     Wani irin rikicewa da daburcewa Dr Olivia tai lokacin data juyo sukai ido huɗu da Lulu da bata san tana bayanta ba. A yanda taga Lulun kuma ya tabbatar mata taji wayar da tai da Dada. Cikin harshen turanci take ma Lulu magana harshenta na sarƙewa. Hannu Lulu ta ɗaga mata kawai alamar bata son jin komai, daga haka ta bar wajen cikin tangaɗin hajijiyar da take ji na kwasarta. Amma koda ta fito sai ta sauya yanayinta saboda bodyguard ɗin da Alh. Sulaiman yasa suke biye da su. Magana taima Ummita akan tazo ta rakata restroom. Ganin ɗaya daga cikin b.g ɗin na ƙoƙarin biyosu ta kallesa sheƙeƙe da faɗin “Can ɗin ma sai ka bimu. Ko an faɗa maka ma na gama abinda nake a asibitin!”. Tsayawa yay kansa a ƙasa dan ya fahimci masifar Lulu tafi tashi.
         Tsaki taja da sake ɓalla masa harara sannan taja hannun Ummita. Ba restroom ɗin suka shiga ba, da ga can gefensa suka tsaya, karo na farko a rayuwar Lulu da taji ya cancanta ta sanarma wani damuwarta, dan zurfin ciki babbar ɗabi'arta ce shiyyasa abubuwa da yawa sukai mata nauyi a zuciya.
     “Ummita so nake na gudu”.
“Sosai Ummita ta waro idanu waje, sai kuma ta kalla inda Bodyguard ɗin nan da Lulu bata lura ya dai biyosun ba a laɓe, ƙasa Ummita takai kamar mai son gyarama Lulu takalmi, dan Ummita wayayyar mace ce da taga jiya taga yau, hasalima tashin ƙauye ce ita, daga baya ta dawo wajen yayarta a cikin Kano, sai dai matsalar data fuskanta ya sata komawa Abuja a yanzu.. “Aunty karki ruɗar da kanki dan munafukin nan ya biyo mu. Muyi tamkar takalmin nake gyara miki”. Lulu ta fahimceta dan haka hankalinta ya sake tashi. Amma sai Ummita ta ce,

Please Login or Register in order to submit comment