You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
da hango halin da Lulun ke a ciki, amma bata cewa komai saboda lokacin cewar bai isa ba...
A ranar da su Lulu ke cika kwanaki biyar da zuwan baƙon duniya su Abba da Daddy suka iso ƙasar Canada, tafiyar da tai masifar tada hankalin su Ummah dan Abba yace musu zasuje duba Smart ne zuwa ƙasar England. Jidali iya jidali rasar su Aunty Amarya sun gani wajen Ummah, dan su Asma'u ma basa gidan Ammah catai su tafi gidan yayunsu har sai sun dawo su dawo. Dan haka suka tafi gidan Aunty Bilkisu da shirin idan suka mata kwana biyu sai su koma gidan Hawwah itama su mata kwana biyu. Babu irin zagin da Ammah bata sha ba ranar har maƙwafta sai da suka shigo, inda mutane da yawa suka fara fassara al'amarin Umman da hassada. Dan sukam basu ga wani abin tada jijiyar wuya a nan ɗin ba...
Oho su Ammah ma basu san tana yi ba, dan suna can a hanya hankalinsu kwance. Ƙasar England su Abba suka fara yada zango wajen Smart. Wanda zuwan nasu yazo masa a bazata sosai, dan sam Uncle Yousuf bai sanar masa ba. Tsabar farin ciki baima san lokacin da ya rungume Ammah ba. Turesa tai cikin jin nauyi da faɗin, “Kajimin ja'irin yaro abinda ka koya a ƙasar turawan kenan kuma?”. Cikin dariya da shagwaɓa Smart ya ce, “Ammah nafayi missing ɗinki ne, ALLAH sai nake ganin kamar mafarki nakeyi”. Tsinguli ta kai masa da faɗin, “Bari na tabbatar maka idonka biyu”.
“Ouch!” ya faɗa cikin turɓune fuska yana kallon Abba a marairaice. Abba ya riƙo masa hannu yana hararar Ammah. Daddy da Uncle Yousuf dai dariya sukeyi, dan basu taɓa zaton Aliyun taɓararre bane a wajen iyayen nasa sai yau. Smart ya gaishe da Daddy cikin girmamawa, Uncle Yousuf kam ai baida maraba da aboki duk da yanzu ana ƴar kunyar surukuta kaɗan-kaɗan. Sosai mazaunin Smart ɗin ya ƙayatar da su Ammah, suka shiga godiya ga UBANGIJI a zukatansu da mamakin wannan rahama ta UBANGIJI. Sunci sun sha daga abincin da Smart ya tanada musu a cikin ƙanƙanin lokaci, dan abinci ne na ƴan Nigeria. Bayan kowa yaci ya ƙoshi suka ɗan tattauna, sosai zaman ya sanyaya ran Smart, inda ya fahimci surukinsa sosai a yanzu ya kuma sakko daga fushin daya tafi. Sun tafi zuwa masauki aka bar masa Ammah da Abbah nan. Hakan ya musu daɗi su duka, dan sun sami damar tattauna abinda ya shafesu sosai shi da iyayen nasa. Inda ya ƙara warware musu cigaban da ya samu da wanda yake fatan samu anan gaba. Ƴan uwansa kaf bai manta da kowa ba sai da ya tambaya, har maƙwafta da abokan arziƙi. Ranar dai ansha hira, dan duk rashin yawan maganar Ammah da Smart yau dai sun sha hira abinsu kamar suyita kasancewa a haka suke ji...
Washe gari da yamma suka wuce Canada har da Smart dake jin wani irin faɗuwar gaba lokaci-lokaci, yakanyi sauri ya ambaci sunan ALLAH. Wannan ziyara tazo ma Lulu a bazatar bazata. Dan bata san wainar da ake toyawa ba sai kawai ganin Usman tai da baƙi. Lokacin da suka shigo tana toilet ne ita da Mamy dake gasa mata jikinta da towel kamar dai yanda ake cikakken wankan jego a Nigeria duk da Lulu tasha maganin da ya dace Mamy bata barta ba kullum sai ta mata safe da yamma ita da ɗan jinjiri.
A hankali take tafiya Mamy biye da ita, tayi fayau da ita sai haske data ƙara da wani cikar ido irin na jego dan tana samun kulawa sosai irin ta malam bahaushe a wajen Mammy duk da cs akai mata. Alhamdullah kumburin ciki da tai duk ya saɓe amma baza'a kirata ramammiya ba kai tsaye. Sanye take cikin doguwar riga mara nauyi dake a buɗe sosai saboda yanayin inda aka yanka ta. Baya tai zata faɗi saboda firgicin ganin abinda idanunta suka gane mata, sai da Mamy ta riƙota tana faɗin, “Mawaddat yi a hankali kinji”. Daga lips ɗin Lulu har zuwa jikinta rawa yake yi, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo tun daga kan Daddynta har zuwa mutum na ƙarshe da ke tsaye ya ɗan jingina abango da harɗe ƙafafunsa waje guda. Sanye yake cikin Suit milk da sukai masifar masa ƙyau da fitar da cikar haiba da kamalar da ya ƙara, ga wani irin ƙamshi mai sanyi da daɗin shaƙa, gaba ɗaya ya canja da ga Smart na Nigeria zuwa wani baƙin bature mai aji a yanzu. Yanda yay tsaiwar ƙasaita da harɗe ƙafafunsa waje guda idanunsa a waya yana daƙila kamar baya a wajen saika rantse ba shine ke zumuɗin azo ba fiye da kowa. Sai da Mamy ta ambaci sunan Lulu ne ya ɗan ɗago idanun nasa a hankali da take kira na macizai kamar zai lumshesu sai kuma ya zuba mata su cikin shammata da bazata.
Wani irin girgiza zuciyarta tayi ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri. Rashin mafita ya sata juyawa cikin tsumar jiki ta basu baya tana mai rumtse idanunta da masifar ƙarfi. Ammah ce ta taka a hankali zuwa gareta, cikin tausayawa da ƙauna ta kira sunanta. Kasa juyowa Lulu tayi sai jikinta da ke ƙara ƙarfin rawa. Riƙo hannunta Ammah tayi ta juyo da ita a hankali, sai kaiwa ta faɗa jikin Ammahn ta rungumeta tsam-tsam tare da sakin kuka mai tsuma zuciya.
A hankali Smart ya sauke idanun nasa ƙasa yana wani irin haɗiyar zuciya da sauri-sauri. Dai-dai nan Ummita ta shigo ɗakin da sallama bayanta goye da baƙon duniya dake barci. Turus tai tana kallonsu itama cikin tsoro da mamaki, yayinda su kuma suka zubama jinjirin bayanta ido. Uncle Yousuf ne yay ƙarfin halin mata nunin ta kunto yaron. Sai ta kalli Mamy. Kai Mamy ta jinjina mata alamar ta kuntosa babu matsala, dan haka ta ɗan saki ajiyar zuciya tare da kunto yaron ta miƙama Uncle Yousuf ɗin. Kamar ko ya sani sai ga idanu ya ɗan buɗe yana motsa baki alamar neman abinci. Dariya Uncle Yousuf ya saki da faɗin, “Oh oh Aliyu dai kawai ne anan babu wani banbanci wlhy sai na shekaru”. Yay maganar yana ƙarasawa gaban Abba da Daddy cikin sassarfa. A hankali Smart da idanunsa ke kan yaron ko ƙyaftawa babu tun shigowar Ummita ya wani lumshe idanun da suka kaɗa a hankali yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Jin al'amarin yake kamar a mafarki, shi Aliyu Hydar ne da ɗa na mutum matsayin mallakinsa a wannan duniyar. Ya arrahaman ALLAH mai alkairi. Furucin Lulu da ke faɗin, Ammah nayi kewarku cikin kuka ya sashi buɗe idanun nasa ya zuba musu su. Murmushi Ammah da ke sharema Lulu hawaye takeyi, kafin ta kama hannunta ta ƙarasa da ita a saman gadon da take jiyyar. Dai-dai nan Abbah ya ƙarasa da Jinjirin ga Smart, nannauyar ajiyar zuciya Smart ya ja tare da fesarwa, sai yaji ma duk ya sake daburcewa. Fahimtar hakan da Abbah yay ne ya sashi sakin ƙaramar dariya da sake miƙa masa yaron. A hankali ya miƙa hannayensa duk biyu Abba ya saka masa yaron a ciki, sai da yay masa kallon kusan sakanni goma kafin ya matsar dashi saman ƙirjinsa ya rungume tsam-tsam dai ga hawaye sharrrr. Uncle Yousuf dake murmushi ne ya ƙaraso gareshi, cikin tsokana ya ce, “A'a ƙanina kaga zauna karka zube mana a ƙasa majiyatan su sake ƙaruwa kuma”.
Furucin Uncle Yousuf ɗin ya sata sake ɗago idanu a karo na biyu ta kallesa, sai akai sa'a shima ita ɗin yake kallo har yanzu yaron na'a rungume jikinsa sai dai ya share hawayen. Harara ta balla masa da ɗauke kanta tana tura baki. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana wani ƙasa-ƙasa da idanu shima. Ammah da ke ankare da su su duka ta ce, “Babana zo mana naga sabon uba dana sake yi, danni kam kai da Mawaddat kun zama Kakannina yanzu kam tunda kun haifa mini Babana”.
A hankali ya tako gaban Ammah cikin yanayin nan nasa na nutsuwa da kasancewa jarumin namiji tsayayye. Maimakon ya miƙama Ammah babyn sai ya kai zaune a kujerar gaban gadon kusan da Mawaddat da hankalinta ke kan Uncle Yousuf da ke mata magana ƙasa-ƙasa.....
Bayan an gaggasa Lulu ta gama ma Daddy da Uncle Yousuf shagwaɓa da koke-kokenta suma sukai mata faɗa akan barin ɗakin mijinta tabi Dada. Ta basu haƙuri da amsar kuskurenta. Sunji daɗin nuna nadamar tata kuwa a gaban kowa. Duk alkairin Ummita da Mamy da Usman gareta bata ɓoye ba. Su Abba sukai musu godiya sosai da wannan karamci duk da akwai sannaya tsakanin mahaifin Usman ɗin da Daddy. Bayan komai ya natsa an fahimci juna Usman yay ma su Abba jagora zuwa masauki, har lokacin kuma bakin Lulu da Smart bai saɓa ba, sai dai ƴar satar kallon juna, koda yake ma shike satar kallon nata, itako tayi biris kamar ta ma manta da shi a ɗakin take nunawa. Baiji komai a ransa ba game da hakan dan halinta kuma ai sai dai ya bama wani labari yanzu. Lulu akwai jan aji, koda wasa bata yarda ta zama a ƙasa ba akan al'amarinta. Lokacin da zasu wuce Usman ya ce ai shi Smart a barshi anan tare zasu wuce gida, suje su ya fara kaisu masauki sai ya dawo ya samesa. Mamy da Ammah kam dama tuni sun fice zuwa ɗayan ɗakin gidan. Itama Ummita sai ta zare jikinta cikin dabara wai bari ta wanke kayan baby data jiƙa ɗazun. Harara Lulu data fara tsarguwa da wannan ƴar zare jikin da ake ɗai-ɗai tabi Ummita da shi, sai dai batace komai ba dan Ummitan ta fita tana mata dariya...........✍️
*_😂Kar naji wani yace komai kuma ehe. Musamman ma dangi dangi Smart ɗinnan. 🙈Koda yake akwai su aunty fa🚴🚴_*
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣
.......Shiru ɗakin yay bakajin komai sai ɗan ƙarar room hitter kasancewar sanyin da ake zubawa. Zaune yake cikin kujerar nan cike da ƙasaita ɗansa rungume a jikinsa ya zuba masa idanu kawai tamkar mai son gama haddace halittar jikinsa gaba ɗaya. Yayinda ita kuma take zaune a gadon jiyyarta ta miƙe ƙafafunta dake cikin blanket hannunta riƙe da sabuwar tab da Usman ya siya mata jiya. A zahiri wayar take kallo da sarrafawa, sai dai a ƙasan zuciyarta mamakin irin canjawar da Smart ɗin yayi take har yanzu, tamkar fa ba drivern nan nata ba, ya wani goge ga tsadaddun kaya wanka iya wanka, koda yake tun ma yana a drivern sa ita shaida ce ya san sirrin saka kaya, sai dai na yau ɗin dabanne, dan ko faratansa ka kalla kasan ya samu canjin rayuwa. Dama can bamai hayaniya bane shi, amma yanayin nasa na yanzu ya sake sakashi a wani matsayin zafafan maza masu aji da jan ajin. Kai itafa ALLAH da'ace a hanya taga mutumin nan maybe bazata iya shaida shi ɗin bane ba duk da kamaninsa na nan a tare da shi, sai ƙyawu da kwarjininsa mai bayyana cikar kamala da haiba da ya sake bayyana. Numfashi taja a hankali ta fesar, sai kuma taja ƙaramin tsoki da ya sakashi ɗagowa a hankali da ga kallon babyn nasa da yake yi ya sauke mata firgitattun idanun nasa da take kira na macizai. Duk da bashi take kallo ba sai da tsigar jikinta ta tashi ta kuma ji kaifinsu a cikin jininta. Sai kawai ta sake ɗaure fuska.
Cikin son ta kallesa da deep voice ɗin nan tasa acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Ashe haka kika ɗauki darasin nan nawa da gaggawa ɗaliba ta? Ai ban san ke ɗin zaki kasance duka ɗauka ba haka, ga result na first class na gani kam”.
Sosai ta danne zuciyarta wajen nuna masa tamkar bama ta jisa ba balle ta fahimce shi. Amma duk da haka sai da ta ɗan saci kallonsa ta gefen ido. Wani murmushin ƙasaita ya saki tare da miƙewa ɗauke da babyn ya isa zuwa gareta, kafin tayi wani yunƙuri ya kai zaune a bakin gadon har jikinsu na gogar juna. Babu wanda baiji shock a jikinsa ba amma kowanne ya basar. Kaifafan idanun nasa ya zuba mata yana mai kai hannunsa ya ɗago haɓarta ta yanda zai kalla fuskarta sosai da ƙyau. Suna haɗa ido sai kawai ta lumshe idanun nata da ture hannunsa zuciyarta na wani irin harbawa, ita kaɗai tasan mi take ji game da shi, amma bata so tayi giving up, not now. Ƙoƙarin sake riƙo fuskar tata yake yi ta buge masa hannu a karo na biyu.
Murmushi yayi mai sauti, tare da faɗin, “Baki son gani na ne?”.
Ba tare data sake iya kallonsa ba a tunzire ta ja tsaki da faɗin,, “Aliyu bana son damuwa, wannan rayuwa ta ce, ka fita kamar yanda na buƙata tun farko please. In ma saboda wannan ɗan kazo kasa a ranka baka da alaƙa da shi, koma kana da ita to yafi ƙarfinka danni da ga yau da ga yanzu na datse alaƙar taku har abada.”
Wani irin murmushi ya saki mai ƙayatarwa tare da tsurama babyn ido, sai kuma ya ɗago yana kallonta cikin lumshe idanunsa da buɗesu duk a lokaci guda. Cikin murya mai taushi ya ce, “Mawaddatan'warahmah! Kin taɓa ganin inda aka raba jijiya da ƙashin baya aka cigaba da rayuwa akan ƙafafu? Duk wanda ya kalla wannan ajiyar ALLAHn yasan zufan Aliyu Hydar Mika'il Idris Mawashi ne ai. Shi ɗin jinin jikina ne, ke da kika haifa min shi kuwa jijiyar ƙashin bayana ce, taya kike tunanin zan rayu a lokacin da babu jini a jikina babu lakar ƙashin baya? Please ki kalla cikin ƙwayar idanuna ko sau ɗaya ne, maybe ki karanci abinda ke a cikin zuciyar Aliyu Hydar ɗin ki. So ɗaya yake miki tak da in sha ALLAHU wata mace bazata sake samun kwatankwacinsa ba. Ko so kike sai na kai ƙasa gaba ɗaya zaki yarda da ni?...”
Harga ALLAH kalamansa sukarta suke. Sannan yamutsa mata illahirin jinin jikinta sukeyi. Duk wani ƙwarin gwiwar ta a garesa neman suɓucewa takeyi. Cikin sanyin jiki da rauni ta ɗago idanunta cike da ƙwalla, sai dai bata iya kallon cikin nasa idanun ɗin ba kamar yanda ya buƙata ta maida su ta duƙar.
“pleaseee!”.
Ya faɗa a hankali cikin wani irin salon jan “e” ɗin ƙarshe data saka tsigar jikinta mimmiƙewa gaba ɗaya. Sai kawai ta samu kanta da sakar masa kuka da faɗin, “I say live me alone please Aliyu. Kace ka sakeni bayan ka keta min haddi akan abinda na bada tsahon shekarun rayuwata na hankali ina karewa, mi kuma ya rage da kake buƙata a gareni yanzu? Ko ɗan numfashin da ya sauramin kuma shima so kake sai ka rabani da shi zaka huta? Ka barni dan ALLAH, ka cigaba da zama a nesa da ni ni yafi min I beg you” ta ƙare faɗa cikin haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo🙏.
A hankali ya kwantar da yaron gefe ɗaya, tare da matsawa kusa da ita. Jikinta ta janye baya tana sake fashe masa da kuka. Ƙoƙarin riƙota yake tana buge masa hannu. Bai damu ba ya riƙota ya saka a jikinsa ya rungume tsam. Tana ƙoƙarin masa magana cikin kuka da fisge-fisge ya hanata kowacce irin dama ta hanyar manne lips nashi cikin nata. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya saki yayinda ita kuma ta sake sake masa kuka da san ƙwatar kanta. Sai da ya tabbatar ya saka jikinta yin laushin da ta daina ƙoƙarin raba jikinta da shi sannan ya saketa dan jikinsa ya fara karɓar al'amarin. Da sauri taja jikinta gefe ta dunƙule waje guda tana faɗin, “Mugu ALLAH sai ya sakamin”.
Murmushi yay da lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. A nutse cikin firzar da huci ya ce, “Muguntar mi nayi ni da halalina kuma. Mawaddat believe me duk wanda ya faɗa miki na sake ki ƙarya yay miki, har abada Aliyu bazai taɓa rabuwa da Mawaddat ba koda ana min azaba da bulalai ina tuɓe a tsakkiyar sanyin ƙanƙara. Har abada Aliyu zai cigaba da kasancewa matsayin mijin Mawaddat ne koda bazata cigaba da rayuwa da shi ba.”
“Aiko dole ka rabu dani, dan inada kalar mijin da nake so in ma auren zanyi amma ba irin ka ba”.
“Ohh just keep your mouth up Mawaddat! Idan ma mafarki kike to ki farka wlhy, kuma duk sanda kika sake ambatar min kalmar wani namiji na rantse miki sai na darje waɗan nan silly lips ɗin naki ta yanda bazasu sake buɗuwa da sunan magana ba”. Ya faɗa cikin hasala da birkice mata tamkar wani bajimin bahagon matashin zaki. Har Babyn da ke a gefensu yana barcinsa na ɗan zabura shima dan tsorata. Da sauri ya ɗaukesa ya mannasa da jikinsa yana mai lumshe idanunsa da suka kaɗa sukai jazur a ƙankanin lokaci. Duk tsaurin ido irin na Lulu ita kanta sai da ta firgita. Dan tsantsar tartsatsin wutar bala'in kishi ta hango a cikin birkitattun idanun nasa. Ta gefen ido ta saci kallonsa, dan ya miƙe yana jijjiga yaron saboda mutsu-mutsun da ya cigaba da yi. Ganin ya fara ƙushin-ƙushin ɗin kuka ya dawo gabanta cikin takun ƙasaita da hasala. Saman cinyarta ya ajiyesa babu alamar wasa a tattare da shi cike da bada umarni ya ce, “Shayar min da yaro abincin sa”.
Ɗago idanunta data ƙanƙance tai cikin hasala da mamakin ƙarfin halinsa. Sai dai hararar da ya wurga mata cikin tashi hasalar ya tabbatar mata wannan fa ba Aliyun baya bane data saba yima yanda taso. Sai ma duk taji tana neman daburcewa. Shiko ganin bata da niyar bama yaro abinda yace kawai ya kai zaune gab da ita kansa tsaye ya tura hannunsa a rigarta ya fiddo, zaro idanunta tai a wani irin razane, sai dai shi ko'a jikinsa dan kallo ma bata ishesa ba hidimar gyara yaron yake da ƙyau ya saka masa a baki. Shiko ɗan albarka ya cafke abinsa da sauri har sai da tai ƴar ƙaran jin zafi. Sai dai ta gagara ture uban da ɗan dan duk ya kanainayeta ga numfashinsa da ke sauka a jikinta wani irin harmutsa mata lissafi yake neman yi gaba ɗaya. Da ƙyar ta iya fisgo kalmar, “Aliyu wai miye haka bana son wulaƙanci f.....”.
Fuskarsa ya matsar gab da tata ta yanda ta kasa ƙarasa abinda ta faro faɗar, ya wani busa mata iska a fuska da wata irin murya acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Naga dai namu ne ai ni da shi. Dan haka bama son hayaniya karmu ƙware”.
“Takaici, haushi, kunya, duk suka kanainaye Lulu a lokaci guda. Ga wani irin neman rikita mata lissafi da kusancin nasu ke neman yi. Shima kansa a wahalen yake da kusancin nasu, dan da ƙyar yake danne zalamarsa da haɗiyeta..... Lips ɗinta da ke rawa-rawa ta buɗe zatayi magana sallamar Ummita ta katse ta, Ummita da ta shafa'a da kasancewar sa a ɗakin bata jira an amsa mata ba ta shigo, hakan ya sashi jan jikinsa baya da gyara mata yaron cike da basarwa. Ita ma Ummitan sai tai saurin juyawa zata koma cikin ruɗewa tana faɗi, “Ya ilahi dan ALLAH kuyi haƙuri, wlhy na shafa'a”.
Smart ne cikin ɗan furzar da iska mai nauyi ya furta, “Karki damu dawo abinki”. Badan Ummita taso ba ta dawo, sai dai kanta a ƙasa ta ajiye bowl ɗin data shigo da shi mai ɗauke da gasashen nama da yaji kayan haɗi da Mamy ke haɗama Lulun duk bayan kwana biyu. Zata juya Lulu dake hararar baby da babansa ta dakatar da ita da faɗin, “Ummita anko samo zam-zam ɗin?”.
Kanta a ƙasa ta ce, “Eh Yaya Usman ya sayo tun ɗazun ai, harma da zumar”.
“Yauwa dan ALLAH haɗo a fidarsa kin sanshi ba ƙoshi yake ba ya gado ci irin na ub....”
Sai kuma ta kasa ƙara sawa ta murguɗa baki kawai. Murmushi Smart ya saki, a hankali ya furta, “Ai dama ƙyawun ɗa ya gaji Ubansa. Baki ji har sunan bai bari ba ya gado. Ashe haka kike son sunan nan amma baki taɓa faɗa min ba?”.
Harararsa tai cikin takaici tana jin kamar ta shaƙurosa. Sai dai batai magana ba dan sai ma yanzu take jin haushin kanta da tace a saka mata sunan. Baki Smart ya taɓe kaɗan shima da ɗaukar bowl ɗin naman ya buɗe, guda ya cira da ɗan tsinken da aka sako a ciki ya kai baki yana lumshe ido. Hakan ya saka Lulu zuba masa nata idanun batare da ta lura da abinda take yin ba har ya buɗe nasa da suka wani ɗan shanye tare da yin luww kamar mai jin barci. (He looks so handsome) zuciyarta ta ayyana mata. A fili kam sai tai saurin fara janye nata tana wani taɓe baki. A kasalance shima ya janye nasan yana jan ajiyar zuciya.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣5️⃣
.......Sai kawai ya miƙe zuwa jikin window ya ƙurama waje idanu yana kallon shuke-shuken fruits da ganyayyakinsu ke sake ƙawata ƙamshin wajen. Da ƙyar ya iya samu ya dai-daita kansa a wajen har Ummita ta shigo ɗauke da zam-zam mai haɗe da zuma a ɗan wani kofi da ƙaramin spoon. Tana ajiyewa bata zauna ba ta fice. Nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauke a karo na babu adadi da takowa ya dawo gaban gadon, komawa yay ya zauna a inda ya tashi tare da amsar yaron data janye a jikinta tana gyara riga. Amsarshi yayi yana goge masa baki, ita kuma sai ta miƙe masa ɗan cup ɗin. Cikin ɗan tura baki a ranta tana faɗin (Kaima ka ɗan ɗana wahalar da nake ci a kansa)
A mamakinta babu musu ya amsa. Kamar kuma dama can wanda ya saba da rainon cikin nutsuwarsa ya ɗibo ruwan zam-zam ɗin mai haɗe da zuma ya zubama yaron a baki kaɗan sai gashi yana ɗan motsa bakin da yamutsa fuska. Hakkanne ya saka Smart sakin murmushi har ya ɗago ya kalli Lulu da itama dai kallon nasu take yi. Kauda idanun nata tai ta maida kan bowl ɗin namanta ta fara ci. Cikin ɗage gira ya ce, “Wannan dai ƙwaɗayinki ne ya gado Madam”.
Da sauri ta ce, “Wa ɗin? ALLAH ya sawwaka mi muka haɗa da shi da zai gado ni, haɗuwa a duniya rabuwa a cikinta”. Sosai maganar tata ta bashi dariya, amma sai baiyi ba yay murmushi kaɗan yana girgiza kansa. Ganin yasha sosai ya goge masa baki ya gyara masa kwanciya a ɗan gadonsa. Lulu ya kama tana kallonsu, amma yana juyowa ta kauda kanta gefe. Kusa da ita ya koma ya zauna gaf, batare da yayi magana ba ya amshi tsinken da take cin naman ya tsira shima ya kai bakinsa, sake tsiro wani ya kai mata baki, idanunta ta zuba
Book Chapters
Chapter 12
Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500