ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki jagora a gidan naki, itama d'auka tayi tabishi, yasa mukulli ya bud'e k'ofar falon, wani k'amshi ya daki hancinsu, suka ajiye kayan, ya ce, "zauna na k'arasa d'akkowa.
Sopy tabi falon da kallo tana jinjina kai, lallai iyayenta sunyi k'ok'ari, falon yayi k'yau, komai acikinsa jaa da farine, kujerune set guda sai santa rok (center rug) atsakkiya kujerun shima jaa anmasa kwalliya da fararen fula woyi, sai tebir a tsakkiyarsa shima dai tare suke da kujerun, falon zagaye yake da labulaye suma jaa da fari, sai tv sitan shima irin kujerun an d'ora filasma k'arama akai ta dai dai talaka.
Takai dubanta a dani (dinning) shima ank'awatashi da kujeru da firij, idan bata mantaba ta dad'e da ganin kujerun dani d'innan a gidan aunty Nafisa an lillib'esu da wani k'yalle ashe natane, hawaye suka gangaro a kumatunta na dad'i, bata san da bakin da zata godema iyayentaba da yayyenta musamman ma uncle kabeer dan yafi kowa taka rawar gani acikin rayuwarta, dama yayyenta sunsha gaya mata saboda aurenta suke sana'a tabbas yau ta shaida haka.
Uncle G! ya kamata ya zaunar saman kujera, dan tun d'azu yana kallonta, yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta, ya ce, "Safiyya ba kuka zakiyi ba addu'a yakamata kiyima 'yan uwanki domin sun taka rawar gani a kanki, ko mak'iyi yaga kayannan saiya jin jina musa, hannunta yakama yanufi kichin da'ita aii sai sukaga abin kallo yana kichin, lallai kicin d'innan ya tsaru nanama komai jaa aka tsara, ya ce, "ga sito d'inki ya nuna mata wata 'yar k'ofa, koda yake zomuje ki gani, suna bud'ewa kayan abinci suka bayyana uncle G! yasaki baki yana kallon ikon ALLAH harda su drinks yasan wannan tabas aikin uncle kabeer ne, uncle G ya rungume sopy cikin farinciki, ya ce sopy narasa bakin maga wlhy saidai muyita yima su baba addu'ar gamawa lfy, zomuje ki ida ganin ko ina.
Bedroom d'inta ya kai ta, sannan sukaje nasa nanma ya had'u saidai nasa komai ruwan ganyene (green) kenan, ya zaunar da ita a bakin gadoyana fad'in Safiyya kinga gidanki sai dai k'aramine dan na talakane, a hakama nakai tsawon shekara hud'u ina ginashi, dan cikin albashi ake cire wani abu ad'anyi aikin, amma mun godema ALLAH da baiwar da yayamana ta rai da lfy, ahakama munfi wasu, ina fata zakizo mu had'a kai mu zauna kfy, mukuma yarda da k'addara aduk lokacin data riskemu, muyi hak'uri a lokacin da babu ta waywayemu, muzama masu wadatar zuci akan abinda ALLAH ya azurtamu dashi, mukuma gode masa.
Arzik'i bashine rayuwa ba dan da wani arzik'in gara dawwama a talauci, nayi alk'awarin zan rik'eki amana, sannan ina rok'onki damuyi hak'uri da juna a yayin da muka samu sab'ani, mukuma fahimci juna alokacin da wani abu yashige mana duhu, na tabbata wannan zai taimaka mana wajen zaman aure.
Sopy ta ce, "insha ALLAHU zaka sameni mai biyayya a gareka.
Ya ce, "ALHAMDULILLAH.
yanzu tashi muje na rakaki d'akinki kid'an watsa ruwa ko?.
Ta ce, "to......................โœ๐Ÿป




๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 3~November~2016



๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท



NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž



๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ6โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.........Har d'akinta yarakata, bayan fitarsa takuma k'arewa d'akin kallo, sannan tashiga wanka, tai murmushi dan ganin jininta yazo, lallai tayi farinci da faruwar hakan, tayi wanka tafito sai dai matsalarta d'aya batada always to yaya kenan zatayi?, tasan daga nan zuwa dare dole ta nemi mafita, inko ba hakaba zai rink'a b'ata mata jikine, tana nan zaune tana sak'a wasik'ar jakai saitaji sallama, ta fito da sauri tana amsawa, saitaga wata 'yar matsakaiciyar budurwace hannunta rik'e da kwando.
"Yarinyar ta gaidata."
"Ta amsa cikin sakin fuska".
Yarinyar ta mik'o mata kwandon dake d'auke da kuloli ta ce, "gashi inji aunty Asiya.
Sopy ta ce, "aunty Asiya kuma?, wace aunty Asiya nasani anan anguwar?.
Uncle G yafito sanye da jallabiya fara, yarinyar ta gaidashi, saida ya amsa sannan ya ce, "Asiya matar kabeer fa, aii bamuda nisa gidansu na nan k'asanmu.
"Lah aii ban saniba".
Ya ce, "na mantane nagaya miki, ni bari naje masallaci lokaci yana k'ara k'urewa, ta ce, "adawo lfy, yafita yana fad'in ALLAH yasa.
Yana fita Sopy ta Cema yarinyar ya sunanki?.
Ta ce, "sunana fatima amma anace mini ummy, nice name sopy tafad'a.
To ummy dan ALLAH ina zaki sayo mini always ?, ummy ta ce, "aii akwai shago nan bayanku kawo na siyo miki.
Yauwa ngd ummy 'yar albarka, taje ta d'akko mata d'ari biyar tabata ta fad'a mata irin wanda takeso.
Babu dad'ewa uncle G yadawo, sannan sopy tana kicin tana d'auraye inda zasuci abinci.
A falo yazauna ya kunna tv dan anhad'a komai, wannan duk aikin uncle kabeer ne, ummy tayi sallama ta shigo, ya ce, "O, baki tafiba?, ta ce, "e, aunty ce ta aikeni.
Okey to kawo, ta mik'a masa ledar da canji ta ce, "bari natafi zanje islamiyyane, ya ce, "to ki gaishesu kice mun gode sosai ya mik'a mata naira d'ari, ta ce, "A'a, ngd, ya ce, "karb'i aii ni nabaki, ta amsa tana godiya ta tafi.
Ya bud'e ledar dan son ganin minene aciki, ya ce, "tofa, abinda kuma yafaru kenan, ya ajiye yana fad'in an rusa mini show d'ina kenan.
Sopy tafito da kayan filet, ta dire a saman tebirin dake tsakkiyar falon ta ce, "ga abinci ko akai dinning?, ya sakko k'asa yana fad'in aii ak'asama zanci, dan nagaji dayawa, saida tafara zuba masa abinci ya ce, "af, nama manta yarinyar ta ce, "tawuce gama sak'onki".
Sopy ta ce, "to, ngd".
Tagama zuba masa farar shinkafar da miya da lemon kwakwa, sai salat.
ya ce, "kefa?, ta ce, "sai anjima, harararta yayi, ya ce, "sa hannu muci kikuma cire wannan hijjab d'in kisha iska.
Ganin ya d'an d'aure fuska, yasata bin umarninsa, ta cire hijjabin tazauna sunacin abincin, dukda tsakura takeyi kuma a kunyace takeci, bai kuma ce mata komaiba yacigaba da kallonsa yana cin abinci.

โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†
Da daddare ya tarar da ita a d'akinta tagama shirin barci harma ta kwanta, ya ce, "taso muyi sallah, saida tayi k'asa da kai sannan ta ce, "ina fashin sallah.
Ya ce, "okey, dama ya tanbayane dan ya tabbatar.
A zatonta d'akinsa zai kwana amma saitaga ya hawo gadon ya kwanta kusada ita, ya jawota jikinsa ya rungume, to ba yadda zatayi tunda babu damar korarsa, saita maida kanta ta kwantar akan k'irjinsa ta hau barci.

โ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™ก
Rayuwa mai dad'i akeyi agidan uncle G dukda har yanzu babu abinda yashiga tsakaninsu, amma suna mutunta juna kuma uncle G yana nuna mata soyayya, danma kunyarsa datakeji tana sashi k'in yimata wasu abubuwan.
Kullum aunty Asiya saita turo mata kalar girkin daya dace tayi masa ta whatsapp, dan haka take girki mai dad'i da gamsarwa, ta kuma gyare gidan tsaf, uncle G yana jin dad'i dan yanason mutum mai tsafta, kullum sai tayi bak'i 'yan anguwar suna shigowa ganin d'aki da kuma amaryar kanta, kunsan amarya da farinjini, har yara da 'yammata ba a barsu abayaba, kuma duk wanda yazo saita kulla masa cin cin da dubulan, dan sopy bata da rowa, abokansama suna zuwa wasu harda matansu, su aunty Nafisane dai har yanzu babu wanda yazo acikinsu, har aunty Asiya datake kusa, garama uncle kabeer yazo sau d'aya shima da daddarene, kuma bai dad'eba yatafi...............โœ๐Ÿป



๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 3~November~2016



๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท



NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž



๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ7โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

............yau kwananta biyu da fara sallah, amma tak'i nunawa uncle G! hakan, batayin sallah saiya fita, kokuma ta kulle d'akin sannan tayi, to gashi gobe zai koma aiki, dan hutunsa ya k'are, suna zaune a falo suna kallon labarai sai sukaji ana kwan kwasa gida, uncle G! ya kalli agogon dake manne a bangon falon, ya ce, "to waye da darennan?, sopy ta ce, "bari naje na duba.
Ya ce, "A'a yizamanki barinaje.
Ta ce, "to.
Yaje ya bud'e wasu 'yammatane su biyu suka gaisheshi, ya amsa fuskarsa babu walwala, dan kunsan uncle G! A gaban 'yammata baya sakin fusaka, ya ce, "yaya dai?, ganin yanda ya had'e fuska sai suka daburce d'aya ta ce, "dama yarinyace tafita gida tun d'azu shine muke tunanin kota zo nan?.
Ya ce, "A'a, babu kowa nan gidan.
Sukace to mun gode saida safe.
ALLAH yakaimu yafad'a yamaida get d'in ya rufe, ya koma cikin gida, sopy ta ce, " Suwaye? ALLAH yasa dai lafiya?.
Uncle G! yazauna yana fad'in wasu 'yammatane wai yarinya suke nema, yarinya kuma anan gidan?, ya ce, "haka dai sukace.
Sopy ta ce, "sudai tasuce ta kawosu zasuce, nima na fahimci haka aii.
Wayarsa ta shiga k'ara alamar kira, ya d'auka, cikin zolaya ya ce, "surikina yagarinne?
Uncle kabeer ya ce, "haba malam daka d'aukeni sikin aii saika kwantar da murya.
Uncle G! yay dariya, aii dan baka kusane amma atsugunne nake yanzuma.
dariya sukayi gaba d'aya, uncle kabeer ya ce, "sonake nace maka yakamata gobe muje wajennan damukai magana ranar.
okey to babu damuwa saimuje, ina uwar biyu?, uncle G ya tanbaya.
Wlhy kaganta nan tana tayimin shagwab'a kasan mai ciki sai ahankali, ina my sweet Sopy?.
tana nan lfy gata nan kusadani.
To kagaishemin da ita saida safe, zataji ALLAH ya kaimu goben lfy.
Bayan ya ajiye wayar ya kalli sopy, kabeer yana gaisheki, ta turo baki cikin shagwab'a ta ce, "shine baice abaniba.
Yanda tayi maganar saita burgeshi, ya ce, "to bari nakira shi saiku gaisa, karkiyi kuka 'yar gatan uncle kabeer, zoki karb'a wayan.
Azatonta da gsk yakeyi, saita tashi taje wajensa, tana k'ok'arin durk'usawa k'asa, ya jawota jikinsa, yana fad'in kinga wajen zamanki nan.
Ta ce, "to kira mini uncle d'in mu gaisa.
Yaja hancinta aikece uncle d'in, bawani kiranshi dazanyi, tashima na aikeki, ta tashi tsaye, saida yayi mata wani shu'umin kallo sannan ya ce, "yauwa je d'akina ki d'akko min ALKUR' ANI yana nan gefen gado.
sofy ta ce, "to, shaf tamanta shirinta, bata kuma gane manufarsa ba, tanufi d'akinsa ta d'akko Alkur'ani, ya karb'a yana wani shu'umin murmushi mai kamada na mugunta, saman tebir ya ajiye Alkur'anin ya ce, "Sopy dama kin fara sallah?.
Gabanta ne ya fad'i rasss dan tanbayar tazo mata a bazata, ta daure ta ce, "e, ya kwanta a kujerar yana wata 'yar dariya ta mugunta.
Sopy ta ce, "mugu d'an masa.
Daga nan kallo suka cigaba dayi, saidai kallo d'aya zakayima sopy kagane tana cikin wani hali mai kamada tsoro.
K'arfe goma dai dai ya mik'e yana fad'in tashi muje mu kwanta dare yayi, Sopy ta mik'e jiki a sanyaye tayi gaba yabita abaya yana mata gwalo๐Ÿ˜œ.
Bayan sun shiga d'akinta ya ce, "ki sameni a d'akina yau acan zamu kwana, yafice abinsa batareda yajira amsartaba , tabishi da kallo kamar zata fasa ihu.
Ba yanda zatayi dole tayi sabon wanka tayi shirin barci, tad'an dad'e tana sak'a wasik'ar jakai, zuciyarta cike da tsoro da fargaba, ya lek'o ya ce, "wai har yanzu baki gamabane?, ta mik'e kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Ad'akinsa ya ce, "tabiya shi suyi sallah, raka'a hud'u sukayi yayta kwararo musu addu'oi, iyakar sopy ta rink'a cewa amin, ya dafa kanta yay addu'a harda 'yan kwallansa, a zuciyar sopy ta ce, "namiji da kuka?.
Bayan sun idar ta linke sallayar, ya canja jallabiyarsa zuwa kayan bari, yajuyo yana kallonta bazaki cire hijjabin bane?, ko bakijin zafi.
Ta d'aga kai alamar e, yay d'an murmushi a zuciyarsa ya ce, "duk dai wayon amrya sai ansha manta, yak'araso ya zauna kusada ita yakama hijjabin ya cire, tad'an takure jikinta kamar maijin sanyi.
Ya ce, "inga fuskarki kamar wani abu a saman idonki, ta d'ago fuska batare da wani tunaniba, ya kama fuskarta da hannu biyu yakai bakinsa kamar zai hure mata abun, bata ankaraba taji bakinsa a cikin nata, kissing d'inta yakeyi cikin kwarewa, ahankali ya kwantar da ita saman gadon, dahaka hannuwansa suka fara shiga inda baitab'a zuwaba, Sopy tafara hawaye, nidai ganin uncle G! yau dgske yake, yasa nayo waje abina, dan kar kallon kurullar yayi yawa๐Ÿ™ˆ๐Ÿ˜œ..................โœ๐Ÿป



๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016



๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท



NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž




๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ8โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

...........Safiyya yau anzama cikakkun mata, saidai tasha wahala sosai sai kuka takeyi, uncle G ya rugumeta yana lallashi da sa mata albarka, ya kwantar da'ita ahankali ya ce, "bari nayi wanka sai kema kiyi.
Bayi yashiga dominyin wanka zuciyarsa cike da farinciki irin wanda baitab'a shigaba a rayuwarsa, lallai aure rahamane kuma ni'ima ne.
Sopy taja bargo ta kudundune danjin sanyi yana shigarta, wani wahalallen barci ya d'auketa, uncle G! yafito yana fad'in my sopy tashi kiyi wankan, ganin tayi shiru saiya hawo gadon, ya yaye bargon saiyaji jikinta da zafi rau, gashi dukta jik'a filon da hawe da zufa, yad'agota zuwa jikinsa yana fad'in sorry Safiyyana, ALLAH yay miki albarka kinji, ya azurtamu da zuri'a tagari, zanin gadon yasa ya goge mata fuskarta, ya kwantar da'ita, yanufi kicin.
Shayi ya had'o mata mai kauri, yatada ita zaune, ta ce, "itafa ta k'oshi, ya ce, "daure kisha kinji, saikisha magani mukwanta, lallab'ata yaytayi tad'ansha kad'an, ya bata magungunan zazzab'i, sannan ya rungume matarsa suka shiga barci mai dad'i.

โ˜†โ™กโ˜†โ™กโ˜†โ™กโ˜†โ™กโ˜†โ™ก
Bai san yayi b'arnaba saida safe, dan sun makara, yatada ita dan tayi wanka tay sallah, amma takasa tafiya, tanayin taku d'aya taji wani azababben zafi ya ratsa har kwakwalwarta, cikin shagwab'a ta ce, "woyyo ALLAH na inna.
Uncle G ya k'araso da sauri ya tallafota zuwa jikinsa ya ce, "yaya dai?, cikin shagwab'a ta ce, "zafi.
D'aukarta yayi cak yakai bayi, ruwan zafi ya had'a yaymata gashi, tanata zuba masa shagwab'a, ya taimaka mata tayi wankan tsarki, sannan ya nad'ota a tawul kamar wata jaririya.
Tana idar da sallah ta kwanta akan sallayar dan barci takeji, uncle G! yashigo da tire a hannu ya dire agabanta, sopyna tashi kiyi break saiki kwanta gaba d'aya, da k'yar ya lallab'ata taci soyayyan kwan da shayi, bai takurataba dan lallab'ata yakeyi, bayan tagama ya kwashe kayan yazo ya canja zanin gadon, sannan ya d'auketa ya maidata saman gadon taci gaba da barcinta, shima ya kwanta yarungume kayarsa suka lula duniyar barci.

Sai k'arfe d'aya da wani abu suka tashi, sopy ce tafara tashi, ta lallab'a ahankali ta gudu d'akinta, uncle G! yana kallonta yay murmushi kawai dan ganin yanda take sand'a, shima tashi yayi yashiga wanka.
Itama sopy ad'akinta wankan tashiga, dan har yanzu jikinta ciwo yakeyi, tafito tayi kawlliya mai sauk'i tasaka doguwar riga ta atanfa, tana tsaye gaban madubi tana fesa turare uncle G! yashigo, ya rungumeta tabaya yana fad'in kingudo kin barni to gani na biyoki aii.
Tai kasa da kai dan kunya, ta ce, "ina kwana?, lafiya law sopyna, yaya kuka?, da kiransu inna da baba.
Hannu tasaka ta b'oye fuskarta๐Ÿ™ˆ, dan takula zolayarta yakeyi, ya ce, "bari naje massalaci nadawo
Ta ce, "to adawo lfy, karfa ki dafa komai zanzo mana da abinci, dan yau ranarkice Autar inna.
Ita dai murmushi kawai take, amma kunya ta hanat yin magana.

Babu dad'ewa yadawo musu da abinci, lokacin sopy ta gyare gidan ta bad'eshi da k'amshi, da kansa yarink'a bata abincin, ita kuma tana zuba masa shagwab'ar datake k'ara masa sonta.
uncle kabeer yakirashi ya ce, "subar tafiyar sai gobe.
aii dama surikina dole abarta sai goben, dan dama zankiraka, yau babu mai ganina a waje.
Kai mutumina saboda mi? Uncle kabeer ya tanbaya.
A'a, basai kajiba kaidai abar kaza cikin gashinta kawai goben ma had'u.
ALLAH yashiryaka youseef kazama marakunya yanzu.
Uncle G yay dariya, idan yatashi ya shiryamu tare nida kai, suka tuntsure da dariya kowa yakashe wayar.

Haka uncle G yacigaba da tarairayar sopy awannan rana, komai shi yake mata, sopy ta ce, "a zuciyar wato su maza abinda suke so kenan?.๐Ÿ˜œ....................โœ๐Ÿป





๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016




๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž




๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ9โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

................JAMA'A!!! yakamata mu way wayi fareeda amaryar Abdul๐Ÿ˜œ,
Saida na d'an lek'a saboda gudun jarabar ummar Abdul sannan nashiga, ba kowa atsakar gidan sai yara daketa wasa, ban kula kowa ba nashige abina, dan yaran gidan ba kunya suka cikaba, atsakar d'aki na tarar da fareeda tayi d'ai d'ai, sai dai kallo d'aya zaka mata kagano tana cikin damuwa, dan kuwa tarame tayi bak'ik'k'irin sai dogon hanci da idanuwa gwalo gwalo, sai ciki ritsitsi a gaba.
Ta tashi da sauri dan jin sallamata, tana ganina tasa kuka yauwa bily! wlhy nayi farincikin ganinki, dan ALLAH ki taimakeni wlhy Abdul zai kasheni a gidannan, ga kowa ya tsaneni bily! plx ki taimaka min.
Na zauna ina fad'in fareeda! wane irin taimako kikeso in miki, kindai san halin mijinki da surukarki.
Bily! wlhy idan baku taimakeniba kasheni zasuyi yanzu haka tun jiya cikina da bayana suke ciwo amma yak'i kaini asibiti, tunda akayi bikin Safiyya! al'amura suka k'ara lalacewa, ya ce, "yanda narabashi da Safiyya! to nima bazanyi farinciki ba a gidansa, ta rushe da kuka mai tsanani.
Kamar daga sama Abdul! yafad'o d'akin, yabini da kallon rainin hankali, wayke bily! kike kowa? Banace karna k'ara ganinki a gidannanba ne?.
Na ce, "haba Abdul, kaiwa "ALLAH DA MANZONSA", kabari na taimakawa fareeda! kaga batada lafiya, kasan kuwa mai ciki saida kula.
Harara ya watsa mini, cikin fushi ya ce, "wlhy idan baki bar gidannanba zan karya miki k'afar dama.
Na zaro ido waje๐Ÿ˜ณ, A'a, Abdul name dazan zauna ka karya min k'afar dama, ka cuci mijina!!, kaga tafiyata, fareeda! ALLAH yabaki lafiya, nai waje.
Abdul! yaja tsaki yana fad'in bak'ar banza kawai, na ce, "oho nagodema "ALLAH" dayayini haka, aii fari bashine k'yauba.
Ina fita yashiga jibgar fareeda! Kamar ALLAH ya aikoshi, dan ubanki banace karna sake ganin wani naki a gidannanba, koda kud'in ubanki muka gina gidan?, dukanta yake kamar yasamu jaka, itako sai ihu takeyi, nanko jini yafara ambaliya, yau dai ansamu ummarsa tashigo wajen, ta ce, "Abdul mitayi makane?.
Umma kibari na kashe shegiyarnan tunda iyayenta ma ba sonta sukeyiba, dak'yar umma ta karb'eta.
Ina tsaye a k'ofar gida tausayin fareeda! duk ya cika min ciki, sainaga an kwasota kamar kayan wanki jini nata kwarara, ko numfashin kirki batayi.
Mai adai daita suka tare, suka tafi asibiti.
To fareeda tsuntsun d'ai da yaja ruwa shi ruwa kan doka,, kowa kuma yataka rawar wani tofa yarasa filin taka tasa,, ALLAH dai ya shirya.


โ˜† โ˜† โ˜† โ˜† โ˜† โ˜† โ˜† โ˜† โ˜† โ˜†
Agidan uncle G! Kam Sopy sai shan tarairaya take, yanzuma suna falo zaune suna hira, kan sopy yana saman cinyar uncle G!, hannunsa na shafa gyararren gashinta daketa tashin k'amshi.
Cikin murya mai dad'i da taushi ta ce, "uncle G!!, ya ce, "Na'am Sopyna ya akayi?, tai shiru dan tana jin shakkar fad'ar abinda ke ranta, yad'an lek'a fuskarta ya ce, "miye damuwarki amaryata?.
Tasa hannu tarufe fuska dan jin kunya, yay 'yar dariya sopyna ai kunya ta k'are kuma, yanzu an wuce wajen, dan Safiyya! tazama youseef!, youseef! yazama safiyya! koba hakaba?.
Ta ce, "hakane"
Ya ce, "ato.
Fad'imin kome kikeso indai baifi k'arfinaba zan mikishi.
Ta ce, "komiye?.
Ya ce, "e.
Dama maganar komawata makarntane dan ALLAH yaushe zan koma, kaga anata wuceni a karatu.
Sai da yad'an murmusa sannan ya ce, "to, kibari saikin warke, saiki koma, tunda nima jibi zan koma aiki, hutuna ya k'are.
Saida ta shagwb'e murya sannan ta ce, "ALLAH nifa lfy ta k'alau.
Kai sopyna fad'i gsky dai, kecefa d'azu kikace min jikinki duk ciwo yakeyi harda kuka kuma.
hannu tasa ta rufe fuska tana dariya, ya ce, "ato, kedai kika fad'a da kanki, dan haka kibari sai nestweek sannan mun k'ara shan amarci saiki koma.
b'oye fuskarta tayi acinyarsa, tana fad'in kai uncle ALLAH kana bani kunya.
Ya d'ago duskarta yana murmushi to bani kunyata sopyna.
Ta ce, "to, bayanzuba.
Ya ce, "nikam yanzu nakeso, yay kissing d'in goshinta, ta runtse ido kam dan kuwa sumbar ta shigeta.
Ya ce, "sopy matsoraciya mai kuka, dan ALLAH uncle kayi hakuri karka min da zafi, wayyo innata baba kazo ka taimakeni, yafad'a yana kwaikwayon muryarta.
D'aki ta nufa da gudu, dan taga zolayar tayi yawa.
Koda sukazo wajen kwanciya saitaita d'ari d'ari dashi, dan tsoron kar abinda yafaru jiya yasake faruwa, uncle G! ya rungumeta yana fad'in kwantar da hankalinki sopyna babu abinda zan miki barci zamuyi, ita dai tayi shiru amma zuciyarta cike da tsoro, ya cire mata rigar barcin dake jikinta way haka yakeso sukwana.
Bargo yaja ya lullub'esu ya cika hannuwa da๐Ÿ™ˆkundai gane, sukayi shiga barci mai dad'i...................โœ๐Ÿป



Assalamu alaikum, ina mik'o d'unbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke, da godiya mai tarin yawa, ngd da bibiyar books d'ina da kuke yi, harma wad'an da suka fara karantawa yanzu, luv u oll๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ‘๐Ÿป.




๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’žU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž...โœ๐Ÿป




๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016




๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž



๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ4โƒฃ0โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.............Yau tsawon kwanan fareeda uku a asibiti, ta haihu amma d'an baizo da raiba, kuma tun randa su umma suka kaita asibitin basu sake way wayarta ba, yau kuma tana tashi tayi gamo da takarda saki uku a gefen gadonta, kuka take rurus tana dana sanin hali irin nata, yau ga wanda ta fifita akan iyayenta ya gujeta, ta raba zuminci mai dank'o da kusancin dake tsakaninta da aminiyarta saboda Abdul, ta cutarda masoyiyarta saboda Abdul, ta yaudari abar k'aunarta saboda Abdul, taci amanar aminiyarta saboda Abdul, amma yau yarasa abinda zai saka mata dashi sai saki uku, sakin wula k'anci da toxarci, itakam ta shiga uku yanzu wazata dosa, tasan daga iyayenta har yayyenta babu mai saurarenta, tasan babu wadda suka tsana kamar ita ahalin yanzu, takuma rushewa da kuka mai tsuma rai, wata sister tashigo tana fad'in baiwar ALLAH lfy kiketa kuka haka?.
Fareeda ta ce, "babu komai.
Okey sister tafad'a, dama an sallamekine, dan wani mutumi yazo yabiya kud'in.
Fareeda ta ce, "to ngd, ta had'a inata inata tabar asibitin, zuciyarta cike da bak'in ciki, dan bata san inda zata nufaba, tasan ko giyar wake tasha bazata fara zuwa gidansuba, Dan mahaifinta ya gindaya mata sharad'i akan zuwan irin wannan ranar, takuma amince saboda lokacin giyar son Abdul tana kwasarta, lokacin da idanunta suka rufe ta manta da zuwan irin wannan rana, yauga ranar tazo mata batareda taci ribar abinda ta shukaba, saima asarori data tafka marasa adadi, wanda bazasu lussafuba, haka tacigaba da tafiya tana zubar da hawaye batarda tasan inda ta dosaba, ga jiri na d'ibarta saboda yunwa dan ta manta rabonta da cin abinci, ji kake wani kuwwwwwwww kacammmmm!!!!!, wani mai mota ya b'arar da ita a titin, da sauri mai motar yafito yana salati, kan kace mi mutane sun fara taruwa a wajen, mai motar ya ce, "a taimaka masa yasakata a mota, asibiti ya nufa da'ita cikin hanzari.


โ™กยคยคยคยคยคโ™กยคยคยคยคยคโ™กยคยคยคยคยคยคยคโ™ก
Sopy tanata safa da marwa dan tun d'azu take kiran uncle G! Yak'i ya d'aga, ta kira uncle kabeer ya ce, "basa tare, aii saita k'ara rud'ewa, can taji ana kwan kwasa k'ofa tatafi da sauri ta bud'e, saitaga

Please Login or Register in order to submit comment