You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kankanar?? Sopy tamik'e tana fad'in wlhy baba idan banbama inna kankanar nanba bazata barni nasha iskaba.
" inna tarik'e baki wayni yaushe safiyya ta rainani agidannan ne malam??? Malam ibrahim ya murmusa bawani raini,, aii ko kurama da 'ya'yanta take wasa a dawa,, itama tana tsokanarkine kaway.
Inna tace" kaidai kana goya mata baya ne kaway,, safiyya tai dariya baba kabarta ai kwanannan zan tafiyata gidan aunty Nafisa hutu saita dad'e bata ganniba,, damma uncle kabeer bashida mata da gidansa zan koma.........yaron dayay sallama yasa sopy yin shiru.
"" kai shamsu lfy ??sopy ta tanbaya,, shamsu yace wanine yace kizo awaje,, wani kuma?? Waye wani?? bashida suna ne??? Shamsu yace nibansan sunansaba amma agidan Alhaji Abubakar mai fata yake.
Baba yace"kaga yaro yitafiyar ka,, gata nan zuwa.
Sopy ta turo baki wlhy nikam baba banason fita tad'innan yau,, baba yace"" tobake kika zab'i mijinkiba da kanki maza tashi kije,, amma kar a zauna wannan doguwar hirar,, tun ana fad'ar gsky har akoma k'arya.
Sopy tace"to baba bari nak'are shan kankanata.
A'a tashikije idan kin dawo saikisha.
Dole tamik'e tatafi badan tasoba.
Inna ta kalli baba,, malam wlhy nidai dan kawai safiyya tanason yaron nan amma nikam bai kwanta min araiba,, banaso akai safiyya gidan nan mai tarin mata da 'ya'ya.
Baba yaja ajiyar zuciya,, hajara babu abinda zamu iyayi face addu'a,, dan neman zab'in ALLAH, ALLAH yazab'a mana abinda yafi alkairi.
"To amin malam"
Awaje kuwa sopy tana fita saita tararda Abdul tare da fareeda suna hira,, lamarin yayi matuk'ar bawa sopy mamaki,, amma saita danne tak'arada wajensu da sallama.
Atare suka amsa mata,, takalli fareeda,, ke sister amma ke 'yar rainin hankalice yanzu nan dama baki tafiba???? Fareeda tace" kibari kawai 'yar uwa wlhy mamace ta kwafsa min tahanani zuwa,, fushi nakeyi shiyyasa kikaga ban shigoba,, yanzuma nazo na ari wayan Abdul ne nakira aunty sadiya nafad'a mata abinda yahanani zuwa.
Sopy taja ajiyar zuciya mai k'arfi,, Abdul yay saurin kallonta gimbiyata miye matsalarki???? Babu komai habibina ykk?? Lfy lau nake gimbiyata.
Nan dai suka dasa hira harda fareeda,, dan tak'i tafiya.
Hakan baisa sopy ta zargi komai ba, dan zuciyarta a tsarkake take,, ta yarda da fareeda da Abdul, d'ari bisa d'ari.
Washe gari saiga aunty sadiya tazo gidansu fareeda,, nanta wuni,, saida mama tashiga sallah sannan aunty sadiya tabama fareeda abinda takawo mata,, tai mata bayani dalla dalla sai dai nima bansan mita bataba masu karatu dan sunshige k'uryar d'akine.
" kukasance tare dani danjin yanda zata kasance.....................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 6~October ~2016
π·πΉNI DA K'AWATAπΉπ·
NA BILKISA IBRAHIMπ
πΆπΈ6β£πΈπΆ
................Yaud'in takasance asabar babu makaranta su sopy suna gida,, fareeda ce tadoso gidansu sopy hannunta rik'e da filet a rufe tashigo da sallama,, inna dake d'aki ta amsa mata,, tak'arasa d'akin inna ta gaisheta inna tace" yasu ladidin?? Lfy lao inna tamace na gaisheki wai anjima zata shigo kuje asibitin dubiyar nan.
"" A toshikenan babu damuwa saita zod'in,, kishiga safiyyan tana nan a d'akinta tana shirin tfy gidan hauwa'u,, nazatama tare zaku??? Eh dama tare zamuje to sai zanje gidan aunty sadiya nakai mata sak'o kinsan ita kuma bata zuwa gidan,, amma inna kai sak'on zan isketa acan d'in.
Ato shikenan ma,, itama d'in shirmene yake damunta kawai,, sadiya ba innarta bace??
Fareeda tayi murmushi bahaka bane inna laifin aunty sadiyarne aii,, tafad'a tana mik'ewa.
D'akin sopy ta shiga, sopy na zaune tana kwalliya fareeda ta zauna kusada ita 'yammata wannan irin kwalliya haka' saikace maishirin zuwa gasa??? Sopy ta harareta ke bakiga takibane??? Nitunda nake dake ma bantab'a ganin kinyi irin wannan gayunba wlhy????
"Fareeda ta tura mata filet d'in datazo dashi, tana fad'in shike nan kin rama.
Sopy ta bud'e filet d'in tana fad'in mikika kawo min??
Wlhy waynar filawace nayi dasafe,, to naga baki shigoba shiyyasa nabiyoki da ita.
Sopy tace" kin k'yauta kuwa dama tund'azu nakasa karyawa.
" saboda mi??
Wlhy bako mai kawai dai yaunatashi duk jikina babu dad'i ga gabana sai fad'uwa yakeyi. Fareeda tace tofa lfy dai""
Wlhy nima bansaniba 'yar uwa.
To ALLAH yatabbatar mana da alkairinsa,,, fareeda tafad'a.
"" sopy tace'' amin dai.
Tare suka fito kowacce tahau mota zuwa inda zata.
hauwa'u tatari 'yar uwarta da murana,, sopy tace" aunty ina Arfat yake?? Yana wajen kareema yarinyar makwaftan mu d'azunnan tazo ta d'aukeshi suka tafi.
" kai aunty wanan d'an yaron kika bari aka fita dashi da wannan safiyar?? To yazanyi auta yariga yasaba dasu,, tashigo kawo min abune yamak'ale mata. Toni dai ki aika akawo min yarona! Karki damu zata kawoshi,, wai yana ganki ke kad'ai ina K'AWAR taki fareeda???
"Itama tana nan zuwa taje gidan sadiyane takai sak'o zuwa anjima zata zo.
To shikenan ALLAH yakawo ta nitashima ki d'ora mana abincin rana,, dama d'inki zanyi.
Kefa kinji matsalarki mutum baya zuwa gidanki ya huta dayazo saikin manna masa aiki, tafad'a tana kumbura baki.
Aunty hauwa'u tace" kekuma gashi baki son aiki ko?? Haka zamu kaiwa Abdul d'in ke,, inma zaki dage kidage wannan gidan nasu mai tarin 'ya'ya da mata,, dan agidan za'a ajiyeki tunda dukkan matan yayyensa anan suke zaune.
Sopy ta tashi daga kwanciyar datayi,, to aishi yace" ba anan zamu zaunaba zai kama mana haya.
Aunty hauwa'u ta tab'e baki to ALLAH yasa hakane???
"Sopy tamik'e tana fad'in hakanema.
Miza'a dafa?? Aii inaga tuwon shinkafa za'ayi. Sopy tace" kai kukam kuda inna bakuda matsalar data wuce ta tuwo?? Aunty hauwa'u tai dariya,, toshi abban Arfat yakeson ci.
Nikam gsky bazanci tuwo daranaba,, zan dafa mana wani abu nida fareeda kafin tazo! Duk yanda kikayi cewar aunty hauwa'u.
Fareeda kam ta isa gidan aunty sadiya,, sadiya tabita da kallo lallai fareeda wannan irin kwalliya haka??? Duk ta tarar Abdul d'ince??? Fareeda tayi dariya auty sadiya ya rankine,?? kefa kikace na cake sosai.
" sadiya tace" gsk yane d'iyata, suka tafa nuna dariya.
Fareeda tace" yaya dai kin kammala girkin??
Aii komai ya kammala yanzu Abdul kawai zamu jira.
Fareeda tai wani ihu ALLAH yabar minke aunty na,, kina cikin aikina.
Sadiya tai dariya ALLAH yashir yaki fareeda,, yanzu dai ki kirashi dan muji yaushe zai iso??
"" to auntyna, fareeda takira Abdul yacemata aii gama shinan ahanyar zuwa,, tak'ara yimasa kwatancen layin?? Fareeda takuma yimasa kwatance sannan ta kashe wayar.
Sopy tagama abinci tazauna kusada aunty hauwa'u tana fad'in wash ALLAH yaudai saina sha maganin gajiya zan iya barci.
Aunty ta harareta way safiyya mikike son zamane?? Da dai keba raguwa bace wlhy.
Sopy tai dariya dama can dan ban gama sanin ciwon kaina baneba,, amma yanzu ina.
"" aunty tace" zaki gaya musu yarinya.
Kareema tai sallama hannunta d'auke da Arfat,, sopy ta karb'eshi da sauri tana fad'in oyoyo my son! Tai kissing d'in kumatunsa.
"" kareema ta gaisheta,, aunty hauwa'u tace kareema sannun ki! Kareema tai dariya kai aunty saikace wani aiki,, umma cema tace nakawoshi yasha nono amma ba kuka yakeba.
Aunty hauwa'u tace" aii nagode wlhy badankeba da Arfat bazai barni nayi d'inkin nanba,,, nibansan yanda zanyiba idan kinyi aure??? Kareema tafita da gudu wai kunya takeji,, su sopy sukasaka dariya.......................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 7~October ~2016
π·πΉNI DA K'AWATA πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIMπ
πΆπΈ7β£πΈπΆ
..............Abdul ya iso yakira fareeda yay mata kwatancen inda yake,, suka aika wani yaro ya taho dashi zuwa k'ofar gidan,, amma sai yaja tunga yak'i shiga gidan,, fareeda tafito cikin dogon hijjab harda saka nik'af shi baima ganetaba dan haka yad'an ja gefe domin bata hanya,, tai masa sallama ya amsa yana binta da kallo,, tai dariya Abdul nicefa fareeda baka ganeniba ne??
Abdul yace"tofa wlhy ban ganekiba naga kinsaka nik'af nina zatama matar aurece!!
Fareeda tai dariya wlhy nice,, kashigo mana!!
A'a yaza ayi nashiga gidan mutane batareda izinin mai gidan ba???
Karka damu baya nan kuma yasan da zuwanka, kashigo kaway dan ALLAH.
sayda yay jim sannan yace" kina ganin babu matsala fareeda!
Babu wata matsala kamar yanda nagaya maka yasan da zuwanka,, kafinma katafi zai dawo gidan.
" to shike nan muje"
Har falon aunty sadiya suka kaishi yazauna yana shak'ar iskar fanka,, fareeda tafito zuwa tsakar gida ta iske aunty sadiya a kichin,, aunty sadiya tace" yaya dai yashigo?? Fareeda tace" yanama falonki zaune. Sukai dariya, sopy tacire nik'abi tad'au wata hoda a cikin leda ta kuma shafawa ta d' au kwalli tashafa,, aunty sadiya tamik'o mata turare ta fesa,, sannan tace" nayi my aunty??? Sadiya ta jinjina kai kinyi d'iyata komai yaji,, d'auki abinci kitafi nima zanzo mugaisa.
To shikenan auntyna fareeda tafad'a tana d'aukar tiren da kulolo ke kai.
Tai sallama ak'ofar palon cikin irin wata murya wadda itama batasan tana da itaba,, Abdul ya amsa tareda mik'ewa yatarota tiren hannunta ya karb'a yana fad'in wannan tire haka aii yayi miki nauyi dayawa.
Fareeda tazauna tana murmushi Abdul yad'ago suka had'a ido,, jiyay wani abu yashige jikinsa tundaga kansa har zuwa yatsun k'afarsa,, yarintse ido yana fad'in yasalam!!
Fareeda tace"Abdul yaya dai???
Yasakar mata tsadadden murmushi babu komai ina cikin wani irin farin cikine dana kasance dake.
"Fareeda tace" tofa Abdul nikuma?? Ko ka manta ba gimbiyarka bace sopy??
Abdul ya b'ata rai kinga idan muna magarmu ki daina sako mana wata sopy.
Fareeda tayi murmushi to nabari my love kayi hak'uri kabar b'ata ranka.
""Fareeda tazuba lemo akofi tabasa, yakarb'a yashanye,, takalleshi abincifa,, yay mata murmushi abani naci dama kamshinsa yanata cikamin hanci.
Fareeda tazuba masa farar shinkafa da miya yaci ya k'oshi suna hira,, saida yagama suka nutsu,, fareeda tace" Abdul yamaganar mune??? Abdul yay mata wani kallo na masoyi zuwa masoyiyarsa yace"ina saurarenki aii dama maganarce takawoni gareki my love!!
Fareeda tai wani murmushin mugunta tace" yayi k'yau,, tasowa tayi tadawo kujerar kusa dashi, takanne masa ido d'aya yay murmushi.
Shima yajuwyo sosai suna kallon juna,, suka k'urama juna ido kamar zasu cinye juna,, fareeda ce tafara janye nata idon tana murmushi,, cikin karsashi tace"my Abdul!!!!
Abdul ya amsa murya asark'e. Taja ajiyar zuciya Abdul ina matuk'ar k'aunarka fiye da mai buk'atar ruwa acikin sahara,, ina begenka fiyeda d'an da ke buk'atar nonon mahaifiyarsa alokacin dayake kuka, ina son kasancewa dakai tamkar bawan dake k'aunar bud'ar ido yagansa a aljanna, ina burin tara zuri'a dakai fiyeda talakan da ke burin tara dukiya, ina burin kozamu mutu mu mutu tare tamkar laila da majnun.
Hawaye suka zubo akuma tunta, Abdul yasa hannu yashare mata hawayen,, cikin sark'ewar murya yace" nima ina sonki fareeda ina k'aunarki, ina burin aurenki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAH kece uwar 'ya'yana.
Fareeda tad'ago kai dasauri tana kallonsa dan ALLAH Abdul da gsk kake???
Abdul yay murmushi da gsk nakeyi fareeda insha ALLAHU zaki zama matata.
" fareeda tai dariyar farin ciki,, tace" to amma yanzu yaza muyi da sopy???
Abdul yace" zan fad'a mata bana ra'ayinta yanzu, kece ra'ayina!!
A'a Abdul bahaka za'ayiba kawo kunnanka kaji!! Abdul yamik'awa fareeda kunnansa tafad'a masa,, yay wani murmushi yace" (nice idear) hakanma yayi,, nandai sukaita hira suna zazzagema juna sirrin zuciyarsu.
Agidan aunty hauwa'u kuwa sopy nacan tana jiran fareeda kad'an kad'an saitayi tsak'i, aunty hauwa'u tace auta way miye matsalarki ne???
Sopy tai d'an tsaki wlhy aunty haka kawai yau sai gabana ke fad'uwa tunda safe,, ga fareeda daga kai sak'o amma shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu.
Aunty hauwa'u tace" k'ila gosulo ne yarik'e ta,, zatazo tunda tace miki zatazo,, fad'uwar gaba kuma kita addu'a insha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi.
Sopy tace" to ALLAH ya tabbatar mana da alkairin.
Kubiyoni masu karatu, danjin yanda zata kasance..................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 8~October ~2016
π·πΉNI DA K'AWATA πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIMπ
πΆπΈ8β£πΈπΆ
................Sai wajan k'arfe 3:30 suka baro gidan aunty sadiya, Abdul ya kalli fareeda my love!! Yanzu "k" ina kika nufa??
Tai fari da idanu zanje wajen gimbiyarka ne a d'orayi, dan tana gidan aunty hauwa'u tana jirana.
Yad'an gintse fuska wato wannan gimbiyar bazai fita a bakinkiba ko??
Tai murmushi kayi hak'uri,, amma naga kaine kasaka mata gimbiyar aii?? Eh nine nasaka mata amma a da ba yanzuba,, yanzu kece gimbiyata! Dan haka karna sake jin wannan sunan wlhy natsaneshi.
Ta murmusa insha ALLAH wannan sunan ya goge har abada kamar yanda ALLAH ya shafe FIR'AUNA DA ABU LAHAB a doron k'asa.
"" Abdul yay murmushi harna k'ara sonki my love!!
Itama tai dariya to ALLAH yak'ara maka sona my love!! Amin Abdul yafad'a yana kallonta,, yacigaba toni bari nawuce gida dansu adam nacan suna jirana zamuje fagge.
Okey to saikun dawo,, nima bari nak'arasa dan nasan sopy nacan hankalinta atashe tana zura ido taga ta inda zan b'ullo.
Abdul yace" okey yazaro dubu d'aya yabata ga wannan kiyi k'ud'in mota,, tace to nagode,, saida yaga tashiga mota sannan yatafi shima.
Fareeda tanufi d'orayi cikin farinciki,, irin wanda daka ganta zaka shaida haka.
Ta isa gidan aunty hauwa'u sopy ta harareta aii dama kin koma saimu had'u agida.
Fareeda ta rungume sopy tana fad'in sorry my dear sister wlhy matsalar gosuloce kuma na tarar aunty sadiya bata nan nad'an dad'e kafin tadawo,, plz for giveme my sweet sister ayi hak'uri Amin azuri,, auntyna kisa baki a yafe min.
Aunty hauwa'u tayi dariya karki damu zaku daidaita nasani aii babu mai shiga tsakanin masoya.
" sopy ta tuntsire da dariya ALLAH dandai kawai na yarda dake,, amma da watace sainayi sati bamuyi magana ba.
Fareeda tace" to nagode my darling da kika yarda dani.
Sopy tace" to zauna nakawo miki abinci.
Nan sukaita hira abinsu,, sopy tace" way my sister miye yasaki farin cikine?? Naganki yau cikin irin wata walwala ta musamman; fareeda tayi dariya kibari kawai 'yar uwa wlhy ina cikin farin ciki mai tarin yawa. Tofa k'awata miye sirrin???
"Fareeda tayi dariya nima ban saniba amma ki tayani da addu'a.
Sopy ta dafata to ALLAH ya tabbatar mana da alkairi my dear sister, nikuma kinga yau sai gabana keta yawan fad'uwa bansan daliliba??
Kema aikairine my sopy.
Nan dai sukaita hirarsu har saida mijin aunty hauwa'u yadawo yana tsokanarsu,, my jidda yaukuma mafarkinmu tagwayen inna sukayine?? Aunty hauwa'u tayi dariya kamar dai hakane abban Arfat nima nayi mamakin ganinsu, dan yauma girkinsu aka kaimaka kasuwa.
Haba shiyyasa naji girkin bai dad'iba yafad'a cikin tsokana.
"" sopy tace haba na robar kaidai fad'i gsky nasan yau kaci girki ba irin namatar kaba, zauna kabamu labarin santin dakayi akasuwa.
Gaba d'aya suka kwashe da dariya hauwa'u tace" autafa ya isheku kubarmin miji yasha iskar duniya,, abban Arfat yace" barni dasu my jidda aii duk zan iya dasu ba baki suka fini ba.
Haka sukaita hirarsu da wasa da dariya sai gab da magriba suka tafi gida.
"" kubiyoni masoyana,, ina k'yaunarku kamar yanda kuke son kasancewa dani a books d'ina, ina muku fatan alkairi akoda yaushe...................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 9~October ~2016
π·πΉNI DA K'AWATA πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIM π
πΆπΈ9β£πΈπΆ
...............Yau tsawon kwana hud'u kenan Sopy bataga Abdul ba, duk ta damu dan tunda suka had'u baitab'a kwana biyu baije gidansuba,, amma yanzu har tsawon kwana uku baizoba, gashi tana jin kunyar zuwa layinsu duboshi tagayawa fareeda tun jiya amma tace mata inkaji shiru to lfy ce,, itakam bata gamsu da wannan dalilinba,, wannan ne karo na farko dataji haushin rashin kasancewar waya a hannunta,, datanada waya saita kirashi kodan taji lfy?? Toko wayar baban ta zata amsa to saidai kuma batada nomber Abdul d'in tad'anja tsaki mara sauti,, kai bari uncle kabeer yazo zance masa ya saya min waya kodan irin wannan ranar,, ALLAH dai yasa ya amince kar yace saina gama makaranta.
Fareeda ta tab'ata,, tai firgigit alamar dawowa daga tunani,, sopy way mi kike tunanine inata magana tun d'azu amma kinyi shiriru miye matsalarki ne???
Sopy taja ajiyar zuciya matsalata dai d'ayace kamar yanda kika sani fareeda,, wace matsala kenan?? Fareeda ta tanbaya?? Sopy tace" matsalar Abdul mana,, yaufa tsawon kwana hud'u kenan baizo wajena ba!!
Fareeda tad'an tab'e baki,, aii nafad'a miki lfy itace ke b'uya amma ba ciwoba,, toki kwantar da hankalinki yanzu haka daga gidansu Abdul nake..
Da sauri sopy tace" dan ALLAH da gsk kikeyi?? Fareeda ta b'ata rai tunda mike dake natab'a miki k'aryane??? Sopy tace"A'a" tokuma fareeda ta fad'a, dama bawani abune ya hanashi zuwaba wani aikine abbansu yasakasu,, yace" nabaki hak'uri shima yayi missing d'inki amma zuwa gobe zaizo.
"" sopy ta sauke ajiyar zuciya kai wlhy harnaji dad'i, amma wlhy habibi yad'auki hakkina basai yasanar minba.
Fareeda tace" kedai ki masa uzuri tunda bai tab'a aikata miki maka mancin hakaba.
Sopy tace" hakane kuma na fahimce sa,, kema ngd miki abin k'aunata aminiyata mai sona da son farin cikina,, yau zanyi barci mai dad'i kenan tunda naji dalilin rashin zuwan rabin raina gareni.
Fareeda ta harareta amma bata ganiba, azuciyarta tace" ko ubanki neshi dole ki barshi.
Amma afili saitace lallai kam yau sai ayi barci harda munshari tunda anji labarin habibi.
" Sopy ta kai mata duka fareeda ta kauce tana dariya, itama sopyn dariya take, tace sister dan baki san so bane amma kibari inkin fara zaki san zafinsa dakuma dad'insa.
Fareeda ta tab'e baki tana fad'in naga lailah da majnun indai asoyayyane.
Nan dai sukata hirarsu.
Shikam Abdul kullum saiyazo wajan fareeda hira amma abayan layinsu suke hirar a soron gidan k'anin babanta'' wannan yasa sopy bata tab'a ganinsuba, ko wani d'an anguwar bare akawo mata gulma.
Bayan tafiyar fareeda ma saita nufi inda suke had'uwa da Abdul, dan tasan yana can yana jiranta,, aiko kamar yanda tai tunani yana can zaune yana jiranta,,Tashiga soron da sallama, tazauna kusada Abdul ayya my love! Kayi hak'uri dan ALLAH nabarka kai kad'ai,, Abdul yay mata hararar wasa dama k'yace haka tunda kin barni ni kad'ai tun d'azu nake zaune anan yafad'a yana kallon agogon hannunsa.
"" kayi hak'uri dan ALLAH ina wajen mutuniyar ka, dan ta tada hankalinta saboda rashin ganinka,, ya yatsine fuska wacece kuma mutuniyata?? Fareeda tayi dariya kana da wata mutuni bayan sopy?? Ya harareta mutuniyar ki dai dan dama tare naganku, gashi kuma nabarku tare,, dan hakama kibar had'ani da ita.
Fareeda tad'an zaro ido waje tofa har lamarin yakai haka?? Abdul yace" aii yama wuce haka,, kinga nibama wannan ne agabanaba,, akwai abinda yakawoni.
"" fareeda tagyara zama to miye ketafe dakai my love!! Ya shafa sumar kansa fareeda akwai matsalafa! Matsala kuma wace irin matsala!!! Fareeda babana yak'i yarda da batun aurenmu dan yace bazai zama k'aramin murum ba,, bayan ankai kud'in aurena da safiyya yanzu kuma nace wata nakeso ba itaba,, wlhy nayi iya bakin k'ok'arina danya fahimta amma ina yamak'i saurarena.
Fareeda tai shiru tana tunani, zuwa can taja ajiyar zuciya, takuma gyara zama my love! to idan abba yak'i ita kuma ummafa??
Yaja ajiyar zuciya ita umma dama batada matsala, dan duk abinda nakeso itama tana sonshi kinsan ni d'an gatantane,, kodana fad'a mata catayi ALLAH ya zab'a mana abinda yafi alkairi.
Fareeda ta lankwasa yatsun hannunta sukai k'ara tace" karka damu my love! Shima abban zai yarda da buk'atarka.
Abdul yace" ta halin k'ak'a zai yarda abbana yanada taurin kai fareeda.
Fareeda tai murmushi karka damu kabar komai ahannuna wannan aikinane.
Yace" to shikenan,, fareeda tace" saidai matsala d'aya ke damuna,, yay saurin cewa wace matsala kuma?? Tace" matsalar sopy mana, tana cikin damuwar rashin ganinka yanzu haka saida nai mata k'arya sannan ta kwantar da hankalinta.
Banason dukkan al'amarin aurena yashafi gidansu sopy bare harta zargi wani abu, nafi son kozata san hakan to yazamto an d'aura aurenmu,, alokacin kome zai faru yafaru tunda an d'aura nasan daga baya kowa zai hak'ura yabarmu. Abdul yace" ke nifa ayanda nake jina bana tsoron kowa yasan sirrin zuciyata harda safiyya kuma aciki.
Fareeda ta girgiza kai A'a my love!! Nikam bana fatan faruwar hakan,, har yanzu zuciyata da ruhina suna k'aunar safiyya, bakuma nason abinda zai cutar da k'awancen mu,, kuma bana son ka k'ub'cemin yanzu,, dolene mu dai daita tafiyar mu domin kawcema b'acinran sopy.
Yace" to ta yaya?? Tace" kawo kunnanka kaji,, yamik'a mata kunne ta fad'a masa,, yad'aga kafad'a tareda tab'e baki idan kina ganin hakan zai kwantar miki da hankali sai nayi.
Tace" eh my love! Hakan zai sakani farin ciki,, ya murmisa to babu damuwa nibari na wuce sai da daddaren zaki ganni nazo.
To shikenan suka mik'e tare yanufi gida ita kuma tashiga gidan k'anin babanta domin gaishesu.
KIRA:- kai jama'a cin amana bashida k'yau yanzu idan kaine ko kece haka ta kasance dake kamar yanda take shirin kasan cewa da safiyya dan ALLAH yazakiji?? babu cin amana mai ciwo kamar irin ta wanda kafi k'auna ko ka amince dashi ka yarda dashi,, irin wannan cin amanar yafi zafi da ciwo,, yafi karya zuciya da bak'in ciki,, amana abune mai girma dan tana d'aya daga cikin alamomin MUNAFIKI, akwai irinsu fareeda da dama acikin al'umma,, samari da 'yammata, k'awa da k'awa, aboki da aboki,, masu aikata cin amana,, wad'anda suka maida cin amana bakomaiba acikin laififfikan duniya,, to "UBANGIJI ALLAH" ya shirya zukatanmu ka ganar damu gsky. Amin ya "RABBI"
Ku biyoni danjin yanda zata kasance....................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 10~October ~2016
π·πΉNI DA K'AWATAπΉπ·
NA BILKISA IBRAHIMπ
πΆπΈππΈπΆ
...............Da daddare Abdul ya aiko kiran sopy,, cikin zumud'i tasaka hijjab tafita,, inna ta girgiza kai tana fad'in yaran zamani basu san kunyaba dai.
Inda suka saba zama ta iskeshi zaune, saidai fuskarsa babu walwala tak'arasa gareshi,, Assalamu alaika ya habibina,, yad'an kalleta batare daya amsaba, ya maida kansa kan waya.
" tazauna inda tasaba zama sai kuma jikinta yafara sanyi,, tace" habibina ina yini ?? Ykk? Ya kwana biyu?? Wlhy nayi missing d'inka."
Yad'ago yana kallonta "k" irin wannan surutu haka bakinki baya gajiya?? Cikin mamaki sopy take kallonsa danjin furicin bakinsa,, ta daure tace" habibina miye matsalarka??
Yad'an yatsine fuska yana bin jikinsa
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
β¦500Monthly Support Β· Most Popular30 days of premium access
β¦1,500