ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani hanya nawuce.
Ya ce, "haba gimbiyata ninefa Abdul d'inki mai sonki da k'aunarki, wlhy ina kewar rashin ganinki, dan ALLAH ki tsaya muyi magana.
Ta balla masa harara tareda jan wani mugun tsaki ta ce, "kaga malam tunkafin na shuka maka rashin mutunci kabani hanya na wuce, wlhy Abdul natsaneka.
Ya rinyse ido ya bud'e dan tabbas kalmar tata ta daki zuciyarsa, ya marairaice murya yana fad'in, Sopy nasan baki tsaneniba haryanzu kina sona, kina cikin b'acin ran abinda yafaru abayane, dan ALLAH kibani dama namiki bayani yanda zaki fahimceni, kece kad'ai nakeso kuma ashirye nake dana aureki ahalin yanzu.
Sopy ta tuntsure da dariya, sannan ta tamke fuska tamkar ba ita tayi dariyarba, ta nunashi da d'anyatsa ๐Ÿ‘‰๐Ÿปโ˜นAbdul wai kaine! kake tunanin zama mijina!, tad'an murmusa, Abdul har abada bazan zama shashashar macen dazanyi miji irinkaba, ka d'auka SAFIYYA IBRAHIM KABEER ta sub'uce maka har gaba da abada, ta ciro kati daga jakarta ka karanta wannan shi kad'aima ya isa yabaka amsa, inama gayyatarka, dan nasamu miji mai tarin ilimi k'yau, aji mutunci, kai idan ina lissafa maka abinda ya dangan ceshi tofa sai mu kwana anan,kuma katashimin ahanya kafin natara maka mutane wlhy.
Jiki asanyaye yamatsa mata ta wuce, tunda yafara karanta katin yake fitar da numfashi mai kama da nishi, yajingina da bango gudun karya fad'i, cikin murya kamar mai kuka ya ce, "fareeda kin cuceni ALLAH ya isa tsakanina dake, kuma wlhy yau saikin gayawa aya zak'inta, yanufi gida kamar mayun wacin zaki.
Da sauri muka bishi dan muganewa idanmu abinda zai faru.
To bari mugani fareeda kota zubur da cikin??.
Tunda nagabato b'angarenta nakejin ihun kukanta, wanda inada tabbacin suma mutanen dake gidan sunajinta, amma babu wanda yay yink'urin zuwa yaga abinda yafaru.
Nak'arasa d'akin da sauri nida madina, Abdul ne ke lakad'awa fareeda dukan 'yan danbe, duk yaji mata ciwo, amma wannan baisa ya daina d'irkartaba, dak'yar muka iya kwatarta, ya bimu da kallo yana huci kukuma daga ina??.
Madina ta ce, "tofa, Abdul maida wuk'ar mu bak'in fareeda ne, yaja tsaki tozaku iya tafiya aii ko.
Na ce, "kayi hak'uri Abdul kabari mu taimakawa fareeda kaga duk ciwone a jikinta, wata uwar harara yasakarmin, to aii ko uwar tace tazo gidannan saita fita, tunda sunce sun sallama mini ita, bareku gayyar sod'i, wlhy tun kafin nabud'e idanuna kubar gidannan idan kuwa bahakaba tokuwa jikinku zai fad'a muku.
Aii kafin yagama rufe baki madina uwar 'yan tsoro taja hannuna munyi waje, ta ce, "humm aunty bily naga mutuminnan yafara haukacewa wlhy zai iya dukanmu, kekam gaki lutiya idan yasamu wannan tsokar aii kinga takanki.
Na balla mata harara ina fad'in ALLAH madi kin rainani, ni son k'ibar nan tawa nakeyi idan baki saniba.
Amma gsky Abdul bashida mutunci irin wannan duka dayake mata kamar wata karuwarsa, kuma muta nen gidan sunaji amma sunk'i cetonta.
Madina tayi dariya aii ni dad'i nakeji wlhy ALLAH yasa yay mata abinda yafi hakama, aii maganin maci amana kenan, kad'amma tagani.

To yaudai lefe ya iso na sopy, mota guda muta nen GURUM sukayo domin kawo lefen Safiyya.
Akwati uku da karami na sama, babu laifi uncle G! yataka rawar gani, dan lefennan saidai mak'iyi amma yayi atalauce ba a sarauceba, anyi musu tarba ta mutunci, irin wadda suka tabbatar da sunzo gidan karamci, sun kuma tabbatar d'ansu yasamu d'iyar gidan tarbiyya,agidansu fareeda aka amshi lefen dan babanta ne zai d'aurama Sopy aure, aka had'a musu shatara ta arzik'i sukatafi, suna yabon wad'annan muta nen kirki.

Sopy tagama shirinta tsaf, tafito tana fad'in inna nashirya bari natafi kafin su cinyeni da masifarsu, bakamar aunty Nafisa sai bala'i takemin ina b'ata musu lokaci.
Inna ta ce, "to adawo lfy, kuma aii sunfiki gsky tun yaushe suke jiranki amma kina d'aki kina lank'andi, aii mijinki yaga takansa, mutum yay ta abu kamar kwai yafashe masa aciki.
To yi hak'uri inna bari natafi ina k'ara b'ata lokaci.
To ki gaishesu, kicema yayar taku gobenfa sutaho da wuri dan ayi aikin cin-cin d'innan agama da wuri.
To inna zan fad'a mata, tatafi tana dariyar inna, tunda bikinnan yamatso kullum tana kan aikin abubuwa bata ko hutawa .


๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ1โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

..............Da sallamarta tashiga gidan, suduka suka hauta da jaraba, aunty hauwa'u ta ce, " 'yarrainin wayo, kin zauna kinata yan kwana mu, saikace mu zai amfana, gwarama ki nutsu dan wannan mijin naki d'an kwalisa gara kije masa zam zam d'inki, ki rik'e abinki tunkafin wata takwace miki, irin wad'anna rubibinsu akeyi.
Sopy ta tab'e baki, nidai baruwana, dan tun wurima idan wannan zancen zakumin na koma, aunty asiya matar uncle kabeer ta tuntsure da dariya, barsu d'iyata wad'annan yayun banzane zoki zauna, aunty nafisa ta ce, "karma tazauna aii ita zai amfana bamuba, hakadai sukaita tsokanar sopy tana musu shagwab'a.
Gyarata suke kamar babu gobe, tundaga jikinta harzuwa inda ba'a fad'a๐Ÿ™ˆ sunsha gyara, zata zauna agidan auty Nafisa dan suci gaba da gyarata, tunda bawasu k'awaye garetaba wad'anda zasu takura mata.
Bata zuwa ko'ina daga d'aki sai tsakar gida, kunji 'yar gatan auntys d'inta, wayartama ankarb'a ankashe, hankalin uncle G! Duk yatashi yanaso yaganta kodan su tattauna amma hakan tak'i samuwa.
Ya kira uncle kabeer ya tambaya?.
Uncle kabeer ya ce, "lafiyarta k'alau wlhy, nima haka nemanta nake amma tak'i yarda naganta, way tana wani gida b'oyo.
Tofa, uncle G! Yafad'a, to watake b'oyemawa??.
Uncle kabeer ya ce, "agonta mana.
Uncle G! Yay dariya to shikenan tunda dai lfy ai da sauk'i, amma yakamata kazo gobe mu had'ufa.
Okey to badamuwa, zuwa k'arfe hud'u zan shigo insha ALLAH.
TO ALLAH YAKAIMU.

yau k'unshi amma babu amarya, inna sai fad'a takeyi akan b'oye Sopy amma sunk'i fito da'ita saidai subata hak'uri, can gidan aka kai mai k'unshi tamata ta'iya sosai wlhy karkuga yanda Sopy tayi k'yau kamar ba'itaba, jikinnan yasha gyara, Nadiya kad'ai tasan inda take, dan ita take kula da abinda yashafi k'awayensu na makaranta da wanda sukayi secondary tare.
Sai a daren d'aurin aure aka dawo da sopy gidansu, inna ta rud'e daganin k'yawun da sopy tayi, sai latsa jikinta take tana fad'in kaga yara da dabara mikukaima auta na ne tayi haka?.
Su aunty asiya sai dariya suke ma inna.
Inna ta ce, "A lallai dole nabaku tukuyci dan gyaran dakukaima autata yayi.

MASU IYA MAGANA SUKANCE RANA BATA K'ARYA SADAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA, to haka kuwa wannan ranar take ga uncle G! da Sopy.
Ayau dai and'ara auren Youseef Hussein Ahmad da Safiyya Ibrahim kabeer, karkuso kuga wankan shaddar da ango yayi, yayi kyau matuk'a, da yawan d'alibansa da malamai 'yan uwansa sun halarci d'aurin auren, mutanen GURUM kuwa aii ba'a magana, matasan garinsu d'ai d'aine basu zoba, sai washe baki yake dan farin ciki wasuma bai sansuba, lallai naga taron gagarimin d'aurin aure, abin sai wanda yagani.
Dak'yar na iya nemo muku amarya sopy, itamadai taci gayu cikin wata atamfa mai k'yau, idan natsaya bayyana muku kwalliyarta sai nacika littafin, amma dai tabbas ta had'u tamkar zata gasar sarauniyar k'yau, tana zaune itada k'awaenta agidan su fareeda, dukkanin 'yan professional writer da Zumunta sunje, sunkumayi rawar gani wajen mik'awa Sopy gudummawa, canna hango Hauwa lele๐Ÿ˜˜ kusada amarya, to sopy saimuce ALLAH yasanya alkairi.
Wajen k'arfe hud'u aka shirya amarya domin kaita garinsu uncle G!, dan sai ankaita can sun gama bikinsu, daga baya sai angonta yadawo da ita gidansu dake nan kano.
Sopy sai kuka take, dan iyayene suka zagayeta ana mata fad'a da nasiha, irin wadda akema amare, "sai dai wasu amaren basa d'aukar irin wannan fad'an saboda kunnen k'ashinsu", to ita dai sopy da alama komai yana zama a kwakwalwarta.
Da haka dai aka d'ungunma da amarya zuwa GURUM dake acikin k'aramar hukumar Tsanyawa, tareda gayyar 'yan uwa da abokan arzik'i, a k'awayenta Nadiya ce kawai taje, muma dai munbi ayari nida gayyar 'yan group d'ina dan kar abamu labari...................โœ๐Ÿป





๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 30~October~2016




๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท



NA BILKISA IBRAHIM ๐Ÿ’ž




๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ2โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.........A garin GURUM su Sopy sun sami tarba mai k'yau, daga dangin uncle G!, Suma sunada kirki, ananma biki aka d'ora, da daddare matasa suka warware kid'in daya bama dangin sopy sha'awa, atak'aice an dai sha shagali.
Washe gari bayan sallar azuhur dangin sopy sukayi haramar komawa kano, bayan an k'ara yima amarya nasiha da jan kunne akan sirikanta da dangin mijinta, suka tattaro suka taho, aka baro amarya tana kwasar kuka.
Da k'yar gwaggo ta lallasheta dan ad'akinta suka barota, daga k'arshe gwaggo ta lallab'ata tayi barici, kunga sirikan kwarai masu tattalin matan 'ya'yansu.
Libabatu ta gyara b'angaren da su sopy zasu zauna kafin sutafi, wato b'angaren uncle G! Kenan, acan gefe yake akatange babu ruwanta da sirikanta saidai idan sun shiga, gyara sosai tayi ma b'angaren, ta amshi turaren wuta wajen gwaggo taje takunna, tak'ara da da wasu turarurrukan data gani ad'akin, azuciyarta ta ce, "oh ni liba, kaga d'akin yaya kamar na mace, nan dai tagama tafito.
Uncle G! Kuwa bayan yagama hidimar sallamar bak'i masu tfy, saikuma yashiga sabgogin sallamar 'yan uwa da abokan arzik'i dake nan, dakuma mammaida kayayyakin da'aka aro na mutane.
Sai gab da magriba aka maida Sopy b'angarenta, aunty hafsa da kanta ta had'a mata ruwan wanka, Sopy ta ce, "nagode aunty!, aunty hafsat tayi murmushi bakomai k'anwata jekiyi wankan, dan muma tafiya zamuyi, lubabatu nacan tana jirana, sai da safe.
" Sopy ta ce, "to ALLAH yakaimu.
Bayan fitar aunty hafsa Sopy tashiga wanka zuciyarta cike da tunani iri-iri, tagama wanka tafito sukayi kicib'is da lubabatu, lubabatu ta ce, "to amarya muzamu gudu gida, sai gobe nazo cin kazar amarci, kifa ragemin.
Sopy tayi d'an murmushi ta ce, "to.
Libabatu tana tafiya sopy tashiga d'akin, tabi d'akin da kallo babu wani tarkace, katifa ce k'atuwa an lailayeta da zanin gado, sai wardrobe ta zuba kaya itama k'arama, sai kujera doguwa a gefenta akwai firij, saikuma wani tebir da kujera agefensa cike yake da littatafai, da alama library d'in uncle G! Ne, ba laifi d'akin yayi k'yau a talauce ba a sarauceba.
Ta zauna tashafa mai tayi kwalliya mai d'an sauk'i, wata atamfa tasaka siket da riga, sun kama jikinta sosai, ta ja k'aramin tsaki nikam bana son kaya su matseni, amma na lura duk haka aunty hauwa'u ta d'inka min kayana.
Haka ta zauna tana gyaran kai tana mitar d'inkunan, nace ashe Sopy tanada gashi ba laifi, dan dai tana b'oyeshine, tagama ta gyara gurin, sannan tahau sallah, bayan ta idar ta zauna agurin har aka kira sallar isha'i, ta tashi tayi.
Ta cire hijjabin kenan tanufi waje akwatin ta dan d'aukar k'aramin hijjabi wanda baikai girman wanda tayi sallarba.
Uncle G! Ya shigo d'akin da sallamarsa, Sopy tarikice tarasa inda zata dosa, wajen akwatin ko kuwa wajen hijjabin data gama sallah yanzu?.
Shima uncle G! Tsaye yake kam cikin farar shadda k'al yaukam harda hula, sai bulbula k'amshi yakeyi, fuskar nan tasa fayau da annurin angwanci, ya kasa koda motsi dan d'imautuwa da surar Sopy, ya tambayi kansa? wai dama haka sopy take da diri da cikakkiyar sura ta d'aukar han kali, lallai dolene ya godema ALLAHn daya halicci wannan k'ak'yk'yawar sura.
Ahankali ya k'arasa gareta, tasaka hanu tana kare k'irjinta๐Ÿ™…, ta rintse idanu danjin uncle G ya mannata da jikinsa, cak ya d'auketa ya dire saman kujera, shima ya zauna, kallonta yakeyi sama da k'asa kamar yau yafara ganinta.
Itako kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta, ta daure ta ce, "ina yini?, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda kama hannunta ya r'intse anasa.
Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrrrrrr, yaune rana ta farko da namiji ya tab'a kama hannunta, ta runtse manyan idanunta.
Uncle G! Yay murmushi, cikin muryarsa mai dad'i da amo ya ce, "kin wuni lafiya ??.
Cikin jin kunya ta ce, "lfy law.
Ya ce, "ya gajiyar biki??.
"Nanma saida tayi k'asa da kai sannan ta amsa.
Ya ce, "my Sopy aii kuma kunya ta k'are yau, domin kin zama tawa nazama naki har abada.
Ita dai tayi masa shiru, idonta arufe saboda tsananin kunyarsa datake ji, gashi kuma yak'i sakar mata hannu, ya matso da fuskarsa kusada tata, harsuna jin fitar numfashin juna, batayi aune ba taji ya manna mata wata k'yak'yk'awar sumba๐Ÿ˜˜a kumatu. (Kiss)
Tayi wata 'yar girgiza dan sumbar ta shigeta har cikin kwakwalwa......................โœ๐Ÿป




๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 30~October~2016




๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM ๐Ÿ’ž




๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ3โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

...........ya d'an murmusa dan ganin yanda taketa kare k'irjinta, yasak'ala hannunsa ta bayanta ya rungumota zuwa jikinsa, aii sai jikin mutuniyar taku ya hau rawa, cikin kunnanta ya ce, "tsawon kwana goma kina b'oyema ganina, yau kuma gani daga ni saike!!.
Ita dai jikinta sai rawa yakeyi, takuma kasa magana, ya hura mata iska a kunnenta, ta bud'e ido da sauri, yay murmushi, Sopy sarkin kunya yafad'a yana shafa jikinta, ya kuma matseta sosai ajikinsa, har saida tayi 'yar k'ara sannan ya sassauta mata, ya ce, "haba sopy yau baza a yima uncle G!; magana bane? Ko har yanzu fushin tafiyar su uncle kabeer d'in akeyi?, dan ya ce, "min har kukayi sallama kuka kikeyi, kokuma garinmune babu dad'i??.
Sopy ta girgiza kai alamar A'a.
Ya ce, "to minene yasa aka k'iyimin magana??.
Ta daure ta ce, "ba komai kainane yake d'an ciwo.
Uncle G! Yay 'yar dariya, to ALLAH yabaki lafiya Sopy na!, amma ko dai ana tsoron uncle G! ne??.
" nanma ta girgiza kai batare da tayi magana ba"
Ya mik'e yana fad'in shikenan idan anzo wajen kwanciya zamu gani.
Gaban Sopy yafad'i rasss, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba a kumatu, tayi saurin sharewa, itakam gsky tanada tsoro, ALLAH dai yasa karyay mata komai.
Ledar daya shigo da ita ya d'akko, wadda santin ganin surar sopy yasakashi yarda ta ak'ofar d'aki, ya zauna yana lallashinta akan taci kazar dake ciki, da k'yar yasamu taci akunya ce, yana mamakin kunya irinta sopy, gsky da haka kowace mace take, da ansamu sauk'in lalacewar 'yammata kai harma zawarawa da matan aure, ALLAH dai ya shirya.
Bayan sun gama cin kazar wadda rabinta duk shi yaci kayansa, dan yana jin yunwa sosai, tunda aka fara bikinnan bai nutsu yaci abincin kirkiba, yaje yay brosh ya dawo, itama taje tayo.
Ya ce, "yana zuwa yanzu zai dawo.
Yana fita ta tashi tacanja kayan barci a gurguje, wani zani tasaka da riga tishet mara nauyi, tasaka k'aramin hijjabi, tayi kwanciyarta bisa kujera.
Ya kai tsawon minti talatin sannan yadawo, yarufe ko ina, yabi sopy da kallo yana d'an murmushi, ahankali ya furta safiyya sarkin tsoro, shima kayan barci yasaka, yad'an fesa turare.
Wajen kujerar datake kwance ya k'araso, ya shafa kuma tunta yana fad'in my sopy aii duk wayon amarya sai ansha manta.
Cak ya d'auketa yana fad'in kinga gurin barcinki nan ya nuna k'irjinsa da baki, saman katifar ya direta, tana jinsa amma tayi shiru, tak'iyin ko motsi dan tsoro da kunya.
Yashiga k'ok'arin cire mata hijjabin jikinta, sai asannan ta motsa ta rik'e hannunsa.
Yay murmushi mai sauti ya ce, "aii dama nasan idonki biyu.
"Tai masa shiru"
Ya ce, "okey aii nasan maganinki, bari kiga nasan yanda zanyi kiyi magana, batayi aune ba taji bakinsa cikin nata, duk iya k'ok'arinta na ta kwace kanta amma ta kasa, ta shiga tsungu ninsa, amma ina shikam baisan tanayiba, tsotsar bakinta yake cikin zafin nama, tamkar mafa raucin zaki๐Ÿ…, ayayin dayaga abinci, Sopy tun tana tsungu ninsa harta hak'ura tabarma ALLAH.
sai da ya tsotse bakin tamkar zai rabata dashi sannan ya janye jikinsa yana maida numfashi.
Sai a sannan Sopy tasamu bakin yin kuka.
Ya rungumota tsam akan faffad'an k'irjinsa daketa tashin k'amshin turare, ahankali yashiga buga bayanta tamkar wata jaririya, cikin sark'ewar murya ya ce, "to kukan ya isa haka, kinga yi hak'uri ni babu abinda zan miki, yi barcinki kinji my sweet Sopy, cikin sigar lallaahi yake maganar, iska ya shiga hura mata a cikin kunne mai dad'i, ita kanta bata san sanda barci yay awon gaba da itaba, dama ga gajiyar biki.
Shikam ya dad'e baiyi barcin ba, dan kuwa hanka linsa yakai k'ololuwar tashi, anya zai iya cika alk'awarin daya d'auka na barin Sopy har sai sun koma gidansu, yaja wani gwauron numfashi tareda sake manneta a jikinsa, sanda bashida matarma baidamu ba haka, amma yau kodan yaganta a kusa dashine oho, ya tsurama fuskarta idonu, tanata barcinta, dukda yasan barcin cikin tsoro da fargaba ta yishi, ya shafa kanta tareda sumbatar ida nunta yana murmushi Sopy sarkin tsoro yafad'a yana gyar kwanciya.
Haka yayta sak'a wasik'ar jaki har barci yay awon gaba dashi.

Muma muka fito, dan komawa masaukinmu nida marak'isiyya, da madina, da aunty pii pii, da saratu, dan sunce ba inda zasu labari ya wucesu.
Na ce, "magulmata saiku tsaya, nasan kuna bak'in cikin d'an abinda uncle G! Zai banine, idan nagama yad'a labinsune, to kusani kad'an zan baku eheee๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ .....................โœ๐Ÿป




๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'sala๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 2~November~2016




๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž




๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ4โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

........Da asuba yatashi yay alwala sannan yatada ita ya ce, "nawuce masallaci, kanta ak'asa ta ce, "to adawo lfy.
Bayan fitarsa itama alwalar tayo tayi sallah, ta d'auki alkur'anin data gani a d'akin tayi karatu, zuwa sannan gari yafara haske, harzuwa sannan uncle G bai dawoba, ta tashi ta gyara d'akin fes, tashare d'an lungun nasu ta wanke bayin sannan tashiga wanka.
Uncle G yadawo motsin dayaji abayi ya tabbatar masada tana wanka, d'akin yashiga yashaki wani k'amshi mai dad'i ya lumshe idanu, yay murmushi mai k'ayatarwa ya ce, "lallai ina son mutum mai tsafta da rashin son jiki, gashi kuma ALLAH ya azurtani da samun mace, ALLAH nagodema da irin wannan tarin ni'imomi daka min.
Batayi zaton yana cikiba, dan haka tashigo d'akin kanta tsaye, gabanta yafad'a yayinda taga uncle G zaune, takalli jikinta daga ita sai zanifa, ta faki idonsa ta rarumi hijjabin sallah ta rufe jikinta.
Lamarin yayi matuk'ar bawa uncle G! dariya amma saiya gimtse ya ce, "yayadai ko kina jin sanyi ne?.
Ta ce, "A'a".
Ya girgiza kai yana murmushi, taso wa yayi yanufo inda take, aii tunkafin yazo ta durk'ushe k'asa, ya tallafota zuwa jikinsa, saman kujera ya zauna ya d'orata saman cinyarsa ya ce, "haba autar inna aii komai na Sopy mallakin uncle G! ne, kokin manta baba da uncle kabeer sun bani har abada?.
Ta cusa kanta cikin hijjabi, tana mamakin uncle G wai dama haka yake?, wlhy da idan aka fad'a mata haka yake zata k'aryata, amma dan ALLAH jibi abinda yayi mata jiya da daddare, tamkar ba malamin taba.
Jin tayi shiru saiya d'an girgizata, yasa hannu yacire hijjabin daga fuskarta ya ce, "Safiyya! wannan kunyar takifa tayi yawa, nikam zata hanani shan sharafin amarci, amma bari nafara rageta, yafara k'ok'arin kwance zaninta.
Da sauri ta rik'e hannunsa tana fad'in plz uncle! kayi hak'uri na tuba.
Ya tsaya yana kallonta ya ce, "to kin yarda na shafa miki mai da kaina!.
Ta waro ido waje๐Ÿ‘€ tana kallonsa ta ce, "saikace wata jaririya?", ya lumshe manyan ida nunsa yana murmushi, aii kema jaririya tace, kafin ki haifa mana wasu jariran.
Ta sinne kanta ak'irjinsa dan kunya.
Sallamar dasukajine yasa ta tashi daga jikinsa, ta d'auki hijjabin tasaka, uncle G ya ce, "kowa nene yashigo, Aysha! tashigo da tire a hannu ta, ta dire sannan ta gaishesu, harta mik'e uncle G ya ce, "Aysha akwai ruwan zafi kuwa agidannan?, zanyi wanka, ta ce, "e, yaya akwai wanda aka dafama baki na wanka, ya ce, "okey to d'auki botiki ki d'ebo min, ta ce, "to.
Babu dad'ewa Aysha takawo masa ruwan wankan, yaje yay wanka, kafin ya fito tayi sauri ta shirya, yashigo yana fad'in sopy kedai bak'ya gajiya da hijjab ko? Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba, ya shirya cikin k'ananun kaya, sannan sukayi karin kumallo.
Dole ya fita don muta nen daketa zuwa ganin amarya.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya a Gurum sopy tana ganin soyayya wajen dangin mijinta da iyayensa, kowa sonta ya ke da son faranta mata, sai abinda takeso zata ci, uncle G kam aii yafi kowa nuna mata kulawa, kuma yanzu baya shige mata, dan yaga tana matuk"ar jin kunyarsa, shima yakula idan yaci gaba da shigemata tofa zai cutu, dan haka ya shareta ko wajen kwanciyama kaida k'afa sukeyi.
Hakan yayima sopy dad'i kuwa, takan fita tsakar gida ta taya gwaggo aiki, da gwaggo tafara aiki ita kuma zataje ta karb'e, hakan yana k'arama gwaggo son sopy a zuciya, dan suna yabawa da halayen yarinyar itada baba.
Da haka sati guda yacika suka fara shirin dawowa kano, saidai nakula sopy bata son dawowa dan garin yayi mata dad'i.................โœ๐Ÿป



๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 2~November~ 2016



๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM ๐Ÿ’ž




๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ3โƒฃ5โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.........WASHE GARI suka tashi da shirin tfy, uncle G! Yana kula da sopy bata son a tafi.
Nasiha sosai baba da gwaggo sukai musu, dan sunce sopyma tazama d'aya daga cikin 'ya'yansu.

" Haka yakamata surukai su rink'a d'aukar matan 'ya'yansu, bawai ki zauna kina kishi da matar d'ankiba, wannan ba dai dai bane, idan kika d'auketa d'iyarkima wlhy saitafi girmamaki da baki daraja, amma daga lokacin dakika fara kishi da ita, tofa rainine zai shiga tsakaninku, shima d'an naki yazo yana jin haushinki a baza awofi, ALLAH yasa mugane".

Sai bayan sallar azahar suka tafi sopy harda kuka, shi dariya ma take bashi, har sukazo tsanyawa tana kuka, daya kula idan ya k'yaleta ba bari zatayiba, sai ya fara janta da hira, tun tana amsawa ciki ciki harta ware tana kallon hanya da garuruwa, ya tsaya a bichi suka sha mai, sannan suka cigaba da tfy, ta ce, "to nan wane garine?, ya ce, "bichi kenan indai kinji ana fad'in bichi to itace wannan, A'a ni yauma natab'a jin sunan garin, yay murmushi kawai batareda ya ce komaiba.
Gab da la'asar suka shiga cikin kano, ya ce, "yanzu ina kikeso mu fara zuwa? Kona kaiki ki gaida su inna?.
Da sauri ta ce, "e, muje gidan su inna.
Yad'an murmusa batare da ya ce komaiba.
Ganin sun wuce titin layinsu ta ce, "munfa wuce uncle koka manta ne?, yad'an kalleta sannan ya maida kallonsa bida titi, na canja shawara ne aii.
Saboda mi? Sopy ta tanbaya.
Ya dafe sitiyari da hannu biyu saboda naga kamar bai daceba ne, sun kaiki gidan miji kuma kin zo musu yanda suka kaiki, yakamata a samu canji.
ALLAH sarki Sopy ita kam bata fahimci inda ya dosaba, amma ta lura kamar da wata fassara yay maganar, daga nan tayi shiru bata sake maganaba, shima dai bai kuma cewa komaiba, har suka isa anguwarsu.
Gidan ma daidaicine, ginin talaka mai wadatar zuci, da kansa yafita ya bud'e get d'in sannan suka shiga, inda motar ta tsaya nanne kawai fili, daga ita kuwa babu abinda zai k'ara shiga koda mashin ne, suka fito ya ce, "Safiyya ga gidanki to.
Sopy tayi 'yar dariya ta ce, "naganshi kuma yayi k'yau.
Shima ma dariyar yayi yana bud'e but d'in motar ya sauke kayan duka, ya d'auki wasu yana fad'in namanta kefa makauniyace sai nayi

Please Login or Register in order to submit comment