ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþ*MAKAHO NE*

*NA*

Maman Ihsan ce

*Alhamdulillah na gode Allah da ya bani ikon rubuta wannan labarin da na daWe ina son rubuta shi. Allah

ya bani ikon rubuta abun da zai amfani al'umma.*

"*Ni ce ta ku dai marubuciyar nan da na saba faWakar da ku da misaWantar da ku, to yanzu ma na zo ma"

"ku da sabon labari mai cike da sar™akiya tuggu da makirci, wanda zai bar ku cikin shau™i da zumuWi. Ku dai ku biyo ni kun san dai ba taSa ba ku kunya ba, wannan na daban ne mu je zuwa*"

ŠanWano

Page

"Tafiya yake yi cikin takunsa na natsuwa da kamala, Sandar dake da hannunsa yana dogarawa ne zai"

"tabbatar ma ka da cewa makaho ne shi, kuma sandar ce jagoransa. Sai ba™in glass dake sanye a idanunsa wanda ya zauna a karan dogon hancinsa da ya dace da kyakkyawar fuskarsa. Fari ne dogo mai matsakaicin jiki, sai dai kallo Waya za ka yi wa kyakkyawar fuskarsa ka fahimci cewa shi ba mai yawan fara'a ba ne da sakin fuska. Yana da ™irar jiki da cikar zati irin na cikakken Wa namiji. Sanye yake da wani royal blue yadi mai sau™in kuWi wanda ake kira da yi shirunka maraya, daga ganin kayan jikinsa za ka san sun sha jiki sai dai da dukkan alamu saurayin mai tsafta ne don kayan fes suke babu datti duk da"

kasancewarsa makaho ne.

"Tafiya yake yi a cikin layin unguwar da ta kasance unguwa ce ta ma su hannu da shuni, tun daga ganin"

shimfiWaWiyar kwaltar da ta shiga cikin unguwar ta ko ina har zuwa ™erarrun gidajen dake cikin unguwar.

Unguwar ta kasance shiru ne ba hayaniya.

"Har ya iso daidai katafaren wani gida ya tsaya, shiru ya yi na tsawon mintuna biyu kafin ya yi knocking"

Win dan™areren gate Win dake gidan.

Daga ciki ya ji muryar Musa mai gadi yana cewa.

"""Waye nan?"""

Don tun da ya ji ba'ayi horn ba ya san ko ma waye ba da mota ya zo ba talaka ne.

˜arasawa ya yi don dama daga toilet ya fito yana surutu shi kaWai.

"""Ko ma waye dole za ku ha™ura ku koma, don ita matar kirkir dake da tausayin talakawa kuke zuwa rana"

"ba ku yanzu Allah ya karSi rayuwarta ba ta raye, wacce ta rage a gidan ko mutuwa za ku yi ba za ta lalle ku da gashi ba ballantana ta taimaka ma ku."""

Yana buWe ™ofar ya ga wanda ke tsaye ya ce ya ce.

"""Mallam makaho ne?"""

"Shiru ya ma sa bai yanka ma sa ba, sai ya sake cewa."

"""To daga yau sai dai ka daina zuwa don wacce kake zuwa domin ta take ba ka Allah ya larSi rayuwarta,"

"tsawon kwanaki hamsin kenan yau, kuma na san ka zo ta'aziyya , kuma ka zo bayan wata Waya da"

rasuwar . Ina mai ba ka shawara ka bar nan kafin waccen marar mutuncin ta fito ta ganka uwar Wakinka

"ta rasu ka sani ko?"""

"Gundura ya fara yi da maganar ta Mallam Musa sakamakon ba ya son magana ko hayaniya , ga shi"

"Mallam Musa bai iya magana a hankali ba, cike da mishkilanci ya yamutse fuskarsa yana ™okarin shiga"

cikin gidan.

Da kallo Mallam Musa ya bishi yana cewa.

"""Sai shegen girman kai da mishkilanci, ga shi nakasashshe yanzu an koro ka ka fito."""

Mamy ce ta fito tana kallon Makaho tana washe baki tana cewa.

"""Ango ya iso daukar Amaryarsa kenan Alhamdulillah."""

"Bai ce komai ba sai sake tsuke fuska da ya yi, yayin da Mallam Musa ya cika da mamaki to waye angon"

ba dai makahon nan ba.

Tsuke bakinsa ya yi ya koma bakin aikinsa yayin da Mamy ke yi wa Makaho iso tana cewa.

"""Shigo sirikina."""

"""Alhaji dake zaune a falo ya Wago kai yana kallon Makaho dake shigowa tare da sallama. Yana mai amsa"

sallamar ta sa yana bashi izinin zama. Zama ya yi a kan lallaudan centre carpet dake tsakiyar falon

"""Ina wuni Daddy."""

"""Lafiya lau Khalifa."""

Kallo Waya ya yi wa Mamy ya kau da kai kamar an masa dole ya ce .

"""Ina wuni Mamy?"""

"""Lafiya lau angon Ma'eesaha."""

Ta amsa tana wani dariya na mugunta.

"Shiru falon ya yi tana jiran Dady ya yi magana sai ta ji shiru, gabadaya baya cikin tunanisa."

"""Alhaji"""

Shiru bai amsa ba sai da ta sake kiransa a karo na uku Sannan ya dawo tunanisa yana cewa.

"""Na'am."""

"""Ga shi ya zo Waukar Amaryarsa da aka ce ya zo ya Wauka, ka bar shi zaune."""

"""To ai na kira ita Ma'eesha tana hanyar dawowa."""

"""Okay, ka jira amaryar ta karasa sai ku tafi ta je lalle da kitso ne."""

Bai ce komai ba illa ya sunkuyar da kai ™asa.

_Ma'eesha_

"Fitowarta kenan daga cikin shagon saloon tana sanye da rigar Abaya green colour, tana gyara mayafin"

abyarta hannunta rike da handbag Win ta da wayarta I phone 16 pro max. Wayarta ce ta fara ruri tana dubawa ta ga Inno ce me masu aiki.

"Šaga wa ta yi ta ma™ala wayar a kunne tana ma™e kafaWarta yadda wayar za ta zauna, ta zuge zip Win"

handbag Win ta ta ciro makullin motarta tana cewa.

"""Hello Inno ya aka yi ne?"""

Shiru Inno ta kasa magana don har ya nufi motarta ta bude Inno ba ta yi magana ba.

Zama ta yi a driving seat sannan ta ce.

"""Inno lafiya kuwa."""

Cikin kuka ta ji muryar Inno na cewa.

"""Ma'eesha kada ku dawo gidan nan ki je wani wuri."""

Cikin faWuwar gaba ta ce.

"""Me ya faru ne Inno?"""

Ta ji ta sake cewa.

"""Aure aka Waura ma ki yau da wannan makahon da ya taSa ceton ran mahaifiyar ki har ta ke kyautata"

"ma sa."""

Wani dariya Ma'eesha ta yi tare da cewa

"""No ba zai yiwu ba, kada ki dake Mani wannan wasar."""

Ta katse kiran wayar tana cewa.

"""Haba wane irin aure ba tare da an nemi amincewa ta ba, ko auren ne ma ai sai a ce na fito da wanda"

"nake so amma ba za'a yi ma ni dole ba, ballantana s ce wani makaho wanda ko a mafarki bai isa ya zo mijina ba ballantana a zahiri?"""

Tsuke ta ja tare da yi wa motarta key ta bar harabar Saloon Win.

Horn take dannawa har maigadi ya wangala ma ta gate ta shigar da motar tana mai yin yin parking a

parking space.

A hankali ta sako da fararen ™afafuwanta da suka sha zanen kalli ja ba ba™i.

Fitowarta yi hannunta rike da handbag Win ta da makullin motarta.

Da sallama ta shiga falon gabanta na faWuwa.

Gabadaya suka amsa ma ya sallamar ta shiga ciki. Ganin makaho ya haifar ma ta da wata faWuwar gabar

da ba ta san dalili ba.

Bayan ta gaida Dady da Mamy ta mi™e za ta nufi ciki ta ji Mamy na cewa.

"""Alhaji ka sanar da ita ta fito ta bi mijinta tun da ga shi nan zaune yana jira tun Wazu."

"Mummunar faWuwar gaba ce ta ziyarce ta, wanda har sai da ta saki handbag Win ta a ™asa."

"""Ke Ma'eesha zo nan."""

A hankali ta take taku kamar kazar da ™wai ya fashewa a ciki ta zo gaban Dady ta zube.

"""An Waura auren ki da Khalifa makaho yau, ku tashi ki bi mijinki Allah ya ba ku zaman lafiya."""

"Kallon Dady take yi kamar wata sokuwa ta ma rasa me za ta ce ma sa, don ganin abin take yi kamar wani"

alamara.

"""Da...Da...Da..."""

Ta ma rasa me za ta ce wani kalma za ta kama da za ta yi amfani da shi wajen yi wa Dady magana. Kafin

ta samu ™arfin zuciyar furta.

"""Dady wane laifi na aikata da ka hukunta ni ta wannan han?"""

Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta firgita.

"""Tashi ki kwaso kayan sakawarki ki bi mijinki, idan kika sake yi Mani wata magana a nan sai na ba ki"

"mamakin da ya fi wanda kike ciki?"""

"""Ba da ke mahaifinki ke magana ba kina zaune?"""

Jiki ba ™wari ta mi™e ta Wauki handbag Win ta da makullin motarta ta nufi Wakinta.

"Nan ta samu Inno mai masu aiki, tana ganin Inno ta fada jikinta ta rungume ta tana fashewa da"

"matsanancin kuka."""

Ita ma Inno kuka take yi tana cewa.

"""Allah ya yana tare da ke Ma'eesha, shi ya sa na kira ki a waya na ce kada ki dawo gidan nan. Wannan"

"kishiya mahaifiyarki ba ta tsoron Allah, so take kawai ta ga rayuwarli ta tagayyara shi ya sa ta saka mahaifinki ya aura maki makaho musaki wanda ba ya da cin yau balle na gobe, ta ya ya mace irinki da kika taso cikin gata da jin Wadin more rayuwa za ki auri fakiri nakasashshe? Ita me ya saka ba ta saka ya"

"auri ´arta Agola ba, sai ke da gidan uban ki ne za'a yi ma ki wannan cin kashin?"""

Cikin kuka Ma'eesha ta ce.

"""Mamy ba ta so na ta tsane ta saka mahaifina dake son farin cikina yanzu ya juya mani baya ya tsane ni,"

"duk da haka bai ishe ta ba sai da ta saka ya aurar da ni a inda ta san zan wahala me na yi ma ta ne, Da zuciya daya mahaifiyata ta kawo su gidan nan ita da yaranta suna cin arziki, karshe ta ci amana ta auri mijin aminiyarta suka ci gaba da zama duk da haka Mahaifiyata ba ta nuna ta ji zafin abinda ta yi ma ta na aure ma ta miji ba, ta zauna da ita da zuciya Waya, sai bayan ran mahaifiyata ne za ta ma ni haka"

"sakayyarta ga Mahaifiyata kenan?"""

"Kuka suke yi dukkansu, kamar daga sama suka ji an daka ma su tsawa. A firgice suke kallon ™ofar. Mamy"

ce tare da Autarta Laila.

"""Sannu muna munafuka kina hure ma ta kunne ko?"""

Cikin rawar jiki Inno take ba Mamy hakuri ta fita daga Wakin.

Ma'eesha ta kalle su da idanunta da suka yi ja ta kawar da kai ta cigaba da haWa kayanta a cikin babban

trolly tana kuka.

"""Hi Amaryar makaho ya kike?"""

Cewar Laila tana dariya.

"""Mamy idan ta tafi Wakin nan zan dawo da zama don ya fi nawa girma, ko funiture Win ya fi nawa kyau."""

Mamy ta kalli ´arta ta ce .

"""Kar ki damu Shalele sai yadda kike so za'ayi."""

Kallon Ma'eesha dake hada kaya ta yi ta ce.

"""Ba ke mai gidan uba ba? Har kina yi wa yarana gorin cewa su agololi ne ko? To yanzu ke da gidan uban"

"ki ne na saka uban naki ya yi waje dake, su agolan da kike yi wa ta™ama da gidan uba su ne za su yi iko da gidan, ke kuka sai ki je ki fara cin garin kwaki, don ko kayan Gara da kayan Waki na hana ayi ma ki su ki je can ku ™arata. Kina hutawa anan sai dai masu aiki su gyara Maki Waki su wanke Maki toilet ayi maki"

"wankin da guga, ki sa a girka Maki abinda ranki ke so yanzu duk ba wannan a gidan makaho."""

Laila da Mamy suka sake saka wata dariyar har suna tafawa kamar wasu kewaye.

"Wannan karon Ma'eesha kukanta ne ya ™aru sosai kamar ranta zai fita, ita kadai ta san halin da take ciki"

a wannan yanayin.

Bayan ta cika babban trolly ne ta Wauki madaidaici ta zuba underwears Winta a ciki.

"Sannan ta dauki karamin cikinsu ta zuba kayan kwalliyarta da turarruka, sannan ta dauko set sar™ar"

"zinarenta za ta saka Mamy ta ce ke dakata ba in da za ki je da wannan."""

Wani kallo Ma'eesha ta yi ma ta ta ce .

"""Na mahaifiyata ce ita ta bani kyautatarsa dole ne tafi da shi."""

Daidai lokacin Dady ya shigo yana cewa.

"""Me kike yi ne har yanzu?"""

Mamy ta yi saurin cewa.

"""Alhaji ka karbi sar™ar set Win Gold Win nan kafa ta tafi da shi a sace ka san dai darajarsa."""

"""Ke Ma'eesha kawo Wan akwatin nan."""

"Ta mika masa kawai ta zuge zip Win, sannan ta bude wata drawer ta Wauko card Win ta na cire kuWi."

"""Alhaji ka karbi ATM Win nan, su ma, ta tafi haka nan daga ita sai kayanta."""

Tana rufe baki ya karSa Atm card Win kamar me jiran umarni.key Win motar dake saman handbag Win ta

Mamy ta kalla ta ce.

"""Har da makullin motarta ma ka karba, don gidan da za ta zauna ba ™ofa ballantana a samu gate na"

"shigar da motar, idan aka ajiye waje za'a sace."""

"""Eh haka ne."""

Ya fada yana mika hannu. Ba musu Ma'eesha ta mi™a ma sa ya karSa ya fice daga Wakin.

"""Ai duk wani abu da na san zai Maki amfani ba zan bar ki da shi ba."""

Ta fada tana jan hannun Laila suka fice.

Šayan trolly Win ta fara fitowa da shi ta ajiye falon ta koma ciki.

"""Kai makaho tashi ka dauki babbar akwatin kayanta ku tafi za ta fito da kananan."""

Tashi ya yi yana lalube har ya ji ya ci karo da akwati ya ja yana yi wa Dady godiya da sallama ya fita.

Tana fitowa rike da dayan madaidaicin akwatin sai karami dake da kayan turarrukannta ta nufi hanyar

"fita ba tare da ta kallon Dady ba ballantana Mamy."""

Sakin baki Mamy ta yi tare da cewa.

"""Amarya ba sallama?"""

Ba ta yanka ma ta ba ta fice daga cikin falon.

"""Ikon Allah, ko irin sallama da iyaye a nemi tafiyarsu ba za ki yi ba kin fice ko, za ki zo gidan za ki ga"

wulakanci.

Kasancewar tana bakin ™ofa ta ji komai ya saka ta ce.

"""Idan kin ga na zo gidan nan Mamy duk wula™ancin da kika dama ki yi ma ni."""

Ta saka kai ta fice Mamy ta saki baki yayin da Dady ya sunkuyar da kai ya kasa kallon Ma'eesaha.

"""Ungo Laila ga kudin sadakinta nan dubu uku ki Wauka ki kai ma ta hakkinta ne."""

Da sauri Laila ta Wauki kudin ta fice tana dariyar mugunta.

A harabar gidan ta gan su Yana gaba da babban trolly tana bin sa da kananan a baya.

Daidai lokacin motar Jamil babban yaron Mamy Yayan Laila ya danno hancin motarsa cikin gidan.

"Ko parking Win kirki bai yi ba sakamakon ganin Ma'eesha na kuka, ga makaho na gaba da wata babban"

"trolly wanda ya fi na hannun Ma'eesha girma, ga Laila na mi™a wa Ma'eesha kuWi."

"""Subhanah Ma'eesha me ya same ki kuma ina zuwa da kaya?"""

Ba ta tanka ma sa ba ta yi gaba. kallon ™anwarsa ya yi yana cewa.

"""Munafuka me kuka yi ma ta kuma yanzu?"""

"""Aure Mamy ta saka aka yi ma ta da wancan makahon, shi ne ya zo Waukarta za su wuce, ga kudin"

"sadakinta dubu uku ta ki amsa."""

"""What?"""

Ya yi tambayar a firgice.

"Yana ™arewa makaho kallo ganin yadin jikinsa ba ta wuce dubu Waya ba, kuka daga gani kayan ma sun ji"

"jiki, ko takaman ™afarsa ma na soso ne sai wata hular taSa ni ka ji hadisi da ya saka."

"""Aure da wannan nakasashen?"""

Girgiza kai ya yi tare da cewa

"""Da sake!."""

"Ya bi bayansu a guje yana kiran sunan Ma'eesha, har ya karasa inda suke tafiya ba ta kalle shi ba."

"Haka ya dinga bin su yana rokon Ma'eesha amma ba ta saurare shi ba, haka ya hakura ya bar ta ya dawo."

Kamar zai tashi sama haka yake tafiya har ya isa gidan. Don yau ya kara jinjina makirci da rashin imani

irin na mahaifiyarsa.

*KADUNA*

Da sanyin asuba ta fito daga cikin bathroom dake cikin Wakinsu.

Harara ta watsawa ™anwarta dake zaune saman sallaya tana karatun Alkur'ani mai girma.

Cije laSSanta ta yi cike da takaici ta yi tsuki.

Bayan ta kai karshen surar da take karantawa ta kalli yayat tata ta ce.

"""Aunty Sidra lafiya kuwa?"""

Harara ta watsa ma ta tare da cewa.

"""Ban sani ba."""

"""Allah ya huci zuciyarki."""

"Ta faWa tana mai ci gaba da karatunta, don in da sabo ta saba da halin yayar tata."

Komawa toilet ta yi sakamakon jin wayar dake hannunta tana vibration

"Šagawa ta ji bayan ta rufe kofar toilet Win, sannan ta amsa kiran daga cikin wayar ta ji an ce."

"""Haba Sidra ki yi ki fito ma na kin ce na zo na Wauke ki karfe biyar da rabi ga shi ba ki fito ba, ko na wuce"

"za ki zo da motarki ce?"""

Cikin yin ™asa da murya ta ce.

"""Ba haka ba ne Sadiya kin san ™anwata Nasara tana zaune idan ta ga na fito da trolly za ta gane zan tafi"

"wani waje ne, kin san kuma za ta iya sauro ta faWa a gidan namu idan aka kama ni fa? Yanzu ki bani mintuna kaWan zan tura ta wani wajen idan ta fita zan fito ba tare da motata ba don asirina zai iya"

"tonuwa."""

Tana fadar haka ba ta jira jin me ™awar za ta ce ma ta ba ta katse kiran wayar .

Fitowa ta yi tana kallon Nadra dake karatun Alkur'ani ta kira sunanta.

"""Ke Nadra!"""

Nadra ba ta dakata da karatun Alkur'anin ba sai da ta kai aya ta ce.

"""Na'am Aunty Sidra."""

"""Ki tashi ku je garden ki duba mani zobe na ya faWi ina ganin lokacin da muke fira da Fahad jiya daddare."""

Shiru ta Wan yi kafin ta ce.

"""Aunty Sidra why not ki bari sai da safe, yanzu akwai sauran duhu gari bai gama wayewa ba, idan gari ya"

"waye sai na fita na duba ma ki. Za'a fi gani ma idan ba duhu ai, amma yanzu ba lallai a gan..."""

"Idan ba za ki je ba ne ki fada ma ni, ai ga wayarki nan ki kunna torchlight ku je ki duba ma ni."""

Ba tare da ta sake yin magana ba ta mi™e tsaye tana cewa.

"""Bari na je na duba ma ki."""

"Fita ta yi daga Wakin ba tare da ta cire dogon Hijabin dake jikinta ba, wmhannunta rike da wayarta tana"

cewa.

"""Allah ya huci zuciyar Amarya a gidan Yaa Fahad, ai bai kamata a ce yau za'a Waura ma ki aure kina faWa"

"ba."""

"""Ke dai kika sani munafuka."""

"Sai da ta tabbatar ta nufi Garden Win sannan ta janyo trolly Win ta daga cikin wardrobe, kasancewar"

dogon Hijabi har ™asa ta saka ba's ganin ko me take Wauke da shi.

A hankali ta bude ™ofar Wakin bayan ta rataya handbag ta saka wayarta ciki.

"Akwai mutane a falon wasu na kwance wasu na zaune, kasancewar bikin auren Sidra ake yi ´an uwa da"

"abokan arziki na nesa duk sun zo garin, Wakin Sakin ya yi ma su kadan wasu suka kwana a falon."

Cikin sanWa take tafiya wata ma ta dake zaune ta ce.

"""Ke wace ce nan ke sanWa?"""

Sai da gaban Nadra ya faWi sannan ta juyo ta ce.

"""Ina kwanaku?"""

"""Oh Amaryar ce ashe, lafiya lau ya kike?"""

"Suka hada baki wajen amsa gaisuwar, wata dattijuwa ta ce ni fa ba na banbance wace ce Sidra wace ce"

"Nadra."""

Wata buduwar ta ce .

"""Wacce ta fara fitowa ta karasa ta dur™usa ta gaishe ku ita ce Nadra, wannan ta yanzu kuma ita ce Sidra"

"wacce za'a Waura wa auren yau, ai suna da banbanci ita Amaryar Sidra ai fara ce, ita kuma Nadra ba™a"

"ce."""

Ita dai ba ta bi ta kansu ba ta wucewarta waje.

Sai wata buduwar ta ce

"""Ai wannan Amaryar ba ta da kirki wallahi, jiya da Nadra ta ce mu zo mu kwana a Wakinsu tun da su biyu"

"ne amma fir wanan Amaryar ta ce wai ga falo nan ai, Sidra ba ta da kirki."""

Suna ta firarsu har Nadra ta dawo ta yi ma su sannu ta shiga Waki.

Sai dai ba ta ga Sidra ba a tunaninta tana toilet ne don haka ta koma ta zauna a saman sallayarta tana

cewa.

"""Aunty Sidra ban ga komai ba wallahi."""

Ta cigaba da karatunta don hadda take yi ba da Alkur'ani take karatun ba.

_Sidra_

Tana zuwa harabar gidan ba kowa maigadi dawowarsa daga masallaci kenan ya ga tana kokarin fita ya ce.

"""Amarya lafiya kuwa."""

Kamar ba za ta yi magana ba ta ce.

"""Zan ba kawata sa™o ne tana waje."""

"""A dawo lafiya."""

Ya fada yana zama kan kujerarsa hannunsa rike da carbi.

Tana ™arasawa ta buWe bayan motar ta saka jakar kayanta sannan ta zagaya ta zaune wajen me zaman

banza.

Ba tare da Sata lokaci ba Sadiya ta yi wa motarta key suka bar layin.

"""Na daWe ina jiran ki fa."""

"""Wallahi Nadra ce nake ta so na Wauke hankalinta kar ta ga fita ta da akwatin kaya ta tona ma ni asiri"

"shirina ya lalace."""

Shiru Sady baby ta yi tana rage gudun motar tana rage gudun motar bayan sun bar layin.

"Kiran waya ne ya shigo wayar Sidra, ta Waga tana cewa."

"""Hellow Khadijah ya aka yi ne?"""

"""Kina ina ne?"""

"""Ya kike tambaya ta kamar ba ki san komai ba, amma ai na fada ma ki komai kasancewar ki ™awata."""

"""Sidra abun da kike ™o™arin aikatawa kuskure ne, za ki wula™anta iyayenki ne, bayan kin san sun tara"

jama'a ana shagalin biki yau za'a Waura auren ki a ce kin gudu ya kike so su yi da jama'ar da suka tara? Sannan ga shi Fahad Win da iyayesa su ma sun tara na su jama'ar sai su ji labarin matar da Šan su zai

"aura ta gudu zai ji shi Fahad Win."""

"""Ke ba gudawa fa zan yi ba, da zaran na samu abinda na je nema zan dawo ne sai a sake saka ma na"

"ranar Waurin auren zuwa gaba, don na san Fahad na masifar so na dole ya jira sai na dawo, iyayena kuma"

"za su hakura ne kawai ba yadda za su yi da ni bayan na dawo, kin ga idan na ba su ha™uri ai za su karbe ni"

"ko da sun yi fushi kuwa. kuma ba wani daWewa zan yi ba me yiwuwa nan da watanni uku na dawo."""

Tana fadar haka ta katse wayar tare da kashe wayar gabWaya.

"""Khadijah ™awata ce tun da na fada ma ta plan Wina ta saka ni gaba wai kar na aikata."""

"""Da ma me zai kai ki faWa wa wata idan b ke ba."""

Daga nan ba wanda ya sake magana a cikinsu.

_Nadra_

Tana idar da karatun Alqur'ani ta yi knocking ™ofar toilet ta tabbatar ba kowa kafin ta tura ™ofar. Ganin

"ba Sidra ya sa ta dauka ko ta fita zuwa wajen su Umma ne, don haka ta fita zuwa falon mutanen Wazu ne a ciki, tana sanye har lokacin da hijabi ta nufi part Wakin Umma. Da sallama a bakinta ta tarar da Umma"

"tare da ™anwar Abba wacce suke kira da Goggo Laraba da suka kwana Wakin Umma."""

"Ta dur™usa ta gaishe su cikin girmamawa, suka amsa ma ta cike da kulawa. Gwaggo Laraba ta ce."

"""Ina Amaryar take ne ko tana can tare da ™awayenta?"""

"""Ai ™awayenta tun jiya ta Kore su wai ta sallame su ba ta son kowa ta kwana a gidan."""

"Da mamaki Umma ke kallon Nadra, Gwaggo Laraba ta ce."

"""Sidra ba ta da mutunci wallahi."""

"""Kira ma ni ita."""

Cewar Umma tana budar drawar da take zuba magungunanta a ciki.

"""To Umma bari na je na duba duk da ba ta cikin Wakin."""

Tana fita ta nufi part Win Abba ta gaishe she shi shi da wani wan Umma suna zaune .

Gaishe su ta yi cikin girmamawa sannan ta fita ta koma Wakinsu. Ta nemi Sidra ba ta ciki.

Don haka sai ta yi tunanin bari ta zagaya duka gidan ko tana wanni wajen a cikin gidan.

Umma kuwa ta buWe drawar da take saka magungunanta a ciki dan ta Wauko man maganinta na sha'awa

"a ™afa. Sai ta ga wata farar takarda, tana fitowa ta warware ta fara karantawa kamar haka."

*Assalamu alaikum*

*Iyayena ku gafarce ni zan yi wata tafiya domin cikar burina. Na san za ku shiga tashin hankali a yayin da

kuka ga wannan wannan ya wasi™ar ta wa. Ku ba wa Fahad da iyayensa ha™iri na san yana so na zai jira

har lokacin da na dawo mu yi aure.*

_Sidra Abdallah Maitama_

"Wani jiri ne ya Webi Umma ta yi luu za ta faWi, cikin zafin nama Gwaggo Laraba ta tare ta tare da zaunar"

da ita bakin gadon.

Takardar Gwaggo Laraba ta Wauka tana karantawa.

"""Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un."""

Shine kalmar da Gwaggo Laraba take furtawa.

Kafin ta Wauki wayarta ta kira lambar wayar Yayanta wato Mahaifin Sidra.

"Bugu Waya ya Waga, ta sanar da shi ya zo Wakin Umma yanzu."

"Sannan ta fita zuwa Wakin da Mahaifiyarsu ta sauka, ta tarar da ita ita kaWai, don ba wanda ya je wajenta"

saboda masifarta.

"Ita ma Gwaggo Laraba ba ta sanar da ita abun da ya faru ba, ta dai ce ta zo ana neman ta a Wakin Umma."

"Carko-carko suka yi a Wakin Umma, Daga Abba har mahaifiyar su da suke kira Ammi da Gwaggo Laraba."

"Umma na kuka kamar ranta zai fita yayin da kowa ya kasa magana. Abba ransa ya kai matukar tashi,"

"idanunsa sun yi jajir, Ammi sai alawadai da Sidra take yi yayin da Gwaggo Laraba ta kasa magana."

"Nadra ce ta shigo da sallama, ganin mahaifinsu kwance tana hawaye ya saka ta ruga gabanta ta rike"

hannunta tana hawaye ta ce.

"""Umma me ya same ki ?"""

Ta ji tambayar tana hawaye. Ganin haka ya saka Gwaggo Laraba janyo Nadra tana cewa.

"""Ba abinda ya same ta tana kukan rabuwa da Sidra ce, kin san daga Anjima za'a Waura aurenta shi ke

Please Login or Register in order to submit comment