You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Downloaded From https://arewanovels.com 🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_BUZUWA_*
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_STORY & WRITTEN_*
*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH_*
*_Editing_*
*_by_*
*_SISIN MAMA_*
*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*_```wanan book din gaba daya Sa sadaukar wace ga hazakan fasiyan taurarin Association wayau yan KAINUWA writer's wanan book din gaba daya na kune godiya a gare Ku mai tarin yawa Allah yabar mu tare ya bar so da kauna a tsakanin mu_*
```wanan labarin kirkiran Kaya na nayi ban yishi Dan wani koh wata ba in yayi dai dai da rayuwar ki/ka akasine```
🅿1⃣
Zaune yake akan motar shi dake k'ofar gidan su sai danne-danne yake a wayar shi inda kira ya shigo dayar wayar dake kusa dashi, dubawa yayi ganin mai kiran yaja karamin tsaki sannan yayi picking call din yana dagawa yafara magana a cikin sanyi murya wanda shi a ganin shi fada yakeyi "Malam in za kazo muje kataho mutafi in ba hakaba zan koma gida abina kacemin ga kanan zuwa amman sama da 25 minutes ina zaune a waje ka wani shanyani haba ai koh shanya kayi ya isa ya bushe" bai jira abin da dayan zai fada bah yakashe wayar yana Kara jaan wani siririn tsaki ba afi 10 minutes ba sai ga ABK ya karaso "I am very sorry aboki na wlh har zan fitoh hajiya tace in dan mata lissafin wasu kudi shiyasa kaga na dade" Yasir kallon shi yayi yace "dan rainin wayo to basai kakira ni ka fadan min ba aman kashan yani a waje kowa ya taho saiya karemin kallo toh wai ma ina motar kane na ganka a kafa?
ABK yace wlh duk tayi datti kuma Daddy baya gida bare na dauko tashi kasan ta Mommy kuma tayi kalar ta mata shiyasa na barta a wanke min" Yasir yace "OK saboda ka rainamin wayo ni kake so nazama drivern ka kenan" yana sakkowa daga kan motar hade da jefawa ABK Key din motar "gashi nan sai kajamu in ba hakaba wlh in fasa rakiyar kilama inje Inga yarinya yar ficiciya bata fi a raineta ba duk wanan rawar jikin da kakeyi a kanta" dariya ABK ya tuntsire da ita ta shakiyanci yace "au so kake in nemi uwar mata wadda in an shigo gdana za'ana doubting akan matar gidan ce ko babar me gidan ai ni bazan auri irin yan matannan da suka gaji da boko ba kai dai da kake da wannan ra'ayi Allah ya baka sa'a amma ni nafi gane ma yan shila wanda basu gama sanin mecece rayuwa ba inyi tarbiyar ta da kaina yanda zan....." maganar ce ta makale masa sakamakon yarinyar da tazo wucewa muryar tace ta doki kunnenshi tace "ina yini" cikin zazzakar muryar ta kamar ana busa sarewa tasa hijab dinta mai ruwan blue black yawuce gwiwa wanda yakara fitoh da tsan_tsan kyawun ta da hasken fatarta ga Al,kurani a rungome a kirjin ta ABK baki narawa yace "lafiya lau" bata kara cewa komai ba tai cikin gidan a bin,ta
ABK yace "Abokina kar dai kacemin yarinyar buzayan gidan kuce ta girma haka?"
Yasir yace "mai idon ka ya nuna maka mayen mata" murmushi ABK yayi hadi da sosa kai yace
"Kai abokina wlh dan kawai na riga nawa Hasina al,
'kawarine wlh da nan zan dawo ayi yar gda gaskiya Allah yayi halita a nan kodai-kodai Abokina
shiyasa kaki kula kowace yarinya in akai magana kace har yanzun kai bakaga matar Aure ba ashe kai kasan mai kaboye a cikin gida gaskiya na tayaka murna abokina" ABK ya fada hadi da dariyar shakiyanci irinna abokai ya mika mishi hannu alamar su gaisa yana mishi murna wata uwar harara Yasir ya sakar mishi hadi dajan tsaki tamkar zai tsinka harshe yace "lallai ka rainamin wayo me zanyi da wanan yar mitsitsiyar yarinya wace koh wanka ba agama mataba balle har tasan me kalmar aure take nufi" ya karashe maganar yana hararar ABK
baki bude ABK yake kallon shi yace "kasan mai make fada kuwa Yasir in wasa kake ma ka daina dan nayi maka sha'awar yarinyar nan da a kalla zatakai 17 years dan bazata wuce shekarun Hasina ba wlh mutumina zan baka shawara ka ajiye girman kai a gefe ka bada kai bori ya hau dan kar garin kallon ruwa kwado ya maka kafa kana gani wani yazo ya dauke ta ya barka da cizon yatsa" wanin wawan tsaki Yasir yayi hade da kaiwa ABK duka a kafada yace"wai akan wanan abin kake magana to abinda kake ta hankoron ganowa ni ban ganshi ba kaga Malam in zaka wuce mutafi ka wuce in kuma zakaci gaba da zuban,ne sai kai tayi ni inada abinyi,ya fara karkata akalar shi zuwa get din gdansu da sauri ABK ya riko rigar shi yana haba abokina wuce muje motar ABK yashiga sanan Yasir shima ya shiga yaja motar sai da suka hau titi sosai ABK yace "Yasir"uhmm Yasir din yace dan yasan maganar da ABK zai fada tana da mahimanci a gunshi tunda ya kira sunan shi,kara gyara murya ABK yayi sanan yace abin da nakeso in fadan maka game da yarinyar nan wlh karka zauna ruwan ido a maka abin dabakai zati ba kai da bakin ka kafadan min yar kanwar daddy tafitoh gaba daga tace Sanka take da aure sanan kai da bakin ka kace bakasan,ta saboda rashin tarbiyar ta kuma kasan in daddy yaji wanan magana ba abin da zai hana auren ka da itah sai mutuwa tunda kasan yanda daddy yake ji da kanwar nan ta amman kaga in kace kana sanan wanan yarinyar ta gidan Ku koh da maganar MARYAM ta bullo zai San abinyi aman in ba hakaba ina gujemaka shiga matsala nan gaba saboda tabbas in MARYAM tai tai da kai taki samun kanka ka amen CE da soyayyar ta zata fadan ma maman ta ita kuma kai tsaye zata fuskan,ci daddy da maganar kuma zai na'am da maganar sanan yazaman,ma dole ka aure ta aman kayi tunanin sosai a maganar ka Dan nasan in dai akaci gaba da haka tabbas abin da baka tunani zai faru
Muje next page
By yar Mutan KD
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹
*_BUZUWA_*
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_STORY & WRITTEN_*
*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH_*
*_Editing_*
*_by_*
*_SISIN MAMA_*
*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*_Fisabilillah_*
*_Ina mai fama da ciwon asima ga magani da yarda Allah kisamin garin habatu sauda da man tafar nuwa koh garin,ta kowane cokali biyu garin cokali biyu aman tafarnuwa koh gari cokali biyu sai kisami Zuma mai kyau sosai sai ki kwaba da garin nan da man tafar koh garin sai kisami ruwan lifton koh ruwa mai zafi sai ki zuba wanan garin da kika kwaba da Zuma babban cokalin Cin abinci guda biyu a cikin wanan ruwa zaki sha dasafe kafin kici komai sanan haka zaki zauna sai yakai awa daya dasha sanan zakici abinci_*
_sanan kisa ruwa a tukunya in ya tafasa sai ki zuba garin habatu sauda ya zamana kina sirace dashi in sha Allah Allah zai kawo lafiya_
🅿2⃣
"Aniyarka ta bika"
Yasir yace "wai meyasa Dan Allah kake yawan yimin mugun bakine to bari kaji ko mata sunkare a duniya mai zanyi da wata MARYAM ita kuma wanan yarinyar ba karamar yar raini hankali bace da kake ganin ta,kaga dai yanzun gashi a gaban idonka kai kadai ta gaisar tai wucewar ta kamar Allah baiyi ina wajan ba saboda tsabagen ta rainani haka take min duk sanda ta ganni ,to a haka mafa
bance Ina son taba dubi abin da takemin in nace ina sonta ai nakade dan wlh ba karamin rainani zataiba ni kuma abin da bazan taba dauka ba kenan yar ficiciyar yarinya ta rainani saboda bansan raini shiyasa kaga koh irin,su bana sha'awar kulawa dan ba karamin jinake da mutunci naba shiyasa rannan da su Yusuf suka zo nace a kawo musu abin dan tabawa gashi yar aikin mommy bata nan little ma batanan mummy tasa takawo daman da kai da Yusuf jirgi daya ya kwasoku zo kaga yanda yake rawar kafa a kanta wani irin bakin cikine yakamani Wanda bansan na menene ba haushin ta zanji koh na Yusuf da badan na taka mishi birki ba wlh da yasa ta gama rai nani dan haka kaima ka daina min maganar su dan in ba hakaba wlh zan fasa rakiyar haba" shiru kawai ABK yayi yana kallon ikon Allah wanda ya tabbata gaba kadan abokin nashi zai gane me yake nafi ABK yace "duk da haka kai tunani sosai a kan maganar nan dan gaba nake jiye maka"
Kallon shi kawai Yasir yayi ya kauda kai dan shi maganar da ABK yakeyi bata masa rai take abune yake fad'a da bazai taba faruwa ba a dai-dai nan sukayi parking waya ABK ya dauko call din Hasina yayi "baby gamu mun karaso muna bakin get" banji metace ba yace "OK ki fitoh lafiya" koh 5 mint basuyi ba sai gata ta fitoh
Yasir yace ai daman nasani ta tsuniyar gizo bata wuce koki Dan Allah dubeta ashe duk daya suke dan wannan bazata girme little ba ABK in ban da murmushi yana kallon,to ba abin da yake'yi wani maganadisun kaunar ta yana taso masa,da sallama Abakin ta karaso wajan amsawa sukai Yasir sai wani dan cin magani yakeyi gaisheshi ta Farayi "barka da zuwa abokin mu" murmushi dole ya kakalo "yace yauwa barka da fitoh wa kina lafiya ya mutanan gidan? " lafiya lau tace sai yau Allah yayi zan ganka ganin ka yafi jinka my love sai cewa yake zai kawo ka aman shiru sai yau Allah yayi gaskiya yau ina da babban bako" murmushi yake yakeyi, a zuciyar shi yace lallai abokina ya ebo parrot dube ta koh kunya bata ji a gabana take cewa my love yar ficiciyar ta da itah bata tafasa ba zata kone.
Muryar ABK ce tadawo dashi daga balaguran tunani da yatafi
Mushiga daga ciki koh kasa Yasir yayi da murya kai Dan rainin wayau ba inda zani ABK yace haba abokina karka min haka mana Dan Allah pls help me kaga in bamuje ba wlh bazata ji dadi ba" tsaki Yasir yaja muje maye karka cinyeni a gobe ma rana ce sai dai ka nemi wani ya rakoka wajan jaririyar nan,baby Muje koh Dan duk maganar da sukayi bataji komai ba gaba tashige sukuma suna binta a bayan har suka karasa palon baki gaskiya tamusu tarba ta musan man Dan ga kayan ciye ciye nan kala kala sai da tagama hada musu komai sanan tace ina zuwa taiciki abinta da Yasir kaman bazai ciba aman da yafara sai da yakusan kau da bin da ta hada musu
Ya kalli ABK wanan da ga gani ba ita tayi ba "wata uwar harara ABK yayi mishi yace aman ka lau da komai bari kaji wanan da kake rainawa ba abin da bata iya ba sanan...sallamar tace yasa ABK shiru Yasir ba yabo ba falasa yace godiya meke sanan yacero bandinr din yan 200 yata yace wa ABK in kagama kasame ni awaje bai jira godiyar da take mishi ba yayi gaba
Muje next page
Yar mutan KD
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_BUZUWA_*
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_STORY & WRITTEN_*
*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH_*
*_Editing_*
*_by_*
*_SISIN MAMA_*
*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
```Wanan page din sadaukar wane ga dauka,cin masoya book din nan ```
🅿3⃣
Yasir bai,fi 7mint ba da fitowa yafara kiran ABK amman yaki dagawa
a dan fusace ya kara kiran shi a ransa yana wannan shine kiran,karshe In kaki fitowa sai dai kazo kaga bananan
yanayi yana kara wayar a kunne ringing biyu ABK
ya daga Yasir bai jira daga gareshi ba yafara fada
"dalla malam ka fitoh in ba haka ba wlh inyi wucewa ta kazo Kabar mutum atiti kai gaka dadi soyayya wlh in baka fitoh ba sai dai kazo kaga bana nan" bai jira tajin bakin da ABK zai fada ba ya yakashe wayar yana harararta saikace wayar ce ABK
2 minutes ba ayiba sai ga ABK ya fitoh yana wani shu'umin murmushi wata uwar harara Yasir ya ruga mishi "saboda kai dan iskane kashige kayi zaman ka lokacin da na fitoh nai mata sallama ai kaima sai ka biyo bayana amman dayake kai dan rainin hankaline kabar ni a waje kowa yana wucewa yana kallo na" ya karasa maganar yana kokarin bude mota murmushi ABK yayi yace abokina wlh bazaka taba gane menene so ba sai rananr daya rikeka barin irinku saban shiga baya muku da kyau bazan Yasir yayi dan shi wanan maganar bata mishi rai ma takeyi
"kaga Malam ya isheni haka haba dan Allah wai kai dan Allah baka gajiya da maganar soyayya ce a rayuwar ka wanan jaririyar naga tanaso ta zautar da kai wlh dubeta fa amman a gabana take cema my love ba kunya
Ko kadan a cikin kwayar idonta" murmushi ABK yasaki "kadan ma kaji ai sunana a wajan ta yafi kalla goma bakasan ma wani abuba wlh In nazo wajan,ta tanamin shagwabar nan tata har rasa inda zan tsoma raina nake yana wani dafe saitin zuciyar shi tare da wani lumshe ido
wani wawan tsaki Yasir yasaki "kaga malam in zaka tada mota mutafi ka tada in kuma zaka cigaba da wanan shirman naka bismillah ABK motar ya tada sai da suka hau kan titi sosai sanan yasaki sautin wakar Umar m Sharif ta Bilkisu duk wajan da za a kira bilkisu sai yace hasina abin ya gama zuwa ma Yasir wuya yace "Abubakar me zai hana ka hada kayan,ka ka koma gidan su hasinan nanne gaskiya ka dameni kuma kacika min kune wlh
Kai kawai ABK ya girgiza abokina bazaka taba ganewa ba a dai dai nan suka kawo bakin get din gidan su Yasir horn ABK yayi get man ya bude suna saka hancin motar su
Yusrah su hango tsaye da wani block beauty gays a tsaye Yasir jiyayi kamar an buga mishi guduma a zuciyar har wani daci-daci yakeji saboda tsabagen bacin rai ABK yaga yanayin da yakoma lokaci daya dafashi yayi ABK yace lafiya kuwa abokina? gaba daga hankalin Yasir baya wajan ya kefe inda Yusrah da wanan saurayin suke da ido
Lafiya kuwa abokina ABK yakara fada lafiya mana Yasir yace mekaga nine naga yanayin ka duk ya chanja ne lokacin daya uhmm Yasir yace duba wacan yarinyar tana kwaso mana tar kacan samari gida dube ta sai wani murmushi take meshi bari kaga naje na koreshi yana kokarin bude koh fa da sauri ABK ya rukoshi haba abokina wanan ba girman ka bane sanan ba taifin,shi bane
Yasir yace ok laifinane kenan koh?a a ABK yace
nama gane laifin wacen kodaddiyar ce nan ma ABK a a yace da sauri Yasir yajiyo wai mekake nufine Abubakar nifa nakasa gane ina kasa gaba ma gaba daya aman ka barni da waccan kodadiyar zanyi maganin ta akan yan jaye jaye da take ma mutane har gida
ABK yace look Yasir wai dan kaganta da wani meye naka a ciki kai kace bakasan ta toh ko me zatayi basai ka zuba ido ba, in zuba ido fa kace wataran sokake zuciyata tatarwatse kamar ya?
ABK ya tambaye shi da sauri Yasir yadago badai maganar ta fitoh fili ba? yake tambayer kanshi.
Dan jin amsar da Yasir zai ba Abubakar muje a next page
By yar mutan KD
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_BUZUWA_*
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_STORY & WRITTEN_*
*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH KAINUWA_*
*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*SIGOGIN ISTIGHFARI KALA TAKWAS NE.*
*Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yace:*
*Na rantse da wanda raina Ya ke hannunSa, Allah! Ina neman gafararSa, kuma ina tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau saba'in.*
*Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce:*
*Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare Shi sau dari.*
*SIGA TA FARKO*
*Shugaban Istighfar gaba daya shine:*
"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺭﺑﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺧﻠﻘﺘﻨﻲ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪﻙ ﻭﻭﻋﺪﻙ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺻﻨﻌﺖ ﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﻨﻌﻤﺘﻚ ﻋﻠﻲ ﻭﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﺬﻧﺒﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ".
*Allahumma anta rabbee la ilaha illa ant, khalaqtanee wa-ana 'abduk,wa-ana 'ala 'ahdika wawa'adika mas-tata'ata, a'uzu bika min sharri ma sana'atu, abuu-u laka bini imatika alai, wa abuu u bizanbi, faghfir li fa-innahu la yaghfiruz-zunuba illa anta.*
*Manzon Allah (SAW) ya sunnanta mana karanta wannan istighfari sau daya, safe da kuma yamma.*
*Sannan kuma yace:*
*Duk wanda ya karanta shi da safe yana mai imani dashi, idan ya mutu kafin yamma, zai shiga aljanna. Kuma idan ka karantata da yamma kana mai imani da hakan, idan ka mutu kafin safiya zaka shiga aljanna in sha Allah.*
@Sahihul Jami'i.
*SIGA TA BIYU*
ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ.
*ASTAGH FIRULLAH*
*SIGA TA UKKU*
3-ﺭﺑﻲ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ.
*RABBI GHFIRLI*
*SIGA TA HUDU*
4-ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ.
*ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI FAGHFIRLI FA INNAHU LAA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA.*
*SIGA TA BIYAR.*
5-ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ،ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ.
*RABBI GHFIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUL GHAFUR.*
*SIGA TA SHIDA*
6-ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ ، ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ.
*RABBIGH FIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM*.
*SIGA TA BAKWAI*
7-ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻇﻠﻤﺎ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻭﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻣﻐﻔﺮﺓ ﻣﻦ ﻋﻨﺪﻙ، ﻭﺍﺭﺣﻤﻨﻲ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ.
*ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI ZULMAN KATHIRAN WALA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLALLAH, FAGHFIRLI MAGHFIRANTAN MIN INDIKA, WARAHAMNI INNAKA ANTAL GHAFURUR RAHEEM.*
*SIGA TA TAKWAS*
8- ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﻫﻮ ﺍﻟﺤﻲ ﺍﻟﻘﻴﻮﻡ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻪ
*Astaghfirul lahal lazi la ilaha illa huwal hayyul-qayyum wa atubu I lair.*
```WANAN PAGE DIN NAKUNE YAN BUZUWA FANS GASKIYA INAJIN DADIN YANDA KUKE NUNA KU LAWAR KU GA BOOK DIN NAN ALLAH YABAR ZUMUNCI COMMENT DIN KU NA KARAMIN KARFIN GUIWA SOSAI ANA TARE```
🅿4⃣
Kamar ya zuciyar ka zata tarwatse?
ABK ya jefa mishi tambaya
"don ka ganta da wani ? fuska Yasir ya daure "meya shafeni don na ganta da wani"
ita dince in nagan,ta gaban nawa yake faduwa"
kallon shi ABK yayi yace kamar ya gaban ka yake faduwa?
harara Yasir ya wurga mishi
"ban saniba yaba shi amsa a dakile
kaga malam bazan tsaya kanamin wanan tambayoyin naka kamar dan jarida ba kaga tafiya tah ya bude motar yafice warshi
ABK yadan daga murya yanda zai,jishi "kasani aman nan gaba kai kuka da kanka bani ba saboda gaf kake da kataf,ka kuskure"
ABK baijira jin ta bakin yasir ba yaja motar yayi gaba saboda daman zai je anguwa wajan abokin,sane
Yasir yana zuwa dai dai inda Yusrah take tsaye da saurayin ta samun kanshi yayi da tsayawa kamar an kafeshi
wani kayatacan murmushi take sakin ma saurayin nata
tagan shi tai kamar Allah baiyi tsayiwar,shiba magana takeyi kamar ana busa sarewa muyarta mai dadin saurare juyowar da saurayin zaiyi karaf suka hada ido da yasir
Yasir kara daure fuska yayi tamau kamar an aiko mishi da sakon mutuwa
da dan saurin shi saurayin yakaraso wajan Yasir
yamika ma yasir hannu kallon hannu yasir yayi yaja wani uban tsaki saikace zai tsinke harshan shi sanan ya wurga ma Yusrah uwar harara tare da saurayin yayi gaba abin shi
har cikin ran Yusrah taji ba dadi abin da Yasir yama saurayin ta inda sabo itah ta saba da halayyarshi
kasa sowa yayi wajan ta tunka,fin yace wani abu tariga,shi
"Abba's Dan Allah kayi hakuri wlh ko muma haka muke fama dashi bayi da kirki"
"bakomai Yusrah amman abin yaban mamaki irin kallon da yakemin cike da tsana da irin harara da yake miki"
Uhmm haka halaryar shitake sam wani lokacin bashi da kirki
daina cewa haka in zaki lura ranshi kamar a bace yake kinga yanzun ya shigo
"sai dai amsa sallama,tace da baiyi ba banji dadi hakaba ko kadan"
sorry Abba's Dan Allah karkasama kanka damuwa mana pls kayi hakuri"
bakomai Yusrah komai ya wace nima guduwa zanyi sai Allah ya kaimu gobe tunda rowar kanki kikemin a sati kice so biyu kawai zan ganki ya kamata a Dan karamin kwana ki yafada da sanyin murya irin a tausaya mishi din nan
yar dariya tayi mai kara mata kyau zan duba nagani aman bayan zunba"
bakomai gimbiya inanan inajiran ki sallama sukayi tawuce ciki shikuma ya shiga motar shi yabar gidan
Sauran kanda yakara sa shiga
dakin shi yaji ana kiran,shi yaya Yasir !yaya Yasir!! ko bai jiyoba yasan muryar waye tsayawa yayi dan yasan ba karamin aikin,ta bane tace zata bishi cikin dakin yana ganinta a palon yayi kamar bai ganta yawuce sai kace Mayya sai da tabiyoni
kafin tai magana yafara magana fuska a daure "lafiya MARYAM? kike ta faman kirana"
muryar ta a mutukar raunane tace lafiya lau ya Yasir tin dazun nazo akace ba kanan shine yanzun da naganka kuma naga baka ganni,ba shine na zo in gaishe ka
Uhmm nagode yayi shigewar shi daki tare da banko kofar saikace zai karyata da sauri MARYAM tamatsa zuciyar ta na bugawa
mommy data fitoh daga cikin tace lafiya MARYAM wayake buga kofa haka?
sai da ta sauke a jiyar zuciya saboda ta tsorata sosai sanan tace yaya Yasir ne
Mujame A next page
By yar mutan KD
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_BUZUWA_*
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
*_STORY & WRITTEN_*
*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH KAINUWA_*
*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
🅿5⃣
Girgiza kai Mummy tayi ta wuce ɗakinta itama MARYAM barin wajen tayi ta koma falo zuciyarta cike da tunani kala-kala saboda ita kaɗai tasan irin azabtuwar da zuciyarta ta keyi game da Yasir "wallahi wallahi Yasir ƙarya ka keyi sai ka aure ni kuma sai kaso ni fiye da san da nake maka"
( niko nace anya kuwa MARYAM)
Ɗaukar jakarta da mayafinta tayi tayi gaba dan bata ga anfanin