gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FARASHIN MUTUNCINA Gwagwarmayar Mutunci By Mom Islam Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com 

*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋

Mom Islam

Page 1-2


Cikin Nutsuwa ta iso cikin gidan banda kuka babu abinda take, hawaye sai sintiri yake a saman kumatunta, hatta gaban hijab ɗin school ɗinta duk ya ɓaci da jirwayen ruwan hawaye,

Mama na daga ɗaki ta jiyo sautin kukanta ta fito da sauri tana cewa "Batool mai ya faru gayamin keda waye?"

Mama ta koma kan baba dake zaune a saman kujera ƴar tsugunno hannunsa riƙe da shaving stick yana aske gashin gemunsa ko kallon su beyi ba,

Sai da ta sake magana ne, baban yace "Haba Atine me kikeso ince miki, kinga bawai na zauna a gida dan ki takuramin da ƙananun surutanki bane"

Baba ya ƙare maganar yana tattara kayayyakin da yake amfani dasu ya miƙe tsaye yabar musu gurin,

Mama ta ƙaraso ta dafa kafaɗar Batool, sai kuma ta riƙe hannunta suka koma cikin ɗaki,

"Zauna Batool ki gayamin meke faruwa?"

Batool na share hawaye tace "Mama malaminmu ne ya koreni a aji a lokacin da zan zana jarabawa, har takardar an miƙo min, wata Malama ta shigo tace "ban biya kudi ba, kuma kinsani wannan jarabawar itace ta fita daga makaranta.."

Mama tayi tagumi, cikin yanayi na damuwa, kafin tace "Allah na gode maka, Allah ka dubemu"

Batool muna cikin wani hali, baba ya ɗago idanunsa yana kallon su, kafin ya miƙe tsaye, tare da shigewa cikin ɗaki, kayan jikinsa ya sauya kana ya fice bai bi ta kansu ba,

Mama tace "ki koma kice musu idan Maryam ta dawo daga talla za'a kawo musu"

Batool tace "Uhm mama yaushe zasu amince, makarantar boko ba kamar ta islamiya bace da za'ayiwa mutum uzuri"

Mama tace "hakane, yanzu dai tashi kije kice idan akwai dubu ɗaya a gurinta ta baki sai ki kai musu"

Batool ta miƙe da sauri jikinta na rawa ta nufi tashar mota wacce ake lodin mutane masu yin tafiye-tafiye,

Da sauri ta isa tashar motar, kafin takai ga tsallake titi ta hango mahaifinta a zaune gurin mai gashin tsire, ƙarasawa tayi da sauri, ta durƙusa a gabansa kasancewar shi kaɗai ne, tace "baba Dan Allah ka taimaka ka biya min kuɗin jarabawar fita baba daga wannan team ɗin idan ban zana ba sai wata shekarar"

"Ke dalla tashi ki bani guri, kin koyi munafurci irin na mahaifiyarki da sa ido, to idanma wannan tsiren da kikaga ina cine, ba kuɗi na biya ba, kawai ya bani ne dan na haɗa masa wuta"

Batool ta sunkuyar da kanta tana a durƙushe hawaye na zuba, ta miƙe tana jan ƙafafu kamar wacce ƙawai ya fashewa,

Baba yayi mata ƙarya bayan yanzu yazo gurin,

Ta dinga maimaita maganar baban nata har ta tsallaka titi,

Da sauri ta dinga tafiya gudun kar a kulle karɓar kuɗin jarabawar yasa ta ƙarasa gurin yayar Tata Maryam da gudu,

Da isarta tace "anty Maryam Mama ce ta aikoni gurinki"

Maryam tace "lafiya dai Batool idanunki duk sun kumbura?"

Batool tayi mata bayanin kudin makaranta na jarabawar da zata zana,

Cikin yanayi na damuwa Maryam tace "wlhi tunda nazo roba ɗaya aka siya bai ma bani kuɗin ba, gashi ko sisi babu a gurina, amma tashi muje gurin mai shagon can idan zai ranta min kafin in yi ciniki"

Suna riƙe da hannun juna suka je gurin mai shagon, har yana tsokanar Maryam, tunda tace tazo ne akan ya taimaka mata da bashin dubu ɗaya idan tayi ciniki zata bashi, ya fara masifa shi ina yaga wata dubu ɗaya ashe kasada da ganganci ne yasa kika kwaso ƙafa kika tahomin ki koma idan kikai cinikin sai ki bata amma nikam a'a..!

Mom Islam
*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋

Mom Islam

Page 3-4

Muryar Maryam na cike da damuwa tace "Batool ki koma makarantar ki basu haƙuri ni da kaina zan kawo kuɗin idan nayi ciniki"

Batool bata yiwa yayar tata musu ba, ta kama hanyar komawa makaranta tana tafe tana adu'ar Allah yasa ba'a gama raba papper ba, sai dai da isarta makarantar taga har yara sun fito wasu kuma suna buga ƙwallo da alama dai an gama zama jarabawar,

Raɓewa tayi ta fara kuka dan ta rasa ma idan taje gurin malamin nasu me zata ce masa,

Wata Malama ta fito, saboda ta hango Batool ta iso gurin ta, cike da nuna kulawa tace "mai akayi miki kike kuka haka?"

Batool tace "ban zana jarabawa bane saboda kuɗin makaranta manana mamana bata dashi sai yayata tayi talla ta samo tukunna"

Malamar ta kamo hannun Batool suka shiga office, bayan sun gaisa da malaman da suke zaune maza da mata, ta tambayi waye malamin su Batool, malamin ya amsa, malamar tace "ka taimaka ka bata papper itama ta zana jarabawar kar ya wuceta"

Cike da ɓacin rai malamin yace "sai dai ya wuce ta wlhi dan nikam na riga na gama babu ma ragowar wata papper a gurina,

Ragowar malam da suke zaune babu wanda yasa baki, haka dai Batool ta dawo gida tana kuka,

Mama na ganinta ta ajiye soson wanke-wanke ta taho gurin ta kana tace "Batool ya dai ba'a samu kudin a gurin Maryam bane?"

Batool tace "batayi ciniki ba kuma malamin ya hanani wata Malama zata biyamin yace wai ya ƙare"

Mama ta nemi guri saman kujera ƴar tsuguno ta zauna tare dayin tagumi,

Maryam ce ta shigo tana rusa ihu kamar wacce tasha duka, ta dure kular abincin da bokitin da ta tara kwanuka tana ci gaba da ihu,

Mama ta dubeta kafin tace "lafiya Maryam?"

Mama wasu mutane ne suka sani na sa musu abinci har roba takwas dama kinsan yau bamu dafa da yawa ba, sukace in jurasu, naje ajiye robar da wani mutumi yaci ina dawowa naga sun ajiyemin robobin sun wuce kuma matafiya ne"

Mama ta fara salati tana sanar da Ubangiji tare da cewa "wannan jarabawa Allah yasa munada rabon cinyeta"

Mama ta dafa kafaɗar Maryam tace "kiyi shiru Allah ya musanya mana da Alkairi, damuwar ɗaya ce bai wuce mai shinkafa da mai mangyaɗa da zasuyi min sallama da sanyin safiya ba, amma babu komai ganin goben yafi wahala"

Dukkansu suka shige ɗaki, Batool ta cire uniform ta sauya kaya zuwa na gida, Maryam kuma ta fito ta ɗauki buta tayi alwalah haka ma Batool ɗin alwala tayi suka kabbara sallahar la'asar,

Mama ma na gama wanke kwanuka tayi alwalah tazo ta kabbara sallah bayan sun idar ta tambayi Maryam nawa ne a gurin ta?

Tace "ɗari biyar ne"

Mama tace kije ki auno shinkafa gwangwani biyu sai mu dafa inada wake gwangwani ɗaya, tunda akwai ragowar miya sai muci da ita"

Batool tace zata rakata, suka tafi tare,

Basu jima ba sai gasu sun dawo a tare, suka tsince shinkafar Maryam ta juye a kwano suka koma ɗaki,

Batool tace "anty Maryam baba yana bani mamaki, idan ya fita waje har tsire da shayi yake sha, amma idan mama ta tambayeshi ko ɗari biyu ne sai yace bashi da ita"

Maryam tace "hmm Batool kenan, yanzu a cikinmu ba fata ba, da wata zata kwanta rashin lafiya sai dai ta mutu wallhi baba ko magani bazai siya mana ba, kumafa yana dashi sai dai yaci daɗinsa a waje idan ya shigo ya balbale mama da faɗa..!

Mom Islam
*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋

Mom Islam

Page 5-6

Washe gari bayan sunyi sallahar Asbha, babu wacce ta koma barci sakamakon alhinin abinda zasu saka a bakin salati da sukeyi, suna zazzaune a parlorn mama saman tabarma, Baba ya fito daga uwar ɗaki, Maryam da Batool suka gaishe shi, bayan ya amsa yace "ai gari be gama wayewa ba kowacce ta tashi ta tafi ɗaki, sun wani zazzauna sai kace masu zaman makoki"

Mama dai babu abinda tace ta sani sarai neman fitina yake yi, suna fita ya zauna kusa da Mama kafin yace "Haba matar arziƙi, tun jiya nake kawo hannu ki bani ƴar zumarki in ɗan lasa amma kin hanani"

Mama tace "banyi tunanin fitowar wannan kalmar daga bakinka ba, a halin yanzu, saboda shawarar inda zamu samu abinda zamu saka a bakin salati mukeyi"

Baba yace "Allah zai kawo ƴar buga bugar da kika saba yi ita zakiyi mana mu samu mu ɗumama cikinmu"

Murmishin yaƙe mama tayi, kana tace "to malam kayi haƙuri mu barwa dare kaga yarannan idonsu biyu"

"Nifa babu abinda zaki gayamin dan haka muje cikin ɗaki kawai"

Mama ta miƙe kasancewarta mai biyayya duk wulaƙanci da tauyeta da baba yake yi tana iya bakin ƙoƙarinta gurin ganin bata ɗaga masa murya ba saboda yaranta guda biyu,

Dan haka ta miƙe tabishi zuwa cikin ɗakin,

Zama tayi a bakin gadonta mai rumfa, idanunta sun ciko da ruwan hawaye, sai dai ta taresu da taimakon Allah babu wanda zai gane kukan zuci takeyi,

Baba yakai hannunsa kan zaninta ya buɗe tare da cewa "Sanyi akeyi matso inji ɗumin jikinki"

Mama ta matsa tare da cire kayan jikinta tunda dai ta gane abinda yake nufi, bai kulle ƙofar parlo ba, kuma ya hana mama taje ta kulle a cewarsa wai a matse yake,

Yasa mama ta kwanta idanunta na kallon sama ya haye kanta, wani irin ci ya fara yiwa HQ ɗinta yana yi yana zunkuɗa tare da sake zarewa yana saka sandarsa, ganin lokaci yana tafiya yasa mama cewa "malam yarannan fa zasu iya shigowa dan Allah kayi haƙuri kaga ƙofarnan a buɗe take,

"Kinga gyara min bata shiga sosai ana ga yaƙi kina ga ƙura dan Allah ki tsaya in ɗan samu Nutsuwa haba kekuwa"

Baba ya fada yana sake matse ƙafafun mama tare da danna penis ɗinsa yana sauke numfashi,
Zuwa yanzu babu abinda mama takeji sai azabar zafi, saboda ba wata ni'ima ce da ita ba, mema taci da har zata samu ni'imar,
Haka dai ta dinga daurewa tana cije laɓɓanta har baba ya gama biyan buƙatarsa ya sauka, wandonsa yasa ya fito tsakar gida kana ya ɗauki buta, Batool da Maryam suna zaune ya wucesu, da kallo suka bishi tare da tashi suka koma ɗakinsu,
Bayan ya fito daga banɗakin mama ta fito itama ta buɗe tukunyar dake kan murhu, Allah yasa akwai ruwan zafi a ciki, ta ɗiba ta sirka kana ta wuce banɗaki, sauri take kar baba ya fice bata roƙeshi abinda zata karya ba, sai dai tana fitowa ta samu ya fice,
Abinda bata sani ba, yana gama sa kaya ya fice da uban sauri kamar zai tashi sama, turuss Mama ta tsaya a tsakar gida hannunta riƙe da buta, ranta ya ɓaci sosai, duk da wannan abun da yayi mata ba sabo bane a gurinta, inda sabo ta saba,
Ɗaki ta wuce bayan ta ajiye butar, kana sa kaya, sannan ta fara ƙwalawa Maryam kira, suka taho tare da Batool.
Mama tace "babu abinda zamu ci, amma ku jirani yanzu zan dawo"
Batool tace "mama zan biki.."
Mama tace "babu inda zaki bini amma zomuje zuwan naki yanada muhimmanci"
Maryam tace "mama wane irin muhimmanci kuma?"

Idan mukaje muka dawo in Allah yasa an dace zakiji labari,
Tun a hanya Batool take tambayar mama ina zasuje mama tayi mata banza,
Wata hanya sukabi wacce take nesa da anguwarsu, a bakin wani katafaren ƙerarren gida suka tsaya, Mama ta fara ƙwanƙwasa gidan, mai gadi ya fito ya dubesu kafin yace "daga ina kuke?"
Mama tace "gurin Hajiya Suhaima muka zo dan Allah idan tana ciki ka barmu mu shiga"
Mai gadi yace, "yana daga cikin dokar aikina inje in isar da saƙon cewa kinzo gurinta idan har ta amince sai ki shiga, idan kuma bata amince ba sai ki koma"
Mama da Batool suna tsaye a waje mai gadi ya dawo yace su shiga,
Mama tayi masa godiya kana suka kutsa kai ciki,
Katafaren gida ne babba mai filin tsakar gida, daga gefe kuma bishiyoyi ne masu kyau wanda suka sake ƙawata gidan, akwai guraren hutawa a can gefe harda su lilo da sauransu,
Tunda Batool take bata taɓa shiga gidan ba, dan haka ko ina ya zame mata abin kallo sai dai ta gansa daga waje idan tazo wucewa,
Da sallama mama da Batool suka shiga parlon kana suka zauna a saman carpet,
Wani matashin saurayi ne zaune a saman couch hannunsa riƙe da system idanunsa na sanye cikin farin gilashi, ganin su mama yasa shi miƙewa bayan yace wa mama ina kwana, Hajiya Suhaima ce ta fito tana sanye da wani fitinannen leshi mai tsadar gaske, wuyanta wata danƙareriyar sarƙa ce mai kyau da ɗankunne, kana ta ɗanyi murmishi tare da neman guri ta zauna kafin tace "barkanku da zuwa da fatan kunzo lafiya"
Mama tace "lafiya Lau Hajiya dama neman alfarma nazo dan Allah"
Hajiya Suhaima tace "lahh babu damuwa tashi ki zauna sai muyi magana"
Mama ta koma saman couch ɗin ta zauna kafin tace "dan Allah ina roƙon alfarmar Batool ta dinga zuwa tana yi miki wanke-wanke da shara da sauran abinda kike da buƙata saboda wlhi abincin da zamuci ma garararmu yake yi"
Hajiya Suhaima tace "aiko kinzo a daidai dan ina shirin fita neman ƴar aiki ne saboda ƴar aikina tayi aure"
Mama tace "alhmdulilah"
Hajiya Suhaima tace "amma albashin da nake biya a wata dubu talatine sannan dole sai dai ta dinga kwana yanzu dai zan baki dubu goma idan naga tana aiki inda ya kamata sai in biyata dubu talatin ɗin"
Mama tace "babu damuwa Nagode Allah ya saka da Alkairi hajiya"
Tashi Hajiya Suhaima tayi ta shiga store ta ɗibo taliya guda biyar ta ɗibo macaroni guda biyar indomie biyar da couscous biyar sai mangyaɗa ta ciko mata babbar gora na swan da kuma manja, kana ta ɗora da ledar maggi satar biyu da dubu goma ta saka a bakko bag ta kawo mata,
Ta ajiye a gaban Mama,
Mama ta buɗe bakko bag ɗin tare da saukowa kasa kamar zata fashe da kuka, tana kallon kayan abincin dake ciki tana jadadda godiyarta a gurin Hajiya Suhaima,
"Wannan ba komai bane karki damu, sai dai ina yawan yin tafiya zuwa Dubai London da sauransu, nakanyi two weeks zuwa one week"
Mama tace babu damuwa mun gode Hajiya,
Hajiya Suhaima tace "gobe sai ta fara zuwa yau zabi anguwa"
Mama ta miƙe tare da miƙawa Batool kayan suka yiwa Hajiyar sallama kana suka fice..!

Mom Islam 🍷
*FARASHIN MUTUNCINA*
(Romantic story)
💋💋💋💋

Mom Islam

Page 7-8

A hanyarsu ta komawa gida Batool take tambayar mama,

"Baba bazai yi miki faɗa ba mama?"

Mama tace "idan ma yayi faɗan zai yi ya gama, ai ba wata hanyar banzan muka biba, tunda ya kasa sauke nauyin da Ubangiji ya ɗora masa ai gara mu fara fafutukar inda zamu tsira da mutuncinmu ta hanyar halal ba ta haramun ba"

Lokacin da suka iso gida, bakko bag ɗin yana kan Batool, Maryam na ganinsu ta taso daƙyar take tafiya saboda yunwa da taci ƙarfinta yasa ko magana ma daƙyar take iya yi musu, a tsakar gidan ta durƙusa tare da cewa "mama abin arziƙi kika samo?"

Mama ta dubeta fuskarta da murmishi kana tace "kinga duk ba wannan ba haɗa wuta na sanki bakya jurar yunwa, sannan kinada ulcer dan haka ko taliya ko couscous a ɗora dan shine mai sauƙi"

Maryam tace "mama bazan iya miƙewa ba bayanta ciwo wlhi ga ƙirjina kamar zai ɓalle"

Batool ta isa gaban murhun ta haɗa wutar gawayi da ragowar gawayin da mana take dashi, kana suka haɗa sanwar taliya suka koma ɗaki,

Mama ta tura kayan ƙarƙashin gado saboda gudun kar baba ya gani,

Can an jima jollof ɗin Taliya ta gamu, Mama ta fita ta zubawa Batool da Maryam kana ta zuba nata sannan suka fara ci a parlor,

Sallamar baba da yayi ne yasa ko wanne jin wani iri, koda ya iso gindin murhun ya buɗe tukunyar, kwano ya ɗauka a kwando ya zuba shima ya kutsa kai cikin ɗakin,

Mama bata ce dashi komai ba, ta bishi da idanu, har yana cewa Batool ta ɗibo masa ruwa,

Bayan ta ɗibo ta ajiye a gabansa kana ta koma kan abincinta, bayan sun gama ci Batool ta tattara ta kai gurin wanke-wanke suka fice daga ɗakin,

"Daga ina muka samu wannan abun arziƙin ne?"

Baba ya tambayi mama ba tare da ya kira sunanta ba,

Mama tace "zuwa nayi na kai Batool gidan Alhji na Allah mai kuɗi, akan ta dinga zuwa aiki muna rage na cefane"

Baba yace "shine suka baki taliya?"

Mama ta bashi amsa da cewa "eh guda biyu ce"

Baba yace "Allah ya biya su, yaushe Batool ɗin zata fara zuwa?"

Mama tace "gobe"

Haka sai yayita jan mama da hira har ta gaji da surutansa,

Batool yarinya ce, dan bazata wuce shekaru 15yrs ba, ko 14yrs Maryam kuma ta girme mata sai dai tanada yawan laulayin rashin lafiya ne zatayi 22yrs amma idan ka ganta bazakce zatayi waɗannan shekarun ba, duba da yanda ta tsamure sosai, kasancewar ba wani kulawa take samu ba,
Wunin ranar dai sun wuni babu fargabar inda zasu sami abinci, sai dai baba da yake ta yi mata tambayoyi, wannan dubu goma na gurin mama a ciki befi ɗari biyu taɓa ba, tanason idan Allah ya kai mu gobe taje makarantar su Batool akan maganar zana jarabawar da zasuyi, koma nawa ne ta gwammace ta biya hankalinta ya kwanta,
Washe gari, tun bayan da sukayi sallahar Asbha mama tace Batool kar ta koma barci ta haɗa wuta tasa ruwan wanka da abin karyawa idan gari yai haske su kama hanyar zuwa makaranta,
Baba na zaune a ɗaki kasancewar ya dawo daga masallaci yana jin maganar da mama takeyi,
Kai tsaye ya fito ya wuce ta gabanta, ba tare da yace da ita komai ba, ashe ya gama shirya kayansa a cikin bakko bag ya wurga ya baya window ɗin cikin ɗaki, ya fice, dan ya kwashe wannan dubu goman duka, ya kuma yi rubutu ya ajiye mata a saman wata tsohuwar loka, kasancewar yayi makarantar boko primary,
Mama bata kawo komai a kanta ba, dan haka suka ci gaba da shirinsu, Batool ta shiga wanka ta fito, mama itama ta shiga ta fito, sannan ta shiga ɗakinsu Maryam ta fara kiran sunanta.. ta ƙudundune da bargo tace "bazata iya wanka yanzu ba,
Mama bata takura mata ba ta wuce ɗaki ta shafa mai, lokacin Batool ta gama shafa mai ta saka uniform ta fito tsakar gida duba abinci,
Bayan mama ta gama shirya wa cikin atamfarta ta ɗan fara koɗewa kasancewar bata samun sabbin kaya sau tari na sai dai ƴan uwa da abokan arziki su duba halin da take ciki su taimaka mata, da haka har ta samu zanin fita anguwa,
Bayan Mama ta gama shirya wa ta ɗaga ƙasan katifa ta fara duba tsumman da ta ajiye dubu goman nan bata gani ba, tayi neman duniya har ranta ya ɓaci bata gani ba,
Batool ta shigo da sauri tana cewa Mama ta sauke abincin idanunta ya sauka akan wata farar takarda dake ajiye a saman loka,
Hannu ta miƙa ta ɗauka kana ta fara karantawa a fili,
"Maman Maryam kiyi hakuri bawai na ɗaukar miki kuɗi da niyyar yin sata bane, kawai dai na ɗauka ne dan naga dacewar yin hakan, saboda inason tafiya Kudu neman kuɗi zanbi wata babbar mota, da naga na samu dama shiyasa kawai na ɗauki kuɗin, kuma bazan taɓa mantawa daku ba, baki da waya amma zan yiwa mai shagon dake kusa damu magana akan ya dinga baki duk wani aika da nay ki kulamin da yarana"
Wani irin kuka mama ta fashe dashi mai cike da takaici,
Tabbas gaskiya ya faɗa ba wani abu ba, mai yasa bashi da tausayi ne, mai yasa baya ƙaunar ya gansu suna farin ciki, mai yasa ya zaɓi ya gansu cikin wani hali, idan ita bai tausaya mata ba su ya kamata ya tausayawa yaransa,
Da kin sautin kukanta yasa Maryam dake kwance tasowa ta fito, cikin yanayi na damuwa take tambayar Batool da itama kukan take yi "mai ya faru?"
Batool tace "komai ya faru anty Maryam"
Ta mayar mata da abinda mahaifinsu yayi da maganar kuɗin makaranta da suke son kaiwa gashi ya kwashe kuɗin ko sisi be bar musu ba,
Maryam tace "mama kiyi hakuri Allahan da ya baki wannan shine zai baki wani insha Allah"
Har da Batool ɗin suka taru suna lallashin Mama, tayi shiru tare dayin tagumi, rabonta da kasancewa cikin farin ciki a wannan gidan har ta mance, kowacce rana da kalar jarabawar da take ɓullowa iko sai Allah itakam ta rasa abinyi ko zata gayawa iyayenta ne?
Kawar da tunanin tayi, tace "Batool tashi ki shirya zuwa gidan aiki dan rana ta fara yi idan kikaci abinci ko wuce"
Tashi tayi ta cire uniform ɗinta kana ta je ta ɗauko kwano ta ɗibi abincin kana ta fara ci, bayan ta gama cin abincin ta sanya hijab tace wa su mama itakam ta tafi, mama ta kirawo ta, bayan ta dawo mama tace "Batool ki riƙe gaskiya banda son zuciya sannan Banda ɗaukar abinda ba naki ba, kana ban da munafurci kinji?"
Amsa mata tayi da cewa "toh" kana ta kama hanyar tafiya gidan Hajiyar"
Tana tafe a hanya tana mamakin mugayen halaye irin na mahaifinta, da kuma haƙuri irin na mahaifiyarta, isowarta bakin get tana tsaye wata mota ta fito daga cikin gidan bayan an buɗe wa mamallakin motar get, idanu ya zubawa Batool kamar wanda bai taɓa ganin wani ɗan Adam ba, Alhji Bukar kenan mijin Hajiya Suhaima wacce Batool zata shiga fara aiki gurinta,
Kallo yake yi mata mai cike da ma'anoni wanda shi kaɗai yasan kallon ki na meye..!

Mom Islam 🍷
FARASHIN MUTUNCINA

(Romantic story)

💋💋💋💋

Mom Islam

Page 9-10

Ɗan kaucewa tayi gefe har sai da motar ta gama shigewa kana itama ta kutsa kai ciki ta shiga,

Sallama tayi tun kafin ta ƙarisa ƙofar parlon Hajiya Suhaima ta amsa dan ƙofar tana a buɗe ne ta jiyo sallamar Batool ɗin,

Ƙarasawa ciki tayi nan ma ta sake yin sallamar kana ta durƙusa ta gaishe da Hajiyar, bayan ta amsa tace "ya mamanki"

Batool ta amsa da cewa "lafiya Lau tana gaishe ki"

Hajiyar tace "Masha Allah ina amsawa"

Juyawa tayi ta kalli kyakkyawan saurayin dake kwance a saman 3sitter yana danne-danne a wayarsa, "Barka da safiya tace masa ba tare da ta kira sunansa ba dan bata san sunan nasa ba"

Bai ɗago ya kalleta ba, kuma bai amsa ba, Hajiya Suhaima ta miƙe tana murmishi, kafin tace "Son ƴar aiki na gaisheka"

Saurayin ya amsa a taƙaice kamar anyi masa dole,

"Tashi mu shiga ciki sai in nuna miki abinda zakiyi min"

Hajiya Suhaima tace "tana miƙewa ta fara tafiya"

Itama Batool ɗin miƙewa tayi kana tabi bayanta, kai tsaye bedroom ɗin Hajiya Suhaima suka wuce, tace mata,

"ta fara da wanke toilet sannan ta fito bedroom ta gyara mata gado tayi mopping sai ta dawo parlor sannan ta nuna mata kitchen da corridor zuwa parlor, ta nuna mata inda zata goge kujeru da sauransu,

Bayan Hajiya Suhaima ta gama nuna mata abubuwan da zatayi ta ɗauko Mayafi, dama tayi shirin fita,

Tacewa Batool zataje kasuwa yin cefane, ta gaggauta fara aikin kafin ta dawo sai su gyara kayan miyar da ta siyo,

Cikin ladabi tare da girmamawa Batool tace "insha Allah Hajiya"

Momy ta dubi matashin saurayin dake kwance tace "Farhan idan ƴar aikin ta gama idan akwai abinda kake buƙata ka gaya mata tayi maka"

"Okay Momy"

Farhan ɗin ya faɗa,

Farhan kyakkyawa ne, shi ba fari ba shi ba baƙi ba, sannan yanada kyawun fata uwa uba ya iya ɗaukar wanka, shi ɗin na musamman ne, sai dai miskilanci da jin kai da izza tayi masa yawa, baya son raini kana baya ƙaunar talaka, sannan baya ƙaunar ƙazanta,

Bayan tafiyar Hajiya Suhaima, Noor taci gaba da aiyukanta cikin sauri har ta kammala, ammafa ta gaji sosai, dan ba sabawa tayi ba, kuma aikin akwai gajiyarwa sosai,

Parlor ta dawo ta ɗan rakuɓe ta zauna saman carpet, Farhan ya dubeta kallo irin na wulaƙanci tare da tsantsar tsana, kana yace "ke dalla tashi a saman carpet ɗinnan karki shafawa mutane datti"

Jikinta a sanyaye ta miƙe tsaye tare da rungume hannayenta, tama rasa a inda zata zauna saboda jiran dawowar Hajiyar takeyi,

A hankali ta fara takawa zuwa waje cikin ɗan ɗaga murya Farhan yace "ƴar aiki...!!!"

Batool ta amsa da "na'am" cikin sanyin murya,

Shigowa tayi cikin parlorn bayan tayi sallama, ta durƙusa a gabansa, a ƙyamace yake kallonta yace "kije bedroom ɗina ki ɗauko under ɗina da ves da kuma hanky ki wanke min a washing machine, kuma karki samin datti and then kiyi sauri"

Cikin ladabi tare da girmamawa tace "insha Allah zan wanke, amma ban iya amfani da mashin ɗin wanki ba"

Farhan ya tashi zaune, bayan ya ajiye wayarsa a saman couch..!

Mom Islam
*FARASHIN MUTUNCINA*

(Romantic story)

💋💋💋💋

Mom Islam

Page 11-12

Cikin isa da gadara yace "ke Jahilar ina ce da har zan sakaki wanki kice min wai baki iya amfani da washing machine ba?"

Jikin Batool

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment